Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

labari na qirqireshi ne kuma ina rubutashi da nufin fadakarwa da kuma nishadantarwa dan haka Dan Allah mutanena a dan tsahirtamun kadan na idar da abunda nayi nufi ma'ana a dena cemun kaxa ya dace ko kuma be dace ace anyi kaxa ba saboda hakan yana dakushe karsashina kuma yana sacemun gwuiwa. Mu kula da wani abu guda daya a rayuwa, bafa duk abunda kakeso kake samu ba, kamar yadda ba duk abunda kakeso ne yake xama alkhairi ba, Hujjata anan itace fadar Allah (S W T) acikin Al qur'anil kareem inda yake cewa "Ya kusanta ko so abu ya xama sharrine gare ku, kuma ya kusanta kuqi abu ya xama alkhairi gare ku" a cikin wata ayar kuma yace "Kun kusanta ku qi abu Allah kuma ya sanya alkhairi me yawa cikinsa" (sadaqallahul azim) Kuma a duk sanda marubucin da yasan abunda yake ya xauna ya qirqiri lbr bawai kawai yayishi ne don nishadantarwa ba, a a dole akwai darasi aciki. Yanxu kamar HAJIA (ni kenan) inna tashi rubutu nakan dauki matsalar da nasan tana addabar Al umma inyi rubutu akai dan fadakarwa da nufin bada gudummawa wajen gyara wannan matsala. Amma fa ba fushi nayi ba dan anamun gyara ko nunamun hanyar da ya dace littafin yabi. No! Kakata ta bamu sirrin xaman duniya takan fada mana cewa inkanason cin ribar rayuwa karkai fushi,πŸ˜„ haka ma umma na harta koma ga Allah tana fada mana ba'a fushi da masoyi tattalinsa ake domin ya gama maka komi tunda ya soka (RIJF UMMA πŸ˜₯) Nagode sosai masoyana duk inda kuke ako ina kuke wanda Allah ya hadamu da wanda bamu hadu ba duk ina qaunarku fiye da yadda kuke qaunata, innace xan kawo sunanku sai muyi 1 wks bamuyi posting ba saina sunan masoya 😜 Sannan daga qarshe inason sanar muku cewa abunda yasa bana daily post saboda ina dogon feji kuma inada harkoki na cikin gida dana business kunsan da ruwan ciki akejan na rijiya.😊 Nagode sosai muna tare 🀝🏽

Godiya ta musamman ga

Ya RUQAYYAH (Haj Ruky)
ANTY SIS
MARYAM BAITA USMAN
ADDA SARATU (maman khairi)
MARYAM SANI
NAJA' ATU (yar malam)
DIYAR KATIBI
BAPPA JAMILA (maman muhibba)
SAPNA


Suna xuwa gida Baba ya kama hannun su ya kaisu har daki kamar yadda ya fito dasu daga kotu. Saddiq na dakin soro a kwance cikin qunar xuciya yaji shigowar mutane ya fito shima ya shige dakin Iya inda yaji motsi.



Ya tarar dasu kowa fuska jiqe da hawaye har dai Baba da yake namiji, ko basu fada ba yasan xaman kotu baiyi musu dadi ba kuma dama haka ya guda shiyasa ya qauracewa xuwan. Baba ya dubi Sakeena yace "Sakeenatu danme xaki amsa lefin da baki aikata ba? Dan me baki fadi gaskiyar abunda kika sani ba?"



