Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da duba lokaci almost 1am, da hasken wayan yake haska fuskar matar nasa dake sharan baccinta, yafi mintu uku yana kallonta,,,

  kwata kwata baya son randa suhymah zata san labarin nan, yasan tana da tsananin kishi, kuma yana sonta matuka, ya kuma dan runtse ido a hankali yake furta,,,

  hakane, ina son suhymah, sai dai ba yanda zanyi, saboda itama ummeetah *MATATACE*, da sauri ya dunkule hannunsa yana dada runtse ido, yana takaicin ya tuna wannan kalman, gashi kuma itama tana da hakki a kanshi, ya rika tuna sanda bafullatanin da befi tsaran haihuwansa ba, ya rika magiyan ya auri yer tasa tare da furta kalaman,,,

  habubakar ban yarda naba kowa diya taba, sai kai kadai, saboda na yarda da kai, nasan zaka iya! zaka iya! zaka iya!maganan ya rika mishi amsa kuwwa a kunni, da sauri yake zirara kafafunsa kasa, ya tsaya cak, yana juyowa da kallon matar nasa, kafun ya mike a hankali, sanye da wasu costly pyjamas na riga da wando, rigan botton down, mai karamin hannu, ya zirara foreign silipers dinshi, ya fuce a daga dakin yana rufo mata kofa.


  da dan sassarfa yake sauka downstairs din, kai tsaye ya nufi kitchen yana bude kofan futa da keys din daya kwaso, ya futo wajen, yana kuma nazarin mutum ya kwana shi daya a ta nan wajen, ya nufi dakin, yayi mamaki sosai daya tura kofan ya jita a bude,,,

  ummeetah data samu barci ya dan dauketa, jin motsi yasa ta bude idanu, zumbur ta mike tsaye ganin inuwan mutum cikin duhu, da kuma hasken fitilan waya, ta kwasa kara da furta kalman izti'azah, cikin sauri yayi kanta, ta kuma zabura kaman wata zararra, zata fuce daga dakin, damkota  yayi, tana wani irin firgita, ya zube gwiwansa kasa, yana kamo tsawonta, tare da tallafo fuskanta daya jike da gumi yana faman fadin,,,

  ke, ummeetah tsaya Baffan kine sadeeq, kinga, ya haska mata fuskanshi da waya, a tare suka sauke wata ajiyar zuciya, wanda nata yafi sauti, tana shashekar kuka tare dasa hannu tana son ta cire hannunsa daya damkam mata wajan kunan, da sauri ya janye hannunsa da haska wajan,,,

  subhanallah, dame kika kone haka?idanu kawai take binsa dashi, ta jike sharkaf da zufa, ya mike yana kunna bulb din dakin nan ya jita a mace, ga uban sauron dake dakin, a wani firgice yake fadin,,,

  what, haka kike zaune cikin duhu, kina hauka ne, baki magana ba, ido kawai ta kura mishi, takaici ya isheshi yana mata tsawa da fadin,,,

  wai ba kiji ina miki magana bane?kin kure ni da ido, tayi wani firgigit tana jan ajiyar zuciya, alama bata cikin natsuwanta take fadin,,,

  na'amm, ganin haka yasa cikin taushin murya yake fadin,,,

  da farko dai fada mun yanda kika kone haka, ta numfasa a hankali take kallon hannun da fadin,,,

  mai ne ya konani, kaman zaiyi magana sai kuma ya fasa, yana jan hannunta wajen mattress din da fadin,,,

  zauna nan bari naje na dawo, daga haka ya fice daga dakin, yana futa tayi saurin mikewa a sittin ta sama kofan sakata, dama a tsorace take, ta tsorata da abin da auntyn nata ta mata yau, ta koma bakin katifan tana zama da saka wani sabon kukan,,,

  ya dawo rike da wata standard fan, sai firstaid box da kwalin bulb a dayan hannun, tare da gwangwanin sheltos, da kafa yake tura kofan, saboda kayan dake dauke a hannunsa, amman ya jita bam, mamaki ya rika yie, tare da kulewa yana fadin,,,

