Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta zaro wani kakkaurar dadduma ta shifida bisa, sannan ta kara da zannuwanta, ta ninke wasu ta sanya su sama matashin da sa'ade ta kawo mata.

   a hankali ta maida kai ta kwanta tana sakin ajiyar zuciya, ta lumshe idonta sanda take tuna, jiya uwar haka tana kwance cikin jikin mijinta, koma sai yaushe zata kara ganinshi oho, dan tsaki tayi tana kauda tunanin da fara jero addu'an bacci, kafun wani bacci barawo ya saceta.


***
    bangaren shima kaiwa da dawowa kawai yakeyi a tsakar dakin, kafun ya koma yana zama bakin gado, kamar zai kwanta sai kuma ya mike, yana jefa pillow bisa carpet din dake gefen gadon.

  kwanciya yayi bisa carpet din, can kuma zaraf sai ya mike zaune, gani yake kaman bai mata adalci ba inhar ya kwanta saman carpet din, don baisan a inda zata kwana ba ita.

  saman tyles ya koma, yana daura kanshi bisa pillow, zuciyarsa na faman kai komo da tunanin halin da yer jama'a zata kasance, ganin baccin ya gagari idonsa, ya sanya shi mikewa ya dauro alola tare da kabbarta sallah, don shi yake tunanin zai fiye mishi a rayuwa.

  Asubar ranan daker ya mike tsaye, saboda rikewan da bayanshi yayi, gashi sanyin tyles din had'e da damuwan da yake ciki, na neman saukar mishi da wani zazzabi, da wannan ya gabatar da sallah asuba.

  karfe 7am dot a falon Abba yayi mishi, cikin shigar zuwa office, shima Abban yana falon wanda ya futo don ya saurare abin dake tafe dashi, a natse ya dago kai, cikin kwantacciyar murya yake fadin,,

   Abba don Allah, wani alfarma naxo nema a gareka, dukkan hankalinshi nakan sadeeq din yace,,

  ina sauraron ka, Allah yasa befi karfi na ba, da sauri yace,,

  in sha Allah baifi karfin kaba Abba, dama alfarma nake nema, shin ko zan iya ma ummeetah hidima, ko da banje inda take ba, insa a mata, Abba kaga barinta a wajen nan ita daya yana da hadari, shiru ya biyo falon na kusan minti uku, kafun Abba ya nisa da fadin,,

  shikenan hakan yayi, zaka iya mata hidma, sannan na sassauta maka, zaka iya sanya wani daga bangarenka daka amince da ita/shi, suje inda take, amma da sharadi, ban yarda naji ance kun hadu ba, ko kaje inda take, da sauri yake fadin,,

  Abba in sha Allah zaka sameni mai biyayya a gareka, nagode da wannan damar daka bani, Allah ya huci zuciyarka, da murmushi kan fuska yake fadin,,

  tashi kaje, Allah ya muku albarka, mikewa yayi da fadin,,

  Ameen, daga haka yasa kai yabar falon, sashin maami ya nufa, don yana bukatar ta samo mishi wata amintacciyar dattijuwan daza taje ta zauna da ummeetah.

   bai jima sosai a nan ba, ya futo yana wucewa wajen motarshi da dialing numbern dake rubuce da mahfus, yana dagawa suka gaisa ya daura da fadin,,

  yawwa mahfus ka gane, plss ina son wasu ma'aikata daga cikin masu gina estate din nan na Abuja, shiru yayi kafun yace,,

  a'ah, ina bukatarsu da yawa, wani ginin gaggawa nake son suyi mun, kubar koda kadan ne daga cikinsu a nan, yayi dan murmushi sanda yake fadin,,

  aha, good, daga nan ya sauke wayar, yana cigaba da dialing wasu numbern, harya shiga motar da driver yaja suka wuce.



