Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

koda su kaje gida, iyayansu kawai suka iya fada mawa, amman rashin imanin irin na Baffah lado sai cewa yayi su kama bakinsu suyi shiru, kaman komai be faru ba,,

   Allah ya taimaka, wasu sunje rafin suka ganta, sanda aka futo da ita, ko motsi bata yie, banda zubar ruwa ta hanci ta baki ba abin da takeyi, yana can wajan kiwo aka kiranshi, wannan dalilin ne yasa, kwata kwata baya son barin ummeetah a gida,,

   hankalinsa ba karamin tashi yayi ba sanda ya ganta, baima san sanda ya nufo titi da itaba, yana tafe yana kuka, da faman fadin,,

   a taimaka mun, don Allah, ku taimakeki rayuwan yarinya tah, fillanci hausa duk yie yakeyi, cikin ikon Allah sai gashi bisa hanyar, shi kanshi ya tsorata da ganin yana yin jikin nata, ya amsheta sama sama ya rika matsa cikin nata, ruwa na futowa ta bakinta, kafun taja wani dogon numfashi, ta rika shakuwa a sumen da take,,

   hakan ya sasu danjin dama dama, motar kawai yace ma Affah ya shiga, suka wuce da ita asibiti, ankai an dawo kafun a samu ta farfado, sai lokacin sadeeq yaji hankalinsa ya kwanta, banda Affahn dake can gefe tsaye yana faman zabga kuka, sanda yaga ummeetah ta farfado kuwa idanunta biyu, harta kira sunanshi, sai wani sabon kukan ya saka, yana rungume abokin nasa, don tsaban farin ciki,,

   sosai sadeeq ya kashe musu kudi, kafun a sallamesu, shidai kasa cema sadeeq din komai yayi, amman shi kadai yasan tarin kaunar da yake ma abokinsa, sai ubangiji daya hada su kuma a wannan duniya, ya rika mai godiya kamar bazai bari ba, tun yana amsa mai, harya gajima ya daina, ya tattara yersa suka koma yana dada gode ma Allah, daya hadashi da mutumin kirki irin sadeeq.

 

   kusan shekaransu uku kenan da juna, lokacin ummeetah keda shekara tara a duniya, abin daya lura da yarinyan akwai wayau, indai zai wuce, da taga motarsa ta gane ta rika kwala mishi kira tana daga mishi hannu, wani lokacin ya tsaya wani lokacin kuma ya wuce, yana murmushi,,

   haka rayuwa ta cigaba da tafiya, har aka sanya ranar auransa da suhymah, wanda duk zuwa Abujan wajanta yake zuwa zance, sosai Ali yaji dadin wannan abin, yana burin yaga wannan rana,,

    a yen kwanakin yana yawan wucewa hanyar dalilin biki dake gabatowa, sai dai  baya yawan ganin abokin nasa, sai ummeetah dake kullum zuwa da shanun ta kiwata, tsayawa yayi gefen titi, yana futowa, hannunsa rike da ledar wata peanuts snaks mai dan tsawo da fadi, a hankali yake takawa bisa hill din, yana mamakin abin da yasa bata kwala mishi kira ba,,

   zaune ya sameta wajan bishiyar tayi uban tagumi, tana ganinsa ta mike tana murmushi, ya tsuguna gabanta tare da shafar fuskanta, ba sosai take jin hausa ba, don haka da dan dibaru yake tambayarta Affanta, da damuwa take sanar mishi, Affanta bashi da lafiya, beji dadi ba, yayi mishi fatan samu lafiya, sauri yakeyi don haka saiya bata peanuts din daya siyo mata yana fadin,,

   kie gaida Affah kinji, ta rika murna tana daga ledan gyadan, kafun suyi sallama ya tafi, da wuri ranar ta koma gida, da murnanta ta nuna ma affahn nata gyadan ledar da Baffan nata sadeeq ya bata, murmushi kawai yayi yana ayyana abubbuwa da dama, don kam yana jin jikinsa, ta matsa sai dai ya bude mata suci tare, dole ya bude mata, a baki yake bata, itama saita tana bashi da rigiman sai yaci, duk da ba dadin bakinsa yake jiba hakanan yake amsa, harya kare duka, nan kuma tasa kukan kari takeso, da dai taga ba zata samu ba, sai nade ledar tayi ta adana,,