  ummee zoki bude kofan mana, taki tasowa ta bude, kuma yana jin shashekar kukanta, ransa ya baci da raya,,,

   kai gaba daya yarinyan nan damuwa ce a rayuwa na, ya dan nisa yana kallon yanda dare yayi sosai, ko ina duhu ne, amma yana faman malangarin, ya ije fan din yana knowking kofan da fadin,,,

  ummee nace ki bude ko, idan kika bari na bude da kaina na shigo, saina miki wanda yafi na suhymah, a'ikin jie, a zuciye ta bude kofan tana komawa bisa mattress da saka sabon kuka ta zauna, ya bita da kallo, a zuciya yana raya,,,

  eyyee samun waje, kin ganni ne, shi yasa, amman bacin tausayin ki da nake jie, ke baki isa inxo inda kike ba, yai dan tsaki, yana ije kayan, tare da taka wata yer karaman kujera yana cire tsohon bulb din daya mutu, ya saka sabo, sannan ya kunna, dakin ya dauka kauu, sai da ummeetah ta saki wani ajiyar zuciya, Allah sarki haske rahma, tana jin wani kuncinta ya ragu,,,

  ya rika bin dakin da kallo, komai an shirya shi tsaf tsaf, harta yer katifan da yaji lulubi da zaninta, tsaf yake, ya feshe dakin da maganin sauran, sannan ya koma wajen wani socket yana dukawa da jona fankan, nan kuwa ya kama,,,

  ya dauko firstaid box din yana dawowa gabanta da tsugunawa bisa kafafunsa, ya riko hannunta ta saka sabon kuka tana tabe fuska, kallonta yake da wani murmushin son yin dariya, don yanda tayi da fuskan ne ya bashi dariya, ya daure fuska yana fara mata dresing ciwon, ta soma kokarin kwace hannun, da sauri ya dago yana fadin,,,

  ah ah, lafiya, taimakon kifa zanyi, tabe fuskan ta kuma yie da kuka tana fadin,,,

  Baffah sadeeq da zafi, shima yadan tabe fuska yana kwaikwayonta da fadin,,,

  yenyenyen yen, Baffah sadeeq da zafi, sai kuma ya dan harareta, yana kuma fadin,,,
 
  katuwanki dake kina kuka, shiru tayi tana zuba masa ido, yanda yayi maganan, kaman wata yer shekara uku, idonsa a kasa yana kokarin fara sa mata hydrogen a hannun, ya dago kai da daga mata gira sama yana fadin,,,

  meye kuma? da sauri ta kauda kanta gefe, tare da runtse idanu, harya gama mata dresing din, yaga kokarinta, donshi da ciwon ba a jikinsa yake ba, yana wanke wane yana jin wani yarrr a jikinsa, ya kammala mata, tana juyowa da sauke wani ajiyar zuciya, na tsaban wahala, banda zufan daya jika fuskanta, kaman ta wanke da ruwa, ya kalleta yana fadin,,,

   da zafi ko?kai ta daga sama, alamar eh, ya maida komai, yana rufe firstaid box din, kafun ya dago, tausayinta ya kamashi, a hankali yakai hannu yana ruko tafin hannunta, mai taushi da haske, kallonta yake da fadin,,,

  ummeetah zaki bimu inda zamu, ko kinfi son mu barki a nan wajensu maami, shiru tayi, yana kuma fadin,,,
 
  kie fada mun zaki bimu, da sauri ta kada kai alamar a'ah, yace,,,

  ouk zaki zauna gurinsu maimuna, da sauri ta daga kai, alamar eh, yace,,,

  toh sai kinyi magana tukuna zan gane, cikin sanyi take fadin,,,

  nafi son na zauna gidan su maami, yai shiru, kafun ya cika hannunta yana mikewa da fadin,,,

   shikenan zanyi tunani, kie shirya kayanki gobe zamu wuce, zoki rufe kofan, mikewa tayi da fadin,,,

  toh, tabi bayanshi, har yakai bakin kofa ya juyo da fadin,,,

  karfa kie cire abin dana sa miki a ciwon, magani ne, gobe inxa kie futo kie rufe da hijjab ne, ba xata gani ba, kinji a'i, kaita daga alamar gamsuwa, daga haka ya fice dakin, ta kulle kofan tana komawa ta kwanta, sanda isakan fankan ya taimaka wani bacci mai dadi ya kwasheta.


