Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

magana yayi kawai yana binta da ido, kafun kuma ya dafe kanshi da fadin,,
  
    innalilah wa'inna ilaihir raji'un, da sauri ta juyo tana kalonshi, kafin tayi ajiyar zuciya tana barin wajen, dai dai nan matar gidan ta shigo, da ido tabi ummeetah dake gama shigewa daki, kafin ta matso kusa dashi tana fadin,,

  sweetheart, daker ya iya dago idanu, bai amsa mata ba, ganin yanayinshi kawai sai tayi shigewarta daki, duk tunaninta donta dawo late ne yake daddaurewa, shikam shi yasan me yake jie.



                           ***
   Sosai dare ya tsalla, banda tsitttt ba abin dake wakana, idanunsa sun gagara bacci, tabbas yana ciwo a cikin jikinshi, kuma yana da damuwa, to wazai fada mawa yaji sanyi, dubansa yakai kan matarsa dake shirga baccinta hankali kwance, yayi dan tsaki yana juyawa, yana son zuwa wajen ummeetah amma kuma baya son ya daga mata hankali, can dai daya gaji da kwanciyar mikewa yayi yana barin dakin.
 

    Tura kofan yayi da sallama, a sujjada ya sameta bisa dadduma,   waje ya nema ya zauna yana zuba mata ido, duk sai yaji ta kuma shiga ranshi, ta dan jima kafun ta dago, yana kallonta harta idda tayi sallama, shafa addu'a kawai tayi tana mikewa, da damuwa sosai take fadin,,

    Baffah sannu ya jikin, dan murmushin yake yayi yana fadin,,

  Alhamdulillah, ya daura da fadin,,

   plss zan samu wajen kwana?

  eh, ta fada tana dada gyara pillow kan gadon, duk da a gyattan da suke, ya kwanta sosai yana fadin,,

    zomu kwanta muyi wata magana, a dan razane ta zaro ido waje,  yayi dan murmushi yana fadin,,

   come on, ba wannan maganar bane, zo mana yer fillo nah, sauke wani numfashi tayi tana fadin,,

   to bari na cire hijjabi, ta karisa maganar da rawan murya, yana kallonta ta cire hijjabin, wata yer sleeping vest ne a jikinta, sai zanin data daura, lumshe idanuwa kawai yayi, har sanda ya jita cikin kakkaurar blanket din, ya sauke ajiyar zuciya lokacin da yake jawota jikinsa, sosai ya mannata da jikinshi, kamar baisan a rabasu, yanayin sanyin garin ne ya soma dibarshi, kasancewan har snow ya fara sauka kadan kadan, cikin rawar murya yake fadin,,

   A'isha ina da damuwa fa, duk da abubbuwa da yake mata suna sanya zuciyarta cikin tsoro, bai hanata dakewa ba tana fadin,,

    Baffah wani irin damuwa ne, ka fada mun komai yayi tsanani yana tare da sauki, a hankali numfashisa ke sauka, lokacin da take jiyo heartbeat dinshi dake bugawa da sauri da sauri, sosai yaji dadin kalamanta yana fadin,,

   Humaira ina tsoron wani abu ya faru, bana son rabuwa dake, basan wanda zanbar ma amanarki ba, bana son nayi wasa da amanarki da Affanki ya bani, ummeetah ina da buri sosai akan naga rayuwanki ya inganta, plss kie fada mun mezan yie, zuwa wannan lokacin hawaye ya gama wanke fuskanta, cikin muryan kuka take fadin,,

   babu abin dazai faru in sha Allah, nie ka gama mun komai a rayuwa, don Allah ka daina cewa haka, kara sauke numfashi yayi, yana dada jawota jikinshi, kafun ya cigaba da fadin,,

   ummeetah ya zama tilas in fada haka, saboda yanda nake jie a jikina, na boye mikine, amma maganar gaskiya duk zuwa asibiti sun duba lafia na sunce qlau nake, kirjintane ya kara bugawa, tana karanto addu'a da dama, tana jie yana cigaba da fadin,,

