Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tausayi, yana da taimako, wlhy kie yarda dani ba don wani abu nake sonshi ba, ko lokacin da mukai aure sadeeq bashi da wani kudi, a ganina ma mahaifina ya fishi kudi, daga baya ne sai naga ya kudance, ashe saboda ya hada da dukiyar kine, don Allah kie rokan munshi in koma kinji Yer uwa nah, da yardar Allah zan zauna daku lafia, wani farin ciki yasa Ummeetah fadin,,

  karki damu Aunty Suhymah, zaki koma dakin mijin kie da yardan Allah, na miki wannan promise din da zaran ya dawo, nasan shima har yanxun yana sonki kuma zai yafe miki, haka dai ta rika bata magana, tsantsan nadama kawai kake iya hange a idanun suhymah.

  ba'a kwana ba sai da Ummeetah ta musu settling gaba daya kudin a'ikin da ake nema na Najma, ta kuma taimaka musu sosai, kuka kawai haj. falmata da yagana sukeyi, sunma rasa bakin godiya don tsaban kunya da nadaman rayuwa.

  


         *BAYANwasu shekaru*

Mata ne sosai suke futowa daga dan madaidacin masallaci mai kyaun gaske dashi, bayan tashi daga majalisin da suka kare na karatu misalin 10am, ko wacce na kokarin yinma malamar tasu sallama, wacce tabi wasu tawaga suna futa gate din gidan, tare da wasu ma da suke biye dasu a baya.

  su biyu ne suko nufa kawataccan, yalwataccen cikin gidan, bayan sun gama sallama da yen uwan karatunsu, suna sanye da wata dark green din hijjabi na alfarma har kasa, ko wacce da littafanta a hannu.

  wash, ta fada tana dan dafe kanta dake sassara mata, cike da tausayawa ta kalleta tana fadin,,

  Yer uwas yadai ko ba lafia ne?, dan murmushi tayi tana fadin,,

  lah bakomai, kaina ne kawai ke mun ciwo, sai kuma yaran can da suke holiday, inna tuna zan shiga gidan nan ko, hmm kaina har dada amsamun yakeyi, yer dariya tayi tana fadin,,

  lallai tun yanxun, duka duka yaushe sukai hutun, karki damu dakin haura sama kidan sha magani kie kwanta, maybe kinsan kila gajiyan a'iki ne, ko kuma babyn……...

   a firgice ta zaro ido waje, ya sanya Suhyma sakin wancan maganar, tana tuntsurewa da dariya da fadin,,

  kinga maida wukar, daga magana sai ki kwakwalo mun ido, itama dan murmushi tayi da dafe kirjinta da yake bugawa tana fadin,,

  wlhy aunty suhymah har kinsa na tsorata, kirjina a 80-80 yake bugawa fa.

  hmmm, ta fada da jinjina kanta kafun tace,,

  lallai da gaske kike Yer uwas, gaba daya murmushi sukayi suna karisawa ciki.

  ya numfasa daga tsayen da yake cikin bedroom, ta wani mirror glass dake upstairs din aka rufe wajen dashi, zai iya ganin wanda ke waje, amma na waje baxai iya ganin na ciki ba, murmushi yayi yana dauke kanshi daga kallonsu tare da cigaba da shiryawan shi.



  ……...Cikin natsuwa take danna door bell din, yayin da Ummeetah ta jingina kanta da jikin bango, tana runtse idanuwa, da sauri ta rufe kunnuwanta sanda Fa'ix yaro dan kimanin shekara shida da haihuwa, ya bude kofan yana sanya ihu da fadin,,

  mummy oyoyo, maamaa oyoyo, tuni Nabeel da Eyman yaran munat da suka zo gidan hutu duk basu fie sa'an Fa'ix dinba, suma suka taso suna musu nasu oyoyon.

  ciki dai suka karisa shiga, mummyn na rungume dasu, tare da amsa musu sannu da zuwan da suke musu, yayin da Ummeetah ta yakice fa'ix dake jikinta saboda kanta dake cigaba da buga mata.

