Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nayi, runtse ido ummeetah tayi, tana dan kauda kai gefe, tare da kuma kankame leden, sosai yake binta da kallo, dariya abin keson sashi, amma sai ya daure yana fadin,,

dallah can banxaye, cewa nayi ku fada mun ko menene, kafun ku sanar dani kona waye, kallon kallo suka fara yie ga juna,,

ma......maganin mura, cewar hibbat, ummeetah ta amshe da fadin,,

ehhh eh maganin mura, da dan mamaki yake kallan yaran, har yashema aka haifesu, da zasu sashi a kwana, yabi ledan da kallon yana kuma hangen blue green din ledan dake cikin farin ledan, tana wani baya baya da ledan, tare da yarfa hannu daya bisa kirji da dan fidda sautin tari, kaman gaske,,

ya dago kai yana kallonta, itama shi take kallo da kyawawan idanunta, kafun ta tsaya da tarin, tana dan tsuke baki da daga gira sama, shima giran ya daga sama, yana dan daga kai, alamar da gaske kuke,,

kuje, Allah sawwake, suna sauri sauri suka amsa da, ameen suna barin wajan, hibbat da bata raina abin dariya, ta rika tuntsirawa, har suka shiga ciki, shiko sauke ajiyar zuciya yayi, da ayyana abubbuwa da dama a ransa, ya kare da fadin,,

kai yarinyan can, za ayi da ita, ta fiye wayau da yawa, yayi dan tsaki yana cigaba da danna wayar.

shiru falon yake, yana zaune bisa dinning, inda aka shirya karin kumallo, maami na dakinta ta kwanta, sai babah balarabu dake kitchen tana yen a'ikace a'ikacenta, kadan kadan kuma yake jiyo motsin enmmatan a daki, can hibbat ta futo sanye da hijjab alamar futa zatayi,,

ke!shine abin daya juyo da ita a dan raxane, da sauri tana fadin,,
ina kwana baffah,,

lfylau, ina zuwa shugaban masu iya futa?, ta dan turo baki da fadin,,

zanje suyo ma ummeetah magani ne, yamutsa fuska yayi da fadin,,

me kuma ke damunta yanxu?ba tare da wani tunanin ba, cike da wautarta tace,,

ciwon mara......sai data fada kuma, ta toshe baki tana juyawa dajin kunya, shima kunyar yaji musu yana fadin,,

dalla sakarya bace mun da gani, ta fuce cikin sauri, ya dire spoon din da sakin ajiyar zuciya, yana son suyi wata magana da yarinyan,,

amma...... dakin maami yakai dubansa, kafun ya mike yana daukan goran swan din, yasha ruwan ya maida ya ije, yana wucewa bedroom din.

A hankali ya daga cotton din, tare da karisa shiga ciki, tana kwance rufe da blanket, ta juya baya, cak ya tsaya yana jingina da wardrobe da zuba mata idanu, duk da tana cikin blanket, bai hanashi ganin wasu kyawawan surarar taba, yafi minti uku a haka, kafun ya nisa da raya,,

yarinyan tayi ta ko ina, amman she is not my type, dai dai sanda taji a jikinta ana kallonta, ta yunkura tana cuku cukun juyowa, gabanta yace rass, tana kallonsa, sai kuma ta shiga kokarin tashi, harta dago, sai ta koma tana runtse ido da dafe mararta, ya kariso yana kallonta da fadin,,

sannu zaki tashi ne?kai ta daga alamar eh, kai tsaye ya mika mata hannu da fadin,,

zo in taimaka miki, ya mata kaman wata karamar yarinya, kallonsa kawai takeyi, shima ya zuba mata ido daga kwancen da take, sai daya gama kare mata kallo nanma, sannan ya kuma fadin,,

ko baki sone, in janye hannuna, wani war da ido tayi, kafun ta yarfo mishi duka hannu biyun nata, tafukan hannunta ya fara rikewa, masu tsananin taushi, kafun tayi kaman zata fadi, yayi saurin maida hannayensa bisa damtsen hannunta,,

