Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muryan mummy dake fadin,,

  gaskiya ba amun adalci a gidan nan, haba muheet yana da gaskiya don me za'a rika banbantashi da sauran ye'ye, don kawai shi bashi da abin hannu, da sauri kowa ya dago kai yana kallonta daga tsayen da take tana faman harare harare, sadeeq zaiyi magana maami tayi saurin dakatar dashi da fadin,,

  jeka dauki d'anka ku wuce, gobe in zaka tafi ka biyo akwai sakon da zan baka ka tafin mata dashi, da,,

  toh, kawai ya iya amsawa yana musu sallama, kafun yasa kai ya futa. Abba ya sauke ajiyar zuciya da bacin rai yake fadin,,

  yagana banyi tsammanin wannan maganar daga bakin kiba, duba da irin cin mutuncin da mutallab ya gama mun a gaban idonki, dan tsaki tayi kafun tace,,

  a'i duk rashin adalcin da ake nuna mai ne ya kawo haka, domme za ace sai an mishi auran dole, shin haka akayi ma sauran, maami da zatai magana ya dakatar da ita da hannu yana fadin,,

  kenan kina goyan bayan mutallb, ya saki yarinyan har in akai auran?, kai tsaye tace,,

  to dama ta yaya zai zauna da matar da baya so, banga dalili ba, a barshi ya darxo wacce yake so, Abba ya mike a hankali, goye da hannayeshi a baya yake  fadin,,

   lallai kin nuna mun iyakata, amma na barki haka, inason in shaida miki daga yau na cire mutallab sahun ye'ye nah, na bar miki danki kije kie cigaba da bashi gurbataccan tarbiyan da kika iya basu, ba maami ba harta ita sai data razana, daga haka yasa kai ya wuce daki.

   kuka ta fashe dashi, a zuciyarta tana ayyana an gama mata da miji, shikenan ita kuma, maami dai tabi bayanshi da sauri, don ta tausasa zuciyarsa akan wannan magana, don tasan halinshi da tsatstsauran ra'ayi.




  ***

  kishingide yake yayi luff bisa gadon, yana cike da wani irin nishadi, amma wani bangaren na zuciyarsa na cike da kuncin abin da muheet yayi ma mahaifinsu a yau, yayi dan tsaki yana kauda zancan da fadin,,

  Allah ya shirya mana, wayarshi ya jawo yana budo hotonta tare da folding hannunshi d'aya bisa kirji, sai wani smiling yakeyi yana lumshe ido, bakinshi yakai a hankali yana kissing hotan da fadin,,

  nayi kewarki baby fulani nee nah, dai dai sanda ta turo kofan da dan sallama ciki ciki, da sauri ya kashe wayar yana ijewa gefe, ta tsaya sagale kafun ta kariso tana zama kusa dashi da fadin,,

  me yasa ka boye?, murmushin yake ya danyi yana fadin,,

  haba don fa ina ganin daranjan kine, mai sona, mai kishi na, ya karisa maganar da lakutan hancinta, wani dan murmushi tayi tana fadin,,

  kishin da babu alkhairi, difff yayi na wasu seconds, kafun ya jawo hannunta dake kan jikinshi yana fadin,,

  hakane, suhymah kishi halas ne, amma ba aso ana zafafashi kin gane, kanta da dan daga alamar gamsuwa tare da daura kanta bisa kafadarshi, tana fadin,,

  baby dani da ita wa kafi so?, sai da kirjinshi ya bada wani irin sauti, kafun yace,,

  me yasa kika tambaya? kusan 2minutes kafun ta dago tana kare mishi kallo, tare da shafar fuskanshi tana fadin,,

  yhu change alot, this kasumba, duk kewarta ne haka, ta karisa maganar da sanya idanunta cikin nashi, da sauri ya kauda nashi yana dan murmushi, da wasu yen waske waske, saman kanshi ta kama tana manna mishi kiss da raunin murya take fadin,,

  i luv yhu, kayi bacci saboda tafiyar da za kuyi gobe, kanshi ya jinjina mata da fadin,,

  ouk, luv yhu too, daga haka tasa kai ta fice, ajiyar zuciya ya sauke, sosai yanxun yake mamakin wasu dabi'un nata, duk da bai taba zaton zata sauko kamar haka ba cikin sauki, to amma me yasa?.

  shine amsar daya gagara samu, kawai saiya daga kafadarshi da tunanin maybe addu'an da yake mata ne kullum akan zafin kishin ta, ya fara a'iki.

