Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

thanks for everything, ta dago kai tana kallon cikin idonsa so serious da fadin,,,

my boo nasan kana fushi dani ko?bana son kayi fushi, kusan good three years kenan dana haifi bany Irfan, ba kuma haihuwan wani babyn ba, kuma nasam yara sune abin da kafi so a rayuwanka, am so sorry for the delay, yana murmushi ya dagota suna zama sosai, tare da ruko tafin hannunta yana fadin,,,

  shushsh, angel don me zanyi fushi dake, bayan nasan bamu muke ba kanmu ba, karki damu kinji, nasan inda Allah ya nufa lokacin zuwan wani babyn yayi, zaizo, cikin farin ciki take kaimai kiss bisa kumatu, da fadin,,,

  kaima karka damu, idan time din yayi, baxan haifa daya kadai ba, twin zan haifa maka, hannu yasa yana tallafo kanta tare da sakar mata kiss, bisa saman kai, da fadin,,,

  Allah ya bamu masu albarka, ina sonki suhymah, kuma ke kadai nake so, my dear angel, da sauri take fadin,,,

  kuma dani kadai zaka rayu ko boo nah?cak numfashinsa ya dauke, yana zuba mata idanu, da tambayar baxanta data mishi, cikin zakuwa take kuma fadin,,,

  plsss my boo say something, ya hadiye wani daci, yana dan murmushi, tare da shafa gefe kumatunta yana fadin,,,

  look angel, right now, baxan iya cewa komai ba, saboda bansan kaddara na a rayuwa ba, sannan destiny dinmu yana hannun Allah, muna namu ne, Allah na nashi, kawai dai mu cigaba da addu'an abin da yafi zama alkhairi, kinji tawan, ta yamutsa fuska tare da gutun murmushi take fadin,,,

  toh menene hope dinka, akan mu rayu mu kadai, what's ur plan, yadan zare ido yana tabe baki, kafun yakai hannunsa bisa table din dake gabansa yana daukan cup din drink, ya maida kallonsa kanta, tarw da kai cup din bakinta yana fadin,,,

my angel have this to cool yhu down, gaba daya annurin dake fuskanta ya dauke, tana ture cup din gefe da daurewan fuska take fadin,,,

  don't try to joke with me, in this matter, kasan yanda na tsani kishiya, kuma ban kaunarta, yayi wata yer dariya yana fadin,,,

  hee, why are yhu looking so scarry, ta kuma wani hada fuska tana fadin,,,

  funny right?sadeeeeq a halin da ake ciki fa, kana wasa da numfashi nane, kai dana kowa ma, ka fada mun a'inihin gaskiyan magana, dani kadai kake so ka rayu, ya soma tsorata da yanayinta zuciyarsa na bugawa, dakika bayan dakika, ta matso kusa dashi, tana kankame hannunsa da fafdin,,,

  plsss boo nah, ka fada mun gaskiya, ya ije cup din, yana mikewa da mika mata hannunshi, ta kama itama tana mikewa, tsakiyar daki ya futo da ita, yana sakalo hannusa daya ta gadon bayanta, yayin da dayan ke rike cikin nata dayan hannun, ta daura dayan hannunta kuma bisa kafadansa, magana rada rada take fadin,,,

  plss now tell me, kaman gaske yake fadin,,,

  rayuwana bani da burin daya wuce na rayu ni dake, mu kadai, ya dan matse baki yana daga idanunsa sama da fadin,,,

  amman bansan me yasa nake planning in aure mata har....., ta zaro ido tana wani irin kallonsa yana dan dariya yake karisa fadin,,,

  guda dubu ba, ta sauke wani ajiyar zuciya, tana dukan kirjinsa da fadin,,,

   yhu are still joking, ya soma wani juyi da ita, tana gani jiri, lokacin da take wani irin dariya, tana fadin,,,