   duk wani bincike ya nuna lafiya na lau, amma a jikina fa inajin ciwon, Humaira bana so……...,, 

   da sauri ta dago kanta tana hadawa da nashi, bata barshi ya karisa fadan maganar ba, tasa hannunta tana toshe bakinshi da hawaye take fadin,,

   plss ka daina, in sha Allah ba abin dazai faru, kanta ta girgixa mai alamar bata son yana fadan haka, kasa daurewa yayi ya hada bakinsu waje daya, itama batayi sanya ba ta biye mishi, don bata son ganinshi cikin wani damuwa, sai da labari kuma ya sauya idanunta suka furfuto, jarumta tasa sosai, sukai rayuwa mai inganci, duk da ta dan fada ma jikinta.

  sosai ya samu wata natsuwa yana faman shi mata albarka, har wani bacci mai cike da ni'ima ya daukeshi, tashi tayi ta daura zaninta, gaba daya gobobinta ciwo suke mata, a haka tayo wanka ta tsarkake jikinta ta futo.

   towel ne a jikinta, sai wani data rufa dashi tana gogge jikinta, daga inda take tsaye ta zuba mishi idanu, a hankali ta karisa ta bayanshi, kuma gyara mishi blanket din tayi sosai, tare da zama gefenshi tana dan rankwafo da kanta ta saman kanshi.

   sosai take kallonshi, murmushine mai hade da kuka ya subuce mata, taji dadi data taba jikinshi taji ya rage zafin, sai kuma ta toshe bakinta dake neman fidda sautin kuka, mikewa zaune ta karayi da kyau tana daga hannunta sama kamar zatai addu'a, sai kuma ta dan shiga yarfa hannu, addu'a kawai takeyi masu dimbun yawa da alkhairi cikin zucinta.

    komawa tayi tana dan kwanciya a bayanshi, yayin data jingina kanta da allon gadon, kafadarta kuma na bisa pillown daya tada kanshi dashi, cikin natsuwa ta sanya hannuta ta saman kafadarsa, tana rungumo kanshi samar kirjinta sosai, kamar wani zaya kwace mata shi, tare da saka dayan hannun tana shafa sumar kanshi a hankali, sosai take kallonshi da nazarin wasu abubbuwa.

   tabbas tana jie a jikinta wannan ciwon nashi, na da nasaba da shigowa rayuwanshi da tayi, kusan kimanin shekaru 8 da suka wuce kenan, amma abin ya kasa barin kwakwalwanta, kusan abin daya faru kenan da Affahnta, wata ranar da suka dawo kiwo, shima dai dai kofan dakinshi yasa wata kara yana dafe kai, wanda a ranar itace ta taimaka mai ya shiga dakin, tun daga rana mai kama ta ranar bai kara samun wani sukuni ba, harya bar gidan duniya,,

   iri daya da ciwon Affah ne, ta fada murya kasa kasa da kuka, duk da karancin shekarunta ba zata manta lamarin ba, bakinta takai bisa saman kanshi tayi kissing so lightly, tana fadin,,

   in sha Allahu Baffah nah ba abin dazai sameka, in sha Allah, kukan zuci take mai kuna, kafun wani bacci barawo ya tafi da ita.

     

    Asuban fari ya farka, da hannunta yayi karo da taimai kane kane dashi, murmushi yayi yana juyowa a hankali, tare da zuba mata idanu, hancinta yaja ta dan farka da murmushinsa tayi karo, tayi saurin mikewa tana gyara towel din dake kafadarta, tare da fadin,,

    kayi hakuri, yace,,

    for what?dan shiru tayi kafun tace,,

   na danne……..., sai kuma ta kasa karisawa, murmushi yayi yana fadin,,

   kawo kunniki kijie, a hankali takai kunninta bakinshi, nidai naga ta fiddo ido waje, kafun ta sanya towel din dake bisa kafadarta, tana rufe fuska gagam, shikam dan dariya yakeyi, ita ta taimaka mai yayi wanka tare da tsarkake jikinsa, a dakin ya shirya, sannan sukai sallah tare.

