Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake fadin,,

  karki sake, karki sake kie dauki wannan shiriritan, kie saki jikin ki da yarinya nah, domin ta samu kulawan mahaifaya irin wacce ake bukata, kamar zatai kuka take fadin,,

  nie fa wlhy kunya nake jie, bai saki fuskan ba yace,,

  kinga riketa da kyau, maza maza kie kalli azzikin da Allah ya baki, wanda kudi basa iya siyanshi, kie kuma gode ma Allah, sannan ki sanya mata albarka da addu'a na alkhairi, ya sanya hannu yana kuma gyara mata tattausar showel din babyn ke ciki da fadin,,

  kinga abinki, plsss ki sanya mata albarka kinji, daker ta iya bude baki tana fadin,,

  Allah ya raya ta cikin addinin musulunci, ya lumshe idanu da budewa yana murmushi da fadin,,

  Ameen, Allah ya bamu ikon yin musu tarbiya irin ta addinin islama, a zuciyarta ta amsa da Ameen, kasa kasa kuma take kallon yarinyan tana mamakin irin hasken da take dashi,,

  kowa ta dauko a hasken nan oho, koda ba a nan abin yake ba, sai dai suna kama da,,

   Irfan, ta karisa fada cikin subucewan kalma tana dago kanta, murmushi yayi yana fadin,,

  suna kama ko?, sai lokacin ta fahimce maganarta na karshe ya futo, da sauri ta sanya hannunta ta rufe fuskanta da kunya, yayi yer dariya yana fadin,,

  nikam wlhy baxan cuce kaina ba, kawo tama kie gani, kamar jira takeyi ta mika mishi ita da sauri, ya amsheta sai baccinta takeyi, shidai baya gajiya da kallon yarinyan, sosai babyn ta shiga ranshi.

  ta dayan site din ya koma ya zauna, yana tattankwashe kafa bisa gadon, rungume da yarinyan a hannu, yayin da ummeetah ta koma da baya tana maida kanta bisa pillow, lokaci lokaci kuma tana satan kallonsu, a haka har wani bacci barawo ya saceta.

  shidai kasa baccin yayi don murna, baiki ya kwana yana kallon farin cikin rayuwan shiba, daga karshe dai da yaga tana son ta farka da fara yin yen kananun koke kokenta, sadadawa yayi ya ijiyeta, don dazu ma daker bahba balarabu ta rarrasheta hartai bacci.

  alola yayi ya koma dakin dake kusa da wannan yana kabbarta sallah, don yau jie yake kamar baxai iya bacci ba, nan ya dukufa mika ma Allah godiyansa.

 

   ***
  Misalin 2am na dare suka shiga wajen, banda kidi da warin giya babu abin dake tashi, enmmata kuwa ga sunan birjik sai wanda ka zaba(Allah ka tsare mana imanin mu).

  muheet fa kanshi duk ya kwance, tunda yake zuwa club bai taba karo da mai tsada irin wannan ba, sai wani lashe baki yakeyi kamar wani maye.

  zaune suka sameshi waje na musamman, bisa wata lallausar sofa chair, kafa daya kan daya, sai wata cup din giya dake hannunshi yana sha kadan kadan, gefenshi kuma yaran shine.

   waje aka ba masu muheet suka zauna, sai murna yakeyi da alama wannan yayi kama da cikakken mare imani, duba da irin sutura dake jikinshi yaji chains a wuya, da dankunnaye sanye a kuninshi,
  shiru kawai yayi yana kafe muheet da kananun idanunsa, tare da sauraran bayanin da yake mishi, sai daya tabbatar yakai karshe, sannan ya ije cup din, yana jawo wata small gun din dake gefe kusa dashi.

