Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maganar tana dariya kafun ta koma kan gado, tana dada gyara kwanciya da kyau, wani baccinne yayi awan gaba da ita.

    sanye da rigan wanka ya futo, bisa mirror stool ya zauna, yana binta da kallon mamaki wato baccinta ma ta koma, kalamanta kawai ke amsa masa kuwwa cikin kunni, hannu bibbiyu yasa yana dafe kanshi da wani irin takaici, zuciyarsa ne ke wani irin bugawa, yanxun da ummeetah ba matarsa na sunna bace, shikenan ta jefa rayuwansu cikin halaka, a hankali ya dago kanshi yana harde hannayensa bisa dresing mirror ransa bace yake, fuskan nan babu wani walwala, meya kuma tuna saiya saki wani dogon murmushi yana fadin,,

   suhymah kinyi kuskure, kina kuma gabda fahimtar irin haukar kika a'ikata, baxan iya rayuwa ba ummeetah ba, dole kie zauna da kishiya, sai dai kuma kiyi hakuri, ya dan numfasa yana cigaba da goge ruwan dake kanshi, lokaci lokaci kuma shi kadai yake sakin murmushinsa, har sanda ya kammala shiryawa cikin wata black jallabiya mai karamin hannu, kaiii tafiyar maxan kanshi ya canxa.

   ta gefen ido yake bin matarsa dake baccinta cikin kwanciyar hankali da kallo, girgixa kai kawai yayi, yana zama bakin gadon amma kwata kwata sai yaji baya jin wani bacci ma, gaba daya abin ya kasa barin zuciyarsa, tsawon shekarun da suka rayu da matarsa bai taba samun kwantankwacin natsuwa irin na yau ba,,

   toh me yasa?shine tambayar da yake ma kanshi a zuci, sumar kanshi ya dan shafa zuwa saman fuskanshi da wani big smile, kafun ya koma ya kwanta da kyau, yana faman sakawa da kwancewa, daker wani bacci barawo yayi gaba dashi.  

   

     Bangaren ummeetah kuwa yana futa ta bude idanunta, kuka ta sanya sanda take tuno komai kamar a mafarki, shikenan aure ya tabbata, a da daukan lamarin wasa take, amma yanxun kam tasan an yita ta kare, duk da karancin shekarunta tasan me ake nufi da aure, rayuwane da ake fata na har abada, to amma me, itafa rayuwanta bata kaunar tashin hankali.

   shi yasa tun farko bata ra'ayin miji mai mata, bata son kishiya tsoro suke bata, har yau ta kasa manta tsiyar da akayi tsakanin matan Baffanta lado, daya ta cire ma daya goran kitso, sai data suma gau a wajen, runtse idanuwanta tayi, tana kuma tsunduma cikin duniyar tunanin irin rayuwar auran da zatayi.

    _shin duk randa aunty suhymah ta fahimce ita matar mijinta ne,  ya zata amsheta?._ kuka sosai tayi kafun wani bacci barawo itama ya saceta.

   
                         
                          ***
   da asuba shiya tasheta da jikakkun yen yatsunsa daya manta ya daura mata garin binta da kallo, kokarin tashi ta fara yie, da jikinta da yayi tsami, hannu yasa da sauri yana taimaka mata.

   kunyace ta hanata bude idanu, gashi ba riga a jikinta, sai faman kuma kudundunewa takeyi, cak taji ya dauketa, bai direta ko ina ba sai cikin bahon wanka daya hada mata ruwa mai zafi, ta kankame towel din bata son ya kwance, shikam sai dan dariya yake mata, kafun ya futa ya barta tayi wanka.

   jikinta ta kuma gasawa sosai, sai data jie ko ina ya dan sakin mata, kafun ta dauro alola ta futo, dakin ta sameshi ya idda nashi sallar ya futa, itama shiryawa tayi sama sama, tana bada haraman yin nata sallah.
   