   yalwataccen falo ne mai dauke da abubbuwan ban shu'awa, can saman wasu royal chairs ina iya hangen Ishan d'an dabe wuce 12years a haihuwa ba, gefenshi kuma kaninshi ne Adil, d'an 10yearss da haihuwa, hankalinsu kwance suke kallon kwallo a TV kaman wasu manya.

  maamaa da mummy sannu da zuwa, duk suka fada suna kallon iyayan nasu, da murmushi Suhymah tace,,

  yawwa my boys, Baba nah ina kuka bar dayan Baban nawa?, Ishan dake faman bata rai, ya nuna hanyar bedroom dinsu da hannu yana fadin,,

  mummy yana ciki, da dan damuwa ta zauna bisa hannun kujeran da yake zaune tana shafa kanshi da fadin,,

  Baba nah yadai waya bata maka rai ne?, caraf Adil dake gefe yace,,

  mummy yaya Imaad nefa yake ta mishi gwalo, wai don uncle Abdullah ya kawo musu birthday gift dinsu, na yaya Ishan packet of chocolate, shi kuma na namesake din best friend dishi, sai ya bashi samsung galaxy Note 4, Ummeetah dake rike da karfen upstairs zata fara takawa zuwa sama cak ta tsaya, dai dai sanda mummyn nasu da mamaki take fadin,,

  what samsung galaxy Note 4, are yhu sure?, da tsallensa ya futo falon rike da wata yer kwali mai kyaun gaske da akayi rapping yana fadin,

  tararan, mummy da gaske yakeyi, kyautar galaxy phone na samu, ya karisa maganar da yer wakarsa, yana kara kwalin gefen fuskanshi da wani blushing, daga Ummeetah har Suhymah kallon kallo suka shiga yie da juna, kawai sai suka saki murmushi yana karisowa da fadin,,

  mummy gashi, dama nace saukin dawo zaki bude mun, a bude kowa ya gani yen black stomach su mutu, da hararan gefen da Ishan yake zaune ya karisa maganar, shima ya tabe baki yana cigaba da kallon TV hankalinshi kwance, sosai ta zauna bisa kujeran tana fadin,,

  ouk to bari muga wacce irin colour ne samsung galaxy din, da murnanshi shima ya samu waje ya zauna, duk yaran suka lullubeta suma suna son a bude, ita dai ummeetah girgixa kanta tayi tana haurawa saman da fadin,,

  wautan banxa.



  ……...Sanye take cikin wata yer pink straight gown, sai ta saka wata yer black design hijjab wanda ya tsaya iya cinya, ta futo da hannunta ta cikin hannun hijjab din, yayin data sakalo wani karamin pink veil a saman wuyanta.

  dan farin fuskan nan kawai kake iya hange, tana rike da wata yer cute I-phone a hannunta, kamar zatai kuka take takowa kasan downstairs din da kiran sunan,,

  maamaa, maamaa, dai dai nan sukai karo ita tana hawa ita tana sakkowa, ta dan dafe kanta tana fadin,,

  oh my god, waishin me yasa zaki ta kwalla mun kira ne, Zahra sunana baya miki wuya ne wai?, dan murmushi tayi a shagwabe take fadin,,

  sorry maamaa, ina son fa muyi magana ne?, harara ta zabga mata kafun tace,,

  oya jube kie, up to 14years, amma baki iya komai ba sai shagwaba, zaro ido waje tayi tana bin bayan maamaan nata data cigaba da haurawanta sama tana fadin,,

  maamaa shahararriyan tailor zahra AA ne za ace bata iya komai ba, cike da wani shagwaban take yin maganar, cak ta dan dakata tana fadin,,

  yawwa plsss zoki amsa key ma kije mota, kie kwaso mun saitin rigunan saka dana taho dasu daga makaranta jiya, zahraddeen zai zo ya amsa akai shaguna, tuni ta bata rai tana fadin,,

  maamaa me yasa sai wannan yaya zahraddeen dinne zai zo ya amsa, niefa bana son guy dinnan ya fiye yanga da yaw……...