 

   _plsss&plss, makarantar littafin *so ko wahala* duk mai wadannan pages din ya taimaka mun dasu, page 50,60,61, nagode._


comment
share
vote

*matatace 2019*
Na meemartjj
[14/08, 14:29] Dala Grp: 🕯🕯🕯
    *MATATACE*
          🕯🕯🕯
  

story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjj 

*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty Ummeetah any my Fa'ixation._


    _Wannan pages din nakune, matatace fans both 1&2, hakika ina ganin comment dinku da kuma tattaunawanku, kuna kokari matuka, don haka kuyi yanda kuke so dashi, ina yinku irin sosai din nan, da fatan Allah yabar zumunci, taku haleematu sa'adiya_


page 51~52

____________Shap shap ta kammala breakfast tare da shriya Irfan harya tafi makaranta, matar gidan ma ta futo shirye cikin shigar zuwa office, sai data yie gejin cikinta, kafun ta kara ma ma wadonta iska.

   shi kadai ya rage bai futo ba cikin bedroom din nasu da take jiyo motsinshi kadan kadan, waje ta samu ta samu bisa dinning chair tana zama, tare da zabga ma kofar dakin ido, can kuma ta mike kai tsaye tana lekawa dakin.

   bisa mirror stool ta sameshi zaune, ya dafa hannusa jikin dresing mirror, yayin daya dafe kanshi dake duke da hannun, sai da tayi sallama na uku, sannan ya dago firgigit yana kallonta, murmushin yake ya sakar mata, kafun ya mike shirye tsaf cikin shigan zuwa office, briefcase dinshi ya dauka tare da hada wasu yen takaddu, juyawa tayi zuwa falo kamar yanda shima ya biyo bayanta.

    tsaye take a dinning arean, tana dad'a gyara table din, ya kariso ya zauna tare da dire kayan dake hannunshi bgefe daya, agogan hannunsa ya dan duba yana dagowa da kallonta tare da fadin,,

   Humaira ya baki shirya ba, munyi late fa, ba tare data dago ba take saving dinshi breakfast da fadin,,

   eh, nie baxan jeba yau, da dan mamaki yake fadin,,

    saboda, ba exam kuke yiba?sosai ta zauna kujeran dake kusa da nashi tana fadin,,

   eh, amma dai bana jin zuwa ne yau, ta karisa maganar da nuna mishi agogon dake manne jikin bango da daurawa da fadin,,

   karfa kayi late din office, lokaci na kurewa, kamar bazai magana ba sai kuma yace,,

    Humaira kodai baki da lafia ne, sai naga kamar ina taya ki lau……, da sauri ta dago kai tana kyalla mishi idanuwa, ganin haka yasa yayi saurin fadin,,

   ah maida wukar, wasa nake miki, ajiyar zuciya ta sauke tana yin kasa da kanta, ya fara kokarin daukan briefcase dinshi da fadin,,

  toh nie zan tafi, da sauri tace,,

   baza kayi breakfast ba?dan yamutsa fuska yayi kafun yace,,

  kai barshi kawai, bana jin cin komai, kokarin mikewa yakeyi, tayi saurin ruko hannunshi, idanunsa yakai kan hannun nasu, sai kuma tayi saurin janyewa, shima sai ya fasa mikewan yana kallon fuskanta data marairaice da fadin,,

   Baffah plsss kacie wani abu mana, don Allah karka tafi office da yunwa, shiru kawai yayi yana bin hot breakfast din data hada bisa dinning table din, amma ba zata gane bane, duk yanda yanxun zaici abinci baya jin dadinsa, sai dai ya tura kawai, ita kanta ta lura ya rage cin abinci, ya fuzar da wata zafaffan huci, zaiyi magana ta shagwabe fuska da fadin,,

   plssss, abincin ummeelaton kane fa, baima san sanda wani murmushin dake dada kayatar da fuskanshi ba ya subuce mai ba, shima marairaice fuskan yayi yana fadin,,

  to kie bani a baki, ba tare data kara wani magana ba, ta debo fried chips din tana kaiwa bakinshi, murmushi kawai yakeyi yana kallonta.