*fatan alkhairi*

share
comment
vote

*Matatace 2019*
Na meemartjj
[14/08, 14:29] Dala Grp: 🕯🕯🕯
    *MATATACE*
          🕯🕯🕯
  

story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjj 

*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty Ummeetah any my Fa'ixation._

*_I really hate these words:_* (Wahalar tayi yawa.)
*_Allah shi kyauta, readers namu ina gaisuwa._*

page 67~68

__________Hayaniyar tsayuwan motoci ne, ya farkar da ita daga baccin data koma, wajajan 9am, da sauri ta futo tana bin motocin da suke sauke blocks tare da wanda ke zube yashi da kallo.

  can ta hangi Baffah lamido, wanda ya kariso inda take suna gaisawa cikin harshen yaren su, tare da mata yer bayani, yana bata handbag dinta data barshi dashi a motar Baffanta jiya.

  gefe ta koma tana budewa, da rafan kudi yen 1-1k ta fara karo, sai wayarta, da wata yer farar takarda dake zabga kamshin turarenshi, taci kukanta sosai sanda yake mata bayanin hakuri da juriya kan lamarin daya shiga tsakaninsu.

   ta daga kai tana kallon filin da yace mallakinta ne, yasa a kammala mata ginishi, nan daba da dadewa ba ta koma, don baya bukatar tayi azumi dake gabatowa a wannan gidan, in sha Allah komai zaizo da sauki, da zaran ya samu lokaci kuma zaizo ya ganta, wannan kalaman nashi na karshe sune ta gagara ganewa.

  tayi kuka harta koshi, nan kuwa yen uwan Affahnta suka sanya tsiyar ba za'a gina filin ba, wai mallakin sune, daker dai dattijan garin suka natsa su, duk da sai da ya hada musu da turo securities din da zasuyi mishi maganin su, wannan yasa dole suka natsa.

  ganga ganga aka tada gini, yayin da aka shirya ma ummeetah dakin da take ciki temporary, da wani lallausar carpet sai mattress kanana guda biyu, tare da labulaye, harda wata yer karamar fridge, taja tsaki sanda take kallon fridge din da ayyana,,

  koma me zanyi da fridge babu wuta oho, batai farin ciki ba, sai da taga zuwan baba balarabu, kusan itace mace ta farko da ummeetah zata kira da uwar d'akinta, don in bata manta ba, farkon zuwanta gidan wajenta ya fara kaita, da murna ta tarbe ta suka zauna nan suna hiran bayan rabuwa.

  

   ***

  Su madam suhymah an dawo fa, ta tare a sabon gidan da aka gama kera mata, ita da tilon d'anta, ranar dai yen uwanta fal farin ciki gida su kadai, musamman da mummy tace musu, tana tunanin Abba ma ya raba auran sadeeq da ummeetah ne.

  don haka farin ciki sukeyi suna washshagalensu, yayin da suke faman kashe hotuna a gidan, basu kitchen basu bayi, ita dai oga kwata kwatan gwiwa a sake ta ma dawo.




  ***

   Sati biyu da wasu kwanki aka kammala gina madaidacin gidan, da baza a kirashi da babba ba, ya keru iya keruwa, yayin daya rage katon masjid din dake kusa da gidan suke karisawa.

   ranar da aka kai azumi na uku, ranar su ummeetah suka tare, bayan yasa an saka wani amintaccan mai gadi, dazai rika gadi a gidan, sanda suka shiga gidan ba'a magana, komai yaji masha Allah, baba balarabu sai faman yaba gidan takeyi, ummeetah dai batai wani farin ciki ba, kuka ta sanya ma, don tafi bukatar ganinshi fiye da wadannan abubbuwan.

  Haka dai tasa dangana tana cigaba da living rayuwanta cikin sauki, da kyautata ma mutanan rugar tasu, ko da azumi tayi rabon kayan abinci daya turo mata, haka ma da sallah yaxo, yanxun kam ko daga nesa tafi karfin wulakanci, harta yen gidansu wasun su sun fara shiga hankalinsu.