  kallon data watsa mata ne ya sanyata hadiye maganarta, dai dai sanda suka iso wani kawataccan falon dake nan saman, cire hijjabin dake jikinta tayi tana mika mata tare da littafanta na makaranta, a ladabce ta amsa kai tsaye tana wucewa dashi wani bedroom dake gefe.

  ita kuma ta wuce wajen wata yer single sofa chair mai hade da table dinshi tana zama, sanye da wani riga da zani na super english, laptop ta jawo gabanta da wasu takardu ta fara duba wasu ayyuka.

  kusan 10minutes sai gata ta dawo rike da wasu kwallaye da akai packaging wasu sakan kayan sanyi masu kyau, kusa da kujeran da take zaune ta zubesu inda taga wasu kayan ma, tana fadin,,

   maamaa wai wannan sakan na wasu yen class ne?, ba tare data dago ba take fadin,,

  na yen class din Didin kie ne, nata na nan ciki, kudadanta itama sun fara yawa a account, (yarinyan da tace ma ummeetah yanxun bata dame siya mata silipers), da murmushinta ta zauna a gefe tana fadin,,

  yeee my Didi, maamaa Allah ya kara arziki, bata amsa mata ba, ta zauna itama a gefen kayan tana daga wani foam na kungiyan sana'oi da maamaanta ta kafa a makarantan,,

  Zahraddeen Uba Sa'i, ta karanta sunan dake jikin papern, matashin dan kimanin 24years, shine shugaban jagorantar kasuwancin, daya daga cikin marayun daliban da sukai candy a Aysha Humyhra Academy, passport dinshi dake manne a jikin takardan ta kalla tana dan tabe baki kafun tace,,

  wannan da dan wasu masu dashi ne, da anga banu a rayuwa, don tafiya ma wuya zatai mishi, ta zabga mishi harara da fadin,, 

  ko magana bai iya yinma mutane ba, sai an mishi, toh ke Zahra'u ina ruwan kie dash……...

  na'am kince mene, mahaifiyarta ta katseta da wannan maganar, da sauri ta fiddo ido waje tana wurgi da takardan, da murmushin yake take fadin,,
 
  ahh maamaa bance komai ba,,

  ouk, ta fada tana maida kanta bisa laptop din, itakam saita bata fuska kamar zatai kuka take fadin,,

  maamaa plss ina son muyi magana, kai ta rasa me yasa zahra ta cika kwakwa ne, ita dai kullum ta manne mata tana zuba shagwabanta, ta dan dago tana manna bayanta da jikin kujeran kafun tace,,

  ina sauraran kie, sai da taja wasu seconds sannan tace,,

  maamaa plss ina son kice ma Zeenah ta daina zuwa mana gida ne, da sauri ta fiddo ido waje, don Zeenah na daya daga cikin wadanda za'a kira best friend din Zahra, kuma neighbour din sune yer wata professor, da mamaki take fadin,,

  Zahra'u saboda me?, sosai kamar zata sanya kukan take fadin,,

  because she says she like my daddy, sansaransan Ummeetah tayi sai kuma tayi dan dariya, don ita abinma dariya ya bata tana fadin,,

  Zahra yhu are so funny, maybe she says that because ur daddy is so daring to yhu, luv, caring yhu know, amma ba da wani manufa ba, cije fuskanta tayi tana runtse ido kafun ta bude da fadin,,

  a'ah, maamaa ki fahimta mana, she told me that she like his voice, the way he smile, maamaa so many things, kuma Zeenah ta cika rainin hankali da yawa, mumma bata nace karta kara shigo mana gida, ita kuma tace saita shigo, sai dai in kyace ko mummy kuka hanata shigowa, serious take cigaba da fadin,,

 hmmm, Ummeetah ta fada, don tasan yarinyan idanunta a tsatsaye suke, ta basar tana cigaba da danna laptop din da fadin,,

  Zahra kie barni da wannan shirmen naki plss, ina ce mummyn kuma tace kie daina yawan zuwa inda yarinyan take, tunda ita ta zaba ta rika tara samari tun yanxun a rayuwanta,  kwaba fuska tayi tana fadin,,

  maamaa a'i itace take biyo nie har inda nake, maamaa plss do something, bana son daddy ya kara muku kishiya keda mumm……...