  boo nah, ka daina zan fadi, a hankali ya sadata da jikin bango, yana dire lips dinshi cikin nata, nan ta kama, wani hot kiss yake bata, tare da daukanta cak, sukai saman gadon, kokarin ziping din riganta yakeyi, tai saurin rike hannunsa cak, tare da yunkura ta zauna, ya mike a gigice don ya gano nufinta, tana zare jikinta a nashi sanda yake fadin,,,

  no suhymah karki mun haka, in such a big day, ta yamutsa fuska tana fadin,,,

plss boo nah, not today, nayi maka shirye shirye da yawa yau dinnan, da yasa na gaji, ya kuma kai hannunsa yana rukota da zai magana, ta katseshi da fadin,,,

  shishsh, ka bari mana, wai kullum ne ake abu daya, nace ma na gaji, plss let me be, ta karisa maganan ta ture hannunsa daga jikinta, tare da mikewa tana fadin,,,

  bari naje na sanja kayan nan, sai inxo in ta yaka bacci koh, ya hada rai yana fadin,,,

  indai bacci kadai zaki zo kie tayani, kiyi zamanki bana so, tayi dan farrr da ido tana fadin,,,

ah ah,  boo nah dan rigima, sai tayi wata yer murmushi tana juyawa da fadin,,,

  ouk ni kaga tafiya na, good night, daga haka ta fuce tana jan mishi kofan dakin, ya runtse ido yana daga kanshi sama, tare da budewa yana zubawa bisa side drower da aka jera wasu design cards na kalaman soyayyan, rai bace yasa hannu yana zub dasu kasa, tare da takaicin gaba daya decoretion din dake dakin.

 

   sanye take cikin doguwar hijjabi, green colour, wanda ke dauke da baj din makarantan tilawan da take zuwa, da sauri mai gadi ya futo daga dakin gadinshi, don ya bude mata kofa, sama da shekaru hudu kenan, amman kullum tazo saiya bude mata, don bata iya ba, cikin sanyin murya take fadin,,,

  ina kwana, ya yamutsa fuska da fadin,,,

  lfylau, yer ban iya ba, kullum sai kinsa mutane a'iki, bude kofa kawai, to a'i sauki kulle inkin futa, ya cire lock din yana komawansa daki, taja kofan a hankali tana budewa, kanta a kasa ta daga kafa daya zata sanya waje, dai dai nan shima ya sako kafa, tasan ko kafan wanene, da dago kai sukai ido hudu, a wani razane cikin sauri take maida kafanta baya, tare da kokarin ja da baya, don ta matsa mai ya fara wucewa, nan kuwa tayi baya da yawa, gaba daya ta tafi zata zube a kasa tana kwalla kiran,,,

  ahhhh, azama yayi wajan riko damtsen hannunta, yana dagota da kyau ta dawo kan kafafunta, jikinta har rawa yake, alamar taji tsoron faduwan da zatayi, ya cikata, yana daure fuska, har lokacin tsaye a waje, sanye da farar jallabiya, iri daya dana dansa da yake bisa kafadansa, sai hula mai mannewa akai, wanda ake cema shafa kaji hadith, alama daga masjid suke, yake fadin,,,

  what nonsense, kina hauka ne, come on zoki fara wucewa, ta futo tana zuba mishi ido, da dan rawan murya take fadin,,,

  ina kwana, yace,,,

  lfy, tare da kallon agogan dake fuskar wayansa da fadin,,,

   yanxun ne dai dai lokacin da ake zuwa makaranta, kina wasa da karatu ko?shiru tayi tana wiki wiki da ita, don harta futo zata tafi, uwar gijiyan nata tace, taxo ta mata plushing tutun data titika a lokacin, dole ta haura upstairs din tayi, ta kuma hada da wanke toilet din, sannan ta futo, cikin dan tsawa yake fadin,,,,

  kya baki jin ina tambayar kine, ta dago yen manyan idanunata, tana zuba mishi, wanda sukai rau rau da kwalla, sai hawaye shar,ta soma inda inda, tana son yin magana, shiko ya tsunduma cikin kogin tunani,,,

ita wannan kuka bai mata wuya ne, dole ace suhymah na zalunta mata, ya dan yatsina fuska da fadin,,,