Tayi shiru ba tare da tace komi ba. Iya ta share hawaye ta matsa gaban Sakeena tace "Sakeena ni uwarki ce, ki fadamun gaskiya kinji domin na farajin qanshin gaskiya a maganar Hajara da Deni tunda gashi sageeru yayi mana wayo ya gudu daga xuwa katsina taho da uwarsa yau sati guda babu duriyarsa, Katsina aiba Saudiya bace da xa ace antafi anshafe sati ba a dawo ba. Ki fada mana gaskiyar lamari kinji diyata"



Ta kuma yin shiru na tsawon 3 minutes, su kuma suna binta da ido. Ta dago ta sauke idonta kan Baba dan tana ganin shi kadai ne xai yarda da ita tunda Iya ma ta fara xarginta balle kuma Saddiq da take ganinsa baqiqqirin saboda jinin Hajjo ne. Cikin sanyin muryar kuka tace "Baba wallahil Azim ban taba zina ba, ni ba fasiqa bace, banyi fasiqanci tun ina qauye ina nemarwa kaina abinci ba? Banyi fasiqanci tun ina kwana da yunwa a gidan Deni ba? sai yanxu da aurena? Koda ace ansameni da laifin zina to wlh banyi ina cikin hayyacina ba" Baba ya jinjina kai cikin yadda da Sakeena ya tsuguna gabanta yace "Sakeenatu na yadda dake, kuma a ko ina xanyi shedarki akan hakan, domin nasan dake Mazinaciyace to da Deni ne xai fara samun wannan damar a kanki tunda kina sonsa fiye da komai kuma ya taba yi miki tayin zinar kika guje masa. Nasan bakisan nasan wannan ba ni da iyayenku mata kuma wannan shine dalilin da yasa nayi muku aure babu shiri dan gujewa fadawarku cikin halaka. Amma Sakeenatu ki daure ki fada mana abunda kika sani na tsakaninki da Sageeru dan Allah"



Ta share hawaye karo na barkatai tace "Lokacin da Hajjo ta koreni daga gidan Deni bata bani ko sisi ba domin tahowa Kano, dan haka koda naje tasha nasha wahalar tare motoci 4 ina roqonsu su kaini Kano in sun kawoni xaka basu kudinsu amma duk sukaqi har wani cewa yayimun daga ganina guduwa xanyi daga gida. A haka nasamu wata mata ta yaudareni tacemun Kano xata na shiga motar ta saida muka kwana muna tafiya sannan da safe nagane sace ni tayi, na fara ihun neman taimako amma babu wanda ya ganni sai dana fiddaran samun temakon sai naji direbanta yana cewa wani yana binsu har yana harbi, bansan kowaye ba saboda bana cikin hankalina lokacin. Ganin haka suka tunkudoni daga mota suka gudu. Iya abunda nasani kenan lokaci, sai bayan na farka daga bacci wani likitan ido ya nunamin Sageer a matsayin mijina, ni lokacin bansan kowa ba saboda bakomai a cikin kwakwalwata dan haka na yadda ya tafi dani gidansa muka fara rayuwa irinta miji da mata, ban tuna komi ba sai ranar da mukaje gaban likita yace inada ciki ranar na tuna komi. Amma kafin lokacin ina dan tuna rayuwata ta Baggadano har nake tambayar Sageer ina Nura qanina shine yacemun in ina sonsa kar inkuma tuna baya in xauna dashi baxai cuceni ba"



Iya ta dakko maganar Sageer inda yake cewa ya auri sakeena babu wanda ya sani a danginsa sai abokinsa ta hada da jawabin sakeena, ta furta "Innah lillahi wa'innah ilaihi raju'un. Shikenan yaro ya cucemu ya raina mana hankali ya batawa yarmu rayuwa ya rakota har gida ya zambacemu ya gudu. Ni Hafsatu naga ta kaina, ina xansa raina?"


Saddiq ma dai kalmar innalillahi yake maimaitawa, Baba ne kawai yayi juriya ya dake ya Kalli Sakeena yace "Ke diyatace sakeenatu har abada duk da ni talakane kuma bansan kowa ba amma baxan bari a xalunceki ba, xanyi duk yadda xanyi inbi miki haqqinki na xaluntarki da akai, in shaa Allahu xan daukar miki lauya kafin xuwa ranar komawa kotu baxan taba bari ayi miki hukuncin aikin da baki aikata ba, keba marainiya bace indai Mal Lawan yana raye, ni mahaifinki ne Hafsatu kuma mahaifiyarki, gado nane kawai baki dashi sakeena, kuma shima dan dai hurumin Allah ne, amma duk abunda uba yakewa ya xan miki"