   har Affahnta ya samu sauki suka koma futa kiwo tare, a kwana a tashi biki yaxo, lokacin ne jikin mahaifinta ya kuma rikicewa, sunfi karfin sati biyu basa futa kiwo, kwance kawai yake daker yake iya magana, ummeetah duk ta wususuke, Baffanta lamido kawai ke taimakon su, sai liman dake kawo mishi yen magunguna na hausa, ana jikawa ana sha amman ba wani sauki.

   Wata ranan jumma'a da baxai taba mantawa ba, yen kwanakin da suka wuce hankalinsa ba a kwance yake ba, saboda hidman biki daya gabato, ga al-adu iri iri da suhymah ta sanya mishi wai za suyi, ya kashe kudi dama ba a magana,,

   sosai kuma ya damu, da yaga kwata kwata ya daina ganinsu, yana son zuwa ya duba ko lafia, don ya taba zuwa so daya, da abokin nashi ya bashi kyautar sanuwa, ya matsa sai yaxo ya amsa, dole ya bishi, yaga kuma irin rayuwan da sukeyi, wanda ya tausaya musu sosai,,

  don haka yau data kasance jumma'a, kuma gobenta ne, daurin aurensa da suhymah, gudu sosai suke bisa hanyar Abuja, shida wasu abokansa, dake wasu motar, yana cikin shiga na alfarma, zaune kusa da barr. Abdullah dake driving motar,,

   inda zasu halarta lunch event din da Amarya da yen uwanta suka shirya, gashi kuma sunyi latti, gimbiyar sai kiranshi take a waya, duk ya damu, yaso su futo da wurine, harya leka wajen su ummeetah sannan su wuce, amma kam yanxun ba dama, amaryane da yake matukar jie da ita,,

   har suka wuce hanyar rugan su ummeetah, idonsa nakan wajan, ya numfasa yana saukar da kanshi da nufin yin magana, amman muryanta ya dakatar dashi, tana can bisa hill din da sukan zo kiwo, tana faman kwalla mishi kira, sosai take kiran sunanshi, tana bin motarshi da wani abokinsa keja a can gaba tana cigaba da kiransa, cikin sauri yake kallon barr.Abdullah da fadin,,

   tsaya tsaya Abdullah, ba shiru shima ya taka birki, sukai packing, yana futowa hankali tashe, besan me yasa ba yake jie a jikinsa ba, ba lafiya, sauran abokan ma ganin sun tsaya a dokar dajin, yasa suma suka tsaya, shima Abdullah futowa yayi yana fadin,,

   ban gane ba, wai kai sadeeq din take nufi? bai saurare shiba, ya nufi inda ummeetah ke gangarowa kan tudun da gudunta, tana zufa tare da zubar hawaye,

   ummeetah kar kiji ciwo fa, kie tsaya inxo, cewar sadeeq, amman bata tsayaba, sai data iso gabansa tana haki da shashshekan kuka, ya tsuguna da sauri yana fadin,,

   meya faru, ina Affahn yake?da kuka take nuna site din rugansu da fadin,,

   Affah......Affah nah, gida bashi da lfy, yace in kiraka yau kazo, jie yayi hankalin shi ya wani tashi, ya share mata hawayen yana mikewa dajan hannunta yake fadin,,

  tohh kiyi shiru, bari muje tare, ya karisa inda barr. Abdullah suke tsatsaye, suna kallon ikon Allah, yana fadin,,,

  ban key din motarka, ka hade dasu jameel a nawa, kuje ina nan zuwa, plsss ka lallasar mun suhymah yanxun zan iso nima, jameel ne yayi saurin fadin,, 