  ***

  Yanxun ta shiga watan da zata haihu, ummeetah fa ba zama duk tasa tsoro, bata da burin daya wuce taga randa zata haihu kusa da mijinta, kullum cikin korafin yaushe zaixo, amsar dai bata wuce ayyuka sun mishi yawa, amma yana nan zuwa, sosai yanxun abin ke damunta, sai taga kamar da wata manufa yake mata. 

  yauma daga asibiti suke nan garin Abuja data koma zuwa ANC, don sunfi kusa da nan, bayan suje an duba lafianta dana baby suka kamo hanyar dawowa, ba suyi wani nisa ba tayi karo da wani building, wanda ya sanyata sakin murmushin dole sanda take karanta,,

   A A sadeeq furnitures, dogon building ne wanda yaji glasses mai dauke da hoton furnitures na zamani, sai sunan company a sama, wajen ya tsaru sai kyallawa kawai yakeyi, ga jama'a dake ta kawai da dawowa, da alama sabon wajene kamar yauma za'a bude.

  da dan yatsa take nuna companyn da wani farin ciki, idan bata manta ba, nanne inda yake fada mata za suyi lunching din budewa kwanan nan, da sauri take fadin,,

  plss driver mu shiga wajen nan ina son ganin mijina, sai data karisa ma, ta tuna abin data fada, zaiyi magana, ta marairaice da fadin,,

  don Allah ka taimaka, nasan sunsan motar ba zasu hanamu shiga ba, bai musu mata ba ya juya da akalar motar yana amsawa da girmamawa.

  duk farin ciki ya cikata, yau za taga Baffanta, wani sabon kewarshi ke dad'a kamata, sai da akayi checking dinsu a bakin gate sannan ya karisa da motar ciki.

   ummeetah ta sauke wani ajiyar zuciya, lokacin da yake idda packing motar bayan wata sabuwar kirar optima da itama aka gama packing a wajen, wayar tane a hannunta tana kokarin lalubo numbernshi.

  A tare suka kama kofan motar zasu bude, kowa ta site din da yake/take zaune, ya rigata saka kafarshi daya waje dake sanye da dark brown din shadda, sai wata swet cover shoe, da sauri ya janye kafarshi ciki yana ruko hannunta, tare da maida kofan motan ya rufe.

   da sauri ta juyo tana kallonshi dake fadin,,

  plss suhymah rufo motar, juyawa tayi ta rufo kofan, kafun ta juyo tana binshi da wani kallon tuhuma da fadin,,

  lafia dai?, numfasawa yayi kafun yace,,

  No, drivern dana a'ika yakai ummeetah hospital ne, na gansu a wajen nan, kuma bana son su ganni, wani yar tayi da idanu tana dan bata rai, kafun ta koma tana lafewa jikin kujera da dan guntun tsaki, ya sauke wani ajiyar zuciya da furta kalman,,

  Alhamdulillah, dai dai sanda kiranta ya fara shigowa wayarshi, gaba daya ya wani rude, ya rasa ta in dama zai fara, shin ya dauka ne ko yaya, mema to zaice mata.

   komawa yayi yana kishingida da kujera tare da runtse idanunsa, yana hadawa da matse wayar a hannunshi, lokacin da yake jin bugun zuciyarshi na dad'uwa, komai a idanun suhymah ke faruwa dake satan kallonshi ta gefen ido, tana cike da al-hinin irin rikirkicewan da taga yayi.

  bangaren ummeetah kuwa tun sanda taga ya koma cikin motar jikinta yayi sanyi, kiran ma ta gwada ne kawai, sai yanxun ta fahimce ganin tane baya son yie, sagale take da waya a kunni, wannan shine kira na biyar da tayi mai kuma bai daga ba, cikin sakewan jiki ta sauke wayar da fadin,,

  muje kawai, driver ya juyo da sauri yana fadin,,

  na'am, runtse idanu tayi kafun tace,,

  mu tafi ka mai dani gida, bai kara cewa komai ba yaja motar suka bar wajen.

  sai daya tabbatar da motar ta karisa futa daga companyn sannan ya sauke ajiyar zuciya suna futowa, addu'a kawai yake Allah yasa bata gane kafanshi ba, don yasan halin wayau irin nata.




