Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sannu da zuwa, maganar tane ya dawo dashi hayyacinsa, ya dan sakin hannun kofan, da dan murmushin kan fuska, kamar zaiyi magana kuma saiya fasa, hannun kujera ya isa ya zauna, itama cikin takun sanyi ta iso wajen, ta dan langwabar da kai tana fadin,,

   ka gaji da yawa ko?bari na kawo maka ruwa kasha, gaba daya mamakin yarinyan yakeyi, ita kanta bata sanin sanda take wasu abubbuwan, harta juya taji yace,,

   Humaira, juyowa ta danyi, ya dan daga hannu da daga kafadu sama kafun yace,,

   baby am speechless, gaba daya abin nashi dariya ya bata, amma sai tayi sauri sanya tafin hannuta tana rufe fuskanta don kunya, ya mike yana fadin,,

   muje dinning din kawai, sauke hannunta tayi tana mika mishi hannu da fadin,,  

  to kawo hulan in kaima ciki, ba musu ya mika mata, har tayi hanyar dakinshi da suhymah, yace,,

   no banan zaki kaimun ba, da idanu ya nuna mata dakinta, dole can ta wuce da hulan, da idanu ya bita harta shige kafun ya sauke wani ajiyar zuciya yana wucewa dinning area.

    ita tayi saving dinsu, hankali kwance Irfan ke cin abincin shi, amma shi saiya zuba tagumi kawai yana kare mata kallo, ta zauna itama can gefen Irfan tana cin nata abincin, duk ta kasa sakewa saboda idanun daya zuba mata.

   ido ta dago caraf suka hada dana juna, da dan yatsashi yake nuna mata lips dinshi yana daga mata giranshi, alamar me tasa a lips dinta? dan taba fuska tayi, cikin idanunta yana iya hangen tambayar, be maka bane? da sauri ya dan girgixa kanshi yana manna mata murmushi, tare da lumshe idanuwa yana budewa, alamar abin yayi mishi, sosai tasa murmushi tana cigaba da cin abincinta.

   ta gefen idanu kawai take kallonshi, ya kasa cin abincin, har sanda Irfan ya kammala cin abincishi ya tafi wasa, ture nata plate din tayi dako rabi bata ciba, ya dan kalli plate din kafun ya maida dubansa kanta yana fadin,,

   ya dai?dan bata rai tayi kafun tace,,

  bakomai, kawai dai abincin ba dadi ne, da sauri yayi one spoon, dan jim kafun ya kalleta yana fadin,,

   Humaira abincin nan akwai dadi sosai, ta dan turo baki tana fadin,,

   to bakai naga kaki ciba, ije spoon din yayi yana murmushi tare da folding hannayensa bisa table yana din yace,,

   a'ikece, wannan kyaukyauwan kwalliyar taki ta hanani cin abinci, sai dai in zaki bani a baki, zaro ido tayi waje, ya make kafada da fadin,,

   yes, kinji na fada miki serious indai baki bani ba, to baxan iya ciba, gaba daya kwalliyar nan naki ta rikirkitani, mikewa tayi kamar zata bar dinning din, sai dai ta daure tana dawowa kujeran kusa dashi, shi kanshi bai taba tunani ba, hannu yasa ya shafi yen kitson kalaban da suka ziraro ta gefe da gefe suna faman lilo, kafun yace,,

   baby wlhy kinyi kama da yer fillo, sosai maganar ta bata dariya, wanda yasa dole sai data murmusan da yen hakoranta suka futo, sannan dimple dinta ya lotsa sosai, ya zaro ido da wani big smile yake fadin,,

   wow, baby i saw that beauty, hannu tasa sosai tana rufe fuska, kafun ta cire tana wani dan mazewa, sai data sanja mai wani abincin don wancan yayi sanyi, kafun ta diba a spoon tana kaiwa bakinshi, zaro ido yayi da mamaki, kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru.

   kallonta kawai yakeyi sanda ta fara bashi abincin, yana iya hangen iya dakewan da takai zuciyarta duk don ta faranta mai, sanda ya amsa zai bata nan akai daru wajen kunya, daker tayi one spoon, kafun su cigaba da cin abincin cikin faranta ma juna rai.