  waye kuma zai kara aure, ya katse musu maganar sanda ya futo sanye da wata danyar wagan bari, milk colour, hula da takalmi ma duk milk colour, ya wani kara dan kiba na hutu da kwanciyar hankali, sai dan kasumban nan daya bari sama sama, tayi mai kyau das a fuska, shagala kawai tayi da kallonshi, yayin da Zahra tasa ihu da fadin,,

  that's my handsome dad, ta fadi maganar da daga mishi dan yatsanta babba, shima daga mata fingern nashi yayi da fadin,,

  thanks sweetheart, ya daga ma Ummeetah gira da fadin,,

  yadai madam?, ajiyar zuciya ta sauke kafun ta mike tsam, sosai ta kara girma tare da dan cika, sai dai hutu da kwanciyar hankali sun boye shekarun nata, gashin nan na kwance ta baya, wanda ya futo ta daurin maryam babangida data rangada, hannu bibbiyu tasa tana dafa kafadarshi ta site din dama, har yanxun idanunta nakan fuskanshi, gira daya ya kuma daga mata alamar yadai?,,

  duk da ka tsufa amma ana yayinka?, wani kasaitaccan murmushi yayie yana fadin,,

  nie, waya ce miki na tsufa, har yanxun saurayi nake dan matashi, ya karisa maganar yana wani kashe mata idanu daya, yanda yayi maganar ya bata dariya, tana pointing kasumbanshi da fadin,,

  haba Abban su Ishan, duba fa ka ga furfura ne a nan wajen, a'iko kaga tsufan yaxo, tana mishi dan gwalo ta karisa maganar, Zahra dake gefe ta cunno baki da fadin,,

  maamaa plss kie daina cewa daddy nah ya tsufa, ya dage kafadarshi sama da fadin,,

  fada mata dai sweetheart, hararanta tayi tana fadin,,

  tsoho tsoho tsoho, shine sunan babanki, kixo kiga shaida ma a fuskanshi, da sauri ta taso tana leka kuncin baban, da murmushinta take fadin,,

  maamaa gudu biyu ne fa kawai, daddy kaji bari ma yanxun zan cire maka su, kada a rika cema daddynah tsoho, ta kai hannu kenan Ummeetah ta buge hannun da sauri, tana dafe wajen da fadin,,

  kina hauka ne, kina cirewa wasu ne zasu futo da yawa, daga daddyn har Zahra hada ido sukayi, sai kawai suka sanya dariya yana fadin,,

  ashe wata ma bata son mijinta ya zama tsoho, murmushi tayi tana wani shafa wajen a hankali, wani romantic look take bashi, bama tasan tana yie ba, hannunta daya har yanxun na samar kafadarshi, hasken plash din hoto da su kaji a kansu ne ya sanya su waigowa, tana dariya take kuma snaping dinsu da fadin,,

  perfect couple, Ummeetah tayi saurin janye jikinta don harga Allah ta manta da yarinyan a wajen, cikin fada take fadin,,

  zahra kin mai dani mate dinki ko?,,

  sorry maamaa, ta fada tana wani kanne ido daya da kama kunnita, rai a wani bace take kallonsa da fadin,,

  wlhy Uncle D kaja ma yarinyan ka kunni, in ba haka ba zanyi mata duka, yarinya duk yanda na janye jikina saita kwakumeni, shin nie kadai ne mahaifiyarta a gidan wai?, shima kama kunninshi yayie yana fadin,,

  sorry my yer fillo, a taimaka kar a taba mun ita, yarinyan da nake shirin yin mata aure nan da 2years za'a dakar mun ita, da sauri ummeetah ta fiddo ido waje, yace,,

  yes of course, ta kusa barin miki gidan kie shana yanda kike so, kallonta Ummeetah tayi, itakam saita wani rufe fuskanta da gyalen dake kafadarta wai kunya, ta zabga mata harara da fadin,,

  mara kunyar karya kawai,,

  kema haka, ya fada yana sumbatar lips dinta so lightly, da sauri ta dafe wajen da fadin,,
 