  
[14/08, 14:29] Dala Grp: 🕯🕯🕯
    *MATATACE*
          🕯🕯🕯
  

story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjj 

*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty Ummeetah any my Fa'ixation._

page 69~70

__________Sanye ya futo cikin wata tattausar farar yadi data dauki launir kalan fatarsa, kadan kadan kake iya hango singlet dinshi dake ta ciki, komai nashi fari ne, yana rike da farar hulan saki a hannunshi, ya karisa sakkowa da down stair din yana gyara links din hannun rigan.

  a dinning area ya samesu, Irfan na zaune sanye cikin wasu tsaddun ready made, yayin da take tsaye a kanshi tana saving dinshi breakfast, a tsatsaye suka iya cin wani abu, sannan suka mike, tama rasa gane tsakanin shi da Irfan waya fie dokin wannan tafiyar.

  wasu tela ya ije mata guda biyu na banki, ta dago tana duba abin dake ciki, sunan kanninta ne both a ciki, na school fees din daya biya musu, da sauri ta dago kai tana fadin,,

  duka wannan kudin ka biya haka?, shiru yayi mata yana dada gyara zaman hular da yake sanyawa, tayi dan murmushi da fadin,,

  thanks dear, sai lokacin ya dago yana dan yatsina fuska da fadin,,

  what?, Najma ko Zahira, wacce ce wanda ba kanwata ba a ciki, ya kwasa wayoyinsa dake bisa dinning table yana fara tafiya da cigaba da fadin,,

  kinsan sun fi karfin hakan a wajena, ya fada maganar da rankwafo da kanshi ta gefenta, da suke jerawa a tare, murmushi yake tayi da hawaye dake neman cika idanunta tana rayya,,  

  wayyoo Allah nah, na shiga uku idan na rasa sadeeq, jubi yanda yake ma yen uwana hidma, nasan kuma ba wani sihiri bane yake tasiri a kanshi, tsaban tausayi da taimakone kawai irin nashi, nayi kuskure dana dauka wancan hanyar ta farko.

  jiki a sanyaye ta rakasu wajen mota inda sukai sallama, kamar karta rabu da danta, kafun driver yaja motar suka bar gidan, sai daya biya ta gidansu, sannan suka futo ya tsaya a wani barber saloon aka dan gyara mishi fuska, kafun su dau hanya.




    ***
 
   Gate man ne ya bude mishi gate din, yana faman yashe baki da kwasar gaisuwa, shi kuma ya karisa da motar ciki.

  sosai ya yaba da tsarin gidan, sun sami tarba na mutunci daga wajen baba balarabu, ita take sanar mishi ummeetah na cikin site dinta, tana tunanin ta dan kwanta ne, shidai da to kawai yake amsa mata, don duk ya kosa yayi karo da fuskanta ko da kuwa tana baccin ne.

  tare da Irfan suka wuce site din kai tsaye, tun daga falon ya fara shako kamshin turarenta, komai tsaf tsaf, ga falon dan madaidaci a tsarashi da red and milk furnitures sunyi kyau. 

  kofan bedroom din yaja ya tsaya, yana zuba mata idanu daka kwancen da take bisa gado, ta rufe halve din jikinta da duvet, yayin da kanta ke bisa daya daga cikin pillow dake gadon, tana baccinta mai cike da kwanciyar hankali, Irfan ya matsa kusa da gadon yana blushing da fadin,,

  daddy aunty ummee fa bacci takeyi ko?, kanshi ya daga mishi da fadin,,

   eh bacci takeyi, zo muje karmu tasheta, ba musu ya taho suka fuce, sun dan zaga gidan da ganin ko inna, kafun su dawo, bayan mai gadi ya kunna gen din gidan, Irfan ya bace a falon farko yana kallon cartoon, yayin da shi kuma ya wuce ciki kai tsaye da trolley din daya dauko daga mota.