   sosai ya bada himma wajen hada breakfast din, ya kammala komai kafun ya shirya Irfan ya tafi school, yana jin sukur sukur din madam dake ta shirin zuwa office.

   can sai gata ta futo sanye da wata kishmer gown, kusa dashi ta zauna, dake zaune ya zuba ma waje daya ido, banda blushing ba abin da yakeyi, sai data dan taboshi sannan ya lura da ita, itama murmushi takeyi da fadin,,

   boo ya dai wannan big smile din na menene?ta karisa maganar da daga mishi gira daya sama, wani dan murmushin yayi, yana shafan sumar kanshi, kafun ya janye hannunsa yana nuna mata dinning table da fadin,,

   breakfast, dan yatsina fuska tayi tana duba tima a agogan hannunta, kafun ta mike tana fadin,,
  
     no zanyi late din office, sai dai na dawo, bye, ta wuce tana daga mishi hannun, harta kusa kai bakin kofa sai kuma ta tsaya tana juyowa da fadin,,

  ba zaka office bane yau?ya wani dan rankwafar da kai yana fadin,,

   maybe, ta dan zaro ido waje kafun ta wuce tana fadin,,

   hmm, kana jin dadinka, daga haka ta fuce, ajiyar zuciya ya saki, tare da mikewa ya nufa kitchen.

  

                         ***
     Da sallama ya shigo dakin, rike da wani tray daya jera kayan abinci akai, tana kwance bisa dadduman ta kudundune cikin hijjabi, zazzafar zazabine sosai a tare da ita, ba shiri ya zauna yana hada bayanshi da cikin gado itama mikewa tayi zata zauna, don ba barci take yiba, kawai dai tana kwance ne, da sauri ya rukota yana hadata da jikinsa, kawai saita sakar mishi kuka, duk yabi ya rude yana tallafo fuskanta da hannunshi, hannunta tasa itama saman nashi, idanunta a rufe take fadin,,

   Baffah Allah nidai wannan abin da zafi, na kusa mutuw……..., toshe bakinta yayi da hannunsa yana fadin,,

   plss Humaira kie daina fadan haka mana, come on tashi kici wani abu saimu tafi hospital, make kafada tayi da fadin,,

   a'ah, ya jawo tray din gabanshi yana fadin,,

  plss my Hoor, kinga  ban sanki da musu ba, ta mike daker tana fadin,,

  wash Allah, amma dai gaskiya kadan zanci, ta karisa maganar da alamun jin jiki, duk tabi ta bashi tausayi, zuba mata breakfast din yayi da kalaman rarrashi yake fadin,,

    a'ah nie nafi son kici da yawa, haba jarumar fulani tah, kefa jaruma ce, yarinyan dake iya kiwon shanu har kafa dari, koba ummeetan Affah bane dana sanie, duk jin jikin da takeyi, wannan kalaman nashi sai daya sanya ta dan murmushi.

  sosai tasa jarumtar taci abincin, ya matsa sai sunje hospital, dole ya taimaka mata ta shirya suka tafi.

  sanda suka isa, kwararriyar likita suka samu gani, ta dubata sosai kafun ta bata dukkan drugs din daya dace suka dawo gida.

   gaba ya sanyata sai data sha drugs din sannan ta kwanta, kafun dare ta samu jikinta ya dan saki, sanda ya shigo da dare tana tsaye ta kammala sanya kayan bacci, sai data dan tsorata ganinshi, amma sai tayi kokarin basarwa.

   ya lura ta tsorata da lamarin sosai, dakewa kawai takeyi, don haka taimaka mata kawai yayi ta kwanta, tare da rufeta yana kissing dinta saman gira, kafun ya futa yaja mata kofan, sai da taga ya futa sannan ta sauke ajiyar zuciya,wani bacci na awon gaba da ita.

    yen kwanakin sosai yake bata kulawa, ko a'ikin gidan baya barinta tayi, indai yana nan shine zaiyi, lokaci kankani kuma ta samu sauki tare da sanjawa na musamman, harta cigaba da zuwa makarantarta, sosai yanxun take fargaban ganishi a dakinta, musamman cikin dare, (toofaah) shima ya lura da hakan, dan sabawan da sukayi ma sai tana janye jikinta, ido kawai ya zuba mata.

