Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taji tana kokarin yie tana fadin,,

   miji nafa kika ce kina so, kanta ummeetah ta daga tana fadin,,

   eh aunty suhymah, wlhy nima da farko bansan sonshi nake yiba, nasan dai ko a cikin maza ya futa daban a wajena, amma sai da kika bari muka shaku da juna a US, sabon daya shiga tsakanin mu yasa na fahimce sonshi nakeyi, wlhy aunty suhymah ina sonshi sosai kuma so na gaskiya, kie yarda dani, mu zauna mu sanya mijin mu farin ciki, cikin sanyi take kuma nunata da dan yatsa tana fadin,,

   sai kinyi dana sanin sanin mijina da kika yie, saina maida rayuwan ki abin kwatance, sai nasa kinyi nadama mai tsanani, kuma dole ne kibar mun mijina saboda dani kadai ya dace ya zau……...,, da sauri ummeetah ta katseta da fadin,,

   a'ah, aunty suhymah don Allah koma menene za kiyi, pls karki raba nie da mijina, saboda da sonshi na tashi, haka kuma dashi na rayu, pls karki shiga tsakanina da mijina, cikin karaji take fadin,,

   wai harke kina da bakin da za kice, kina son mutumin daya ije kie matsayin yer a'iki a gidanshi, kina matsayin matarshi, dafe kantaummeetah tayi tana zama bakin gado da fadin,,

   ya salam, aunty suhymah ki gane mana, yayi hakanne saboda yana son farin cikin ki, nie kuma na fada miki a rayuwa, ba abin dana fie burin son gani saman da farin cikinshi, kuka ta kuma fashewa dashi, tama rasa abin da za tace, yarinyan nan ta wuce da tunanin ta, jikin dresing mirror ta buga tana runtse ido kafun ta bude ido da fadin,,
 
   farin cikinshi, farin cikinshi, farin cikinshi, kina nufin kin fina son shineeeee?, ta karisa maganar da tsawan daya haddasa mata wani sarawan kai tun daga sama har kasa, ta kuma dafe dresing mirror hannun bibbiyu.

   d'aga kafa take kokarin yie tabar wajen, amma ya rike, duk yanda taso ta motsa kafan yaki d'agawa, ga cikinta dake faman jujjuyawa, ta dafe cikin tana runtse idanu da karfi don azaba, a firgice ummeetah ta mike tana nuna kasan tyles da jini ya fara tsiyaya, a rude take fadin,,

   aunty suhymah jini, jini yana futowa, da sauri itama ta bude idanunta a kasan tyles,,

  ahhhhh, shine abin data fada a rude, tana kuma sanya kuka, gashi ta kasa motsawa, gado ta fara nunawa da fadin,,

   sadeeq sadeeq, kira mun sadeeq, wayyo baby nah, bana son nayi losing baby nah, da sauri ummeetah ta jawo wayar a rude tana dialing numbern shi, sai dai duk yanda tayi kiran yaki shiga, a rude take fadin,,

   aunty suhymah yaki shiga, tana numfarfashi tace,,

   dauka naki wayar ki kirashi mana, maybe ya dauka, jiki a sanyaye take fadin,,

  a'i kiran yaki shigane, kuma sim din dake wayana baxai yi kira ba, da sauri ummeetah ta cillar da wayan, tana kama gashinta da ribbon, tare da yafa karamar viel din abayan dake jikinta, ta kwasa wayoyinsu, tare da key din motar suhymah data gani a wajen tana fadin,,

   aunty suhymah plss muje kawai in kaiki hospital din, sai data zabga mata harara kafun tace,,

  kyece zaki iya kamani, kira mun gate man ya taimaka mun, girgixa kanta tayi da fadin,,

  plss bamu da isashan lokaci, ki bari in taimaka miki zan iya, hannunta ta dago daker tana daurawa saman kafadan ummeetah, wani jiri jiri take gani, moves din ummeetah ne ke taimaka mata tana takawa daker da ciccijewa, har suka sauka downstairs.