  ya cire hulanshi yana ijewa bisa side drower, tare da zama kusa da ita yana kare mata kallo, sai yaji kamar sun wani shekara goma ne ba suga juna ba, ya dan shafi kumatunta da fadin,,

  kumatu girl, motsawan da yaga ta dan fara yine ya sanya shi janye hannunshi da sauri, don baya son ya katse mata baccin, da alama tun bayan sallah asbah ne ta koma, yanxun misalin 10am, yasan maybe ta kusa farkawa, ya numfasa yana mikewa da barin wajen.

  gaban safe ya nufa yana budewa, komai na jere bisa tsari, yayi murmushi sanda yake jera nashi kayan ciki, kamar daga sama ya sinkayi muryanta dake fadin,,

  Baffah, da sauri ya juyo tana zaune, harta dan kishingida da pillow, wani kallon mamaki take mai tare da kifta yen idanuwa, can kuma tayi dan hamma irin namai bacci tana sanya bayan hannunta ta rufe bakinta, tana dan runtse idanuwa.

  tsaki ta dan yi kanta a kasa tana faman babata rai, dajin haushin kanta yanda ta kasa yakice shi a ranta kamar yanda ta dauki alkwari, maimakon hakama sai ya koma mata gixo gixo, ta kuma jan tsaki tana kokarin sakkowa daga kan gadon.

  tana durowa, dai dai sanda ya iso wajen, ya dagata cak da mata daukan yen jarirai, donshi kanshi yasan bata gasgata abin data gani ba, a matukar firgice ta dago idanu,,

  kenan shine da gaske, shine abin da take ayyanawa, tana faman lumshe ido da budewa, hura mata iska ya shigayi a fuska, sai tana ganin abin kamar a mafarki,,

  kai impossible, mutumin dake can da matarshi hankali kwance, donme zai tuna da nie, sai dai in mafarki nak……..., bata karisa tunanin da takeyi ba, ta sanya yen yatsu gefen kuncinsa, da karfinta ta mintsinleshi yace,,

  oucchh, da sauri ta fiddo ido waje, sai kuma tayi saurin maida hannunta a wajen tana shafawa da murzawa tana faman fadin,,

  oh my god, i thought am dreaming, plss Baffah kayi hakuri, sorry kaji, tasa bakinta tana hura wajen da iska, a cikin kunni ya dan duko da rada mata,,

  kina mamaki ne?, tsamm ta runtse idanunta, lokacin da taji muryanshi, tana faman raya,,

  Allah da gaske shine, Baffah nah ne, kanta ta dago tana kallonshi kamar yaune rana ta farko data fara ganinshi, shima ya zubata ido kawai da murmushi,

  wlhy baby nah nayi kewarki sosai, ya fada a hankali saman labba, wanda ya dawo da ita cikin duniyar tunanin data tafi, tana zuba ma yen yatsunta idanu dake bisa kuncinsa inda ta mintsinle shi, da sauri ta janye hannunta tana kokarin kwacewa, ganin haka yasa ya direta a hankali, yana fadin,,

  ba zaki rungume mijin kiba, matsayinshi na wanda yake cike da kewar matarshi, baki ta dan turo gaba, can kasan zuciyarta kuwa na cike da wani tsananin farin ciki, amma saita dan basar daja da baya tana fadin,,

  Baffah yaushe kazo? hannunshi harde bisa kirji yake kallonta da fadin,,

  bamu dade ba, munxo lokacin kina bacci, da sauri tace,,

  kai da wanene?,,

  Irfan, a rude take fadin,,

  Irfan, yhu mean my sweet darling boy, ta karisa maganar da wani murmushin farin ciki, kafun tasa kai ta fuce dakin, tana faman kwala mishi kira, shima bayanta yabi yana sauke ajiyar zuciya.