  what, me kake shirin yie haka sadeeq, kasan halin madam dinka, kuma kamata yayi yanxunfa muna wajan, amsar key din kawai yayi, yana bude ma ummeetah dayan site din ta shiga, kafun ya rufe yana zagayowa wajen zaman driver da fadin,,

   plsss ku gane, wannan ma yana da muhimmaci a gareni, kuje in sha Allah zamu hade, Abdullah zai magana, amman ya shige yana rufo kofan da yinma motar key, yayi reverse yana juyawa, da komawa ya dauki a'inihin hanyar da zata kai mutum rugar tasu a mota,,

  har lokacin ummeetah na zubar hawaye, alamar jikin mahaifin nata ya tsananta, ya rika bin yarinyan da kallo kafun ya maida hankalinsa kan hanya da dan numfasawa...........

  pin pinn pinn...shine abin da yayi saurin dawowa da sadeeq daga duniyar tunanin daya tafi, yana sauke wani ajiyar zuciya, da kallon driver dake yin slow da motar, yana fadin,,

   yallabai zamu tsaya mu kuma gyajin tank din motar, mai yayi kasa, handkerchief ya ciro yana share zufan saman kanshi, duk da AC dake cikin motar shi zufa yakeyi, kafun yace,,

   ouk, toh muje mana, ya rika bin katon gidan man aliko da suka kutsa ciki yana mamakin dama har sunxo nan.

comment
share
Matatace
*2019*

meemartjj...........✍🏻
[14/08, 14:29] Dala Grp: 🕯🕯🕯
            *MATATACE*
     🕯🕯🕯

     

story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjj

   
*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty Ummeetah and my Fa'ixation._

page 21&22

__________A hankali driver ke shiga da motar cikin gidan man, tare da samun waje yayi packing, jama'ane sosai, ga motocin na matafiya da suma suke barbaje a wajan, driver ya bude motar ya futa, yana kallan sadeeq da fadin,,

   yallabai akwai cikuwan mutane a wajan, bari naje na samu wasu daga cikin ma'ikatan wajen, kai kawai ya daga mishi alamar gamsuwa, daga haka driver ya maida kofan ya rufe,,
 
   ya rage daga shi sai ummeetah da suke zaune a baya, fuskanta na facing waje, ta glass take kallan jama'an dake kaiwa suna dawowa, ta juyo a hankali tana kallonsa, kanshi na kasa yana danna wayarsa, cikin wani sanyin murya take fadin,,

   Baffah plsss zanje waje insha isaka, gaba daya maganar sai daya amsa mishi cikin jikinsa, ya dago yana zuba mata ido, fuska ba annuri yake fadin,,

  duk AC dake cikin motar nan be isheki ba, ya karisa maganan yana dan kasa da idanunsa, turo baki ta danyi, da dan bata rai tana zuba mishi ido, a hankali ya dago idanunsa, shima yayi mata kuri, ta koki kauda nata idanun, dan tsaki yayi kafun yace,,

   don Allah jeki, karki cinyeni, murmushin tasa tana bude kofan ta futa, shima zafin ya jie yana jie, don haka ya bude kofan site din da yake kadan, yana kishingida tare da cigaba da danna wayarsa,,

   can wani dan tudu inda taga wasu classy enmmata, da yen uwansu haka, sun futo daga nasu motar suma suna hutawa, itama ta samu gefe daya ta zauna, tana jie suna yer hiransu ana dariya, ita dai ta cigaba da kallon jama'an dake kaiwa da dawowa a wajan,,

    masu tallace tallace kala kala, mutane daban daban, wata yer matashiyar yarinya ce, da bata fie shekarunta ba, siririya yer doguwa, kallo daya zaka mata ka gane bafullatana ne, kodan zanen dake fuskanta, sanye da hijjabi mai roba, sai yer zani data daura ya dingile can sama, katon tray din silver ne bisa kanta, mai dauke da bread, an tsitsirasu, tana tafe tana talla da fadin,,

