Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dake kunninta, sai zobenshi mai matukar kyau, ya sanya mata abin wuyan sannan ya jawo hannunta na hagu, a yatsanta na kusa da karami ya sanya mata zoben,  kiss ya sakar ma yen yatsun, sannan ya dago yana sauke mata wani light kiss bisa yen labbanta.

  a hankali take lumshe idanunta da budesu, ta cikin mirror take kallon jewel din, bullet shape ne dasu sunji design, sai faman kyallawa suke da bada star, tafukan hannunsa yasa yana tallafo kafadunta, cikin sansayar murya yake fadin,,

  nakine halak malak, ta kasa yarda ma kanta abin da take gani, ta shafa wuyanta, tana dago pendal din abin wuyan, murmushi tayi mai hade da kwalla cikin idanunta, tana fadin,,

   Diamond, kanta ta dago cikin natsuwa tana saukewa a kanshi da fadin,,
 
    Baffah nogode Allah ya saka da alkhair……, girgixa mata kanshi yayi alamar ta wuce hakan, ya ciro hannunsa daya yana dago fuskanta da tayi kasa dashi, da idanu yake tambayarta,,

    lafia?tayi yer ajiyar zuciya tana fadin,,

   Baffah anya ya dace in hallarci wannan taron, aunty suhymah zata iya gani, ko a fada mata, shima sai daya sauke wani nannauyar ajiyar zuciya, kafun ya maida hannun daya ciro bisa kafadan yana fadin,,

   ummeetah zuwa yanxun babu wani dalili da zai rage mu cigaba da boye abin da Allah ya kaddara a rayuwan mu, kona boye, ya kalli cikinta da fadin,,

  wannan babyn namu baxai boye ba, komai ya futo fa yanxun a bayyane yake, don haka kie daina damuwa, taro ne aka shirya musamman saboda nie, kinga nima tunda ina dake, ra'ayina ne kie bini saboda ked'in *Matata ce* kuma in alfahari da kasancewanki hakan, wani dan murmushin yake ta saki, fuskanta na nuna alamun damuwa har yanxun tace,,

  nifa Baffah har bana son na tuna da zuwa gida, saboda bansan irin kallon da za a rika mun ba, sannan bana son ku samu matsala ta dalili……...,,

  shishshsh, ya fada da daura yatsanshi bisa labbanta, da dan damuwa yake fadin,,

   Humaira bana ce kie cire wannan damuwan ba, ko baki yarda zan iya musu bayanin da zasu gamsu bane, hannunta ya kama yana zaunar da ita bakin gado tare da zama a gefenta, wayarsa ya zaro daga cikin aljihu yana dialing numbern da taga ansa,,

  munat sist. da sauri ta kalleshi, yana fadin,,

  miko mun system din nan?, ya fadi maganar yana maida hankalinshi sosai kan wayar da yake karawa bisa kunni, ba musu ta mika hannu tana jawo laptop din dake bisa side drower.

                    Naija 2am

   misalin 2am ne na dare a lokacin, suna zaune ita da yen uwansu suna hira, bayan su kammala da packaging wasu kaya, wasu dake hiran harsun bingire da bacci, aunty Amrah dake sanye da jan lalli dan sudan a kafanta, har ta fara gyangyadawa daga kinshingidan da take, sai munat da take kokarin gyara musu inda zasu kwanta, aunty Batulah kuma tana sanya kananan yaransu fitsari.