  kai tsaye ya saita bindigar a saitin goshin muheet wanda ya zazzaro ido ciki ya duri ruwa, kusan 4minutes kafun ya sauke bindigar yana komawa baya da kinshingida,,

  ummm, ya fada da jinjina kanshi, wannan alama ce dake nuna p.A dinshi dake kusa yace wani abu, gyaran murya wancan yayi, so serious yake kallon muheet da fadin

  kace d'an uwan kane, B~man kuma nada condition, idan ya futa operation baya d'iba ya tafi, saiya kashe sannan zai dauka, in ka gamsu da bayanan nan, sai ka bamu hoto, da sauri muheet ya mika musu hoton sadeeq da fadin,, 

  oga nidai koma menene, plss in kun samo dai a tuna damu ko yaya ne, donfa ya tara da yawa, wani murmushin oga at the top din yayi, kafun ya ije bindigar gefe yana daukan hoton da muheet ya ije bisa table din dake gabanshi, mamakine ya bayyana a fuskanshi yana fadin,,

  kana nufin wannan?, muheet yace,,

  eh my oga boss shifa, wata yer dariya yayi yana kallon hoton da fadin,,

  mutumin, ya maido hankalinshi sosai kan muheet yana fadin,,

  kai baka san wannan mijin marainiya ne ba, kuma rabi da kwatan dukiyarsa a'i ba nashi bane, natane, ya koma da baya yana kishingida da kyau, da mamaki muheet ke fadin,,

  oga boss kasanshi ne?, wata yer dariya mai hade da tari yakeyi, kafun ya kece da mai gaba daya, sai da yayi mai isarshi, kafun ya kalli wasu yaranshi dake wajen yana fadin,,

  boys ina bukatar target file na A A sadeeq, cikin hanzari suka kutsa cikin wani d'aki, sai gasu da file din, ya jefa ma muheet gabanshi, hannu na rawa ya shiga budewa, harda passport din dan uwan nashi makale jikin bayanan papers din dake cikin file din, a firgice ya dago kai yana kallon wanda aka kira da B~man dake zabga murmushin mugunta, kafun yace,,

 3months kenan da suka wuce naso kai mishi wata yer ziyara, na kwashe yen abin daya tara, sai dai tarihin marainiyar yarinyan daya shigo cikin bayanansa ne, ya sani jin tausayinshi kadan, kasan me yasa?,,

  ya fadi maganar yana duko da fuskanshi saitin na muheet, wanda kirjisa ke bugawa fat fat fat, a tsorace ya kada kai alamar a'ah, ya cigaba da fadin,,

  saboda nima ina da marainiyar kanwa data dalilin tane na shiga wannan rayuwan, ba don komai ba sai don inga rayuwanta ya ingata, don nima maraya ne kamarta, nasha wuya a rayuwa, ya daga da numfasawa yana fadin,,

   kai labarin yana da tsayi, yanxun maganan da nake ma Neenat tana kasar india, inda take karantar medicine, yanda bazan so rayuwanta ta shiga garari ba, haka baxan so na wancan marainiyar ya shiga garari ba, bari na sanar maka wani abu da baka sani ba,,

  mijinta shine jigon rayuwan tah, dan uwanka bashi da abin da zan dauka a wajenshi, matarshi ne keda abin dazan dauka, ya daga kafadu alamar ko a jikinsa yana wani tabe baki da fadin,,

  well, duk iskanci nah, ina dan raga ma maraya, ya kalli boys dinshi da fadin,,

  plss kuje dasu daga ciki, kuyi musu kyautar wata yer Bugatti, ko ku basu Ferarri, a zabure muheet da abokinshi daya rakoshi suke fadin,,

  what oga, plss mekake nufi da haka?, yayi yer murmushi mai sauti da fadin,,

  zaku gane idan kun shiga ciki, babu mai sani sanja waje don dole, sun riga da sunsa maboyarmu, ya karisa maganar da yinma yaran da suka jasu signa da ido, kansu kawai suka jinjina suna barin wajen dasu, ya doka tsaki sanda yake kallon hoton sadeeq da fadin,,

  stupid, na rasa me yasa nake tausayin guy din nan da yawa, ku dauke mun file dinshi, a'i cancel dinshi gaba daya a wajen nan, ya karisa maganar cikin tsawa, da sauri suka tattara file din suna barin wajen.



