Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hasale yake fadin,,

   amman a'i naga babu takura a a'ikin ko? ko guda goma kikeyi, kyace zaki tsara ma kanki yanda zaki rika zuwa, ba kullum kibar mun gida haka ba, jikin safe taja ta jingina tana mishi wani kallo kasa kasa, kafun ta saki wani shu'umin murmushi mai hade da sauti, tana fadin,,

  toh wannan kuma naga ra'ayina ne, yanda nake son a'ikina haka zanje, kalamanta ne suka daki zuciyarsa, kwata kwata bai fiye son rigima da tashin hankali ba, ya sanyaya murya wajen fadin,,

  suhymah ya kina karkashina, kina fadan irin wannan maganar, ki duba fa, d'ana bashi da lfy, amman kika iya sa kafa kika futa kika barshi, ta mike daga jinginar da tayi da kammala cire jacket din, tana kokarin cire karamar ciki, take fadin,,

   oh wai Irfan ke ciwo?da mamaki yake kallonta yana fadin,,

  so yhu are asking me question?bama ki sani ba, ta cire kayan daga ita sai bra da skinny can saman cinya, tana wani girgixa da fadin,,

  sweet plss kabar wannan maganan, be kamata ka dawo mun gida da rigima ba, it doesn't suit yhu dear, ta karisa maganan da zama tana huging dinsa, ta rage murya kasa kasa da fadin,,

  i miss yhu baby, zo na baka......, samun kanshi yayi da tureta gefe, iya rainin wayau ta gama mishi, da yike ta mai dashi jarababbe shine zata bullo tanan, yana fadin,,

  plss let me be, da mamaki take kallonsa, kafun ta mike tana dan dariya da fadin,,

   da gaske kake sweetheart, ta tabe baki tana shigewarta bayi, sai dai abin yadan sosa zuciyarta, ta jima bata ga irin haka ba, dole ta futo da wasu kayan a'ikin,,

  haka harta kammala wankan ta futo daure da towel, gaba daya a sukurkuce take, wani mugun kewanshi ke kuma ratsata, gashi bata iya rarrashin saba, sai dai ya rarrasheta, amman kam yau taga da gaske yakeyi, don juya mata baya yayi sosai, alama ma har yayi bacci,,

  shima a nashi bangaren fushi ya tsinci kanshi dayi da ita, dabe taba yiba, amman kuma shi kanshi yasan yana da bukata, kaman wasa ya jita ta bayansa, juyowa yayie, yana wani mammazewa, da dan tureta, dariyan mugunta tasa, tana kuma rungumoshi, tuni ta soma bi dashi ta wani hanya, suka manta damuwa tare da lulawa wata duniyan, kowa na kokarin faranta ma dan uwanshi rai.

   sanye da wata bathrobe ya futo daga bayin, sai karamin towel dake hannunsa, yana cigaba da goge jikinsa, tsaf ya shirya cikin black jallabiya, a hankali ya koma ya kwanta, yana binta da kallo dake faman shirga baccinta hankali kwance,,

  murmushi ya saki da lakuta kumatunta, yayi kewarta sosai da mamakin hali irin nata, duk yanda zaiso su kara kara kasancewa tare, ba yarda za tayi ba, haka kuma duk yanda zai fahimtar da ita yanda bata gamsar dashi, ba zata taba ganewa ba, ita dai kanta kawai ta sani, ya dan ja tsaki yana juya mata baya, da tunanin da suka cika mishi kwakwalwa, kafun wani bacci ya tafi dashi.
  