suma don taushi kaman yatsunsa sa nitse, ba shiri ya nemi wuri kusa da ita yana zama, da taimaka mata ta zauna da kyau, bubu gown ne a jikinta, sai dankwalinsa data yafo a kai, ta zauna tana gyara wuyan riganta, da dada rufe jikinta da dankwalin, duk yana lura da ita, itakam a hakan ta yarda dashi ne, kasancewan tasan tun bayau yake shigowa inda take ba, kuma be mata komai,,

ke bari wani adana jikin kie, sadeeq bashi da lokacin wannan kayan, ya ayyana hakan yana hada rai, hannusa na gogan gwiwowinta data hade waje daya, tana dana matso da kafanta, tana facing dinshi ta gefe,,

ina kwana Baffah sadeeq, ta fadi hakan cikin wata irin murya, na mare lfy, ko kuma bacci, sai daya amsa mishi daga tsakan kanshi har yatsa, ya daure da fadin,,

lfylau, ya jikin, hibbat tace baki da lfy, meke damunki?shiru tayi da wani tunanin, zatai magana kuma yace,,

wait ba sai kinyi wani karyan ba, inaso muyi magana ne, akan abin dana zo na taras yana faruwa keda muheet, wani irin zaro ido tayi, yana fadin,,

plss, karki cinye namana danye, ta numfasa kaman zatai kuka take fadin,,

Baffah sadeeq nifa ba ruwana, don Allah ka yarda dani, bansan komai ba, jawoni kawai naji yaya muheet yayi cikin dakin, amman bama da kaina na shiga ba, ya danja numfashi da fadin,,

kin tabbata, wannan ne karo na farko zuwan kie BQ din, cikin natsuwa ta daga kanta da fadin,,

eh, ya daura da fadin,,

bai kuma taba miki komai ba?dan shiru tayi, kafun tace,,

nifa ban gane me yake nufi bama da hakan, da sauri yake fadin,,

kamar yaya?tace,,

tambayar daka mun itama ban fahimta ba fa?kallonta yake da mamaki, kafun ya sauke kanshi da dan sosawa yana raya,,

hmmm sadeeq gafa yarintar ta futo, dama girman jikin ne kawai, ya kuma wani daure fuska yana fadin,,

sex, hope baki bukatar explanation, ya karisa maganan da kin kallon cikin idonta, tai dan dara dara, kafun tace,,

sex, an fada mana, shine banbanci tsakanin male and female, cike da takaici ya dago sai yaga kaman da rainin wayauma take mai hakan, yana fadin,,

a'ah, ba male and female ba, boy and girl, ko kuma man and woman, za kice ba'a muku fiqhu ne a islamiya, cikin sanyi sanyi da nokewa ganin yana surfa mata masifa take fadin,,

ana mana, bama mu dade da fara sabon littafin, da muka siya ba, ya zabga mata harara yana fadin,,

sai ki kuma dagewa, don nasan, kun kusa zuwa wajen,,

toh in sha Allahu, ta fada da gaskenta, abin ya bashi dariya, har sai daya dan dara kadan, yana raya ,,

hmm, ummeetah kenan, yarinya da sauranki ashe, can idanunsa suka hango masa farin ledar dake bisa mirror, kusa da site din da yake zaune, hannu yasa yana jawowa, dama ummeetah tun sanda yakai idanunsa wajan ta dauke kai, ya bita da dan kallo, yana kallon yanda take faman cice baki, tare da juya mishi keya, ya kuma sakin murmushi yana budewa da fadin,,

maganin mura ne wannan ko?harda lekawansa, har ta fara using wasu, ta kuma runtse ido, a'i bata san lokacin data saka kanta cikin cinyoyinta ba, lokacin da taji yana fadin,,

zaifi in baku shawara, in kuje siya kuce ya rika saka muku a bakar leda, basai yayi iyayin sa muku a mai siteeka ba, ko kuma ku rika sakawa cikin hijjab, no need ku rika tafiya kuna nuna ma duniya kun fara period, kuma matse kanta tayi cikin cinya don kunya, yana kallonta da dan dariya, abin nata ma burgeshi yayi, ya maida ledan inda ya dauka yana cigaba da fadin,,

