Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

me yasa kuke irin haka ne?, baku ganin condition din da take ciki, don Allah ku bari mana, aunty batulah taja hannunta tana fadi,,

  muje kawai, aunty Amrah dake gefen ummeetah ta kashe ta tsare, tace,,

aunty ku kira goggon cikin gida ne, hibbat dake gefe ta sharen hawaye itama tace,,

aunty Amrah a'i goggon cikin gida sun futa da mama umma,,

ya salam, ta fada tana dan tsaki da zabga masu mummy harara, wadanda ke masifa makarrabansu na tayasu baji ba gani.

 A can cikin gida kuwa, kan maami yayi zafi da bakin data tara, aminan azziki, ba abin da kika gani sai yer hakorin makkan dake faman kyallawa a bakinta, sai fara'a takeyi, don haka koda suka sameta da zancen, cewa kawai tayi su kira mijin yaxo ya dauki abinshi, ita tana fama da jama'a, bata da lokacin masifa, dole haka ya rage a garesu, munat ta kira ta shaida mishi.



   ……...Hankalin kowa ya maida kan gate din da ake faman jera horn, da sauri mai gadi jiki na rawa ya wangale gate din, cikin tukin kwarewa da natsuwa ya kariso yana idda packing da azama, cikin sabuwar kiran corolla daya hayo, kowa ya zuba ma motar ido, ana mamakin ko wanene.

  kafar damanshi ya fara sawowa waje dake sanye da wata tsadaddiyar takalmi, sannan ya idda futowa, cikin wata danyar black yadi, mai kyaun gaske daya saka, rigar iya gwiwa sai hannunta karama, kanshi babu hula, wannan ya bada damar ganin lallausar sumar kanshi dake kwance, tare da sajen daya gangaro mishi gefen zanen mallacinsa.

sai mamaki yen uwan suke yanda ya kara sanjawa, hutu da jin dadi ya zauna mai sosai, daurewa kawai yayi yana takowo, amma sosai zuciyarsa ke tafasa yanda yaga jama'a damke a wajen, kaman wani filin dambe.

kallo daya tayi mishi ta kawar da kanta tana runtse idanu da wani irin takaici, duk sai taji wani haushin shima take jie, hibbat dake kusa da ummeetah taja baya, baice da kowa kalla ba yasa hannu yana jawo hannunta dake dafe da cikinta, cikin sanyin murya yace,,

Humaira muje ko?, kafadarta ta noke tana ja da baya, har lokacin hawaye na cigaba da kwaranya a idanunta, su mummy kam kallon mamaki suke binshi dashi, ganin zata bata mishi lokaci ne, yasanya shi sakin dan guntun tsaki, sai wani kasa kasa yakeyi da kai.

hannunshi ya zagayo dashi ta saman kafadarta yana tallafowa, da sauri mummy taja da baya, sai daya lura sosai ba maami a wajen sannan ya sungumeta cak, a razane ta bude idanuwa tana sanya hannunta ta daura bisa kafadarashi.

cikin ido suke kallon juna, kamar yaune rana ta farko da suka fara ganin juna, hawaye ke cigaba da sauka saman fuskanta, ya dan nisa yana lumshe idanu, kafun yasa kai yabar wajen, yana jin doguwar salatin da haj. falmata ta sanya, kasa kawai ummeetah tayi da kanta, da wani kunya dake dawainiya da ita, aunty Amrah ta saka guda da tsiwa, kowa kallonsu suke, musamman yen matan wajen maybe sun burgesu ne.

  kamal ne yaxo da sauri ya mai bude motar, site din kusa da driver, shi kuma ya duka ya sanyata ciki, yana ijeta ta fashe da wani irin kuka, baibi ta kanta ba ya maida kofan ya rufe, site din driver ya zauna, kamal yayi musu tranfer trolley biyu daga paradon zuwa booth din corolla, yaja motar suka bar gidan, komai a idanun muheet daya shigo gidan kenan, still da zugan abokansa, yayi kwafa kawai ya wuce.

