Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fadin,,

kayi hakuri, ya numfasa da fadin,,

kexam bama hakuri, basan kin dau abin serious ba lokacin, dana tsaya na miki bayani, but am not in the mood that's why, plss stop this crying, ya fadi hakan yana wani irin murza mata tafin hannunta, kasa tayi da kanta tana runtse ido, mikewa tsam yayi da fadin,,

tashi ki shirya muje hospital, musa mishi za tayi ya mata wani kallo, yana kokarin ya taimaka mata ta mike,,

ahhhh, shine abin data fada tana dafe mararta, da sauri yake fadin,,

what's wrong?, bata masan sanda tace,,

marata zai fashe, sai lokacin ya lura da stain din dake jikin bedsheet din, wato shine dalilin daya sa taki mikewa tun dazu, itakam yana kokarin tayar da ita gaba daya ciwon marar ya dawo mata sabo,,

bayin dake dakin ya nufa, shap shap ya hada mata ruwan wanka, ya dawo yana cire dark green suit din dake samar farar, yana nannade longsleeve din hannun rigan, ya kariso inda take,,

ya taimaka mata har bathroom, duk wani kaya da suka dace shi ya mika mata, hardasu pad daya gani cikin safe dinta, duk da halin ciwon da take ciki, bai hanata jin kunya ba, ta dai samu ta fara wanka dama shi take bukata, kota gasa mararta daya rike.

ta futo wankan tana dingisawa daker, harta da pillow ya sanja musu riga komai need, kunya ta kuma jie, tana jin wani nauyi data sashi hidima haka, bisa gadon ta zauna tana dukunkunewa cikin duvet, sanda wani sanyi ke ratsata, rike da cup bisa soccer dinshi ya dawo, sai yer karamar tea spoon din dake hannunsa, turiri kawai ke tashi cikin cup din,,

tashi kisha, kafun muje hospital din, kar yaxo suce za suyi miki allura, ba musu ta mike zaune tana jan blanket har wuya, bebi takan wannan ba ya zauna kusa kusa da ita, yana mika mata hot coffee din daya hado mata, cike da kunya take amsa, harta kammala sha idanunta na kasa, murmushi yayi wani lokacin kunyanta yana burgeshi, ta marairaice sanda yake ije cup din bisa side drower, da fadin,,

don Allah Baffah karka kaini wani asibiti, tayi kasa da kanta sosai ciki ciki take fadin,,

nasan abin daya samun zazzabi, kuma this time bansha magani ba, plss ka bari ina dashi, dana sha zan samu sauki in sha Allah, yana son yanda ta iya bayani dallah dallah, ya dan numfasa da fadin,,

ouk, yanxu ina drugs din suke?, side drowern dake kusa dashi ta nuna mai da fadin,,

kamar yana na kasa, ba bata lokaci ya bude drowern yana fito da kayan da duka suke ciki, can ya ga drugs din, daukawo yayi yana maida kayan dake ciki, harda wata yer memo hardcover na biki, bisa tsautsayi yana maida memon wata farar plane sheet ta fado fara sol, amman jikinta ya nuna alamar tsufa sosai,,

da mamaki yake daga takardan da akai folding, jie yayi yana son ganin abin dake cikin takardan, ba bata lokaci ya soma kokarin budewa, dago kanta tayi dake kasa, karaf idanunta suka sauka kan hannunsa, dake kokarin bude papern, a razane take fadin,,

NO!, ta yunkuro a rude tana rike hannunsa, a hankali ya juyo suna fuskantar juna, ya kasa gane ko menene dalilinta nayin haka,,

lafia?, ya jefa mata tambaryar looking so suprise, hawaye ke sauka bisa kucinta, murya kuka kuka take fadin,,

Baffah don Allah karka bude, plss na rokeka, sirri nane a ciki, yayi dan shiru kafun yace,,

sirri kuma, wani irin sirri ne wannan?da kukanta mai cike da shagwaba take fadin,,

