Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mum dinku kina kallo yanxun ba a'ikin, komai ya tsaya an dakatar muku, surayya tace,,

  hummm, tana jawo jakarta da dauko wani yer kwalba kamar na zuma, ta mika ma suhymah da fadin,,

  gashi kawas, wannan kie zuba mishi ko a tea ne yasha, bana cutarwa bane ki bude ma ki gani, kamar wacce aka zare ma laka a jiki ta shiga bude kwalban, da sauri kuma ta kauda kanta tana rufe hancinta, surayya tayi dan dariya tana mikewa da fadin,,

  kawata soon soon za kiji sunan mrs A A sadeeq na amsawa, sai munxo taron bude International Academy, daga haka ta mike tana musu sai anjima, mummy kawai ta iya amsa mata, amma har surayya ta fice suhymah bata samu daman iya yin katabus ba. 

  tana dan dariya ta fada motarta, dai dai sanda kira ya shigo wayarta, da sauri tayi picking sai data gama jera mata kirari, kafun ta fara mata bayanin duk yanda su kayi da suhymah, tayi yer dariya tana fadin,,

  a'ikinki yayi kyau surayya, naji dadi data bude sakon nan, don itama ba haka zamu barta ba yer taurin kan tsiya, in mukai wasa saita nemi tona mana asiri, surayya tayi dan dariya da fadin,,

  wannan haka yake shugabar kungiya, karki samu wani damuwa, don nasan mun riga da mun gama da wannan matsalar, sauran kuma wanda ke gaban mu, daga can site din ta jinjina kai, suka dan tattauna kafun su ije wayar, surayya taja motarta tabar gidan.

  a can bangaren kuwa suhymah kuka ta sanya tana fadin,,

  aunty bana son na rabu da mijina, bana son nabar wannan daular, amma plss ku gane ina son d'ana, menene shawara ne?, cikin tausayawa take rarrashinta da fadin,,

  daughter bamu da yanda za muyi, in mukai ganganci asirin mune zai tonu, mu kuma rasa komai, kina kallo shima yaya bulama a halin da ake ciki, yana can saudian sun tsareshi suna tuhumarshi da safaran kwayoyi, duk wani account dinshi dake a'iki sun dakatar dashi, kina kuma sane da cewa daga dukiyar yer uwa nah har nawa, da wanda kikasha tura mishi kina US, da sunan ya juya mana, duk suna wajenshi, ta dawo kusa da ita da rungumota tana cigaba da fadin,,

  yanxun ta inama zamu fara daughter, a'i amincewa ya zame miki dole, daganan sai musan yanda za muyi waje da shegiyar can, yaya falmata ma ta sanar mun akwai wajen wani mai magani da zamu ya iya aiki, dole nema zaku bar kasan sai a kafeshi a can kawai, daga ke sai mijin kie kinji, plsss ki daina wannan kukan, kanta ta jinjina alamar gamsuwa tana share hawayenta cike da kuncin rayuwa.

 



  ***
  Daga wankan yamma ta futo nan bayin dake backyard din gidan, sanye da hijjabin data zumbula, baba balarabu ta futo rike da wani katon baho a bayanta, a tsakar gida ta wuce su aunty munat da sauran yen uwa dake zaune suna a'iki da yer hiransu.

  tukan kan ta karisa cikin kitchen din take juyo hayaniyansu, yen gidan sune, matan su Baffah lado  kullum suka shigo raba abincin sadaka, idan suka kammala za'a raba abin daya ragu, sai anyi ta tsiya kamar ayi fada, aunty batulah ce ma ke tsaye tana raba rigiman, ummeetah ta girgixa kanta kawai tana wucewa ciki.

