Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daina, hannunta ya ruko a hankali yana dawowa saman carpet din shima ya zauna da fadin,,

  "nagode matar mutunci nah, sannan shugaban mata nah har a gidan aljanna in sha Allah", murmushi ne ya subuce mata, tana mai jin dadin sunan sosai, cikin sanyin murya take fadin,,

  "yaya jikin Irfan?", shiru ya danyi da damuwa sosai a fuskanshi, kafun ya sauke wani ajiyar zuciya da murmushin yake, yake fadin,,

  "toh da sauki, amma bema san wanda ke kanshi ba, Humaira har yanxun ganin abin nake kamar a mafarki, sai dai kawai mu bishi da addu'a", kamar zatai kuka, don tuni har idanuwanta sun tara hawaye take fadin,,

   "in sha Allah babu abin dazai sameshi, yanda kullum kake kokarin wajen tallafa ma rayuwan yeyen wasu, haka Allah zai tallafi rayuwan naka, in sha Allah zamu cigaba da mishi addu'a, Irfan yafi karfin su da yardar Allah", sosai yaji dadin kalamanta, koba komai sun sanyaya mishi zuciya, a hankali ya jawota jikinshi yana shafa bayanta da rarrashi, saboda kukan dake neman kwace mata,,

  "plss karki wannan kukan", ya fada da dan damuwa, kafun ya daura da fadin,,

  "likitan daya dubashi ya sanar mun jininshi nada karfi, sannan duk da kasancewarshi yaro yana da rukon ibada, don haka baxa su iya mishi ba", ya numfasa kafun ya cigaba da fadin,,

  "yanxun matsala daya ne firgitan da yakeyi, shima saboda jininshi da suka fara samu ne, shi yasa yake irin wadannan abubbuwan, wanda maybe kuma ya iya shafar kwakwalwanshi, ammma ina tunanin in sha Allah nan da 3days zan futa dashi kasan, baxan iya juren ganin Irfan a haka ba", muryanshi yayi zafi alamar tsantsan baci rai yake cigaba da fadin,,

  "har yanxun na rasa dalilin dazai sa suhymah ta a'ikata irin wannan mummunar laifin, duk irin so da tattalin dana nuna mata saita hadani da irin wannan kazantar, ban taba tunanin son kanta harya kai haka ba, ya zama tilas in nuna mata irin kuskuren da tayi a rayuwa", a sanyaye ta dago kanta tana zuba mishi ido kafun tace,,

  "hakane, ta a'ikata babban laifi, amma don Allah Baffah kayi mata haku……." wani kallo daya bata ne, ya sanya ta hadiye raguwan maganar ba tare data shirya ba,,

  "tashi mun a jiki" ya fada maganar cikin zallar bacin rai, a sanyaye ta janye jikinta, yana cigaba da fadin,,

  "zan iya samun wani abin inci, don yunwa nake jie?", da sauri ta jawo basket din data shigo dashi tana fara saving dinshi abincin, ta kammala zuba mishi white rice din tare da sanya miya, cokali ta sanya tana dibowa da kawowa wajen bakinshi, amma saiya amsa yana wani hada rai da fadin,,

  "no thanks", shiru kawai tayi tana kallonsa kamar tai kuka, ganin yanda yayi cukun cukun da rai, ta ruko hannunshi tana mishi magiya da fadin,,

  "Baffah plss don Allah ka kawo mana in baka", banxa ya mata sai kuma ya saki spoon din cikin plate din, serious yake kallonta da fadin,,

  "Humaira yau rana ce me muhimmaci a wajena, ranar dana dade ina jiran zuwanta, ranar farin ciki a gareni, amma suhymah ta lalata komai da wannan bakin cikin data dasa mun, kamar matata ce za ace tana wani kungiyan asiri", ya girgixa kanshi da fadin,,

  "unbelievable, sannan ke kina maganar wani hakuri ko?", da wani irin huci ya karisa maganar, narai narai tayi da idanuwa, daga bada hakuri sai ya zama rigima, ta dan runtse idonta tana budewa, kafun ta kama kunninta daya tana kyalle mishi idanuwa da fadin,,

