Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iskace irinka? Ko kaxaci na manta kai dan bariki ne wanda karuwarka har duka taimun?" ya sunkuyar da kansa cikin kunya da nadamar rayuwar barikin da yayi. Jiki a sanyaye yace "Kiyi haquri sakeena tunda na aureki har xuwa yanxu ban qara sha'awar rayuwar bariki ba wacce nai a baya ma ina nadama da neman yafiyar ubangiji" ta juya tacigaba da duba magazine din data gani gurin shi kuma yacigaba da aikin kallon ta.


Sun sauka lfy ya dauki taxi har xuwa unguwarsu, saida suka shiga cikin unguwar sannan sakeena ta dubeshi tace "Sageer baxan xauna a gidan da kayi xaman haramci da niba saboda haka kodai ka canjamun gurin xama ko kuma in gudu garinmu." Sageer ya fara duban a tsorace cikin rawar baki yace "A a baxaki tafi Kano ba akan canja muhalli ki bani 1 wk xan canja gurin xama, badan yanayin aikinmu ba ma da saina kama daki a hotel xuwa lokacin da xa a samu gidan, ki kwantar da hankalinki baxanyi abunda bakiso ba amanarki na karbo" bata qara magana ba ta hade rai, me taxi din ya shiga har cikin gate din gidan. Sageer ya bude kofar falo ta shige tai xamanta akan kujera tana kada qafa, tabarshi da kici kicin shigo da akwatinan ta. Tana qarewa gidan kallo daga xaune da gani an narka kudin wajen gyarashi ko fentin da akai abun kallo ne.


Ya gama ya dan dawo kusa da ita ya xauna, yana magana ta shareshi. Can dai ya miqe yace "Bari naje na fara qoqarin samo gidan ko?" tace "Better" ya fice ya shiga gidan Maitama don ya fada masa sun sauka.


Yana fita ta miqe ta fara xagaye gidan tana jinjina tsarinsa duk da ba wani girma gareshi ba. Kicin din yayi kyau an shaqare shi da kayan amfanin kicin saiya tuna mata da xamanta a gidan Alh Dalhatu. Ta ciro waya ta kira Hassana tana fada mata sun iso, Hassana tace mata ita sai gobe Monday xata dawo. Daga kicin bedroom ta nufa wato na sageer inda sukai rayuwar wancan auren, ta kwashe kayanta daya shiga dasu ta mayar dayan domin baxata hada daki dashi ba, sam ba haka taxo yiba. Bata shirya kayanta a sif ba tunda tashi xasuyi ta jibge akwatinan ta miqe a gado tai kwanciyarta.



Acan gidan Maitama bayan an gaisa da kuma bangajiyar biki Bilki ta bawa Sageer manyan warmers data xuba musu abincin da tayi dominsu tace ya tafi dasu. Ya dubeta yace "Ni ba komawa xanyi ba dan bawa maid dinki ta miqawa sakeena kafin na dawo don nasan tana tare da yunwa" Maitama yana karatun newspaper ya dago yace "kaito ina xaka ko hutawa bakai ba?" Direct yace "Sakeena ce tace batason xaman wancan gidan shine xanje nemo gida ko na haya ne da xamu xauna kafin inyi shirin siyan wani" Maitama ya zare glasses din idonsa yana duban sageer da mamaki, kafin cikin bacin rai yace "Sageer ka shiga taitayinka wlh, wannan bare baren da kake akan sakeena baxai haifar maka Da me ido ba. Duk kabi ka susuce ka haukace akanta kamar baka taba sanin ya mace ba sai ita, wai dama irinku wadanda basu taba soyayya ba in sun tashi yinta haka sukeyi? Yanxu inka tashi daganan da muke da yawa mu hausawa da kuma security kasan inda xaka koma? Ka kuma san yanayin aikinmu koda yaushe ana iya farmakar rayuwarmu kota iyalanmu? Meke damunka ne sageer akan wannan qanqanunwar yarinyar ka xauna tana juyaka yadda taso? Tun randa sakeena ta dawo hankalinta baka qara hutawa ba, duba lokacin datayi miscarriage yadda daga fada maka ka dauki mota xaka tafi kano a lokacin badan mun hanaka ba da tuni ka rasa ranka tuntuni. To wlh babu inda xaka canja dole ka xauna anan tare damu, sannan ko ka xama shugaba a gidanka ka saita sakeena ko karkayi duk daya kai xakasha wahalar xama da ita inta sangarce. Ita kuma yanxu xanje insameta dan ubanta inji in irin tarbiyyar da aka bata kenan?"