  jekie, kin tsareni da wasu idanuwa, amma kafun nan, plss ki dan share hawayen, kar ayi tunanin dukan kie, mu kayi da safen nan, da sauri ta juya ta tafi, tana shashsheka tare da share hawayenta, ta gefen idanu yake binta da kallo, shikam har yau yana mamakin tafiyar yarinyan, ko tsaban natsuwa ne, yakesa tafiyar nata yayi cike da yanga, dai dai dai take tafiya, wani lokacin jikinta har wani motsawa za kaga yana yie, ya dan tabe baki da raya,,,

  wannan yarinyan ta girma za ayi da ita, mai gadi ne yaji yana gaisheshi, yayi saurin dawowa hayyacinsa yana amsawa, tare da shigewa ciki, mai gadin na kulle kofan.

An tashi makaranta yau daliban sai murna sukeyi, kowa na rike da takardan da aka basu na waliman taro,da za ayi na yaye daliban da suka gama tilawan al-kur'an din, wanda ciki harda ummeetah, da take mai karancin shekaru, a cikin daliban, hawaye ya ziraro mata, tasan bata da wanda zata bawa wannan takardan  ba zatai wahala bandawa ba, ko dai taci zagi gurin aunty suhymah in takai mata papern, ko kum shi Baffah sadeeq ya manta data bashi wani takarda ma, don haka bata da wanda zaixo mata, ta nufi gida, kaman wata yer shekara shida take tafe tana shashshekar kuka da tuna Affahn tah.

Da wani style suke packing din motan a packing space din gidan, cike da farin cikin zuwa gidan, enmmata ne, harsu uku, suka futo, guda biyu na sanye cikin wani doguwar rigan kishmer, dana gyallen da suka yafa bisa kai, suna ratayoshi ta saman kafada, ita kuma dayan na sanye da riga da skirt, itama ta yafo dan gyallen, da murna suka nufi katon mansion din suna kiran,,,

,,aunty suhymah, aunty suhymah, kie futo, Najma, zahira da saudat sunxo, da gudun gaske ta sakko daga upstairs din tana bude musu kofan, suka rungume juna cike da farin ciki, tare da karisawa ciki, ko wacce tayu dai dai bisa cushion, Najma ta nufi wajen electronics din, tana jona wayannta jikin home speakers din da suke bada sauti tare da saka waka, tana bie tana miming, zahira na kallon auntyn nasu da fadin,,,

  girman kujeranki ur excellency, ur majesty, saudat kuma na fadin,,,

  mrs yong Alhaj, el-sadeeq, da gake ba wata, Najma ta zauna da karawa da fadin,,,

  Americana madam, Americana lady, itako kanta sai fashewa yakeyi, da iya shege, take wani gyara wuyan riga tana wani yarfa hannu da fadin,,,

  yesss, nine nan, Americana woman, the queen of king sadeeq, suka sa ihu suna fadin,,,

  yauwa aunty suhymah, akwai wulakancin fa a US din nan, ta kuma gyara zama tana fadin,,,

  sosai ma kuwa, can't wait to saw me there, dole rawa zai sanja, zan saki wulakancina, zanyi abin da nake so, daga nie sai mijina da boy dina, sai wancan banxan, suka dada sa ihu, kanta na kara wani fashewa take cigaba da yarfa hannu, kaman wata mai rapping waka, take fadin,,,

  yesss, lokacin da zan koma har real majesty, ita kuma zata zame mun real servant dina, zan wahalar da yarinya, kowa sai yasan nie gimbiya suhymah na taho da yer a'ikina ummeeee taaah,  a tare suka karasa ihu, tana ba zahira hannu suka kashe, Najma na fadin,,,

yawwa aunty suhymah don Allah karki bar yarinyan nan, kie wahalar da ita, yen nan haushi take bani, ba abin da yafi bani haushi da ita, sai tafiyarta, harfa wani girgixa za kuga tanayi, kaiiiii yaran nan akwai salon gulma, natseni house maids, zahira tace,,,

