Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sofa chair din da take zaune, yana cigaba da amsa kiran daga tsaye, kasa kasa kuma yake kallonta, da ayyana,,

  hmmm, wa yaga ummeetah uwargida, ita dai kanta na kasa, tana wasa da gefen viel dinta, can kuma ta dago kai, caraf suka hada ido, tana dan tsuke bakin nan, da kyalla mishi yen idanuwa, ba shiri ya nemi waje kusa da ita ya zauna, har suna kokarin gogan juna, sosai yake kallonta da cigaba da fadin,,

   gata nan kusa dani zaune, da sauri ta dago kai tana kallonsa, da tunanin killan su auntyn sune, shiru yayi kafun taga yayi yer dariya da fadin,,

  ohh baki yarda ba, can kuma yace,,

   hmm, hakane gimbiyata am just kiding, da sauri tayi kasa da kanta, gabanta na wani irin fadi, da alama matarsa ce, yayi wata yer dariyan suna sallama da fadin,,

  luv yhu too, ya sauke wayar suna bin juna da kallo, kawai saiji tayi yace,,

   Ranki shi dade barka da safe, ta zaro ido, kafun ta gama mamakin zancen nasa, taga ya daga wadannan papers din dake zube bisa table, da wani gintse fuska, da gaske yake kuma fadin,,

  amm, Ranki shi dade dama wani alfarma zaki mana, kisa mana hannu a wadannan takardun, ya karisa maganan daga kallon papers din, yana maida idanunsa kanta, da wani mamakin take kuma zaro ido, koda tasan yana da wasa da dariya wani lokacin, amm......,  ya katse mata tunani da fadin,,

  kina mamaki ne, murmushi kuma yayie, yana maida papers din ya ije, da kishingida bayansa jikin kujeran, yana fadin,,

  ya gajiyan kuka kuma, kin gama?wannan karon murmushi ta sakar mishi tana kasa da kanta, ya kuma gyara zama da fadin,,

   karki damu, nasan damuwan da kike yie, so serious yake fadin,

  nayi miki alkwari, in sha Allahu ba zaki kuma maimaita rayuwan da ki kayi can baya ba, zan tabbatar na cika alkwari, kamar yanda na daukan ma Affahn kie, da murmushin farin ciki ta dago kanta tana fadin,,

  to, Baffah nogode, ya dan nisa da dagowa yana fadin,,

   kin iya signature ko?

   eh, na iya, munyi lokacin da zamu rubuta junior weac dinmu, hakama ID card dinmu na islamiya sai da mukayi, ya zaro wata yer design pen, gaban milk din dakakken shadar daya saka da fadin,,

  good, so nake kisa mana hannu, a wannan takardun, ganin beyi maganan da wasa ba, ya sata amsan pen din, yana nuna mata inda za tayi signing din, ba bata lokaci ta zana, yana fadin,,

  wow, such a lovely signature, a tare suka dago da murmushi, suna kallon juna, ta mika mai pen din yana amsa da cigaba da fadin,,
 
   wadannan takardun zakka ne, da za'a fitar, yayi dan shiru kafun yace,,

   amma ina tunanin ko in bada duka ne, da sauri take fadin,,

    zakka fa kace uncle, yace,,

    yess, kin sani a'i, tana jujjuya ido tace,,

  eh, malamin mu ya fada mana,  yana daga cikin rukunan musulinci, abune mai kyau, Baffah ka bada duka kawai, Allah zai baka ladan, tunda ta soma maganan kallonta kawai yakeyi, kafun ya mike yana fadin,,

   ouk, ammafa bani ne zan fitar zakkan ba, kece zaki fitar, da sauri ta dago kai da fadin,,

   nie kuma, gira kawai ya daga mata sama, da jefo mata tambayar,,

  ko a fasa badawa, girgixa kanta tayi da fadin,,

  a'ah, kafun tayi wani maganan yayi hanyar futa da fadin,,

  ouk, ki shirya kayanki yanxun zanzo mu wuce, daga haka yabar dakin, sosai yaji dadin kalamanta, itakam ajiyar zuciya ta saki da mamakin kalaman ita zata fidda zakkan, kai bata gane, can ta basar da zancan da wasa ne kawai yake mata, kafun ta fara jin dadin abin da yace, kan rayuwan da tayi a can baya, Allah yasa haka.


