Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kanta zata kai kanta, taja tsaki tana komawa cikin bedroom dinsu.

A falon maami ya zube, inda kayanshi da driver ya shigo mishi dashi, yake ije gefe daya, ya jingina bayanshi da kujera, yana lumshe idon na fama, da tunanuka da suka mishi yawa,,

haka su muhibba, munirat da auta muneeb suka dawo school, suka tarad dashi, dukansu ta site din maami suka shigo, nan kuwa suka sa oyoyo, ana sakashi a tsakiya, da tambayar tsaraban su, ya zauna da kyau, kanshi na wani irin juyawa yake kallonsu, duk sun kara girma, harda muneeb da ya zankale kafa a tsawo, da dan murmushi yake fadin,,

kunga ku bari na huta, yanxun kaina ciwo yake mun, kuma kuje ku cire uniform, duk suka mike, shima ya mike, muneeb na tayashi da daukan jakarsa sukai sashin baki, yayin da munirat tayi nasu sate din, muhibbat kuma ta wuto dakin mu.


itakam ta makale cikin bayi, ta kasa futowa, muhibbat ta cire nata uniform din, tana daura towel da knowking kofan bayin, alamar itama wanka zata shiga, jin muryanta ne, yasa ummeetah bude kofa ta futo, wanka tayi amman sai zufa takeyi, tana kallon hibbat dake kallonta da mamaki, take fadin,,

Baffah sadeeq ya bar cikin falo?kai ta daga mata, da dan mamaki tana fadin,,

me ya faru, kin mishi laifi ne?,,

a'ah, shine abin da ummeetah tace, tana nufa hanyar wardrobe dinsu, kaman zata kara tambayarta, sai kuma ta shige bathroom din, da tunanin abin dake faruwa,,

ta kammala wankanta, ta futo ta shirya, tai salla, tare da nufa dinning don taci abinci, duk da nan ma saida tayi fama da ummeetah taxo suje suci abincin taki.


Sai bayan sallar la'asar su maami suka shigo, da ihunta ta shigo tana faman fadin,,

yeeee ance big bros ya dawo, ina yake muje mu tarbeshi, su uku ne zaune a falon suna kallo, don yau ummeetah ta kunshe a daki, kaman wata konanniya, ta kasa manta abin daya faru, hibbat na fadin,,

sweet mum, yana sashin baki, maami sannu da zuwa, maami tai murmushi tana fadin,,

yawwa sannun ku, mainat kuma tayi wani uturn tana nufa kofa da murnanta, munirat ce tayi saurin dakatar da ita, da muryanta da yake dan babba tana fadin,,

aunty mainat, na rantse miki karkije, am mishi laifi, sister tace ranshi a bace ya dawo, maami dai ta karisa shiga dakinta, mainat ta dawo da fadin,,

me ya faru, kaman suda ta gama zayyane mata komai, gaban mainat yace rasss, tana dafe kirji da fadin,

na shiga uku, yanxun ina ummeetahn, hibbat ta nuna dakinsu tana fadin,,

tana bedroom, shi yasa tun dazu ta kasa futowa, ta mike tana nufa bedroom dinsu hibbat, xaune ta sameta tana duba littafin makarantan ta, kaman kullum, tayi saurin ije book din, tana fadin,,

auntyn mu, sannu da zuwa, kusa da ita ta zauna tana fadin,,

yawwa ummeetah ashe abin daya faru kenan, hope dai babu abin da muheet yayi miki? kai ta daga alamar eh, tana dan dukad da kai, mainat na fadin,,

Alhamdulillah, sai kuma ta dafe kirji tana fadin,,

yanxun nasan nie kuma na bani da yaya sadee.... muryanshi da taji daga falo ne, ya sata zaro idanu, ta mike cikin sanda tana lekawa falon, ummeetah tabi auntyn nasu da kallon tausayi, don tabbas taji sanda yake tambayar mainat din,,

ya zauna sanye cikin black jallabiyan mai karamin hannu, yaran na dada gaishe shi, sanda yake tambayarsu maami, dai dai nan ta futo da fara'ar daya bayyana akan fuskanta, alama taji dadin ganin dan nata, tana fadin,,

manya manya, yau kune a kasan, ta karisa maganan tana zama, da dan murmushi yake fadin,,

maami nayi kewar kufa, tace,,

lallai kuwa kayi kewa, irin wannan zuwa babu sanarwa, ya dan sosa kai yana fadin,,