   Da safen ranan ta rika bulum bulum cikin hijjab, ta kirata zata bata sabon ghana bag, tare da kaya sabbi kala hudu, sai wanda zata sanya ranan, cewanta, ba zataje mata US a fatare ba, a jie dadin rainata, don haka ta bata kayan, tace sauran tsoffafin ta barsu, dariya sosai takeyi da fadin,,,

  gulma, wa yaga matar liman, yau kuma salon da kika tashi dashi kenan, ta tabe baki tana fadin,,,

  tashi kibar nan, ummeetah ta kwashi yen kayan da aka bata tana barin falon, tare da sauka downstairs, dai dai sanda yake hayowa, sanye cikin wata tattausar farin yadi, dinkin kaftain, dishi dishi ake hangen farar singlet din daya saka, yana gyara zaman hulan kanshi, tare da zuba kamshi na musamman, yayi kyau sosai, ya kauda kai yana hayewa, yayin da ita kuma take sauka kasa, gab da juna suka zo, suna bin juna da idanu, harsun dan gota yaja ya tsaya yana fadin,,,

  baki iya gaisuwa ba kenan, da sauri take gaishe shi, ya amsa yana karisawa upstairs, ita kuma ta sauka.

   haka dai suka kammala shirya komai da komai, lokacin da driver ya gama zube musu kaya cikin booth din mota, itama yasa mata karamin ghanabag dinta, sanda Alhaji mai gidan ya gama tattaunawa da care taker din gidajansa, yabar mishi keys din gidan, inda za'a zuba yen haya. 


  ang.rimi suka nufa, driver nayin packing a haraban gidan, mrs sadeeq dake gidan baya hashinke ita da mijinta, ta futo da sauri, sanye da riga da skirt na wani super, anci dauri, sai dan gyalen da aka yafa, shima ya futo ta dayan site din, kafun yayi magana tayi hanyar site din auntynta da fadin,,,
 

  my boo, kaga nayi nan, zanje inga aunt. dina, don nayi missing dinta da yawa, daga haka tasa kai tayi tafiyarta, ya dan numfasa, shima yana wucewa site din mahaifiyarsa, dai dai sanda ummeetah ta futo daga gidan gaba, ya kalli driver yana fadin,,,

  plss dakko mata jakarta, kie biyoni ciki, ummeetah taji kaman tasa tsalle, Allah yasa a barta a nan, don yanxun ko Abuja suka je, sai ta gama wahala gidan su aunty suhymah, kafun su nufi inda zasu, batasan wani kalan wuyan zata sha ba, driver taji yana fadin taje ta dakko jakar, da sauri tayi wajen booth din, garin rawan jiki, har hijjab dinta ya makalewa da hannun wani trolley, tayi tayi ta cire ta kasa, driver dake can yana rufe kofan mota, yake fadin,,,

  wai me kika tsaya yine? zanfa rufe booth dinne, cak ya tsaya da tafiyar daya fara, ya waigo sanda driver yayi baya wajen booth din, da sauri ya dawo, ta dayan site din yake karisawa inda take tsaye harde da hijjabi jikin trolley, shi kuma driver na kokarin kama mata hijjab din ya cire, yana da kishin auransa, don haka da sauri yake fadin,,,

  uhmn uhmm, sai kuma ya waske da fadin,,,

   barshi malam Nura, jeka abinka ka karisa a'ikinka, bari na taimaka mata, ya mike da barin wajan yana fadin,,,

  toh yallabai, tsugunawa yayi yana hararanta, cikin sanyin murya yake mata fada, da fadin,,,

  ke komai sai an miki ne, baki iya abu da lura ba, ta kauda kanta gefe, sanda yake cuku cukun cire mata, harya samu yayi nasara, zai mike kenan sukai karo, kanshi ya bigi nata, bata jie wani zafi ba, nan kuwa shi ya dafe kai yana fadin,,,