  "ouk am sorry if i say anything wrong", tasa hannu tana dibo abincin tare da kaiwa bakinshi tana fadin,,

  "don Allah kaci abinci, kace fa yunwa kake jie", bai tanka mata ba sai zuba mata idanu da yayi yana bin gashin kanta daya futo ta dan gaba gaba baki sumul da kallo, ta dan langwabar da kanta cike da shagawaba take fadin,,

   "haba mijina na alkhairi, plsss ka amsa mana, kaji Abban Irfan......"

  "sai kuma wa?", ya fada yana tsareta da idanuwa, sai data dan taba fuska kamar mai kuka tace,,

  "zahra'u", yanda tayi maganar ne ya sanya dan murmushi ya subuce mishi yana fadin,,

  "wai nikam shin daxun wajen taron nan da nasha bunch of kisses, me kike fada, sai naji kamar kin fada wani abu, dan maimai……" bai karisa maganar ba saboda abincin data zube mishi cikin baki, sai daya hadiye lomar sannan yace,,

  "kai Humyhra zaki mun dure ne?", a kagare tace,,

  "aunty mashkura tace kar in dade, kuma kaga dare nayi", bai kara tankawa ba harta kammala bashi abincin, bisa gefen gado ya koma ya zauna yana binta da kallo, lokacin da take karisa tattara kayan abincin a natse,,

  kai komai nata ma na daban ne a rayuwa, ya ayyana hakan sanda wayarshi dake ije gefe yasa kara, wani dogon tsaki yayi sanda yaga mai kiran nashi, kai tsaye ya rufe wayar baki daya yana jifa da ita cikin kunan rai, da sauri ummeetah ta dago kai suna hada ido, tayi sauri saukar da nata, sosai ya koma ya zauna bisa gadon yana kishingida bayanshi da pillow, yayin da hannayeshi ke rungume bisa kirji, duk sai taji babu dadin yanda ya bata rai, juyawa tayi dai dai sanda yake fadin,,

  "zo nan Humaira", ya fadi maganar cikin taushin murya, dole tazo a hankali tana dofanewa kusa dashi, ya dan yunkuro yana ruko tafin hannunta da fadin,,

  "meye faru kuma naga kin wani bata rai ne?", a sanyaye tace,,

  "bakomai, kawai dai bana son ina ganinka cikin bacin rai ne?", idanu kawai ya zuba mata sanda ya tallafo kuncinta da tafin hannunshi daya, sai bakinshi kawai taji saman nata, da sauri ta runtse idanuwanta tana kuma kankameshi saboda lulawan da suka fara yie wani duniya.

  kai mutumin nan wlhy solonshi na daban ne, gudun karsu zurma da yawa ne, ya sanyata dagowa daker tana janye jikinta daga nashi,,

  "Baffah plss dare yayeee", da wani kankance ido ya dago yana kallonta, sai kuma yayi baya yana rungumota a kirjinshi,,

  "baby nah zanyi kewar kie, plss in kunje can kie kula mun da kanki da my sweet zahra kinji", yayi kissing saman kanta da fadin,,

  "i luv yhu soo much baby"

  "i luv yhu too my lollipop", ta fada cikin rawar murya, dagota yayi yana mai da mata rigarta dai dai, sannan suka mike.

  tare suka jera har zuwa bakin kofan site din maami, itafa dole sai dai ya barta a nan, shi kuma yace har daki zai rakata, kamar tasa ihu, daker ta samu ya barta a nan, sai da yaga ta shige sannan ya juya.
 
 

  ***
  Shagargarin ranar su ummeetah suka wuce ita da yen uwanta zuwa Adamawa, duk da sai da suka biya ta asibitin da Irfan yake taga jikinshi, har yanxun dai yana kan alluran da suka mishi, tasha kukanta harta gaji tare da jera mishi addu'a, da wannan suka dauki hanya, su munat ma kowa ta koma gidan mijinta.

  hankulansu bai kuma tashi ba, sai da suka jie halin da muheet ke ciki, don zuwa yanxun har an yanke shawaran wucewa dashi secartry, don samun cikakken kulawa, Allah sarki sadeeq shine wanda ya rattafa hannu akan komai, har aka wuce dashi can.