  
                        ***

   Alarm din dake jikin wayarsa ne ta tashe shi, dai dai lokacin daya kamata su tashi sallar asubah, da sauri ya mike da addu'an tashi daga bacci, ya nufi bayi tare da dauro alola, ya futo yaxo ya shimfida dadduma, sai daya tasheta kafun ya kabbarta sallah,,

   amman harya idda sallolinsa, ya kammala tasbihi bata tashi ba, dan tsaki yayi yana nade dadduman, da nufa inda take kwance, hannunta yake dan bubbugawa da fadin,,

   suhymah, suhymah tashi mana kiyo wanka kie sallah, juyi kawai take da kuma jawo duvet, ya dan nisa da fadin,,

    wai ba zaki office bane yau?da sauri ta ware ido da fadin,,

   what, sai kuma ta shiga kokarin tashi da fadin,,

  oh my god, sadeeq ka kasa tashina, ta jawo wayanta da duba lokaci, kafun ta mike zaraf tana fadin,,

  oh shet ina da meeting da zanyi attending early this morning, da ido kawai yake binta da kallo, ganin yanda jikinta na rawa ta nufi bayi, amma da yana mata maganan wanka da sallah, tana wani juyi, dan tsaki yayi da kuma tsanar wannan halin nata na yahudanci, agogo ya kalla dake jikin bango, yayi saurin waro ido yana futa daga dakin da sauri.

    _tom, Allah ya nufa gamu mun dawo, sai kuma fatan Allah yayi mana jagora, yanxun labarin ya soma, yanda kowa ya fara rubutunsa lafia, Allah kasa mu kare lafia, sharhi/comment yana da matukar muhimmaci a rubutu, ban taba tabbatarwa ba sai gabda zamu hutun ramadan, don haka ina bukatar sharshi, fatan mu shine mu hadu dukkan mu, mu karu da juna, don haka maganar gaskiya shine, zan dakatar da rubutu, a duk lokacin da naga babu comment/sharhin, hakan yakan nuna mun kaman ma ba'a karanta littafine, babu amfani ka rubutu abin da ba'a karantawa, Allah yasa mu dace._



comment
share
vote

*matatace 2019*
Na meemartjj               

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
[14/08, 14:29] Dala Grp: 🕯🕯🕯
            *MATATACE*
     🕯🕯🕯

     

story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjj

   
*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty Ummeetah and my Fa'ixation._

page 31/32

___________Dakinta ya wuce kai tsaye, a hankali ya tura kofan da furta kalman sallama ciki ciki, zaune ya hangota bisa dadduma hannayenta bisa sama suna fuskantar fukanta, murmushi yayi tana kokarin shafa addu'an da takeyi, ganin bata lura dashi ba, yasa ya maida kofan a hankali ya rufe.

dakin Irfan ya wuce daga nan, yaji dadi sosai yanda jikin yaron yayi sauki, cak ya saba shi a kafada, wanka yaso yin mishi, sai kuma wani tunani yazo mishi, kai tsaye ya kara futa zuwa bedroom din,  knowking kofan yayi tare da dan tura kofan,,

   dai dai sanda take mikewa daga kan dadduman, sanye cikin white hijjab har kusan kasa, hannunta nata cikin hannun hijjabin, ta kariso inda yake tsaye tana gaidashi cike da ladabi, kaman yanda ta saba koda yaushe, shima amsa mata yayi, a ranshi yana dada mamakin yanda ta tashi sallah, yasan dai ba waya ne da ita ba, bare yace alarm tasa, maganan tane ya dawo dashi tana kallon Irfan da fadin,,

  Irfan ya jiki, kaji sauki? shiko yaron sai dada manewa yake jikin babanshi, alama bai gama sabawa da ita ba, dan murmushi yayi da kallon yaron yana fadin,,

   say good morning to aunty ummee, kuma nokewa yayi, yana gaisheta ciki ciki, da fara'anta take amsa mai, ya mika mata shi da fadin,,

  plss gashi nan, wanka zaki mishi, zai tafi school ne, ba musu ta mika hannu ta amshe shi tana fadin,,

  tom, daga haka ta nufi cikin dakin da yaron, shi kuma ya juya ya nufi kitchen, ba bata lokaci ya soma hada musu breakfast, kaman yanda ya saba wani lokaci, sauri sauri yake komai, nan da nan ya kammala.