Saddiq yana kuka yana girgixa kai, Baba ya miqe xai fita Saddiq ya rufa masa baya, ya juyo ya dakatar dashi yace "Ka fita daga harkarmu indai kasan Hajara kakewa rahoto, banason munafurci" Saddiq yayi wuf ya dakko qur'ani kan bed side xai rantse. Baba ya kwace yana masa fadan akan me xai rantse da littafin Allah. Yace "Baba dan ka yarda dani ne, wlh Baba na dawo rakiyar Hajjo tun lokacin datayi silar rabuwar Deni da sakeena ta hanyar asiri. Kuma kema sakeena ina neman yafiyarki kan abunda ya faru a baya kiyi haquri ki yafemun" Baba ya jinjina kai, ya juya ga Iya yace "Hafsatu karki qara taba duk abunda kikasan Deni ne ya kawo daga kan kayan abincinsa har xuwa kan kayan masarufi ki bar musu abunsu shi da uwarsa. Xan dunga baki kudin awo dana cefane ki dunga siyan abunda xaki dafa mana ni da ke da sakeena. Kuma duk abunda Hajjo xatai karki kulata dan Allah" ya fara lalubo kudin aljihunsa xai bata tace "to malam, akwai ma kudi a hannuna wanda sageeru ya bayar a kula da sakeena ko dasu xa ayi amfani wajen daukan lauyan?" Saddiq cikin sanyi jiki yace "Baba dan Allah a hada dani a cikin tukunyar Iya domin nima yanxu Hajjo batayi dani tunda nace ta janye qarar data shigar" Baba yayi murmushi ya shafa kan Saddiq yace "To, taho mugani"




Su Hajjo basu shigo ba sai azahar, lokacin har Iya ta gama yin abincinta ta juye a warmer takai daki ta tasa sakeena gaba sukai alwala suka shige daki suka rufo.



Su Hajjo anbaje a tsakar gida ita da ragowar mutanen da sukayo mata rakiya xuwa gida. Suka dunga maida yacce akai a kotu kuma suna fadar yadda yan jarida sukai da Hajjo yanxu acan gidan radio. Wata qawar Hajjo Laraba tace "An shige daki an qule hmm kunyar duniya ma kenan saura ta lahira" haka dai suka cigaba da sakin habaici da kalaman tunxura har xuwa kiran sallar asarr lokacin majalsar ta tashi kowa yayi gidansa.



Da daddare a shirye shiryen gidajen radio duk inda ka kunna acikin kanun labarai labarin sakeena ne wacce ta tafi yawon bariki da aurenta ta dawo da cikin shege da cutar HIV. Baba yana daki Iya ma tana nata dakin da sakeena agaba Hajjo ta ware sautin radio ya cika gida domin su sakeena su jiyo don basu kunna radio ba. Muryar Hajjo tas a cikin radio tana kuka tana fadar tarihin sakeena na qarya har xuwa kan abunda tayi, wanda tace silar haka mijin sakeena wato danta Deni baqin ciki yasa ya gudu ba a ganshi ba ko a waya ba a samunsa. Daga angama shirin a wannan gidan radio saisu juya wancan.



Sakeena dai tana xaune kamar gunki daga ita har Iya da Baba babu wanda yaci wani abu tun safe dan cikinta sai kusur kusur yake alamar yunwa ta dameshi.



Kafin wayewar garin talata labarin karuwancin matar aure sakeena ya xama batun da ludayinsa kekan dawo domin gidajen jaridu na hausa da turanci sun bubbuga labarin da photon sakeena da Hajjo ta bayar. Gida ya kuma dadewa kowa ya kama gabansa, Baba ya tafi fafutukar neman lauya su Hadixa sun tafi skull. Sai Hajjo da Iya da sakeena dake can daka jikinta xafi rau.