   baima san yaci da yawa ba, sai da tace, abarshi haka kar yayi late din office, sai mamaki yakeyi, ta mike da sauri tana tattara mishi kayan daya futo dasu, shi kuma ya mike yana hamdala, kofa suka nufa, har yasa kafa zai futa tace,,

   addu'an futa gida, kallonta yayi sai kuma ta noke kafada tana fadin,,

   sorry na tuna maka ne, murmushi ya kuma yie yana fadin,,

  nogode kin kyauta, sai daya jero addu'an sannan suka futa, suna tafe yana tambayarta wasu addu'oin data sani ta fada mai, har wajen motarsa da mr. jerry ya futo dashi ya kammala goge mishi tas ta rakashi, tare da bude dayan site din tana zube mishi briefcase dinshi.
  
   zaune yake a mazaunin driver, kafa daya ciki daya na waje, ta zagayo tana mishi sai ya dawo, tafin hannayenta ya ruko sosai, yayi dan murmushi yana zuba mata ido, ganin yanda tayi kasa da kanta kafun ta dago tana fadin,,

   Baffah plss ka tafi, karkayi late din office, yafi 5minutes yana kallonta ita kuma tana kara fadin,,

   lokaci na kurewa fa, ajiyar zuciya ya sauke a hankali, kafun ya kara matse hannunta cikin nashi yana fadin,,

   Humaira bana son rabuwa dake ne, idan har muna tare sai inji gaba daya ciwon da nakeyi ya tafi, amma da zaran mun rabu sai inji ya kara dawowa, plss karki barni a rayuwa, ke alkhairi ce a gareni, idanunta ke neman tara hawaye, tayi saurin dakewa tare da kokari wajen fadin,,

   in sha Allah duk wuya ina tare da kai, duk runtsi da wani tsanani baxan taba barin ka ba, duk wasu iyaye na kwarai suna zabama yeyensu abin da suka san zai zama alkhairine a garesu, kaima alkhairi ne a gareni, Allah kuma zai baka lafia, kallonta kawai yakeyi cikin idanuwa, murmushin ban tausayi ne dauke a idanunsa, so cool yake fadin,,

   zanyi kewarki jarumar fulani tah, a razane ta dago kanta, ya bata wani big smile da fadin,,

   ina nufin zanyi kewarki cikin motana yau, dan murmushi tayi tana kasa da kanta da sauke wata ajiyar zuciya, kafun ta daure wajen fadin,,

   karka damu, in sha Allah duk inda kake tunanina, kulawana tare da addu'a suna nan tare da kai, yanxun dai kaje kaga kana kara yin latti, ta karisa maganar da dan dago kai ta kalleshi, hannayenta ya hada waje daya yana kaiwa bakinshi tare da kissing, sai kuma ya sauke yana dada kankame hannun, ta dan taba fuska tana fadin,,

  Baffah plss kaje karkayi late fa, kafada ya make da fadin,,
 
   a'ah, nidai saikin mun abin da zan kasa mantawa har in dawo gida, zare ido waje tayi, ya dan yastina fuska yana fadin,,

  yess, ki damun abin dazai rage mun kewarki mana, ya karisa maganar kamar wani dan baby, dariya ya bata, amma saita waske tana kasa da kanta, ta lura da gaske yakeyi, ganin lokaci na kurewa ya sanya ta zare hannunta a hankali, juyawa tayi da ninyar barin wajen sai kuma ta juyo, ganinsa tayi ya zuba mata ido.

   saukar tafukan hannunta kawai yaji bisa kuncinsa, ta tallafo fuskanshi da kyau, bai gama ankara ba, sai tausasan labbanta yaji saman nashi, wani lovely light kiss ta bashi tare da zare bakinta, idanunta a runtse suke, ta kuma kasa sakin fuskan nashi.