  kaiii, ya salam, ya dago kai da kallonta yana fadin,,,

  waike ke wata irin mutum ce, kullum sai kinsa rayuwan bawa cikin kunci, ya mike yana kuma hararanta da cigaba da fadin,,,

  da wani kanki kaman dutse, ya juya kenan kuma yayi tuntube da tayar mota, nan yayi kaman zai fadi, ya samu ya tsaya cak, tare da kuma juyowa yana mata tsawa da fadin,,,

  bar nan, kin tsare mutum da ido, daga haka ya juya, harya fara tafiya kuma, sai wata zuciyar tace, waigo kayi mata magana don bata raina abin kuka, ku shiga gidan, a dauka wani abin kuka mata,,,

  da sauri yake juyowa dai dai sanda take tsaye tana murmushi, da dimple dinta daya lotsa, kullum in yana mata fada, saiya buge ko ya kusa faduwa, sauri tayi wajan gintse dariyanta, tana waskewa da daukan jakarta tabar wajan, shiko tsayawa yayi, so yake ya tuna last da yaga tayi murmushi, kafun ya saki ajiyar zuciya mai nauyi yana bin bayanta.


  _toh Anfara.......a nan kuma ruwan al-kalamina ya kafe, kuyi hakuri dani, abin da muka rubuta dai dai, Allah ka datar damu, wanda kuma nayi kuskure, ubangiji Allah ka yafe mana, ina ma kowa da kowa fatan alkhairi, taku har kullum....._
            *_Halima ja'afar yakubu_*

comment
share
Matatace
*2019*

meemartjj...........✍🏻
🕯🕯🕯
            _*MATATACE*_
     🕯🕯🕯

     

story&written by Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@meemartjj

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚

   *Dedicated to lovely sisters*
_Jameela ja'afar yakubu_
_Fateema ja'afar yakubu_
_Fa'iza ja'afar yakubu_



*_page 9&10_*

――――Da sallama ta shiga falon, babu kowa ciki, dai dai sanda mainat ke futowa daga site din kitchen, rike da mug a hannunta, ta tsaya sagalele tana kallon ummeetah dake tahowa cikin falon rike da yer ghana bag dinta, tana gaisheta, ta amsa da fara'a tana fadin,,,

  kariso kie zauna mana, ummeetah ta kariso tana zama cikin natsuwa, can gefe bisa carpet, dai dai sanda maami ta futo tana fadin,,,

  a'ah, wa nake gani kaman ummeetah, da sauri take fadin,,,

  ina kwana maami, da murmushi take fadin,,,

  lfylau, ina iyayan gidan naki? dai dai nan yake furta kalman sallama da zazzakar muryansa, maami ta amsa tana fadin,,,

   manya kaurin wasa, kune da sassafe haka, duk suka zauna yana gaisheta, mainat ta gaishe dashi, maami na fadin,,,

  ina suhymahn take, ba tare kuke ba?sai da yayi dan jim, kafun yace,,,

  tare muke, ta wuce sasan mummy ne, mainat ta dan tabe baki tana fadin,,,

  sashin mummy kuma, ita daya kamata ta fara shigo....tamke fuskan da yayi ne suna hada idanu, shine ya hanata karisawa, ya harareta, can kuma saita kalli ummeetah tana kallonsa da murmushi take fadin,,,

  yaya sadeeq naga ummeetah da jaka ne, ko nan zaku barta, kanshi a kasa yana faman ciccika yace,,,
  eh, saiki zuba ruwa a kasa kie sha, cike da murna take fadin,,,

  kai yaya sadeeq thank yhu so much, in sha Allah baxan baka kunya ba, ya dan dago da mamaki yana fadin,,,

  tohhh, maami tace,,,

  Allah ya tayaki ruko, da murna take fadin,,,

  Ameen, shiko sai kasa yayi da kai yana raya,,,

  da gaske kuke, maami tace,,,

   tafiya taxo ko?ya dago kai da fadin,,,

  eh maami, in sha Allah gata jirgin mu zai tashi, zamu kwana biyu a Abuja, tace,,,