  sister ba kya kadai ba, ni jin dadi nama, da yarinyan bata da wani kyau, kinsan yen iska burinsu kenan a kullum, balle ma ace ta kwace miki yaya sadee..... da sauri suhymah ke fadin,,,

  what, tasa wata yer dariya tana cigaba da fadin,,,

come on, kibar wannan maganan, ku daina ma damun kanku, abune da baxai taba faruwa ba, nie da wancan abin,  no no no no, a'i sadeeku nawa ne, nie kadai, kai ku bani amshi, ta fara fadin,,,

  zan rayi dashi....su kuma suna bata amshi da fadin,,,

   zaki mutu dashi.....

   abadan dani dashi..... suka kuma karisa mata da,,,

   zaku zauna, a tare suka kyace da wani dariya, saudat na fadin,,,

  sisters, a'ini duk cikin masu a'ikin gidan mu babu wacce na tsana irinta, tun lokacin, hmmm ban baku labarin sist mainat ba, munirat taji yanda sukayi da yaya sadeeq a dakin mami, shine taxo tana fada ma mummy, Najma tayi tsaki tana fadin,,,

  kai na rasa yaushe ne, sist mainat zata fahimta, dan a'iki dan a'ikine fah, suhymah ta tabe baki tana kallon saudat da fadin,,,

  kinji yer uwa fada mun yanda akayi, nan ta kwashe komai ta fada musu, tasa ihu tana fadin,,,

cau cau, saini suhymah, the queen of king sadeeq, a'ina fada muku, i will be the queen, and forever, she will my servant, servant of madam.....suka karisa da fadin,,,

   suhymahhhh, akasa dariya, zahira na fadin,,,

  inama take taxo ta daura mana girki, nidai jollop rice nake so, kuma, ko wacce ta soma fadin abin da kuke so, suhymah na dariya da fadin,,,

  kai, kufa baku da mutunci, ga abinci can professional Ruma nasa ta hada muku, me za kuyu dana  wancan yer kauyen, zahira tace,,,

  a'i saita yishi, ta dan wahala, suka kuma saka wani dariyan, ana kwala ma baiwa kira taxo ta daura abinci.

  Yau ta kasance weekend,
🕯🕯🕯
            _*MATATACE*_
     🕯🕯🕯

     

story&written by Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@meemartjj

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚

   *Dedicated to lovely sisters*
_Jameela ja'afar yakubu_
_Fateema ja'afar yakubu_
_Fa'iza ja'afar yakubu_

  *_wedding bells are ringing for zainab mu'az umar, mufeeda, marubuciyar ni da dangin mijina, fatan alkhairi yer uwa, da fatan za ayi biki lfy a gama lfy, Allah ya sanya alkhairi, yasa amarya ta tare gidan mijinta lami lfy, we really gonna miss yhu dear, kie huta over, Amarya ta ango,_*  _yours haleematu ja'afar yakubu_

  *Gargadi: pls ina kara fada, ban yarda wani/wata a karisa mun labari ba, ko a juya mun ba.......meemartjj💕* 



_*page 7&8*_

――――Tsaye take saman upstairs din, dafe da karfen stairs din dake can sama, wanda suka kawatu a wajan, ta dafe hannunta duka biyun a jiki, duk ta kosa ya budo kofa ya shigo,,,

  a zuciye ya turo kofan yana wani cika, tare da wucewa straight tsakiyar falon yana ja ya tsaya, kafun ya fara kwalla kiran sunan,,,

   ummeetah!ummeetah!tana zaune a kitchen din, zata fara cin abincin da suka kammala yie ita da Ruma, ta zuba mata, tsam ta janye hannunta tana zaro ido, cike da fargaba take runtse su, tare da dafe kirji tana fadin,,,

   innalilah wa'inna ilaihir raji'un, kafun ta mike zumbur tana yin falon, sanye da wani kodandan riga da zani na atamfa, kwancan makota da suke bata, sai gyara wuyan rigan da yayi mata yawa takeyi,,,