 

……...Aunty batulah ne ta dan rike haba da fadin,,

ohh nie batula, rashin kunyan turawan zai gwada mana, aunty mrah ma murmushi tayi tana fadin,,

to ya son ranki mutum da matarshi, a tare sukai dan dariya, harda munat dake dan murmushi, nan kuwa rigima yaso ballewa, dawowar yayan Abbansu gidan ne, ta kashe zancen taron ya watse.

mutane da dama na kuma juya al~amarin da mamaki, ba abin da wasu ke fadi sai matar mutum kabarinshi, yayin da mukarraban suhymah suke cikin wani hali.



...……A daki suka kule haj.falmata sai sumbatu takeyi tana fadin,,

shikenan suhymah ta a'ikata kuskuren da har abada ba zata daina dana sani ba, da sauri mummy dake faman raira kuka ta dago da fadin,,

haba yaya falmata karki mata baki mana, komai zaizo da sauki, kaiwa takeyi da dawowa tare da yarfa hannu tana fadin,,

yagana wani sauki, kina kallo yagana diamond ne hannunta, diamond ne kunninta, yagana diamond ne wuyanta, wani sauki kuma, ta karisa maganar cikin tashin hankali daya sanya mummy rasa abin fada, tana kuma fashewa da kuka. 



                          ***

Kuka sosai takeyi bil hakki da gaskiya, har suka isa wani katon gida gate man ya wangale gate yana faman kwasan gaisuwa, a hannunshi ya amsa wasu bunch of keys sannan ya karisa da motar packing space.

ya karisa kashe motar da sauke wani ajiyar zuciya, kaman zai tanka mata sai kuma ya fasa, ya bude site dinshi yana futowa, site dinta ya nufo zai bude, ganin haka ya sanyata saurin bude motar ta futo tana faman share kwalla, yayi dan murmushi kasa kasa  kafun ya kulle motar suka shiga ciki.

ta yaba da kyawun gidan, dama tun daga waje ta lura dazai kawatu, bare kuma ciki, yanda ta lura sabon gidane, kuma komai sabo ne a ciki, ta rika zabga ma gidan harara duk da kyaun da yayi mata, a zuciyarta tana ayyana,,

wani shegen gida sai girman tsiya, wannan a'i in wani abin ya faru da mutum shi kadai, saiya gama kare neman taimakonshi ba ajishi ba bare axo……, lallausar maganarshi ne ya tsai da ita da yake fadin,,

madam muje ko?, upstairs ya nuna mata, sai wani ciccika take, ta fara hawa matakalan da wani kalan yanga, a'iko stairs din farko ta kusa turgudewa, da sauri ya sauke hannunshi samar kugunta yana fadin,,

careful fa, kar kije kiji ciwo keda babys dinmu, tsamm tayi kafun tasa hannunta ta zare hannayensa da har lokacin suke zagaye saman kugunta, tayi wasu yen sakwanni kafun ta juyo da fadin,,

ka barshi zan iya, bai iya amsa mata ba sai ajiyar zuciya daya sauke, ya bita da kallo harta haura saman sosai, kafun yabi bayanta.

wani kayataccan bedroom suka yada zango, ta samu waje ta coge tsaye, idanun nan sunyi luhu luhu don kuka, shikam bakin gado ya samu ya zauna, yana dafe kanshi da hannu bibbiyu, kamar daga sama ya jiyo sautin kukanta sosai take rerawa, ya dago kanshi da sauri yana kallonta,,

da gaske takeyi, shine abin da yake ayyanawa, baya son kukan nata don yana taba heart dinshi, hannunshi ya mika mata da fadin,,

baby fulani nah, zoki fada mun meye damuwan, kinsan bana son mrs dina suna damuwa, musamman a irin wannan condition din, girgixa kanta tayi daga inda take tsaye tana fadin,,

nidai bana so, cike da rashin fahimta yake fadin,,

baki son mene?, ta make kafada kafun tace,,

Baffah bana son wannan auran, plss&plss, ban dace da kaiba, bana son ana cigaba damun kallon mayaudariya, don Allah kayi hakuri bana son wani matsala tsakaninka da aunty suhymah, ta karisa maganar da wani fashewa da sabon kuka, daya haddasa mishi sarawan kai.