    ***
     Tun a motar take kokarin danne damuwarta, suna isa gida driver yayi packing ta fice, yau ko dan sannu da driving din bata mishi ba, ta wuce gida tana knowking gate din, mai gadi dake faman jera mata sannu da zuwa, ko iya amsawa ba tayi ba ta wuce ciki.

  bedroom din da yake mallakin nata ta wuce, tana shiga ta maida kofan ta rufe tana dafe bakinta da kuka ke neman kufce mata da lumshe idanuwanta, tare dasa dayan hannun tana dafe kirjinta dake bugawa da sauri da sauri.

  tafi karfin 2minutes tsaye a haka, tana sosomun kuka, kafun lokaci daya kukan yaxo mata tana rushewa.

   a zafafe tayi cilli da handbag din dake hannunta saman gadon, tana durkushewa gefen gado tare da daura kanta bisa gadon, kuka takeyi bilhalki da gaskiya, tana son tasan amsar wadannan tambayoyin,,

  shin wai auran ne yanxun baya so da ita, ko kuwa so yake su rabu ta wannan hanyar, ko kuwa ya zabi zama da matarshi ne fiye da ita, shin menene laifinta da baxai mata irin soyayyan da yake ma aunty suhymah ba, me yasa ne……...?

  da wani matsinacin kuka ta karisa tunanin tana rufe bakinta, don bata bukatar Baba balarabu ta jiyo ta, ta shiga girgixa kanta sanda take jie kaman a jikinta yanxun Baffanta ya daina sonta, cikin kuka ta fara fadin……..,,

    Affah kaga abin da yake mun ko, nima na daina sonshi, baxan kara mishi magana ba, indai yace rabuwa za muyi ba ruwa dashi, baxan kara zuwa inda yake ba, komai nashi bana so, ta shiga dube duben dakin da cigaba da fadin,,

  harda wanna gidan, komai zan bashi abinshi, har……, harma babyn nan inna haifa, koma menene na haifa bashi abinshi zanyi, sannan in tafi wani waje mai nisa, baxai kara gani naba, babu ruwan dashi tunda shi baya sona, ya daina sooooo naaaahh, ta karisa maganar a hankali tana sassauta sautin kukanta.

   kanta ta kuma mannawa da mattress din dake bisa gadon, tana sauke wani ajiyar zuciya, ta jawo wayarta tana goge duk wani phone numbers dinshi dake cikin wayar, ta cire hotonshi a screen saver din wayar, duk wani abu daya daganci nashi sai da tayi deleting, kafun tayi wurgi da wayan tana sa wani sabon kukan, hardai wani bacci barawo ya tafi da ita a haka.





    ***

  Kawataccan dinning area ne, da yaji dinning table na alfarma, mai dauke da 12dinning chairs, yana zaune sanye da wata farar shirt, sai black three quarter trouser dake jikinshi, ya zuba ma abincin dake cikin plate a gabanshi ido kawai yana kallo.

  karisowa wajen tayi cikin takun isa isa, gaba daya ta fahimce tunda suka dawo baya cikin hayyacinsa, kai tun kafun ma su dawo, ta numfasa sanda take zama kujeran kusa dashi da fadin,,

  sweetheart wai me kake tunani haka?, ur dinner is getting cold fa, yana wani faman hada rai ya kalli abincin, sai kuma ya daure yana yin one spoon, da sauri ya ije spoon din yana hadiye na bakinshi daker, tana fadin,,

  lafia?, a masife ya ture abincin yana fadin,,

  oh shet, plsss kie sanja wannan mai dafa abincin, cos da alama ba tasan komai ba, kafun tayi wani magana, ya mike yana jan wata doguwar tsaki da nufa design upstairs din dake can gefe, da ido ta bishi kafun tayi firgit din kiran sunanshi da fadin,,

   sadeeeeq, ba don komai ba sai don ganin yana kokarin sulalowa daga kan stairs din, harta mike, sai taga yaja ya tsaya yana dafa karfen stairs din, tare da dafe kanshi da yake ganin wani jiri jiri, da sassarfa ya cigaba da haurawa upstairs din.