  gabanshi ta tsaya can dan nesa dashi, tana fadin,,,

  ganie, ya wani bata kallon wulakanci da fadin,,,

  ouk nie inxo inda kike kenan, cikin sanyin jiki take kuma matsowa, suhymah dake sama tasa wata dariya, tana zuba tagumin jin dadi, tare da karkacewa tana kuma botsarewa, ta kosa taga ta inda zaya fara dukan yarinyan, dai dai sanda driver yayi sallama rike da littafan,,,

  ya bashi daman shigowa, ya kariso yana ije littafan bisa center table, tare da ficewa, gaban ummeetah yace rasss, tana bin littafan da ido, ya dukule hannu cike da takaici, sanda yake jin kaman ya daketa, yana daka mata tsawa da fadin,,,

  uban meya hana kie zuwa makaranta, kinsan iya kudin da nake kashewa a karatun kie, kinsan iya kokarin da nakeyi a kanki, sannan ba a gani, nan gaba idan baki samu ilimi ingantacce ba, ace sadeeq ne ko?ki hadani da bala'i, uban me ya hana kie zuwa, tell meee!jikinta na kyarma, sanda take magana a rude, cikin harshe fullanci take mishi bayani, ranshi ya kuma baci yana fadin,,,

   uban wa kike ma magana da wannan yaren, sadeeq ne zaiji miki fillanci, kie mun magana da harshen dana fie ganewa, tun kan in zane miki jikinki, hawaye suka sauko shar bisa fuskanta, tana fara shashshekar kuka, ya zabga mata harara, yana binta da wani kallon rainin wayau kafn ya kalli littafan yana fadin,,,

  na rasa wani irin kokari ne suka ga kinyi, da shegen wasan nan naki, har suka baki kyaututtuka haka, maybe dai akwai malamin da yake admirering naki ne, shi yasa suka b...... dariyan da aka kyece dashi ne na rainin hankali, yasa shi juyawa yana kallon upstairs din, tayi dan taku biyu tana sakkowa stairs na biyu, da fadin,,,

  come on baby, kalaman ka sun bani dariya, admirering fa kace, ina abin admirering a nan, tasa yatsa tana nunata da fadin,,,

  wannan ta kuma sa dariyan dadi, har tana toshe bakinta da tafin hannunta take fadin,,,

    no, yhu must be joking, banga abin da za ayi admirer ing a nan ba, sai dai in gifts din wata yarinyan aka baka, idanunsa na kanta da wani irin tunani, ya juyo yana kallon ummeetah da kare ma halittanta kallo, kafun ya juyo yana kallon suhymah da har yanxun take dan dariya, da fadin,,,

  so, it funny right?ta girgixa kai tana wani tabe baki da big smile take fadin,,,

  of course, very funny, juyawa yayi yana runtse idonsa da wani takaici, kafun ya bude yana daka ma ummeetah tsawa da fadin,,,

  dalla malam zoki bace mun da gani, har wani girgixa tayi da tsawa, da sauri tayi nufin juyawa tabar falon, bisa kaddara kafanta ya harde ta gefe take hantsalawa zata fada ma glass center table din, cikin azama yake dukawa dasa hannu ta bayanta yana rukota, harsai data hadu da kafadansa, kafun ya cikata yana damtsen damtsen hannunta da wani irin kallo takaici, tsananin tsoro da fargaban daya gani a idanun tane, yasa shi tsayawa yana binta da kallo, itama ta kuresa da nata dake zubar da hawaye,,,

  suhymah dake bisa upstairs, ta zaro ido a haukace tun sanda taga ya rukota,,,

  kambura uba, shine abin da take rayawa, ganin bashi da ninyar sakin hannun ummeetah, a zabure take sakkowa downstairs da kwala kiran,,,

  sadeeeeq!ya juyo da sauri, kafun ya finciko ummeetah tsakiyar falon yana sakin hannunta da fadin,,,

  kina hauka ko?zaki jamun bala'ine? yana magana cike da tashin hankali, tare da cigaba da fadin,,,