   da taimakon ummeetah ta shiga mota, a rude shima gate man ke wangale gate, ummeetah ta fada gidan driver tana ma motar key, duk da halin da take ciki, bai hanata mamakin yanda yarinyan ta iya mota haka ba.

  lallai anyi bata, dai dai bakin gate tace ta tsaya, gate man ta yafito da hannu, yaxo ta site din da take zaune, daker ta iya mishi magana kasa kasa, ya wuce yana faman jera,,

  to ba damuwa, Allah ya tsare ya kara lafia, daga haka ya wuce cikin gidan tare da nufa kitchen din dake gidan, ummeetah taja motar suka bar gidan.
 
    driving kowai take da addu'a, don tasan bata da natsuwa, ganin yanda bleeding din ke dada karfi, motar duk ya baci, ita kam banda kiran sunan baby nah, ba abin da takeyi, kadan kadan kuma take iya nuna ma ummeetah hanyar hospital din da zasu, kasancewan ita bata san wajaje bama sosai.


                       
***
  Sosai hankalin ummeetah ya tashi, ganin tun suhymah na iya magana kadan kadan, harta daina, yaraf kawai take a zaune, kuka ta sanya tana driving da fadin,,

   aunty suhymah don Allah kiyi hakuri kie tashi, don Allah ki tashi, plss na rokeki, himma ta kara badawa wajen driving din, Allah yasa sun iso kan street din asibitin kenan, da taimakon sign bord suka karisa.

   tun daga abnormal driving din da takeyi, da yawan wadanda suke wajen suka fahimce ba lafia, ko idda packing ba tayi ba ta bude kofan motar, tana kashe motar ta diro waje, yanda take a firgice ya sanya nurses din dake haraban wajen antayowa a guje, yayin da wasunsu suka antaya don dauko gadon da za'a turata ciki.

   kuka kawai takeyi sanda nurses suka ciccibo suhymah waje, dai dai sanda aka kawo gadon, daurata sukayi, kowa ya tsorata da irin jinin da take fitarwa, ta rufe motar tana bin bayansu.

   emergency suka wuce da ita theater room, tuni doctors suka futo suna wucewa ciki, a'ikin gaggawa take bukata, tare da jini, nan da nan ummeetah tasa aka bude mata file, don ta fada musu basu futo da kudi ba, amma mijinsu nakan hanya, plss duk abin daya dace a musu.

  ba musu suka a'ikata hakan, kasancewan asibitin na kudi ne, jini aka fara nemowa aka daura mata hannu bibbiyu, yayin da ummeetah ta sanya hannu a ciserial section din da za'a mata.

  kaiwa da dawowa take faman yie, wata nurse data zo wucewa babbar mace da ita, tabi ummeetah da kallo yanda duk ta damu, gashi sun lura da alama kishiyoyi ne, sai taji duk sun burgeta, da gani akwai fahimtar juna a tsakaninsu, nace(hummmm.)

  hannun ummeetah ta kamo musamman, itakam tana binta da kallo, sai data zaunar da ita bisa wasu yen design chairs dake wajen sannan tace,,

  kema kina bukatar hutu, ki kwantar da hankalin ki, in sha Allah komai zaizo da sauki, kanta ummeetah ta jinjina ma matar da musayan murmushin da sukai ma juna, sannan tasa kai tabar wajen.

  ajiyar zuciya ummeetah ta sauke, tana sake kiran numbern shi a wayar suhymah data taho dashi, wani ajiyar zuciyan ta sauke sanda kiran ya soma shiga, da sallama ya daga wayar ta amsa mai itama, jin muryanta ne yasa da sauri yake fadin,,