    Sai dare kamar kullum madam ta dawo gidanta, tana faman wani daddaurewa, baibi ta kanta bashidai tunda yaga gudan jininshi lafia shikenan, daga baya da taga bai magana ba, itama saita share ta cigaba da futa abinta kullum ba shamaki, shima ta bangarensa sabgogin gabanshi ya cigaba da gabatarwa, don yen kwanakin yana da ayyuka sosai a office, tare da cigaba da amsar kulawa na musamman daga uwar gida ummeetah.

    

                         ***

    Door bell din gidan ake faman latsawa, karan duk ya dameta, ga na kamshin kwan da take soyawa, duk ya gama addabar zuciyanta, da sauri ta kashe gas cooker, tana futa don ta bude kofan.

    da fuskar madam tayi karo dake faman blushing, suna hada idanu ta wani hada fuska tana fadin,,

  oya bani waje in wuce, sannan ta dan juya tana mana bayanta magana da fadin,,

   salma ku shigo, su ukune harda matar DR. khamis  suka karisa shigowa, ummeetah ta gaishesu dukkansu cikin sakin fuska suka amsa mata, kafun ta maida kofan ta rufe tana juyawa ta koma kitchen abinta.



       _over nake jin dadin comment, kuyi hakuri da yanda kuke jina jefi jefi, abubbuwa ne suna da yawa, sannan wasu suna so in rika bada daily update, to amma ina da eye problem kuma, dole sai da lallabawa, ina fatan kun fahimce nie, fatan alkhairi gareku._



comment
share
vote

*matatace 2019*
Na meemartjj
[14/08, 14:29] Dala Grp: 🕯🕯🕯
    *MATATACE*
          🕯🕯🕯
  

story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjj 

*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty Ummeetah any my Fa'ixation._


         *_To yhu my dear darling Deejaah, Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafia, Allah kasa amarya ta tare gidan mijinta lami lafia, kin huta over aunty amarsu ta ango, really gonna miss yhu dear._*


page 49~50

___________Bisa kujera suka zazzauna, ta ije jakarta gefe tana jawo tv remote dake bisa tv stand, salma dake fadin,,

   maman baby kinfa kusan sauka musha suna, dan dariya tayi cike da feleke take turo cikin da fadin,,

   hmm, salma my friend kenan, sai yau nake ganinki a gida na tace,,

  haba kinsa tun yaushe nake zuwa bana samunki, tai dan yatsina tana fadin,,

   eyyah kinsan a'iki baya barina zama, yauma bana jin dadi ne shi yasa na dawo, dan dariya salma tayi da fadin,,

   a'ikina kokari sosai, daga sabuwan key din mota tayi tana fadin,

   ba kiga new car din da aka bani ba,,

   wow, congrat, salma ta fada, mrs. khamis na karawa da fadin,,

  yhu really deserve it dear, tayi dan far tana fadin,,

   thank yhu, fadeela dake can tana bin gidan da kallon gulma tayi dan yake tana fadin,,

  auntyn mu Allah sanya alkhairi, a yatsine ta kalleta tana fadin,,

   Ameen, kafin ta dan juyawa tana shirin kwalla mata kira, sai gata dauke da tray tare da drinks&cups, bisa center table din dake wajen ta ije musu, zata zuba salma tayi saurin fadin,,

   a'ah mungode hakama, da murmushin ta mike suna kallon juna kafun ta wuce, har zuciyarta taji yarinyan tayi mata, fadeela dai da mrs.khamis kallo suke kare mata, da sauri mrs. khamis ke fadin,,

  kai mummyn Irfan kinga yanda kuwa house girl dinki ta canxa, salma dake zuba drink cikin cup ta dago tana kallonta da fadin,,

   kai shaakirah, tace,,

  Allah aunty ina fada miki ta sauya sosai, suhymah tayi dan dariya tana maido hankalinta garesu da fadin,,

   a'i tasan yanayin yarinyan, gaskiya ta fada, kinsan US ba wasa baa, bare kuma irin wadannan in suka samu waje, ta karisa maganar da dan dariyanta, dai dai sanda ya futo daga bedroom dinsu, yana dan sauke hannun longsleeve din rigar dake jikinshi, ruwan dake hannunshi yake nuna alamar alola yayi, kanshi a kasa yake kwalla mata kira da fadin,,