Baffah nidai na rokeka, don Allah ka rufa mun wannan asirin, shiru ya kuma yi da kara shiga halin mamaki, kafun ya juya yana cigaba da kokarin bude takardan, bisa mamakinsa, saiji yayi ta kuma yunkurowa tana mannewa da jikinsa ,tare da ruko papern tana saka wani sabon kukan, da faman rokanshi karya bude,,

wannan karon tsoro abin ya bashi, yana mai dimbun mamakin abin dake cikin takardan, ya sauke idanunsa a kanta, yana kallon yanda tayi wurgi da duvet din, ga towel din dake kokarin kwancewa har jikinta ya bayayyana, amman ita wannan bashine damuwan taba, tana rike da takardan, dayan hannuta kuma nakan nashi,

duk kunya irin na ummeetah, toh har meye cikin paper, ya ayyana hakan da zurfafa tunani, wata zuciyar na raya mishi ya ije mata kawai abinta, yayin da shaidan kuma ke shigo mai da wasu kalolin wasi wasi, ya numfasa yana fadin,,

toh sakeni in ije miki, ba musu ta sakar mishi papern, sai lokacin ta lura da jikinta tayi saurin jawo towel din sama, tana kuma daurewa, dai dai sanda ya dan duka zai maida mata cikin drowern, kawai sai gani tayi ya kuma dagowa, tare da bude takardan kai tsaye,,

ya zaro ido da mamaki sanda yayi karo da hand writing din mahaifin nata,,

bude ido yakeyi yana runtsewa, abin kaman a mafarki yake mishi, kafun ya fara tattaro dukkan kalaman dake cikin papern, yana karantawa,,

*_Amincin Allah ya tabbata a gareki yake diyar Affahn tah, na rubuta miki wannan takardan ne, saboda a duk sanda kikai wayyau, ya zama shaida wajen tabbatar miki da abin dana fada miki, na bama Baffanki sadeeq aurenki, don haka kin sani shi matsayin mijinki yake, kiyi mishi biyayya, nasan zai rike ki tsakani da Allah bisa amana, kuma har abada bana fatan auranku ya rabe, kimun alkwarin zaki zauna dashi, sannan ki sanya shi farin ciki, Allah miki albarka, innar Affahn tah._*

Ana wata ga wata, Matatace fans, next week in sha Allah zan fara removing duk wadanda basa comment, da yardan Allah, my commenters ina godiya, da addu'oinku, much fatan alkhairi.



comment
share
vote


*matatace 2019*
Na meemartjj
[14/08, 14:29] Dala Grp: 🕯🕯🕯
*MATATACE*
🕯🕯🕯

story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@MeemartjJ

*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty Ummeetah any my Fa'ixation._

page 39~40

__________Tsaf ya kammala karantawa, da wani mamaki yake kallonta data daskare waje daya, yana jefa mata tambaryar,,

*Umeetah dama kinsan nie mijin kine?* luwww tayi tana komawa ta kwanta bisa pillow da rushewa da sabon kuka, ta saka tafukan hannunta duka biyun tana kare fuskanta, kuka take sosai, shikam ya juya ga takardan yana kara maimaita karantawa,,

gaba daya sai yaji wasu kwalla sun cika mishi ido, a zuciyarsa yana raya,,

lallai Aliyu sai abarshi, bai taba tunanin dibaransa yakai har haka ba, shin dadi zaiji ne ko akasin haka ma, wani murmushin farin ciki ya samu kanshi da saki, yana kuma bin abokin nashi da addu'a cikin zuciya, kafun ya maida takardan yana ijewa bisa side drower, sannan ya juyo da kallonsa gareta, har lokacin shashekar kuka take, da hannunta bisa fuska, gaba daya sai ta kara bashi tausayi, lokacin da wani abu game da ita ke kara samun matsuguni a karkashin zuciyarsa,,

rankwafowa yayi dai dai saitin fuskanta, a hankali yasa hannu yana zare nata hannun, ya zuba ma fuskanta ido, kaman yaune rana na farko daya fara ganinta, itakam idanunta na lumshe sai hawayen dake sauka akan fuskanta, tana sauke a jiyar zuciya irin na mai kuka, so cool ya kira sunanta,,

ummeetah, ummeetah bude idonki muyi magana, sai data dauki wasu yen seconds, kafun ta bude idon da suka kankance don kuka, da fuskanshi tayi karo, ga kirjinsa kaman zai taba nata, sai kawai ta kara fashewa da kuka tana fadin,,