     Allah ya sauke ku lfy, badai kaje kunyi sallama dasu yarinya ba(batulah), Amratu ma sai faman kira take, yaushe za kaje, gashi tafiyar taku harta zo, ya dan sosa kai yana fadin,,,

    Allah, lokacine ya kure, amman na tura musu da wasu kudade, kuma in sha Allah za muyi waya dasu, ta dan tabe baki tana fadin,,,

  a dai rike zumunci, don kafi musu kudadan nan da kake tunanin, shi suka fi bukata, ko wacce dai Allah ya rufa mata asiri, shiru yayi don yasan bashi da gaskiya, dai dai nan su suhymah suka shigo, saudat na rike da Irfan dake sanye cikin wasu ready made masu tsada, ya dire yana karisawa wajen daddynsa da gudu, shima ya sunfuce shi, ba kunya yake kissing dinshi da fadin,,,

   my boy how far, shima yaron yana kissing daddyn nasa, maami ta girgixa kai tana fadin,,,

  oh nie zamani, nan dai suka zauna, ana yer dariya, da kirkiraran yanganta na fama take gaishe da maami, wace take amsawa da fara'arta, tabi mainat da kallo dake mata wani murmushin nasara, ta dauke kanta, mainat na fadin,,,

  auntyna, ina kwana, da dan yatsina take amsawa, da fadin,,,

  lfy, kafin idonta yakai kan ummeetah da yer jakanta, tana zaro ido da kallonta take fadin,,,

  what, ke kuma wa yace kie dakko jaka, come on tashi kie maida shi, ance miki nan zamu zauna, tana wani yer dariya take kallon saudat da fadin,,,

    duba mun yarinya da karfin hali, sukai yer dariya a tare, ummeetah dake gefe, gabanta ya shiga dukan uku uku, kowa ya zuba mata ido, ta kuma daka mata dan tsawa tana fadin,,,

   baki jie ba kenan!da sauri ta  mike tsaye, maami tayi saurin fadin,,,

   a'ah, baka fada mata a nan zaku barta bane? kallonsa tayi da mamaki, ya dago kai daga danna wayansa yana fadin,,,

  no, maami ban fada mata ba, cos sai da safen nan na sanja ra'ayi, ya kalleta yana karisa fadin,,,

  karki damu suhymah, nayi magana da Dr. ango, yace zamu samu masu a'iki a can,  sai da tayi shiru na wasu yen mintuna, kafun ta girgixa kafada da fadin,,,

  a'ah, gaskiya ka sanja wannan ra'ayin, cos na riga dana sa duk wani ayyuka anyi training dinta, infact gaba daya ayyukan na ita t....... ya cice wajan fadin,,,

  plsss suhymah  kibar wannan maganan, saboda na riga dana yake hukunci final, daga haka ya mike rike da dansa, da kallon maami yana fadin,,,

  Abba yana ciki ko?maami ta nisa da fadin,,,

  yana nan ciki, daga haka ya wuce barayin da zai kaishi sashin mahaifinsa, tabi mainat da kallo wacce ke tsaye gaban ummeetah ta amsa jakan hannun yarinyan tana fadin,,,

  ummeetah zo muje, yarinyan ta wuce suka shige ciki, suhymah ta mike a sittin, hankali tashe mukarabanta na binta, suka koma sashin auntyn nasu, maami dake zaune ta kuma gyara zama tana fadin,,,

  Allah ya shirya mana, kafun itama ta mike ta koma ciki.