ina tunanin, zai taimaka muku ma wajan rage karyan maganin mura kuka siyo ko, tunda area shop ba chemist bane, ta kasa dagowa, bare tace wani abu, ya wani dada gyara zama, irin shi yana tare da mata, zaiyi magana kenan, yaji muryan maami na faman kwala kiran,,

hibbat!hibbat!a razane ta dago, duk da shine a dakin, amman sai taji wani iri, ta kai dubanta kanshi, dake wiki wiki da ido, yana tunanin ta inda zai fice, da kunya maami tazo ta tarad dashi a nan,,

da ido yake mata alamar taje ta duba, ta yaye blanket din, tana gyara dankwalinta, da sauka kasa, a hankaki take lekawa, maami na dakinta tana cigaba da kiran sunan hibbat, ta juyo itama da shegen wayau take magana rada rada,,

tana bedroom dinta, tsam ya mike da yer arsh jallabiyan shi, sai daya kariso inda take tsaye, ya daure yana kallonta da fadin,,

kinsan dai a stage din da mace ta fara period, ba aso namiji yana taba ta ko?

eh, shine ta fada dayin kasa da kanta, tana cigaba da fadin,,

auntyn mu da maami sun fada mana, ya sauke ajiyar zuciya da fadin,,

good, kie tsaya a nan har in futa, daga haka ya fuce daga dakin, kaman wani mare gaskiya, sai da yaje can kofan futa falon, sannan ya juyo yana mata singing ta amsa kiran, fit ya fuce daga falon, ta sauke ajiyar zuciya tana nufa dakin maami da fadin,,

na'amm, maami bata nan, tana tafe tana gyatta dankwali.

***
ummeetah fa an kammala jarabawa, walima sosai sukayi, sai murna take an wuce junior class, yayin da hibbat ke mata dariya, ganin su sun wuce da wajan, don yanxun ss 2 zasu shiga, maami, mainat dashi kanshi uban gayya, sun kashe mata kudi sosai, har walimanta tayi cikin gida,,

shagargarin ranan su zahira suka zo gidan, tunda suka zo bata da sukuni, basu da wajan hira sai sashin maami, anayi ana mata habaici tare da cin mutunci, ita dai data gansu zata tashi tabar musu wajan, in suna dakine tana falo, in kuma suna falo to tana daki abinta.

a haka dai, wani ranan saturday, maami ke fada mata ta shirya gobe, kawunta zasu sauketa garinsu taga yen uwa, toh kawai ummeetah tace, amman hankalinta ya tashi sosai, bata kaunar zuwa garin ko kadan.

Ranar ya shigo sanye da grey colour na wata shadda mai tsadan, hulan nan mai tsada na saki, sai kafansa dake sanye da tsadaddan takalmi sau ciki, sai kamshi yake na alfarma, ya shigo yana gyara links din hannun riga,,

sun jima suna hira da maami, kafun ummeetah ta futo cikin shiga na mutunci, riga da zani na lace, coffee sai milk a jiki, duk cikin sabbin kayan sune da ake musu na sallah, ta saka milk din hijjabinta, dan dai dai, tare da dan plat shoe dinta, hibbat naji kaman ta bisu, sukai sallama da maami tana bata kudi tayi tsaraba, ta futo suka wuce wajen mota.

suko su saudat gulman aka kai, yayansu zai kai ummeetah gida, maybe ma tafiyar kenan, sosai mahaifiyarsu kejin dadin hakan, tana fatan hakan ta kasance, hankali kwance suka cigaba da sabgogin rayuwansu.