   Humaira lafia kuwa?, da dan damuwa tace,,

  Baffah ba lafia fa, aunty suhymah ce ke asibiti zata haihu, yace,,

   ya salam, kuna ina yanxun?,

   muna hospital ne, summa ce a'iki za'a mata, a rude yake fadin,,

  akwai matsala kenan, sai da tayi dan shiru kafun tace,,

  eh, bleeding takeyi, amma yanxun dai tana dakin theater ma, a hankali ya runtse idonshi da kirjinsa dake bugawa, kafun ya bude da fadin,,

  ouk, yanxun kinsan menene, plss duk wani abu daya dace, suyi mata, nima mun kusa shigowa kaduna, da zaran mun iso, in sha Allah zan wuto hospital din kai tsaye, a sanyaye tace,,

  toh shikenan, Allah ya kawo ku lafia, daga haka ta sauke wayar, tana maijin tausayinsu su duka ukun.

  kaman daga sama saiga haj. falmata da ita da surayya sai kannin suhymah, tsaban rikicewa basu ma lura da ita ba, sai daga baya, a'ikam tasha tsaraban harara, suka zauna nan, itama aunty batulah sai gata, ita da kanwar maami aunty yalwaty.

   wajen su ummeetah ta nufa, sai sannu suke mata itama, aunty yalwaty na kuma zaunar da ita gefe kan kujera.

   kusan thirty minute, kafun wata nurse ta futo daga theater room din, phamacyn asibitin ta nufa sai gata da babbar kwali, ta koma cikin theater room din.

  kusan 5minutes sai gata ta futo rike da kwalin tana fadin,,

  ina neman relatives din patient din dake ciki, da sauri su haj. falmata suka matsa kusa, dake fadin,,

  ke nurse yadai, babu jaririn ne?, mika musu kwalin tayi da fadin,,

  sai dai kuyi hakuri, daga haka tasa kai ta koma dakin, da sauri ummeetah ta kalli aunty batulah da fadin,,

  aunty batulah me suke nufi da haka? kafadar ummeetah ta dafa kafun tace,,

   ummeetah ba bu babyn, ya koma, da sauri ummeetah ta kai dubanta kan kwalin dasu zahira suka bude suna faman rera kuka, itama sai ta sanya wani kuka da raya,,

   Allah sarki, duk tanajin dasu Baffah suka gama yie akan babyn nan, ashe Allah ya rubuta ba rayayye bane, hannu ta sanya tana toshe bakinta, aunty batulah ta zauna gefenta da rarrashinta tana fadin,,

  ummeetah babu yanda za kuyi, wanda ya bata ya amsa abinshi, sai dai muyi mata addu'an Allah ya bata wani mafi alkhairi kinji, kie daina kukan nan karki sama kanki wani ciwon, kinga kema kina bukatar natsuwa, share hawayenta tayi da fadin,,

  to aunty batulah, Allah sarki aunty suhymah Allah ya maida miki da wani mafi alkhairi, duk suka amsa da Ameen, haj. falmata dake daga can gefe sai banka harare harare takeyi, wama yasan tana yie.

   wajajen 6pm, suka futo da ita, don daker aka samu jinin ya tsaya, donma yana futane wani na shiga, kwace take kawai sharaf, har sanda aka kammala gyara mata jiki, vIP na musamman su kayi admiting dinta, nan da nan yen uwa suka fara safa da marwa, kowa na tausaya mata.

  shima hankali tashe ya shigo asibitin, aunty batulah take sanar mishi komai, ta kalli inda ummeetah take zaune da fadin,,

  plss sadeeq ka rarrashi yarinyan can, duk ta damu kanta, kamar wacce ta rasa nata, wucewa kawai yayi wajen ummeetah bama tasan yaxo ta wajen ba, kafadarta da taji ya dafa ya sanyata dagowa.

   da sauri ta mike, kawai saita shige cikin jikinshi tana sanya sabon kuka kasa kasa, shima maida hannu yayi yana rungumeta, tare da kissing din saman kanta, sunma manta a wani reception suke, ya dagota a hankali tana fadin,,

  Baffah shikenan mun rasa babyn aunty suhymah, murmushin yake kawai yayi mata yana shafa kumatun da fadin,,

  karki damu Allah zai kawo wasu masu albarka, ya share mata hawaye tare da kama hannunta suka wuce office din doctor.