  ajiyar zuciya ta sauke tana zama, tayi dan shiru tana kare ma abincin dake plate din kallo, kafun takai bakinta da gwada testing, dan kafada ta daga sama alamar, a'iko ba laifi, taja yer karamar tsaki tana zabga uban tagumi da tafiya duniyar tunani.

  ko dai da gaske ne dasu mum dinta ke cewa ba haka yarinyan ta barshi ba itama, jubi yanda sadeeq dinta duk ya sukurkuce akan wata yer kankanuwan yarinya, ko ita data tafi gidansu tsawan watannin da tayi, ba taga yayi irin wannan damuwar ba, duk da barazanar da mum dinta ta rika yie akan ba zata dawo ba.

   kenan yarinyan harta fini matsayi?, ta fada maganar so silent, tana nuna kanta da dan yatsa, zumbur ta mike tana fadin,,

  no never, da sauri ta nufi kitchen, rana ta farko a rayuwanta da taji tana shi'awar girka wani abu, ganin girki take mai sauki a rayuwa, ba bata lokaci ta kunna gas cooker tana daura tukunya, jollop supergetti tayi niyar dafawa.   
 
  hankali kwance ta fara a'iki, come see suhymah a kitchen, ba aje ko ina ba komai ya cukurkude mata, sai data hada da gogglising, sannan ta samu rass ta kammala girkinta.

  sai murmushi takeyi, ganinshi ido tsaf tsaf, sai dai tana kaiwa bakinta, a'i bata bari ya wuce cikin cikinta ba, ta fiddoshi waje, don wancan ma ya ninnka wanda tayi a dadi.

  ajiyar zuciya ta sauke tana zube abincin a wanke wanke, don wannan baxai cuwu ba, dai dai sanda taji door bell na faman ringing, falon ta nufa donta bude kofa.

  DR. Rayyan shine wanda ta gani, family doctorn sune, wanda sadeeq ya kira yaxo ya du bashi saboda ciwon dake nemam kwantar dashi, tare suka haura saman, sai rawan sanyi yake cikin blanket, doctorn yayi mishi duk abin daya kamata kafun yayi musu sallama ya tafi.

   idanu kawai ta zuba mishi tana kallon ikon Allah, hannu na rawa, amma yana rike da waya da faman dialing numbern dake rubuce da,,

  my fulani Girl, tasan ba kowa bace face ummeetah, sai tsaki kasa kasa yakeyi, saboda tun tana kin daga kiran harta rufe wayar baki daya, a haka wani bacci yayi awan gaba dashi, ta gyatta mishi blanket din kawai tana barin dakin.




     ***

  A hankali yake takowo daga saman stairs din, yana saukowa, sanye cikin shiga na alfarma, na wata milk din shadda, hannunsa makale da wata yer tsadaddan briefcase, murmushi ya tsaya yana saki sanda yake binsu ita da Irfan da kallo wanda ke fadin,,

  mummy ba nan zaki samun ba, a nan ake sawa, harara ta zabga mishi daga zaunen da take bisa expensive cushions din dake daga can falon, shi kuma yana tsaye tana cigaba da shiryashi cikin uniform din makaranta, tace,,

  oukk, kullum nake shirya ka sai kamun gyara, musayan murmushi sukayi yana yashe yen hakora da fadin,,

  sorry mummy, itafa aunty ummeetah ta fiki iyawa, kullum itace take mun gyara, ke kuma kullum nine nake miki……...,,

  would yhu shout up, ta fada maganar a dan tsawace, daya sashi guntse raguwan maganarshi, yana gimtse dariyanshi, shima da d'an dariya ya karisa sakkowa, ya zauna kusa da ita Irfan na fadin,,

