Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

black american suit sai kalli sukeyi, alamun sabbi ne ya sanya su a yau.

   wata tsadaddiyar sabuwar I~phone ce a hannunshi, yana daddannawa, hotanshi yake setting kan wallpaper dake wayar, kafun ya dago kai yana kallo Irfan dake zaune gefe kusa dashi, kallonshi yayi da kyau yana fadin,,

   yawwa Irfan tell me something, sosai yaron ya kalleshi yana maido hankalinshi kan daddyn nashi, ya nisa kafun yace,, 

   yaushe aka maka allura a hannunka?, shiru kawai yayi yana binshi da kallo, hakan ya kara tunzura zuciyarsa ya daka mishi tsawa da fadin,,

   ba magana nake maka ba, a tsorace yaron ya rufe bakinshi, hawaye na wanke mishi fuska da fadin,,

   daddy am sorry, a fusace yace,,

  sorry for ur self, fada mun wani abin ka coka ma kanka ne?, girgixa kanshi ya shiga yie, ummeetah ta kariso daga kitchen din data koma ta dawo, da katon dan cikinta daya mata kyau sosai, kujeran dake kusa dana Irfan ta zauna, tare da ruko hannunshi tana fadin,,

   Irfan d'ina kaji fadamun, a school ne aka muku allura?, cikin shashshekar kuka yace,,

   a'ah, mummy ce takai ni aka mun, tace kuma kar in fada, ina fad'a zata bulaleni da cain mai zafi, kallon kallo suka shiga yie da juna, a zuciye yake fadin,,

   miko mun wayar nan in kira inji dalili, wayarshi ta miko mishi rai bace yayi dialing number, har wani kumfa yakeyi sanda tayi picking tana fadin,,

  hello, ya daura da fadin,,

   suhymah donme zaki kaimun yaro hospital a caka mishi allura, ba tare da sanina ba?, wani mahaukacin ajiyar zuciya ta sauke kafun tace,,

   kai sweetheart, wlhy har kasa na wani razana, nasha wani abinne, kaishi fa kawai nayi medical check up, shine ya zama laifi, ya runtse idanu da budewa yana fadin,,

   to donme zaki kaishi ba tare da izini naba, sannan kice karya fadamun, for what reason, yanxun basan wani irin allura bane aka mishi, ga wajen nan ya fara bashi problem, gabanta ne yace rasss, amma saita waske tana fadin,,

   sadeeq nifa don lafiyar d'anmu nayi, me zaisa ya zaba abin masifa a gareni, ta karisa maganar da dan tsaki ciki ciki, tana harare harare, ya sauke wani ajiyar zuciya yana lumshe idanu da fadin,,
 
  look suhymah, baxan jure wani abu ya faru da d'ana ba akan alluran nan, tom, daga haka ya katse wayar a zafafe, kallon yaron yayi da fadin,,

  saima na kaika hospital an duba mun lafiyanka, kafun na wuce office, go on with ur breakfast, ya karisa maganar da nuna mishi karamin mug din dake gabanshi, ummeetah ma ajiyar zuciya ta sauke da fara yin karin kumallon.


                   £……£……£

  Nata bangaren kyamm ta tsaya da waya a kunni, kafun ta yunkura tana saukowa daga makeken gadon auntyn nasu, wacce ita ke tsaye gaban safe, tana jin wayar da suhymah keyi, sosai ta kalleta tana fadin,,

    meya faru ne?, dan tsaki tayi kafun tace,,

   nida dan rainin wayaun nanne, sarkin son ye'ye, saboda yaga mark din allura a hannun Irfan, shine yake ta wani sababi, da sauri aunty ke fadin,,

   toh, ya gane wani abu ne?, dan dariya tayi kafun tace,,

   aunty kenan, tayaya zai gane wani abu, baxai taba ganewa ba, iyaka ya kaishi hospital ayi duk binciken da za ayi akai, kie rabu dashi kawai, duk na kosa gayen nan yaxo hannu wlhy, yer dariya auntyn tayi itama tana fadin,,

   karki damu, Allah dai ya raba lafia, don wannan babyn shine namu, kie samo mana wani fine baby boy din, kai ranar akwai shagali, za aga expensive naming ceremony, dariya take sosai ta nufi bayi tana fadin,,

    Ameen my aunty, daga haka ta shige bayin, ita kuma auntyn na faman murmushi.