Abban Ishan, cikin kwaikwayon muryanta yace,,

  Ummun Zahra, kuma hade fuska tayi, ihun da suka jiyo daga downstairs ne, ya sanyashi dan yatsina fuska yana fadin,,

  lafia dai, ihun wa nake jie?, Zahra ce tayi saurin fadin,,

  daddy Imaad nefa, wai uncle Abdullah ya kawo mishi birthday gift dinshi na daban, shine yace wai samsung galaxy ne Note4,,

  what!, shima ya fada da mamaki, kafun yace,,

  a'ah, mu rankaya don kar ayi babu mu, Ummeetah dai murmushi tayi ta kashe laptop din sannan tabi bayansu.



  ***
Tana zaune tsakiyar yaran, tana karisa bude package din da tun daxu ya wahalar dasu wajen budewa, Imaad dake zaune ya harde kafa daya bisa daya yana fadin,,

  samsung……, sai kanninshi su karisa mishi da fadin,,

  galaxxxxxy, da sauri ya mike yana bama daddy wajen ya zauna da fadin,,

  yawwa daddy, zauna kaima kaga big phone dina,,

  toh yaron daddy, ya fada yana zama hannun kujeran, kafun a fara counting daga 12-zuwa kasa, da-dai sanda aka kammala bude gift din, tsadaddan kwalin shampen ya bayyana, har kana iya hangowa ta cikin transparent covern da yake ciki, sosai Suhymah ke gumtse dariyanta sanda take zaro kwalban da fadin,,

  wow expensive, ta kalli inda Sadeeq yake zaune, Ummeetah na tsaye gefenshi, dariyan shima yake gumtsewa, kawai saita nunashi tana fadin,,

  a'ah, sweetheart plss don't laugh, ya dage kafadarshi sama da fadin,,

  ouk, am not gonna laugh or say anything, sauran yaran take bie da kallo wadanda suka dauke kansu daga kan shampe din dake hannunta, suna maidawa kan Imaad da yayi wani gingiringin kamar ya nutse don kunya, Zahra ce wacce ta fara bushewa da dariya tana fadin,,

  shammmpen, sauran kuwa duk suka amshe da fadin,,

  galaxxxxxy, tuni Suhymah tasa dariya, shima dariya yakeyi da dafe habarshi da hannu, Ummeetah ma dake gefenshi dole ta dara, kowa ya sanya dariya, harda Ishan daya taso ya amsa kwalban yana dagawa sama da kwatanta yanda Imaad din ke prouding kafun a bude.

  me zai yie banda rarumar wani trow pillow yana bin dan uwan nashi dashi, tuni aka fara kokarin yin dambe kuma, sai daya tsawatar musu sannan suka nastu, Imaad ya kalli Zahra dake raguwan dariyanta yana fadin,,

  daddy ka gani ko, Aunty Zahra taki daina mun dariya, kallonta yayi yana fadin,,

  zahra'u ya isa haka, duk a daina mishi dariya, ya dube Ishan yana fadin,,

  kuna twin brothers kuna fada, ku daina fada, cos nie da abokina dan fillo bamu fada, Aliyu da sadeeq ba fada a tsakanisu sai zallar mutunci, ku zama yara na kwarai kunji, kansu suka jinjina, Imaad na fadin,,

  daddy to kace su daina mun dariya, nie bansha shampen bane, na daukan samsung galaxy ne, wani dariyan ake kumshewa, mummynsu ta maida nata daker tana fadin,,

  toho kaji Baba nah, kuma mai gidan na kammu, wajenta ya nufa tana rarrashinsa, yayin da daddyn ya cigaba da fadin,,

  oya a daina mishi dariya, if not toh tabbas yayan ku zai koma yau dinnan, da sauri kowa ya natsu harda Zahra dake fadin,,

  daddy plss we are sorry, baxa mu karaba, kar a rabamu da big brothern mu,,

   yes nima plsss a barni, kar a rabani da yen kanni nah, ya fadi hakan sanda ya futo daga hanyar site dinshi, duk ido aka bishi dashi, sanye da wata milk din yadi iri daya dana babanshi, sai dai shi  wandon nan a dagale, ina fada muku real ustaz, yaro fa an girma yanxun yana kusan shekara 22years kenan,,