   Humaira, daga can kitchen din ta amsa da,,

   na'am, dai dai sanda ya dago kanshi, sai lokacin ya sanma da mutane sun shigo, cikin mutunci suka gaisa, fadeela ce tayi dan kasa da murya tana biye na bakin su misha da fadin,,

   uncle sadeeq, sai inta kiran waya ba'a daga mun, nace ko nayi laifi ne?, dan murmushi yayi yana dan daga gira sama alamar tooh, itakam madam sai ciccika take baibi ta kanta ba yake fadin,,

   a'ah baki kira bane, inkin kira a'i dole a daga, sosai taji dadi tana satan kallon inda suhymah take, wacce ke jan dogon tsaki, dama duk tsokalan fada takeyi, ta kuma wani rankwafar da kai tana fadin,,

  ouk an bani damar in kira kenan duk lokacin dana s……..., da sauri ta katse maganar da fadin,,

  sweetheart plsss tafee mana inda zaka, ta karisa maganar tana dalla mata harara ta gefen ido, murmushi kawai yayi, kafun yace,,

  angel a'i bamu gama maganar ba, kuma hada fuska tayi, fadeela zatai magana, salma ta katseta da fadin,,

  ke fadeela kie ma mutane shiru, ita dai shaakirah dariyan ciki kawai takeyi, dai dai sanda ummeetah ta futo daga kitchen, tana dan yarfe ruwan dake hannunta da fadin,,

  Baffah gani, sosai ya kalleta kafin ya dan waske yana tafiya da mata yer alama da hannunshi, kai tsaye ta wuce dakinta, shi kuma yayi hanyar futa yana musu sai anjima, yayin da matarsa ke daga mishi hannu da fadin,,

  bye sweetheart, shima dan daga mata hannu yayi yana karisa fita, kusan 2minutes itama ta futo daga dakinta tana bin bayanshi, da ido sa'idawan suka bita da kallo, yayin da madam kecan ta wangale baki suna hiran office da salma, fadeela ta kalli shaakirah suka hada ido, sai kowa ta waske tana dariyan ciki.

     yana tsaye wajen entrance door din, murmushi suka sakar ma juna, tana mika mishi agogon data dauko mai, maimakon ya amsa saiya mika mata hannun, da gira yake mata bayanin ta sanya mishi, ba musu ta shiga daura mishi, a daddafe ta gama sanya mai tana fadin,,
  
    tom a dawo lafia, da murmushi yake fadin,,

  take care, ta juya da sauri, yayin da shikuma yayi ta wajan motarshi, hannu ta sanya cikin azama tana dafe kirji, tare da kokarin danne aman dake taso mata, tana faman kakkari tayi saurin wucewa ciki.

    kamar walkiya ta shigo ta shige daki, gaba daya na falon daskarewa sukeyi a wajen, suna binta da kallo, banda madam suhymah data bita da kallon tabe baki, salma tayi saurin fadin,,

   bata da lafia ne?yatsina fuska tayi tana fadin,,

   oho mata, kusan yaran nan in suka samu waje, yanxun haka wani ciye ciyen na fama taje tayi, tswww, sai kuma taja tsaki, fadeela ta jinjina kai bata sanma sanda take fadin,,

   kai amma aunty suhymah nidai ina matar gidan nan, baxan iya ije yer a'iki irin wannan ba, wani dan dariyan yake tayi kafun ta kyace dame gaba dayan, tayi mai isarta sannan ta dago tana fadin,,

   akan me?sai dai in baki yarda da kanki ba, ko kuma baki yarda da mijin kiba, amma nie ina fada miki zan iya ije wacce tafi wannan babu abin daya dameni, abin dana sani kawai shine yarinya ta bautu, tayi kuma abin daya kawota, zata kara yin magana salma tace,,

   pls abar wannan maganar, da wannan suka sanja hiran, ita kanta salma halin suhymah ya soma bata haushi, amma akwai ranar dana saninta na nan zuwa.