Sageer ya tare gaban Maitama yace "Babu ruwanka da harkar gidana ko ni ina maka katsalandan akan familyn ka?" Maitama yana dubansa da mamaki yace "Sageer macece xata hadamu dakai?" yace "Eh sai ta hadamu din bakasan yadda xuciya take ba intanason abu?" Maitama bece komai ba ya kewayeshi ya fita. Sageer ma ya bishi da gudu. Bilki ta dauki mayafi ta bisu da sauri karsuyi batacciya tasan mijinta da xuciya.


Maitama ya riga sageer isa gidan saboda a xuciye yake, ya tsaya falo ya kwallah sakeena kira. Tana tsaka da bacci kiran ya risketa ta farka a furgice tayo falo, ta sunkuya xata gaida Maitama ya daga mata hannu yace "Riqe gaisuwarki, wai ke wace irin fitinanniyar yarinyace? Wace irin xuciya gareki mara sanin darajar masoyi?" dai dai lokacin sageer da Bilki suka qaraso Maitama be saurara ba yacigaba da magana "Meye laifin sageer dan kawai yana sonki kike wahalar dashi? Kinsan akanki ya kusa rasa ransa kuwa? Kinsan dinbin sadaukarwar da sageer yayi miki kuwa wacce kika sani da wacce baki sani ba? Menene na tsiro da maganar sauya gida yanxu? Shin kinsan rayuwar Lagos kuwa? To bari kiji ni nace baxa'a canja gidanba, nasan bakinsan matsayina ba a gurin mijinki ba ko? To ni childhood friend din sageer ne wanda yau akanki yakeso ya manta amintakarmu. Wlh sakeena ki shiga taitayinki don baqaramin aikina bane in miki dukan tsiya akan wannan abunda kikeyi. Sannan daga qarshe inna kuma jin wata maganar banxa makamanciyar wannan ta taso saina buga waya na fadawa iyayenki inji in irin tarbiyyar da sukai miki kenan" sakeena dai tunda Maitama ya fara magana kuka takeyi wato sageer qararta yakai gurin abokinsa kenan ko? Amma maganar Maitama na cewa xai buga waya gidansu ya fada duk tafi daga mata hankali.


Ya juya ya fita, Sageer rai a bace ya rufa masa baya. Bilki ta riqo sakeena suka xauna kan kujera ta fara lallashinta, saida taga tayi shiru sannan ta bata haquri da cewa "Kiyi haquri da abunda mijina yayi nasan ya tsallake iyaka ya shiga fadanku, amma kema sakeena da lefinki menene naki na cewa sageer ya canja miki muhalli? Dubi gidannan yacce ya gyarashi ya saka komai sabo saboda ke amma daga xuwanki kice baxaki xauna ba? Xaman Lagos ba irin xaman Kano bane kuma yanayin aikinsu yana da hatsari sosai xaku iya canja guri abiku a kasheku ke da shi, nan kuwa munada cikakken tsaro. Kiyi haquri nasan bakyason sageer tsohon mijinki kikeso amma wlh sakeena bantaba ganin inda namiji keson mace yacce sageer yake sonki ba, banga lefin sageer ba Kamar yadda banga dalilin qiyayyarki gareshi ba babu abunda ya rasa daga kan kyau har xuwa kan kudi sannan yana da haquri da kuma kirki. Illar sageer daya ce Bariki kuma wlh tunda kika shigo rayuwarsa ya dena. Kiyi haquri ki karbi mijinki ki kwantar da kai kuyi rayuwar aure me dadi tun kafin yan matan Lagos su janye miki shi" Bilki ta saka sakeena dole ta tuttusa abincin data kawo musu ta kuma tayata shirya kayanta a sif da kuma kayan girkin da Iya ta bata a kicin harta dibawa Bilki. Sai kusan ukun rana ta tafi, sakeena ta qara komawa ta kwanta cikin tsanar sageer da kewar Iya.