    kudine kimanin miliyan6, wanda aka raba biyu, 3-3million, cunkushe a viva leda guda biyu, su biyu ne mutanan magidanta, sai Nurien dake gefensa, wanda ke kula da harkokinsa na gari ABJ, kuka sosai daya daga cikin magidanta yakeyi, ganin yau shine da kudi jaree na kanshi, har 3million, yayin da dayan ke faman xuba godiya, toh daga wanda dan uwa ya rasu ya bar mishi marayun yeyenshi, ga nashi, sai dayan da yawancin yeyen shi sikla patient ne, ga mahaifyarsa ma dake kan jinya, sun kasa dena godiya, shidai murmushi yakeyi, da fadin,,

   kunga, ku ruke godiyan ku, burina shine kuyi amfan da kudin ta hanyar daya dace, saboda wata rana kuma ku bama wani, kaman yanda aka baku, sun jima suna tattaunawa, kafun kowa yasa hannu a nashi takardan, suka tashi kaman yanda yake kuma sanar musu, zai sa a sasu a hanyar kasuwanci, suka tafi da dumbin farin ciki.


   An kammala kai musu kayansu cikin mota, sannan sukai sallama da abokan azzikin sa, wadanda zaima dan alkhairi yayi musu, wasu kuma yace za suyi waya, daga nan suka wuce, yau kam tare suke zaune a gidan baya, minute by minute, sai ya juya ya dan kalli inda take, kayan ya mata dass a jikinta, yafe da dan gyalenta bisa ka,,

   haka suka isa airport din, tun a nan ummeetah ke baxa ido, basu wani jima ba, fasijojin suka fara shiga, ummeetah ce a gaba, bayan wasu mata guda biyu, dake gabanta, saishi dake bayanyta, sanda zata daura kafanta bisa stairs din jirgin, rankwafo da kanshi yayi yana fadin,,

   karki manta addu'an, abin hawa, cak ta tsaya tana juyowa, da murmushi take dan daga kanta alaman gamsuwa, don kuwa ta manta, kafun ta juya tana jero addu'an, suka fara taka matattakalan jirgin,,

  idanu kawai ummeetah ta bude da kallon cikin jirgin, data sha gani a TV ko kuma littafi, mutane da dama suna yin wani site, amman su sai taga nasu barayin daban yake,,

  wow, shine abin da take ayyanawa, wannan wajen shine ake kira da VIP, aka nuna mata seat dinta dake site din dama ta zauna, yayin da shi kuma ya zauna a bangaren hagu,,

   ta gefen ido yake kallonta, cikin natsuwa take bin komai da kallo, kafun ya maida hankalinshi kan wayarsa yana latsawa, can kuma aka fara sanarwa  da a saka belt, tare da kashe wayoyinsu,,

  wannan yasa ya kashe wayar yana maidawa aljihu, tare da saka belt din dake seat dinshi, ana faman cigaba da bada sanarwan mintocin daya rage jirgin ya tashi, da sauri yake kai dubansa site din da ummeetah ke zaune,,

  ya sauke ajiyar zuciya, sanda yaga daya daga cikin ma'ikaciyar jirgin na taimaka mata, ta sanya nata belt din, ummeetah tayi tsamm sanda taji jirgin na fara tashi sama, komawa yayi yana kishingida da kyau, tare da lumshe ido, hakanan yake jin wani nishadi game da wannan tafiyan, ya dan nisa kadan, so silent yake fadin,,
 
    Allah yasa ya zame mun alkhairi, da wannan jirgin ya tashi, da fara keta haxo, suka dauki hanya.