                          
***
  Zaune suke a kujerun da suke facing din juna, yana magana da doctor wanda ke zaune can gefe, yana mishi wata razananniyar bayani cikin salama, a rude yake fadin,,

   yanxun DR kana nufin matata ba zata kara haihuwa ba, DR. dake wasa da wata yer pen a hannunshi, ya nisa yana ije pen din waje daya da fadin,,

  calm down plss, ba muce ba zata kara haihuwa ba, tunda iko na Allah ne, amma gaskiya ta samu mammunar rauni a mahaifa daya sata zubar da wannan jinin, samun wani cikin da haihuwa kamar wata barazana ce a rayuwanta, shi yasa muka juya mata mahaifar kawai, aka rufe mata haihuwa, amma ba don mun so ba.

   ba sadeeq ba, harta ummeetah sai data shiga wani hali na tausayin aunty suhymah, zufa kawai ke keto mishi, da daura dukkan laifin a kanshi, sun dan jima suna tattaunawa, kafun wata nurse ta shigo rike da kwallin da suka bama su haj. falmata, tayi uwa makarbiya dashi, harta mai d'an an hanshi, shine DR. ya musu dibara aka amso babyn.

   babu inda babyn ya barshi a kama, ummeetah ma da wasu hawayen take bin jaririn da kallo,  Allahu akbar, Allah mai yanda yaso, a duk sanda yaso, shine abin da suke nanatawa a zukatansu, ya dan jima a asibitin da shiga da fice, kafun yasa kai ya tafi.

                          
***
   Misalin 8:30pm aunty batulah ta futo daga dakin da akayi admiting din suhymah, ranta bace ta dubi ummeetah da suke zaune ita da aunty yalwaty a reception din wajen tana fadin,,

   ummeetah wai ina mijin naku ne?, a sanyaye tace,,

   a'i tun dazu ya tafi, so yake yaje su rufe babyn, ta dan nisa da kallon auntyn nasu tana fadin,,

  kinga nikam aunty yalwaty gwara kawai muzo mu tafi, don nan wajen babu fuska ko kadan, in Allah ya kaimu gobe ma dawo, aunty yalwaty dake zaune duk ta gaji da zaman itama tace,,

   dama haka nake tunani, kayi ta zama a waje daya jabas, mu tafi gida kawai, ko kiye kiye naje na taya yer uwanah, ta kalli ummeetah da fadin,,

   ita wannan da mijinta zasu tafi ne?, aunty batulah tace,,

  ta taso muje kawai, bana barta a nan ba, ba musu ummeetah ta mike, har zasu futa saita kalli wayoyin dake hannunta da sauri take fadin,,

  oh, aunty batulah bari na dan kai musu wayar aunty suhymah,,

  ummhumm kie sauri, cewan aunty batulah da suke kokarin futa waje, ita kuma ta juya ciki.

   Da sallama ta shiga gabanta na lugudan fadi, duk sun jinta sukai banxa da ita, harda haj. falmata dake gyara hannun suhymah data tankwara, wanda ke makale da blood giving set jini na faman a'iki.

  ta dan nisa kafun ta karisa ciki tana mika musu wayar da bayani, fuwww zahira taxo ta fisge wayar, da jan wata doguwar tsaki, juyawa kawai tayi tabar dakin.

  dan dakata mana, muryan Najma ya katseta data taho ta bayanta, cak ta tsaya tana juyowa, dai dai sanda ta kariso inda ummeetah ke tsaye, da wani kallon wulakanci ta bita dashi kafin tace,,

   humm, tsintacciyar mage bata mage, abin fa da mamaki, mara dangi mara usuli kamar kie, wlhy sai kinyi nadama, bake kin saka yer uwan mu a wani hali ba, to bari na shaida miki, tana farfadowa ba zata kyale kiba, ta nisa kafin ta cigaba da fadin,,