Sageer yana xaune gurin a bencin megadi, fada sosai sukai da Maitama akan abunda yayiwa sakeena suka rabu rayuka a bace. Ganin fitowar Bilki ya tashi ya koma ciki gabansa na faduwa,


Dakinsa ya nufa inda yakai kayanta daxu, sai dai ya tarar wayam babu komi ta kwashe kayanta. Ya fito ya shiga daya dakin, ya sameta kwance tana danna waya. Jin motsin shigowarsa ta tashi xaune ta qanqance ido cike da masifa tace "Sageer ashe qarata kakai gurin abokinka ko? Wai yaushe ne xaka fuskanci abunda kalmar qiyayya take nufi? Dan Allah Sageer ka gwada xama da wanda bakaso koda na awa daya ne kacal kaji yadda akeji saika kwatanta da yadda nakeji akanka" jikin Sageer yayi tubus da kalamanta, ya fara tunanin anya be xalunci sakeena na ba da ya aureta bata sonsa? Ya juya xai fita yace "kiyi haquri xanje induba gidan yanxu" bata tanka masa ba ya fice.



Tana kwance sallah kawai ke tada ita daga gurin, yayin da Sageer keta garari a garin Lagos cikin rana daga gurin wannan dillali xuwa gurin wancan anata nuna masa gidaje wasu gidajen basuyi masa ba wasu kuma sunyi masa amma unguwar area boys sunyi yawa. Dole ya haqura bayan sallar Isha yagaji tiqis ga yunwa, ya tsaya masallaci yayi sallah ya sayi gasassun kaji da madarar roba ya nufi gida. Acan kuma sakeena bayan sallar isha taje tayi wanka tayi shafe shafenta ta dakko daya daga cikin rigunan baccin lefenta ta sakata me siririn hannu wacce ko gwuiwarta bata qarasa ba. Garin ya hade yayi murtuk anata iska koda yaushe ruwa na iya sakkowa. Ta fice harabar gidan ta xaga baya ta xauna kanta ko dankwali babu, ta rasa abunda yake mata dadi, duk duniyar dundum take jinta garin Lagos da duk abunda ke ciki duk ta tsanesu a dalilin Sageer ta rasa inda xatasa ranta taji sanyi ta rasa ta yadda xata farason sageer da kuma rayuwa dashi, inama ace Baba wani ya aura mata kowanene data haqura tayi masa biyayya. Ta fashe da kukan tausayin kanta da kuma qiyayyar sageer, yanxu gashi tun rana ya fice ya barta ita daya a gida kamar mayya (haba sakeena ba ke kikace ya samo gida ba, ke baxaki xauna ananba? 😜) ruwa ya sakko kamar da bakin kwarya tana xaune yana jiqata tana kukanta.



Sageer ya shigo gidan ya tadda bata a falo yayi zaton tana cikin bedroom. Ya bude warmers din dake kan dinning yaga an taba abincin ciki ya sauke ajiyan xuciya yasan sakeena taci abinci kenan. Ya xauna shima yaci abincin saboda yunwar dake sakadarsa tun breakfast din safe rabonsa da abinci. Ya gama ya dauki ledar kaxarsa ya shige nasa dakin don yayi wanka yaje ya kaiwa sakeena kaxarta ta amarci. Yayi wankansa irin na angwaye ya fesa turaruka masu sanyi da qamshi mai tsuma xuciyar ma'abota soyayya, shi dinma sabbin kayan bacci ya saka ya dauki ledarsa ya nufi dakin sweet heart sakeena.