  Abba kuwa yayi nadaman auran mummy yafi a kirga, dama tun ranar daya jiyo tana waya da wani malami, kan a juya musu kan sadeeq sai yanda suka yie da dukiyarshi, yaji wani mugun tsanarta, wanda shine dalilin da yace sadeeq din ya bude sunan makarantar kowa ya gani, sai kuma ga wannan ya biyo baya, 80% mummy ce wacce ta taimaka wajen rugujewan tarbiyan yaron, dole ne kuma yanxun tasan matsayinta a gidanshi.


  ***
A wannan ranar ne sadeeq yayi reporting case din kungiyan su suhymah, wacce aka tasa keyarta har gidan da suka ije don meeting, an kuwa samu sa'an sun hadu baki daya suna gudanar da taro akan yaron dake nemar fin karfinsu, wanda hakan shi zai iya kawo rugujewan wannan kungiya.

  sanda sadeeq yaga irin muhallin nasu duk wasu abubbuwa tsifface tsifface, da jajayen doguwar rigar dake jikinsu, ga wasu tambulan a gaban ko wannesu dake dauke da wani red tik liquid, wanda baxai iya tantance jini ne ko menene ba oho, tabbas kuwa wannan ya kara bashi tabbacin abin nasu da gaske suke.

  ranar dai dubunsu ta cika, kunya iya kunya sunsha, ba kamar shugaban kungiyan wacce mijinta ya kasance babban malami, harda hawayen bakin ciki sai da yayi, yana mai tsantsar mamaki, itama kam ta muzanta iya muzantuwa, aka tarka tasu baki daya zuwa mota, mazajen da suma su kaji sunan matansu suka rika tir da halayensu.

   tijara iya tijara police ke musu, tare da daddaka musu tsawa sanda zasu dura su a cikin mota, harda surayya dake faman ciccika, suhymah dai dake baya baya sai kuka takeyi, muryanta harya dishe.

  yana daga cikin motar daya jawo da kanshi, ya jingina bayanshi da kujera tare da daga kanshi sama don tsaban takaici, ya numfasa yana dagowa sanda yake dad'a jujjuya wata yer brown envelope a hannunshi, ajiyar zuciya ya sauke kafun ya bude handbag dinta dake ije gefe daya, ya sanya mata ciki sannan ya maida jakar ya rufe.

  hankalinshi ya mayar wajen police din dake waje, ta cikin window motar, wani police ne ya kallenta bayan sun kare sanya su a ciki ita zata shiga last, a yatsine yake fadin,,

  "madam pls jeki, ke an riga da an gama warware case dinki da mijinki", a raxane ta kalleshi tana kallon inda motar sadeeq yake a pake, shi kuwa sai yai saurin kauda kanshi, cikin sanyin jiki taxo ta shiga motar tana rufe kofan, murya a dakushe take fadin,,

  "sadeeq nagode daka taimaka mun, wlhy tsoro nake baxan iya zaman prison ba", fuska babu walwala yayi ma motar key yana fara driving da fadin,,

  "karki damu, ba wannan hukuncin bane wanda ya dace dake", cikin sanyin jiki ta kalleshi sosai, shima juyowa yayi yana facing dinta da fadin,,

  "ina son kie fahimce wani abu, ba a shuka alkhairi da sharri", ya karisa maganar yana maida hankalinshi ga titi, cikin dan shashshekan kuka take fadin,,

  "sadeeq me kake nufi, duk fa akan sonka nayi komai", a zafafe yake fadin,,

  "duk don kina sonah saiki kauce hanya, sai ki biye ma son zuciyanki, suhymah tell me something, ina ce ranar da kika fara cemun kina sonah, ba a kwana ba sai dana maida miki da martani, kinsan saboda menene?", kanta ta girgixa da sauri tana nokewa jikin mota, ganin yadda yake masifa, sai daya tausasa murya kafun yace,,