 

    *_wasu suna complain da sun kosa a gane matsayin ummeetah gun sadeeq, tom kuyi hakuri, labarin ne nima yana bani ciwon kai, amman da yardan Allah, in muka dawo after ramadan, za a cigaba daga inda aka tsaya, abin da muka rubuta dai dai Allah ka bamu ladanshi, kuskuren dake ciki kuma Allah ka yafe mana_*

  *a wannan wata mai alfarma da zamu shiga, ubangiji Allah ya gafarta mana zunuban mu, baki daya, Allah ya amshi ibadun mu da ayyukan mu na alkhairi, Ameen.*



_fatan alkhairi, Bissalam_



comment
share
Matatace
*2019*

meemartjj...........✍🏻
[14/08, 14:29] Dala Grp: 🕯🕯🕯
            *MATATACE*
     🕯🕯🕯

     

story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjj

   
*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty Ummeetah and my Fa'ixation._

Assallamu alaikum
*_Ina miko gaisuwan fatan alkhairi, gareku enuwa, da fatan kowa yayi salla lafia, Allah ya maimaita mana, ibadun da kuma mukayi Allah ka amsa mana, ka samu cikin entattun bayi, Allah ka gafarta mana dukkan zunuban mu, ka yafe mana kurakuran mu, Allah kasa mu dace da alkhairi...Ameen._*

   *_plss a rika ije karatun lokutan sallah, makaranta, tare da ayyuka masu muhimmaci, kar a manta da azumin sitti shawwal, a daure, a'ikin lada yana da yawa._*


_Da sunan Allah mai rahma mai jinkai_

  page 29/30

   ___________A hankali fasijojin ke sakkowa daga cikin jirgin, ta dan numfasa sanda ta sauka step din karshe, shima dake bayanta ya karisa sakkowa, sauran fasijojin na cigaba da futowa suma.
  
    sosai yayi mamaki, ganin suhymah bata zo tarbanshi ba, duk irin zumudi da dadin bakin data gama mishi a waya, abin yadan sosa ranshi, yana ganin wasu mazan da suma iyalansu ke kasan sunxo tarbansu, amman banda nashi,,
     
   Allah ya taimaka, mota daga companyn da yake a'iki, tazo daukansu, har gida aka saukesu, shi yayi amfani da extra keys din dake wajensa ya bude suka shiga,,
  
  gaba daya agajiye yake, bisa wata sofa chair da sukayi zobe a tsakar madaidacin falon ya zube, kanshi bisa sama yana lumshe ido, yayin da ummeetah ke cigaba da shigo musu da kayansu,,
 
   gefen kayan taja ta tsaya, tana kare ma falon kallo, gidan ya tsaru fiye da tunanine mai karatu, kusan minti uku, kafun ya bude idanunsa yana juyo da kanshi da sauke kallonsa a kanta, dai dai sanda suke hada ido, ya dago daga kishingidan da yake, yana zama da kyau, wani daki ya kalla dake kallon bayansa, da idanu yake dan nuna mata da fadin,,
  
  kie kwashi kayanki kie shiga dasu can dakin,,

   tom, kawai tace  tana fara jan babban trolley din tare da nufa dakin daya nuna mata, a hankali ta turo kofan ya bude, kai tsaye ta shiga ciki, dakin dan dai dai, mai kyau dashi, yaji medium bed, da safe dinshi da mirror, da sauran yen kayayyakie, sai wani kofa da take tunanin ko bayi ne, taja trolleyn har wajen safe din kafun ta koma ta dauko dayan,,

  sanda ta futo harya kwasa nashi kayan yabar wajen, ta numfasa, tana kare ma falon kallo, kujerun sun mata kyau, sai dan glass center table dake tsakiyansu, can daga gefe, wani design TV stand ne, mai hade da yen drowers masu kyau, sai books bar dake daga gefe daya, komai na bisa kan tsari,,