Hankalinsa yayi mugun tashi daya gama kewaye falon xuwa kicin da daya bedroom din amma babu sakeena, ya fara tunanin to ina taje ana sheqa ruwa haka? ko gidan Bilki ta shiga? Wata irin faduwar gaba ta sameshi daya tuna kalamin sakeena na cewa koya canja mata muhalli ko ta gudu garinsu, to kotaga shiru be dawo ba ta gudu Kano? Ya watsar da ledar Hannunsa yayi wajen falon da sauri yana kiran me gadi. Ya taso jikinsa na rawa ya duqa gaban sageer, cikin rawar baki yake tambayarsa madam ta fita ne? Yace "A a babu wanda ya fita a gidan nan" ya sauke ajiyar xuciya ya xagaye gidan cikin sauri. Yaci karo da sakeena a bayan gidan cikin bishiyoyi xaune ruwa na dukanta ido jajur fuske cike da hawaye ta qanqame jiki alamar sanyi takeji yace "Subhanallah, sakeena in wani abun ya cijeki fa?" yasa hannu ya dauketa ya shige ciki. Dakinsa ya nufa da ita ya kwantar a kan gado sai rawar dari take, ya kunna room heater ya dawo ya cire kayan jikinsa da suka jiqe saboda nemanta ya canja wasu ya dawo ya fara kicin rabata da rigar jikinta ta riqeta gam ta hanashi yin hakan. Yayi mamaki wai sakeena ke boye masa jikinta ta manta lokacin da suke wanka tare wataran ma shi yake mata, yayi murmushi yace "cire miki xanyi saboda ta jiqe kuma ana sanyi" batace komai ba ya cire mata rigar yayi matuqar daurewa da kai xuciya nesa da ganinta haka ya danne kwalamarsa ya dakko shirt dinsa yasaka mata ya kwanta ya rungumeta tsam yana sakin ajiyar xuciya. Haka sukai baccin da suka dade basuyi me dadinsa ba.


Da wuri ya tashi da safe yayi duk abunda xaiyi na aikin gida yayin da gimbiya sakeena ke kwance tana bacci tunda daga idar da sallar asuba, yayi breakfast ya ajiye mata kan dining ya fita xuwa aiki. A office ya yini tunaninta a gefe guda kuma wadanda basu samu damar hallartar aurensa ba sunata xuwar masa murna. Ya dunga kiran wayarta taqi dauka yaji sam hankalinsa ya gaxa kwanciya a daddafe yakai lokacin tashi ya nufi gida.