  "saboda ina matukar girmama wanda yace yana sonah, atleast mai sonka yafi makiyinka wanda kullum shi burinshi yaga bayanka ne, amma ba don wani abu ba, naji kunyar matsayin kie na ye'mace harki furta mun kalman so, sannan in kasa amsa miki a ranar, sai ina ganin kamar bai dace ba, na daure hakanan na maida miki da martani, gradually kuma sai naji kin fara kwanta mun a rai, saboda son da kike nuna min, duk wannan bai isaba sai kin hada da tabaibayeni da igiyoyin sharri"

  ya karisa maganar yana dukan steery, idanunsa sunyi jaxur, tuni hanjin cikinta suka kada, komai da ya fada gaskiya ne, bata iya magana ba, sai kuka data sanya, harya faka motar a haraban asibitin da aka admiting mahaifiyarsu, ta share hawayenta tare da daukan jakarta, cikin sanyin murya take fadin,,

  "sadeeq i luv yhu, i luv yhu soo soo much, har abada kuma baxan daina sonka ba, rashin ka zai zama babban tabo a rayuwa nah, zan iya jure komai amma……"

  "enough", ya fada cikin daurewan fuska, kafun ya daura da fadin,,

  "madam plss ina da abubbuwan yie a gaba nah, zaki iya adana kalamanki in mun hadu next", a sanyaye ta kuma gyada mishi kanta daga haka ta fice daga motar, tana daga mishi hannu da fadin,,

  "bye sweetheart", daga mata kai kawai yayi idanunsa a lumshe, sai daya tabbatar ta rufe motar ta juya sannan ya bude idonsa, ya jima yana kallonta harta shige ciki, kafun yaja motar ya bar wajen.

  itakam cike da murna ta karisa shiga asibitin, bata taba tunanin zai bi ta sauki irin haka ba, ashe sadeeq yana sonta har haka.

*~(hmmmm, alkhairi yaafeee inxa kai shukawa).~*

  _2days bani da caji a waya nah, kuyi hakuri shi yasa kuka jini shiru._



*fatan alkhairi*

share
comment
vote

*Matatace 2019*
Na meemartjj
🕯🕯🕯
    *MATATACE*
          🕯🕯🕯
  

🇳🇬®
*_ABORIGINAL WRITER'S ASSOCIATION📚✍️._*
[❄Dance above the surface of the world,let your thoughts lift you into creativity that is not hampered by opinion.]

story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjj 

*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty Ummeetah any my Fa'ixation._

   _These pages goes to:_
  *_Sadeeqjj, Basmajj, Rabi'atjj, Khadeejatjj, Habib Al-amin, Ahmad Al-Amin, Yusrah Al-Amin, Muhhibba Nasir, Haleematu Abubakar, Al-Amin Junaid, luv yhu all my little one's_*

last page 79~80

_________Hankalinta kwance ta shiga ciki tana labarta ma yen uwanta da mahaifiyarta duk yanda akayi, sosai suka jie dadi suna murna.

   sai da hankalinsu ya tashi sanda tayi karo da envelope din dake cikin jakarta, sai data gama jujjuya envelope din a hannu, kafun ta bude tana karance abin dake ciki kamar haka...