   ta futo rike da khaleesa, karamar yer aunty Amrah, ta shifideta kenan wayar munat dake gefe ya fara ringing, tayi dan firgit tana fadin,,

  waye da daddaran nan nie Batul, munat ma dago kai tayi tana zuba ma wayan idanu da mamaki, kafun ta mika mata wayar ba tare data lura ba tana fadin,,

  amsa kila fitinan nan ango kine, gobe dai zamu kai mishi ke mu huta, ta karisa maganar da dan dariya, amsa munat tayi tana fadin,,

  kai auntyn batulah, dan zaro ido tayi da fadin,,

   lah yayan mune fa, da sauri aunty batulah ke fadin,,

  wani yayan naku?, kina nufi sadeeq, tace,,

   eh shifa, bari na daga naji ko lafia, da sallama ta daga wayar, ya amsa mata serious yana daurawa da fadin,,

  munat kie bude system dinki za muyu magana ta video called,,

  toh, ta fada tana katse wayar, ta zauna tana fada ma aunty batulah abin da yace, da jimamin ko lafia itama ta zauna inda take tsaye, tana fadin,,

  to bude kiji ko lafia, budewa tayi ba musu, na wasu yen minutes kafun kiran ya shigo, sai daya gama connecting sannan hoto ya bayyana, kamar daga sama ummeetah tayi karo da auntyn su, da sauri ta fiddo ido waje, tare da rufe fuskanta da tafin hannunta, shikam yana rungume da kafadarta. 

   munat ma a firgice ta zaro ido tana bin katon cikin jikin ummeetah da kallo, tama rasa abin da zata ce, kafun ta zuba yatsunta tana dan dafe bakin data wangale da fadin,,

   what!yayan mu meke faruwa l?, harara ya zabga mata kafun yace,,

  karki raina mun wayau, Abdullah ya riga daya fada mun ya gama bankade mun sirri, so stop pretending, dariya tasa tana fadin,,

   lah, wlhy yayan mu munyi murna da wannan lamarin, abin ashe harya kai haka, ta zuba ma ummeetah ido da fadin,,

  ke ummeetah bude mun idonki in ganki, kene kika koma wata fresh americana girl haka, oh my god nie munat mafarki nake ko gaske, duk ta wani giride da murna, yayin da bakinta yaki rufuwa, ta mike tana nufa inda aunty batulah ke zaune, ta saki baki ta kallonta, da tsananin mamaki itama ta fiddo ido waje, kafun ta yashe hakora da murmushi mai kama dana kuka tana fadin,,

  masha Allah, Alhamdulillah, aure yayi albarka, ummeetah kece kika dawo haka, kuma manna kanta tayi da kafadarshi, tana dada dantse fuskanta da hannu, da nuna tsananin kunya, shikam sai wata yer munafukin murmushi yakeyi da fadin,,

  aunty batulah ashe kuma kun sani, ta dan harareshi tana fadin,,

  tunda kai ka boye mana, a'i yer uwan mu ba zata boye mana ba, munat ya kalla da sauri, ta langwabar dakai da tsananin murna tana fadin,,

  wayyoo yayan mu, na kasa na boye ma yen uwa nah wannan daddadan labarin ne, aunty batulah ta amshe da fadin,,

  kai amma nayi farin cikin, Allah sa ma rayuwa albarka, ya dan sosa sumar kanshi da fadin,,

  Ameen aunty batul, ina aunty Amratu take?, tace,,

   ga tana nan tana bacci, munat ta mike da nufa inda aunty Amrah ke kwance tana fadin,,

   aunty Amrah tashi kar ayi bake,  tashi tashi, farkawa tayi tana dan mumumtseke idanuwa, yayin da munat ta zauna a tsakiyarsu rike da laptop din, dishi dishi take kallon laptop din da fadin,,

   wa nake gani kaman s~diqus, yen yatsu ya daga mata da fadin,,

   hello, sai lokacin ta lura da abin dake faruwa, da sauri take kallon su munat tana fadin,,

   a'ah  wannan ummeetah ce ko?, aunty batulah tace,,

  eh itace, Amrah kinga rabo mai alkhairi, ihu zata sanya, sai kuma tace,,

   oh, Alhamdulillah, kai amma kanina ka biyani, Allah yayi ma rayuwa albarka, kai inama ina kusa da kai mu dan kashe, ta karisa maganar cike da murna, tana mai tsananin farin ciki, ya dan daga gira sama da fadin,,