mikewa kawai yayi, ya fara cire rigar dake jikinshi, white singlet din dake ciki ya bayyana, tana can tana raira kuka sai ganinshi tayi a gabanta, zai ruko hannunta, a razane ta matsa baya, yace,,

Humaira meye haka ne?, girgixa kanta ta shiga yie da fadin,,

a'ah, bana so plss, baya baya ta soma yie yana binta, ta cigaba da yarfa hannu da kuka take fadin,,

ban taba jin na tsani kaina ba, irin na yau, tayaya zan zauna da mijin daya wuce da matsayin yer talakawa iri nah...……,,

bata karisa ba ya cafko hannunta tare da jawota gareshi caraf ya daura bakinshi bisa nata, ta soma mutsu mutsun kwacewa, amma ina ya mata ruko mai kyau, tuni darasin ya soma ratsata, ganin suna kokarin zubewa a wajen ne, ya sanyashi daukanta cak sukai gado, nan kuwa labarin ya sanja.



   ……...Wanka ya futo daure da towel, sai wani karami dake rataye bisa kafadarshi na dama, ya sanya hannun damanshi yana sarce ruwan dake sumar kanshi, bude idanunta tayi a kanshi tana kallonshi, suna hada ido ta wani waske tana lumshesu.

da murmushi ya zauna a gefenta yana cigaba da sarce ruwan kanshi a fuskanta, cike da tsiwa ta bude idanunta tana yarfa yen yatsunta samar fuskanta da fadin,,

umm umm, yayi wata yer murmushi mai dan sauti kafun yace,,

madam ba zaki wanka bane?, yamutsa fuska tayi cike da kasala, ya daura hannunshi samar kanta da huci ke futa, cike da kulawa yake fadin,,

plss tashi kiyo ko alola ne, in yaso daga baya in kika tashi sai kiyi wanka, amma baya yuyuwa ki kwanta a haka kinji, ba musu ta daga kanta alamar gamsuwa, tana yunkura da mikewa zaune,,

washhh, ta fada da dafe kanta hannu bibbiyu, da sauri yace,,

ciwo ko?, nan ma kai kawai ta daga mishi, yace,,

eyyah sorry kinji, futo bayin sai kici wani abin kisha maganin, ya mike yana dauko mata towel, tare da taimaka mata ta shiga bayin, jallabiya ya saka mai yakkaken hannu ya nufi katon kitchen din dake gidan.

sanda ta futo wanka, tsaf ta samu wata arebain jallabiya, da kuma hijjabi, shiryawa tayi kafun ta dau dadduma ta shifida tana kabbarta sallah harta idda, ta shafa addu'ointa tana dan kwantawa a wajen.

dauke da wani tray da jero supergetti ya shigo, tun daga kan kamshin abincin ya burgeta bare ita da take jin yunwa, ta zauna tana tattankwashe kafa, shima zama yayi yana fadin,,

bari na baki a baki, kinsan ke amarya ce fa yau, da dan mamaki take fadin,,

amarya kuma?, serious yace,,

yes amaryan muheet mana, ko bakisan kece amaryan da da zai aura ba, yace kece first luv dinshi?, a razane ta dafe kirjinta tana fadin,,

niee?, yace,,

of course, haka ya fada ma kowa, shi yasa cikin rashin sani Abba yaso bashi auran kie, nima sai nayi tunanin ko shine na farkon a zuciyarki, kamar bata fahimce mai yace ba ta dukar da kanta kasa, harya cire rai da zatai magana sai kuma tace,,