   ***
  Kukan babyne ya farkar da ita daga baccin da takeyi mai dadi, sai tajin abin kamar a mafarki, a hankali ta bude idanunta tana saukewa kan babyn dake shifide kusa da ita.

  da sauri kuma ta mike tare da zuba ma jaririyar idanu, sai ta kalli cikin jikinta, ta kalli jaririyan, a karshe kuma saita fara shafa cikin nata kamar wacce tayi mafarki.

  murmushi takeyi kasa kasa tana kallon yarinyan dake faman wanwantsala yen yatsu tana tsala kuka, bahba balarabu data sallame sallar subahin da idda ta rika haba da fadin,,

  ho ho ho nie balarabu, shin baki iya daukan yarinyan ko nono kie bata, kin wani tsareta da ido, da sauri ta jawo babyn tana daurata kan cinyarta, bahba balarabu dai ta shafa addu'a tare da mikewa, taxo ta taimaka mata don ta bata nonon.

  ana kuwa sa mata a baki ta kama, dama shi take nema, sai wani kauda kai take akan yarinyan, yayin da bahba balarabu ta wuce bayi don ta hada musu ruwan wanka.

  samun kanta tayi da shagala da kallon babyn, ta runtse idanunta a hankali tana tuno mahaifayarta, wacce ta rasa rayuwanta ta dalilin haihuwanta, a hankali take furta kalaman,,

  Allah sarki inna tah, ina kewarki, Allah yaji kanki yakai haske kabarinki keda mahaifi nah, tare da sauran musulmai da suka ruga mu baki daya, ta bude idanunta sanda taji ta kuma sanya wani sabon kukan, nonon ta kuma daidaita mata daya kauce daga bakinta, tako kama ta cigaba da shan abinta.

   ta sauke wani ajiyar zuciya sanda take kallon yarinyan da murmushi, sai data samu ta dan koma bacci, sannan ta lallaba ta ijeta, bahba balarabu kuma ta tasa keyarta bayi don yin wanka.

  sun dan jima a waje inda yake sanar da mutanan da suke abin azziki, arzirkin daya samu, su liman ana ta mishi barka, kafin suyo cikin gida shida Irfan, daya kosa yaga suprise din daddynshi yace zai bashi this early morning.

   da sallama suka shiga dakin, duk suka amsa musu, bahba balarabu na zaune bisa wata kujeran kitchen din gargajiya, ga dan baho a gabanta tana ta ma babyn wanka, yayin da ummeetah ke zaune can saman gado daure da zani, saita lulluba da wani babbar towel har kanta, Irfan yasa ihu da fadin,,

  lah daddy new born baby, da sauri kuma yayi wajen ummeetah yana fadin,,

  aunty ummeetah kin haifa mana babyn ne?, duk ya giride da murna, itakam sai wani dan blushing takeyi kasa kasa, bisa wata yer sofa chair dake gefe ya zauna yana gaisawa da bahba balarabu, kafun ya juya yana amsa gaisuwan ummeetah.

  ya zuba ma babyn ido wacce aka kammala ma wanka, bahba balarabu na dan cilla ta sama tare da cafewa da fadin,,

  cika masakin kie yarinya, da sauri ya kwakwalo ido yana fadin,,

  bahba ba zata fadi ba?, bata tanka mishi ba ta cigaba da cilla yarinyan sama tana yer dariya, ummeetah ma dan dariyan takeyi, ganin yanda idanushi suka furfuto waje, kamar yaje ya fige abinshi.

  can dai da taga d'a da uban su matsu a basu jaririyar, nade musu ita tayi cikin towel tana mika musu, har rige rigen daukanta su keyi, kusa dashi Irfan ya zauna, ya daidaita mishi yarinyan da kyau yana daura mishi ita kan jikinshi,,
 
  oya see ur face, ya fada maganar da nuna mish fuskar yarinyan, hakora a yashe yake fadin,,

  daddy iri da iri munyi anko ko? dariya akayi gabaki daya, ya kuma gyara mishi towel din daya bude da fadin,,

  baka mata addu'a ba, kace Allah ya raya fadimatu zahra'u, (favorite name ever, sister zarahjj, my aunty ummeelato, my fateen baba, kie taho kinyi takwara tawan) da saurinshi kuwa yace,,