  *_Assallam, nasan za kiyi mamaki a duk sanda kikai karo da wannan takardan, to ba komai bane face shaidan daxai tabbatar miki cewa, nie Abubakar sadeeq na sakeki saki d'aya, cos i can't tolerate yhu any more, kiyi hakuri kinyi kuskuren daukan sharri akan zai gina miki alkhairi, hanyar da kika dauka babu abin dazai haifar miki sai ruguza miki alkhairan gidan aure, kamar yanda yanxun ya lalata komai, ina miki fatan alkhairi a rayuwa, Bissalam_*

  Ahankali ta sulale bisa wajen tana rushewa da wani irin kuka da fadin,,

  Sadeeq plss karka mun haka, wlhy ina sonka, kana da kirki, baxan iya auran wani ba kaiba, plsss na rokeku ku fada mishi zan iya yin shekaru goma a prison, indai zai hakura ya zauna dani, nayi nadama baxan kara ba.

  kuka takeyi mai ban tausayi, yen uwanta da mahaifiyarta suna tayata, a ranar dai sai da aka sa mata karin ruwa, ciwo ranga ranga, kullum cikin kiranshi takeyi, amma wayar baya shiga.

  abin da bata sani ba tuni yabar kasan zuwa egypt, inda Irfan zai cigaba da samun cikakken kulawa a wata islamic school daya sanya yaron, ya kuma dan jima kafun ya dawo, don sai da yaron ya samu lafia sosai, sai dai yanxun ya rage yawan fara'a da magana.

  Abba shima ya sallame mummy, sannan yasa sadeeq shima ya bata sallama a companynshi da take a'iki, sauran yeyen kuma ya kwashe ya mai dasu wajen maami, dole su saudat suka natsu, suna cigaba da tafiya bisa tarbiyan da maami ke daurasu, mai cike da tsaftar rayuwa.

  A yanxun munat ne ke cigaba da dawainiya da ita, harda muheet dake can secartry, kullum sai tayi kuka inta tuna da wani abu, da namijin data fie buri shi ya zame mata kaya, yayin da macen da bata kauna, ita take cigaba da bata kulawa a rayuwa.


                         ***
  Tuni ummeetah ta kammala wanka, kasan waje mahaifinsu DR khamis yasa musamman akaje akayi mata siyayyan sabbin kayan furnitures, da shatara na azziki ta dawo ta tare a sabon gidanta, inda suka suka shigaba da gudanar da rayuwan auransu cike da kulawar juna.

  ta fara karatu a fannin kasuwanci, inda kuma yake daurata akan wasu harkokin kasuwancin tun yanxun, makarantar tama tuni akai nisa da karatu, ummeetah nada hannun kyauta da taimako, don haka ko yen uwan mijinta sunsha abin azziki, harda munat data bude mata wani tamfatsetsen beauty saloon, kullum cikin tallafi da taimakon jama'a sukeyi, shima nashi bangaren hanyoyin azziki nata dada buduwan mishi, sai godiyan Allah.

  kafun wani dan lokaci sunan Ummeetah ya fara zaga ko ina, musamman data kasance mai karacin shekaru, rugar suma ta gina makaranta both boko da islamiya, harda wani karamin clinic data gina musu, tuni yen uwan Affanta suka kama kansu, don yanxun kam rijiya ba wajen wasan makaho bane, a wannan lokacin ne kuma Baffah lado yace ga garin ku (Allah kasa muyi kyakyawan karshe, Ameen.)

   Zahra nada shekara daya da rabi, Umeetah ta samu ciki, dole ta yayeta, yanxun cikinta harya tsufa don yana cikin watan haihuwa ne, kullum cikin tattali da kulawa take, musamman da akayi hoto akace yen twins ne, mutumin kamar ya zuba ruwa a kasa yasha don murna.




                          ***
  A gajiye ta bude motar ta fada tana zama da rufo kofan, duk ta gama gasuwa da zafin rana take fadin,,

  Surayya kin wahalar dani da yaw, a'i da ta wajen junction din arean mu kika zo da bansha wuya haka ba, tana mata wani kallon yatsina da kada makullin mota take fadin,,

  hmmm, Suhymah kenan nie baxan iya zuwa wannan baraket din arean naku ba, don Allah jube yanda kika koma, ta karisa maganar da nunata da dan yatsa, murmushin takaici sukayi su duka, surayya na fadin,,
 
  namiji kanin ajali, namiji ba dan goyo ba, wanda ya dauki miji uba tabbas zai mutu maraya, sai lokacin Suhymah ta iya fadin,,