  Assallamu alaykum, shine abin daya fada yana karisowa harabar falon, duk suka amsa mishi, ya kalli iyayenshi da fadin,,

  daddy na futo, mummy barka da gida, maamaa sannu da hutawa, ummeetah ce ta amsa da murmushita tana fadin,,

  yauwa yaro nah, ina alfahari da kai, yer dariya yayi yana fadin,,

  nagode maamaa nah, Zahra dake kashe mishi hoto, da sauri yake kare idanushi da hannu, Ishan ya bata rai da fadin,,

  kai Aunty Zahra kin fiye son daukan hoto, bata rai tayi itama tana fadin,,

  eh din, eh din an dauka, ganin ta bata rai ne, cikin sanyi da tsantsan natsuwa yake fadin,,

  no my sweet kanwa, in zaki mun hoto kie dena sanya plash, saboda bana son haske fahimtun, da murmushinta ta gyada kanta da gamsuwa, ya jawo hannun Imaad suna zama da fadin,,

  haba my little bro i know how to remove this mood in ur face, ya sanya hannu a aljihu yana ciro wani tsadaddiyar head phone a kwalinshi, murna ya sanya yana tsalle, su Ishan ma da Adil duk suka matso ya basu nasu, sauran kuma yace tsarabansu saiya bude kayanshi, Nabeel ya matso yana fadin,,

  yaya Irfan nie dai momma ta tace maka motan sojoji nake so ko?, yana murmushi yace,,

  yes mr soldier karka damu, ya kalli su Imaad dake cigaba da murnansu suna bubbudewa da ganin na juna, yana fadin,,

  kunga gaba daya complete qur'an ne a ciki, idan na samu wani abu sabanin hakan zanyi duka seezing dinshi, da sauri suke fadin, baza su a'ikata hakan ba, sadeeq dake zaune yana kallon yaran nashi cike da farin ciki ya mike yana fadin,,

  toh mu zamu wuce, Suhyma ta kalleshi da fadin,,

  sai ina haka?, ido daya ya kashe mata, kafun yace,,

  zan dan shiga office ne, shima Irfan na dan fara nuna mishi yanayin ayyukan, daga nan zamu wuce mu gaida su maami, in sha Allah tare da fa'ixa zamu taho, kinsan nayi missing yer autana 2days kusa dani, tana dan dariya takai bakinta dai dai saitin kunninshi tana fadin,,

  wata yer auta, ina fada maka mutumiyar naka dazu muna hada breakfast, tana jin kamshi kwai duk ta wani rikice, um...um...um, ka gane a'i, da sauri ya kalli inda Ummeetah take tana fadin,,

  kai Aunty Suhymah, dubanshi ya dawo dashi kan Suhymah, a wani rude yake fadin,,

  kai haba, amma gaskiya angel kin iya bada daddadan labari, dole ne a saka miki da sakamako mai kyau, ya kalli Irfan da fadin,,

  Irfan ka tuna mun in mun futo, mu biya ta moto Range dinnan, dole ne a samo ma mummyn ku koda wata yer hummer4 ce, Zahra tasa murna da fadin,,

  Allah ya biya daddyn mu, plss daddy inje in shirya zan taya yaya Irfan zaba ma mummy motar nima, kai kawai ya gyada mata, ta juya ciki da sauri, cikin sanyin murya tayi murmushi da fadin,,

  ka dawo da wuri pls, ur lunch is gonna be ready in time, Ummeetah ta amshe da fadin,,

  and ita ganno be ur favorite, kanshi ya jinjina yana mai cike da farin ciki, kafun yayi magana fa'ix ya rigashi, serious dan yaron ke fadin,,

   daddy kaji dadi kai dan gatan su mummy ne, lallabaka akeyi kullum kaci abinci, muko sai an doke mu wani time din, gaba daya dariya akayi, ya wuce yana fadin,,

   kunga idan na biye naku, baxa ku barni in futa ba, suka fuce su uku, duk sai sun dawo sukai musu, ya karisa futa yana ma Allah godiya daya bashi wannan kyakywan zuri'a.