*fatan alkhairi*

comment
share
vote

*matatace 2019*
Na meemartjj
[14/08, 14:29] Dala Grp:      🕯🕯🕯
    *MATATACE*
          🕯🕯🕯
  

story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjjlllated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty Ummeetah any my Fa'ixation._

page 57~58

   _________Kwana uku kacal ya rage biki, ta ko wani fanni anata shirye shirye, amarya munat sai dada hadewa akeyi ana hasken amarya, yayin da ango muheet ke fama da rawar kai har yanxun, da hada fatuka iri iri.

  cike da farin ciki ta tunkari site dib  mummynsu, kasancewan yau yen uwanta mantan auren zasu iso, a falo ta samu kafatanin su, suhymah dake zaune tarkashe tarkashe ana sa mata lalle a hannu, ta kalleta tana fadin,,

   umm, kaga Amaryan Abdullah, itama zama tayi tana yer dariya da fadin,,

   aunty suhymahn mu kenan, uwar gidan yayan mu, ta yatsina fuska tana fadin,,

   fadi kie kara, nice nan one in town, dai dai nan saudat ta futo rike da wani tray anci kwalliya, mummynsu dake zaune gefe tana fadin,,

   yawwa kin zube dukkan sakon nan dana baki a ciki ko?, tace,,

  yes mummy na zuba, da sauri munat ta kalle mum dinsu, bata son wannan dabi'ar na mummynsu, tasan yanxun haka saurayin saudat dinne yaxo, shine aka mishi wadannan yen barbade barbaden da suka saba, ta marairaice murya da fadin,,

   kai mummy, wai yaushe zaki daina haka ne, bafa dole bane sai ta wannan hanyar zasu samu mijin aure fa, a fusace ta yunkuro tana fadin,,

  kazan kazan kie dahiru, kaman zatai kuka take fadin,,

  mummy mahaifin Abban gaba daya, tace,,

   eh na fada, kije kie fada mishi in yaso yau ya koreni a gida,,

   Allah ya baki hakuri, ta fada ranta a dan bace, suhymah tayi mata galala kafun tace,,

   ummm, kekam munat an barki a baya, gashi mai mata zaki aura, dama dai ba sakeena ba, yanda nasan tana son Abdullah ba hakanan zata barki ba, dan dariya tayi kafun tace,,

  wlhy aunty suhymah ko kadan, kisan yer uwa da suke kwana su tashi tare, to haka muke da aunty sakeena, in sha Allah kuma sai munba kowa mamaki, wani murmushi takaici tayi, kamar ba zata kara magana ba kuma saita dago kai tana fadin,,

  amma dai Abdullah ya gama da sakeena, shikenan ya daina yayinta kenan, munat ta bata serious look kafun tace,,

   aunty suhymah tunanin kie kenan, tace,,

   yes, tunda gashi zai karo wata, mummy tayi caraf din fadin,,
 
   shareta daughter ita ta sani, taje ta koma bora, munat dai ba tace komai ba, a zuciya take raya,,

   indai tunanin kie hakane, to ke tabbas an dade da daina yayin k……..., muryan hibbat ne ya katse mata tunani dake faman kwala ihun,,

   oyoyo mama, oyoyo aunty Amarah, da sauri ta mike ta fuce da murnanta, suhymah ta rike baki tana kallon mummy dake fadin,,

  keko ga kannin uwan ta sun iso, girgixa kanta tayi cike da yatsina, na zuciya na zucci.

  

    kamal ne ya faka katuwar henesin da mijin aunty batulah ya bada a kawo su, shine ta tsaya tayi picking yer uwanta, suka wuto tare.