idanu kawai ya zuba mata, yana cikin black optima kirar zamani, tafiyan nan nata najan hankali na dada tsatso da a'inihin kyaunta, ta zaga zata shiga gaban motar, wani iri yaji, ta glass din mota ya dan leko, yana kallon driver dake shirin shagi mazauni driver shima, yana fadin,,

wannan ta zagayo ta nan ne, cikin girmamawa yake fadin,,

toh yallabai, yana nuna ma ummeetah ta shiga baya ne, ba musu ta bude bayan ta shiga, yana faman ciku cikun ciro waya a aljihu, kusa da kunninta ya rankwafo, driver na kokarin tada motar, baya son maganan ta futo da karfi ne, so silent yake fadin,,

maami ta damu kije kiga yen uwanki, ya nisa yana ciro wayan a aljihu, da dan kallan gefe har yanxun yana kusa da ita, yake cigaba da fadin,,

yanxun dai ina tunanin zaki bimu muyi zumuncin da zanje yie, amman babu batun zuwa rugan rogo, fatan kin fahimta, kanta ta daga da dan murmushin murna tana kallonsa, ya janye jikinsa yana dada zaunawa da kyau, da maida hankalinshi kan wayarsa, yana fadin,,

good, don yanxun mu kaje garin nan, sai sun kusa soya mu danye, maami ba zata gane hakan ba, ya karisa maganan yana juyowa da kallonta, itama shi take kallo, ta gefe take zubama kyawawan zanen mallancinsa idanu, da sai yau ta taba lura dashi, kasancewan nashi sirara ne, dake tsakanin fine sajen fuskansa, ya dan daga gira da fadin,,

what?da sauri take waske idanuwa, amman fuskanta na kallon site din da yake, harda taguminta, kafun ta kallesa sosai tana fadin,,

bakomai, sai kuma ta cire tagumin tana komawa ta zauna da kyau, da cigaba da kallon cikin anguwansu da driver ke ketawa, numfasawa yayi da kauda kanshi yana raya,,

shegen wayau kaman na Affanta, kawai shima saiya kinshingida da kyau jikin kujeran motar, yana dan daga kai sama, da tuno abokin nasa, kuma amininsa na har abada............

**shekarun baya**

Gudu sosai yake zubawa, bisa hanyarsa na zuwa Abuja, lokacin da ya fara amsa sunan shi na dan kasuwa, amman ya maida kanshi stingy na karfi da yaji, kasancewan ya saka burin gina companyn shi na farko, wato food and beverage unit, don haka motar da yake hawa ma ba wata babba bace,,

Dajine sosai wajen, mai tudu, sai dai dan gaba akwai wata katuwar fili mai fadin gaske, wanda ke dauke da kuyya kuyya, alamar ana shuke shuke a wajan, baisan meyasa ba, duk inzai wuce wajan saiya ta kallon wurin, yana jin wani nishadi a ransa, gefe daya ga kyawawan bishiyoyin da suke wajen, kullum zai wuce saiya kai idanunsa wurin,,

sai dai yau, koda yakai idanunsa wajen, da sauri ya kara kai dubansa, ganin halittun shanaye, wanda tun yana hangensu baki bakin hill din, har ya daina ganin iyakansu, mamaki yakeyi yanda fulanin suka zo dokar dajin nan kiwo, sai dai yabar hakan, a killan irin masu yawan kiwo ne, suka sauka wajen,,

da sauri yake taka burki yana packing bakin titi, saboda motar dake neman tsayawa da kanta, ya daki steery da fadin,,

shet! ya futo yana bude gaban motar, injin ne yayi zafi, alama ruwa yake bukata kafun ya cigaba da a'iki, ya numfasa yana tunanin ta inda zai fara, kawai sai ganin bafullatanin yayi yana gangarowa, sanye da kayansa riga daban wando daban, sai takamin robansa da yer sandar kiwonsa, har ya kariso sadeeq da dan shakku a zuciyarsa da raya,,

ju mutum kaman aljani, sallamar da yayi mai ne, ya sashi sakin ajiyar zuciya, yana amsawa, kai tsaye ya mika mai hannu su gaisa, sai daya danja lokaci kafun ya mika mishi hannu sukai musabaha, bafullatanin yayi murmushi, cikin hausarshi na fulani yake fadin,,

karka damu, nie mutum ne kamarka, haka kuma rugan mu yana can ta baya, cikin mamaki sadeeq ke fadin,,

kana nufin akwai mutane dake rayuwa a wajan nan, murmushi ya kuma yie da fadin,,

tabbas kuwa, za kayi mamaki in kaga irin halitun da suke rayuwa a wajen, mu mutane da kuma dabbobin mu, ya numfasa da wani dogare sanda yana tsayuwa, da kallon motar yake fadin,,