  Allah ya raya mun sister zarahAA nah, duk aka amsa da Ameen, saitin da ummeetah take ya kalla da take wani faman kasa kasa da kanta, suna hada ido ya kashe mata ido daya yana jefa mata kiss ta isaka, da sauri ta kauda kanta, bahba balarabu data futo daga bayi kai ruwan data ma zahra wanka ta kalleta da fadin,,

  toh ke shatu me kike son cie ne?, shiru tayi tana tunani, yayi sauri fadin,,

  ana tambayar kine fa?, idanu suka hada tayi wani saurin basarwa, kamar ba da ita yayi maganar ba, baisan sanda ya rike haba ba da fadin,,

  toh nie sadeeq mijin yer fillo, kowa sai daya dara, harda ita data rufe fuska da towel, bahba balarabu na yer dariya tace,,

  na dai nika farar shinkafa, da zan miki masa ce, da sauri tace,,

  yawwa bahba wannan ma yayie, dama wainar nake son cie, tace,,

  to kie dauke flask din nan, ga kofi nan kie zuba kunun tukan ya huce, tukan inma fadima wanka na hadashi, da,,

  to ta amsa, Irfan na mika ma bahba zahra don a shiryata, ba don yaso ba daddynshi ya jashi, suma suje suyi wanka don yana so su futa, harya kai bakin kofa sai kuma ya tsaya ya juyo da fadin,,

  yawwa bahba, don Allah inason a rika yin abinci mai yawa na sadaka, kullum har na tsawon kwana bakwai, in sha Allah zan karo wasu kayan abincin, da fara'anta tace,,

  toh Allah ya yarda, ya kuma bada lada, da,,

  Ameen bahba, ya amsa kafun su fuce, a falo ya saka karatun al~qur'ani mai girma, cikin kira'an shiek Abdullahi Abba, iskan dake hurowa ta cikin windows ne, tare daddadan kamshin dake yawo a gidan komai tsaf tsaf, ya hadu ya bayyanar da wani irin natsuwa da rahma.




     ***
  10am dot munat suka iso ita da hibbat, sosai ummeetah taji dadi, ga kaya ma'ishi da maami ta hada aka kawo mata, harda su ferfesun dadi kala kala, kai mai jego dai na morewa, sai da tayi hawayen dadi ganin irin gatan da ake nuna mata.

  yen rugarsu ma suna ta shigowa, duk da wasu ganin gidan ke kawosu, dama an basu labari, sai ace babu sillar shiga, a bari saita haihu, a'iko taga tururuwan jama'a, harda wanda suke makotan rugar tasu, munat dai hana daukan babyn ma tayi da suke cike da zumudinta.
 
  haka dai su kayi ta amsar yen barka, yayin daya dawo da siyyaiyar kayan baby mai yawa, tun ana shigo dashi suna mamaki har munat ta koma dariya, shikam a wajenshi bega wani abin mamaki ba, munat ta kare dai tace,,

  yayan mu hala dai kudinka duka kaje ka zazzage musu, shiru ya mata kafun yace,,

  a'ah, kawai dai wani super market mu kaje nace su hada mun komai na kayan babys, wani dariyan munat keyi da fadin,,

  a'iko sai kayan babys, don wannan sai tayi haihuwa uku basu kare ba, ko a jikinshi ya tabe baki yana kishingida jikin sofa chairn da yake zaune da fadin,,

  ouk, is alright, dama haihuwar nie konan da wata shekaran ne, ina fata Allah ya ka……..., wani irin kallo da ummeetah ta bashi ne, ya sashi kasa karisa abin daxai fada, duk suka tuntsire fa dariya, har dashi daya manta rabon da yayi dariya irin haka.