   bisa dinning ta sameshi yana faman jajjere komai, duk da karancin shekarunta be hanata yin mamakin ko ina matar gidan take ba, kardai ace har yanxun aunty suhymah bata daina halinta ba, can kuma wani sashin na zuciyarta na raya mata,,

  toh ke ina ruwanki, dan tabe baki tayi, tana karisowa dinning arean, sabe da Irfan dake cikin towel, sai kamshi daddadan sabulunta yakeyi, kallon juna sukayi, shima dai sai daya jie wani nauyi, amman ya maze tana fadin,,

  Baffah daka barshi naxo nayi, murmushin yake yayi da fadin,,

   a'ah karki damu, yanxun dai kije ki shirya Irfan, ga bedroom dinsa can, za kiga sport wear din da zaiyi amfani dasu yau cikin wardrobe dinshi , plss shap shap, karyayi late kinji, ya karisa maganan so serious, hakan yasa ta wuce kai tsaye tana amsa mai da,,

  toh, yayi sauri kallon agogan dake sagale can seating room, da sauri yake fadin,,

  oh my god, ya saki komai ya nufi daki, zaune take gaban dresing mirror har tayi wanka ta shirya, tana faman fente fente, bebi ta kanta ba ya fada wanka, ya futo ya kammala shiryawa sauri sauri.

    tsaye yake gaban safe din daya jie wani standard mirror, sanye cikin wasu american suite pusher golden, sai kyalli suke  kayan dai dai jikinshi, yana faman gyara neck tied, sumar kanan kwace baki sidif, ga sajen nan dake kara ma fuskan kyau, ya gyara komai need,,

  idanunsa a lumshe suke, tunani yake barkatai, kafun kuma ya bude idanu da dan tsaki, tuna in beyi da jiki ba zai iya late din office, wajen wata tsadaddan briefcase ya nufa, yana karisa hada wasu yen takardu a ciki, kafun ya rufe tare da dagowa, idanunsa a kanta suka sauka,,

   tana sanye da wata yer slim pinch armless dress, rigar har kasa, an gyara gashin nan, tare da zuba wata fashion dauri da black headtie, kallonta yake yaga ko a haka za tace zata futa, don yasan halin yen kayanshi, sai yaga ta jawo wata kimoni black ta daura a sama, ajiyar zuciya ya saki, yana komawa gaban dresing mirror, yayin da ita kuma take daddaure kafanta da wani igiyoyin takalmi mai tsinin gaske,,

   ji kake takalmin na bada sauti kawai, ta kasan ido ya dan juyo yana kallon kafan nata, saima taso bashi dariya, yana waskewa da juyawa da cigaba da daura agogansa, ita dai kullum cikin siyan fashion takalma take masu tsada, amma haryau bega wanda zaice tasa yayi mata kyau ba,,

   ta jawo wata kwalban turare tana budewa, da fara feshe jikinta, tun tana na hankali, har abun ya koma na hauka, cak ya datse turaran da murfinsa, yana kallonta itama shi take kallo da fadin,,

  sweetheart yadai, da ido yake mata bayanin ya isa haka, tayi wata yer dariya tana sakin mishi turaren, da fadin,,

   baby nah dan rigima, maida turaren yayi ya ije, tana kuma dan gyara fuskanta jikin mirror, kafun ta nufi wajen bag hanger, ta ziri wata black fashion bag, tana makalewa a hannu da fadin,,

   to nie na wuce, ye, juyowa yayi suna kallon juna, ta cigaba da tafiya tana dan dariya, don tasan kallon da yake mata, kafun yayi wata maganan ta ida futa tana fadin,,
 
   enjoy ur day sweetheart, da sauri ta karisa futa daga gidan, karya dagula mata lissafi, da wani saita saka babban mayafi, ko takan danta bata yiba, bare wata ummeetah data manta an taho da ita, ta fada  motarta, tana saita ma kanta hanya.

 
    shima nasa bangaren ajiyar zuciya ya saki yana dan girgixa kai, tare da juyawa, yana kammala shiryawa tsaf, ya dau briefcase dinshi, sai wata tsadaddan i~pad dake dayan hannunsa, hade da wayoyinsa, sai kamshi ke tashi a jikinsa na alfarma, kafafunsa sanye cikin costly black cover.
 