Su Amina suka shigo da gudu suna nunawa Hajjo jaridar turancin hannunsu me dauke da photon sakeena sukace sun fita kenan sukaganta ana siyarwa shine suka siya suka dawo nuna mata. Ta goge ruwan hannunta na wanke wanke ta karba ta duba tace "To ku karantamun abunda sukace mana Allah ya sa dai yadda na fada musu haka suka rubuta" Amina tahau karanto turancin jikin jaridar cikin grammatical errors (RIP English🀣) Tana fassarawa da son xuciyarta domin abunda aka rubuta daban abunda take fada daban tunda turancinta beyi riqar daxata karanta jarida ba kuma tafi qarfin tace baxata iya ba, Hadixa na gefe na gyada kai kamar qadangaruwa tana cewa haka akai da kyau, har gara Amina akan Hadixan dan ita diskindarice brain din a dode take.



Hajjo tace "To maxa ku ajiye jaka ku fito muyi aiki tunda kun makara gobe kwaje" Deni wanda ke gudun Hijira a hostel din BUK sai gashi ya shigo a burgija kama duk ya fita hayyacinsa cikin kwana takwas kacal, fuskarsa duk qasunba. Shima jaridar ce riqe a hannunsa har hostel abokinsa ya kawo masa, akai masa chaa ana tambayarsa ala dole ya gudo daga can xuwa gida don gidan yafi security.




Ya dagawa su Amina yace "Meye wannan? Abunda kukai be isheku ba sai da kuka hada da Newspaper? Ina ruwanku da rayuwata? Har yanxu inason Sakeena kuma ni ta batawa ba ku ba" Hajjo tasha gabansa tace "Nice nayi ba suba, bayan haka kuma har qara na kaita kotu jiya aka xauna kuma wani satin xa ai mata hukunci tunda ta amsa lefinta kaima kuma alqali yace axo da kai ranar. Kuma inka kuma tsoma baki cikin lamarin ko ka kuma kiramun sunan karuwa acikin xuri ata Nono na dana baka Allah ya isa" fuskarsa bata nuna mamaki ba ko tsorata da kalamanta ya juya ya koma daki.



Hadixa ta rage murya tace "Sai fa kinbi ta qarqashin qasa xai rabu da ita, ada ma ya haukace kanta bare yanxu data xama yar gayu mace sosai?" Hajjo ta girgixa kai tace "Tabbas, yanxu kuwa"




Iya ta fito riqe da sakeena ta rakata kofar bandaki ta tsaya jiranta, Hadixa ta fara rera waqar "Wayyo ni Allah namadi ya gudu ya barni namadi da tsohon ciki namadi" suka kwashe da dariya. Hajjo tace "Hadixa xan fita ku dafa mana taliya jellof da dankalin turawa tunda ga yayanku ma ya dawo nasan xaici sosai ga 200 asai kifi asaka tayi xaqi. Aini wannan raba girki yayimun dadi na huta ciyar da qattin banxa daya juya dayar kuma me shege aciki. Naga ma anfara wata sabuwar tsirfa jiya an daina taba kayan abincin gida sai awo ake yowa a kanti" Amina taja tsaki cikin tsabar futsara tace "Aikin banxa, isar da ba a isa ba, in da gaske xuciyar akai adawo da kudin da yayanmu ya bada mana aka kafa jarin tunda na tabbatar acikinsu ake awo da cefane" Hadixa tace "Wlh kuwa, ai baxa a dawo dasu ba yunwa ta kashe shege aciki" Hajjo tace "Hafsatu ki tanka musu mana in kin isa?" Iya xuciya ta kawo mata wuya amma tayi matuqar qoqari ta danne tabi umarnin mijinta.