   kusa dashi ta zauna tana huging dinshi, yasa ihu da fadin,,

  aunty ummeetah i miss yhu so much, ta dagoshi tana jan kumatunshi da duka hannunta da fadin,,

  miss yhu too my darling boy, yace,,

  aunty ummee kinsa menene?, kanta ta girgixa mishi yana fadin,,

  kuka na rika yinma daddy, nace ina son zuwa wajenki, shine ya kawoni, dai dai sanda ya kariso wajen yana zama kujeran dake kusa da nasu, jiki a sanyaye ta sata kallonshi kafun ta juya da fadin,

  Allah sarki my Irfan, nasan kai dama mai so nane, thank yhu so much da kaxo inda nake, tayi kissing saman kanshi da cigaba da fadin,,

  ka kara zama big boy yaro nah, zumbur ya mike yana kneeling down da fadin,,

  babyn kima ya kara yin girma, daddy yace ya kusa futowa ko?, wannan karon harara ta jefa mishi yana yashe yen hakora, kafun tace,,

  come on, yanxun dai ka fada mun duk abin da kake so, today am gonna cook ur favorite meal, da murnanshi kuwa ya shiga zayyano mata duk kalan abincin da yake so, suka gama da wannan tana tambayarshi labarin new school din daya koma.

  shima nan labari yake bata bilhaki da gaskiya, kamar sunma manta da wani sadeeq a wajen, shidai yana zaune yana kallonta, bai sa musu baki ba, har dai ya gaji da zaman haka ya mike ya shige ciki abinshi.




    ***

  Tun bayan sallar azahar da suka futa, har yanxun basu shigo ba, sai faman turo baki takeyi da korafin,,

  kai, shi Baffah nan ya tashi yaje ya wani dade a waje tun dazu, plss ku dawo mana, sai faman kawai da dawowa takeyi, can ta juyo maganarsu da sauri ta shige kitchen tana murmushi, baba balarabu dake kitchen din tana yen a'ikace a'ikace, tayi yer dariya, shiriritan ummeetah nada yawa.

  A tsakiyar falon ta jibge musu kayan abinci, komai da Irfan yace yana so shi aka girka, harda gwullisuwa(alawan madara), daya ce yana so, ta zauna daga gefe d'aya tana saving dinsu abincin, Irfan daya dauki gwullisuwa daya yana sha da fadin,,

  yawwa aunty ummee gobe birthday din daddy, pls zaki ma daddy nah birthday cake?, murmushi ta danyi kafun tace,,

  exactly as yhu wish, yace,,

  thank yhu aunty ummee, ya kalli dad din dake zaune gefe yana danne dannen wayarshi kafun yace,,

  daddy zaka yanka cake gobe, aunty ummee zata maka cake ko?, ya karisa maganar da dire tambayar still a kanta, kumatunshi ta dan ja da fadin,,

  ehmana, saboda farin cikin kane nawan, ya fadada murmushinsa yana tabo daddyn da fadin,,

  daddy kaji ko plss zaka yanka, ajiyar zuciya ya sauke yana aje wayar gefe, da jinjina mishi kanshi kawai alamar eh, duk motsin da yakeyi idanunta na kanshi, tana faman satan kallonshi, nan suka zauna cin abincin hankali kwance.

  kadan ya iya cin abincin, saboda rabi da kwatan hankalinshi yana wani wajen, ya rika juya spoon din kawai cikin plate din, lokaci lokaci kuma yana dan duban inda take zaune, wacce ko kallon inda yake ba tayi.

   can yayi dan tsaki yana daukan drink dake cikin cup tare da kaiwa bakinshi, da sauri ya janye cup din, sanadiyar wani shakewa da yayi yana dan tari, a firgice ta juyo barayin da yake, ganinta kawai tayi a gabanshi tana daura hannunta bisa gadon bayanshi, ta fara shafamai tare da faman jero mishi sannu.

  ya dago kanshi yana wani lumshe idanu, kafun ya zuba mata su, da sauri ta janye nata idanun tare da janye hannunta daga bayanshi, ta zuba ruwa a cup tana mika mishi a sanyaye.

  thanks, ya fada yana amsar ruwan, tare da mikewa kai tsaye ya wuce ciki, da ido ta bishi da kallo harya shige, shidai Irfan yana nan yana kwasan girkin aunty ummee mai dadi, dama an dade ba'a hadu ba. 