  daddy good morning, da murmushi ya shafi kumatun yaron yana fadin,,

  my cry cry boy morning, yah, ka dain kukan aunty ummeen?, da sauri yace,,

  a'ah, daddy plss nayi missing din aunty ummeetah da yawa, plss ka kaini in ganta, ya karisa maganar kamar zai kuka, yana dariya yace,,

  karka damu, yau za muje wajen grandpa mu nemi alfarma, ya barmu ko weekend ne muje mu ganta ko?, da sauri yake fadin,,

  are yhu sure daddy,,

  yea of course dear, in sha Allah, zaraf ya kwace daga hannun mummyn tashi dake zaune kawai tana sauraran su, yana rungume daddyn nashi da fadin,,

  am so proud of yhu daddy, kanta kawai ta dafe da raya,,

  oh mya god, ba mijin ba, ba d'an ba, duk ta kwace, tayi dan guntun tsaki sanda take dagowa da zube mishi littafanshi cikin school bag dinshi, kafin ya dago yaron daga jikinshi yana fadin,,

  barka dai ranki shi dade,,

  ina kwana, shine abin data dago da fadi, kafun ta daura da,,

  ya jiki, hope ka samu lafia, shiru kawai yayi yana nazarin wasu abubbuwa, anya wannan suhymahn daya sani ce, kauda tunanin yayi yana amsa mata cikin sakin fuska.

  yana kallo ta karisa shirya yaron, ta rataya mishi school bag dinshi, tare da mikewa rike da lunch box dinshi suka futo farfajiyar gidan inda zasu hau mota.

  da sauri driver ya kariso zai bude ma yaron kofa, ta dakatar dashi tana bude motar ta sakashi, tare da mika mishi lunch box din, a saman fuskanshi aka bishi da wasu kisses sunyi biyar, kafun tace,,

  ouk bye darling, kayi karatu mai yawa kaji, da murmushinsa yake fadin,,

  ouk mummy bye bye, ta daga mishi hannu tana rufe motar, shima matsowa tayi tana bashi wani light kiss saman kunci, kafun suyi sallama, driver yaja motar suka wuce.

   ta sauke ajiyar zuciya sanda driver ya karisa fidda motar daga cikin gidan, tayi dan murmushi tana juyawa ciki, dai dai sanda ta juyo karan text massage din daya shigo wayar dake hannunta, ta wuce ciki tana dubawa.

  rasss gabanta ya wani fadi, sanda take karanta abin da yake ciki, gaba daya ta shiga rudani, wato tanan suka bullo mata ko, dafe kirjinta tayi dake bugawa da karfi tana zama gefen kujera, kafun ta rushe da kuka tana fadin,,

  wlhy karya kukeyi, baxan taba baku d'ana ba, sai dai ku fada mishi inya so ya tsaneni har abada, inma saki nah zaiyi ya sakeni, am not afraid, duk abin da za kuyi kun dade ba kuyi ba, azzalumai kawai yen sharri, ta kuma barkewa da kuka, gaba daya rayuwan ta mata kunci.




  ***

   Kai tsaye gidansu ya wuce yau, bayan sun dauko Irfan daga makaranta, zuciyarshi sai dukan uku uku yakeyi.

  suna zaune a falon Abban shida Irfan dake lafe jikin kakanshi, sai maami dake can gefe zaune, su mummy suka shigo itama biye da d'anta a bayanta, kusa da Abba ta samu ta zauna, yayin da muheet ya nemi waje ya zauna bai gaisa da kowa ba, kai gaba daya hallayyar muheet sun isheshi, don haka bai kalli inda yake ba, yake cigaba da ma jikanshi wasa da fadin,,

   kana son kaje ka ganta, da gaske kake?, ya karisa maganar cikin kwaikwayom muryan yaron, shima a shagwabe yake fadin,,

  yes Abba, plss kabarmu muje, nayi missing aunty ummeetah alot, zaiyi magana ya kuma make kafada yana fadin,,

  plsssss my sweet grandpa, murmushi su maami su kayi, har Abba daya murmusa irin na manya da fadin,,