tsaf ta kammala gyara dakin mai jegon sai kamshi yakeyi, aunty Amrah dake daga gefe bisa sofa chair tana waya da mijinta, ta lura da motsin da zahra keyi daga dan babys bed dinta mai kyau da take kwance, ko kafin tayi magana ta tsala ihu tace,,

  to to sarkin rigiman ta tashi, hibbat to ga kanwarki nan ta tashi zata cika ma mutane kunni, hibbat dake jera pillows a gado ta taho da murmushinta tana daukanta da yin mata wasa, dai dai sanda ummeetah ta shigo dakin, cikin salon tonan tsiwa hibbat ke fadin,,

  maman zahra har anyi wank……..., a'i bata kai karshe ba ta gimtse raguwan maganarta, saboda hararan da aka jefa mata, itakam sai dariya takeyi tana tsokanarta da fadin,,

  baby zahra, kinga maamaan kie tana harara, oh muce maamaa sorry ko, ummeetah data nufa gaban safe saita runtse idanuwa don kunya ga aunty Amrah a wajen, ganin hakan ne yasa aunty Amrah yin murmushin, tare da mikewa ta fice zuwa waje inda su aunty batulah ke a'iki, nan kuwa ummeetah ta taso ma hibbat da masifa.

   a kofar falo suka kusa cin karo da yake sauri saurin shiga site din ummeetah, da sauri ta danja baya tana fiddo ido waje da fadin,,

   Alhaj irin wannan sauri haka, to kardai a manta jego takeyi, yana wata yer munafukin murmushi yake sosa sumar kanshi da fadin,,

  kai aunty Amrah har kinsa naji kunya, wajen d'iya tafa zani, harara ta zabga mishi kafun ta futa tana karisa fadin,,

  Allah ya shirya, wlhy sadeeq duk ka zama wani mare kunya akan yen nan,,

  naji dai……, ya fada yana karisawa ciki, cak ya tsaya a bakin kofan, yana kallon yanda take zuba ruwan masifa, hibbat kuwa na faman kyalkyale dariya, taja wani dogon tsaki tana juyawa gaban safe da fadin,,

  sai kiyi tayi, nima in Allah ya yarda akwai ranan dazan rama, amma wlhy ki kiyayeni da wannan sunan……,, gyaran muryan da yayie ne ya sanya su dawo da hankalinsu kan kofan, hibbat ta mike rike da zahra tana mishi sannu da zuwa, ya amsa mata yana daurawa da fadin,,

  dijan maami meya faru ne, dama wannan madam din ta iya masifa har haka?, tana yer dariya tace,,

  wlhy kuwa uncle, daga fa nace mata maman zahra, shine take zabga wannan masifar, karisowa yayi yana zama bisa sofa chair, yayin da hibbat ta mika mishi zahra ya amsheta da fadin,,

  au dan wannan abin, a'i da kin sani kin hada duka, maman fadimatu zahra, sai muga ta tsiya, kuma bata rai ummeetah tayi tana cunno baki, yayin da hibbat ta dauki hanyar futa tana mata dariya harda gwalo, da sauri take fadin,,

  toh kuma ina zaki don gul……, sai kuma tayi shiru ganin hibbat harta fice abinta, ya kishingida da kyau yana rungume yershi tare da zuba mata idanu, kusan 2minutes kafun yace,,

  wai shin kedai halan jegon tsiwa kikeyi? ta gefen ido ta kalleshi, kafun tayi wani dan war da idanun yace,,

  good +yanga ma duk kin kara, kamar zatai kuka take fadin,,

  Baffah plss ka futa mana, jego fa nakeyi,,

   hmmm jego manya, ya fada da dan dariya, sai kuma ya mike ya doshi kofan kamar zai futa, a firgice ta zaro ido ganin yana kokarin sanya ma kofan key, ta kuma marairaice fuska tana fadin,,