   ***

  Daren ranan kallonsu suke ita da Irfan hankali kwance, baba balarabu data futo daga dakinta, harta fara baccinta ta farka shine ta jiyo karan TV ta futo, ummeetah ta kalla dake zaune tana fadin,,

  keko ummeetah baki zuwa wajen mijinki ki kyalle kallon nan, dare yayi shima ya taso yaje ya kwanta, ta karisa maganar tana kallon Irfan daya kura ma TV ido, da,,

  tom, ummeetah ta amsa kafun ta mike tana kashe kayan kallon, shi kuma Irfan baba balarabu ta tasa shi zuwa dakin dazai kwanta, yana ma aunty ummeetah sai da safe.

  cikin natsuwa take takawa zuwa falon, komai gani take kamar a mafarki, fuskanta dauke da murmushi ta kama handle din kofan ta  bude kadan tana leke.

 can ta hangoshi yana zaune bisa daya daga cikin kujerun dake falon, sanye da kayan bacci, ya maida hankalinshi sosai kan laptop din dake gabanshi, ta kuma sakin wani gifted smile din, tana rankwafar da kanta jikin kofan tare da lumshe ido, kasa kasa take furta kalman,,

  i miss yhu alot my Baffah darlin……..., bata karisa ba tayi saurin mikewa da kyau, sanadiyar kofan daya kufce mata daga hannu, dai dai sanda ya dago kanshi yana sauke idanushi a kanta, da sauri ta wani waske tana dafe ciki, kafun ta fara fadin,,

  wash, wash, ya mike cikin hanzari yana karisawa gareta, hannunshi ya sakalo ta bayanta yana rike hannun data dafe cikin nata dashi, yayin da da yasa dayan hannun yana rike hannun da take faman yarfawa cike da shagwaba, a haka suka karisa kan kujera mai zaman mutum daya ya zaunar da ita, yana faman jero mata sannu, da dan damuwa ya tsuguna a gabanta yana rike da hannunta yake fadin,,

  Humaira yadai, ko dai haihuwan ne muje asibiti?, da sauri ta dago kanta tana fadin,,

  a'ah, Baffah karka damu juyi ne kawai, amma haihuwan da saura a'i, tunda ta fara maganan ya tsura mata ido, yayi dan guntun murmushi kafun yace,,

  ouk hakane fa, in haihuwan ce taxo a'i baxan ganki haka ba, sai data turo baki sannan tace,,

  kai Baffah tsoratar dani fa kakeyi,,

  sorry, ya fada yana dan kama kunninshi daya, kafun ya mike yana cigaba da fadin,,

  amma naga kamar in haihuwan taxo ne, ba zaki samu damar wannan surutun ba, ya karisa maganar yana juyawa kamar zai koma inda yake zaune, da ido ta bishi da kallo, har lokacin tana jin wani kewarshi, yana juyowa tayi saurin dauke kanta.

  yayi murmushi tare da dawowa inda take zaune, hannun kujeran ya zauna yana hada kirjinshi da bayanta, yayin daya sakalo kanshi ta saman kafadarta, yasa hannayensa ya zagaye sama cikinta dashi, idanunsa a lumshe yake fadin,,

  wai baki san nayi kewar kie bane jarumar fulani tah?, tsam tayi tana lumshe idanu itama, da jin irin sakon da yake isar mata da hannayensa da suka fara yawo a saman kirjinta, da sauri ta sanya hannayenta tana rike nashi, cikin sanyi tace,,

  plsss bacci nake jie, a hankali ya bude idanunshi, ba tare da yace wani abu ba, ta janye hannunshi daga jikinta tana mikewa da fara tafiya zata bar wajen, bisa kujeran ya zame, kanshi kasa yake murxa yen yatsunsa saman giransa da runtse idanuwa.