   anse biredi, in taje wajan wannan motar taje nan, wani wajan a siya, wani wajan kuma ba'a siya ba, haka harta kariso inda su ummeetah ke zaune, tana kallon yen gayun mutan nan da fadin,,

   hajiya kuse biredi, cikin hausarta na fulani, shiru suka mata suna cigaba da hiransu, ta maimaita yafi so uku, ba wanda ya tanka mata, ummeetah na kallon komai, ko sun jita ko basu jita ba, oho, sudai hiransu suke, wata yer yauki dake gefe, tana zaune cute bag dinta ije a gefe, da suka hada ido da yarinyan, sai daukar jakarta tayi tana rungumewa, ganin haka yasa yarinyan barin wajen da sauri,,
   
    sai dai shigowan wani mai motane da gudu ta kan hanyar, yasa yarinyan yin baya, wanda yayi sanadiyar xubewan bread din nata, kadan ya rage bata fadi ba, wasu kuma daga wajan suka fara mata fadan laifin tane, na tsayawa a hanya da tayi, tuni idanunta suka kawo kwalla,,

   ummeetah ta mike da sauri, tan tayata kwashe bread din, kasancewan kan hanya ne, tare suka mike tana daura mata tray din da fadin,,
 
   yer uwa kiyi hakuri, yarinyan ta sauke ajiyar zuciya, da sharan kwalla tana fadin,,

   kawai don mutum an daura mishi talla, ya zama abin wulakantawa, nima a'i bason raina bane zaka rika yawo a titi, cikin rana kana wahala, komai munayi saboda mu samu abin da zamu cie, amman sai wulakanci za ayita ma mutum, cike da tausayawa ummeetah ke fadin,,

   Allah sarki, kiyie hakuri, wata rana sai labari, sorry kinji, share hawayenta tayi da murmushin, tana fadin,,

   bakomai, nagode da taimako, cikin harshen fillanci ummeetah ta amsa mata, harta juya ta juyo da zare ido, itama da fillanci take fadin,,

   lah, kina jin fillanci, kowa dake barayin wajen sai da suka juyo, don da karfi tayi maganan, ummeetah tai murmushi tana kallon both site da aka xuba musu ido, kafun ta daga mata kai  tana kuma bata amsa da yaren nasu, a'iko ta dire tray din sai faman yie sukeyi, kafun su nufi wajen booth din motar da yake zaune, yana kallon komai dake faruwa,,

     hira suke sosai, yarinyan ta dire tray din bisa booth din, nan suka shiga ciniki, ana daddaga bread din, shidai idanu kawai ya zuba mata, mamaki sosai yakeyi, har yanxun yaren na nan radau a bakinta, baya jin me suke cewa, yaga dai ummeetah ta ciro 1k cikin hijjab ta bata, yarinyan ta bar tray din nan, tana nufa wani waje kafun ta dawo rike ledan viva, sai canji data mika ma ummeetah, ta zuba bread din kusan guda biyar, kafun ta mika mata extra one,,

   yana kallo dai ana yer ki barshi, yarinyan na turewa da dan girgixa kai, alamar gyara ne, murmushi kawai yayi, da kauda kanshi, ummeetah gaba daya halayenta irin na mahaifinta ne, yaji dadin yanda ta taimaki yarinyan,,

    dagowan da zai kuma yie, sai neman su yayi ya rasa, da sauri yake dan dube dube, da nufin futowa daga cikin motar, can ya hangota da wasu enmmatan fulanin, dake dauke da kwarya bisa ka, da alama introducing dinta akeyi, sai faman fara'a take musu, ya numfasa, da sauke wata ajiyar zuciya, dai dai sanda driver ya dawo wajen, ya kallesa da fadin,,

  plsss mal. Nura kira yarinyan can taxo mu wuce, ba musu ya a'ikata abin da aka sashi, ummeetah naji kaman karsu rabu, yaran sai kallonta suke suna daga mata hannu,,