   Farin ciki sosai tayi da ganin yen uwanta, aunty Amrah data futo motar suka tarbi juna jikin matukar kewa, aunty Batulah ma ta futo tana faman fadin,,

  masha Allah, amaryan mu ta hade, ita dai sai dariya take tana musu welcum, aunty Amrah ta ruko hannunta da fadin,,

  kinji yer uwa muje ciki, akwai wasu sirrin dana taho miki dashi, kamal dake can yana fama da yaransu ya dago mata hannu da fadin,,

  aunty munat hi, hannu itama ta daga mishi tana fadin,,

  hi bro, ya hanya?,,

  lfylau our bride to be, dan hararanshi tayi da fadin,,

   kaiko zaka sani, dariya yakeyi sanda ya bude buth yana ciro musu kayan trolley dinsu, hibbat sai murna take taga sisters dinta, suka rungume juna da step sister dinta da suke mate daya Nabila, kafun taje tana rungume mamanta wanda suka doshi hanyar cikin gida tana fadin,,

   maman mu me yasa su khaleefa da sultan ba zasu zoba?,,

  kai hibbat d'agani kin wani kankameni, ta fada fuska daure, kwaba kwaba tayi da fuska tana fadin,,

  maman mu ina fa murnan ganinki ne, aunty Amrah tace,,

  daga ta rungume kie, kinji deja nah zo nan, nie inji dumin yeta, da murnanta ta koma wajen aunty Amrah ta rungumeta da fadin,,

  yawwa my mummy Amrah, dariya sukeyi, haka suka karisa dai dai bakin kofan suka gamu da Abba, sai fara'a yakeyi sanda yaga yen jikokinsa, nan kuwa suka baibayeshi, sai wasa yake musu, ya dibesu sukai site dinshi.

  sun karisa ciki, inda suka samu gidan yaji gyara na musamman, da sabon fenti, sun sami maami bata nan taje ganin wasu kaya da za a saima amarya, su hibbat na karisa shiga da kayansu daki.

  basu wani jima ba, aunty batulah ta matsa sai suje su gaida mummy, ba musu aunty Amrah ta mike suka wuce, amma a zuciyarta sai faman masifa takeyi, sun isketa cikin girmamawa suka gaisar da ita kaman ko wani lokaci, yayin data amsa musu cike da izza, ko hiran azziki babu.

   can saiga suhymah ta futo zasu futa galaxy mall da sisters dinta, ko kallon inda suke bata iya yiba, sai da munat tace,,

  aunty suhymah gasu aunty batulah fa, sai data danja fasali kafun ta juyo da fadin,,

  ohh sannu fa, a fusace aunty Amrah ta mike tana balla ma munat harara da fadin,,

  a'i sai kiyi, tunda bata da ido ne, daga haka ta fice, mummy tayi saurin fadin,,

  Allah shi kara, maganinki kenan, aunty batulah ta girgixa kanta da fadin,, 

   munat tashi muje, mummy sai ajima, da harara take fadin,,

  mu jima da yawa, duk suka fuce, suhymah na faman zabga musu hararan wulakanci kafun ta fara zage zage a bayansu.

    Aunty Amrah suka samu a falo dake ta faman cika tana batsewa, suma zama su kayi aunty Batulah na fadin,,

  kedai Amrahtu baki da hakuri, ranta bace take fadin,,

   haba aunty batulah na gaji da wulakancin matar nan, wai me matar sadeeq ta dauki kanta ne, da d'an uwan mu take takama, amma ta rika taka mu, tswww ta saki tsaki, munat a sanyaye tace,,