  duk me kuma ya kawo wannan maganar, tabe baki tayi tana daga hannun arebain gown din dake jikin Suhymah wanda ya kode stones din jiki duk sun zazzare, tana fadin,,

  da wannan mara mutuncin mijin naki nakeyi, duk son da kike nuna ma guy din nan, ya rasa dame zai saka miki sai wannan, shi yasa ban taba shu'awar yin aure ba, Suhymah da tayi dan tsaki tace,,

  plss mubar topic dinnan, naji dadi sosai kawas da kika nemi inda nake, kinxo a dai dai sanda nake bukatar taimako, a yatsine tace,,

  kawas meye damuwar?, sai data numfasa kafun tace,,

  wlhy Najma ce ke asibiti, kusan two months da suka wuce taje kunna gas zata daura girki, kinsan halin sangarcinta bata iya komai ba, shine fa wuta ya dawo mata, a halin da yanxun ake ciki gaba daya fuskanta yayi damage, kuma kudi ake nema masu kauri ayi mata plastic surgery, gashi kinsan yanayin yanxun komai sai a hankali, surayya in fada miki gaskiya sai inyi almost 2days ban rike 100Note na kaina ba, ta karisa maganar da zallar hawaye cikin idanunta.

  hmmm, toh ke yanxun ba kina a'iki ba?, kanta ta jinjina da fadin,,

  surayya baxan boye miki komai ba, ina a'iki a wata karamar ma'ikata, to amma kudin ne duk ba masu yawa bane, ga hidiman jikin dad dinmu, a halin da ake ciki yanxun ko makaranta su zahira sun daina zuwa saboda school fees, yanxun haka kin ganni nan ina yawon neman babbar a'ikine, duk inda naje surayya sai an hareni da wani manufa kafun a daukeni a'iki, hawaye suka wanke mata fuska muryanta na rawa tace,,

  surayya wai me yasa jama'a basu da tausayi ne, doctorn fa da yake kula da case dinta, har yace zai taimaka mana, kawai sai na samu labarin zahira yake kokarin lalata ma rayuwa, bai isheshiba sai ya hada dani, duk don zai taimaka mana, haba wannan wacce irin rayuwa ne, ta karisa maganar cikin kuncin rayuwa, ajiyar zuciya surayya tayi da fadin,,

  toh a'ini banga laifin su ba, yanxun rayuwan ne bada in baki, nima da kika ganni nan, wani tsohon minister ne ya tsaya mun a case dina harna kubuta, amma ina fada miki uwar kungiya ana can prison har an sauya kamanni, ta zaro wani hoton huge man tana jefa mata jikinta da fadin,,

  gashi nan, sunanshi larex baron, gani daya yayie miki hotunan nan da kika turo mun jiya, kinga dai a wusussuke kike ko, amma guy din nan ya rude, kawata kina da sa'a a rayuwa ina fada miki, akwai kudi fah, kixo kawai muje a dama dak……...

  karya ne Surayya, ta katseta tana jefa mata hotan a jikinta itama kafun ta daura da fadin,,

  nie Suhymah, abin da banyi da kuruciya bane zanyi yanxun, haba Surayya kyamun fada a'i, wlhy don baki san yanda na tsani kazantar nan bane, ina secondary school ko hannu nah namiji ya rike sai munyi dambe, dambe mukeyi in fada miki, na gummace in kare a tsiyace da in fada wannan harkan, nidai yanxun ina rokanki kie taimaka mun koda bashin kudi ne daga……...