   tafi karfin ta hada miji dake, ke bake kadai ba, harta shi sai yayi bayanin kalar yaudarar daya mata, ko kunya yayi abin kunya zai…………,,

   ummm ummm, ummeetah ta fada da dan runtse idanuwanta, hakan ya nuna alamar taji d'acin kalmar, a hankali ta bude idanunta akan Najma dake tsaye har lokacin, a sanyaye take dan girgixa kanta da fadin,,
  
  karki sake, zan iya juran duk wani cin mutunci, amma karya ketare wannan layin, baxan iya juren jin wani kalma mare dadi ba akan rayuwan aurena, wanda na shimfida shi tare da mijina na sunna, da sauri ta fiddo ido waje tana kare ma ummeetah kallo, anya kuwa itace wacce ta sani, a harzuke take fadin,,

   mijin kie, waye mijin naki?, sai da tayi dan murmushi kafun ta kunna mata fuskar wayarta dake hannunta, tana nuna mata da fadin,,

  akwai wanda ya wuce wannan ne, *Abubakar sadeeq Al-amin Tahir*, shiru kawai tayi da rasa abin cewa, ummeetah ta sauke wayarta tana danja da baya, harta juya sai kuma ta juyo da fadin,,

  plss karku bata mana rayuwan aure nie da abokiyar zamana, ku zama kanni na kwarai, ban fiye son hayaniya ba, ku kiyaye, daga haka tasa kai tabar wajen, Najma ta fashe da kuka tana fadin,,

  Allah ya isa, wlhy baxa mu taba yafewa ba, ta rika zage zagenta da kuka, har sanda yer uwanta taxo ta jata ciki suka koma suna faman yie.

  ummeetah kuwa nata barayin ranta bace suka koma gida, bata son tashin hankali da harkan tsiya, duk sai taji ta shiga cikin wani kunci.

  suna komawa dai dai sanda yen kai amarya suka dawo, harda hibbat dake faman tsula ma ummeetah surutu, sun gaisa da maami cikin matukar kunya, ita sai abinma ya bata dariya.

   ruwan wanka na musamman aka tanadar mata, ta gasa jikinta kafun ta futo an jera mata rayayyen abinci mai rai da lafia, suka zauna nan dakin da zasu kwana ita da hibba da yer uwanta suna hiran bayan rabuwa.

   

                      
***
    Asuban fari ta farfado, ta rika jujjuya kai daga kwancen da take, da sauri sukayo kanta suna faman jera mata sannu,,

   baby nah, shine abin da take fada cikin dishashshiyar murya, ta cigaba da fadin,,,

  mum plss baby nah, ina suka kaimun?, kwane kwane suka soma mata, ta yunkuro kamar tana son ta mike, da sauri ta maida ta kwance, a wahalce take kuma fadin,,

   shikenan na rasa baby nah ko, wayyoo mum na shiga uku, ajiyar zuciya haj. falmata ta sauke kafun tace,,

   a'ah, kwantar da hankalinki, ga babyn kinan yagana na mishi wanka, dan murmushi ta sanya daga kwancan da take tana fadin,,
 
   oh thank god, baby nah yana da rai, na kuma samun wani baby boy din, aunty plss ki wanke mun shi da kyau kinji, haka dai ta rika sumbatu suna tausarta da kwane kwane, har lokacin daya iso misalin 6am.

   banda shariya da tsaraban harara ba abin da yake samu, gaisuwarma daker aka amsa mai, su zahira ko kallo bai ishesu ba, inama shi yana can yana ta matarshi, don maganan gaskiya ta bashi tausayi, harta fada na kwana daya.

  duk ya damu kanshi, duk tunaninshi akan maganar auransu da ummeetah ce yasa ta shiga wannan tension din, kallon inda yake ma taki yie, har sanda nurses suka shigo yin mata toileting.

   gaba daya suka futa dakin, sai da suka kammala gyarata tare da bata medication dinta na safe, sannan suka koma ciki, lokacin ma harta kara samun wani baccin yayi gaba da ita, kafun yen uwa su fara tururuwan zuwa, banda dai ummeetah don maami tace ta zauna ta huta yau.