Baffah don Allah kayi hakuri, nidai babu ruwa nah, Affah ne, don Allah ka kyalle wannan maganan, Allah nie bana son na zauna matsayin matarka, ni nafi son na zauna a yer kace, plss yhu my uncle not my husba......,,

shishshshsh, shine abin da yayi saurin datse mata magana, da daura manunin yatsanshi bisa soft lips dinta, tayi shiru tana cigaba da shashsheka, kallo kawai yake binta dashi, sai yanxun ma ya kara jin yana matukar son auran nasu, ga wani irin feeling yake jie game da ita, da sauri ya janye yatsanshi, ya mike sosai, yana jawota itama ta zauna,,

wani sabon kukan ta saka, tana wani irin narkewa, zata kara komawa kwancen da take, sosai yasa hannunsa ta bayan kugunta yana rukota, ta zauna da kyau, amman idon nan a rufe tana faman zabga kuka, bama tasan halin da take ciki ba, fuskarsa sosai yakai kusa da nata yana tallafo kuncinta,,

kuka take tana masa magiyan ita bata son ta zauna matsayin matarsa, duk yanda yaso ta natsu tayi shiru ya gagara, ya zuba mata idanu kawai yana kallonta, a hankali yakai nashi fuskan kan nata, yasa kuncinsa yana wani irin bin fuskanta da shafa, ya sauko har saman labbanta masu dan kauri kasa daurewa yayi ya hada bakinsu waje daya,,

tsamm tayi lokaci daya ta dauke wuta, jin wani bakon al-amarin dake wakana, yana jin tana mutsu mutsun kwacewa, amma yayi mata ruko mai kyau, dole daga baya natsuwa tayi,,

daker ya iya tattaro wata natsuwa sannan ya zare bakinshi da bude idanunsa a kanta, idanunta a lumshe suke suna kallon kasa da zubda hawaye, duk sai yaji wani iri, cikin tafin hannunsa ya kamo fuskanta, yana share mata hawayen da yen yatsunshi, wani sabon kukan take shirin saka mishi, yayi saurin dagowa yana toshe bakinta da hannunsa, sosai ya natsu kafun yace,,

ummeetah plss kie natsu mana, kodai ban isa nace kiyi shiru bane, tun yanxun mun fara kenan, biyayya da Affahn yace kiyi mun kenan?da sauri ta girgixa kanta, idonta a rufe tana fadin,,

kayi hakuri, ya numfasa da fadin,,

ouk bude idonki muyi magana, daker ta iya budewa, har yanxun da kuka a cikinsu, sai dai ta kasa hadawa da nashi,,

Baffah plss karka mai dani matarka, ta karisa fadan hakan da dire idanunta a nasa, maganar ta zo mishi a baxata, yana fadin,,

kamar yaya?shiru tayi tana kallonsa, kafun tayi kasa da idanuwanta, ya kuma tallafo fuskanta da fadin,,

come on yie magana mana, da hawaye sharashara ta dago tana fadin,,

nidai bana so, bana son wadannan abubbuwan plss......, ta kasa karisa maganan, tana dukar da kanta, da kokarin ture hannunsa dake ta bayanta, idanunsa yakai gun na wasu yen seconds, kafun ya sassauta rikon da yayi mata, kaman zai basar da maganan sai kuma yace,,

me yasa kikace baki so?, kanta na kasa tace,,

nidai kawai banso, auntyn mu da maami sunce yin hakan bashi da kyau fa,,

what, ya fada yana zaro ido da mamaki da fadin,,

keee, nifa mijin kine karki manta, sai data runtse idonta kafun tace,,

ehh, nidai haka aka fada mana, kuma nima bana so, ta karisa maganar da sigar kuka, a zuciya yake raya,,

lallai yarinyan nan da sauran kie, janye hannunsa yayi yana gyara zamansa da kyau, da fuskantarta so serious yake fadin,,