   gaskiya abun da aunty suhymah keyi bata kyautawa, a harzuke take fadin,,

  munat bama kinsan wani abu ba, kwanaki matar nan tayi matukar ban mamaki, kawata zan kira samiha, mistakly saina dialing numbern suhymah, could yhu believe yer matan nan saita katse mun kira, abin ya matukar bani mamaki, da gangar na kuma dialing, ta kuma katsewa, sai da mukai haka sau uku, nayi ninyar in tura mata da rashin mutunci ta text massage, baban su kausar yace inbar maganan kawai, amma abin ya bani haushi, aunty batulah ce tayi dan tsaki tana fadin,,
 
   ke kika ga zaki rika damuwa da lamuranta, kiba banxan ajiyarta, munat tace,,

   gaskiya aunty batulah bata kyautawa ne baxan boye muku ba, tunda taxo fa haryau bata shigo ta gaida maami ba, zaro ido sukayi da bacin rai da mamaki, a kufule aunty batulah ke fadin,,

   gaskiya maami ba tayi sa'an sirika ba, amma ba komai, a'i maami na nan da plan akan mijinta, aunty Amrah tace,,

  yawwa aunty meye plan din, kie kenkesa mana plss, Allah yasa aure zata sashi yayi, aunty batulah tace,,

   hmmm, kwanaki munyi magana da maami, tace tana son inya dawo ne, ta hada auransu da umm……, sai kuma tayi dan shiru, munat na fadin,,

  plss aunty da wane?, tayi yer dariya tana fadin,,

   saura aje amun yawan surutu, ba naga an zuba mun ido ba, aunty Amrah tace,,

  ohhh plss kie fada mana, wannan a'i maganar mune imu imu, ajiyar zuciya ta sauke tana fada musu plan din maami akan hada auran sadeeq da ummeetah.

   aunty Amrah tasa murna, don sunsan yarinyan tana da natsuwa, munat dai labari na cinta amma an bata promise, itama farin ciki takeyi sosai, kafun su barke da hiran kyawawan hali irin na yarinyan.
 

                            ***

   Tsananin murna yasa ummeetah ta rasa inda zata sanya kanta, murna take sosai zata gida taga su hibbat, maami dasu auntyn su, abin da bata taba kawowa nan kusa ba.

  sai dai inta kalli cikin jikinta, jikinta kan mutu, bata san irin fassaran da za a mata ba, kafun Baffahnta yayi musu bayanin ita wacece a wajenshi.

   ajiyar zuciya ta sauke tana cigaba da shiryawa, Irfan ne ya shigo dakin sanye cikin wasu expensive ready made, kan gadonta ya dare yana jawo sabuwar i~phone dinta, tare da fadin,,

  aunty ummee i like ur phone,,

  thank yhu, ta fada da murmushinta, inda sabo ta saba jie, tunda aka siya wayar, kullum sai yace yana son wayar, ya zuba ma cikinta idanu, kafun yace,,

  aunty ummee daddy yace, kema zaki haifo mana baby, zan samu 2sisters or 2brothers, serious take fadin,,

  haka daddy yace maka?, kanshi ya daga cike da zumudi ya mike caraf yana tsalle, tare da fadin,,

  yes, yace ke matarsa ce ta sunna, nima inna girma yace zai samo wata yer fulani girl yamun auran sunna, sosai maganar ya bata dariya tana toshe bakinta, ya marairaice fuska yana fadin,,

  aunty ummee plss inkin haifi babyn kie nie zaki bamawa, nafi son naki, bana mummy ba, rolling din gyalenta ta kammala yie, tare da amsar wayanta da yake fadin,,

  lah aunty ummee cikin wayan ki hotan daddy, ta jawo hannunshi ya sauka kasa, tare da zira yen takalmanshi tana fadin,,

  to mr. talkative, muje kafun ka fara surutun naka na fama daddy na jiran mu, ba musu ya wuce gaba tana biye dashi a baya

   shopping sukayi sosai, harda tsaraban da za suyi, yaji dadin yanda take diban ma yeyen yen uwanshi kaya, duk ta gama cika siyayyan da tsaraban su, da haka suka kammala siyayyan ya biya kudin sannan suka dawo gida.