Hajjo cikin jin haushin rashin tankawar da Iya tayi tace da Amina "Shiga dakinta ki fitomin da duk abunda kikasan Deni ne ya bata, don tunda malam yaqi goyan bayana wlh ya tarko tashin hankali. Ke kuma Hafsatu inkinji haushin abunda nayi ki haifi naki Dan ko kuma sakeenar da kike ikirarin yarkice tayi miki magani"



Amina da Hadixa suka shige dakin Iya suka dunga fito da kayanta na masarufi data kafa jari da kudin Deni, kai basu tsaya nan ba har kujerun dakin guda 2 da Deni ya raba musu saiti da Hajjo saida suka kinkimo da center carpet da kuma qaramar TV Toshiba da receiver. Hajjo tace "da kyau kukai kujerun daki ku hademun da nawa dama nawane akaimun qarfa qarfa, kayan kuma ke Amina ki shishshiga maqota ki fada musu nadawo sai da kayan kanti."




Iya ta riqo Sakeena tada gama wanka suka taho, dai lokacin kuma Deni ya fito da belt daga daki da alama yaji batun su Hadixa. Ya qurawa Sakeena ido, inaga hakance ta hanashi gane Hajjo ce tsaye gabansa ta boye su Hadixa a daki data ganshi da belt. Su Iya na shiga daki, ya daga belt iya qarfinsa ya saukeshi kan Hajjo a xaton su Amina ne. Ta tsanyara ihu dan dukan ya shigeta ya juyo a firgice, yayi arba da Hajjo tana sosa baya yace "Ina yan iskan yaran suke?" tace "Nasakasu a daki ni ka dakeni a madadinsu tunda Hafsatu ce ta haifeka. Wlh Deni xan maka baki rayuwarka ta lalace akan Hafsatu da sakeena"




Iya ta fito riqe da kudi ta miqawa Hajjo tace "Ga kudin cinikin kayan da akai" Deni ya riqe mata hannu ya durqusa yana bata haquri, batama ji abunda yake fada ba balle ta bashi amsa. Hajjo ta fusge kudin ta soke a cikinta, Iya ta juya ta koma daki Hajjo ta shige nata dakin akabar Deni tsugune a cikin rana yana ayyana kodai ya hada kayansa ya gudu ne? To inya gudu yaje ina? Kuma aikinsa da karatunsa fa? Yace a cikin xuciyarsa inama ba Hajjo ce ta haifeni ba, inama ana canja uwa daya canja Hajjo, sai dai kash! In aka haifeka an cuceka domin ba a canja iyaye.



Hajjo ta nunawa su Amina kudin da Iya ta bata, suka irga tace "Masha Allah, ta bani kudin xuwa gurin teacher, yanxu can xan nufa ayimun aikin akan raba xuciyar Deni da mayataccen son sakeena sannan a tasomun da maganar auren Hadixa naji har yanxu basu aiko ba" ta canja kaya ta fita tare da Amina wacce xata shiga maqota fadar Hajjo na saida kayan kanti.



Iya kuma ta fara gyaran dakinta dasu Amina suka birkita mata garin kwashe kayan Deni, ta gama ta dora girki.



Hajjo bata jima sosai da fita ba sai ga wasu gungun fusatattun matan unguwar(mahaukata masu ara su yafa) sun yiwa gida tsinke, Iya ta taresu tana tambayarsu lfy? Dayar ta dauke Iya da mari tace "Tunda ke mahaukaciyace dabba baki haihu ba balle kisan ciwon yaya shiyasa yarinya tayo yawan dandi da aurenta harda ciki kika bata mafaka ko? Salon namu yayan suga abunda tayi kuma suga ba a dau mataki ba suma suje suyi? Saboda haka inkinason kanki da lfy ki fito da sakeena ki koreta tunda ba yarki bace ke bakomai bace gurinta sai yar uba. Inkuma kinqi wlh saimun qoneku keda Sakeena da rai" ta fito da jarkar fetur da kuma ashana.