toh kie natsu kie bani hankalin ki nan, nima don kina kuka ne, shi yasa na miki haka don kiyi shiru, saboda ina son muyi magana na fahimta ni dake, zamanta ta gyara, ya taimaka wajen mika mata duvet ta rufe jikinta dashi, tana faman yin kasa da kai, ya dan nisa da fadin,,

dago kie kalleni da kyau, dago kai tayi amman taki hada ido dashi, shiru na wasu yen minutes kafun yace,,

me yasa kikace baki son zama a matsayin matata?, ta share hawayen dake dada gangaro mata da fadin,,

kawai nie bana so, kai da uncle dina ka dace, murmushi yayi yana shafar sajensa yake fadin,,

nayi tsufa da yawa ko?da sauri ta girgixa kanta tana kallonshi da fadin,,

a'ah, ba kayi tsufa ba, Baffah kaine ka rikeni tun ina yarinya shi yasa, kuma kaga aunty suhymah bata son kishiya, bana son ku shiga damuwa saboda nie, Affah bai son da wadannan matsarba shi yasa ya hada auran nan, idan akwai maganar data bata maka rai kuma kayi hakuri, shiru yayi yana nazarin kalamanta, kafun taga ya mike tsam, kusa da inda take zaune, ya duka bisa kafufunsa, tare dakai hannu yana kamo hannunta dake ta waje, kallonta yake, itama saita rika binshi da ido, bata san mezai biyo bayan abin data fada ba, ya dan numfasa kafun ya fara fadin,,

ummeetah ina son kie sani, nima sanda na tsinceki matsayin matata, kasa yarda nayi, na kasa fahimta, kinsan me yasa?girgixa kanta tayi alamar a'ah, ya nisa da fadin,,

saboda ina ganin kaman kinmun kankanta, ko bai dace ki zama matata ba, amman yanxun na lura kece mace wacce tafi dacewa da rayuwa nah, wacce tasan hakkin dan adam, ummeetah bazan iya rabuwa dake ba, koda ace ban daukar ma mahaifinki alkwarin zan rike kie da amana ba, bazan iya rabuwa da matar kirki irinki ba, dake nake son na zauna kuma na rayu har abada, ina fada miki wadannan ne straightforward daga zuciya nah, don haka kie manta da maganar baki son zama matsayin matata, kisa a ranki cewa ke *MATATACE* nie kuma Abubakar sadeeq mijin kine na har abada, wani kukan take shirin sakawa da fadin,,

aunty suhymah fah, bana son shiga tashin hankali, dan tsaki yayie da fadin,,

manta ta kawai, a'i kinga maamin mu nada kishiya, kuma itama hakuri tayi, don haka dole itama tayi hakuri ku zauna tare, yayi dan shiru kafun yace,,

ummeetah don Allah ina mai baki hakuri akan rayuwan da kika tsinci kanki, plss kie yafe mun, bana so nake ganin ki a wannan matsayin, nima bansa me yasa nakeyin haka ba, ya karisa maganan cike da ban tausayi da sauri take fadin,,

nifa Baffah bakamun komai ba, na yafe maka koma menene, idanu kawai ya zuba mata yana murza yen yatsunsa a nata kafun yace,,

nagode, nagode sosai yer albarka, ina son rokanki wani alfarma, ina son sai bayan suhymah ta haihu, zamu zauna akwai maganar da nake so ta sani game dake wacece?, da kuma matsayin kie a wajena, kinsan halinta, nie kuma bana son tashin hankali, bana son na rasa gudan jinina, da hawaye dake cigaba da kwaranya take fadin,,

nie Baffah bana son ma ta sani kwata kwata, bana so ku daina rayuwan farin ciki saboda nie plss ka yarda nidai kawai......,,

shishshshs, ya fada da daura yatsanshi bisa lips dinshi, kafun ya sauke yana fadin,,

plssss, kie daina fadan wannan nidai din, ummeetah kie hakura mu zauna da juna, matsayin mata da miji, ko shin ba zaki iya mun biyayya bane, da Affanki, shima ba zaki daure ki masa biyayya ba, matsayinsa na wanda ya tsayu a rayuwa don son ganin rayuwanki ya inganta, wani kuka ta saka mai cin rai tana fadin,,