Allah maami, zuwan ne na lokaci daya na shirya mai, na dawo ma ba kwanan, tace,,

a'iko munje suna, wata diyar aminiya tace ta haihu, yarinyan kuma kawar maimuna ce, sai muka tafi tare, dai dai nan mainat tayi shahada ta futo, goye da hannayenta a baya, tana dan tafiya, cike da nuna alamar nayi laifi, da murmushi take fadin,,

big bros highly welcum, ya zabga mata harara, komai daya faru dazun, yana dawo mishi, ta zauna tana gaishe shi, bai amsaba yake fadin,,

kin kyauta, ta gane me yake nufi, amman don tsiwa sai cewa tayi,,

me ya faru?, ransa ya kuma baci yana fadin,,

ohh, baki sanma meya faru ba ko, don wulakanci nabar miki yarin........ ya kage da maganan, itafa wani lokacin in yana masifa irin haka, takan ga kaman zata iya dago wani abu, amman koma menene aje zuwa, burinta kenan, ganin da maami a wajan sai cewa tayi,,

Allah sarki, yaya sadeeq bafa abin daya faru, amanarka na nan lfy, yanda ka tafi ka barta, gaba daya maganar nata kunya ta sashi jie, sai yaga kaman kowa ya dago dalilin masifar tashi, yayi kasa dai kai, da raya,,

lallai mainat ta rainani, zata kara kwabo wata magan.... cikin zafi ya mike daga kinshingiden da yake, yan dukule hannu kaman zai taso da fadin,,

uban wa kike ma wannan rashin kunyan, kodan kinga na kyalle kie, da sauri ta mike tana komawa bayan maami da makewa, don tasan zai iya tasowa ya faffalla mata mari, maami na dan murmushi, don duk taji abin da munirat tace ya faru, take fadin,,

a'ah, kaga baba na, maida wukar, mainat a'i bata da laifi, ya koma yana dada zama, rai bace yake hararan mainat da fadin,,

maami, Allah kuwa, baki kiga tashin hankalin dana dawo na taras bane, kuma tasan yarinyan nan marainiyace, abin dake tsoratar dani kenan, maami tace,,

hakane maganan ka, amman inaso ka gane, itafa mainat bata da laifi, tana iya kokarinta sosai, abin daya faru kuma ya riga daya faru, sai mu gode Allah daya tsaya a haka, shiru kawai yayi, mainat na fadin,,

yaya sadeeq don Allah kayi hakuri, banxa yayi mata, ta kuma gyara murya tana fadin,,

Allah sarki aunty suhymah nah, nayi kewarta, baka taho mana da ita ba, sai lokacin yayi dan murmushin saman fuska, maami na fadin,,

da me gida nah, ba'a kawo mun shiba, ko yana makaranta ne?ya dan numfasa da fadin,,

suna can suna fama da karatu ne, naso mu taho tare, amman Allah bai nufa ba, maami tace,,,

Allah sarki, muneeb dake faman bata rai, yake fadin,,

yayah, tsaraban bafa ka bamu ba, munirat na fadin,,

nima nawa, ya dan runtse ido da fadin,,

kaiii, maami tace,,

gaskiyan sune, anyi tafiya za'a dawi, sai a kawo ma kowa tsarabansa, yace,,

maami kwata kwata na manta dayin wata tsaraba, saboda dawowa sauri nayi, ya kalli mainat da fadin,,

amman zan baki kudi, sai ku shiga kuyo tsaraban da kanku, yaran suka sa murna, maami na fadin,,

madallah, Allah ya kara budi, duk suka amsa da ameen, ta kalli hibbat tana fadin,,

wai ina umeetah ne?,,

tana daki taki futowa, ko abinci taki taci, saitin dakin ya kalla yana dan tabe baki, maami tace maza dauki abincin kice nie nace taci, ba musu ta mike tana a'ikata abin da aka sanyata,,

ya zauna nan suna shan hira da mahaifiyar tasa, ita kanta ta lura wannan zuwan nashi ya dan sauya ba laifi, sai gabda kiran sallar magrib ya mike, ya futa don gabatar da sallah.