Allah shi kyauta, to hell with him, yaji dadi sosai a zuciyarsa, amma a fili sai yace,,

muheet din, big guy irin shi, to wanene na farko farkon ne?, sai data dago idanuwa ta wani kyalla mishi, a zuciya yana raya,,

shegen wayaun tsiya, kafun ta dan tabe baki tace,, 

wani ne, kuma yana cikin raina sosai, yanda tayi maganar da serious duk saiya damu kanshi, ya bsta rai yana fadin,,

kina da auran kike fadan wani na cikin ranki, da sauri tace,,

oh sorry, ka tambayen ne shi yasa, ta karisa maganar tana wani dan langwabar da kai, yaja dan karamin tsaki sanda wayarshi ke ringing, mikewa yayi yana fadin,,

cie abin kie, nama fasa bakin, harda hararansa ya karisa maganar, wanda ya kusa sa ummeetah dariya, ta gimste dai tana fara cin abincinta, shiryawa ya shiga yie ta kauda kanta, harya kammala shirinsa cikin golden din tsadaddiyar gezna, kyallinshi kawai ya isa ya tona asirin tsadarshi.

karamar rigane mi karamin hannu, wanda ba a'iki ko kadan a jiki, cuku cukun da taji yana yine, ya sanya ta dago ido,,

wow, masha Allah, shine abin data ayyana a zuciyarta, tana mai kare mishi kallo, sanda yake gyatta babbar rigan da yaji golden din a'iki na alfarma, suna hada ido saita waske da fadin,,

Baffah bafa kaine angon ba, sai daya juyo sosai don ya tabbatar da ita tayi maganar, da murmushi yake fadin,,

Humaira manyan mutane sai da babbar riga, maganar yaso bata dariya a zuciyarta take raya,,

ummm su Baffah son girma, sai kuma tayi dan murmushin ita daya tana murza fork cikin taliyan da taci ta koshi, kafun ta dan dago tana dan kallonshi, caraf suka hada idanu yana kashe mata idon dama, ba bata lokaci ta mayar mishi da kashe mishi idonta na hagu, a tare sukai dan dariya, tana fadin,,

amma karfa kaxo kafi angon aunty munat kyau, kasan yau ranar shine, baiyi magana ba sai cigaba da daura agogan da yayi a hannu yana yer dariya, ya gama ya murza wata tsadaddiyar hular saki, ta mike tana kauda tray din gefe daya, dai dai sanda yake juyowa da fadin,,

hmmm, amma fa enmmata ina son wannan salon naki, to nagode kwarai da yaba wannan shiga nawa da akayi, ta dan turo baki a zuciya tana raya,,

nidai ban ceba, sai kuma ta kariso tana daukan turare tare da fesa mishi, sai wani ciccin magani takeyi, harta taimaka mishi ya kammala shiryawa tsaf, komai takeyi binta da ido kawai yakeyi.

wai nan fushi takeyi, hoo ummee tah yer rigima, ya karisa tunanin d jawota jikinshi, yana wani lumshe ido, sai da suka bata wani lokacin a nan, kafun tasha drugs dinta, ya wuce sai jaddada mata yake ta kula da kanta, ba zasu dade ba zai dawo, ciki ta koma bayan tafiyarsa tana faman leke leken ko ina.



                           ***

wajajen 4pm suka dawo gidan, bayan sun samu motar ta tashi da ker, suna faka motar ta futo ta nufi cikin gida, har wani dishi dishi take gani, tun a falo kanninta suka tareta da kuka kamar wanda suka rasa mahaifi, tasha jinjin jikinta tana karisawa cikin dakin.

wani harara mahaifiyarta ta sakar mata tana jan doguwar tsaki, jakarta ta aje bisa mirror stool tana fadin,,

mum meya faru?, kaman jira takeyi ta harzuko da fadin,,

me kuwa zai faru, shashashan duniya na kasa baki daya, dakikiyan duniya na kasa baki daya, wawiya wacce bata san me duniya ke ciki ba, cike da nuna tsananin mamaki take jefo mata tambayar,,

suhymah ke ko kina ina, har mijin kie zaima yer a'iki ciki baki sani ba, dafe kirji tayi tana runtse idanu,,

da gaske ne kenan abin data gani a waya gaskiya ne, surayya data biyo bayanta ta cigaba da sauraran duk bayanin yanda lamarin ya faru, sama sama take jinsu saboda tsananin tashin hankalin data shiga, so take numfashinta ya dauke ko zata huta, amma hakan ya gagara.