  ya salam, kwata kwata baisan ya zaiyi da ummeetah ba, bai taba tunanin har haka yake sonta ba, sai da sukai wannan nisa da juna, amma ita ya lura da gaske take...……,,
 
   tunaninshi ne ya tsaya cak sanda yaji kamar ana kallonshi, da sauri ya dago kai, tana tsaye tsakiyar falon tana kallonshi da murmushi, suna hada idanuwa duk ta daburce, da gira yake mata tambayar,,

  lafia, ta girgixa kanta da sauri tana juyawa tare da shigewanta daki, kofan ta maida ta rufe tana dafe kirji kafun ta dago tana dariya da toshe bakinta, natsuwa tayi tana kura ma waje daya ido da wani murmushi,,

  ina sonshi da yawa, ta fada so silent, sai kuma ta dungure kanta da yen yatsunta tana fadin,,

  fool ummeetah, da wannan ta wuce bayi tayo wanka sai faman blushing takeyi, kafun ta futo ta shirya cikin kayan bacci masu kauri, bisa gado ta kwanta amma saita kasa baccin, murna da wani nauyin jiki duk sun hanata bacci, dole kasan carpet ta dawo ta jefa pillow ta kwanta, daker nan ma baccin ya tafi da ita.

  bangarenshi kuwa sai daya kammala a'ikin da yakeyi, sannan ya tattara kayan ya dawo daki, ganinta a kasa sai ta bashi tausayi, yasan nauyin cikin dake jikin tane ya takura mata, Allah yasa ma cikin nata baiyi girman da sukai zaton zai kara ba a wannan stage din.

  a hankali ya duka kusa da ita, kusan 5minutes kafin ya shafa kumatunta, ya dan rankwafa yana kissing saman kanta.

  alola yayo kafun ya dawo kusa da ita shima yana sanya pillow, ya dada gyara musu duvet din daya rufesu dashi yana kamo hannunta, fuskanta ya tsura ma ido da take bacci cike da kwanciyar hankali, har wani jaxur fatar ta kuma yie najin dadi, ya lumshe ido sanda ya lakuta hacinta da fadin,,

  enmmata inacan ina fama da zafarfan soyayyan kie, da dumbin kewar kie daya hana rayuwa nah sukuni, ke kuwa kina nan hankalin kie kwance, ya sanyaya murya sosai yana cigaba da fadin,,

  ummeetah why, me yasa ba zaki so nie ba, kisan yanda kuwa kika mamaye zuciyar Abubakar sadeeq, ya dauke kanshi daga facing din fuskanta da yakeyi yana zuba ma roof idanu, tsintar kanshi yayi da tuno soyayyarshi da suhymah.

  abin daya sani ita ta fara kiranshi tun randa ta fara ganinshi a gidansu, daga baya kuma suka kulla friendship, daga nanne kuma baisan yanda akayi ya faru ba, suka tsinci kansu a duniyar soyayyar juna, ya ruko yen yatsun hannunta da kyau yana kissing dinsu tare da rungume hannun a kirjinsa, a saman labba yake furta,,

  sonki na daban ne jaruma tah, ya lumshe idanunsa yana karanto addu'an bacci, kafun wani bacci barawo ya saceshi.

   idanunta ta bude a hankali da suka cika da ruwan hawaye, fuskanshi ta zuba ma idanu, tunda ya shigo dakin ta lafe da baccin pretending, ta daura hannunta tana shafa kyakyawan sajen daya kwanta luf a samar fatanshi, takai bakinta tana kissing saman giranshi, kafun ta gangaro bisa kuncinsa, ta dago da fadin,,

  i miss yhu too, i miss so much my darling husband, dai dai sanda hawayen dake cikin idanunta suka gangaro saman fuskanta, duk saiya bata tausayi.

  kenan akwai abin daya hanashi zuwa inda take kenan, ajiyar zuciya ta sauke sanda take share hawayenta, tana murmushi ta daura kanta saman kirjinsa tare da rungume mijinta so tight, wani bacci itama yayi gaba da ita.