bayan sallah isha'ima ya dawo, sai dai mainat kadai ya gani a falon, ya tambayeta maami, tace tasha magani ta kwanta, zama yayi, sai gashi suna hira, can kuma ya lura da anata kiran wayarta, alamar wani ne keson yin firan dare, ya dan tabe baki yana mikewa da fadin,,

bari naje nabarki kiyi tadinki, ta dan zaro ido, da fadin,,

kai yaya sadeeq just a friend nefa, murmushi kawai yayi, yana fadin,,

a kawo mun dinner na, don yunwa nake jie, tace,,

tom za'a kawo, yana juyawa kuwa ta daga wayar ana faman smiling, ta gefen ido yake kallonta da raya,,

ko wani garan kuma aka samu oho, ya bude kofan yana futa, yana cigaba da raya,,

kai enmmata ba'a rabasu da en samari, cak ya tsaya da tafiya, dai dai entrance din wajen, da kuma raya,,

hakanefa, yarinyan nan itama fa ta shiga sahun enmmata, yai dan tsaki da cigaba da tafiya, yake fadin,,

ya kamata inxo inyi tunani a kanta, daga haka ya wuce site din baki, yana dada mamakin yanda ta girma lokaci daya haka.

luv sosai take zubawa a waya, ba tare da tasan dare na kuma yiba, can ta tuna da batun kai mishi abincin da yace, ta katse wayar da neman excuse, kafun ta nufi dinning tana shirya komai, dakin su hibbat ta nufa da fadin,,

sweet child, sweet child an baje bisa gado, can up ana sharban bacci, ummeetah ce zaune bisa mirror stool tana karatun exam, ta zuba mata ido a up din, tana fadin,,

kai wannan akwai banxa, ke da anyi isha'i sai bacci, ta kalli ummeetah tana fadin,,

yawwa don Allah ummeetah zonan kikai ma yayanku zance ko baffan ku oho, abinci, ta dafe kirji tana dan zaro ido da fadin,,

nie kuma, murmushi mainat tayi tana fadin,,

eh kefah, karki damu kin fie kowo sanin halinshi, basai na fada miki ba, mikewa kawai ummeetah tayi zata saka hijjab bisa riga da skirt din da suma suka kamata, wanda dankwalin shine kawai rataya bisa kanta zuwa kafadarta, mainat tace,,

no, don Allah zoki dauka, tun daxu yace akai mishi fa, dole ummeetah ta wuce tana bin bayan auntyn nasu, bisa wani tray ne aka shirya komai, ta dauka tana nufa kofa, ita kuma mainat tayi dakinta tana kuma daga kiran masoyi habibi.

Zaune yake bisa cushion, ya mimmike kafa kan center table din daya matso dashi, jallabiyan ta dan ja sama, ana ganin chocolate dogayen sharabansa daya jie gashi a kwace, ya kishingida bayansa da kujera, tare da dabi'ar na lumshe ido,,

gefe guda kuma ga TV dake faman a'iki, ana watso zafafan labaru a tashar NTAi, amman shi nashi labarun nacan BQ din, yana kuma hada hotunan yarinyan sanda ta mike tsaye, har lokacin mamakin girmanta yakeyi, sai kuma ta rika wulka mishi sanda ya jawota gaba daya jikinta ya girgixa, yayi saurin cije lebe da kuma runtse ido, yana raya,,

kai, wannan wani irin girma ne tayi haka, just three years da wasu yen watanni, _ahhhhhaf dama kuncin gidan kane ya tsotsar da ita_ dai dai sanda take knowking kofan, yadan bude ido yana fadin,,

yess, waye?,,

nice ummeetah, ta fada cikin sanyi, gabanshi yace wani ras, ya sauke kafafunsa yana dada gyara zama, da natsuwarsa, kafun ya daure fuska yana fadin,,

come in, turo kofan tayi a hankali ta shigo, ya bita da idanu, kafun ya kauda idonsa yana raya,,