   duk suka bita da kallo, sanda driver ya bude mata booth din ratsatsiyar motar ta saka bread din, sannan ya zaga ya bude mata kofan baya ta shiga ciki, itama kallonsu take da musu fatan alkhairi, gefe daya tana gode ma Allah da Affahnta ya hadata da Baffahnta sadeeq, ba a barta a can rugan suba, da yanxun itama maybe tana irin wannan rayuwan,,

   ta numfasa sanda suke hada ido dashi, yana mata wani kallon tambaya, ta dan tsuke baki da murmushi, kafun ta dan noke da fadin,,

   kawaye nane, ya balla mata harara da fadin,,

  karukon kawaye, ya baki bisu ba, dan turo baki tayi, ya saki ajiyar zuciya da fadin,,

    shi wancan kayan bread dinfa da kika yi, ina zaki kaisu?

  ohh maami ce ta bani kudi inyi tsaraba, shine na siya, nayi ma su aunty batulah tsaraba, zaro ido yayi da dan mamaki yana fadin,,

  ya akayi kika san gidan batulah zamu? tai dan war da ido kafun tace,,

   naga a'i baku da wasu yen uwa a kano sai ita, shiru kawai yayi yana kuma mamakin wayanta, harta gane hanyar kano suke, saima yanxun ya tuno bai musu tsaraba ba, dole driver ya kira yana bashi wasu kudi, yayo musu siyayya nan ciki,,

    kusan 10minutes sai gashi ya dawo niki niki da kaya, ya bude booth yana zuba kayan, daga nan ya shiga motar, inda ya karisa da ita wajen da za asa ma motar mai, suka kuma mikar hanya.

   Gidan aunty batulah suka sauka, farin ciki ya baibayeta sanda taji yaranta nama uncle din nasu oyoyo, don sai sa'a zaka ganshi a gidanka, tunda yayi aure zumuncin su yayi kasa, ta girka wannan ta sauke wancan,,

    nan suka wuni, ya rika mamakin yanda yaranta harda na kishiyarta suka san ummeetah haka, haulat ma kanwar hibbat kanta ta tsefe ita dole sai ta mata kitso, tana jin dadin kitsota, yayar nasa ke sanar mishi a'i sun san ummeetah, tun zuwa bikin yayar su hibbat da sukayi, ya dan tabe baki da fadin,,

   ta fiye shige ma mutane da yawa, kinga yanxun fa da muka tsaya zamu sha mai, sai dana sa aka kirata, tabi yaran wasu fulani can zata bisu, dan dariya aunty batulah tayi da fadin,,

   ba haka bane, wani yaron yana da farin jini da kuma son mutane, bikin da suka zofa last 4months, kar kaga autan su mijina yanda ya like shifa sonta yakeyi, kadan ya rage ba muxo kd ba, sosai maganan ya daki zuciyarsa, amman saiya waske kawai suna wani hiran, tana cigaba da zayyane kyawawan halayen yarinyan,,

     sai after Azhar suka dawo shida kamaluddeen, junior brothern sa, daga masjid, sun jima suna hira, kafun su soma shirin tafiya, sukai sallama ana kewan juna.

    Daga nan zaria suka tsaya gidan aunty Amrah, itama taji dadin ganin dan uwan nata, nan ma mamaki yakeyi, ganin yanda su kausar yaranta suka makalkale ma ummeetah, banda inteesar yer 5months da haihuwa dake tsala kuka, ya dauki yarinyan, sai faman rarrashi yake, taki yin shiru,,

  ummeetah na daukanta ta goya a baya tayi tsit, nan ma complain yake ma yer uwan nashi, bayan su ummeetah su futa daga waje, tana dariya da fadin, ya daina mamaki ma, indai ummeetah dasu inteesar ne, shiru kawai yayi, a nanma sun dan juma kafun su tafi, su kausar na faman kukan zasu wajen maami da aunty mainat, nan dai suka taho suka barsu da kewa.