ta kama labule ta saki tana dafa bango, mummy ce da sauri ta rukota tana zaunar da ita, har lokacin hawaye ya kasa zuba daga idanunta, a rikice take fadin,,

aunty Irfan, Irfan, Irfan, an yaudareni an cuce rayuwa tah, da sauri aunty ta dafe mata baki tana fadin,,

a'ah daughter kar kice haka, nifa ba yarda da labarin nan ba, banma yarda sadeeq zai iya yin wani abu makamamciyar wannan ba, da sauri ta mike zumbur tana nufa wajen jakarta, ta fisgi gyallenta tare da jakar ta nufi kofa, da sauri surayya ta rukota tana fadin,,

suhymah ina zaki?, a rude take fadin,,

aunty tayi gaskiya, dole sai naje na gane ma idanuna gaskiya, daga haka ta futa fuwww, duk suka biyota suna kiranta, tuni ta nufa wajen motarta kirar wata tsadaddiyar jeep, a haukace ta figi motar mai gadi na bude mata kofan ta fuce a sittin.

driving kawai takeyi, wani abu ya tokare mata kirjinta, sanda ta tuno da maganar mum dinsu da tace a gabansi ya dauketa cak,,

lallai sadeeq ka taro tashin hankali, ta ayyana hakan da zaro wayarta ta shiga dialing numbernshi na nan kasan, ba bata lokaci kuwa ta samu ya shiga, da addu'oin dake bakinshi ya daga wayar, tambayar dai da yayi zato itace.

wayan takeyi kawai tana sauke ajiyar zuciya da girgixa kanta, a karshe kawai saita katse wayar, kuka takeson tayi amma yaki zuwa, ta kuma fisgar motan, sanda yake faman dawo mata da kiran, ko kallo wayar bai isheta ba, harta faka a katon gidan nashi.

sai da driver yasha zagi, kafun ya ganeta yana bude mata gate din, ta kutsa ciki, cikin sanyin taku ta karisa ciki, tana bin ko ina da ido, tana mai cike da fargaban abin da zata gani, a haka ta fara taka matattakalan stairs din da haurawa sama.

tafi karfin 5minutes kafun ta yunkura tana tura kofan bedroom din da take jiyo motsi kadan kadan, dai sai sanda ummeetah ta futo daga bayin daure da towel, wanka ta kuma yie bayan tayi sallar la'asar saboda zafin da taji tana jie.

baby zara'u dai ita ta fara ma suhymah sallama, kowa nama juna kallo kallon, ummeetah fargaba ne cike da zuciyarta, sai dai hakan bai hanata furta duk addu'an da taxo bakinta ba, yayin da suhymah ke cike da rudanin gasgata abin data gani.

kamar mutumiyar azziki takariso wajen dresing mirror tana ije jakarta da key, yayin data dago wayar ummeetah dake ijiye samar dresing mirror tana jujjuyawa, hannu tasa tana kunna wayar ta kawo haske nan kuwa hotan mijinta ya bayyana, wani ajiyar zuciya mai sauti ta sauke, tana runtse idanuwanta.

lallai wayar ma iri daya da nata, sannan a gidan da ita ta zaba aka gina musu, ya kawo wata ta rigata fara shiga, ta bude idanunta da suka sauka kan cikin ummeetah, cikin daci take raya,,

fool suhymah, ina can ina hauka munyi ankon night gwon, ashe abin ya wu……..., bata karisa tunanin da takeyi ba, ta watsar da wayarta hade da key din mota bisa gado tana futa a zabure, ( nie kam nace ummeetah maza ki sama dakin key kafun ta dawo), amma ga mamaki na, sai naga ta maida hankalinta kan wayar suhymah dake kawowa yana daukewa mai dauke da rubutun,,

my baby boo, murmushi naga ta sanya ta daga wayar hankali kwance, a rikice yake fadin,,

suhymah, suhymah plss kie saurareni kar kije gidan nan,,

Baffah nah, ta fada cike da muryan shagwaba, ajiyar zuciya ya sauke yana fadin,,

Humaira kece, ta kariso kenan, meya faru ta miki wani abin ne?, kanta ta girgixa duk sai ya bata tausayi, atleast dai tasan ya damu damuwanta, cikin muryan kwantar da hankali take fadin,,