kai ita wannan bata da wasu kaya ne na mutunci,,

yaya sadeeq sannu da hutawa,,

yawwa sannu kema, meye wannan? ya fada da wani basarwa, ta kalli warmer din, kafun tace,,

abinci ne, auntyn mu tace in kawo maka, ya dan tabe baki da fadin,,

sai yanxun aka gadaman kawo mun, ya karisa maganan da daga kai ya kalleta, caraf idanunsa kasan wuyanta da dankwalin bai gama rufewa ba, kai komai masha Allah, yayi saurin kauda idonsa, da sauri yake fadin,,

pls ije a nan ki wuce, ta duka a hankali har kasa tana ijewa, spoon ne yayi kaman zai fadi, ta tsaya tana kokarin gyarawa, ya kuma kai idonshi kanta,,

shet, ya fada yana komawa ya kishingida, da dan tsawa yake fadin,,

waike ba zaki tashi bane, ko nima saikin gama baxa mun jikin da kik..... cak ya tsaya da maganan sakamakon hannunsa daya daki remote dake ije gefe daya, har sai daya fadi kasa, ya rike yen yatsunsa yana cije baki da fadin,,

ouch, ummeetah kuwa dama yana fara mata tsawa ta mike a tsorace, ganin abin daya faru ya sata saka hannu a baki tana baya baya, kobai dago ba, yasan dariya take, a hankali ya dago kai suna hada idanu, murmushine sosai akan fuskanta, tana dan toshe bakinta,,

runtse ido yayi yana budewa da shirin daka mata wani tsawan, da sauri har tana wani juyi, wanda yayi sanadiyar motsawan dukan jikinta, tabar falon tana futa, baki bude ya bita da kallo, yana mamaki, sai yaga kamar da gangar take juya mishi jikin nata, yadan kada kai, yana kuma fadada murmushin dake saman fuskanshi.

***

Cikin shiga na mutunci kamar kullum ya shiga sashin mahaifin nashi, nan ya tarda auntyn nasu zaune kusa da kujeran da mijin nata ke zaune, tun jiya ranta a bace yake da abin daya faru, sai dai tafi ganin laifin muheet, tunda bata sonshi da yer a'iki, bare kuma shi yaro da kudi da baya laifi,,

ya samu waje ya zauna, cikin girmamawa yake gaida iyayan nasu, ta tarbesa da fara'a, da mishi tayin karin kumallo dake gaban mijin nata, ya zauna yana fadin,,

Alhamdulillah, tare da daurawa da fadin,,

Abba tun jiya nake ta jira ka shigo gidan in kawo gaisuwa, ya dago fuskanshi wanda shima yaji mallanci radau yana kallon dan nasa cikin farin ciki da fadin,,

ka ganni, ina can zaria, family house, sun tsareni da meeting, daga fada adalin sarki ke son kara ma gidan sarauta, shine suka matsa saina amsa, nie kam har yanxun ina kan bakana na bana son sarautar, tayi dariya irin ta manya tana fadin,,

Abban sadeeq maimakon ka amsa, musha nadin sarauta, yace,,

a'ah, a'ina fada musu har abadan ni bana bukata, da suna maganan, tunda naki amsa, yaro da kudi, nace, ah yaro da kudi harkoki sun masa yawa, halin yanxun ma baya kasan, sai gaka, wani yaxo ya ganka zaice, shikenan Alh. Aminu ya iya sharata, duk sukai dan dariya, yana fadin,,

a'ah, Abba ba wanda ya isa yace haka, mudim su kaji bayanin jiya na iso, suka kuma dan dariya yana fadin,,

hakane kuma, nan dai suka zauna suna dan tattaunawa, kafun ya mike yana musu sallama, Abba yace,,

ammm, muheet ya kawo mun karan kunyi rigima ko,,

eh, shine abin daya fada, yana danyin shiru, Abba yace,,

shikenan Allah yayi muku albarka baki daya, yace,,

Ameen, ya fuce yana jin auntyn nasu na fadin,,

a'i laifin muheet dinne, yayi mun dai dai da haka, alhalin na ciki na ciki, dada gyara zama mijin nata yayi yana fadin,,

mutallab lamarinsa na bani tsoro, amman munyi magana dashi, yace zai iya auren mai a'ikin, don haka ina tunanin yanke shawaran binciko asalin yarinyan......