   zuciyarta na cike da tausayinshi, jin harta lips dinshi zafi radau suke, tana jie a jikinta yana jin jiki, sautin murmushinsa taji a kunninta, tayi saurin zare hannayenta, da saurinta kuma tabar wajen, yana,,

    Humaira, ina ta ruga, ta shige gidan tare da banko kofa tana dafe kirji, futowa yayi ya tsaya banda dariya ba abin da yakeyi, tabbas indai yana tare da ita, wani natsuwa yake jie na daban a rayuwa, motar ya koma ya shige da fadin,,
  
   hakane, ke alkhairi ce a rayuwa nah, in sha Allah, da wannan ya wuce office din hankali kwance, sai dai yana zuwa kamar kullum kasa a'ikin yayi, yayin da jikinsa ko ina ya dauka, daurewa kawai yayi, kamar yanda maami ta karfafa mishi gwiwa da sukai waya, sannan ta gargadeshi da jin wakokin nan nashi na fama, kasancewan tasanshi da son wake wake, tun tasowanshi.

  karatun Al-qur'an ya sanya a wayarnshi, cikin suratul bakarah yana saurara, tare da komawa ya cigaba da a'ikinshi, lokaci lokaci kuma yana tuno da fuskanta, sanda ta lumshe ido bayan ta sumbaceshi, murmushi kawai yakan yie inya tuna.

 

                           ***

   Nata barayin kuwa, tana shiga gida, a hankali ta zauna gefen kujera tana nazarin wasu abubbuwa, tafi minti goma a haka, kafun ta mike ta fara gyara gidan, sosai tasa natsuwa cikin zuciyarta ta gyara ko ina fes fes, sannan ta koma kitchen, girki taso daurawa sai kuma taji duk ta kagara tayi abin da tayi ninya.

   dube dube ta fara yie a kitchen din kaman me neman wani abun, can kuma saita koma daki, hijjabi ta sako har kasan gwiwa saman doguwar rigar dake jikinta, sannan ta koma kitchen din.

    mukulli ta sanya ta bude kofar dake futar da mutum waje ta kitchen din, tare da fucewa ta nufa can garage din gidan, tsaye tayi dai dai wajen da ranar ya daura kafafunshi, tana zuba idanu tare da wasu kalololin tunanin, ta rasa ta inda zata fara m……...,,

  ummeetah, shine abin daya dawo da ita daga duniyar tunanin data tafi, da sauri ta dago kai tana kallonshi, DR. khamis ne tare da wani baturen yaron gidanshi dake mishi yen a'ikace a'ikace, cikin girmamawa tai gaidashi, shima ya amsa mata cikin mutunci kafun ya daura da fadin,,

   dama ina son ganin kie,  akwai maganar da nake so muyi kan rashin lafiyar Baffahnki, jin maganar da yayi ne, yasa ta maida hankalinta sosai, yana cigaba da fadin,,
 
    ummeetah kwanakin baya sadeeq ya fada mun komai kan yanda lamarin auranku ya kasance, ya sanar dani cewa ke matarsa ce, tabbas ba abin dana taya shi sai farin ciki da kuma fatan alkhairi, kasa ummeetah tayi da kanta, tana mamaki,,

   kenan da gaske yake da zaran aunty suhymah ta haihu zai sanar da ita wacece a gareshi, tunda gashi yanx……, DR. khamis ne ya katse mata tunani dake cigaba da fadin,,

   ummeetah ciwon uncle dinkine ya sanya nie a rudani, saboda yayi yanayi da ciwon da ya fada mun mahaifinki yayi, da sauri ta dago kai tana fadin,,

   uncle khamis wlhy shine, irin daya da ciwon Affah nane,  a can baya nayi tunanin gadon ciwon mahaifina yayi, saboda yasha bani labarin iri daya da ciwon da iyayanshi su kayie ne, to amma sai yanxun na fahimce akwai wani abu, inhar gado ne abin, nie ya kamata ciwon ya kama ba Baffah na ba, ta karisa maganar kamar zatai kuka, jinjina kanshi yayi da fadin,,

  na lura da hakan, tabbas yana tare dani a asibiti sanda ake binciken lafiyarsa, kuma babu abin dake damunshi, cikin muryan kuka take fadin,,
  
   uncle khamis don Allah ka taimaka mun, plss na rokeka, tsoro nake wani abin ya faru dashi, nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, duk sai suka bashi tausayi, ba ita ba ba Baffan nata ba, kafun ya kalli inda yazo ya sameta tana kallo, dagowa yayi yana kallonta, cikin harshen fillanci yake mata tamabaya, da sauri ta girgixa kanta alamar eh.