Baffah karka damu, in sha Allah babu abin dazai faru, ka kwantar da hankalin ka, a rikice yake kuma fadin,,

tayaya zan kwantar da hankali na, bayan suhymah tana gidan nan, daga ke sai ita……...,,

sai kuma Allah daya hallice mu, in Allah ya yarda shi zai tsare mu daga faruwan dukkan wani abu, ajiyar zuciya ya kuma saukewa, da danjin sanyi sanyin kalamanta, cikin muryan natsuwa yace,,

ouk, shikenan yanxun ga munan zamu taso daga zaria, plss ki kula da kanki, in kinga da matsala kibar gidan kinji, zanyi waya gida wata taxo nan din, tace,,

to, karka damu, kayi tafiya fa a hankali, kayi driving da kulawa plss, lallausar murmushi ya saki, jin irin muryan da akayi mai amfani dashi,,

i will in sha Allah, ya fada a takaice, kafun ta yanke wayar tana dan murmushi.


……...A haukace ta shigo kitchen din, store ta nufa kamar wata mahaukaciya tana lalubar mangyada, can ta hangi wani galan din turkey, ajiyar zuciya ta sauke, tana diddilewa duka cikin tukunya.

gas cooker ta nufa, hankali tashe ta fara kokarin kunnawa, tana kunnawa tasa mishi wuta ya biyo ta, da sauri tayi baya tana sanya ihu, sai kuma taga ya daidaita, wasu tagwayen ajiyar zuciyan ta sauke tana daura tukunyan mangyadan, sannan tasa kai tabar kitchen din.


*fatan alkhairi*

share
comment
vote


*Matatace 2019*
Na meemartjj
[14/08, 14:29] Dala Grp: 🕯🕯🕯
    *MATATACE*
          🕯🕯🕯
  

story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjj 

*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty Ummeetah any my Fa'ixation._

   _wannan pages din naku ne, Auren fari fans, ku kad'ai kuyi yanda kuke so dashi, daga yer uwanku Haleematu sa'adiya, much fatan alkhairi._

page 63~64

___________Tsaf ta kammala shiryawa, tana cikin taje kanta da tun wankan farko da tayo, bata barshi ya bushe, harta kwanta bacci  duk sai taji ya dameta yanxun, gashi ta lura babu hand dryer kusa.

    ta dan numfasa, sanda take bude trolley din daya kwaso su ya zube a wajen, yanda ta lura ba kayanta ko daya, duk nashi ne dana aunty suhymah, da alama kamal bai dauko su dai dai ba, maidawa tayi ta rufe, tana komawa gaban dresing mirror da take tsaye.

   cumbing gashin ta cigaba dayi cikin natsuwa, tare da watsashi don yasha iska, cak ta tsaya da cumb din dake hannunta, sanda ta fara jin motsin dawowanta dakin.

   da sauri ta ije cumb din, tana daukar wayan suhymah data ije bisa dresing mirror bayan kare wayar da tayi, tare da maidawa inda ta dauka, sai dai tunkan ta aje, madam din ta turo kofa sai nishi takeyi sama sama, alamar dauriya kawai takeyi da kaiwa da dawowan data sanya kanta,,

   ke, shine abin data fada tana nuna ummeetah da dan yatsa, wacce ta idda ije wayar bisa gado, da sauri ta danja baya, kasa kasa kuma take karema suhymah kallon tausayi, don da alama tana jin jiki, muryan ummeetah na rawa tace,,
  
    don Allah aunty suhymah kiyi hakuri na dauka ne kawai munyi magana da Baffah, kinga bai dace ya taho hanya hankalinshi ba'a kwance ba, idan wani abin ya faru kinsan mu duka ba za muji dadi ba, shiru kawai tayi da kalaman ummeetah, bakin ciki, mamaki duk sun rufeta, da dan yatsanta ta kuma nunata tana fadin,,

   mu duka fa kika ce, kin manta da matsayina ne, kin manta da matsayin kie?, cikin natsuwa ta kuma gyara tsayuwanta jikin wardrobe tana fadin,,