  ya yer uwan nayi dai dai ko?, da suka hada ido da aunty batulah sai dan dukar da kanshi yayi, aunty Amrah na fadin,,

   yes nawan kayi dai dai, Allah ya muku albarka, ke diyar ga kanwar mu dan dago mana in ganki, plss dago kai mana, kuma runtse ido ummeetah tayi a haka take gaidasu, daker dai aka samu ta dago kai, munat sai tsokanarta takeyi, tayi murnan ganinsu amma kunya ya hanata sakewa, gashi data zauna sai cikin yafi futowa, ya sauke ajiyar zuciya yana fadin,,

  sisters nagode da wannan fahimtar da kuka yie mana, kun ganta nan tana murna zata zo gida, amma wannan twin babys din namu sun hanata sakat, sai damuwa takeyi, aunty batulah tace,,

   Allah sarki, ummeetah karki damu, in sha Allah ba abin dazai faru da auranku sai alkhairi, muna miki murna shigowa familyn mu mai albarka, Allah ya albarkaci rayuwanki, ya saukeki lafia, duk suka amsa da Ameen, inka debe ummeetah data kuma yin kasa da kanta, aunty Amrah tace,,

  yes karku damu little darlings dina, zamu ma fada ma maami ko ya kika ce aunty batulah?, munat na fadin,,

  eh haka yayi, a fada mata kawai, aunty batulah tace,,

   ba ruwan mu, ku kyalleshi gulman da yasa ya boye da farko, shi zaisa yayi mata bayani da kanshi, rankwafar dakai yayi cike da fuskan tausayi yana fadin,,

  haba the whole big sister, a taimaka mun,,

   hmmm kaiko za kayi bayani, aunty Amrah tace,,

  kaji my s~diqus karka samu damuwa, yanxun yaushe zaku dawo?,,

  gobe in sha Allah muna nan tafe, ya fada da murmushinsa, gaba daya suka amsa mishi da,,

   to Allah ya dawo daku lafia, da wannan sukai sallama, daga nan suka balle da hiran lamarin, kowa na cike da mamaki, ita aunty Amrah murna takeyi, yayin da aunty batulah ke cike da tausayin suhymah, tana ganin shashancin suhymah na gaske da gaske, sunma kasa komawa baccin da sukai ninya, yayin da suka barke da hiran ana tattaunawa.

                         ***

   A jiyar zuciya ya sauke yana kallonta da fadin,,

   to shikenan, yanxun saiki ije duk wani damuwa ko, damtsen hannunsa ta ruko, can kasan zuciyarta take jin wani irin nishadi, koba komai su aunty munat susan da auransu, da d'an shagwaba take fadin,,

   amma dai gaskiya naji kunya sosai, shima cikin kwaikwayon muryanta yace,,

   nima naji kunyan a'i, ba kiga abin dana a'ikata bane, ya karisa maganar da kallon cikinta yana kashe mata ido daya, mikewa ta shiga kokarin, cak ya rike hannunta tana fadin,,

   Baffah zansa takalmine fa, lokaci na kurewa, mikewa kawai yayi, yana zaro tsadaddan dark green din takalmin daga kwalinshi, a gabanta ya tsuguna yana dago kafar nata.
  
    a hankali ya zira mata yen cover din masu kyaun gaske, wanda keda dan tudu kadan, sai aka bude wajen yatsun ta gaba wanda suka bayyana kadan, sai spakling takalman suke, gashi shima yayi matukar daukan kafan nata, ya mike yana ruko hannunta suka mike tare.

   fuskanta ya saka cikin tafukan hannunshi, kallon juna suke da wani sako da yake kai ma zuciyar ko wannen d'ayan su, ita kanta bata taba tsayawa ta kalli kwayan idanunsa irin na yau ba.

  sosai taga ya kara mata kyau, jin dadi da kwanciyar hankali yasa shekarunsa sun dada boyewa, a barayinsa kuwa wani abin yake jie na zaga jini da tsoka na jinin jikinsa, a dan zaman wata dayan da sukayi su kadai, abubbuwa da dama ya kara shiga zuciyarsa, jie yake kamar suyi rayuwansu su kadai.