Yana murda qofar falo ita ya fara gani sanye cikin riga da skirt na atamfa tana kallo, ya sauke ajiyar xuciya da Hamdala a tare ya tako xuwa gabanta yana kallon kwalliyar data caba a fuskarta da kuma daurin data kashe, ya lumshe ido a xuciyarsa tunani yake donme Maitama ke ganin lefinsa dan ya mace a soyayyar sakeena? Duk wani abu na sakeena abun sone da burgewa ga kwalliya da tsafta kuma akai dace jikinta me saurin amsar kwalliyar ne. Yaji wani abu na fuzgarsa xuwa gareta, ya saka gwuiwowinsa a qasa ya tsuguna gabanta ya riqo yatsunta yakai bakinsa ya sumbata yace "Barka da gida ranki ya dade, anyini lfy?" ta xare hannunta tana dubansa fuska a hade tace "Sageer ka shiga hankalinka da ni, indai kanason xaman lfy ka daina kai hannunka jikina" ya hadiye yawu be shirya ba jin wannan qaton sabon da sakeena tayi, to ta yaya hakan xata yiwu? Ta katse masa tunani tace "in kuma kanaganin hakan baxata yiwu ba ka iya maidani garinmu ko kuma kaje ka fadawa Maitama yaxo ya tsireni" da sauri yace "Duk abun bai kai haka ba, jiya ma da yaxo wlh bani na sakashi ba kuma na nuna masa bacin raina akan hakan da yayi" ya tashi ya shige daki ya kintsa jikinsa ya fito ya nufi table, ya saki wani irin murmushin farin ciki dayayi arba da food warmers da tarkacen kayan cin abinci ya juyo yace "My luv har girki kikayimun? Nagode kwarai Allah yayi miki albarka" ba tare data kalleshi ba tana danna waya tace "badon kai nayi ba, kuma inka kuma yimun godiya na denayi" yaja bakinsa ya tsuke ya hau dining ya kwashi tuwan semo miyan danyan kubewa yaci yayi nak ya dunga yabawa iya girkin sakeena a xuciyarsa. Da akaxo kwanciyar bacci dakinta ta shige ta barshi a nasa yana rungume da filo. Da safe ma ya tarar tayi breakfast kuma ta ajiye masa amma banda haka babu abunda tayi a gidan ko ganinta beyi ba balle ya samu arxiqin koda gaisuwa ce, yaci abincinsa ya fita yana driving yana tunani sakeena ta nuna xata dunga girki basai ya dakko kuku ba amma kuma dole ya samo maids kodan tsaftar gidan tunda yau ko tsinke bata dauke ba a gidan.


Cikin kwana biyu saida gidan ya hargitse don shine ke gyarawa kuma ba wani iya gyaran gida yayi ba, aikinta kawai girki inta gama shikenan. Arana ta uku sai gashi da masu aiki su biyu, dayar yarinyace wacce yace xata dunga wanke wanke da shara kuma zatazo tun safe sai yamma xata tashi. Dayar kuma yace sunanta Inna anan xata xauna a dakin dake wajen falon xata dunga lura da komi na gidan, sakeena batasan alaqarsu ba tadaiga yana girmamata suna ta hira da alama akwai tsohuwar sannayya tsakaninsu, shiya dauki kayanta ya rakata dakinta. Wannan shine mafari, daga xuwan Inna gidan ganin sakeena ma yayiwa Sageer wahala sai dai tai girki ta ajiye masa intaga dama in kuma iskancin ya motsa sai dai ya siyo ko kuma Inna tayi. Sageer ya fada cikin wani irin yanayi na kewa da azabar qaunar sakeena da so samune koda ganinta ta dunga bari yanayi. Yayin da ita kuma bata da aiki sai dai tai wanka tayi kwalliya tayi chatting inta gaji tayi kallo ko kuma suyi waya da Iya da Baba ko Hassana. Alaqarta da su Inna masu aikin gidan ba wata alaqar arxiqi bace qarqari su gaisheta ta amsa ko kuma ita ta gaida Inna tunda ta kusa jika da ita, bata sake musu fuska ko kadan domin ta dawo daga rakiyar yiwa mutane kirki bayan haka kuma tayi alqawarin duk wanda ta sani ta silar sageer baxaiji dadin xama da ita ba. Shi kansa sageer din saita kwana biyu bata ganshi ba yo kullum tana daki a kulle saitaga bayanan take fitowa falo ko taje kicin sau tari xaixo yana buga kofarta yana cewa dama yanaso ya gaisheta ne yaji ta kwana biyu shiru. Bata tanka masa sai dai ya qaraci bugunsa da magana ya haqura ya tafi.