Iya tayi wuf ta fada daki ta danno tasa sakata ta dafe qirji tana haki. Sakeena ido jajur taji duk abunda akace tace "Iya danme xaki rufe qofa? Meyasa baxaki miqani garesu ba?" Iya ta kamo sakeena ta qanqame tace "Duk uwar duniya tana sadaukar da ranta dan danta ya rayu, ke yatace Sakeenatu xan iya sadaukar da tawa rayuwar dominki sai dai a kashemu tare, ko kuma a kasheni kafin a kashe ki"




Matan da suka ga Iya ta shige ciki suka hau buga kofar iya qarfinsu suna cewa ko ta miqo sakeena ko su balla kofar su shigo ta qarfi.




Deni tunda yaji abunda suke fada ya fice a sace don basusan yana gidan ba, ya tari napep ya kaishi police station na Gwale a gaggauce ya fada musu cewar wasu gungun matace sukaje xasu qona mutane da rai in ba'ayi gaggawa ba komi na iya faruwa. Jin cewa abun be afku ba suga gaggauta sukayi mota guda da police Deni ya shiga suka tafi.



Umman Amir ta nuna mata gidan tace tsaya anan Hajiya Hassana don nidai kamar nan sukaimun kwatance, Hassana ta kalli gidan ta glass din motar ta dake rufe ruf tace "anya kuwa maman amir? Nan fa kamar gidan babu lfy baki ga mutane cike ba?" Umman Amir tace "To bari su dan ragu sai inshiga inga, inma banan din bane sai inyi tambaya don kusa da nan Babar sakeena taimun kwatance" sukayi xamansu a mota suna jiran mutanen su ragu su shiga ciki. Dai dai wannan lokacin kuma motar police ta tsaya suka diddiro suka shiga ciki da hanxari.




Suna saka kai sukaji wata tsohuwar jaka acikin matan tana cewa "Tunda mun kasa balle kofar kawai musawa dakin wuta mu cika aiki mu raba kudinmu mu tafi" yan sanda suka daka tsawa ogansu yace "duk a tattara kansu ayi station dasu" yan sanda suka daka musu wawa suka kwashesu duka, suna ihu wasu suna cewa "Ayi haquri Hajjo ce ta basu 500 kowacce suxo su tsorata sakeena da Iya su koresu daga gidan" Ogan yace "kofur duk ka kwashemun yayan iska tumaki wadanda kudi kesa suyi kowane irin aiki, kunsa kanku a uku, wlh kotu xan miqaku Hajjo taxo ta ceceku da bamuxo ba kenan kisa xakuyi?" aka watsasu mota wata kan wata 🀣 Suka tafi dasu.



Deni ya koma daki yana dafe qirji, xuwa yanxu ya fara tunanin Hajjo tana da mental problem dan wannan abun da tayi ba aikin masu hankali bane. Tausayin sakeena da Iya ya dirar masa.



Suma su Amina sai a lokacin suka bude daki domin suma sun tsorata da abun kuma basusan Hajjo xatai haka ba da sun hanata gashinan buri be cika ba sai ma asirinta daya taunu.


Iya ta sauke ajiyar xuciya bayan tafiyarsu, Sakeena tace "Iya kiyi haquri, riqona be miki rana ba, ban share miki hawayen rashin haihuwa ba sai janyo miki masifa da nakeyi"


Hassana ta fito daga mota bayan tafiyar yan sanda suka shiga cikin gidan, ta dunga sallama can Hadixa ta amsa musu ta umman Amir tace "nan ne gidansu Sakeena?" Amina ta amsa "Eh ga dakinsu nan a rufe" Umman Amir ta fara bugawa tana kiran sunan sakeena amma tsoro ya hana Iya budewa sai da Hassana tayi magana da cewa "Dan Allah inda mutane ciki a bude Hassana Dalhatu ce taxo gurin sakeena" da sauri sakeena ta miqe ta bude kofa ta fada jikin Hassana suka rungume juna.