   john ya kalle dake tsaye gefe, yayi ma magana da harshen turanci, kafun yaron yabar wajen, garage din nasu gidan ya nufa, can sai gashi ya futo da wani karamin shovel, shida DR. khamis suka tsuguna a wajen suna yen dubarunsu, yayin da ummeetah taja gefe daya ta tsaya.

   sosai ya fara hake wajen, shima DR. khamis mikewa yayi yana ja gefe, baiyi wani nisa ba ya fara hangen bakin wani abu, himma sosai ya bada, can yasa hannu yana barbasa kasan wajen kafun ya zaro abin, ba ummeetah har DR. khamis zaro ido sukayi waje da tsananin mamaki, ya amsa layun har kusan guda takwas, wanda ko wanne ciki yaji wasu irin surkulle a kuma daddaure.

  mamaki ne ya rufe ummeetah, to ta ina wadannan abubbuwan suka zo, har wani zufa ke keto mata, shikam shi da john kaman dole suka dage wajen warware layun, murmushi kawai yayi yana dagowa da fadin,,

   dama na san haka zai iya kasancewa, akwai wani kakan mahaifina, shima irin fulanin dajin nanne, to mukan zauna wani lokacin in muna hira, yakan bani labarin irin wadannan sihirce sihircen, sihiri ne da yace ana hadawa da bakaken aljannu, kuma mai hadari ne, sai dai yanxun mu gode Allah, in sha Allah komai ya wuce.

   da sauri ta amsa, tana karanta yaren da yake cikin layun, ko wanne akwai sunan Baffanta radau, tare da munanan kalamai, wasu hawayen farin ciki ne ya wanke fuskanta tana fadin,,

    uncle khamis nagode, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya albarkaci zuri'arka, cikin jin dadin addu'ar data mai yace,,

  Ameen, karki damu yanxun kiba john ya kona su, sannan saiya gyara wajen, amma fa akwai abu daya, don kaka nah yace, idan har aka tone, to abin zai koma kan wanda yayi ne, da sauri take fadin,,

   nidai fatana Allah yaba Baffah nah lafia, sai data fada ma sannan ta danji kunya, shidai dariya ta bashi sukai sallama yana barin wajen, hankalinta bai kwanta ba sai da taga an konasu duka, sannan ta koma cikin gida, tana barin john yana gyara inda ya hake.



                          ***

  Futowanshi kenan daga bayin dake cikin office din, yana sauke hannun rigarshi, tare da shafe fuskanshi dake jike da ruwa, wayanshi ne ya fara ringing dake ije bisa table, murmushi yayi sanda ya dauki wayar yana karo da sunan,,

  Abba nah, dai dai sanda kiran ya tsinke, ya zauna kan wata yer design sofa chair dake gefe yana fadin,,

  Alhamdulillah, shidai tunda wani dan bacci ya kwasheshi sanda yake a'iki bema sani ba, sai karar kiran sallar da yayi setting a wayarshi ne ya tasheshi, ya farka da jin wani rahma a jikinshi, banda hamdala ba abin da yakeyi, maida kira yayi ma mahaifn nashi tare da karawa a kunni, dai dai sanda ya daga wayar da sallama, shima amsa mai yayi yana daurawa da fadin,,

   Abba nah, daga can bangaren shima mahaifin nashi murmushi yayi, don duk cikin yeyensa ba wanda yafi so irin sadeeq da kuma munat, yana fadin,,

  dan Abba ya kake, maamin ka tace mun kana ta fama da rashin lafiya, murmushi yayi kafun yace,,