  can dan gaba kuma ta hangi wani dan corridor mai dauke da two bedrooms da suke kallon junan su, tana tunanin maybe nan ne site din daya shiga, daga nan kuma sai kusa da dakin da ta shiga da kayanta, wani yer karamar dinning area ne, mai dauke da dinning table da four design chairs dinshi masu kyaun gaske, sai wata standard fridge dake gefe daya, daga dan ciki kuma tana hangen wani dan corridorn, dake dauke da kofa, inda take tunanin ko kitchen ne,,
 
    ta numfasa tana bin mayan windows din, da suke kasa kasa, sunji cottons na alfarma, da alamu milk ne kalan cottons din, amman tana tunanin maybe datti ne, ya mai dasu me ruwan golden, jin alamun kaman za a futo ne, yasa tayi saurin jan dayan trolley din daya rage tabar wajen.

  Daki ta koma tana sakin ajiyar zuciya, tabi ko ina da kallo tsaf tsaf, amman akwai inda za ace yayi kura, gaban safe din ta isa ta bude, kurane sosai a ciki, yayin data shiga goge ko ina, sannan ta jera wasu kayanta cikin safe din, tare da shirya komai yanda ya kamata,,

  bayin dake dakin ta nufa, a hankali ta tura kofan tana budewa, baki kawai ummeetah ta saki, bayi kaman ba bayi ba, komai tsam tsam, wata katuwar washing machine na gefe, da dai sauransu, ta dan karisa wajen wash hand, tana murmurde kan design tap din dake jiki, babu kyauyanci ruwa ya shiga zubowa, murmushi ta samu kanta da saki, kafun ta kashe ruwan tana futowa bayin,,

   bakin gado ta dan zauna, tana nisawa, da tunanin ko wace irin kalan rayuwan za tayi a nan oho, hayaniyar yara taji kaman ta bayan wani window dake facing din backyard din gidan, yasa da sauri ta mike ta nufi wajen tana yaye cotton din wajen,,

  wow ta fada tana bin beautiful flowers din dake zagaye da gidan, gefe can kuma wani gidan ne iri daya da wannan, ta lura gidajan a jajjere suke, kuma iri daya, flowers dinne kawai ya rabasu, daga kai sama take da leke leke, can kuma ta zuge glass din window, tare da saka kanta waje, murmushi take, sanda ta hangi yara yen uwanta yen nigeria, me kimanin shekara shida da yer shekara hudu, sanye suke da lace, an musu wani dikin design bubu gown, sai sauran wasu yaran turawa, wasa suke sosai a wajen wani kofa da take tunanin ta kitchen din gidan ya bullo, can ta hangeshi,,

   wancan kaman Irfan, shine abin da take ayyanawa, sanda ta hangi yaron da befi 5years ba, kwace bisa tyles din  dake varender wajen, ya ziraro da kafafunsa bisa yen stairs din wajan, ga yara nata wasa amma shi yana kwace yana kallonsu,,

  ummeetah, tajiyo muryan Baffanta dake kiranta, wannan ya sata saurin barin wajen, tana garxayawa falon.

  yana sanye cikin farar jallabiya, alama har yayi wanka ya sauya kaya, kallo daya zaka mishi ka gane alola yayi, yana ta gyara hannun rigan da kallonta dake fadin,,

   Baffah gani, kai tsaye yake fadin,,

  tym din sallah yayie, zaki iya zuwa kiyi, zaki kalli nan site din, in zaki fuskanci alkibla, ya nuna mata wata agogo dake manne jikin bango tana a'iki, da fadin,,

  sannan zaki iya duba lokutan salla in yayi, da fatan kinsan lokutan da ko wacce sallah ke shiga ko ?, kanta ta daga da fadin,,

    eh, yace,,

     good, nie na tafi masjid, kie kula da gidan, daga haka ya fice, tana karisa fadin,,

  saika dawo, ta koma ciki tare da nufa bayi, sai data wanke ko ina, kafun ta dauro alola ta futo, har lokacin tana saka wacce irin rayuwa za tayi, ta ciro daddumanta da aka sako mata sabo, sai hijjabin sallanta tun na gida, littafan addininta dama ta shiryasu cikin wani dan steps data gani a tsakiyar safe din, ta shimfida dadduman ya kalli inda ya nuna mata nan ne gabas, tana kabbarta sallah.