   itakam ummeetah sai da tayi mai isarta a bayi sannan ta tsaya, lokaci daya tsanar kwai ya dirar mata a zuci, dama Irfan ne yace yana son cie, ta soya mishi, jie tayi ko kitchen din bata kaunar komawa, Allah yasa ta gama a'ikinta don haka sai ta koma ta dan kwata, da jirin dake dibarta.



                       £££

   Tsaye yake cikin wani kayataccan dakin na alfarma, glass din window yake facing dake kallon waje, wanda aka ja cotton dinshi gefe da gefe  sanye cikin shiga ta alfar na wata tsadaddan shadda, hade da babbar rigan daya sha mayan a'iki.

    ransa bace yake, yayin da fuskarsa ke nuna tsananin damuwan da yake ciki, a hankali ya sauke wani doguwar ajiyar zuciya, yana juyowa da facing maami dake zaune bakin kayataccan gadon dake dakin, sai daya dan nisa kafun yace,,

    wai meyasa ne?me yasa kullum mutallab bashi da wani buri daya wuce yaga ya tada mun da ciwon hawan jini na, eyee fisabilillah haj. indo mutallab kadai na haifa ne, dazai rika dauko mun rigima da maganganu, tsakani da Allah fa, sosai fuskarta ya nuna alamar damuwa tana fadin,,

   hakuri za kayi Abban kamalu, dole sai da addu'an mu garesu komai zai tafi dai dai, fatan shiriya kawai zamu cigaba da mishi, dan shiru yayi kafun yace,,

  amm am amma me yasa bana fuskantar irin wannan cin mutuncin daga sauran yen uwansa, shiko koyi da dan uwanshi bazai yiba, yana kallon yanda Abubakar ya kafu da kanshi, banda kamaluddeen da yake kaninshi, danme shi baya irin wadannan shashancin, da yatsa yake nuna kanshi da fadin,,

   ace kamar dan dana haifa, ban isa in fada mishi ba, kaman mutallab ne yake da kudin dazai kama club ya kwana da mata, sannan harya biya ma wasu ma suyi tsiyar da ransu keso, daga karshe ma a kare da dambace dambace, yanxun bacin Allah ya tsare, d'an gidan pro. Mu'azzam daya rotsa ma kwalba akai, inda wani abin ya faru, daya jawo ma kanshi muma ya jawo mana ko, yaja doguwar ajiyar zuciya da cigaba da fadin,,

   kai kai na gaji da halin mutallab, kullum lamarinshi dada tabarbarewa yakeyi, ya karisa maganar da juyawa yana cigaba da kallon window, maami ta numfasa tare da jinjina kalamansa kafun tace,,

    Abban kamalu kar kace haka, hannunka baya taba rubewa ka yanke ka yar, in sha Allah komai zai dai daita, yaran yanxune ka haifesu baka haifi halinsu ba, ta danyi shiru kafun ta cigaba da fadin,,

   nie da nace, Abban kamalu me zaisa baza a mishi aure ba, kila ta hanyar haka ya natsu ya dawo kan hanya, yafi minti biyar kafun ya juyo yana fadin,,

   hakane maganar kie, nie nayi wannan kuskuren, don kwanakin baya ya fada mun yana son aure, harya zaba yarinyan ma, amma ganin mahaifyarshi bata son abin saina shashantar da zancan, wanda bai kamata kuma in biye mata ba, amma yanxun in ganin dole haka za ayi, ya kariso inda take zaune da amsar hulanshi dake hannunta tare da karisa fadin,,