    ***
  Sosai yen uwa ke murna da haihuwan nan, duk sai jikin suhymah yayi sanyi, musamman yanda taga yen uwa naji da wannan haihuwar, shima Abba ya bada tashi gagarimin gudummuwan, sun aunty batulah ma sun isa ana saura 3days suna da nasu dumbin alkhairin, komai sai dai ace Alhamdulillah.

  suhymah dai zuwa yanxun hankalinta a tashe yake, gaba daya kuncinta ya dawo sabo, ko barka ta kasa yin mishi ma.

   tunaninta kawai yanda yarinyan zatai ta xubo mishi ye'ye ita kuma ta koma juya, hawaye suka silalo mata, gaba daya duk ta sauya ta fada saboda tasota da kungiya suma su kayi a gaba, shi kanshi gogan tunda akai haihuwan bata kara sashi a idanunta ba, yana can kai na rawa tare da barin nairori,,

  tswwww, taja wani tsaki da ayyana,,

  dama haka rayuwa yake, duk ka gama haukarka kan d'a namiji, ka kauce hanya, ka cutar da kanka, sanda wani iftila'i kuma ya sameka, bashi zai hana shi cigaba da rayuwan jin dadinshi ba da wata matar, kana kall……...,,

  kiran daya shigo wayarta ne ya katse mata tunanin da takeyi, tana harare harare ta dauki wayar, sun gaisa sama sama, kafun ya daura da fadin,,

  angel kin duba kuwa pictures din zahra dana turo miki, a dan yatsine tace,,

  oh na manta bari na duba, daga haka ta katse wayar tana bude hotunan, murmushin ne ya subuce mata tana fadin,,

  she is just like my son, ta jima tana kallan hotunan, sake kiranshi ne ya katseta, tayi picking call din yana fadin,,

  kinga baby zahra tah, cikin daurewan wani fashewan kuka take fadin,,

  eh sweetheart na ganta, yerka tana kama da d'ana, sai dayi dan jim kafun yace,,

  suhymah ye'ta tana kama d'anki, da wasu harare harare take fadin,,

  ehmana sadeeq, mexan ce bacin wannan, naga dai yer kace ko, murmushi kawai yayi don ya lura giyan kishin ya motsa, tayi dan tsaki kafun tace,,

  amma duk da wannan bai hana nie jin son yarinyan ba, wlhy sadeeq babyn ku ta shiga raina, kamar ku bani, da sauri yake fadin,,

  suhymah a'i abin dana mallaka kamar naki ne, kece dai kike ganin kamar ba hakan ba, kin gane kie dauki zahra kamar matsayin d'anmu Irfan, kanta kawai ta jinjina tana amsawa da,,

  toh, sauri sauri sukai sallama, tana datse wayar saboda kukan daya zo mata lokaci daya, ba abin data tuna sai nata d'an daya koma.



*fatan alkhairi*

share
comment
vote

*Matatace 2019*
Na meemartjj
[14/08, 14:29] Dala Grp: 🕯🕯🕯
    *MATATACE*
          🕯🕯🕯
  

story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjj 

*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty Ummeetah any my Fa'ixation._

   *_wannan pages din naku ne, Peena Novels, ina yinku over, Allah yabar zumunci_*

page 73~74

__________Door bell din da aka latsa ne, ya sanyata dago kanta data daura bisa dinning table din da take zaune, ta share hawayenta tare da nufa kofan donta bude, da murmushinta take fadin,,

  kawas, sai kuma tayi sansaransan ganin yanda suhymah ta kode ta sauya kammani, cikin sanyi jiki ta bata hanya da fadin,,

  kie shiga mana ciki, ba musu surayya ta kutsa kai ciki, ita kuma ta rufo kofan tana bin bayanta.