 

  ***
Misalin 1:25pm sun kammala hada special meal dinsu, tsaye suke a wani tsantsararran dinning area suna ta jera expensive warmers din bisa dinning table.

   Ummeetah ce sanye cikin wani dinkin atamfa na super sharoton, dinkin pited riga da rapper skirt din daya bude, tasha daurinta.

  sai kuma Suhymah dake sanye da wani dinkin atamfa na super wax, dinkin pited play da single zani, itama tasha daurinta, daga mai red lips, sai mai pink lips.(aradu mata fiye da daya dadi ne dasu, ka juya nan kaga fara, ka waigo nan kaga baka……...lol). 

  da murmushinta ta kalli Ummeetah tana fadin,,

  kai amma Yer uwas kinyi kyau, dinkin ya amsheki, Ummeetah dake murmushi tace,,

  kema aunty Suhyma wlhy kinyi kyau, dinkin kamar bana yarinya ba, da sauri ta amshe da fadin,,

  kedai bari, a'i ina alfahari da yarinya tah, don zahra tana kokari, kinga wanda tayi ma Hibbat na sunan babynta sunyi kyau, Zahira ma tace inta haihu duk ita zata kwaso ma kayan ta dinka mata, murmushi kawai Ummeetah tayi suna cigaba da jera kayan abincin, da sauri ta kuma fadin,,

  yawwa Yer uwas kinko yie gwajin nan, dana baki shawara, kamar zatai kuka take fadin,,

  nayi Aunty Suhyma kuma wlhy positive, yanda tayi magana yabata dariya, ta hau kuwa tuntsura mata, ta kuma marairaicewa tana fadin,,

  au Aunty Suhyma dariya ma kike mun, da sauri ta dakata tana rike ciki da fadin,,

  sorry Nawan kyece kika bani dariya, meye a tsoron haihuwa na shida, tace,,

  Aunty Suhyma ba zaki gane bane, in aka koma hutu, ina da ayyuka da yawa, ga cikin nan kamar da laulayi yaxo mun, nie gaskiya daya dawo zan mishi complain, da sauri tace,,

  a'ah Yer uwas kar kice haka, kinsan halin Sadeeq sarai baya son complain irin haka, kiyi hakuri kie gode ma Allah, wasu ma suna son haihuwan amma basu samu ba, ta taka har gaban Ummeetah tana ruko hannunta da fadin,,

  a kullum na bude ido nah a gidan nan, kinsan me nake son fara gani, girgixa kanta Ummeetah tayi, ta numfasa tana fadin,,

  Ummeetah ye'yen kie, wanda nasan nima kamar ye'ye nah suke, duk sanda na kalli Zahra, Ishan Imaad, Adil, Fa'ix, Fa'izat, nakan jie gaba dayansu tamkar Irfan, gaba daya so iri daya nake musu, ye'yen nan suna sani farin ciki, idonta suka cicciko da kwalla tana fadin,,

  na baki bakin ciki mai yawa a rayuwa nah, ke kuma kin saka mun da alkhairi, kin bani farin ciki, Umeetah kullum jie nake kamar nayi ta zubewa bisa gwiwa nah, ina baki hakuri, kullum saina roki gafarar ubangiji, na kasa……,, da sauri Ummeetah ta katseta da fadin,,

  a'ah, Aunty Suhymah don Allah kie daina fadin haka komai ya wuce fa, mun zama tamkar yen uwan juna, abin daya rage mana kawai shine, mu manta baya mu daura gaba, tare da yinma mijin mu biyayyan aure mai daurewa.

   kanta ta girgixa tana share kwallanta da murmushi, dai dai sanda ake matsa door bell din gidan, ta dan juya tana fadin,,

  oh kin jima ina tunanin sune suka dawo, Ummeetah tace,,

  su nema don

Please Login or Register in order to submit comment