 

  dai dai sanda take futowa daga dakinta rike da hannun Irfan, sai empty plate&cup din dake hannunta, yayi dan murmushi yana fadin,,

  yawwa ummeetah yayi breakfast ko?kallo daya tayi mai, ta basar da fadin,,

   eh, amman besha drugs dinshi ba, a sanyaye ya ije karikitan dake hannunsa bisa dinnig table din, yana daga danshi sama daya taho da dan gudunsa, yana kiran sunan,,

  daddy, yakai mishi kiss saman cheek, suna magana da yer dariya,  da sauri kuma ya kalleta yana fadin,,

  oh plss bani drugs dinshi, yanxun school bus dinsu za kiga ya iso, da sauri ta wuce inda suke ijeye, ta dakko tana dawowa, har tana tuntube, da sauri yake fadin,,

   be careful, ta tsaya kan kafafunta, tana karisowa tare da mika mai, amsa yayi yana binta da kallo kasa kasa, kafun yace,,

   kifa rika yie hankali, nan ba irin tyles din da kika saba dasu bane can gida, ga mamakinsa sai yaga ta wani dago ido caraf suka hada, tana kuma kaudawa da dan basarwa, abin ya bashi haushi tun dazu take mishi kallon yatsina, ya dakata da bude maganin daya fara yana kallonta da fadin,,

  oh, ina miki magana ne, kina wani basarwa ko, to kiyi wasa, in kika fadi ke zaki fada ma jikinki, dariya ya bata yanda ya dage yana masifa, amma sai tayi dan murmushi da nuna mishi agogo tana fadin,,

  Baffah time yana tafiya fah, harara ya zabga mata, yana cigaba da abin da yakeyi, ta dan kauda kai da raya,,

  sana'a sa'a, da suka kuma hada idanu, sai murmushin yake tayi, da daukan dayan maganin tana fara budewa, ya dan girgixa kai da cigaba da abin da yakeyi, dai dai sanda school bus din ke faman jera horn acan waje, ya dago da sauri yana fadin,,

  oh my god, na manta lunch box din.......,,

   yana ina?shine abin data katseshi da fadi,  da sauri yake nuna mata kitchen, yana mata bayanin inda yake, shap shap sai gata dashi, yana kokarin yin mata bayanin yanda zata sa komai, sai gani yayi ta fara shirya komai yanda ya kamata, yana makale jikin baban yake fadin,,

  daddy i want biscuit?fridge ta nufa tare da budewa, kaloli biyu ta gani ciki, don haka ta dauko duka biyun, daga inda take take daga mishi da fadin,,

  vanilla or strawberry?,,

  vanilla!ya fada da murmushinsa, itama murmushin tayi, tana maida dayan, tare da dawowa ta saka mishi, ta gama ta rufe mishi, tare da rataya mishi bisa kafada, yana fadin,,

  thanks aunty ummee, da dan murmushin ta shafa kanshi tana fadin,,

  kayi karatu da yawa kaji, kanshi ya daga sama, shidai yana tsaye yana kallonsu, da alama akwai abin daya burgeshi, kafun ya daukeshi cak suna futa, har wajen school bus din dake tsaye can wajen light fence din daya zagaye gidajen dake arean wajen, ya mika shi suna ma juna waving, driver yaja motar suka tafi, ajiyar zuciya ya sauke yana komawa ciki.