  kafun su wuce sai da suka biya family house dinsu, nan ma ya gaida yen uwa, da suka shiga sasan yayar Abbansu, wanda suke kira da goggon cikin gida, da yike bata wani san ummeetah ba, da yayi mata bayanin ko wacece, dan dariya tayi da fadin,,

  harna fara shirin saka guda, nasha wata yer amarya za kayi, ka kawo mun ita mu gaisa, kunya yaji da feeling so embrace, shin da gaske ummeetah tayi kama da kalan matar sadeeq, lallai ya kamata a siyo ma goggon nasu glass, da alama idanunta sun fara samun matsala,,

   ummeetah dai bata fahimce komai ba kan maganan, hankalinta na can kan TV, ita dai ta cigaba da tsitsiyeshi, da yike tana da wasa da dariya, tana cigaba da tsigale matar nan nasa mare son zumunci, shidai tsit yayi mata, har sanda ya gama musu wankan kudi, nan ma sukai sallama suka futo.

   A cikin mota ya rasa tunaninsa, mamaki yake yanda ummeetah ta tafi da zuciyar yen uwansa, waisu haka suke ne da saurin shiga rai, kuma lumshe ido yayi, sanda driver ke shararan motar bisa hanyar KD, komai na dada dawo mishi kaman yau yake faruwa..........
                 

                       ***

  Jiki a sanyaye yayi packing motar kofan gidan, ya bude ma ummeetah ma ta futo, sai dai mamaki yakeyi ko karya ummeetah ke masa, ganin yen uwan Affahn nata zaune bisa tabarma, wata zungureriyar redio ne, da kidin shata ke tashi, gefe ga sandunan rake ana faman masga, ga kuma kifi da yaji, shagalin rayuwansu kawai sukeyi,,

   yabi ummeetah dake kallonsa, kaman zaice wani abu, sai kuma ya fasa, ganin lamido dake matso su cikin sauri, cikin harshen fillanci yake mata magana, itama ta bashi amsa, shi yayi mishi jagora har ciki, yabi dakin jikan da kallo, kafun ya duka yana shiga ciki,,

  salati kawai sadeeq ke saki, sanda liman ya mike daga bashi maganin da kusan rabi da kwata, waje suke dawowa, kishingide yake jikin pillow bisa yer katifansa, cikinsa daya lakume ne, kawai ke bada alamar har lokacin yana numfashi, saboda lotsawar da tasowan da yakeyi da sauri da sauri, cikin tashin hankali yake fadin,,

   me yake faruwa, ya zaku bar mutum a irin wannan halin, babu asibiti, asibita ya kamata ku kaishi, bayani suke son yin mishi amman ya kasa fahimta, sai yaga kaman ma Affahn baya iya magana, cikin sauri ya futa yana fadin,,

  bari inxo, wayarsa ya zaro, yana lalubar numbern Abdullah da suke shirin shiga garin Abuja a lokacin, da yike garin yafi kusa da nan, a kidime yake rokansa ya bar komai yace hospital su taho da ambulance, zasu samesu ko a hanya ne, yana mishi kwataccan rugan,,

  Abdullah nason mishi bayani halin da ake ciki a nan, amma ya kasa fahimta, dole yabar komai na nan, yace mishi ga sunan zuwa, ya dawo dakin yana fadin, su saukeshi a sashi a mota, lamido yace,,

  ka tsaya ka fahimce abin da yake son fada maka, yana son kuyi wata magana ne, kwana uku kenan da yake ta fadan haka, cikin mamaki sadeeq ke fadin,,

  dama yana iya magana,,

  kwarai kuwa, cewar lamido, liman na fadin,,

   amman saika duka za kaji maganar nasa, mun barku lfy, daga haka suka fice daga dakin, dama ita ummeetah na waje tana faman rera kuka, ya duka da kyau yana kallonsa, gaba daya jikinsa yayi wani bakin safa, da tausayawa yake fadin,,

   sannu Aliyu, in sha Allah zaka samu lfy, bansan jikin naka yayi zafi haka ba, kokarin daga yen yatsunsa yaga yana yie, da sauri ya saka hannunsa cikin nasa, dake dan yauki yauki, saboda safar dake jikin fatar, kallonsa sadeeq yake, shi kuma ya zuba ma hannun nasu ido, ko yen uwansa kyamansa sukeyi, amman jubi yanda shi ya rukoshi, shi yasa ko so daya baya dana sanin abin da yake shirin a'ikatawa,,