   ina son a samo mun bayani akan yarinyan nan da tai miki a'iki, kwanan nan in sha Allah za'a tura magana wajen magabatan ta, ya gyara zaman hulanshi da kyau yana fadin,,

   ina fatan kin fahimta, a daskare a wajen ta daure da fadin,,

   in sha Allah, za ayi yanda kace, da murmushi yake fadin,,

  good uwar gida nah, ina so wannan ya zama sirri a tsakaninmu, na lura harda tarbiyan yagana ke taimakawa wajen lalata mun yara, tunda itace mai mara musu baya akan koma menene, maami ta mike cikin sanyin jiki tana fadin,,

  Abban kamalu anya ayi haka kuwa?kallonta yayi da kyau yana fadin,,

  of course, tasa burinta na hofi kan sai dai mutallab ya aure yer manya, nie kuma wanda zata dawo mun da tarbiyan yaro nah mai kyau da tsafta nake nema, naga yarinyan a wajenki ta taso kuma nasan irin tarbiyanki, fatana shine iyayanta su amince mana, dan nisawa tayi sanda take takamai zuwa bakin kofa da fadin,,

   to Allah yasa a dace,,

   Ameen, ya fada kafun suyi sallama, ya wuce wajen a'iki, ita kuma ciki ta koma sai data gyara ko ina fes a dakin, sannan ta rufe kofan tana komawa sashinta.
     


                           £££

   Motacine na kyace raini, cikin shiga ta alfarma, gaba daya yen uwan Alh. Aminu sa suka je a matsayin magabatan muheet tsayawa kawai su kayi suna kallon irin wannan kuryan dajin kyauyen, kamar yanda suma mutane da dama suka taru suna kallonsu, dai duniya zakice basu taba ganin mota ba ko kuma irin suturan dake sanye jikinsu, da wannan dai suka isa ga Baffanin ummeetah don yin maganar auren muheet daya kawo su.

      sosai sarai suka san mahaifin su sadeeq, don haka koda suka jie sunce danshi suka zo neman ma auran ummeetah, ba wnda suka kawo sai sadeeq din, kasancewan kwata kwata basu san da maganar auren ba  sai lamarin yazo musu a sabon abu,  sunso tuburewa  amma ganin dukiyar da aka fara tsibe musu, yasa hannu bibbiyu suka amshi batun, akai komai cikin mutunci tare da tsaida lokaci, sannan yen uwa suka kamo hanyar dawowa.

   da tashin hankali Baffanin nata suka zuba ma kudi idanu, yayin da jama'an gidan sukai carko carko, wasu ma mamaki suke har yanxun ashe yarinyan na raye, su dai a'inihin masu hankalin kuma hatsabiban ciki, kasa hakura sukayi, musamman lado da yen uwanshi, da suke ganin kaman sadeeq yayi hakan ne don ya aure ummeetah yaji dadin mallake dukiyarta, don haka suka kudirce aniyar yabar ganin hakan, kudadan da aka fara basu matsayin kudin sallama, suka tattara don ziyartan babban bukkan da suka saba zuwa.



                           ***
    Jarabawa sukeyi na school, sosai ta maida hankali, duk da yawan kasalan jikin dake damunta, hakanan take daurewa, wani abin yana lura da ita.