                              ***
     Yau da wuri ta dawo a'iki, kasancewan tun safe ta tashi jikinta bai mata dadi, amma saboda kwakwa sai data futa, ba shiri ta dawo gida sanda taji d'an cikinta nayi kamar zai futo.

   a kan gado tayi wurgi da jakarta tana nufa bayi, jin da tayi kamar wani abu na binta, ilai kuwa jini ta gani, duk da ba wani mai yawa bane, amma hankalinta yayi matukar tashi, a sittin ta futo daga bayin, dai dai sanda ya shigo dakin, a rikice take fadin,,

   sadeeq……sadeeq my baby, am bleeding,,

    what bleeding!, ya fada cikin karaji, sai kuma ta kara komawa bayi da gudu, can kuma sai gata ta futo, karo sukayi daya biyo bayanta, ta kankame hannunsa sai lokacin mararta ke wani irin juyawa kamar zata sanya kuka take fadin,,

  sadeeq na rokeka ka kaini hospital, inna rasa cikin nan mutuwa zanyi, plsss ka kaini hospital karka bari wani abu ya faru da babyna, gaba daya ta rikice, sosai kuma soyayyar da take ma cikin nan yanxun ke bashi mamaki, a da yayi zaton ya fita son cikin kamar yanda yake da yakinin yafi son dansu na farko Irfan, amma yanda ya lura kamar ta fishi son wannan cikin.

   a firgice ta dauko key din mota tana mika mishi, ya amsa da fadin,,

  suhymah calm down, bazai yuyu kije a hakaba, kin dan sanja kaya mana, ta marairaice fuska tana fadin,,

   haba sadeeq ina fada maka babyna……, katseta yayi da fadin,,

   come on zoki gani, wajen safe suka nufa, ya samo mata wata yer abaya ta shiga bayi ta dauraye jikinta, shap shap ta futo ta shirya suka wuce. 

   
   kusan hankalinsu a tashe suka isa asibitin, sai dai sunci sa'a suna zuwa jini ya tsaya, anyi mata duk abin daya dace, kafun su dawo gida da shawarwarin da likita ta basu, don sunce tana bukatar hutu saboda yawan zirga zirgan da takeyi.

    hankalishi duk yabi ya tashi, yana tsoron wannan yawan na suhymah yasa su rasa gudan jininsu, tsaki yayi sanda ya bude motar yana futowa, itama sarai ta futo, yanxun cikinta na wata na biyar kenan, kadan kadan ake iya ganinshi cikin abayar dake jikinta, duk da faman tutturawan da takeyi mai cike da feleke, ganin ya hada fuska sai itama ta hada rai suka nufa cikin gidan.

    zaune take kan daya daga cikin kujerun dake falon, sanye cikin wata light purple lace, dinkin yayi mata kyau sosai, ta kashe daurin ZB dake matukar mata kyau, gashin nan kwance a gadon baya, gaba daya ta sanja daga haske zuwa cika a yen weeks din da tayi da amarcewa, duk wanda ya ganta saiya lura da yanayin sanjawan da fatarta tayi, banda kamshi ba abin dake fita daga jikinta.

   ta dan harde kafa daya kan daya, tare da dan kishingida da hannun kujera, sosai ta bada hankalinta kan wani tashar islam, da suke gabatar da wani shiri kan aure, natsatstsiyar maca ce cikin shiga irin ta musulunci, take zaune tana watso zafafan lecture akan biyayyar aure, cikin harshen turanci, sosai take fayyace yanda mace zata iya zama tauraruwa a gidan mijinta, sannan ta zamto shugabar matansa har a gidan aljanna.