 

  yana shigowa tana futowa daga kitchen, alama akwai abin data kai, ya kalli agogan hannunsa da fadin,,

  shet, da sauri ya kariso yana tattara kayanshi, rike da briefcase a hannu, sai I~pad din dake rike a dayan hannun, yake kallonta da fadin,,

  nie na tafi wajen a'iki, ga breakfast nan, in kuma be miki ba, zaki iya shiga kitchen ki hada wani, sannan pls kie gyara ko ina, kie kuma kula da gidan, 12pm Irfan zai dawo school, hope kin fahimta, tana dafe da dinning table din tace,,

  tom, kaifa?harzai juya ya dan juyo da fadin,,

  what?da ido tai pointing table din tana fadin,,

  breakfast, sosai yaji dadi, amman saiya wani basar da fadin,,

    no, Alhamdulillah, kiyi naki kawai, sai ki gyara gidan, itama dan basarwa tayi tana kasa da kanta da fadin,,

  ouk saika dawo, shirun da taji yayi ne, yasata dagowa, yana tsaye ya kafeta da ido, mai cike da alamar tambaya, kafun taga kuma ya kalli jikinsa daga sama har kasa, ya dago da fadin,,

  halan dai akwai abin da ki kaga be yi bane a shigata?da dan mamaki ta kuma zaro ido tana kallonshi, tare da girgixa kai tana fadin,,

  a'ah, ya dan taba fuska yana kuma kallon shigarsa, kafun yace,,

  toh meye, naga tun daxu kike mun wani kallon yastina?, sosai yaso bata dariya, da dan murmushi murya sanyi sanyi, take fadin,,

  tom kayi hakuri, shigarka tayi kyau sosai, jin abin yayi wani iri, kaman daga sama, yana fadin,,

  da gaske, ta daga kai a hankali, tana fadin,,

  eh sosai ma, murmushine saman fuskansa, yayi dan shiru da wani tunanin, kafun ya kalleta da fadin,,

  nogode, saina dawo, daga haka ya juya yana nufa kofa da wani nishadi, shi kanshi besan na menene ba, kai tsaye ya wuce building din garage din dake ta baya, already suhymah harta dauka motarta tayi gaba, dan tabe baki yayi, suna gaisawa da mr.jerry dake yen share share, sauri sauri ya shiga motar yana barin wajen, da rika duba wristwatch din dake makale a hannunsa, ganin ya kusa yin late ne, ya sashi kara ma motar gudu, yana daukan hanya.

   

    Ummeetah kuwa yana futa, ko breakfast din bata yiba ta fara gyara ko ina, shara zuwa moping, komai sai da tayi, dakin sune kawai bata shiga ba, don tana ganin kaman be dace ace ta shiga dakin nasu ba,,

  dakin Irfan ma yasha gyara, ta gyara corridor dake dauke da playing toys dishi, sai mamaki yawansu takeyi, kaman ba'ason kudi, shine abin da take ayyanawa, cottons din gidan ne ke bata kyama, tana son ta sanja, amman tana gudu kar matar gidan tace ta mata karambani, haka kuma bangaren girki taso tayi, saidai shima ba'a bata ixini ba.

    dakinta ta dawo, sai data gama gyara nan ma, sannan tayo wanka tare da shiryawa, tana kwance kasan wata carpet dake gefen gadon, hannu tasa ta bude side drowern dake kusa da ita, tare da ciro wata yer hardcover din memo, ta zaro wani plane sheet, tana budewa sai hawaye, haka ta zuba ma papern idanu, tana karanta rubutun dake jiki, kuka ta cigaba dayi harda shashsheka, kafun wani bacci barowa yaxo ya tafi da ita a wajen.

  

   knowking din kofan da akeyi ne, ya farkar da ita, da sauri ta tashi zaune, tana maida plane shet din cikin memon, tare da mishi kyakywan boyo, kafun ta mike taje ta bude mishi kofan,,

  da karfinsa ya shigo, yana wancakali da lunch box dinsa, taji dadin yanda jikinsa yayi sauki, wasa nacin ranshi, tana cire mai sport wears din ya kwasa kayan wasa zai futa, daker ta lallashi ya bari tayi mai wanka, sannan ta shirya shi, tana kammala shiryashi ya arce, fridge ya nufa taga ya kara zaran wani biscuit din sannan ya futa rike da wata katuwar mota, tana,,

  Irfan, ina ya fuce, ta window ta lekashi taga ya shiga dayan gidan dake kusa da nasu, ta dan numfasa kafun ta wuce bayi da dauro alola.