  duk bisa rounded cushion din dake falon suka zauna, surayya tayi dan jifa da jakarta gefe daya tana fadin,,

  suhymah kinga yanda kika koma kuwa, kawata wai me yake damun kine?, wani dan murmushin yake tayi kafun ta fara kwalla kiran,,

  merry, merry, da sauri yarinyan da aka kira da merry ta futo daga site din kitchen, a yatsine ta dan kalleta kafun tace,,

  kie kawo ma bakuwata wani abu na sha, da girmamawa yarinyan ta amsa da,,

  ouk ma, daga ta juya ciki, sosai ta dawo da hankalinta kan surayya tana fadin,,

  kawata ina cikin matsala, itama wani ajiyar zuciya ta sauke da fadin,,

  hmmm, ke kike cikin matsala ko nie ke cikin matsala, kawata akwai matsala fa, kie taimaka mana kie duba lamarin nan, gaba daya kungiya na cikin wani hali, kusan meeting na uku kenan da aka hada baki hallarta ba, kawata ina jiye mike matsala, da wani irin kallo suhymah ke fadin,,

  me kike nufi?

  hmmm, shine abin da surayya ta fada tana dan dube duben gidan,  kafun tace,,

  kawata irin wannan daular, irin wannan duniyar da kike ciki, kike son kie bari, wlhy kungiya na gabda tona miki asiri, haj. biswa sun hada meeting mai zafi a kanki indai baki basu yaron nan......, da sauri suhymah tace,,

  dakata surayya, idan har abin daya kawo kie gida na kenan, to kie sani……..., door bell din da aka kara dannawa ne ya katse mata maganar, ta mike tana dan tsaki tare da zuwa ta bude kofan.

  a tare suka dawo cikin falon da mummy data hallara itama yanxun, dai dai sanda yer a'ikin ta kawo ma surayya drinks tana zuba mata, mummy ta zauna itama ta zubo mata, bata amsa ba ta dubi surayya da fadin,,

  keep that drink aside, surayya ya ake ciki ne?, ajiyar zuciya ta sauke tana dire cup din dake hannunta da kallon side din da suhymah take zaune, ta hada giran sama dana kasa tamau, kafun tace,,

  hmmm aunty kenan kawata ta kasa ganawa fa, ta manta sanda kuko xo ta shiga kungiyan nan, sai da aka jaddada mata duk wasu conditions, duk kuma tace ta amince, a karshe shine take son sakamu cikin matsala ta saka kanta, don na tabbatar miki kungiya na gabda miki tonan siriri, da sauri mummy ke fadin,,

  na shiga uku nie yagana naga ta kaina, plss daughter na rokeki kiyi nazari akan wannan lamarin karmu bata bamu batar ba, cikin sosomun kuka take fadin,,

  haba aunty abin zaimun yawa ga mari ga tsinka jaka, da wanne zanji, Irfan ne kawai sanyin idaniyan daya rage mun inna kalla zanji dadi, cikin tashin hankali mummy ke fadin,,

  na sani daughter, nasan akwai ciwo, kuma baxan boyemiki ba, koni naso ace an bar mana Irfan, ko ba komai shi wani tsani ne da zaki taka yakai kie wani matsayi a gidan daula da nairori irin wannan, amma ya muka iya, idan fa asirin mu ya tonu to komai fa ya baci, surayya tace,, 

  aha aunty fada mata, abin da kawas ta gaxa ganewa kenan, zasu tona mata asiri, kuma ta rasa Irfan din, wanne yafi zafi, ta dubi suhymah sosai da fadin,,

  kawas kisan gaskiya gwara kie zauna da mijinki cikin wannan azzikin, bafa dole bane saika haihu za kayi walwala, mutane nawa ne suka rasa haihuwan kuma suke rayuwan jin dadi, mummy da sauri take fadin,,

  umm humm, daughter kinji ko, duba, duba nan kie gani, ta miko mata faskekiyar tab dinta data bude photos din wani building na makaranta,, 

  wow, shine abin da suhymah ke fadi, makarantar ta tsaru ta keru ta bugu iya buguwa, kai za kace daga turai aka dakko aka dasa, da sauri take bude wasu video coverage da akayi na school din, ta dago kai da sauri tana fadin,,