    gaba daya ummeetah sai ta tsunduma cikin kogin tunani, jie kawai tayi tana son ta rabauta da wannan rahman, dan numfasawa tayi sanda wata zuciyar ke bata kyawawan shawara.

   toh amma anya zata iya, shine abin da take ayyanawa.

   budo kofan tayi da watsa mata kallon tsana, alama taji haushin yanda taxo ta sameta a falonta, ta dan ije hand bag dinta bisa hannun kujeran, tana cigaba da watsa mata kallo, shima kallonta yake ganin zata fara rashin mutuncin nata, yasa shi fadin,,

     suhymah muje ciki za muyi magana, kallonshi tayi zatai magana ya ja hannunta, yana daukar jakanta data ije hannun kujera suka wuce daki, ita dai ummeetah da ido ta bisu har suka shige.

   Tana huci ta fisge hannunta, da fadin,,

   sadeeq ban gane bane, a sanyaye ya kalleta kafun yace,,

   a'i dama ba zaki taba ganewa ba, ke kullum a haka kike, to bari na fada miki bazan dauki wulakanci ba, suhymah baxan zauna ba ina kallon na rasa gudan jinina, don haka dole kie natsu daga yawan zuwa wani office, dan tsaki tayi tana fadin,,

   wannan ne kuma baxai yuyuba, saboda a'iki yan zuma muke kan yie, ta karisa maganar da zama bakin gado, a zuciye yake fadin,,

   ouk haka kika ce, to dani dake zanga wanda ke auran wani, abin ya bata mamaki amma saita sha kunu tana fadin,,

   oho nidai na fada maka, ba yanda za'ayi nabar a'ikina, kuma naga a'i abin nan a jikina yake, so no need ka rika wani tada hankalinka, don na tabbatar dana fika son cikin nan, da mamaki yake kallonta kafun ya zauna gefenta, rigima ba halinshi bane, amma sai gashi yau ya zake da fadin,,

   to Allah ya baki sa'a, ni kuma na fada miki idan har gobe ina cikin gidan nan, zanga ta inda zaki futa, alkwari na miki, daga haka yaja tsaki yana faman huci, sai kuma yayi saurin mikewa yana kallon kayanta data cire masu jini a wajen da fadin,,

   oh my god, wannan kayan dake floor baxa a samu damar dauke su bane?dan war tayi kamar bata damu da masifar da yake faman yiba, kafun ta shiga kwala kiran,

   ummeetah, baima san sanda ya watsa mata yer hararaba yana fadin,,

   ba ummeetah ba, saura ummeelato, dai dai sanda ummeetah ta iso wajen, yana cigaba da fadin,,

   me zata miki da kike faman kwala mata kira?,itama a zuciye take fadin,,

    a'ah, sadeeq a'ikinta mana, zata kwashe sune ta wanke mun, sai daya mata wani kallo mai kama dana rainin wayau kafun yace,,

   toh baza tayi ba, bai bata damar yin wata magana ba, ya dora da fadin,,

   nie sadeeq nace ba zata yiba, baki da wani a'iki, sai dai kisa a miki, kai daga yau na rantse babu yarinyan da zata kara gyara dakin nan, a'i sirrin mune ma, bai kamata ace wata tana shigowa ba, inhar ba zaki iya gyara ko ina ba, atleast kya gyara dakinki, don haka daga yau na soke, cancel ina fada miki, sosai ta saki baki tana kallonshi, yace,,

    yes, tunda har kina da karfin zuwa office, shima wannan kiyi abinki, sosai kuma ta gano bacin rai a idanunsa daya hanata yin katabus, dama ita ummeetah tuni ta sulale tabar dakin, don haka shima futa yayi yabar gidan gaba daya.

   abin ya tashi hankalinta sosai, abune da bata taba gani ba, tsawon shekarun da sukayi da aure da juna, amma sai tabar lamarin maybe don saboda abin daya samu unborn child dinsune, yasa shi shiga wannan mood din, tasan halinshi da son ye'ye, amma tayi alkwari duk da haka ba zata bari ya juyata ba.

   da wannan ta kwashi kayan tayi bayi, har tana zamewa da jinin daya diddiga kofar bayin, kadan ya rage bata zame ba, rai dai duk ya hadu ya baci.