   3pm shima ya dawo gidan, a gajiye kaman kullum, ga uwar yunwa, rike da ledoji kaman yanda ya saba, mrs khamis dake cikin gidanta tana hangesa ta window, tasa dan dariya da fadin,,

    Allah sarki, an dawo fa kenan, har an fara riko leda, mr. na suhymah so pity, kafun ta tabe baki tana komawa ciki, da cigaba da shirya dinning din data kammala nata hot lunch din, Irfan ma yana samu ana karashi, kafun ta fara kwala musu kira da suke can suna wasa da yaranta, Esha da misha.

 

    sannu da zuwa tayi mishi, ya amsa ba wani walwala, yana mika mata ledojin take away din dake hannunsa, ta bisa da kallo da alama a gajiye yake, kafun tabi ledan hannunta da kallo, tana mamakin ko me yasa ba'a girki a gidan oho, sai wadannan abinci masu tsami, itakam bata wani iya cie sosai.

   bedroom dinsu ya wuce, sai da kanshi ya sara, ganin yanda suka tafi suka bar dakin kaca kaca haka yake har yanxun, ya zauna dafe da kanshi, kaman zai kirata ta gyara sai yaga be dace hakan ba, yaja wata tsaki yana kuma rike kai dake sassara mishi.
    
  sanda ya futo falon sanye cikin wasu kananun kaya, alama wanka yayi ya canxasu, sai lokacin ma ya lura da yanda falon yake komai need, murmushi yayi yana zama bisa dinning chair din, ya lura dakin sune kawai bata shiga ba,,

   ta kuma kyauta, ya fada yana jinjina kai, tare da ciro abincin, sai dai kaman kullum tsakula kawai yayi ya tashi ya koma ciki, ita dai ummeetah tana can daki karatun kur'ani takeyi, sanda zai futa, sai da yayi dan jim yana sauraran muryanta, kafun kuma ya fasa mata magana, gudun karya katse mata karatun ya fice.



                           ***
      yau da wuri ta dawo gidan, sai dai bata wuce gida kai tsaye ba, sai data shiga wannan gida, ta fito ta shiga wannan, har lokacin daya futo zuwa sallah magrib, ga motarta amman bata, tsaki kawai yayi ya hau tashi motar ya wuce, don masallacin da yake zuwa yana da dan nisa daga nan.

   zaune ya sameta, lokacin daya dawo, bayan sunyi sallar isha'i, tana sanye da wata friendly jacket, sai yer pencil trouser kaman kullm, kannan a bude pake a tsakiya, laptop ne gabanta bisa hannun kujeran, sai wata yer tambulan rike a hannunta dake dauke da lemu, kafa daya kan daya tana girgixawa,,

   yaji dadi da yaga yaron bisa cinyarta yana bacci, ita kuma ta bada hankali sosai kan laptop din, da alamu akwai abin da takeyi mai muhimmaci a wajenta, ta dago kanta sama, sanda ya kariso inda suke da fadin,,

  wlcm sweetheart,,

   thanks, ya fada yana dan rankwafar da kanshi gefen fuskanta, ta sakar mishi kiss a kunci, shima dagawa yayi yai kissing dinta, daga nan ta maida kanta bisa laptop din tana fadin,,

  plss ka dauke Irfan, jikina na gaji, da murmushi ya daga yaron cak, yana komawa dayan site din kujeran, ya zauna da kwantar da yaron a jikinsa yake fadin,,