  aunty ina sadeeq ya samu kudin kera school din nan?, wata yer dariya mummy tayi kafun tace,,

  ina kuwa suhymah aljuhunshi, kina nan kin tada hankalinki a banxa, bakisan cewa mijinki ya riga daya zama billionaire ba, da sauri surayya ke fadin,,

  ke kawas yanxun ko ina kika zauna, indai ana maganar masu dashi sai mijinki ya biyo sahu, venture venture nawa ne da yake faman ginawa kika sani, kawata kina nan zaki tada hankalinki a banxa, kina tunanin duk randa mijinki yasan da wannan maganar zai cigaba da zama dake matsayin matarshi ne, hawaye ne suka silola bisa kuncin suhymah sanda take karanta sunan makaranta,,

  A A sadeeq International Academy, tabas tasan da zaman wannan makantar, amma bata san sanda aka kammala bama, ba kuma ta taba tunanin haka makarantar zai tsaru ba, gaskiya an kashe kudi iya kashewa, ta sauke ajiyar zuciya sanda mummy ke fadin,,

  daughter ina mai baki shawara kiyi hakuri, ki basu abin da suke nema, akwai tabbatarwan da jackson yayi mun kan cewa, yana tunanin ma d'aya daga cikin matanshi zai baiwa shugabancin makarantar, kina tunanin wacece wanna……..., tun kan ta karisa suhymah ta katseta da fadin,,

  aunty matarshi mana, wacce zata rika zazzage mishi ye'ye ye, surayya taja dogon tsaki da fadin,,

  baki da tunani kawas, har ana sako waccan mushen in ana magana, kinbi duk kin damu kanki akan wata yer kankanuwan yarinya, to bari na miki albishir haj. biswa ta miki alkwarin gyara abubbuwa su dawo dai dai, tass mijinki zai dawo naki ke kad'ai, kedai kawai kie cika ma kungiya alkwarin da kika dauka, wasu hawayen ne suka wanke mata fuska tana fadin,,

  baxan iya bar muku Irfan ba, shi kadai nafi bukata a rayuwa, don Allah kubar mun d'ana ku barmun miji nah, kallon kallo akeyi da mummy da surayya, kafun ta juyo da fadin,,

  oh my god kawas kie gane, nifa ina son in taimake kine, uwar kungiya bassu da tausayi, plss kie fahimce nie, ta gyara zamanta da kyau wajen cigaba da fadin,,

  kinsan duk wacce data shiga kungiyan nan sai da ta rasa wani abu nata, kuma bamu taba samun wata matsala ba, ke kadaice naki a'iki yaxo a karkace, suhymah kina fa kallo haj. mujibat akanta akayi a'iki last, kanwarta ta bada, a hannunta yarinyan kuma ta taso, da auranta ya tashi ita tayi mata komai na kayan daki, at last 8months da auran akai a'iki akan yarinyan, zo kiga yanda haj. mujibat ke kuka, wazai ce da hannunta a ciki, don haka kema waskewa kawai za kiyi, kuma kawas kinsan wani abu?, ta numfasa kafun ta cigaba da fadin,,

  a yanxun haj. mujibat bata kasan ma, tana can cairo ita da ye'yenta da mijinta, kinsan ye'yenta duk mata ne, kishiyarta kuwa Tana kauye mijin ya barta acan ita da yeyenta ko karatun azziki babu, ke sai ya share up to 6months beje inda take ba, a haka kuma zata gaji ta nemi sakinta da hannunta, sai abin da haj. mujibat tace dashi ake a'iki, suhymah kema haka nake fatan miki, kie zama shining star a gidan mijin kie, plss aunty ki tayani fahimtar da ita, mummy data zabga tagumi ta numfasa da fadin,,
 
  a'i daughter hakuri kawai za kiyi, nie kaina yanxun da a'ikin da nakeyi a companyn sadeeq na dogara, ga

Please Login or Register in order to submit comment