   hannayenta ta daura saman nashi, ganin yana kawo bakinshi kan natane, ya sanya tayi saurin fadin,,

  o'oh, Baffah we are going to be late, bude idanunsa yayi da suke lumshe a kan  fuskanta, sai kuma yayi dan murmushi, yana daga ta sama cak da fadin,,

   I luv yhu ummeetan Affah, da sauri tasa hannu tana sakalowa ta bayan wuyanshi, dariya take sosai shima yana dariyan da kallon kyakyawar smiling face dinta, wayarshi dake gefe ya fara ringing, dole ya direta yana fadin,,

   wai Humaira next month baxan iya daga kiba, kinji yanda tun yanxun weight dinki ya karu, cikinta ta kalla da dan turo baki,,

   duk wadannan babys dinne a'i, yayi yer dariya yana lakutan hancinta da fadin,,

  heee come on, yhu still look beautiful, even though with this tummy, murmushi tayi, dai dai sanda yake daga kiran DR. khamis dake fada mishi time fa na kurewa, gasu nan yace, yana katse kiran.

  ta daura kakkauran gyallenta, daya sauka sosai, yaji yen duwatsu sai kyalli yakeyi, saman kai ta yafoshi, tana matse shi da wata yer pretty cute bag da yake shima kala daya da kayanta.

  dakinsu ta bishi tare da taimaka mishi ya saka suite din saman, ya kammala shiryawa tsaf, sosai suka futo kamar wasu taurari, shi kanshi bai tunanin za suyi kyau har haka ba.

   suna futowa DR. khamis ya fara kashe musu hotuna, itama matarsa dake cikin mota cikin gayunta tare da Irfan da yaranta, sai yaba kyaun da sukayi takeyi, wata zukekiyar mota ummeetah taga sun nufa .

   baturen driver motar ke kokarin bude musu gidan baya, da sauri yake tsaidashi da hannu, shi yasa hannu ya bude mata motar ta shiga sannan ya maida ya rufe, shima zagawa yayi ta dayan site din,  driver ya bude mishi motar ya shiga, kafun ya rufe motar yana komawa gidan gaba, tare dama motar key suka wuce, motar DR. khamis na binsu a baya.

   Tarone mai amsa sunan shi aka hada mishi, daga kamfanin da yake a'iki dasu, saboda nuna kwazanshi da kuma alkhairan daya jawo ma kamfanin masu tarin yawa, komai a tsare yake, waje na musamman aka musu shida ummeetah.

  ganin yanda suke karramashi sai abin ya bama ummeetah shu'awa, kowa nashi ne, harda wasu bakaken fatan yen uwansu dake zaune a kasan, kowa na mishi fatan alkhairi tare da kyaututtuka na musamman.

   anyi taro lafia, ummeetah na sakale da hannunta cikin nashi, duk yanda yaso ta samu waje ta zauna taki, saboda enmmata dake kaiwa da dawowa suna rawan kai kusa dasu.

  Nadeen ma na kusa dashi sai mamaki takeyi wai yana da 2wifes, tana fadin zaiyi na uku da ita, ummeetah dai hararanta ta rika yie ta gefen ido, ta lura itama wannan tana kishi irin na wancan, amma ita bata da hauka.

   su salma ma sunxo, da yike mijinta duk abokan junane dasu DR. khamis, mamaki kam a'i sun shashi, ba kamar fadeela da har video ta rika musu don sun matukar mata kyau da burgewa, a zuciya take faman a'yyana,,

  suhymah ta kare miki yer bayan gari, sai wajen 10pm aka watse taron, gida suka koma basu zauna ba suka fara tattara kayansu, don a daren nan flight dinsu zai tashi.