Suka shiga dakin Iya tai musu shimfidar tabarma a gurbin center carpet da Amina ta nade daxu suka xauna har qasa Hassana ta gaida Iya ta Kalli sakeena ta ciro News paper a jakarta tace "Sakeena bayan rabuwarmu dake munje Law school mun gama kuma munxama cikakkun lauyoyi ni da Usaina a shekarar kuma mukai aure wata 5 kenan baya akai bikinmu ni da usaina da yaya Ahlan. Ni ina Lagos acan nake aure da kuma aiki a chamber dita da Abba ya budemun. Usaina tana ukirine acan take aure sai yaya Ahlan dake Abuja. Naxo ganin gida ranar Friday naketa cin karo da labarai marasa dadi akanki a social media, sai kuma jiya naji a radio yau kuma na fito da safe naci karo da wannan Newspaper din. Labarin ciki na cin xarafin dan adam ne, koda ace kin aikata abunda ake tuhumarki dashi be dace ayi miki hakaba, bare wannan abun da aka fada beyi kama da abunda xaki aikata ba Sakeena. Na fadawa Mama da Abba harda mijina sun bani goyan bayan tsaya miki a matsayin lawyer shine na nemi umman Amir ta rakoni gidanku. Ki budemun komi sakeena xan temaka miki in kwatar miki yancinki ke qanwarmuce kamar yadda mukasha fada miki abaya."




Sakeena batai magana ba sai gyara kwanciyarta tayi akan cinyar Hassana. Iya ta muskuta ta fara basu labarin duk yadda akai bata rage musu komi ba. Domin ta gane Hassana sosai tasha jin xancensu bakin sakeena.



Suna daki xaune suna tattauna matsalar har Baba ya dawo da Saddiq suka shigo suma suka fadi daga nemo lauya suke amma ko ina sai da kudi, sunji dadin jin Hassana xata tsayawa sakeena kyauta. Suka tattauna yadda xasu bullowa lamarin. Hassana tayi musu alqawarin nemo sageer duk inda yake a Nigeria bama a Lagos ba da take gida a gareta. Anrabu suna farin ciki jin alamun nasara har mota saddiq da Baba suka raka Hassana suka tafi.



Baba ya dawo cikin dakin Iya ya tsaya yana kallon dakin ankwashe komai, ko Iya bata fada ba ya sani Hajjo ce tayi sanadin raba Iya da kayan da Deni ya sai mata. Saddiq ma sai a lokacin ya lura domin harga Allah farkon shigowarsa be lura ba, (hankali shike gani wai wani yaxo Kano bega mota ba πŸ˜„) ya fita yaje dakin Hajjo yaga kayan Iya acikin falon Hajjo dan hauka TV har guda biyu, be cewa su Hadixa komai ba saboda kar suyi masa rashin kunya ya dakesu Hajjo ta tsine masa.



Baba ya shiga dakinsa ya kwallawa Amina da Hadixa kira, suka shiga a darare a xatonsu fada xai musu, sai dai me? Gani sukayi ya nado duk abunda yasan mallakin Deni ne daya bashi a dakin ya tattara yace "ku kwashe kukai dakin uwarku kafin nima taxo taimun gorin" suka fara bashi haquri da fada masa wai ai Iyace ta watso kayan tace bataso. Yace "To madallah nima gashi na watso nace banaso" suka dunga jidar kayan suna kaiwa dakin Hajjo suka cushe dakin da kayan.


Hajjo bata shigo ba sai bayan la'asar shigo faran faran kamar korarriya. Taga kaya sun cika daki tayi turus tace "Wadan nan fa daga ina?" sukai mata banxa, ta nemi guri ta xauna akan kujera tace "Auta magana nake kunmin banxa" Amina taja tsaki tace "Hajjo na rasa abunda yasa kike da over acting wlh, gaskiya yau kin mugun batamun rai kuma kina nema ki bata mana plan" cikin kwantar da murya tace "Me kuma nayi na batamiki rai auta?" Hadixa cikin masifa kamar xata daki Hajjo tace "Yanxu meye naki na debo hayar mata da basu kudi suxo har gida su qona sakeena da Iya? Meye ribarki in sakeena ta mutu

Please Login or Register in order to submit comment