naga kamar motarkace ta samu matsala,,

eh, wlhy injin ne yayi zafi, ina bukatan ruwa, gashi babu cikin motana, sosai ya rangada,,

subhanallah, ashsha, ka danyi hakuri, yanxun nawa ruwan ya kare, amman na a'iki yarinya tah rafi ta samo mun wani, kadan jira kadan, can ne babu nisa, sadeeq yaji dadi yana fadin,,

can kuma, kasan fa ku fulani can dinku ba kadan bane, a tare sukai dan dariya yana fadin,,

hakane amman ta dan juma da tafiya, yanxun ka ganta, jingina yai da motarsa yana fadin,,

babu matsala, tunda nayi karo da bafullatanin dake jin hausa radau haka, shima dada gyara tsayuwa yayi yana fadin,,

a'i inma bana jin hausa, sai in maka irin ta bature, is zeye ani problem, a tare suka kuma sa dariya, wato yana so ya nuna mishi har turanci ya iya,,

Affah!Affah!shine abin da suka jiyo a kansu, da sauri mahaifin ya juya da murmushi a fuskanshi, yayin da muryan yasa sadeeq jin wani yarrr a jikinsa, yana kai dubansa saman hill din.


comment
share
Matatace
*2019*

meemartjj...........✍🏻
[14/08, 14:29] Dala Grp: 🕯🕯🕯
            *MATATACE*
     🕯🕯🕯

     

story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjj

   
*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty Ummeetah and my Fa'ixation._


page 19&20

__________muryanta kawai suka rika jiyowa, har suka fara hangenta, yarinyan ce da bata wuce kimanin sheka shida ba, sanye cikin kaya irin na usulin fulani, gashin kanta ma yaji kitson fulani,

   taja ta tsaya,  tun daga nesa taka faman murmushi, rike da farar goran ruwa, sai wani leda a dayan hannun, ta cigaba da gangarowa tana kiran sunan mahaifin, shima gani yayi ya yarda sandar nan, yana komawa kan tudun da fadin,,

  ummeetah yie a hankali, itama tana cigaba da gudunta, tana Affah, yana ummeetah, harta iso inda yake, yayi saurin riketa, yaga dai ya duka suna magana, tana daga mushi ledar dake dayar hannunta, kafun ya amsa goran ruwan da murmushi yana shafa kumatunta, ya juyo yana dawowa inda sadeeq yake, lokacin da ita kuma tayi wajan wata yer bijiya da suke zama, tana cigaba da kallon tarwadan data samo cikin ledan,  ya kariso yana fadin,,

   kayi hakuri fa, kasan yaro da wasa, da tuni ma ta dawo, ya amsa ruwan sanda yake taimaka mishi ya sanya ciki, ya kammala yana mishi godiya, ya mika mishi roban ruwan da kallon ummeetah dake can yana fadin,,

   amman yarinyan kace wacan?da murmushi yake fadin,,

  kwarai da gaske, kayi mamaki ko?y'etace, kuma jinina, sadeeq ya zaro ido yana fadin,,

  kana nufin kana da aure, har ka haifi yarinya kamar wancan, dan dariya yayi kafun yace,,

   to bari in fada maka, ina da shekara goma sha tara nayi aure, matata kuma nada shekara goma sha shida a lokacin, hakan ma na aureta a babbace sosai, shima yer dariyan yayi da fadin,,
 
   what!sha shida, itace babba, yace,,

   kwarai kwarai kuwa, yoh yarinyan iyayi wuta ne a bari takai sha biyar, anma kaga shekara sha hudu yawacin yara na dakin mijinsu,  mamaki yakeyi, ganin shi matar dazai aura kusan shekaru ashirin da hudu tabama baya a lokacin, bafullatanin na cigaba da fadin,,

   kaga ummeetah ma baxan aurad da ita a shekara sha hudu ba, tana da shekara goma sha shida zan aurad da ita, lokacin ta girma sosai, a tare sukai dariya yana fadin,,
 
