Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kallonsa shima yake, kaman zai magana sai kuma ya fasa, ya karisa wajen fridge din yana dukawa tare da budewa ya ciro maltmilk din, sannan ya rufe yana mikewa, kujeran dake facing din sadeeq din yaja yana zama, ya dan numfasa yana jawo wasu glass cups dake nan bisa dinning din, yana zuba drink din, ya mika masa daya da fadin,,

kaga kasha wannan, ko zaisa kaji dan sanyi sanyi, ya bata rai sosai yana fadin,,

oh, wato Abdullah kana daukar damuwata kadan ne ko, ba kasan cin mutuncin da aka mun bane akan yarinyan nan ba ko?murmushi yayi yana kai drink din bakinsa, tare da one sip ya sauke yana fadin,,

karka damu, munyi maganan da barister kasim, ya fada mun komai, kayi hakuri, komai lokacine zaizo ya wuce, yai dan shiru kafun yace,,

Allah yasa,,

Ameen, cewar barr.Abdullah, kafun shima yayi dan shiru da fadin,,

amma sadeeq sai naga kaman lokaci yayi daya kamata ka bude lamarin, kowa ya san......

what!kowa yasan mene?idan na fahimce ka, ka manta da matsayin ummeetah a wajenan, right, barr. Abdullah ya dire cup din dake hannunsa bisa table, da fadin,,

look sadeeq ban manta komai, amman banga laifi ba, don ka futo ka fallasa kowa ma ya sani, yaja wani dogon tsaki da fadin,,

Abdullah, ummeetah fa, ba rukonta nake yiba, matatace, matar sadeeq, kasan yanda nake fargaban tuna wannan kalman da irin damuwan da nake shiga, kai in kare maka magana, wannan kalman tana iya tarwatsa farin cikina na har abada, da dan mamaki yake fadin,,

kaman yaya ya?ya wani basar da kallon gefe kafun ya maida kallonsa garesa yana fadin,,

farin ciki nah, suhymah nah, ina tabbatar maka duk ranan dana furta wannan kalman, saita kusa hadiyen zuciya ta mutu, yace,,

da sauki, tunda ba zata hadiye zuciyar ta mutu ba, ya karisa maganan da yer dariya, da wani takaici yake fadin,,

funny, ya kuma dan dariya yana fadin,,

no, ka dain cewa haka, gani nayi suhymahn ba wani kula mana dakai takeba, mamaki nake yanda kake sonta me take maka, serious jubi yanda ka dawo, matsayin kana cikin turawa, kuna dan shan sanyi, ka gane irin daga kai sa ita dinnan, kamata yayi muga tubin nan ya zauna ba a nema a rasa ba, idanu ya zuba masa don ya lura gaba daya tsokanarsa yakeyi, ya wani basar da fadin,,

what ever, matata dai, matatace, kuma nie nasan me take mun, inda kwai damuwa na, serious ina fada maka, bai wuce wancan village girl dinba, gaba daya an takura ma rayuwa nah, kaji na rantse maka Abdullah, inda akan business dina ne, na samu labarin wasu matsala, bana taba dawowa kasan nan, duk wannan ina yine don rayuwanta ya inganta, ina kuma dawowan banci karo da matsalan kowa ba, sai nata, barr. Abdullah ya kurbi maltmilk din, yana sauke cup din da fadin,,

Abokina karka damu, ina fada ma watarana sai labari, kuma ladanka na wajan Allah, hakika kana kokari, Allah ya kara taimakon ka, ina tabbatar maka za kaji dadin auranka da ummeetah, ya dan tabe baki da fadin,,

kai, ban jinba, infact to tell yhu the truth, kunyan kiran wannan abin matata nake jie, ya zaro ido da fadin,,

kut, kalaman ka sun girmeni, nie ko kaga, kwanan nan, zanyo ta biyu, galleliya nake fada ma, da sauri sadeeq ke fadin,,

what, matar taka fa, duk soyayyan da kake mata, yai dan tsaki da fadin,,

kaga sadeeq, soyayya baxai sa na zauna da kunci ba, na gaji da halin sakeena na kazanta, wannan ne kawai matsala na da ita, kuma dalilin da zaisa na kara aure, muhalli bata gyara, ita kanta bata gyara kanta ba, to ta ina zan zauna, cikin tausayin sakeena, don yasan yanda itama tana son abokinsa sosai, sadeeq ke fadin,,

kai amman baka mata adalci ba, yai dan dariya yana fadin,,

adalcin kenan, ana maganar 6years da aure nefa sadeeq, ka zuba ido kwanan nan, zaka ga bab din mai zafi, ina fadama, dai dai sanda ake kwalla kiran sallah, sadeeq ya fara mikewa tsaye, da gyara kwallan riganshi daya cukurkude, shima barr.Abdullah ya mike da fadin,,