  aunty suhymah ban manta ba, nasan ke matarsa ce, kamar yanda nima nake matarshi, don Allah ki bari muyi magana na fahimta,,

  heeeee, ahhhhhh, shine abin data fada tana waige waige da dafe ciki, murya na rawa tace,,

   mijina ne, mijin ki, wannan shine sakamakon da zaki mun, ina can ina bacci, ashe kuna can kuna yaudarana ko?, kasa ummeetah tayi da kanta kafun ta dago cikin salama take fadin,,

   aunty suhymah don Allah kiyi hakuri, wlhy bani da yanda zan yine, banyi don inci aman...……,,

   sai don me?, ta karisa maganar cikin tsawa, da daurawa da fadin,,

   kina nufin dole yayi miki, nasan waye sadeeq, baya sex dole da mace, me kike nufi?, tayi narai narai da ido kafun tace,,

  aunty suhymah plss ki fahimta, nasan da haka, ba dole yayi mun ba, cikin amincewa muka kasance da ju n a, ta karisa maganar da dai dai da dai dai, dafe kirji kawai tayi tana bin ummeetah da kallon mamaki, kawai saita fashe da kuka sosai, abin ya razanar da ummeetah itama kukan ta sanya tana fadin,,

  aunty suhymah don Allah kiyi hakuri, banyi don na yaudare kiba, kuma banyi da gangar ba, plss karki tsaneni, wlhy……,,

  shout up, ta fada cikin tsawa, da daurawa da fadin,,

  karna tsaneki, karna tsane kifa kika ce, kinsan irin sadaukarwan da nayi, don kawai mijina karya kasance da wata d'iya bayan nie, kinsan irin sadaukarwan da nayi?, duk wannan maganganun tana yinsu ne cikin kuka, da tsantsan rikata, kafun ta dan nisa tana fadin,,

  me yasa kika biye mishi, me yasa har zaki amince mishi, why idan ba yaudarata kika so yiba?, ummeetah ma wani kukan ta sanya da fadin,,

   aunty suhymah plss kie fahimce nie da gaske nake miki, baxan iya hanashi abin daya bukata ba, kuma baxan boye miki ba, tun lokacin dana fahimce nie matar Baffah sadeeq ne, na cire kaina matsayin yer a'iki, ta sanyaya murya tana rage sautin kukanta sosai taci serious da fadin,,

   kinsan me yasa?, tambayar ne taxo ma suhymah a diran ce, bata ma san sanda ta girgixa kanta ba, alamar a'ah, numfasawa tayi kafun ta bude idanunta tar akan suhymah tana dafe cikinta da fadin,,

   aunty suhymah tun farkon rayuwa na, tunda na taso bansan kalan murmushin mahaifina ba, haka dariya da kuma farin cikin shi, amma kinsan wani abu?, ta numfasa da hawayen da suka taru a idanunta tana cigaba da fadin,,

   Baffah sadeeq yana shigowa rayuwan mu ya sanja komai, lokaci na farko da zanga mahaifina na murmushi, yana dariya tare da farin ciki a tare da wani, har hira suna yie, kai ko sunnan Baffah sadeeq kika ga an kira, sai kinga mahaifina ya dara, duk da karancin shekaru nah, bai hana na fahimce shi d'in na daban ne a cikin rayuwan mu, ina son mahaifina so mai tsanani, don haka nake son duk wani farin cikinshi, ta kuma numfasawa kafin tace,,

   shiyasa nima a rayuwa, bani da burin daya wuce naga Baffah nah cikin farin ciki mai daurewa, banyi don in yaudare kiba, amma nasan nayi duk wani iya kokari, don in cika ma mahaifina alkwarin daya ce in daukan mai, ta sanyaya murya da siraran hawayen dake sauko mata bisa fuskanta da fadin,,

   don Allah kiyi hakuri, kibar mu mu zauna da juna, saboda duk duniya bansan son ko wani d'a namiji ba, daya wuce Baffah nah, a razane suhymah ke dafe dresing mirror saboda fadin da

Please Login or Register in order to submit comment