 
 
 
    Motarsa ya faka a haraban gidan, bayan ya biya wata restaurant yayi musu take away, futowa yayi daga site din driver yana kulle kofan, tare da komawa ta dayan site din yana ciro wasu ledoji, nan ma ya maida ya rufe, yana sanya ma motar security, ya nufi entrance door din, kaman daga sama yaji yana kwalla mishi kiran,,

   daddy!daddy!cak ya tsaya da furta kalman,,

  Irfan, da sauri ya juyo, shine fa yana rugowa a guje da murnansa, shima dukawa yayi kasa da sauri, yana ba yaron wani huge hug, dake fadin,,

  daddy i miss yhu, i miss yhu so much, ya fada maganan kaman zai kuka, yarr jikinsa yayi mishi, sakamakon hucin daya jie ya daki wuyansa, dake futowa daga jikin yaron, da mamaki yake dagosa yana kare masa kallo, da sauri yake fadin,,

   Irfan, are yhu alright, baka da lafia ne? kai ya daga sama, da jawo tafin hannun babansa yana fadin,,

   daddy jikina zafi, so hot, tausayin yaron ya kamashi, kobai fadaba yasan yaron beda lafia, a hankali yake kuma fadin,,

  mummy fa?,,

   tayi tafiya office, ya fada maganan yana langwabewa jikin  baban, sai da idanunsa suka ciko da wani kwalla, a hankali yakai bakinshi saman goshin yaron yana kissing dinsa, tare da kuma rugumeshi a jikinsa,,

  dai dai sanda yaran neighbours dunsu suka kariso, kowa na gaisheshi da mishi welcum, da murmushi yake amsa musu, tare da tambayar iyayansu, yana basu sakon su gaidasu, kafun ya kawo musu tsarabansu, sai da suka bar wajen, sannan ya mike sabe da dansa bisa kafada, ya nufi cikin gidan.

  kiranta ya kuma yie, ta futo sanye da hijjab data idda sallah, tana mishi sannu da zuwa, tare da kallon Irfan dake kafadanshi cike da annurin fuska take fadin,,

  lah Irfan dama kaine kayi girma haka, yaron dabe gane teba ya shiga mammakewa jikin daddynshi, yayin dashi kuma yaji dadin yanda tayi ma Irfan din, yana kallon yaron da dan nunata da ido yake fadin,,

  kaga aunty ummeetah, yhu know her right?kada kai yayi alamar a'ah, yana kuma nokewa, itakam sai blushing takeyi, ya mika mata wani yer farar leda da fadin,,

   ansa wannan lunch dinki ne, in kina bukatar wani abun ga kitchen can zaki iya shiga, ga kuma fridge dake dinning, nie zan kai Irfan hospital in dawo ne, cike da kulawa ta amsa tana fadin,,

   Allah ya kara lfy, sai kun dawo, sai daya ije sauran ledojin bisa dinning table, sannan yayi hanyar futa da fadin,,

  Ameen, ta bishi da kallon tausayi harya futa, Allah sarki tunda ya dawo be zauna ba, ta dan kada kanta tana wucewa ciki.

  sai data cire hijjab sannan ta zauna zaman cin abinci, koda ta bude take away din, abincine mai rai da lafia, ga uban nama a ciki, sai dai ko rabi ba taci ba taji yana son bata mata ciki, saboda rashin sabo da irin abincin, don haka ta tattara ta nufi kitchen,,

   nan ma sai data gama kare mai kallo, komai masha Allah, ga store da yaji kayan abinci, amman kaman ba'a diban komai, ta dan tabe baki tana barin kitchen din, ta bude fridge ta dauki goran ruwa sannan ta koma ciki, sai sakawa da kwacewa take yanda haduwarsu da uwargijiyan nata zai kasance,,

   Allah dai yasa komai yaxo mata da sauki, shine abin da tafi ayyanawa, sai kusan 4pm suka dawo, ya mika mata Irfan dake bacci tare da wucewa master bedroom din, nan ma alolan sallah la'asar ya kara yie sannan ya fice, itama ta shimfide yaron bisa gadon dake dakin, tana daura ninyar yin nata sallah.