   ***
  Duk ya saka rayuwanshi cikin kunci, tun ranar da abun nan ya faru ko baccin kirki baya iya yie, zuwa yanxun yasan yana can tare fa yarinya daya kwallafa ma rai,,

  why why, meyasa a komai ne saiya finie, ya mike zumbur daga kwancen da yake yana girgixa kanshi da fadin,,

  no no wlhy baxai yuyu ina kallo ka mallake komai da komai ba, ya shafi labbanshi da suka kumbure yana cigaba da fadin,,

  na daina zama kana cibga na kamar wani wawa, zan shayar dakai ruwan mamaki, zan kuma maka tabon da har abada ba zai taba gogewa a tarihin rayuwanka ba, da sauri ya zauna bakin gado yana jawo wayarshi da fadin,,

  yes yhu are not longer my brother, ya dago da wani mummunar fuska dake nuns tsantsan rashin tausayi yake fadin,,

  sadeeq yhu are my enemy, ya karisa maganar yana matse wayar dake bisa kunninshi, dai dai sanda akayi picking called din, ya numfasa wajen fadin,,

  mamzet plsss inason wani a'ikine daga wajenka, ka gane so nake ka nemo min contact din wani shahararran rikakken dan fashi dake yanda yake so a yanxun, plssz yau zuwa gobe na baka, shiru ya danyi kafun yace,,

  no, ka manta da wannan ogan naku, kai dai ka nemo min na gasken, akwai wani young billionaire da nake son hadasu dashi, shiru ya biyo baya na wasu yen minutes kafun yasa wani murmushin mugunta yana fadin,,

  good my mamzet i trust dear, sai na jika, daga haka ya katse wayar yana jifa da ita, tare da komawa da baya ya kwanta ragwaf da baje hannayensa bisa gadon yake fadin,,

  takare maka A A sadeeeeq billionaire.

 

  ***
   Cak taji anyi sama da ita daga baccin da takeyi, firgit ta farka za tasa ihu, yayi saurin direta saman gadon yana rungumota tsam a jikinshi da dariya yake fadin,,

  come on, ki natsu wanka za muje muyi, ta bata rai kamar zatai kuka take fadin,,

  Baffah wannan irin tsoratarwa, a'i sai mutum ya kamu da ciwon nakuda bai shirya ba, sassauta rukon da yayi mata yayi yana dago habarta da fadin,,

  da gaske, to nie in hakan ta faru murna a'i zanyi, kisan yanda na matsu naga zareriya nah ta futo duniya, oh my god i can't believe that daya, Allah dai ya saukeki lafia, ya daga mata dan yatsarshi alamar jinjina da fadin,,

  manya manya kinga irin naku nan a labour room, da sauri tasa tafukan hannunta tana rufe fuskanta da murmushi, ya fara kokarin cire mata rigan baccin dake jikinta, ta kuma turo baki tana rike hannushi da fadin,,

  Baffah plss nifa alola zanyi, sai zuwa anjima zanyi wanka, ya zabga mata harara sanda yake kammala cire bottons din gaban rigar yana zame mata da fadin,,

  baki isa ba ki sani wanka nie daya?, ta bata rai da fadin,,

  nie kuma?, yace,,

  tambaya ma kike, ko da ba zaki saniba, tunda sanda kike can kina baccin kie hankali kwance, nie inacan ina fama da mafarkin kie, kasa kawai tayi da kanta donta lura da gaske yakeyi, ta runtse idanunta sanda yaja hannunta zuwa bayin.

  basu wani dade ba, saboda kiran sallar asuba din da akeyi, suka kammala abin

Please Login or Register in order to submit comment