                            ***

  safiyar yau din na friday ne, tunda yake shirinsa na zuwa office, ya zuba mata idanu, kwance take tayi likimo cikin blanket, murmushin jin dadi yayi kafun ya kammala duk abin da yakeyi, briefcase dinshi ya dauka tare da nufa inda take, a hankali ya duka yana sakar mata kiss bisa kumatu, kafun ya mike da fadin,,

    bye angel, da dan murmushi take fadin,,

   enjoy ur day sweetheart, ya kuma sakar mata murmushi yana tafiya da fadin,,

   same to yhu dear, luv yhu, daga haka ya fice, ummeetah ya samu dake jiranshi a falo, tana ganinshi ta mike tare da amsar briefcase din nashi, gaba tayi yayi saurin saka hannunshi cikin nata, dole ta saki jikinta suka jera tare har wajen motar, kafun ya bude mata ta shiga, sannan shima ya zaga ya shiga bangaren driver, hoping that sunbar amarya a gida ta musu gadi, a cewarta, tana jin karar tashin motarshi, itama ta shirya ta fuce abinta.

     Tare suka dawo gida, bayan ya biya school dinsu ya dauketa, a gajiye ya futo kamar kullum, da Irfan yayi karo dake cin uban wasa da karnukan gidan mr. Nelson, ga school bag dinshi can wancakale gefe, kayan jikin yaron yake bie da kallo da sukai datti sosai, ya taho wajen baban nashi da murna yana fadin,,

  daddy welcum daddy……, tunkan ya kariso ya tsayar dashi da daka mishi wani irin tsawa yana fadin,,

   stop there, karka matsoni, kana haukane zaka rika wasa da karnuka, are yhu a dog?da sauri ya girgixa kanshi alamar a'ah tare daja ya tsaya tsam, ya cigaba da fadin,,

   jubi kayanka yanda kayi datti dasu, ummeetah ce ta futo jiki a sanyaye, ta karisa wajen school bag dinshi tana picking da fadin,,

    Irfan me yasa baka shiga cikin gida ba?kamar zai kuka yake fadin,,

    aunty ummee kofan a kulle ne, kuma haka ma gidan su misha, da sauri ta kalleshi daya zaro ido waje yana kallon Irfan, kafun kuma ya taka yen stairs din entrance door din wajen yana murda kofan, amma gam ya jita, runtse idanu yayi.

  taf taf taf taf, ya sauka yana komawa ta backyard din gidan, garage ya duba nan yaga motarta wayam, tuni fuskan nan ya koma kamar battle yard, ransa iyayi dubu ya baci, jie yayi kamar yaune rana ta farko data fara mishi rashin biyayya, hakanan ya dawo ya bude musu kofar da key din dake wajenshi rai bace, gaba daya ummeetah na lura da mood din daya shiga, don haka tuni itama fuskarta ya nuna alamar damuwa.

   bisa kujera ya zauna yana daga kanshi sama da runtse idanu, tsoro kawai yake wani abu ya samu unborn child dinsu, baya jin zai iya yafe ma suhymah, ya dunkule hannayensa yana jin kamar yakai wani nushi, ran maza fa ya baci, Irfan ne ya dafashi yana fadin,,

   daddy am sorry, baxan kara b.....,

  sakeni!ya fada da tsawa, yana bude idanunsa, ummeetah tayi saurin fadin,,

   come on Irfan zo muje kayi wanka, ya dalla ma yaron harara yana fadin,,

  dirty boy wuce kaje ana kiranka, a tsorace ya wuce, ita kuma taja hannunshi rike da school bag dishi suka wuce.
   