   ya dago idanu daker yana kallonsa, da wani farin ciki a fuskanshi, na ganawan da za suyi da juna, kafun na Allah ya kasance a gareshi, shi kadai yasan abin da yake jie, ya numfasa yana bude baki da fadin,,

   abokina naju dadi da naga kaxo inda nake, inaso muyi wata magana, kuma in baka labari, sannan na rokeka alfarma, ya kuma numfasawa dayin shiru, shima sadeeq dan numfasawa yayi kafun yace,,

   ina jinka Affahn ummeetah, kuma ina sauraranka, dan damke hannun sadeeq yayi a nashi, da murmushin daya yalwanta a fuskanshi, yana jin dadin sunan nan, a duk sanda zai kirashi dashi , ya soma da fadin.....

    Nie Aliyu ina daga cikin yeyen mahaifin mu jumare, wato wanda ya haife mu, sai dai nie mahaifiyata, nie kadai ta haifa, kuma itace Amarya, sabanin uwargidan mahaifin mu, data kwatsa yeye, wasu sunyi rai, wasu kuma Allah ya amshe abinshi,,

   komai ya fara da hassada ne, baga kowa ba, saiga inna tah, wanda tun tasowa na, na lura mahaifin mu yafi sonta, killan don tafi mishi biyayya ne, kullum kuma ita tana gida, sabanin yer uwan zamanta da bata da wani a'ikin yie daya wuce tallan nono, kwata kwata babu tarbiya tare da ita, haka ma yaran data haifa, duniya kawai suka sani,,

   lokacin da mukai wayau sai mahaifin mu ya lura da yen uwana suna mishi algishshu cikin al-amuransa, don haka saiya daura nie akan komai da komai, hassadarsu ta karu garemu, ina fada maka, kaga irin wanna ciwon da nayi, shi mahaifiyata tayi ta rasu, ba wasu dangin azziki ne da ita ba, na koma tilo bawan Allah, lokacin da mahaifin mu ya tattaro soyayyan gabaki daya, ya dawo dashi kaina,,

   bakin cikinsu ya kuma karuwa, wata rana mun tafi yawon kiwo, can gabas maso yamma, muka hadu da wasu yen uwan mu fulani, cikin xur'a suke tafiyansu, abin nufi shine, matayensu da yeyensu, suna da matukar azziki na dabbobi, munyi zaman mutunci dasu,,
 
    lokacin da autarsu, wacce suka fi jie da ita duk cikin zuri'ar, ta nuna bata son binsu, mu take so tabi mu tafi da ita, abin nufi shine, aure take so a mana, kasancewan  muna mutunci nie da ita, kafun mu gane muna son juna,,

   wannan ya tada hankali yen uwana sosai, don kyakyawane, farar sol, kai duk inda zan fada maka, ta shafe diyarta ummeetah a kyau, duk da suna yaya yie da juna, anso akai ruwa rana, don duk ciki mahaifinta yafi sonta, amman yafi son abin da take so, don haka ya amince da sharadin ba zata kara ganin kowa nata ba, don muna da nisa da juna,,

   ta yarda da hakan, saboda son da take mun, nima kuma ina sonta, a wannan tafiya aka daura mana aure, mahaifina yayi farin ciki sosai, inda ya tsaya mun gaba, sanda zamu rabu, suka ware mata kason azzikinta mai tarin yawa, aka rabu ana kewar juna,, 
     
  haka muka dawo gida, na cigaba da kula da matata, mai suna fadima, mun zauna da juna tsakani da Allah, lokacin dana shiga jagorantan abin kiwonta, kasancewan ina da hannun kiwo, lokaci daya Allah yasa masu albarka,,

   wata goma cikinta ya tsufa, kullum ina cikin zullumin mezai

Please Login or Register in order to submit comment