   ka daina dariya, kasa ido ka gani, indai da rai a'ikune masu bada auran nata, cikin dan mamaki sadeeq ke fadin,,

   harda ni kuma, ya kada kai da fadin,,

   ohh, kayi hakuri fa, kawai dai lokaci daya ka shiga raina ne, shine na maida kai abokina, ba tare daka sani ba, amman yanxun na fada maka, da fatan zamu zama yen uwan juna, murmushi kawai sadeeq yayi, don ya lura mutumin akwai barkwanci, ya mika mai hannu yana fadin,,

    shikenan sunana Abubakar sadeed, ya mika mai nashi da fadin,,

  Allah sarki sadeeku, nie kuma Aliyu, maxan fama kenan, musabaha suka kuma yie da dan dariya, kafun su zare hannayensu, yana juyawa da kiran sunanta, cikin harshen fillanci yake mata magana, sai gata da gudunta, kafan nan yaji yen sabbin silipers, amman yaji tabo da uban kura, mahaifin ya dafa kan yer tasa, yana kuma mata fillanci, da sauri take fadin,,

  Baffah ina wuni,,

   lfylau, shine abin da sadeeq yace yana murmushi, kafun ya kuma jin Affahn na mata magana da yarensu, tana kuma kallon sadeeq din da fadin,,

   gud aftanun, dan zaro ido yayi, haryana shafa kanta da fadin,,

   wow, afternoon, sukai dariya, Affahn yana mika mata sadar kiwo taje ta kado wasu shanu, da gudu kuwa ta nufi wajen, sadeeq ya bita da kallo kafun ya juyo ga abokin nasa dake nisawa da fadin,,

   ka ganta nan ita kadai na mallaka, gaba da baya, sai kuma yen dabbobina, ina son ummeetah sosai, shi yasa nake iya kokarina don ganin rayuwanta ya inganta, yanxun haka wata yer primary nake kaita, can can gaban rugan mu, saboda nisarshi so uku take samun zuwa a duk wani mako, jinjina kai sadeeq yayi yana fadin,,
 
  Allah sarki, ka kyauta, kuma ummeetah tayi sa'an mahaifi irinka, kamar yanda zanso inga wannan uwar gida data haifi yer lele ummeetah, shiru yaga Ali yayi, kafun ya dago yana sanar dashi a'i tun wajan haihuwan ummeetah ya rasata, kaman zai kuka, dole sadeeq ya dafashi, da kalaman rarrashi,,

   kafun suyi sallama zai tafi, nan kuwa yace, dole saiya tsaya ya amsa ma ummansu madaran shanu, duk yanda yaso ya barshi amman ya kafe, da sauri yake dauko wani clean gora ya nufi wata uwar shanu mai shayarwa, sannan ya tatsi nonon ya kawo mishi, fari tass cikin goran, godiya kawai yake mai, kafun ya shiga motarsa ya wuce, yana ayyana irin dibun kirkin bafullatanin,,

   shima din kallo yabi sadeeq din dashi, daya ja motarsa yabar wajan, wannan ba shine mutum na farko daya fara taimaka ma akan hanyar ba, amman baisan me yasa yaji sadeeq din shi na daban bane, ya numfasa yana komawa ga shanayensa.

 

   a nan sukai sallar la'asar,  biyar nayi ya soma hada kan dabbobinsa, shanaye da awakai, masu tarin yawa, suka nufa hanyar gida, ummeetah rataye da roban ruwansu, tana rike da kinfin data samo a rafi, yayin da yake goye da yer sandarsa a baya, ya tasa abin kiwonsa dake tafi zugwi zugwi a gaba.