   
  

***
  Kwana uku cur yau da yinmata CS, zaune take kishingide jikin pillow dake bisa gadon, sanye da wata yer abaya data fara samun daman sawa, ta hade giran sama dana kasa, yayin da idanunta sukai jaxur suka kumbure don kuka.

   tun sanda ta samu labarin abin data haifa ya koma, ta rasa sukuni, kullum kuka da sumbatu, yaune ma kawai aka samu abin yayi sauki, wata nurse ce ta shigo cike da firirita zata bata medication dinta na rana.

  bisa wata yer plastic chair ta zauna kamar wata doctor, tana jawo hannun suhymah dake zaune kamar gunki, tare da fara a'ikinta na sauya mata canular da za tayi, kamar an tsunguleta ta dago da fadin,,
 
   madam kece wacce akama CS on saturday ko, kika haihu ba babyn sannan aka juya miki mahaifa, ta karisa maganar cike da makalkale murya, a sanyaye suhymah ta dago daskararrun idanunta tana fadin,,

  what aka……, sai kuma ta waske da fadin,,

  eh nice aka kawo on saturday, daidaita canular take a cikin jijiya da fadin,,

   eyaah kiyi hakuri fa, a'i kinyi bleeding sosai, shi yasa DR. masrur kawai suka yanke shawaran rufe miki haihuwa, saboda in aka barshi zai iya zaman miki matsala, ba suhymah ba, harta haj. falmata da sai yau tasan da maganar daskarewa tayi a wajen, dai dai sanda wata colleague dinta ta shigo tana fadin,,
  
  ke hajjo, kin bani da kalan wannan surutun naki, inkika fara a'iki, tsaf za'a iya koranki da wannan dabi'ar, kina da hankali kuwa?, da sauri ta mike zaraf, sanda taga suhymah ta fisgi hannunta data gama kare sanya mata plaster tana dafe kirji da fadin,,

   na'am, eyeeeee, nie suhymah aka juya ma mahaifa, na shiga uku na lalace, wayyoo mum, wayyoo Irfan d'ina, ku kawo mun yaro nah, plsss plss s ss……...,,

  ta kasa karisawa saboda numfashinta daya fara yin sama sama, da sauri haj. falmata ta rukota tana daka musu tsawa dasu kira musu doctors, da sauri wancan ta futa tana kiran doctor.

  tsananin bacin rai ya kusa watsa ma yarinyan mari, shi yasa be fiye son student suna binsu theater room ba, in za ayi a'iki, gudun masu hali irin na hajjo iya surutu, a zafafe yake fadin,,

  don't yhu know ur profession, are yhu mad?, ko so kike kie karisa patient din, da sauri ta girgixa kanta da wan katon murya take fadin,,

  no sir……,,

  shout up&get lost, before i deal with yhu nonsense, da sauri tabar waje, cikin kwarewan a'iki ya soma bata taimakon gaggawa, daker aka samu ta dan dawo normal, suka mata allurai don ta samu hutu.

   dai dai sanda sadeeq yaxo, hakuri doctor ya rika basu shida sauran relatives din, haj. falmata dai in hankalinsu yayi dubu ya tashi da wannan mummunar labarin (Allah shi kyauta).

***
A kwana biyun duk ta rasa natsuwarta, sai fadi take a kawo mata Irfan d'anta, tare da kiran auntyn nata tana jera mata kuka, itama sosai ta razana da lamarin, abubbuwan duk sun cushe musu.

  da gudunshi ya shigo, sai kuma yaja ya tsaya yana kare mata kallo, kanta na kasa tana danna waya, tana dagowa ta ganshi ta cillar da wayan tana mika mishi hannu da fadin,,