na daina Baffah, baxan kara ba, na hakura zan zauna, wani farin cikine ya lullube rayuwansa, ya mike tsam yana zama kusa da ita, da fara rarrashinta, yana son ya rungumeta, amman ya lura kwata kwata bata son yana taba ta, kuma ita bata san wannan karatun ba,,

dole a haka ya rarrasheta, ya share mata hawaye, tare da taimaka mata tasha magungunan, ya fiddo mata da kaya mai dan sauki da zata sanya taji dadi, kin saka kayan tayi, dole ya fice kusan 10minutes kafun ya dawo ya sameta,,

sanye da kayan harta soma bacci, ta kudundune kanta da duvet, ga zufa data fara hadawa, yaye mata duvet din yayie, ya duka a hankali yana kissing saman giran tah, sannan ya mike, kusan 5minutes ya dauka yana kallonta, kafun yabar dakin yana jawo mata kofa.


Baisan dalilin da yasa ya tsince kanshi a farin ciki ba yen kwanakin, harta matarsa sai data lura ta tambayeshi, amman shi kanshi baisan amsar ba, shi dai yasan abin daya samo ya fada mata.

bangaren ummeetah kuwa, sai da taji bakin cikin ganin takardan da Baffanta yayi sosai, wanda kullum take boyewa, tsawon lokacin da Baffanta lamido ya kawo mata har islamiya, sanda ta cika shakara goma shashida dai dai, ya kuma sanar da ita Affanta ne ya rubuta, ya kuma ce ya bata sanda tayi wayau sosai, duk da daker ta iya gane Baffan nata lamido, bai hana ta gane rubutun Affanta ba lokaci daya,,

hankalinta ya tashi sosai, don zuwa lokacin tasan me ake nufi da aure, hakan ya tabbatar mata da abin daya fada mata a wacan lokacin da karancin shekarunta, bata kuma tabbatarwa ba sai randa Baffanta ya dawo kasan, a dakin muheet, duk da bata cikin natsuwanta, kuma bai karisa ba, amman taji sanda yaso yayi katobaran fadin ita wacece a gurinsa,,

wannan ya kara taimakawa wajen sata kuka sosai a ranan, haka kawai ita dai bata son auran, tana matukar ganin girman Baffanta, tayaya za'ace ya zama mijinta, a wannan karon ma dai damuwarta kenan, gashi shi yanda ta lura yana matukar son auran nasu, tattalin da yake nuna mata ne, da tarairaya a ciwon da tayi na yen kwanakin, yasa ta kara shiga halin bakin cikin ganin papern da yayie, itakam bata son wanga harka.

£££

.........Barayin munat kuwa sun samu maslaha, barr. Abdullah tasa ya kira yayanta yayi mishi bayanin halin da ake ciki, haka kuwa yayi sun jima suna waya suna tattaunawa, yace subarshi da mummyn, gefe daya kuma yana kara mamakin kishi irin na suhymah, bama ita za'a mawa ba amman ta shiga ciki tayi tsage tsage, ita daya kamata ta taya yer uwanta farin ciki ta samu mijin aure na kwarai irin Abdullah, shine za taje tana tare ma duniya,,

Allah shi kyauta, shine abin daya fada, kafun yayi dailing numbern mummy, sun dan tattauna, lokaci kankani sai gashi ta sanja ra'ayi, harda cewa ita Abbansu takeji, don baice komai ba game da magana, shima wannan cewa yayi tabar mai za suyi magana, tom barayin Abba daima ba wata matsala, aka dai samu aka shawo kan magana sanda aka fara shirye shiryen tsaida lokaci.