no, no Alhaji kar kace haka, ta nuna kanta da yatsa tana fadin,,


dana muheet, don Allah kar kace haka, ba jinin shi bace ita, yer dariya yayi yana mikewa da fadin,,

kyaji kie da wani magana, shi aure ina ruwanshi da jini, zan dai duba lamarin, tun bai dakko mana abin magana ba, daga haka ya shige daki, hankalinta tashe ta nufi site dinta, cabdi jinin talaka, talakan ma yer a'iki, ina na rantse baxai yuyuba.

yer uwanta ta kira tana zayyane ma komai, itama hankali tashe take bata numbern wani sabon malaminsu, daya yi mata wani a'iki, so suke kar a kara tada maganan,,

tana sauke wayar, da kokarin kiran numbern malamin daya kie shiga, kaman daga sama taga kiran number na kasan waje, wanda tayi saving da my daughter, ta daga cikin sauri, tana fadin,,

my daughter, can bangaren hankali tashe suhymah ke fadin,,

aunty wani mummunar labari naji a bakin mum dinmu, plss aunty kiyi kokari kar ki bari hakan ta faru, cikin tsatsan mu, wani iri hauka muheet yakeyi, ta dan numfasa cike da tashin hankali, tana fadin,,

karki damu, har abada baxan bar hakan ta faru ba, zansa a musu farrarku, tace,,

yawwa aunty, wannan shegiyar ummeetan ne ko?sai kuma ta tabe baki da fadin,,

kinsan menene, kice ma malamin kawai anyi mishi nisa da ita, kwata kwata abar da ita gidan, yanda zai manta da ita a rayuwansa, na tsani yarinyan nan, bana son tarihi ya maimaita kanshi, auntyn tace,,

hakane daughter kin kawo shawara, haka za muyi, in sha Allah, zamanta a gidan nan yaxo karshe, bari kawai na samu layinsa, kudi zan sakar mishi masu yawan gaske, suhymah ta saki ajiyar zuciyan farin ciki tana fadin,,

yawwa aunty nah, nasan zaki iya, banda abin muheet har wannan abince abin so, tswssssssss, sai kuma taja tsaki, suna cigaba da kulle kullensu, kafun su gama suna ije wayan.

Allah ya dad'a tsare mu, da imanin mu, Ameen.



comment
share
Matatace
*2019*

meemartjj...........✍🏻
[14/08, 14:29] Dala Grp: 🕯🕯🕯
*MATATACE*
🕯🕯🕯


story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjj


*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty Ummeetah and my Fa'ixation._


page 17&18

__________Janye da karamin trolley dinta ta futo, tasha black abaya, tare da rolling viel din bisa kanta, zaune ta samu maami a falon tana kallon tashan sunna TV kaman kullum, gefenta ta zauna tana fadin,,

maami na futo, nie zan wuce, da murmushi maami ke fadin,,

Allah ya taimaka, sai anxo mana sati kennan, tace,,

a'i ina tunanin sai sati na sama zan dawo, dai dai sanda ya shigo falon da sallama, sanye cikin bugaggen skye blue din shadda, zama yayi suna gaisawa da maami, mainat ma ta gaishe shi, ya amsa yana kallon trolleynta da daurawa da fadin,,

sai ina kuma?,,

school zan koma, cewarta, ya dan tabe baki da fadin,,

ke sai yau kika gadaman komawa kenan?ta dan bata rai da fadin,,

sunan babyn kawata fa naje,,

kema dai, da aurad dake akayi, ga kanin kani nan har sun fara tasawa, maami tai saurin fadin,,

ba wanin nan, in Allah ya kawo lokacin babu fashi za'ayi, Allah dai ya kawo musu mafi alkhairi, da dan murmushin kunya take wani makewa jikin maami, ya harareta yana amsawa da,,

toh Ameen, kafun ya kalleta da fadin,,

wani level ma kike wai yanxu?