      _nayi alkwari ban cika ba, kuyi hakuri, abubbuwan da yawa, luv yhu my fans._

*fatan alkhairi*

comment
share
vote

*matatace 2019*
Na meemartjj
 [14/08, 14:29] Dala Grp: 🕯🕯🕯
    *MATATACE*
          🕯🕯🕯
  

story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjj 

*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty Ummeetah any my Fa'ixation._

  _Tunatarwa_

    _*A rika amfani da abin da ake nuni shine mai kyau, kaima kaga ya dace kabi, bisa hanya madaidaciya, plss a watsar da marasa kyaun ciki, a ije karatu lokutan ibada, makaranta, da ayyuka masu muhimmaci, tnx.*_

  Not edited

page 57~58

   _________Sauri sauri ta kammala shiryawa, tana sanye da wata tsadaddiyar super english, ta karkata wani dauri, ga kitson kalaban da aka mata labta labta na attach sun zubo ta gaba da baya, banda wuyanta da kunninta da su kaji gwala gwalai.

   wayane a hannunta duk ta damu da kufula, tana daga wayar ta fara masifa da fadin,,

   haba surayya kinsanfa ke nake jira, ke kuma kikace wajen nan da nisa fa, daga can bangaren surayya dariya tayi tana fadin,,

  madam kwantar da hankalinki, kixo gani a wajen gate, kie futo kawai mu wuce a motata, da dan dariya tace,,

  yer zaban kinsa harna rude nayi tunanin ba zaki zo bane, plss bani 5minutes, daga haka ta katse wayar mum dinta dake zaune dabas tasa yer dariya da fadin,,

  lallai suhymah da gaske kikeyi, 6am nefa yanxun,,

  umm mum a'i barni kawai a kagare nake shi yasa, ina so kuma mu dawo da wuri, kar a nemeni ace ban tsaya bikin kanwar miji ba, mum tace,,

  good, kuyi duk yanda kika ga ya kamata, gaba daya yarinyan ta gama fice mun a raima, ta sakale jakarta data gama dura kudi harda su american dollar, tana fadin,,

  ba ke kadai ba mum, korarta ma zanyi, plss kice ma haj. ladi mai kawo miki yen a'iki, nima ta kawo mun yen a'iki koda su hudu ne sun isheni, mum din ta jinjina kanta da fadin,,

  karki damu, yanxun dai ku dawo lafia, kie kula da kyau saboda tsohon cikin dake jikinki, dai dai nan mummy ta shigo sun dan tattauna kan tafiyar, kafun ta kalketa tana fadin,,

  yawwa sannan daughter plss kije kie gaisa da sirikanki kafun kie wuce, in huta da kananun magana, shima Abbansu ya dameni da complain, an riga da an gama zugeshi, zumburo baki tayi mum dinta na fadin,,

  kin gane kije fisha ko a tsatsaye ne ku gaisa, muje kiga saisu Najma su rakaki, da wannan suka fice daga dakin.

  Tare da sisters dinta suka shiga, taji uwar takalmi mai tudu kamar bamai ciki ba, sai yatsina take ma jama'a, a tsatsaye ta gaisa da maami wacce kanta ma yayi zafi anata shirin daura abincin biki, daga haka ta wuce da sisters dinta zasu futa.

   ganin a kitchen suke don haka ta juya zasu futa ta kofan baya, yen uwa da yawa suna ta wajen dai dai bakin kofan wata yer uwansu irin sai a hankali din nan, da gama kauye suke, tana rike da danta sunata shirin daura girki, suturar jikin suhymah ne ya sanyata sakin baki tana kallonta ga tsantsan hutu daya zauna a jikinta, tana rike da waya tana wannan iyayi, ga hannunta daya jie zoben gwal, a yatsine ta kalleta  kafun ta daga mata tsawa da fadin,,

  malama tashi mana zan wuce, ta karisa fada maganar da nuna alamun kyankyamin matar, da sauri matar taja baya har babynta na kusa faduwa, aunty Amrah dake tsaye bakin famfo daga waje, tana hangen komai, a'iko tace dawa Allah ya hada, kamar wasa sai gashi an fara zage zage, fada sosai, aunty batulah taxo ta janye hannun aunty Amrah ana tausata, suhymah na fadin,,