***

sosai taji sauki, sai dai kuwa ta gaji da zaman gidan, kewar karatunta takeyi, gashi a gabanta wacan lokacin kafun su taho yace ma maami zata cigaba, kusan watanni nawa kenan suke shure amman shiru......,,

kamshin turaransa ne ya katse mata tunani, ta bayanta take jinshi yana karisowa inda take, cikin kitchen din, da take gaban gas cooker tana gogewa, ta juyo kenan yana tsayawa daf da ita, shirye tsaf cikin shigan zuwa office, danja da baya tayi tana gaisheshi, yayi dan murmushin da mamakin wannan halin nata, kafun ya amsa mata yana dorawa da fadin,,

matata nie zan tafi wajen a'iki, sai na dawo, ya fada with full confident, itakam bata son wannan sunan, ya zatayi, hakanan ta kakalo murmushi da fadin,,

tom saika dawo, Allah ya kaika lfy ya dawo da kai lafia, Allah ya bada sa'a akan abin da akaje nema, murmushin jin dadi yake da dan jan kumatun yana fadin,,

thank yhu so much, shi yasa nake son zuwa in miki sallama, kinsan saboda me yasa, girgixa kanta tayi a hankali, yayi wani murmushin da fadin,,

saboda in samu wannan kyakywar addu'an naki, hope babu wata matsalar, dan shiru tayi kafun tace,,

Baffah dama school..., cak ta tsaya da maganarta ganin yana duba wrist watch din hannunsa, alamar duba lokaci, kafun ya dago da fadin,,

umm hmm, ina sauraranki,,

kaje kawai kar kayi late din office, ta fada cike da kulawa, yana son halayenta da yawa, gyara tsayuwa yayi da fadin,,

ouk, idan na dawo zamuyi maganan, karki manta fa, kona manta ki tuna mun, kanta ta daga almar toh, daga haka sukai sallama ya fice, da ido ta rakashi, kafun ta juya tana cigaba da a'ikinta.

Da wuri ya dawo office, lokacin suna zaune a falo tana ma Irfan assignment dinshi, shima zama yayi suna mishi sannu da zuwa, ya amsa musu a gajiye, Irfan ya mike yana nadewa kan jikinshi, da zuba mishi surutun nashi na fama, itakam mikewa tayi ta nufi fridge, goran ruwa ta dauko mai sanyi tare da cup, ta dawo da zuba ruwan tana mika mai, harya amsa ya kalleta da fadin,,

kai, na manta fa am fasting today, thanks for ur job, ya karisa maganar da murmushi yana mika mata cup din, amsa tayi itama da fadin,,

ohh, ya mike da fadin,,

bari naje ciki, oya continue with ur homework, ya karisa maganar da dire Irfan a kasa, tare da wucewa bedroom dinsu kai tsaye, maida ruwan tayi ta dawo tana cigaba da yinma Irfan homework dinshi, lokaci lokaci kuma ta kosa ya futo don suyi maganar makarantan tah, ta dan jima kafun taji yana kwalla mata kira,,

Humaira, da sauri ta mike tana amsawa, a bakin kofan ta tsaya tana jera sallama, yace,,

shigo mana, ba musu ta shiga, yana zaune can gefen gado, sanye da wata black trouser, sai wata farar singlet, kanta kasa ta isa inda yake zaune dan nesa dashi tana fadin,,

Baffah gani, kallonta kawai yakeyi, shi bema san ta inda zai fara cire wannan nauyin nashi da take jiba, wata zuciyar na rayan masa,,

sabar mata za kayi, wani irin sabar mata, yarinya bata san komai ba game da aure, akwai gyara a lamarin ummeetah, dan tsaki yayi yana fadin,,

matso mana kin tsaya can nesa, karisowa tayi tana kokarin zama bisa kasan gadon, yayi saurin ruko hannunta, da ido yake mata alamar ta zauna bisa gadon, ba musu ta zauna, har lokacin kanta a kasa, ya dan nisa da fadin,,

ina jinki, daxun mun fara magana, meye matsalarki?dago kai tayi da fadin,,

Baffah dama maganar makaranta ne, plss ina son in cigaba, both boko da isalamiya, shiru yayi kafun ya dan sosa bayan kanshi da fadin,,

amma isalamiya nasha a'i kunyi candy?, kai ta dan girgixa da fadin,,

a'ah, muna class 5ne zumu 6 na futa, akwai kuma most littafan da aka fara mana ba'a gama dani ba, ta dan daga kai sama tana faman lisassafawa da hannu kaman an tambayeta take fadin,,