  Abba karku damu, in sha Allah na samu lafia, cikin jin dadi mahaifin nashi yace,,

  good dan albarka, Allah ya baka lafia, addu'anmu kullum zata kasance a gareku da yardan Allah, shima cike dajin dadin kalaman mahaifin nashi yake fadin,,
 
  Ameen, Abba nah nagode, sun dan taba hira, kafun Abba ya tuno wani abu yana fadin,,

  yawwa, sai kuma maganar auran mutallab kar in manta ban fada maka ba, cike da annurin fuska yake fadin,,

  muheet ne zaiyi aure, lallai yaro zaiyi hankali, Abba yayi dan murmushi yana jinjina kanshi da fadin,,

  kwarai kuwa, Allah yasa yayi hankalin, don bikin ma ina sone a hada dana maimunatu ayi a wuce wajen, shidai bakinshi yaki rufuwa yake fadin,,

    Allah ya sanya alkhairi, a nan kaduna ya samu matar?kai tsaye yake fadin,,

   ummmm, toh eh dai zance, amma ina ganin tabbas lokacin bikin ya kamata ku hallara, zaka dawo tare da iyalin, ya dada gyara zama yana fadin,,

  Abba har damu, yace,,

   kwarai da gaske, kai nefa babban wa, kuma uba wata rana a garesu, dan shiru yayi kafun yace,,

   to Allah ya kaimu lokacin, ya dan nisa kafun ya cigaba da fadin,,

   akwai kyautar gida da mota na ango, sannan zan tura ma aunty nah kudi a hada duk wani abu daya dace na bangaren lefe, da yardan Allah harta sadakin aure muheet yana hannu na, sosai Abba yasa murmushi yana fadin,,

   a'ah sadeeku karfa ka takura kanka, cikin girmamawa yake fadin,,

  Abba menene amfanin nemar in banyi musu ba, cike da farin ciki yake sambada mishi albarka, tare da binshi da kyakyawar addu'a, da wannan sukai sallama kowa na ije wayar, ya mike don zuwa gabatar sa sallah.




                 £……£……£

  Dattijuwar maca ce, amma wahalar duniya da kutsa kutsa, ya sanya ta zama tsohuwan karfi da mai da yaji, bata dade da dawowa nan rugar tasu ba, daga inda tayi aure, yanxun auran ya mutu, shine ta tattaro ta dawo, macen da take mafarin duk wani kulle kullen sharri da tsabar mugunta.

   mahaifiyar su lado kenan, kishiyar mahaifiyar Affahn ummeetah, ciwon idanu takeyi dake neman kai ga makanta, amma tunda taji karar mota, aka kuma bata labarin abin daya kawosu, sunxo neman auran shatu karama, jikar shatu kishiyarta, shikenan ta sanya kuka, ita baxai yuyuba wani abinma kamar tabara, kuka sosai ta rikayi da tsiyayyaku.

   sai dai ye'yenta suka dawo, lado shine gaba gaba yana fada mata, a'i anyi an gama, tare da zayyane mata duk yanda ake ciki, sai lokacin ta danji sassauci tana maida kwallarta, jama'an gidan da dama sunyi farin ciki.

    sai dai kash, mikewar da babban dan nata yayi don nufa turakarsa, taka kafa dayan da zaiyi, tunda ya kwatsa wani ihu, bai kara takawa ba, sai nishi da yakeyi yana kiran a taimaka mishi, a rirrike aka karisa shiga dashi dakin, (tom dama ance in zaka gina ramin mugunta…………)




                            ***

    Umeetah ma nata bangaren cikin walwala ta cigaba da gabatar da ayyukanta, cikin zuciyarta bata daina yin mishi addu'a ba, harta kammala girkinta, wanka tasha akasha kwalliya, sai dai har lokacin dawowashi yayi bai dawo ba, wannan ya sanya ta dan damuwa, matar gidan ma harta dawo, don yau da wuri kam ta dawo.

   Lokacin tafiyarsu makaranta ne da Irfan

Please Login or Register in order to submit comment