    kinga jikin Irfan yaji sauki sosai, da dan mamaki ta dago tana fadin,,

    what, sauki kuma?, wani kallo ya bata da yasa tayi saurin fadin,,

  oh, sweetheart dama a'i kaine kake damuwa da yawa, akan ciwon dabe da wani zafi da yawa, daga haka ta cigaba da latse latsenta, dan girgixa kai kawai yayi, yana jawo remote tare da maida hankalinshi kan tv, can kaman daga sama ta dago tana fadin,,

   wait, sweetheart wai ina house girl din da kace zaku taho tare?kallonta kawai yayi yana nuna mata dakin da remote din hannunsa, tare da cigaba  da kallonsa, ta kuma jefo tambaya da fadin,,

  wai kana nufin tare kuka taho, since ban ganta ba?, be kalleta ba yake fadin,,

  to ya za'ayi kie ganta bayan baki zauna a gidan ba, dan yatsina fuska tayi tana fadin,,

   shine ta wani kunshe a daki kaman munafuka, a'i daka sanar dani, ta fara a'ikinta tun yau, ta gyara zama da kyau tana faman kwala kiran,,

  keee ummeetah, ummeetah!da sauri ummeetah dake shirin kwanciya ta mike, sanye take da wata yer rigan bacci mai dan kauri, har kasa, sai karamin hannu, duk da wannan be hana surar jikinta futowa da kyau ba, jin irin kiran da take faman kwada mata na tashin sense, yasa ummeetah yafo wata yer gyale bisa kanta tana futowa da faman jera addu'a, tare da amsawa da,,

      Na'am, cikin natsuwa ta kariso wajen ta tsaya, shi kanshi da yake zaune, gabanshi sai luguden fadi yake, baya son suhymah tayi wani tozarci ga yarinyan, ya kasa kallon inda suke, sunfi 5minutes a haka, ummeetah na tsaye, yayin da shugabar ke faman daddanna laptop da murmushi, kome take dubawa oho, can kuma da hannu take pointing dinta da fadin,,

   kar a tsaya mun akai, ta fahimta me take nufi, don haka ta silale a nan wajen, sai lokacin yakai dubansa gareta, ya kasa janye idanunaa daga kallonta, zuciyarsa ke raya masa abubbuwa iri iri, haryau yana mamakin irin surar dake ga karamar yarinya kamanta,,

   jie tayi kaman ana kallonta, ta dago kai a hankali, da sauri ya waske idanunwa, ta maida kanta kasa, bai dandara ba kasa kasa yake kara kallonta, ga mamakinsa sai yaga tana kuma gyara gyalenta, haushin kanshi yaji, yana yer tsaki da fadin,,

  wai angel yadai, kin kira yarinya, kin kuma koma a'iki, dan numfasawa tayi da fadin,,

  umm hmm, ina son ki saurareni da kyau, farko dai ina miki barka da dawowa garemu, da fatan baki manta da wacece aunty suhymah ba, sannan US ba kaman kasan babanki yake ba, don haka saiki kula da kyau, bana son wani rawan kai da kauyanci, tana magana hankalinta nakan laptop din, tai dan shiru kafun tace,,

   kije dai, gobe zan gabatar miki da dukkan ayyukan daya kamata kiyi handling, ta jawo glass cup dake table din dake gabanta tana fadin,,

  sweetheart sannan ina tunanin bedroom dincan yayi mata girma, infact gidan nan yayi mana kadan da za ace house girl na tare damu, why not ta koma karamin dakin dake tacan building din garage, ta maida cup din ta ije tana cigaba da danna laptop din, da fadin,,

   anyway hakama za ayi, kie tattara kayanki gaba daya, gobe zaki koma can da zama, tuni cikin ummeetah ya duri ruwa, don taji anyi maganan can waje, a razane ta dago kanta dake kasa, tana zuba mai idanunta da suka cika da hawaye, shima ita yake kallo, gaba daya sai yaji tausayinta ya kamashi, ya numfasa yana kallon

Please Login or Register in order to submit comment