   shegu kaddararru, wadanda basu iya komai ba sai sama mutum ido gidan auranshi, shashashu kawai, abin ya bama aunty Amrah haushi wacce harta saka kafa cikin gida a'iko ta juyo da fadin,,

  ga kinan babbar shashasha, kina jie kina gani zaki ga mijinki da mata harda ciki, kishiyar nan da baki so sai kin ganta, a razane suhymah ta dago kai, tako shiga zuba ruwan masifa, itadai aunty Amrah aka iza keyarta, harda maami data zo ta daka mata wata tsawa, dole ta wuce.

   itakam rai bace ta fuce tana faman zage zage, waje ta nufa yayin da sisters dinta sukai cikin gida don sukai tsegumi.

   a motar ta tarda surayya dake kishingide tana faman latsa waya da duba wasu new update din da aka watso a instagram, wani video event ta gani couple dinne suka burgeta, tana kokarin bude video suhymah ta shigo tana zage zage, kallonta tayi da dan dariyan shu'umanci tana fadin,,

  ran hajiyar sadeeq ya dade, kin samu sadeeq baki da damuwa, a harzuke tace,,

  a'iko nie keda damuwa tunda ban gama da wadancan yen kutumar kazan yen uwan nashi ba, dole inmu kaje zan hada dasu amun a'iki gaba daya, ruwa sai nace susha zasu sha, surayya tace,,

  meya faru kuma?,tace,,

  kedai tuka mota, bani akaima fatar kishiya ba gobe ba zata karaba, ba tare da surayya ta cigaba da duba abin da take dubawa ba, tayi jifa da wayar tana ma motar key suka dau hanya.

   wannan yer matsalan taso ta hada wata yer fitina, daker dai aka kashe wutar maganan, su aunty Amrah ma hankali kwance suka cigaba da gabatar da sha'anin bikinsu, so suke maami ta samu sukuni ta zauna suyi magana da ita.



                        ***

   ……Lamo ummeetah cikin jirgi da saka abubbuwa masu yawa, tunda suka taho gabanta ke fadi, tashin hankali ne kawai abin gudunta, bata kuma san yanda wasu da yawa zasu amsa maganar auran nasu ba, musamman aunty oganniya, ta sauke wani ajiyar zuciya tana jujjuya english novel din dake rike hannunta tana karantawa.

   bata son wani abin ya taso, tasan yanda aunty suhymah ta tsani kishiya, mawuyaci ne ta gaxa shiga wani hali, tasan kuma yanda yake matukar son matarshi, anya zata iya barin auransu kuwa, dan guntu tsaki kuma tayi tana bude yar hand bag din dake rataye bisa kafadarta, tare da maida novel din ciki.
 
   yana kallonta ta gefenta da yake zaune, wani yer cute joter ne ya fado daga cikin jakar, ba tare data lura ba ta maida jakar ta rufe, tare da komawa ta kinshingida da kujeran tana lumshe ido.

  hannu yasa ya dauko  yer karamar joter mai kyau dashi, yayi murmushin sanda yake bude page din farko wanda ke dauke da rubutun,,

  _my love story_, da mamaki yake bin kalmomin da kallo da wani tunanin, ya dan kauda tunanin dake zuciyarsa yana budo next page, baitukan soyayya ne rubuce kawai a ciki, ya rika bi yana karantawa da murmushi, wani murmushin ya saki sanda yake karanta last one din daya tsaya mishi a rai, dake rubuce da,,

   _soyayyah idan har bai kaine ba, bana mijin da zanso muyi zaunawa, tabbas._ shiru yayi da wani dan murmushin gefen baki, kafun ya rankwafo da kanshi dai dai kunninta yana rada mata,,

  baby wannan love songs din nawa ne?, da sauri ta yunkura tana kai hannu zata amsa jotern, shima da sauri ya janye hannunshi tare da boye joter a bayanshi,,