                         ***

  Yau ta kasancewan safiyar friday, tsaye yake gaban mirror yana karisa shiryawa, dishi dishi take iya hangenshi, kafun ta bude idanunta tangararasa a kanshi.

  sanye cikin wata dakakkiyar sabuwar shadda, nude colour, yaji dinki na alfarma, sai zuba kamshi kawai yakeyi, gashin kan nan kwance yaji gyara, tare da kyakyawan sajen nan mai dada kayata fuskan nashi.

  ciwon kaine ya dameta da asub, shine tasha magani ta kwanta, sai yanxun kuma ta farka, ta mike tana kuma gyara zama da kyau, ba tare data san tambayar taxo bakinta ba take fadin,,

  Baffah ina zaka haka?, ta fada looking so suprise, shikam da sauri ya juyo don yana can yana fama da sanya wristwatch, murmushi ya sakar mata da fadin,,

  my dream girl, kin farka, ya jikin naki?,,

  Alhamdulillah, ta fada da dan murmushi, kafun kuma tayi dan shiru can dai tace,,

   kayi kyau gaskiya sosai, plss zaka je wani waje ne?, idanu ya tsareta dashi, itakam saita kauda nata, wani yer murmushi mai sauti yayi kafin yace,,

   Humaira zanje office ne, kinsan yau ne last day dina a office, sosai tasa murmushi tana fadin,,

  ohhh, naga baka taba sanya irin wadannan kayan bane in zaka tafi, shi yasa na tambaya, baice uffan ba ya juya yana sanya turare, muryanta ya juyo da take kuma fadin,,

  yhu look handsome dear, da murmushi ya juyo yana fadin,,

  thank yhu my super star, dai dai sanda yaga ta daga wayanta tana daukanshi hotuna, fuskanta nakan wayar dauke da wani murmushi, shikam sai faman blushing yake yana matse links din hannun riga, ta sauke wayar tana duba hotunan da fadin,,

  kai gaskiya sunyi kyau, a hankali ya kariso gaban gadon, yana amsar wayan tare da kallon hotunan yana fadin,,

  wow nice shot, sosai ya yaba da yanda hotunan su kayi kyau, kafun ya maida mata wayar hade da nashi yana fadin,,

  kisamun cikin waya nah, amsa tayi yana cigaba da fadin,,

   akwai wata friend dina da take son pictures dina, ta ije na tarihi, cak ta tsaya da danna wayar data fara, faken idanunsa tayi tana kashe wayar nata, tare da zirara ta sakon gado, sai da taji ya sauka kasa, sannan ta maida nashi ta ije mai.

  wanka ta futo sanye da wata yer pink bathrobe da ya zauna cas ya mata kyau, ga cikinta daya futo sosai ta ciki, karamin towel ta nado bisa kanta, ta zuba mishi idanu daya kammala da komai, sai faman dan dube dube yakeyi, alama akwai abin da yake nema, can ya juyo yana kallonta da fadin,,

     ina wayar kie, kinsa mun hotunan nan kuwa?, sai da tayi dan war kafun tace,,

  tohh, ina na jefa wayar ne, sai kuma ta kalli agogon bango tana fadin,,

   gashi kuma za kayi late din wajen a'iki, bari nazo kawai na rakaka, karka bata lokacinka, ta karisa maganar tana ware towel din dake kanta, da cigaba da wani taku daya tafi da tunaninsa.

   hijjabi ta zira har kasan gwiwa, sanna ta dauko mishi briefcase dinshi, tare da tsadaddan hulan sakin dake ije gefe daya, hannunta kawai yaji cikin nashi, cikin wani irin salo take murxa hannun da fadin,,

   muje in maka rakiya kaji, kasa musa mata yayie, har suka futa falo, a bakin kofa ta tsaya ta ciki, yayin da yake daga waje, ta mika mishi briefcase dinshi tana sanya mishi hulan da fadin,,

   saika dawo, Allah ya kaika lafia, da murmushi ya amsa briefcase din yana fadin,,

  Ameen my dream girl, akwai breakfast dinku na nan bisa dinning, karki wahalar mun da baby fa, kanta ta daga mishi alamar gamsuwa, saman cheek yayi kissing dinta, kafin ta rufe kofan suna daga ma juna hannu, ajiyar zuciya ta sauke tana furta kalmar,,