  Da kuka ta koma site din aunty yagana, wacce ke zauna tana rubuce rubuce, ta gama zayyane mata komai hankali tashe, saudat na karawa da fadin,,,

  kuma mummy duk sister mainat dinnan ne, burinta ya cika, a kufele take fadin,,,

  a'ini wannan yer baxan yarinyan na jima da cireta sahun yeyena, da alama ba nono na kadai aka bari tasha ba, maybe dai an faki idona anyi mata mix da wani, amman lokaci nake jira zata gane kuranta, ta kalli suhymah da fadin,,,

  kinga daughter kie kwantar da hankalin kie, indai house girl ne, tunda yace zai sama miki wata a can, nasam zaiyi hakan, kie daina bata ranki a banxa, cikin kuka take fadin,,,

  aunty dole in damu, gaba daya girke girke nasa an gama training dinta, sannan yace sai munje da Irfan, yasan baxan iya wani rainon yaro ba, ga karatuna dazan daura da munje can, ya ake son inyi da rayuwa na, nifa gani nake kaman maganin jikin sadeeq ya daina a'iki, da sauri take fadin,,,

   karki damu, akwai wasu ma, zan baki kie tafi dasu, suna da kyau nayi amfani dasu na gani, ta rika lallashinta, har ta samu dai hankalinta ya dan kwanta, suna cigaba da yen kulle kullen su, Allah shi kyauta.


   shiko zaune yake bisa wani tattausar carpet, gaban mahaifin nasa, wanda ke zaune a kasan shima, ya mimike kafafu, dan lele muneeb na kwance bisa ciyarsa, yayin da hannunsa ke rike da news paper yana karantawa,,,

   kaman kullum ya gaida mahaifin nashi cikin ladabi, ya amsa cike da annurin fuska, yana mishi yer nasiha tare da fatan sa'an akan abin da akaje nema, kafun ya mike suka  futo, aunty yagana ma suka futo ita da suhymah, maami da mainat ma duk sun futo, har packing space ana musu fatan sauka lfy, kafun su shiga mota driver yaja suka wuce.




  Duniya labari, dakin su muhibbat mainat ta kaima ummeetah kayanta, mai dauke da kyararran gado, up and adown, sanda munirat tasa kukan ita ta gama kwana a dakin, don ba xata hada daki da mai a'iki ba, tuni mainat ta fatattaketa da fadin, dama ba site dinsu bane, saita koma nasu, ta kwashe kayanta tabar dakin, lokacin da mainat tace ummeetah ta rika kwana down step, ita kuma muhibbat dama tana up, ummeetah ta kasa yarda itace zata rika kwana bisa gado,,,

  sanda mainat taga kunan dake hannun ummeetah mamaki tayi sosai, daker ummeetah ta fada mata wacce ta mata, ta rika mamakin tsaban mugunta irin na suhymah, kafun ta nisa da fadin,,,

    ouk, waya sa miki magani a ciwon naki?tace,,,

  Baffah sadeeq ne, shima shiru tayi, tana tunanin ashe dai yana da tausayi, ta girgixa kai tana fadin,,,
  Allah shi kyauta, ta kalli muhibbat tana fadin,,,

  plss muhibbat ki taimaka mata, ta tsefe kannan nata, sai tayi sabon kitso, da murnanta ta amsa da fadin,,,

  toh, don suna shiri da ummeetah, sai dai kam data fara tsifan da gudu ta koma cikin gida tana faman kiran,,,

  aunty mainat, Allah kixo kiji kan ummeetah doyi yakeyi, tare suka futo wajan, mainat na dan sinsina gashin tace,,,

  a'a a'a a'ah, yaushe rabon kie da kitso halan, baba balarabu dake cikin local kitchen din ta futo da yer dariya tana fadin,,,

  ina ruwan ummeetah, yanxun haka ruwa take lafta ma kan, mainat na fadin,,,

  a'iko abin daya fie ruwa ma, akwai a gashinan, ta kalli muhibbat da fadin,,,

  kwaso mun mayukan wanke kaina a bathroom, da sauri ta juya tai ciki, sai gata dasu, mainat ta wanke mata kai tas, sanda ta kammala tsefewa ana mata oiling, banda kyalli babu abin da gashin nata keyi, har gadon baya, muhibbat na faman fadin,,,

  Allahumma arzukni gashin irin wannan, mainat na hararanta da murmushi, ta gama mata sannan tace ta shiga wanka, ta futo su tafi gidan kitso ita da muhibbat. 
 