muna shirin shiga 400level, daga nan kuma in sha Allah sai service, ta karisa maganan da murnantan, ya xaro wayansa a aljihun riganshi, tare da kishingida yake fadin,,

iyee ashe an kusa, Allah ya taimaka, ita da maami duk suka amsa da ameen, tare da komawa suna maganan su a hankali,,

shidai hankalinsa nakan wayarsa, numbern matarsa ce ke nuna alamar an turo sako, yana son ya bude wata sashin na zuciyarsa nason kallon wani gefe, bai ankaraba sai ganin idonsa yayi akan kofan dakin, yana raya wasu abubbuwa, can kuma yayi saurin dauke idonsa gefe, dajin wani haushin kanshi, ya dan lumshe idanu da raya,,

what nonsense sadeeq, wannan zubar da girma ne, yer da bata fie haihuwan cikin kaba, never har abada, ya bude idonsa, tare da maida hankali kan wayarsa yana karanta zafaffen morning text din da aka turo masa, murmushi yake sosai, kafun ya bude shafin tura sako yana tsara mata nashi,,

faduwar mathset din da yayi ne, ya dawo da hankalinsu kan dakin, ta duka tana dauka tare da futowa rataye da school bag dinta, sai dogon hijjab dinta bisa uniform din, da mamaki suke binta da kallo, ta kariso gun maami cikin sauri tana gaisheta, mainat na fadin,,

ummeetah baki tafi school dinba, tun daxufa naga kin shirya, yanxun fa karfe 8 da kusan rabi ne, ran maami bace take fafin,,

kuma tasan jarabawa sukeyi, me kika tsaya yine?idanunta rau rau da hawaye take fadin,,

bintu ce taxo ta kirani, mummyn su munirat tace, muxo mu mata wanki,,

tswssssssss shine abin da mainat ke fadi, maami na karawa da fadin,,

baki fada musu makaranta zaki ba, tace,,

eh, a'i haka nace mata, sai sister saudat itama taxo tace ana kirana, cikin zafi mainat ke fadin,,

kaii mummy, tasan fa mu bamu kiran bintun taxo ta mana a'iki, wannan bai dace ba, ran maami ya kuma baci sosai, lura da shaidan marin dake fuskan ummeetah da tayi, itama cikin zafi take fadin,,

ummeetah jini da kyau, dama inaso in fada miki, maganan kaima muheet abinci in an saki, da a'iki lokacin makaranta, ba ladiyo ba, ko yagana ce, kice nie A'isha indo nace, kar kiyi, maza wuce kie tafi makaranta, Allah ya taimakeki su barki ki shiga, da sauri ta wuce tana fadin,,

toh, duk su biyun suka bita da kallon tausayi, don sunsan da wata manufar aka shirya haka don aci mutuncinta, na abin daya faru jiya, can hanyar futa tayi, sai lokacin ta lura dashi, zaune bisa daya daga cikin a kujerun da suka juya ma kofa baya,,

gaisheshi tayi, tana wucewa ta futa, ko amsa mata bai yiba, dama tunda ta futo yaki kallon inda take, bare daya gama sauraran meke faruwa, gaba daya rayuwansa dauka yake bashi da matsala sama da ummeetah, gashi lamarin har cikin gidansu, kwata kwata beji dadi kalaman maami ba, a gaban mainat, wanda kuma be taba jin tayi hakan ba, ita macace mai saukin kai, ya gyara zama da kyau, so serious yake fadin,,

maami zan daizo na tafi da yarinyan nanne, inzan koma, kona rage muku hayan.......

da kata, shine abin da maami ta fada rai bace, tana cigaba da fadin,,

babu inda ummeetah zata tafi, karatu takeyi, kuma tana son karatunta, don haka hakuri za kuyi, ta zauna a nan harku dawo, zaiyi magana ta katseshi da fadin,,

bana son maimaita wannan maganan, sannan inaso kafun ka koma, inta kammala jarabawan da sukeyi yanxun, ka kaita ta gana da yen uwanta, shekaru ba watanni bane, don mutum yana maraya baya nufin bashi da dangi, suma zasu so suga yer uwansu, da fatan ban takura maka ba, cikin sanyi yake fadin,,

ko kadan maami, Allah ya kaimu su kammala, da murmushi take fadin,,

Ameen, Allah yi albarka, ya mike zai wuce office, mainat ta mike tana rokansa su rage mata hanya, zata biyama kawanta su wuce a motarta, futa kawai yayi, tasan amsan don haka ta mike da sauri tana ma maami sallama, dake binsu da addu'a, shidai daci yaji zuciyarsa na masa, haka kawai yaji hukuncin da maami ta yanke, yayi mishi tsauri.