ya kamata ku zauna da mutumin nan, don a tattake magana, akan lafazin da yayi gareka, ya nufi wajen babban table din yana fadin,,

no, kyalle wannan mahaukacin, inda sabo na saba, ba yau ya fara fadi ba, countryn ma zan bari, don ba zama naxo yiba, in nayi ra'ayi sai nayi zamana acan, barr. Abdullah na dan dariya da fadin,,

ah, dole ummeetah zata dawo dakai, dan tsaki yayi, yana karisa cire wrist watch din dake tsintsiyar hannunsa, tare da ijewa bisa table din, ya wuce wajan wani kofa da nake tunanin ko bayi ne, yana fadin,,

kaga, nie bari na shiga na dauro alola, inaso na wuce gida ne, in mun futo masjid, don kasan tunda na diro, nan na fara wutowa, barr. Abdullah na fadin,,

yayi, ka futo nima inyi alolan, sai mu wuce masjid din tare.

comment
share
Matatace
*2019*

meemartjj...........✍🏻
[14/08, 14:28] Dala Grp: 🕯🕯🕯
*MATATACE*
🕯🕯🕯


story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjj


*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty Ummeetah and my Fa'ixation._


page 13&14

-----------Da wuri yau suka taso makaranta, kasancewan jarabawa suka fara, duk ta gaji, gefe guda kuma ga fargaban da inta tuna, zata dawo gida taga dodon nata muheet, duk yabi ya gama takura ma rayuwanta, in tana da matsala a yanxun bai wuce nashi ba,,

ranta bace ta dire school bag dinta, gefen gadon dake dauke da up step, ta zauna da dan numfasawa, tare da kwabe hijjab din dake jikinta, gidan tsit da alama su muhibbat basu dawo daga nasu school din ba, mikewa tayi tana jawo wani towel dake ninke gefe daya, ta soma cuku cukun cire uniform din,,

bayin dake bedroom din ta fada, shap shap ta gama wanka tana dauro alola, tare da futowa ta bude site din wardrobe dinta, tana ciro undies da zatai amfani dasu dake tsare gefe daya, shap shap shima ta kammala shiryawa, kafun ta zaro wata pited gown na plane material, sabo ne, bata taba sanya kayan ba, auntynsu tasa aka dinka musu ita da muhibbat, na muhibbat ya jima da shiga cikin ruwa, itako son da take ma kayan ne, yasa ta kasa sawa, sai yau kawai taji shi take son sakawa,,

kaman zata sanya, sai kuma ta ije gefen mattress, tana jawo wani zani clean one dashi, ta daura bisa black skinny din da ya tsaya mata dai dai gwiwa, tare da vest a saman shi, ta maida hijjab dinta, tana shimfida dadduma da kabbarta salla,,

bayan ta idar ta shafa addu'an, tare da mikewa, ta nade dadduman, sauri sauri ta kammala yen shafa mayukanta, dake gefe daya bisa dan design mirrorn, wanda suke kallon kayan shafan muhibbat, kowa da site dinshi,,

ta saka rigan da addu'an saka sabbin kaya, tare da ziping dinshi, das yayi mata, komai ya zauna dai dai, dikin up shoulder ne, don haka kyawawan kafadun suna bayyane a waje, golden colour ne, sai adon wasu flowers guda biyu royal blue, a saman rigan,,

kuri tayi ma kanta jikin mirror, tana bin fuskarta datai fayau, tare da fatar jikinta daya kuma washewa da taushi, ta dan tsuke labbanta tana kuma kallon yanda rigan ya kamata, daga saman har kasan komai ya zauna da kyau, ta danja rigan da tsaki, tare da raya,,

kai wannan ma ya cika matsewa da yawa, meta tuna kuma, sai tayi wuf, tana kwance ribbon din data tamke gashin dake tsefe, sama sama take tajewa, nan kuwa ya cika mata wuya zuwa gadon bayanta, don tsaban cikan da gashin yake dashi, ta kammala tana maida ribbon din, a tsakiyar ka tayi packing,,

da dan murmushin take maida wani dan viel ta yafa, tare da maida komai muhallinsa, sannan ta wuce dakin maami, inda zata kai mata gaisuwan rana, kafun ta wuce waje su karisa a'iki da baba balarabu.

har ta nufa dakin maami, sai kuma ta tuna da safe, sunce zasu futa, ita da aunty mainat, don haka kitchen ta nufa, ta samu baba balarabu na faman a'iki,,

babah, sannu da a'iki, cewar ummeetah, ta dan juyo da fara'a tana fadin,,

yawwa ummeetah, an dawo?tace,,

eh, naga su maami basu dawo ba, tace,,

a'i yanzu haka suna hanya, ta nufi wajen kulolin da babahn ta shirya abinci, da nufin fara kaiwa dinning, da sauri take fadin,,

a'ah, barsu zan shirya, maza kije tun dazu ladiyo ke faman a'ike kije, ina jin zata saki wani a'ikin ne, gaban ummeetah yace rass tana raya,,

nie kuma, mezan mata, ta tsani zuwa sashin, sai kuma ta juya zuwa dakin su, gyallen ta cire, tana saka hijjab iya gwiwa, sannan ta wuce.