   

   Tsoro ta rika jie ganin har kusan 8:30pm be dawo ba, ga Irfan daya tashi yana ta faman rigima, dole ta ciro wani zaninta ta goyashi, tana faman rarrashi, nan da nan kuwa ta samu yayi bacci, ga jikinsa ya dada zafi, ta kasa zama a dakin, don haka ta futo falon tana faman kaiwa da dawowa, sai da taji tsayuwar mota sannan ta saki wani ajiyar zuciya dadi, duk da bata san waye a cikin suba,,

  shine ya murdo kofan ya shigo, a idanunta kawai yaga yanda take a tsorace, tare da bin bayanta da kallo, yanda ta goya yaron das a bayanta, ya rufo kofan yana karisowa inda take rike da wasu ledojin, murmushi ne a fuskanshi yana fadin,,

  ya dai, naga kin wani firfito da ido ne, badai tsoro kikeji ba?,,

  Allah Baffah da tsoro, mu kadai nefa a gidan, ta fada kaman tai kuka, da dan mamaki yake fadin,,

   what, auntyn ki bata dawo bane?, kai ta daga sama alamar eh, sai kuma ya dan wayance da fadin,,

  ouk maybe tym din dawowanta be yiba, ya karisa maganan yana zama bisa kujeran a wani gajiye, tare da jingina bayansa, yana daga kanshi sama da lumshe ido, kafun ya bude yana juyowa da kallonta yake fadin,,

  hmm, kika iya goya wannan katon yaron a bayanki, da dan damuwa a fuskarta take fadin,,

  jikin shine yayi zafi......, a wani rude ya dago daga kishingidan da yayi yana faman fadin,,

  oh my god, kawo shi mu gani, da sauri ta soma ciku cikun sakkoshi, ta mika mishi shi, ya bude ledan dake kusa dashi, yana ciro wasu roban take away, tare da nuna mata tv stand da fadin,,

   dakko mun drugs dinshi, dana shigo dasu dazu, can ta kwasosu, tazo ta ije mai, sai faman cuku cuku yake da yaron daya farka yana rigima xai bashi abinci, yana faman rarrashinsa, yama rasa ta inda zai tallafo yaron, tsaye take a bayansu tana kallon komai, kafun ta zagayo tana dukawa bisa tyles din dake kasan kujeran da yake zaune, ta mika hannu cikin natsuwa tana fadin,,

   Baffah kawo shi, bari na bashi, ba musu ya mika mata shi, tare da abincin, duk ya wani tashe hankalinsa, sai kace shi ke ciwon, ta soma dan rarrashin yaron tana bashi, ga mamakinsa sai gani yayi yaron ya natsu waje daya, yana amsan abincin, ya saki wani ajiyar zuciya, yana cigaba da kallonsu,,

   sosai yaci abincin, ta kammala bashi, a tare suka taimaka suna bashi drugs din, ta gama tana mika mishi yaron dake kai hannu wajen daddynshi, shima amsarsa yayi, yana faman lallashi kaman wani jariri, ita ta gyra wajen tana maida komai muhallinsa, ya kuma mika mata wani take away din, bata fuska tayi da fadin,,

  Baffah wannan, nikam bana jin yunwa na koshi, harara ya jefa mata da fadin,,

  ouk tambaya nama kika tsaya yie, ko so kike saina baki a baki ne kaman yanda kika bama Irfan, zaro ido tayi da sauri, kafun ta amsa tana godiya ta wuce bedroom dinta, ita dai kawai ta amsa ne amma kam ba zata iya cie ba, wani murmushi yabi bayanta dashi, kafun ya mike sabe da Irfan da yayi bacci bisa kafadansa, ya wuce dashi nashi bedroom din, dake kallon nasu.