   Alhamdulillah, daga haka ta koma ciki, itama shap shap ta kammala shiryawa, ta shirya Irfan sannan sukai breakfast, school bus dinshi yaxo ya daukeshi, yayin da ita ta wuce a motarshi da yake hawa da, don sosai ya lura bata son hawa na suhymah da yace ta rika hawa, don haka sai kawai ya bar mata key din nashi, shi ya dauka na suhymah.

   driving take sanda ya kirata a waya, da murmushinta ta dauka suna ma juna sallama, yayin daya daura da fadin,,

  kina ina ne, makale wayar tayi tana cigaba da juya steery motar da fadin,,

  ina driving ne yanxun, da sauri yake fadin,,

  ouk bari zan kira inkin sauka, daga haka ya katse wayar, dan turo baki tayi kamar tana gabanshi take fadin,,

   Baffah nifa zan iya waya ina driving, don na riga dana zama kwararriyan driver, sai kuma ta saki murmushi, tana ije wayar bisa seat din dake kusa da ita, a saman labba take furta,,

  ya katse mun daddadan muryanshi, murmushi ta kuma yie tana maida hankalinta sosai kan titi.

   A school ma yaxo mata dai dai da kammalawan karatunta, don sosai ta maida hankali aka kare da ita, ta samu sakamakonta mai kyau, yayin da suke ta hotuna da friends dinta yen mata, sai cewa suke za suyi missing dinta, haka har aka tashi suka rabu cikin kewar juna.


                  £……£……£

  Banda sautin kukanta ba abin dake tashi a dakin, sai faman jan majina takeyi, suhymah dake gefe tayi shiru zugum tace,,

  kai aunty kie daina kukan nan, dole zamu san abin yie, ba zamu zuba ido haka nan ba, mum plss ki mata magana mana, ta karisa maganar da kallo mahaifiyarta wacce ke zaune dabas kusa da mummy, numfasawa tayi itama tana fadin,,

   hakane, yagana kibar wannan kukan, amma gaskiya an cuceki, kuma Alh. Aminu bai kyauta ba, ya rasa wacce zai bama danki sai yer a'iki, ina baxai yuyuba, dole musan abin yie, wani majinan ta fyace cikin muryan kuka take fadin,,

  aunty wlhy ba abin daya bata mun rai sai yaudaran da aka mun, ace  har haj. indo tasan wacce muheet zai aura, don gulma nie sai daren ana gobe sannan za a sanar mun, miye matsayina ne wai a wajenshi, ta kuma jan majina da cigaba da fadin,,

  kina kallo irin kayan lefen da muka hada, duka kudin da sadeeq ya turo mun sai da suka kare, kai harta kudadena sai da suka shige, sannan daga baya ace ba wacce za a kai mawa sai yer a'iki, wacce ta futo daga ruga, kawai saita karasa wani sabon kukan, haj. falmata tace,,

  yagana nace kie daina damuwa, duk da sun rufemu da maganar, amma lokaci bai kure mana ba, na miki alkwarin gobe da sassafe ko ina zamu sai maganar auran nan ta fasu, basai anyi auran ba sannan zama akaima amaryan lefen, kie sa ranki a inuwa, suhymah tace,,

  yes aunty gobe ma kawata surayya zata zo, da ita zanje ta rakani wajen wani malamin da mukai magana, kawai muje ayita a gama, mum din ta amshe da fadin,,

  yawwa haka kawai zama ayi, plss kie daina wannan kukan, gobe da sassafe sai suje, ko nie da kawar taki muje, tunda kinga tsohon cikin dake jikin kie, da sauri tace,,