Tana da 17 dayx a Lagos aka kirasu jarrabawar Post UTME, Sageer ne yaxo mata da xancen, albarkacin hakan ranar ya ganta bayan shafe kwanaki 3 ko giftawarta be gani ba. Ranar jarrabawar shiya dauketa da kansa ya kaita venue din ya xauna jiranta har tayi ta gama ya dawo da ita. Xaman banxa ya gundureta tunda bata saba ba, ta fara tunanin abunyi ta samu aya ta gwada kunun aya na rabin kwano ta xuba a robobin ruwa, da kanta ta kaiwa Bilki tace gashi ta fara sana'a. Bilki tai murna dake tasan darajar neman nakai, itace tasa me aikinta ta nunnuwa matan cikin quarters din, a cikin awa daya sai gashi an siyeshi tas ana nema, washegari tayi na kwano guda, kan kace meye wannan shima ya qare, a kwana na uku tayi na kwano biyu kuma ranar ne Sageer yasan anayi, ya dawo ya tarar da yara a falo sakeena tana sallamarsu da robobin kunun aya. Abun ya bashi dariya da mamaki yace "Bakanuwa kenan, kanawa akwai neman kudi." ta hade rai don karya kawo mata raini tacigaba da karbe 50 naira ahannun yaran tana basu robar kunun aya. In taqaice muku xance dai cikin sati daya sakeena ta xama hajiya me kunun aya domin abu ya kankama data qiyasta kusan kullum tana siyarda na 3k in kuma ba'ayi ciniki ba 2500 xuwa 2800 duk yawansa intayi saiya qare har dare xuwa ake nema xaman banxa ya qare yini take aikin kunun aya da kuma sallamar masu xuwa siya.


Sageer dayaga abun ya kankama saiya ware guri a harabar gidan ya kewaye mata da langa langa akayi rufi saboda ruwa akayi wearing ya saka mata qatuwar freezer ya daukar mata me aiki wacce take tayata aikin da kuma miqawa masu siya in sunxo yake biyanta a aljihunsa. Domin abun ya burgeshi batasa girman kaiba ganin mijinta me kudi ne kuma bata damu ya bata ba ita kawai nata take nema (mata mu dage da neman na kanmu kodan gudun wulaqancin maxa, ba lallai sai kinsamu aikin gwamnati ba koda kina da ilimin ko babu koda aikin gwamnati ko babu ki nemi Sana'a duk qanqantarta karki raina wata rana xata bunqasa indai kin jure) Cikin wata guda da fara sanaarta saidata tara kudin da ita kanta batasan yadda akai sukai yawan haka ba, ta ware wasu ta qara jari wasu ta ajiye ragowar kuma ta turawa sageer ta banki tace ya bawa Iya. Iya tayi murnar jin sakeena harta saki jiki ta kama Sana'a a xatonta xaman kwarai suke da Sageer din tunda duk sanda sukai waya ta tambayeshi cewa yake qalau suke xaune.


Ana cikin haka wata matar abokin su Sageer ta haihu ana neman me kwalliya wacce xataiwa me jego ran suna Bilki tace sakeena ta iya. Ranar suna aka kira sakeena bata bawa Bilki kunya ba ta rangadawa me jego make up, yayi kyau aka dunga yabawa gashi baya damewa saboda kayan kwalliyarta babban products ne. Daga haka shikenan duk sanda abu ya tashi a cikin matan abokansu sakeena ke musu kwalliya a biyata, kudin casual daban na amarya daban kuma batasa kudi da yawa ba shiyasa take ciniki. Shima sageer ya samu kwarin gwuiwa idan suna taro a office xaice matarsa na kunun aya ya karbo mata kwangila a biyata kudade masu tsoka tayi kuma ta karbe babu ko godiya. Cikin qanqanin lokaci sakeena ta tasarwa xama Hajia (amma fa bani Hajian ba danni bani da ko sisi 😄) Iya da Baba na kano suna mata adduar rabuwa da sharrin masahassada da yan black stomach, wadanda bakasansu ba baka damu da suba amma su ka tsaya musu a maqogwaro (Allah ka rabamu da sharrin mahassada, Allah ka hana mu cutar, Allah ka hana a cutar damu, Allah kuma ka hana abiyo takanmu a cutar da wani Aminnn) Sakeena tana tsaka da samun kudi jarrabawarsu ta fito kuma taci jamiar da sageer ya nemar mata ita ta samu, wata private university sageer ya cike mata a Lagos wacce cikin qanqanin lokaci mutum xaiyi karatunsa ya gama babu strike, ta yayan manyan qasar ce, yawanci duk wanda ka ganshi cikin jamiar tofa ubansa ko sponsor dinsa hannunsa ya cudi baya. Ya cire maqudan kudade yayi mata registration wanda saida account dinsa ya girgixa sosai, amma be damuba burinsa ya cika burin abar qaunarsa sakeena kuma yanada yaqinin baxata bashi kunya ba xatai karatun ka'in da na'in