  ouk my sweet grand child, ya dago yana kallon sadeeq, kafun yace,,
  
   a kaishi ya gaisa da auntynshi, jiki a sanyaye yake amsawa da,,

  toh Abba, sai insa driver ya kaishi, ya karisa maganar da matsinacin faduwar gaban amsar da Abban zai bashi, karaf mummy dake gefe tace,,

  a'ah, Abbansu ya za ayi akai yaro kauye, anya kuwa zai iya zama?, yayi wata yer dariya kamar ta fadi shirme, kafun yace,,

   ita wancan da take zaune a can ba mutum bace, a'i zama kamawa yake yagana, daga haka ya daura da kallon sadeeq din again yana fadin,,

  a'ah, kar kasa akaishi, kuje tare ne, zaka iya zuwa kaga matar ka, da sauri ya dago kanshi yana zubama Abban da wani murmushin farin ciki, kowa sai daya lura da hakan, da sauri kuma yayi kasa da kanshi saboda kunyar daya jie.

   sosai Abban ke murmushi da gira yake nuna ma maami d'an nata, itama dai murmushin kawai tayi tana kasa da kanta, cikin farin ciki yake fadin,,

  to Abba nagode, yace,,

  ku gaishe da mutanan rugar in kunje, Allah ya muku albarka, ya amsa da fadin,,

  Ameen, dai dai sanda muheet yasa doguwar tsaki a kufule yake fadin,,

  nifa gaskiya bansan me yasa aka tsaneni ba, Abba ce nayi zaka raba auran……..., dakuwa ya watsa mai da sauri yana fadin,,

  kaga naka, shashasha kawai zaka barni in karisa magana na, ko a'ah, bubbuga kafa ya shiga yie da turo baki,,

  nidai nidai gaskiya gidan nan ba'a sona, mummy tace kace, zaka aura mun wata yer gidan mal. tanimu, to nie gaskiya ko yer gidan mal. tanima ne bana so, na hakura da auran gaba daya, tunda ba'a kauna na, gaba daya shiru su kayi suna zuba mishi ido, kafun Abba ya zafafo da fadin,,

  baka isa ba, tunda nie na haifeka bakai ka haife niba, sai anyi auran nan inhar ina numfashi, don ma ka samu yarinya yer mutunci zata rufa maka asiri, mikewa yayi zaraf kafun ya daga dan yatsanshi da fadin,,

  to nie kuma na rantse yau aka daura auran nan, ba za'a kara koda kwana daya ba, sai na saketa saki har uku gyam, ba Abba ba harta sadeeq sai daya girgixa da kalaman yaron, a zafafe ya mike ko kafun muheet ya samu damar arcewa, ya cafko wuyar riganshi, mari kawai kakeji ta ko ina yana fadin,,

  kana hauka ne, mahaifin namu ne ke fada kana fada, are yhu mad!, kokarin kwatar kanshi yakeyi da faman furta kalman,,

Allah ya isa, ina baya ma jie, harda maami dake faman mishi magana ya kyalleshi, mummy kuwa ganin za a sabauta mata d'a, ya hada da garu sai jibga yakeyi, ya sanyata saka kuka tana fadin Abban ya mishi magana.

  daker ya kyalleshi bayan Abba ya tsawatar mishi, muheet da fuska ta kukumbure ya sanya kuka, da d'an yatsa yake nuna sadeeq din da fadin,,

   nie ko nie ko, wlhy saina nuna maka nie dan halas ne, sai kayi kay nada……...,,

  get out!, shine abin da Abba ya fada yana nuna mishi hanyar waje cikin tsawa, da sauri muheet din ya fuce, yana rakashi da kalaman,,

  nonsense, inhar kana tunanin karfina ya kare dazan iya hukunta ka, to ina da wanda zansa yayi mun maganinka, sai kuma ya dafe kanshi kamar zai fadi, da sauri sadeeq din ya rikeshi yana taimaka mishi ya koma zaune, da faman jero mishi sannu, maami ta karisa kusa dashi da sauri, dai dai sanda suka jiyo

Please Login or Register in order to submit comment