  

    wanka ta mishi ta kammala shiryashi tsaf cikin shigar wata sabuwar dakakkiyar shaddda na kwalliyar jumma'a, arsh colour da taji a'iki na alfarma, sai data gama shiryashi sannan ta koma dakinta, tana bude kofar tayi maza ta koma ta rufe da runtse idanu a zuciya take raya,,

    oh nie ummeetah yanxun daki ya zama mu biyu, shikam kallonta kawai yayi yana cigaba da shiryawanshi, tafi karfin 10minutes kafin ta kara budo kofan ta shigo.

    sanye yake tsaf cikin tsadaddan shadda iri daya dana dansa Irfan, har lokacin ransa bace yake komai, sai faman cuku cukun sanya botton din wuyar rigan yakeyi, tsaye tayi a tsakiyar dakin tana kallonshi da saka abubbuwa iri iri, kafun dai ta dake zuciyarta iya dakewa, cikin takun natsuwa ta isa gabanshi.

  idanu ya dago yana kallonta da cigaba da kokarin sanya botton din, gaba daya saita jie ta kasa hada ido dashi, yana shirin tambayarta ko lafia, yaji saukar hannunta bisa nashi hannun, kai tsaye ta janye hannun nashi tana yakice wani kunya da fadin,,

   bari na taimaka ma, ta karisa maganar da kallonshi sama sama, kafun ta maida hankalinta wajen sanya mishi botton din, sakar mata yayi yana wani dan munafukin murmushi, tsaf ta kammala sanya mishi, ta kamo hannayensa nanma ta sanya mishi links, sannan ta ja mirror stool tana takawa, trolly dinta ta jawo ta ciro wani kwalin turare mai shegen kyaun gaske, kafun ta rufe trolly din ta maida.

   gabanshi ta dawo, komai takeyi  cikin natsuwa, amma ita kadai tasan yanda kirjinta ke bugawa, ta zaro turaren daga kwalinshi, gaba daya turaren abin kallo ne da shu'awa, kwalin ya jawo data ije bisa dresing mirror yana kallo, yaji tsada sosai daga kasa an rubuta for men, da dan mamaki yake kallonta yana fadin,,

   a ina kika samo wannan turaren?kanta na kasa tana kokarin fesa mishi turaren tace,,

  ya muheet ne ya ban……...., bata karisa ba taji ya ruko hannunta dake rike da turaren gagam, har sai datai dan kara saboda zafi, ta sanya hannunta daya tana dafe kafarshi, tare da marairaice murya tana fadin,,
 
   wayyoo Baffah kayi hakuri, wasa nake ma fa, wani ajiyar zuciya ya ije, yana sanya hannunta samar kirjinsa dake faman harbawa da fadin,,

   Humaira kinji yanda kuwa kika kusa fasa mun kirji, da sauri ta janye hannunta tana fadin,,

  eyyaah kayi hakuri, kwanaki da mu kaje shopping ne na gani yayi mun kyau, shine saina siya..., ya karisa fadin,,

  kika siyanmun, kai ta daga alamar eh, ba tare data bari sun hada ido ba take fadin,,

   kana so ko?sosai yaji dadin abin da tayi mishi, murmushi yayi yana fadin,,

   of course, ina so sosai, nagode matata, ya bude hannayensa alamar ta fesa mai turaren, ba bata lokaci ta soma fesheshi dashi, ya shaki kamshi yana dan runtse idanu da fadin,,
  
    woww, kamshin da dadi, a tare sukai dan dariya, ta maida murfin turaren ta rufe zata ije, caraf ya kama hannun, sosai yake bin turaren da kallo, kafun yakai bakinshi yana kissing kwalban turaren da fadin,,

   nagode matata, Allah saka miki da alkhairi, a tare suka ije turaren, sai faman blushing takeyi, ta jawo hular sakinsa daya jie tsada asrh color tana daidaitawa, hannayensa ya goya bisa bayanshi, yana dan rankwafo da kanshi, ita kuma ta daura mai hulan tana fadin,,