  tunda kika xo rayuwa na, gaba dayanki matsala ne, an saka nie cikin damu...... yai shiru da kuma dan runtse idanu, kafun ya bude, dai dai sanda suhymah ta karisa sakkowa da gudu tana tsayawa kusa dashi, tana da bin ummeetah da wani kallon tsana, sannan ta kallesa, cikin sanyin murya yake fadin,,,

  kie kwashe littafan nan, saura suma kiyi wasa dasu, hope kin jini?kai ta daga sama alamar eh, ta wani zaro ido da matukar mamaki tana fadin,,,

  boo, kana nufin ba zaka hukun tata ba, gobe fa karawa za tayi, ba tare daya kalli inda take ba, yake nufa haryar futa rai bace, kai a sama, tare da fadin,,,

   madam plsss let me be, duk suka zuba mishi ido su biyun, bisa tsautsayi, yayi karo da trow pillow dake yashe a kasan tyles, nan kuwa ya harde ya kusa fadi, yayi saurin tsayawa da kyau, dama ga tension din da yake fama dashi, ya juyo yana faman masifa da fadin,,,

    ohhhh my god, idanun fa, na menene, shie kuma wannan da aka bari a nan fa, da sauri ummeetah take karisawa wajan ta dauke, shi kuma ya saki tsaki yana barin gidan, tsaye kawai take daskare a wajan, ta kasa fahimtar meke faruwa, ba abin da yake mata gixo a idanunta, irin rikon da yayi ma ummeetah, jikin mijin nata, ta girgixa kai tana bin ummeetah dake fucewa daga falon da sauri take raya,,,

  tabbas kuwa dole inyi maganin yarinya.

  mangyada ne mai zafi yake soyuwa bisa gas cooker, sai data bari yayi zafi radau, sanna ta kashe gas din, tare da sake mangyadan a dan wani bowl mai hannu, ta nufi inda ummeetah ke zaune gaban fanfo tana wanke wanke, sabule da hannun rigan daya sauka kasan kafadanta,,,

  a hankali ta sadado, hankalinta na can tana a'iki, tafi karfin 5minutes a wajan tana kallonta da wani mugun harara, kafun ta daga bowl din sama tana shatata mata mangyadan bisa kafada,,,

  a firgice ummeetah ke wancakali da plate din dake hannunta, tana rike hannu tare da saka wani kuka mai cin zuciya, duk ta giride, can kuma ta mike tana ja da baya da fadin,,,

  aunty suhymah da zafi, kinfa konani, ta zabga mata harara tana jan wata doguwar tsaki da fadin,,,

  nasani, dama haka nake so, wannan shine sakamakon hada jiki da mijina, kinji ko, mayya kawai, tsawon shekaru hudu kenan da nake so naga ranan dazai lallasaki, amman kullum yaxo sai dai nashi ran ya baci, sannan abin ya kare a kaina, to bari na fada miki zakici kanki, kisha bakin ruwa, witch kawai, ta kuma jan tsaki tana cilli da bowl din cikin wanke wanken, tare da kallonta tana kuma fadin,,,

  dallah zauna ki karisa mun a'iki, tun ban tattakaki ba, a girede ummeetah ta zube wajan, tana wani irin kuka, ita kadai tasan irin azaban da hannun yake mata, a haka ta karisa wanke wanken, da tayi tayi, ta rungume hannu tana fadin,,,

  wash, innalilah wa'inna ilaihir raji'un, na shiga uku, Affah hannuna zafi, da dare kuwa yayi ta kasa yin bacci zafi yake mata, ga duhun daya baibaye dakin, don bulb din dakin ya jima da mutuwa, ga zafi anayi,,,

   hakanan ta bude windows tare da sakayo kofa, wai duk don iska ya shigo kota samu saukin azaban da take jie, sauro kuma suka cika dakin, sai faman fifita hamnun take da littafi, tana yie tana numfarfashin wahala, can kuma ta saka kuka, kuka takeyi sosai, kafun ta share hawayenta, sanda take tunawa da kalaman mahaifinta lokacin da yake da rai,,,