***

Duk yanda zasuyi sai da sukayi, burinta na farko ya cika, ganin mijin nata bai kara tada maganan ba, kudi ta saki ma malamin yana fada mata anyi an gama, da bata shawarwarin wasu yen sadaka na karya, (hmmm) shidai ya shaki yen kudadansa, sanda sukai waya da suhymah kan hakan, dadi taji sosai, zuba ido kawai suke suga ta inda zata bar gidan.


Shiko duk yanda yake kokarin kauda idanunsa daga kallonta, hankalinsa da tunaninsa na kanta da muheet, ko school zata saiya leko ta window, wata lokacin kuma yasa ido akan futarta,,

yauma daya kasance weekend, misalin 9pm ya kammala shiryawa cikin wata yadi coffee colour, an mata a'iki da zare na alfarma, rigan iya gwiwa, haka hannunta ma karami, kanshi babu hula don haka kwantaccan sumar kan nan na bayayya ne,,

sashin maami ya nufo, munirat ce zaune a falon ita daya tana kallo, ta gaidashi, amsawa yayi yana mamaki da bega su hibbat ba, don indai mutum daya na falon to dukkan su zaka gansu, amman maimakon yace, ina su hibbat, tunkan ya zauna yake fadin,,

ina su ummeetah?da sauri take fadin,,

sun futa tun dazu, ya fasa zama yana fadin,,

what!har ina suka je haka, tai dan shiru, tana son zuko karya, sai kuma tace,,

bansan inda suka jeba gaskiya, komawa kawai yayi yana futa daga falon, kirjinsa na wani irin fat fat, shifa ya tsorata da lamarin daya dawo ya riska,,

samun kanshi yayi da nufa wajen packing space, yana samun daya daga jikin motocin ya jingina a jiki, yana crossing kafafunsa, tare da ciro wayansa yana daddannawa, lokaci lokaci kuma yana kai dubansa bakin gate,,

can sai gasu, hibbat ce ta fara turo karamin kofan, da dan dariya tana komawa da kallan waje tana magana, alama wacce suke tare take ma maganan, ya tsaya daga danna wayar, yana zuba ma kofan ido, can ta sawo kafa ta shigo, sanye cikin hijjab marron colour yana da dan tsayi, saita futo da hannayenta ta hannun hijjabin,,

ya sauke ajiyar zuciya, yana maida kanshi bisa wayar dake hannunsa, da sauri ya kuma dagowa yana bin karamin white ledan dake hannunta da kallo, dauke da tambarin shagon da su kaje siyayyan abin da zasu siya, hakanan yaji yana son saiya fahimce abin dake ledan, dayike yana da dan haske, kuma suna daga dan nesa, ya samu daker yana hada kalman,,

_Always_ da sauri ya dauke kanshi sama, yana jin wani yarrr a jikinsa, da raya,,

lallai kam, yarinya ta girma, ya sauke kanshi yana kuma kallon hannun nata, suna tafe suna magana, tana dan cilla ledan, kawai saiya samu kanshi da sakin murmushi, a hankali yake furta,,

ummeetah da always, ya gyara murya da dan karfi yake fadin,,

ke hibbat, ta juyo yana dan yafito su da hannu, alamar suzo, ta kalli ummeetah dake son escaping tana jawo hannunta, dole tare suka iso wajan, kanshi na kasa suka gaisheshi ya amsa da dagowa yana fadin,,

ina kuka je?hibbat ta amsa da fadin,,

area shop muka je, ya dan tabe baki da kuma gyara tsayuwa, yana kallon ledan hannun nata, da fadin,,

wannan fa, meye kuka suyo kuma na wanene?tambayar yaxo musu a baxata, a tare gabansu yace rass, ummeetah na saurin fadin,,

na hibbat ne, hibbat ta zaro ido, da sauri take nuna ummeetah da fadin,,

na rantse Baffah sadeeq nata ne, ba nawa ba, rakata kawai fa

Please Login or Register in order to submit comment