  Baffah don Allah ka rufa mun asiri, bafa aso miji yana shigowa dakin matarshi in tana jego, shi yasa na maka maganan, yanda tayi maganar saita bashi dariya, amma sai ya dan maxe da fadin,,

  ina matar take, ina mijin? kamar ta rushe da kuka ta hada jikinta da jikin wardrobe, ya wani hade fuska yana fadin,,

  na rantse in baki tanka ba, zan sanya ma kofan nan key, da sauri tace,,

  kaine mijin, yayi wata yer murmushin mugunta da fadin,,

  mijin wa?, idanunta a lumshe take fadin,,

  mijin ummeetah, sai da yayi yer dariya kafun yace,,

  ke kuma matar sadeeq ko?, kanta ta daga a kagare, ya danja numfashi, kafun ya dan dago zahra daga kirjinsa dake fama tsotsar dan yatsanta da fadin,,

  wannan fa, wacece ita a garemu?, sosai ta fiddo idonta waje kafun ta daura hannunta duka bisa ka, alamar naga ta kaina, yana dan dariya ya maida kofan ya bude sosai, kafun yace,,

  come on, maida wukar karki daura mun hannu a ka, ta sauke ajiyar zuciya tana kauda kanta daga kallonsu shida yer, bisa sofa chair din ya koma ya zauna yana nuna mata gefe kusa dashi, so serious yake fadin,,

   Humaira zo muyi wata magana, bata musa ba ta kariso inda yake tana zama a dofane, ya zuba mata idanu sosai kamar yana son ya gano wani abu a fuskanta, kafun yace,,
 
  kinsan menene?, yanda yayi maganar serious yasa ta girgixa mishi kanta kai tsaye, alamar a'ah, ya numfasa da fadin,,

  wlhy Humaira kina kama dasu?, da dan mamaki take fadin,,

  Baffah su wa kuma?, komawa yayi yana kishingida da kyau kafun yace,,

   a nawa, a farashi nawa zaki biya wannan daddadan labarin dana zo miki dashi?, marairaice fuska tayi da fadin,,

  Baffah kasan bani da abin dazan iya biyanka dashi,,

  hmmm, da gaske, ya fada yana bata wani romantic look mai cike da kewa, murya a sanyaye yake fadin,,

  baby to kie bani melon mana ko paw paw, kinga kin biya farashi mai tsada kenan, turo baki tayi tana kallonshi, ya dan yunkuro da fadin,,

  toooh, nima za'a masifeni kenan, yanda yayi maganar ne ya bata dariya, ta dan dara tana fadin,,

  kai Baffah ba haka bane fa, na kagu inji story dinne, kuma kace saina baka melon……..., kasa karisawa tayi, ya dan kafeta da idanu yana fadin,,

  umm hmm, ina jinki, tayi dan war kafun ta wani sauya kalan murya tana fadin,,
 
  a'i kaga yanxun daminan ya sauka, ba su riga da sunyi ye'ye ba, shiru kawai yayi na wasu yen dakikai yana kallonta, kafun ya fadada murmushinsa yana juyo da fuskanta da take wani kakkaudawa da fadin,,

  hmmm, babyn nan wlhy ina son wayaun kie, kina burgeni da salonki, da sauri ta sanya hannu tana rufe fuskanta, ya ije zahra gefe daya, yana janyota jikinshi, itama sai tayi luf tana shakar daddadan kamshin jikinshi, a hankali cikin kunni yake rada mata,,

   babyna zanyi kewarki matuka, ina ma kanyie, gashi har Adamawa zaki tafi kie barni enmmata, da sauri ta dago kanta da fadin,,

  Adamawa?, baice mata komai ba ya dagota da jikinshi, tare da zaro wayarshi yana budo mata hotan wata mata, da bata wuce sa'an aunty Amrah ba, sai kuma yer yarinyan dake kusa da ita wacce tayi 12to13years, gaba daya sai fuskokinsu suka fara rikide mata zuwa nata face din, musamman matar da suke kalar fatarsu daya dana ummeetah, don ita yarinyan fara ce, cikin sanyi yace,,

  kinga kuyi kama ko?, ta kasa amsa mishi da baki, sai girgixa kanta da tayi alamar eh, yayi wani murmushin yana amsar wayan tare da maida hankali sosai, sanda ya budo mata wani family photo da fadin,,

  cikin nan wa kika sani?, sosai ta zuba ma hotan ido, duk yawancin ahalin suna kama da ita, da sauri ta dago kai cike da mamaki take fadin,,