akwai hadith, seera sai fiqhu, dama wasu kuma duk ina son in kammala su, yana kallonta, wata lokacin har mamakin surutunta yakeyi, yace,,

shi fiqhu a ina aka tsaya muku?kai tsaye take fadin,,

amm, karkasuwan jana......, cak ta tsaya da maganar tana kallonsa, ya karisa mata da fadin,,

karkasuwan janaba right?dan girgixa kai tayi da sauri, kafun tace,,

a'ah na manta bamu kawo nan ba, nama manta inda aka tsaya mana, kallonta yake da mamaki, da wasu kalolin tunanin, kafun ya dan tabe baki, yana cigaba da mata wasu tambayoyin da suka shafi sauran littafan, ajiyar zuciya ta sauke da taji ya saki wancan zancan, sosai suke tattaunawa, tana mamakin irin ilimin da yake dashi, amman wata lokacin yake wasa dashi,,

taji dadi sosai daya ce zaya sasu islamic school ita da Irfan, sannan maganar makarantanta har an kammala komai, zata fara zuwa wata high school dake gaban nasu Irfan, sai dai nasu tsarin karatun ya banbanta da wanda ta gama can gida,,

murna ta rikayi tana mishi godiya, kafun ta mike ta nufi hanyar futa, cak ta tsaya kuma tana juyowa da kallonsa, jin yana faman jero tsaki, kanshi na kasa ya dafe da yen yatsunsa, yana dan murza saman giranshi,,

Baffah me kuma ya faru?ta jefo tambaryar kai tsaye, dan dagowa yayi yana kallonta kafun yace,,

nothing, murmushi tayi tana juyawa, sai dai bata cigaba da tafiya ba, a zuciya take raya,,

shidai mutum kullum bashi da a'iki saina tsaki, kerere ya tsaya yana kallon yanda ta kie tafiya, ita batai gaba ba ita batai baya ba, sai kuma ta juyo da kanta tana kara kallonsa da mamaki yake fadin,,

lafia?ta juyo sosai tana fadin,,

kawai dai naga kamar akwai abin da kake nema ne, shiru yayi yana juyawa da kallonsa kan safe din data site daya yake a wangale, ya dan nisa yana taba fuska da fadin,,

wata white shirt dina nake nema, mahadin wannan trouser, tace,,

wannan botton down din mai short sleeve,,

eh shi, kai tsaye ta wuce wajen safe din, wasu yen sakwanni, kafun ta juyo rike da rigan, mamaki yake sosai, duk da itace mai shirya musu kayan, amman ba inda bai nema ba, har suhymah yace jiya ta dubo mishi, ta gama sukurkuta kayan tace bata gani ba,,

wow thanks, na nemeshi sosai ban gani ba, ya fada da murmushi, itama murmushin tayi tana mika mai da fadin,,

kayi hakuri nina sashi can kasa shi yasa, yasa hannu yana amsa da mata wani irin kallo, kafun yace,,

ba zaki karisa ladanki ba kisamun, zaro ido tayi waje, yana kokarin ruko hannunta, ta sakar mishi rigan da sauri ta fuce, yer dariya yayi yana rakata da kallo tare da sanya rigar, gaban mirror ya karisa yana karisa saka botton din rigan, tare da kara gode ma Allah cikin zuciyarsa, daya bashi ummeetah matsayin matar aure.

***
Kaman wasa saiga ummeetah a makaranta, tayi farin ciki sosai, don makarantan na yaran masu dashi ne ko a can, ba kuma laifi tana gane karatunsu, sosai ta maida hankali, bangaren islamic ma ya sasu, sai dai da nisa ne, so uku suke zuwa a ko wani week.

kullum shike direta school, dama matar gidan takan riga kowa futa, sai Irfan dake bin school bus dinsu, sai ita dashi a karshe, ranar farko tare suka shiga ciki a kammala komai sannan ya tafi.

yau kuwa a farfajiyar school din ya sauketa, ta nufi katon

Please Login or Register in order to submit comment