   Irfan dina zo, zo wajen mummynka, dai dai sanda mummy ta shigo, ta ruko hannunshi har gaban gadon tana fadin,,

  jeka mummy ko?, hannun mahaifiyarsa ya kama, zata dagoshi mummy tayi saurin dakatar da ita da fadin,,

  daughter a'iki fa, kuka ta sanya tana rungumeshi tsamm, sanda mummy ta daura mata shi a jikinta, ya sanya hannunshi yana share mata hawaye da fadin,,

  mummy plss kie daina kuka, ciwo ko?, zai daina kinji, wani kukan ta sake fashewa dashi, tana fadin,,

   wayyoo aunty na cuce kaina, d'an da yake mallakina kwaya d'aya tal na bama kungiya, yanxun wazan kalla inji dadi, aunty haj. Biswa sun yaudareni, basu tara komai ba sai kungiya cin amana, da sauri mummy ke dafe mata baki da fadin,,

   daughter plss kie natsu mana, maganar dana zo muyi kenan, ta jawo Irfan dake binsu da kallon  rashin fahimta, tana fadin,,

  jeka wajen daddy a reception, ya kalleta da fadin,,

  zaki lallashi mummy nah ne?, kanta ta daga mishi da murmushin yake, a kumatu ya sakar ma suhymah kiss yana dira daga kan gadon, daga haka ya fice daga dakin.


*fatan alkhairi*

share
comment
vote

*Matatace 2019*
Na meemartjj
[14/08, 14:29] Dala Grp: 🕯🕯🕯
    *MATATACE*
          🕯🕯🕯
  

story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjj 

*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty Ummeetah any my Fa'ixation._

page 65~66

__________A hankali take sauke ajiyar zuciya, tare da share Hwayenta, sanda mummy ke dialing number haj. biswa da video call, sosai suka natsu lokacin da kiran ya fara shiga.

  hoton hamshakiyar macace ya bayyana, tana zaune bisa wasu tsadaddun dinning chairs, taji gwala gwalai a hannu, wanda ya futo ta cikin hannun zumbulelen hijjabin dake jikinta har kasa, cikin salama mummy ta fara kai gaisuwa da fadin,,

  ina gaisuwa shugabar kungiya, da fatan an tashi lafia?, cikin kasaitaccan murmushi ta amsa,,

  barka dai haj. yagana, inace me jiki dai taji sauki?, ajiyar zuciya mummy ta sauke tana fadin,,

  to sauki da dama, dama dai kan lamarin nan ne da mukai magana, uwar kungiya a duba mana, a'ikifa ya lallace, komai ya sukurkuce, plsa ki duba…………, da sauri ta dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu da fadin,,

   dakata, ban fahimce kiba, mun riga da mun gama wannan maganar tuni dake, haj. yagana ko kun manta ranar da kuka zo, a gaban idonki yerki ta shiga kungiyar mu akan biyar bukatanta da yarjejeniyar da mukayi akan kar wata mace ta rabi mijinta, an jaddada mata tace ta yarda, baxan manta ba ana gobe daurin auranta, to sai yanxun zata dawo mana da hannun agogo baya, ko dan taga yanxun ta haifeshi ne harya girma, shine tak……,,

   da sauri suhymah ta fisge wayar, da wasu hawaye da suka wanke mata fuska tana fadin,,

   wlhy ban yarda ba, munyi yarjejeniya akan zan samu biyan bukata nah, kun zalunce nie kunce zan samu yanda nake so, a karshe kuma ina zaune saiga mijina da mata harda cikinta, ta tsananta kukanta da fadin,,

   haba haba, wannan zalunci yayi, yawa, wacce irin kungiya ce wannan mara adalci, to nie gaskiya yanxun bana bukatar komai daya wuce d'ana, bani da burin daya wuce inga na haifi yara da yawa, suna kaiwa da dawowa, amma yanxun mafarki na ya zama ba gaskiya ba, Irfan ne kawai wanda ya rage mun inna kalla zanji dadi, plsss na rokeku kubar mun d'ana, baxan iya rayuwa ba Irfan ba, wani

Please Login or Register in order to submit comment