  lah Baffah uncle khamis, da murmushi yake fadin,,

  wise girl, yasa hannunshi ya ruko nata da kyau kafun ya fara fadin,,

  Humaira wannan shine family Ribado fulani, Affahnki ya taba fada miki kina kama da mai sunan zahra, da sauri ta girgixa kanta alamar a'ah, ya numfasa yana nuna mata wani dan tamikakken tsoho dake tsakiyar ahalin, kafun ya cigaba da fadin,,

  wannan shine malam Ribado fulani, shahararran fulanin daji mai tarin azzikin gaske, Humaira labarin ya samo asali ne, tun lokacin daya rabu da matarshi ta farko wayayyan mace, nan suka raba kan yeyen, yayin data kwashi wasu daga ciki, shima yaja mahaifiyarki yer autan cikinsu wacce yafi kauna duk cikin yeyenshi, mahaifin su khamis kuwa, ya nuna mata wani babban dattijo wanda ke kusa da tsohon, shima yana da kammanin fuskan ummeetah a tare dashi, ya cigaba da fadin,,

  shine babban danshi Alh. Rabi'u Ribado, yana kuma daya daga cikin wanda mahaifiyarsu ta dauka, shi da yer uwanshi, wacce naji suna kira da goggo shatu, itace wacce na fara nuna miki hotan ta, daga ita sai mahaifiyarki, a yanxun tana aure da wani senator ne jahar sokoto, ta kusa da itan babbar yer tace, suna kiranta zuhra, ya dan numfasa kafun ya kuma cigaba da fadin,,

  tun kafun rasuwar mahaifayarsu Alh. Rabi'u suke son mahaifinsu ya daina yawan kiwo daji daji, kuma gari gari, kai har kasan ma suna futa, amma bashi da alamar dainawa, yawancin yeyenshi mata daya haifa a tafiyar yake aurad dasu, kuma idan ya aurar da yersa baya waiwaye wannan kuma wata al-adarsu ce,,

  Humaira hankalinshi bai kuma tashi ba sai daya aurar da mahaifiyarki ga Affah, tsananin son da yake mata yasa har kwanciya ciwo sai da yayi, yayin da lokaci daya ya watsar da yawon kiwo, Alh. Rabi'u wanda a lokacin ya dade dayin aure da hayayyafa, shine ya dauki mahaifinsu ya cigaba da zama karkashin kulawanshi, da sauran kanninshi da suka rage duk suka mai dasu karatu, a yanx……...,,

  kukan da zahra ta tsandara ne ya katse mishi maganar, duk suka sauke wani ajiyar zuciya, ummeetah duk ta zaku taji karshen wannan labarin, daukanta yayi ya daura bisa kirjinshi yana jijiga bayanta a hankali, kafun ya cigaba da fadin,,

  a yanxun tsawon shekara biyar kenan tunda suka gano inda yer uwansu tayi aure, Alh. Rabi'u ke faman zaryan zuwa, amma ba abin da suke fada mish sai cewa,,

  a'i mahaifiyarki ta rasu wajen haihuwa, ba tare data haife abin dake cikinta ba, shi kuma Affah bayan wasu shekaru bakin ciki shima yasa ya bita, da wannan karyan kanzan kuregan da suke labta mishi, suka sanya dangana, Humaira yanda na lura ahalin suna matukar son mahaifiyarki sosai, ya sauke zahra daga kirjinshi yana shifideta a jikinshi, cikin rawar murya take fadin,,

  shi uncle khamis me yasa bai sanar mun shi dan uwa na bane?, da sauri ya dago kai ya kalleta, hannunta ya kuma rukowa yana fadin,,

  Humaira tabbas sanda khamis ya fara ganin kie, ya fada mun yana jie a jikinshi kamar ke yer uwan shine, sai dai bamu maida abin serious ba, sai lokacin dana bashi labarin auren mu sannan hankalinshi ya karkata, don suma suna da tarihin yer uwan mahaifinsu, kuma kullum yana son yinma mahaifinsu maganar amma ya fiso suyita ba a waya ba, toh a maganar da nake miki yanxun,,

  yau kwanan su uku da suma suka diro kasan, shine ya nuna ma mahaifinshi hotunan kie, tare da labarta mai labarin dana bashi, yau a office ina zaune saiga kira, mun jima muna tattaunawa dasu, yayin da nima na sanar dasu kadan daga cikin abin dana sani na tarihin rayuwanku, ya numfasa da fadin,,