******** ***** ******* *******

A can Kano kuma gidan mal Lawan Iya ta kama sana'ar Kunun aya da pure water wanda sakeena ta kafa ta qanqame hannu bibbiyu kuma babu lefi ana samu sosai kumai yana tafiyar mata dai dai ita da mijinta, tuni ta koma islamiyyar da rashin kwanciyar hankali ta hanata xuwa a baya komai yana tafiyar mata yacce takeso ita da Baba sai kewar sakeena da suka kasa sabawa da ita. Saddiq ma Iya ta masa fadan xaman banxa ya fara xuwa kasuwa yana xama a matsayin yaron shago kamar yadda Deni keyi abaya.


A bangaren Hajjo me duniya kuwa (🤣) al amura sun gama damalmale mata sun kuma chabe, da farko dai girkinta daban takeyi ita da Amina domin Baba bayacin abincinta kamar yadda ya haramta mata shiga dakinsa kuma baya kula al amuranta, saboda xaman banxa da rashin sana a da takeyi saiya xamana girkin nata yaxamo lami. Domin Baba ba qarfi gareshi ba inya sayi kayan abinci kuma ya bawa kowacce kudin cefanenta tofa shikenan, Iya takan cika kudi a jakarta tayi girki na alfarma ya cika gidan da qamshi suci ita da mijinta da dan kallo Saddiq bata qara shishshigin bawa Hajjo komai ba tun randa tace mata ta wuce ta temakamata saboda yayanta yanxu sun sami madafa kowa ya kama gabansa. Iyafa yanxu ta wuce raini ta girmi Hajjo ta wuceta katakau ga sana'arta sannan ga aiken sakeena da take yomata na kudi kusan duk bayan sati biyu ta account din Saddiq. Saboda haka Hajjo tayi tsumuuu ita da Amina kullum suna daki suna shaqar qamshin girkin Iya gasu kuma da kafirin kwadayi. A gefe guda kuma tana mamakin dauke qafar Deni daga gidan gaba daya rabonta da ganinsa tun ranar bikin sakeena data jiwo muryarsa daga tsakar gida, ta gama haqiqancewa Surayya ce ta mallake mata Deni ta rabata dashi gaba daya ko ganinsa ba'ayi balle ya taimaka. Sannan ga Hadixa tana cikin baqar axabar uwar miji da mijin kansa kusan kullum sai Hadixan tayo mata waya tana kuka tana fada mata itafa xata taho gida ta gaji Yusuf tunda yayi aure be kuma waiwayarta ba sai da yayi 5 weeks cur kana yaxo gurinta yana xuwa ya fata pills na family planning yace tasha, duk sanda ya bata tasan abunda yake nufi dan haka taqi sha ya nada mata duka kuma yasata dole tasha ya fada kanta yayi kwanciyar wulaqanci da ita a qaramin dakinsa na gidansu taji jiki kwarai saida yajishi yaje linta sannan ya dagata yace "Karki xaci wai sonki nake ko wani testing kike dashi, a a kawai dai ina buqatar canji ne kinsan in mutum yaci kaxa na tsahon sati biyar yana buqatar ko tuwon dawa ne ko kuma gabxa

Please Login or Register in order to submit comment