                       ***
    Ta karisa shiga da motar nata, cikin garage din dake ta bayan gidan, tare da kashewa sai wani murmushi takeyi da farin ciki, ta futo tana barin tsohon mr. jerry dake musu a'iki, ya rufe motar sannan ya rufe musu garage din, kamar yanda ya saba kullum,,

   tana wani kalailaita ta kariso bakin kofan entrance din, sai lokacin hasken bulb din dake wajen ya haskata, sanye cikin wasu riga da wando fela, sai american jacket din data daura a sama ya kawo mata har iya gwiwa, tasha rolling da black viel, tare da wata katuwar google bisa idanunta,,

  ta kara kiba, ga kuma wani haske da fresh da tayi na musamman, kai alamu ya nuna tana jin dadin zaman kasan na kanin babanta, makale da wata yer jaka, ta zira hannu ciki ta kwaso keys, tare da bude gidan, ta shigo tana maidawa ta rufe  tare da kwabe gyalen dake kanta bisa wuya, wannan ya bada daman ganin gashi dake kanta har dana kari, pake saman gadon bayanta, tana faman kwala kiran,,

   sweetheart sweetheart, tsam yayie sanda yake kuma runtse idanunsa da takaici, yana kishingide bisa makeken bed din dake bedroom din nasu, ummeetah ma dake lulube cikin blanket, gabanta ne yace rass, tayi saurin mikewa zaune tana furta kalman izti'axa, (toke suhymah taki ta sameki, Allah ka bamu ikon yin alkhairi, mu kuma shukashi), a hankali ta kuma koma ta kwanta tana lumshe idonta, tare da cigaba da karanto addu'an bacci da takeyin zuci zuci take baccin yayi awon gaba da ita.

   dinning ta nufa tana bubbude ledojin data gani bisa table din, hakan ya bata tabbacin ya dawon, tayi dan murmushi tana zare glass din idonta, da fadin,,

   ina ka shiga ne bby boo nah, ta tura kofan bedroom din, tare da shiga ciki, ko motsawa be yiba, bisa bag hanger ta rataye jakarta, tana cire gyallen gaba daya, tare da cillar da yen pencil shoe din dake kafafunta, tunaninta bacci yakeyi, ta zauna a hankali kusa dashi tana daura kanta bisa kirjinsa, da wani rungumesa tsam, ya bude idanunsa ta dago suna kallon juna da wani ihu take fadin,,

   my sweetheart yhu welcum!da sauri ya rufe kunnuwansa, yana yamutsa fuska da fadin,,

   angel zaki fasa mun kunni fa, tayi wani far da fadin,,

   yesss, nayi kewarka ne da yawa shiyasa, ta kuma huging dinsa da fadin,,

   i miss yhu i mss yhu imss yhu so badly, welcum back my baby boo, wata ajiyar zuciya ya saki, sai lokacin yake jin farin cikin ganinta, ya rungumeta da fadin,,

   i miss yhu too my angel, ya dagota da fadin,,

  amman na lura missing din nawa da yawa ne, yasa kika kasa zuwa kiyi picking dina airport ko?shiru tayi da rasa kalaman bayani, kafun tace,,

  am so sorry sweetheart, a'ikine sukai mun yawa shiyasa ban samu daman zuwa ba, ya dan girgixa kai da mamaki yana fadin,,

  wani irin a'iki, angel weekend nefa muke, atleast ko saboda dawowan da zanyi kya zauna ki tarbe mijinki, ta mike tsam da fara cire jacket din dake jikinta tana fadin,,

   oh shet, baby wai kai baka gajiya dayin complain ne, so nawa kake son in maka bayanin irin a'ikina, karfa ka manta a'iki har biyu fa yanxun nakeyi, ransa ya kuma baci a

Please Login or Register in order to submit comment