  Humaira yau mutumin nan har kukan dadi sai da yayie, ya kuma tabbatar mun cewa gobe dukkan ahalin sun tafe in sha Allah, cewa fa su kayi zasu baki suprise, amma na kasa hakura, tunda muka kammala wayan sauran yen uwan ke faman kirana, goggo shatu ma munyi waya da ita, sai babbar yan khamis dake aure a saudia mashkura, ita tace saima sunxo suna da yeyenta, ke suna da yawa sosai, na lura duk sun zaku suxo suga yer uwansu, hawayen da suka taru a idanunta ne suka karisa silalowa, murya a raunane take fadin,,

  wayyoo dadi, Allah na gode maka, ban taba tunanin zanga wannan ranar ba, inason mahaifiyata don haka nake burin na hadu da wani nata koda mutum daya ne, ashe zan gansu da yawa, nima wlhy  Baffah na kosa gobe tayi, hawayenta yasa hannu yana goge mata da fadin,,

  nima Humaira nayi farin ciki da wannan lamarin, koba komai zaki sami ahalin da zasu nuna miki soyayya na gaske da gaske, har maami da Abba sai dana fada ma, suma sunyi farin ciki tare da taya kie murna, donshi Abba yasan mahaifin khamis din ma, cikin zumudi ta ruko hannunshi da fadin,,

  Baffah don Allah da gaske zasu zo inda nake gobe, kai gaskiya yau baxan iya bacci ba, baxan iya bacci na yau ba, yana yer dariya yake fadin,,

  kinga madam kie rufa mun asiri, ban fada miki ba don kie kasa bacci, samar kirjinshi ta fada da fadin,,

  Baffah wlhy farin ciki ne zai hanani yin bacci, ka yarda dani, a hankali yake shafa bayanta tare da kissing saman kanta da fadin,,

  na sani tawan, nima ina tayaki farin ciki mai dumbin yawa.

 ranar dai gaba daya fuskan ummeetah ya cika da walwala, kowa ya ganta yasan tana cikin farin ciki, da dare ma hiran suka dasa dasu aunty munat, da yike tasan wata kanwar khamis din, kusan ma course mate dinta ne, Janan sai dai itama bata jima dayin aure ba, sun jima suna hiran, duk ummeetah ta kagara gobe tayi. 

  ***
   Shagargarin ranar kuwa suka hallaro, wanda gobenshi ne suna, ranar dai ba'a maganar farin ciki, hakika ummeetah taga gata, kowa so yake ya nuna mata soyayyarshi tare da kulawa ita da abin data haifa, ba kamar mahaifin su khamis da goggo shatu da suke jie kamar su mai data ciki, matar DR. khamis ma taxo, tuni su misha suka kankame ummeetah, don sun santa farar sani ma, kowa ma na mamakin yanda suka saba da ita.

  nan aka shiga hidiman suna gida fa ya kaure, mai jego tuni ta futo wal, harda su gyaran jiki, tasha kitso da lalli, suka cigaba da gabatar da shirye shiryen suna hankali kwance.

  

  ***
  Zaune yake a falonshi, ya maida hankali sosai bisa laptop din dake gabanshi, yen kwanakinan ayyuka sunsha kanshi, wayarshi ne dake gefe ya dau ringing,,

  Abba, ya fada yana picking call din da sallama, amsa mishi yayi suna gaisawa, kafun Abba ya daura da fadin,,

  sadeeq wai yaushe ne ma taron nan na bude makarantar nan da kace?, sai da yayi dan shiru kafun yace,,