  Baffah plss ka bani sirri nane, ta fada tana mai runtse idanunta, sai daya gama kare mata kallo, kafun ya hura mata iska bisa fuskanta, ta bude idanunta tar a kanshi, gira ya daga mata da fadin,,

  ouk zan baki, amma saikin fada mun, baitukan love din nawa ne? taba fuska tayi kamar zatai kuka tana girgixa kanta  da fadin,,

  no, wannan tsohon joter nah ne, plss ka bani, dif murmushin dake fuskanshi ya dauke, yana zaro hannunshi ta baya, tare da kare mata kallo har sanda ta zare joter daga hannushi tana maidaiwa cikin jakarta.

  komawa yayi kawai yana jingina da kujera, yana mai lumshe idanunsa a hankali, wani abie ke kuna can kasan zuciyarsa.

   kenan akwai wanda ke cikin rayuwanta shi kuma yaxo ya shiga tsakanisu,,

  ya salam, ya fada yana dafe kanshi, da sauri ya runtse hannunwanshi,,

   Humaira why why, me yasa baki fada mun ba, me yasa kika bari na rabeki, me yasa kika bari sai dana dasa ma zuciya na sonki mai tsayawa a rai, me yasa kika bari zan cutar da taki zuciyan?, kuma runtse hannu yayi hade da idanusa,,

  to waye wannan?, ya tambaya kanshi da furtawa a saman labba, kwata kwata rayuwansa ya tsani yaga ya takura ma mutum akan abin da baya so, duk sai yaji hankalinshi ya tashi.

  itama nata bangaren shiru kawai tayi, kowa da abin da yake sakawa, har sanda jirgin ya sauka ta garin Abuja daga nan kuma wani flight din suka samu zuwa kD. 

 

                   £……£……£

  Biki fa ya kankama, ta ko ina ana farin ciki, harda haj. yagana da take washshagalenta, tunda yer uwanta tace ta saki ranta ayi biki, kodan su bama yen bakin,ciki haushi, sannan in wani abin na fasuwan auran ya faru, kar zargesu wani abun, da wannan ta saki ranta ana shagalin biki.

   manya tent tasa aka sanya a wajen, ga waiters dake faman yawo da abinci ko ina, ta tara manya manyan kawaye, gefe kuma ga kidi dake tashi enmmata sai cashewansu sukeyi, kar kiji su saudat da suke faman tallatsi da kudi.

   muheet ma ya halarto wajen da abokanshi dake faman mishi kirari, da tsula rashin kunyan da suka iya, ya rika kwasan rawar shaku shaku sanye da wata danyar tsadaddiyar shadda daya gama gatalata da dinkin tsiya.
 
  wata yer git din malum malum aka ma kayan, ya matse hulan sakin nan mai tsadda a hammata, yayin da gashin kanshi yaji aski irin na rashin da'a, an kwashe gefe da gefe.

  yana faman kwaso rawa, sanda sisters dinshi ke ihu da mishi liki, kafun kuma ya fara rawan koroso, suka dai gama iya shegensu suka fice a filin, inda suka nufa mota don hallarta taron daurin aure da za ayi a friday masjid din dake anguwan nasu.

                          ***

  shiru kawai tayi da tsananin mamaki wanga lamari da yeyenta suka gama labarta mata, munat dake sanye cikin wara super holland dinki irin na amare fuskanta yasha make up, tayi kysu sosai, ta tsuguna gaban maami wacce ke zaune bakin gado ta zabga tagumi tama rasa ta inda zata fara, hannunta da yaji lalli ta daura bisa gwiwan maami tana fadin,,

  maani don Allah kar kice komai, munsan kema abin da kike so kenan, don Allah kisa musu albarka kibi lamarin da add'a kawai, dagota maami tayi tana zaunar da ita gefenta da fadin,,

 

Please Login or Register in order to submit comment