  duk da karancin shekarunta ba zata manta ba, don cin mutunci ne sosai akai mishi, sanda Baffan ta lado ya samesu suna tsaka da kiwon shanu, yaci kwalar mahaifin nata, sannan ya zazzageshi, tare da mishi wankan manja har galan daya, tunda take a rayuwanta bata taba ganin anci mai mutunci ba, yayi kuka sai ranan, don haka itama ta shiga taya shi, suna kukan tare, can kuma ya rungumota yana share mata hawaye da fadin,,,

  yie shiru ummeetan Affah, duk wanda kika ga yayi kuka wata rana shi zaiyi dariya, mai hakuri yana tare da riba, don haka ki daina kuka wata rana za kiyi dariya, ta girgixa kai da fadin,,,

  a'ah, Affah nafi so kai kayi dariya bani ba, dan murmushin yake yayi yana kallonta tare da share hawayensa, cike da kuncin zuciya yake fadin,,,

  ashsha, ummeetah indan har kikayi dariya, to kaman nayi dariya ne, sai kuma ya kara fashewa da kuka yana fadin,,,

  ummeetah, rayuwanki kawai nakeji ba nawa ba, bana so kie kare kaman na mahaifiyata da mahaifiyarki, ina so kiyi rayuwan farin ciki, don haka nie Affahnki ina tabbatar miki, in sha Allahu wata rana za kiyi dariya, zanyi kokari sosai wajan ganin rayuwanki ya inganta, tuno da wannan ne ya sata kuma fashewa da kuka tana faman kiran,,,

  Affah har yanxun fa kuka nakeyi, don Allah wani yaxo ya taimaka mun, ciwon nan zafi yake mun, azaba yake mun, Allah na rokeka, Allah ka kawo mun dauki, kuka take sosai mai tsinke zuciya, jin irin radadin da hannun yake mata, tana faman fifitawa, tare da hurawa da bakinta, ga uban sauro da suke yagan fatan jikinta.



  Ba abin dake tashi a dakin sai wani sassanyar iskan Air condition, suna kwance a kafcecen gadon, daya jie shimfidu katifa da matasai na alfarma, yana kwance a site din dama, ya juya mata baya, da take kwance a site din hagu tana narka baccinta mai cike da kwanciyar hankali,,,

  shiko idanusa biyu, kuri cikin duhu, yayi matashi da hannunsa biyu, abin duniya ya hadu yayi mishi yawa, shi mutum ne daya tsani ya zauna da laifukan zunubi, musamman hakkin wani, baya son zama da laifin wani, ya numfasa, zufa na dada keto mai, tare da mirginowa yana yin rigin gine, da kallon sama yake cigaba da tsunduma cikin halin tunani, da raya,,,

  sadeeq akwai matsala fa, zumbur kuma ya mike zaune, yana hada bayansa da jikin gado, tare da daga kanshi sama, yana lumshe idanu, sanda yake hada hotunan lokacin data hadata da jikin handle din kofa, kan yarinyan ya bugu, yana kuma tuna irin ramar daya lura dashi yau a jikin yarinyan,,,

  anya kuwa yayi adalci, yana so ya gama lfy, ummeetah fa bata da laifi ko daya a kaddaran rayuwansa, abin da Allah ya nufa ga bawa, dole saiya faru dashi, to menene dalilin saka kyara da tsana a tare da yarinyan, ya sauke kanshi kasa da bude idanuwansa yake kuma raya,,,

  kai sadeeq marainiya ba uwa ba uba irinta, kayifa tunani, ba komai banefa yasa mahaifin yarinyan ya dauketa ya baka, sai don so da kauna da amintaka, sadeeq soyayya ce mai karfi yasa ya dauki yersa tilo guda daya ya baka AURANTA, don kuma yana tunanin zaka iya ne, zaka taimaka, sannan zaka fidda ita daga kuncin wancan rayuwan da sukayi,,,

   ya kuma numfasawa tare dasa hannu yana jawo wayansa dake bisa side drower,

Please Login or Register in order to submit comment