  banda shie, Surayya ta katseta itama tana daurawa da fadin,,

  tunda ance miki ga hanyar azziki, kin kawo wasu maganar banxa to baxan bada ba, saiki dakeni kie diba, cikin sanyi Suhymah tace,,

   babu maganar duka na barki lafia, amma nikam Allah ya nufeni da rahama, in sha Allah baxan kara koma ma wani zunubin ba, kema ina miki fatan shirya da sannu zaki……..., bata kai karshe ba ta daka mata tsawa da fadin,,

  oyah madam get loss from my car, da mamaki Suhymah ta bita da kallo, wani kunci na taso mata a zucci, daurewa tayi tana fice mata a mota, ta figi motar da fadin,,

  a haka zaki mutu ba a taimaka muku ba, harda su tsitta yawu ta wuce abinta, Suhymah ta runtse idanunta tana bin kwatalallen motar Surayya da kallo, bacin rayuwa ita har yaushe zata mata wulakanci har haka, kawai saita rushe da kuka, ta juya kenan zata karisa wajen wani dan tudu ta zauna, yer plat shoe din dake kafarta ya katse, a haka ta karisa wajen tana zama tare da cin kukanta harya isheta.

  mikewa tayi tana cigaba da tafiya, tama rasa ina zata dosa, ga takalmi a katse, horn din wata jeep ce data tsaya a bayanta ya sanyata juyowa, driver dake gaba yayi winning glass din motar kasa yana fadin,,

  madam kina bukatar wani taimako ne?,,

  hmmm, ta fada cike da takaici, tafa gaji da rainin wayyon wadannan Al-hazan, sai kace tana mannawa a goshi ita bazawarace, basu iya komai ba sai dai suga mace akan hanya suyi kokarin maida itamistress din……, drivern ya katse mata tunanin wajen fadin,,

  Haj. ke muke saurara, mai gidan yace in kina da bukatar zuwa wani waje ne ki shiga mu rage miki han...……,,

  baxan shiga ba, nace baxan shiga ba, ana dole ne, don Allah malam ja motarku kubar wajen nan, tunkan ban muku wulakanci ba, da sauri yake fadin,,

  kiyi hakuri ranki shi dade, a hankali akai winning glass din baya kadan, aka sako mata wani compliment card, sannan aka maida tintet glass din aka rufe, driver na bada sakon da aka bashi da fadin,,

  madam mai gida yace gashi nan, in kina bukatar wani taimako daga gareshi, zaki iya samun shi a wajen dake cikin katin nan, daga haka ya maida glass din nan ma ya rufe tare da jan motar ya bar wajen, kamar ba zata dauka ba sai kuma tasa hannu ta dauka,,

  A A Sadeeq Enterprise, a firgice ta zaro idanunta, tana toshe bakinta sanda ta karanta abin dake saman katin,,

  Sadeeeeq Sadeeeeq, ta fara kiran sunanshi hopelessly, amma ina motar ta mata nisa, kuka takeyi sosai tana cigaba da dingisa kafa, kai tsaye ta wuce companyn nashi, dake nan na branch din garin Abuja.

  sai dai kash, sun sanar mata yana Mr&Mrs galaxy mall da suka bude dake nan garin shima, don haka kai tsaye ta wuce can, daker aka barta taga shugaban wajen, amma tana shiga ciki sai aka kuma samun error, don mrs. dinshi ne yau a office din ba shiba.

  sun firgita da ganin juna, Suhymah na kallon yanda Ummeetah ta sauya da katon cikinta, yayin da ita take kallon yanda Aunty Suhymah ta kode ta lalace, kuka kawai ta sanya, batai kasa a gwiwa ba ta zube nan tana rokanta gafara, da zayyane mata duk halin da take ciki, Allah sarki Ummeetah sarkin tausayi itama kukan takeyi ta duke a wajen tana fadin,,

  Aunty Suhymah don Allah kie tashi, in sha Allahu zan taimaka miki, kinyi wauta da baki shiga motar ba sun rage miki hanya, don Airport zai wuce a lokacin shida zahra, zasu ma Irfan visting, amma next week in Allah ya yarda zai dawo zaki ganshi, ruko hannun Ummeetah tayi da fadin,,

  Yer uwa nah in rokeki wani abu?, da sauri Ummeetah ta daga kanta, ta cigaba da fadin,,

  don Allah kisamun baki kie roka mun alfarma na koma gidan miji nah, duniya ban san son wani da namiji ba sai sadeeq, yana da kirki yana da

Please Login or Register in order to submit comment