  no mum kyalleni kawai zan iya, inkin san yanda yarinyan nan ta tsaya mun a rai ko, na tsaneta bana kaunarta, kuma har abada ba zata taba zama dai dai dani ba, matar kanin mijina, tayi wata yer dariyan takaici tana fadin,,

  no no no no, bazai taba yuyuba, dole in shiga in futa ko da danyen jego ne, mum din ta rika jinjina kanta da fadin,,

  yess good, hakan yie, da wannan sukai ta dan bata baki, daga baya mum din ta tashi ta futa, suhymah ta kalli auntyn serious take fadin,,

  aunty sannan kima shugabar kungiya magana, maybe akwai taimakon da zata iya mana itama, dan shiru tayi kafun tace,,

  ouk ba matsala, zan kwatanta yin hakan shima, amma in akwai abin dana tsana yanxun a duniyar nan shine auran muheet, yer a'iki ina baxai yuyuba, itama haj. indo da aka rufeni da maganar da ita, saina nuna mata nie karfen kafa ne zama dani dole, kuma yanda nake so.

                     US……8pm  

  Ina iya hangenshi tsaye gaban mirror safe, cikin wata tsadaddiyar dark green din wandon suit, tare da light green shirt din dake sama, yasha toking da wata costly classy belt, sosai yayi kyau, rigar ta dan kamashi, yana karisa sanya botton din dake saman rigar.

  a hankali ya juya bisa saman gadon, inda dark green din suit din na sama ke ijeye, harya kai hannu zai dauka, sai kuma ya fasa, kai tsaye ya juya ya futa zuwa dakinta.

  Tsaye take itama gaban dresing mirror, sanye take cikin wata dark green din flowing gown, na wani material mai tsadan gaske, banda spakling ba abin da yakeyi.

  wuyan rigar up shoulder ne, sai yer dogon pencil hand din daya zauna mata cas, rigar ta zauna mata ta bude sosai, kadan ta baya keja da kasa, ga dan cikinta daya futo ta cikin rigar yayi matukar mata kyau.

   a hankali yake takowo yana binta da wani kallo mai tafiyar da zuciya, yazo ta bayanta, kanshi yadan rankwafar yana shakan daddadan kamshin turaren dake futowa ta kasan wuyanta, ya karisa shakar kamshin direct yana tsayawa ta gabanta, tare da sauke idanunshi tar a kanta yana fadin,,

  masha Allah, itama slowly ta dago ta kalleshi da wani murmushi mai rasta zuciya, kafun ta maida kallonta bisa mirror, tana karisa kama gashin data kamashi kasa kasa, tare da sanya mishi band, ta jawo wani plane din dark green din yadi mai taushi sai kalli yakeyi shima, daurawa ta soma yie, gaba daya saita koma mishi mirrorn, ya zuba mata idanu, tare da harde hannayenshi bisa kirji.

  tsaf cikin natsuwa ta kammala daurinta na style din ZB, babu wata kwalliya a fuskanta, daga powder sai kajol da tasa a idanunta, tare da gyara giranta da kullum yake kaman tayi cabin dinsu, wetlips ta dauko zata sanya, yayi saurin rike hannunta, tare da girgixa mata kai alamar a'a, dole ta maida ta ijeye, ta jawo wasu yen fashion earring zata sanya.

   caraf shima ya rike hannunta, a hankali ya amshe wadannan yana ijewa gefe daya, hannu ya saka cikin aljihun wandonshi har lokacin idanunshi na kanta, cikin natsuwa ya zaro hannunsa daga aljihun a dunkule, kusa da saitin fuskanta ya kawo hannu kafun ya bude a hankali, da sauri tasa hannunta tana dan rurrufe idanunta, saboda kashe mata idanun da suke faman yie.

  murmushi ya sakar mata, tare da kamma yen kunnanta ya makala mata su, dayan aljihun ya kara sa hannu ya ciro wata yer chain mai dauke da pendal din earring din

Please Login or Register in order to submit comment