    A hankali yake idda packing motar nashi cikin garage, ummeetah ce ta fara budo site din da take tana futowa, shima ya fato sanye cikin wasu suite masu kyaun gaske.

   saman motar ya dafa yana zuba mata ido, da take kokarin daukan mishi briefcase rike da wata textbook dinta, ta dauka tana kulle kofan site dinta, tare da dagowa suka hada ido da juna, ganin ya zuba mata ido ne, yasa tayi saurin janye nata, muryanshi ta juyo dake fadin,,

   Humaira yhu change alot fa, da sauri ta dago kai tana kallonshi, sai kuma ta dan waske, tana cigaba da takawa da barin garage din, a jiyar zuciya ya sauke, yana jinjina jan aji irin na yarinyan, kafun shima ya rufe motar yana biyo bayanta.

   ouch, ya fada da karfi, bayan ya sakko kafanshi daya bisa grass carpet din dake wajen, da sauri ta juyo a razane, idanunta a inda kafanshi ya sauka suka dira, ta kariso da sauri har lokacin yana dafe da saman kai dake faman sassara mai, gabanta ne yace wani irin rasssss, da sauri cikin zuciya take maimaita kalmar,,

  innalilah wa'inna ilaihir raji'un, Allahumma ajirni fie musibati, wa'aklifli khairan minha, ta kasa furta komai ma, sai da taga ya sauke hannunshi, ta iya fadin,,

   Baffah meya faru?murmushi kawai yayi yana fadin,,

  karki damu, muje ko, numfasawa tayi kafun tayi gaba, yayi saurin sawo hannunshi cikin nata, daga kai tayi taga shima yana kallonta cikin kwanciyar hankali, a haka suka karisa ciki.

    Tun lokacin ta fara lura da yanayinshi, ita kanta a'iki kawai take ba natsuwa, amma rabi da kwantan hankalinta na gunshi, sai da taga ya sake yana ta harkokinsa sannan ta samu natsuwa.
      
                    

     
                        ***
   Yauma zaune yake a falon, bayansa kinshingide jikin kujera, yayin da laptop ke gabanshi bisa side table din dake jikin kujeran da yake zaune, sosai ya bada hankalinshi akan laptop din, amma can cikin jikinsa da jijiyoyi daurewa kawai yakeyi.

   ta kariso wajen sanye da wasu tausasan kayan sanyi, riga da wadonshi, wanda ya tsaya mata dai dai gwiwa, sai rigar mai high neck, hannun longsleeve, kayan masu ruwan kanwa, saita daura wata light army kemoni a samansu, amma bata daure ba, wannan ya bada damar ganin kayan da sukai mata cass a jiki, kanta yane da wani dan gyale.

   da sallamarta ta zauna bisa daya daga cikin kujerun dake falon, hannunta rike da wayarsa da take jujjuyawa, shima dagowa yayi a natse yana amsa mata salamar, bayanshi manne da jikin kujeran ya zuba mata idanu, da dan murmushin jarumta yake fadin,,

   enmmata irin wannan kayan a'i sai kisa in gigice, murmushi itama tayi tana kokarin daure igiyoyin dake gaban rigar, ya dan yunkura zaune da kyau yana ruko hannunta da fadin,,
 
  come on ki barshi mana, kinyi kyau fa, ba musu ta barshi, tana mika mishi wayarsa da fadin,,

   gashi maami na gaisheka, na fada mata baka da lafia, tayi maka addu'a, dan murmushin jin dadi yayi yana amsar wayan da fadin,,

  kodai kinkai karanane naki zuwa hospital?shiru ta danyi kafun tace,,

   a'ah, kawai dai nace ne, ta dan cema kaje asibiti saboda lafiyarka, shine tace za kuyi waya, ya ije wayar gefe yana dada manna jikinshi a kujeran, kasa kasa kuma yake sauke numfashi, da fadin,,

  babyn nan kin cika wayau fa, meye maraban dame da fada, cike da dan damuwa take fadin,,

   kayi hakuri, bana son ina ganinka cikin wani halin ne, shiru kawai yayi yana kallonta, wato duk yanda zaiyi mata pretending lafiyarsa qlau, saita fahimce wani abu, ya sauke yer ajiyar zuciya yana fadin,,

   karki damu kinji, zan samu sauki in sha Allah, cike da fuskan tausayi take fadin,,

  to Allah yasa, ganin yanda tayine ya sanyashi daurewa yana zama da kyau tare da fadin,,