  Abba dama on monday ne, shagargarin ranar suna amma yanx……, da sauri ya dakatar dashi da fadin,,

  a'ah kaga, ka barshi a hakan yayie, inason kuma in sanar dakai abu daya, plss a bayyanar da a'inihin sunan mai makarantar a fili daga goben zuwa jibi in Allah ya kaimu, sauran tsare tsaren naku kuma ku kuka san yanda zaku sanja su, kamar Admission latter da sauransu, umurni nake baka ba shawara ba, cikin sanyin murya ya amsa da fadin,,

  shikenan Abba, in sha Allah za ayi yanda kace, yace,,

  good, Allah yayi albarka, da,,

  Ameen, ya amsa, har Abba zai kashe wayar yayi saurin fadin,,

  yawwa Abba saura maganar muheet, mummy ta kirani daxu hankali tashe kan cewa har yanzu dai shiru ake jinshi, gashi kaki cewa komai, dan tsaki Abba yayi cike da takaici kafun yace,,

  da Allah sadeeq share wannan, sai yanxun ne yagana ta fahimce ina da rana, kuma nie ubane a gurin mutallab, cemun tayi yaje plateau state neman a'iki to mezan n
mishi, don kwana biyu ba'a samu wayarshi ba, kai su karata can, da sauri sadeeq ke fadin,,

  Abba don Allah kayi hakuri, baxa ayi haka ba, nima ina nan ina iya bakin kokari na, plss kayi hakuri kasa hannu, dan dariyan takaici yayi kafun ya amsa mishi da fadin,,

  hmmm, zanga abin daxan iya, sun dan jima suna tattaunawa kafun sun ije wayar, dai dai sanda ta shigo falon rike da hannun Irfan dake tafe yana layi, kamar mejin bacci, hannunshi ya zare yana nufa inda daddynshi ke zaune, bisa cinyarshi ya langwabar da kanshi ya kwanta, da dan damuwa yake fadin,,

  waishin ni kuwa Irfan bayi da lafia ne?, tana zama kusa da kujeran da yake tace,,

  a'ah, meka gani?, bai bata amsa ba, sai dan tsakin da yayi yana taba wuyan yaron da yake normal qlau, kafun ya dago da fadin,,

  he seems so weak these days, bana jin dadin yanda nake ganinshi babu kuzari, sai da gabanta ya wani amsa a goma goma,,

  hmmm, ta fada da dan murmushin yake tana kasa da kanta, tare da danne wasu hawaye, daker ta iya tattaro kalaman,,

  kasan yanayin rayuwan ne, kullum jujjuyawa take, amma lafiyarsa qlau sweetheart, ya dameni in kawo shi wajen daddy zaiyi bacci, ajiyar heart ya sauke yana dan murmushi da fadin,,

  hakane angel, hope dai kin kammala duk wani shirye shirye don gobe da wuri zamu wuce, cikin dan basarwa take fadin,,

  oh kaga kuwa harna manta, bari naje na kammala, daga haka ta mike tana komawa downstairs.

   A falon dake downstairs ta tarar da kanninta, dasu saudat da munirat da suke zaune suna hira da arerewa, ta dan dafa cushion da hannunta tana fadin,,

  waiku ba zaku sunan ba da gaske?, zumbur zahira dake kwance ta mimmike kafa take fadin,,

  wa? mune zamu kauyen nan, god for bid, over our death body, Najm ta sauke novel din dake hannunta da fadin,,

  hmmm, aunty suhymah nie har kinsa zuciya nah ya tashi, me za muje muyi a taron mayu alakakai, kedai daya zaman miki tilas, so bye bye saikin dawo, duk suka sa dariya harda ita da take dan murmushi da fadin,,

  da gaske kukeyi, saudat tace,,

  a'ikuje dai ku dasu mummy kawai, amma mu muna nan, sai monday za muyi namu a A A sadeeq……,

  International Academy!, duk suka karisa su dukkan su, ita dai ta wuce site dinta, suna zaune suna cigaba da zuzuta shirin da sukai ma wannan taron, saima in brother sadeeq ya mika ma yayarsu key din makarantar, don rade rade da gulma ya nuna cewa daya daga cikin matarsa zai bama makarantar, su kuma sunga babu wacce dai tafi dacewa dashi sai yer uwansu(hmmm).

  shagargarin ranar da sassafe suka wuce, mummy ma da yer uwanta haj. falmata da tace sai taje taga kwal uwar daka suka duri jiki, sai wani yatsina sukeyi sanda suke keta dajin dazai kaisu rugar su ummeetah, waisu zasu kauye.