  Haka ummeetah ta cigaba da rauyuwan farin ciki, duk wani a'ikace a'ikace iya sashin maami kawai suke ita da baba balarabu, sai ladiyo da yerta bintu suna sashin aunty yagana, don haka ba abin dake kaita sashin su munirat, bare taci karo da rashin mutunci, ba ruwanta da karambani, ba wani a'iki take yiba, iyaka ta tsaya tana taimakonta da miko wancan sai wannan, sai kuma wanke wanke, da suke haduwa suyi da bintu, kafun wani lokaci ummeetah hartai dan kiba, fatarta ta washe, sosai ta samu saukin rayuwa, kullum tana kara gode ma Allah.



 A dakinta ta sameta zaune bisa dadduma, bayan sallah magrib, tana lazimi, ta zauna gefenta tana fadin,,,

  maami don Allah kiyi mun wani taimako, maami da murmushi take fadin,,,

  ina jinkie diyar maami, ta numfasa da fadin,,,

  dama yaya sadeeq ne ya bani wasu kudade, yana son in saka ummeetah private school mai kyau, da islamiya, shine yace, amman baya so asan shine zai dauki nauyin karatun nata, maami ta dan zaro ido da fadin,,,

  toh, shine kuma kike fada mun, da sauri tace,,,

  a'ah, maami bafa keba, su mummyn mune baya son su sani, nie kuma idan nace nie zan sata, mummy zata iya hanani, shine nakeso plss kice kece zaki sata, shiru tayi da tunanin,,,

  ikon Allah, wato bacin karfin addu'a, da sai dai yazo ya zagaya, harya tafi bata saniba, don iya lura ta gama lura, an gama dashi, ta nisa tana fadin,,,

   shikenan Allah ya taimaka, ya kyauta da yayi hakan, don yarinyan ta cancanci fiye da haka, duba da irin rayuwan da tayi a baya, mainat da murna take fadin,,,

  Allah kuwa maami, wannan ne dalilin da yasa nake tausaya ma yarinyan, saboda a rayuwa taci wuyar aunty suhymah kaman mene, tace,,,

  karki damu akwai ranar sakayya, kowa yayi na gari don kanshi, ta mike tana fadin,,,

  hakane maami, Allah ya nuna mana wannan rana, nagode da kika amince da shawara na, daga haka ta fice daga dakin, maami na dan girgixa kai da murmushi, gaba daya yarinyan duk cikin yeyen itace mai kyawawan halaye irin wannan.   

  

                     ***
   Lokacin kankani a kammala mata komai, class 6 aka sata, kasancewar tana da kwakwalwa, kuma fataran karshe suke, don haka ba jimawa suka zana zarabawan futa, ta wuce jss1, ummeetah tayi farin ciki sosai, don tana matukar son karatu a rayuwanta, gashi school din bayi da nisa dasu, don haka da an tashi gida, za kie ganta a gida, karatu take ba wasa, karfe hudu kuma suje islamiya, sai saturday sunday inda suke zuwa makarantar hadda.

  Rayuwa ta koma mata fari kal, bata da wani matsala a rayuwanta, kullum tana cikin farin ciki, tun a jss2 ta fara zama enmmata, tana shiga jss3 duk wani abu na emmatan taka, sun bayyana a jikinta, kasancewan tana da dan girman jiki, bata da wani kiba, amman dirin dake gareta yasata yin wata yer duma duma, dama gashi tana da dan tsayi, sai abin yayi mata das, daga sama har kasa, ba'acewa komai, sai barakalla, don idan ba an fadin shekarunta 16 ba, wani baxai yarda ba, duk tafi su muhibbat jikin girma, shie yasa itama tunda ta zama yen mata ba kasafai take yawo ba hijjab ba, ko ina zata da hijjab dinta, ita kunyan ma jikin nata takeyi,,,

   lokacin da natsuwanta da tafiyarta najan hankali ya kara futowa, bata da wani yawan magana, amman inta fada maka wani magana daya zaka dade kana mamaki, tana da saukin kai, da kuma kama mutuncin kanta, bata da yawan tara kawaye, kawayenta biyu ne, daga muhibbat sai bintu, tana kuma da

Please Login or Register in order to submit comment