   kayi kyau Baffah nah, kyau da kwalliyar jumma'a, sosai yake murmushin dadi, da fadin,,

   nagode y'er Affah, matar Baffanta, amma dakinsa mijinki wajen Baffan nan daya fie dadi, hannu tasa ta rufe fuskanta da dan kunya, dai dai sanda Irfan ya shigo dakin, cak ya tsaya yana zaro ido da dan tsoro tare da fadin,,

   kai dakin mummy na shigo, kallon junansu sukayi suna dan dariya, kafun ya wani hade fuska yana fadin,,

   ka tabbatar kayi knowking kofa kafun ka rika shigowa, kanshi ya daga da fadin,,

   to daddy, ummeetah ta jawo hannunshi tana fadin,,

   zo insama turare, da tsallesa yake fadin,,

    yeee irin na daddy zaki samun, mai kamshin dadi, da sauri yace,,

   a'ah, kar asama mai wasa da dogs turarena, kamar zai kuka yake fadin,,

   daddy am sorry, baxan kara ba fa, itama taba fuska tayi da fadin,,

   Baffah yafa baka hakuri plssssss, kallonta kawai ya tsaya yie, gaba daya in tana wannan shagwaban nata, baya tantance shekarunta dana Irfan din, yace,,

   ouk fine, amma inya kara ko abinci baxan cie tare dashi ba, da sauri yace,,

   daddy a'ina daina, aunty ummee a'i baxan kara ba ko?da murmushi take fadin,,

   yes yaro mai kyau baya wasa da karnuka, kaji, kanshi ya gyada alamar gamsuwa, yana faman blushing, haka ta taimaka musu suka kammala shiryawa, kafun ta rakasu har kofa suka tafi.

    suna futa ta gyara gidan sosai, banda kamshi ba abin dake tashi, dakin sune kawai bata gyara ba, shima nan don ya hanata gyarawa ne, ta kammala tsaf, tare da shirya girkinta mai rai da lafia, komai ta jerashi tsaf bisa dinning, wanka tayi tare da dauro alola taxo ta gabatar da sallah, kafun ta fara shiryawa.

    sosai ta hade cikin wata farar material lace mare nauyi, dikin riga da skirt daya jie budewa sosai, sai yer rigan da take dai dai jikinta, daga rigar har hannunshi yaji style na alfarma, shap shap ta kitse gashinta da wasu kananan kalaba masu kyaun gaske, sai kalli kawai gashin keyi.

    ribbon tasa ta kama kalaban daga dan kasa, ta gaba kuma ta ziraro da guda bibbiyu ta gefen hagu da dama, sosai ta gyara fuskanta da light make up, bakin gashin giran nan yaji gyara, sai tayi lining black lipstick, ta gyara shape din dan bakin ya futo sosai rass, ta mike tana feshe jikinta da daddadan turaren kamshi, kafun ta dakko dankwalin kayan daya kasance black, sosai ta kalmasashi sannan ta rangada daurinta na ZB, har wani dan karkacewa daurin yayi, gashi ya zauna da kyau.

   mikewa tayi tana dan jujjuyawa gaban madubi, tayi kyau sosai, amma sai taji tana jin wani kunya, dai dai sanda taji tsayawar motarsu, Irfan ne ya fara shigowa da sallamarshi, daker dai tayi shahada ta futa.

   wowww, aunty ummee beautiful, ya fada da bata stars da yen yatsunsa, da dan murmushi take shafa kumatunsa tana fadin,,

   thank yhu, dai dai sanda ya juyo daga juyawan da yayi yana rufo kofa, baki kawai ya saki yana kallonta, shibe saki door handle dinba, shi bai taho ba, Irfan dai ya ruga da gudu dakinshi ya ije hulanshi, itama jie tayi tana neman daskarewa a wajen don kunya, amma dai ta dage tayi na mazaje, cikin tafiyarta mai matukar daukan hankali ta isa gareshi tana fadin,,
  
  Baffah

Please Login or Register in order to submit comment