  Ruga ne mai dauke da jama'a da dama, zaka iya ganin ginin jinka, ko kuma ginin dakunan kasa, masu shafaffen rufin kwano, wanda ta ciki su kaji silling da ledar madara kona biscuit, dai dai ne gidajan, don daga nan za kayi tafiya da dan dama, kafun ka kai wani gidan, babu katanga, amman daga wannan dakin zuwa wannan dakin yana nufin sasa sasa ne,,

  shima Ali wata gida naga ya nufa, mai dauke da ginin jinkokin da dakunan da yawa, gefen dama wata katuwar makwacin shanayen, sai gefen hagu kuma yer karama, wacce ke dauke da yen tsirarun shanaye, salihu kaninsa ne cikin wannan rugan yana faman daure wasu awaki, yayin da Audi, wanda yake yayan shine shi kuma, yake bama shanayen abinci, dole ta nan Ali zai wuce kafun ya isa nashi ma'ijiyar dabbobin dake gefen dama,,

  salihu ya banka mishi harara kaman yanda ya saba, kafun su fara zuba mishi habaici wani lokacin harda zagi da cin mutunci, sai dai ya kada kai kawai ya wuce,,

  da sanuwansa ta nufi rugar tasu shanayen, zasu taso da sauri suna maka masu sanda, shidai Ali yajasu zuwa nasu wajen, inda zai shiga dasu yana gyara musu wajan cin abinci da zuba musu sabon ruwa,,

   itama ummeetah data shiga ciki ta ije goran zata zo tana tayashi, wata lokacin lamido abokinsa yaxo yana tayashi, wanda daga shie sai liman din garin, banda su biyun nan babu mai kaunarsa shida diyersa, yen uba duk sun gama bata mishi suna da cewa shie maye ne, ba don komai ba, sai don hassadar tarin dukiyar daya fisu,,

   hakama cikin gidan gaba daya kanni da yayyi, matayensu da yeyeyensu, sun sa musu kahon zuka, harda babbar yayarsu dake zaune a gidan, lamiso wacce duk wani rashin mutunci na cikin gida ta iyashi, yayin dana waje shi kuma kaninta lado yafi kwarewa a fannin,,

   wata yer jinka naga ya nufa, wacce take gado yayi wajan mahaifinsa, babban dane ya kamata ace ya gada dakin, amman saboda son da mahaifin yake mishi, yasa ya barma shi Alin gadon dakin, da wasu dukiyar masu yawa, wanda ya karasa kyashi da hassada a zuciyar yen uwan nashi,,

   Lado ya futo daga nashi turakan, matarsa biye dashi, karo yayi da fuskan Ali dake kokarin bude yer dakin jinkan dake kusa da nasu, wani mugun harara ya sakar mishi, kafun ya tara uban yawu yana tsitta mishi, kadan ya rage bai sameshi ba, itama matar tana hararansa suka wuce, bayi da abin yie, daya wuce ya numfasa tare da bude yer dakinsa ya shige,,

   sanda yayi alola kuma can ya hangi jummai itama kanwarsa ce, tana kibar ummeetah dake faman dumursu a kasa tana kuka, bashi da abun yie a nan ma, magana ma bata lokaci ne, dole ya wuce masallacin ko ya rasa jam'i,,

  daya idar ya shafa addu'a zai dawo, nan bakin dakin zai sameta tana rera kuka, inhar ya dawo ya samu ummeetah bata kuka to ta tafi dandali, shi kuma baya son tana zuwa can, amman tabbas zai futa ya dawo to zaizo ya tarda an kibeta,,

   shi yasa kullum gefen yer katifansa ledan gyadane aya da sauransu, data fara kuka ya lallasheta ya bata, wani lokacin yana mata karatun da tun bata fahimta harta koma fahimta, shine mahakurci mawadaci, wannan shine rayuwan da sukeyi a cikin rugar tasu mai cike daban tausayi.  

   lokaci kankani suka zama good friends shida sadeeq, sun shaku da juna, indai zai wuce, saiya tsaya sun gaisa, shikuma ya hadashi da nono, wata lokacin harda fura zai taho dashi ya bada akai ma ummansu, tuni maami itama tasan da zamanshi, don indai sadeeq din zaije Abuja ya dawo sai ya taho mata dashi, sakon bafullatanin da kullum take sama albarka, har tana burin wata rana ya kaita su gaisa.

  Abokan takansu ta kara kwari, lokacin da maciddo yaron Baffanta lado suka dilmiyata tsakiyar rafi suna wasa, ummeetah ta rika shakewa tana kasa kasa, tsoro yasa suka gudu suka barta,

Please Login or Register in order to submit comment