 

*fatan alkhairi*

share
comment
vote

*Matatace 2019*
Na meemartjj
[14/08, 14:29] Dala Grp: 🕯🕯🕯
    *MATATACE*
          🕯🕯🕯
  

🇳🇬®
*_ABORIGINAL WRITER'S ASSOCIATION📚✍️._*
[❄Dance above the surface of the world,let your thoughts lift you into creativity that is not hampered by opinion.]

*_wannan pages din nakune, sabuwar kungiyan mu👆🏻, da fatan Allah ya hada kanmu baki daya_*

story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjj 

*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty Ummeetah any my Fa'ixation._

page 75~76

__________Tuni aka fara shan shagalin suna, yen uwa an taru ana ta a'ikace a'ikacen kayan abinci girki kala kala, kai nie baxan iya kirgawa ba, abin dai komai zash shu'awa.

  can na leka amarya itama tasha kyau, sanye take cikin wata peach din atamfa super english na riga da skirt, tasha kyau da daurinta na burgewa, saita sanya wani peach din gyalle mare nauyi da yaji adon stones sai kyalli yakeyi samar kafadarta daya, kafarta na sanye cikin wata weight shoe na kamfanin vincci, tana ta fara'a cikin gidan sunan, yayin da yen uwanta suke ta daukanta hotuna.

   sanda suka iso suhymah bude baki kawai tayi tana duban gidan, tabbas an kashe kudi mai suna kudi, tare suka futo daga gidan baya, Irfan dake gaba yana futowa yayi karo dasu misha yasa tsalle kuwa yana karisawa wajensu, itama tayi mamakin ganin yaran, wato harda DR khamis kenan aka munafurceta suna US.

  masu kidin kwarya ne jera a farfajiyar gidan gefe daya, wanda su aunty Amrah suka kira, anata shan shagalin suna, sanda ya iso barin kudi kawai ya fara yinma mai jego, yen uwanshi na mishi nasu, suhymah dai saita zama yer kallo, yayin da masu kidan kurya suka kuma bada himma wajen dukan kwaryansu, kafun yasa kai yana barin wajen shida yen uwanshi, da suke tafe suna magana tare da nufa sabon site dinshi.

  cikin girmamawa ummeetah tayie ma suhymah tayin shiga ciki, daker ta iya cire kafa tana bin bayanta, suna barin wajen matan su Baffah lado suka fara rububin kwasan kudi, sun hade da masu kidin kwaryan ma, baka iya tantance su.

  su ummeetah na shiga ciki wacce naji suna kira da janan ta iso wajen, da sauri tayo kan ummeetah tana fadin,,

  ummeetah tsaya, tsaya a gyara nan karya kwance, ba musu ummeetah taja ta tsaya, ita kuma ta shiga gyatta mata daurin dankwalin, sai da taga ya koma normal kafun tayi dan murmushi tana dagowa da fadin,,
 
  yawwa sai in dan kara miki turare kuma, ta fada maganar tana fesa mata wani design perfume dake hannunta, kafun tace,,

  wai ni kuwa daddyn zahra ya iso yaga wannan wankan, donfa sai ya siya, da sauri ummeetah ta rufe fuskanta da gyalle tana fadin,,

  kai aunty janan, itama tace,,

  kai aunty ummee, dai dai sanda dan kaninsu khaleefa ya iso wajen rike da selfie stick yana fadin,,

  yawwa aunty  ummee, aunty janan ku tsaya in mana selfie, da sauri janan ta kauce tana fadin,,

  in ka soma kayi mun hoto banyi wanka ba, sai na make ka, ya taba fuska yana fadin,,

  kai aunty janan just one snap fa, zuhra ma ta iso wajen duk so suke suyi

Please Login or Register in order to submit comment