   come on cire wannan fuskan, nie da nake sa ran dana samu sauki, in kuka samu hutu mu danje wata trip, kin gane irin muje koda rairayin bakin ruwa, mudan shawo sanyeee, cike da muryan yangan nan nashi yake cigaba da fadin,,

   kin fahimta, irin ina tafiya kina daga dan gefe na, umm hmm muna jin dumin jikin juna koooh, ya karisa maganar yana daga mata gira sama, sosai yanda yake maganar ya sanya ta dariya, ta dan dafe bakinta tana fadin,,

   to aunty suhymah fa, a ina zamu sata, dan shiru yayi kafun ya dan yatsina fuska, da daga idanu sama alamar tunani yake fadin,,

   ummm, saimu sanya ta daga dan can gefe, saboda……..., sosai ta kalleshi, yana mata alamar wai cikinta, wani dan dariyan takeyi da fadin,,

  nidai babu ruwana, ya dan zare ido, so serious yake fadin,,

   a'iko da ruwanki, saboda har goya kifa zanyi in mu kaje, zaro idanu tayi, sai kuma ta sanya hannu tana rufe fuska, sosai ya saki jiki suna hira da dariya, duk dashi daurewa kawai yakeyi.

   kadan kadan kuma yake daddanna laptop din dake gefenshi, can dai ya kasa daurewa saboda wani zuwww zuww da kanshi kemai, ya dafe kai da runtse ido yake fadin,,

   ya salam, tsam ta mike tana dawowa gefenshi, batai aune ba kawai taga hannunta saman kanshi tana fadin,,

   jikin ko, Baffah nah sann......, bata karisa ba tayi saurin janye hannunta, tana janye jikinta data hada da nashi, dai dai sanda yake bude idanunsa a kanta, wani murmushi mai tafiyar da zuciya ya sakar mata.

   kokarin mikewa takeyi, yayi saurin sa hannu ya jawota jikinshi, boyayyan ajiyar zuciya ta sauke, tana juyo zazzafar hucin dake fita daga jikinsa, daddadan kamshin turarenta ya soma shaka, gaba daya ya fara birkice mata, hannu tasa daker tana rike hannunshi dake kirjinta cike da shagwaba take fadin,,

  nidai plss bana so da zafi, a hankali ya zare hannushi daga nata yana dada manna ta da jikinshi, cikin kunni yake rada mata,,

  plss Humaira karki tashi, stay with me, natsuwa kawai ta koma tayi, sunfi minti 5 a haka, kanta na kwance bisa kafadarshi, yayin da yake shafa gashin kanta a hankali, gaba dayansu idanunsu a lumshe suke, hawaye ne ke nema sauka a fuskarta, cikin rawar muryar take fadin,,

   Baffah plss na rokeka kaje hospital, jikinka yayi zafi sosai, murmushi yayi har zuciyarsa, yana jin dadin yanda take nuna damuwa a kanshi sosai, bude idanunsa yayi da suka sauka kan tafin hannunta dake bisa jikinsa, a hankali ya dago hannun yana kallo kafun yace,,

  Humaira kefa ya kamata nakai asibiti a duba mun ke, ya karisa maganar yana dada jujjuya hannun,,

  nie kuma?ta fada, lokacin da yake dagota da kyau, dai dai sanda suka jiyo karar motarta da take packing, mikewa ta shiga kokarin yie, da sauri ya kuma rungumota, zatai magana ya toshe bakinshi da nata.

   kasa biye ma salon nashi tayi, daker ta zare bakinta, tana danja baya, wani kallon tuhuma yake mata, duk sai taji ba dadi, kamar zatai kuka ta tausasa murya sosai tana fadin,,

   Baffah don Allah kayi hakuri, kaga aunty suhymah ta dawo, baka da lafia, bana so a kara maka wani damuwan, murmushi ne ya bayyana akan fuskanshi, itama ta mike cikin natsuwa tana murmushi da fadin,,

   Allah ya baka lafia, sai da safe, kasa

Please Login or Register in order to submit comment