Ta back yard din sashin ta shiga, tana bakin fanfo tana fama da wanke tunkuya, yayin da bintu ke cikin local kitchen din sanye cikin uniform na junior government school, white and navy blue, tana daka cikin turmi, ansha hijjab din nan dan guntu, da uban acuci daya daga can sama, sai fuskan daya sha local make up, kaman ba makaranta za aba, da murmushi na karisa ciki ina fadin,,

bintu baki tafi makarantan ban?, ta amasa da,,

eh, yanxun zan tafi, ke harkin dawo ko?

eh, kinsan muna exam n...... maganan innarta ya katseta dake fadin,,

ke yennan, zonan ki mun abin da zan saki, ta juyo tana gaisheta, ta dan yamutsa fuska tana yafito ta da hannu, alamar zo kawai, binta tayi cikin modern kitchen din, ta kinkimo wani basket da yaji kayan abinci na alfarma tana fadin,,

maxa wannan, ki kaima muheet, can sashin su, abincin ranan sane, cikin fargaba ta zaro ido da fadin,

yaya muheet kuma?ta zabga mata harara tana tabe baki, cike da tsana, kwata kwata haushin yarinyan take ji, yanda aka maisheta kaman ba yer a'iki ba, tana masifa da fadin,,

eh, shifa uwar tsirfa, da Allah dauka ki wuce mishi dashi, tun dazu yake jira, ranta bai soba ta dauki basket din, tana fadin,,

to bari na kira bintu ta rakan......

a'ah maza ki wuce, baki ganin ita makaranta zata, ta daka mata tsawa da wannan, dole yasa ummeetah wucewa tayi can haryar boys quarters din, gabanta na wani irin fadi, ko wani addu'a yazo bakin yie take.

Taja birki bakin kofa ta tsaya, sai data runtse ido, kafun ta fara knowking, tafi minti biyar kafin ya bude kofan, daga shi sai three quarter da singlet, ya saki wani murmushin nasara, lokacin da yake ganin kaman ya gama samun abin da yake so ne, yadan zuba hannu bisa kai yana shafa sumar kanshi da fadin,,

enmmata kece, ta kauda kanta gefe a dake take fadin,,

gashi lunch dinka ne a kace in kawo maka?ya dan matsa daga kofan yana fadin,,

ouk shigo mana, sai lokacin ta dubesa, da madaran yaudaran da ta gani cikin idanunsa, kai tsaye ta ije basket din a kasa, tana dan ja da baya da fadin,,

a'a, basai na shiga ba, sauri nake, ta juya kenan taji ya fisgo hannunta, ba tare data shirya ba tajita cikin karamin falon, ya cikata yana saurin maida kofan ya kulle, tare dasa key, aka bar basket din abinci nan wajen,,

sosai ta shiga halin tsorata, tana ja da baya, ya juyo rai bace, yana wani hararanta da fadin,,

banxa harke nan, jikinta ya soma kyarma tana fadin,,

yaya muheet don Allah kayi hakur......

shout up, stupid, kinsan irin enmmatan dake rushing akaina kuwa, yaja yana jingina da jikin bango tare da harde hannu bisa kirji, yana binta da wani kallon wulakanci, da cigaba da fadin,,

saike banxan a banxa, zaki nemi ki bata mun lokaci, ki bata ma kanki, tuni zufa ya rufe ummeetah tana hadiye wani kunci, a zuciya kuwa fadi take,,

plsss wazai taimake nie, ta soma fadin,,

innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, ganin yana matso inda take da murmushin mugunta, itama ta soma jan baya da raya,,

wai me yaya muheet yake nufine, wayyoo maami, aunty mainat, muhibbat, don Allah ku taimaka mun, can kuma zuciyarta ta dage tana fadin,,

yaya muheet kaga, nace don Allah ka rabu dani, koma menene zan maka ta lalama, sai kuma tayi shuru, da dan shashshekan kuka take fadin,,

don Allah kayi hakuri, najie zan dauko abincin in shigo dashi, sannan in sa maka, plss na rokeka, cak ya tsaya da tafiya, kafun yasa wata dariya yana dan tafa hannu da fadin,,

what!, kima daina wahalar da kanki, ba wannan nake bukata ba, da dan mamaki take fadin,,

me kake bukata?ya kuma kyacewa da dariya, yana matsota da fadin,,

wait, yanxun zan nuna miki, a razane tayi ninyar barin wajen, tanu nufa bakin kofan, yayi nasaran kama hijjab dinta, ta saka wata razananniyar kara, kaman wacce ya rike ma jiki, yana fadin,,

tun yanxun, ya soma cuku cukun rukota, ita kuma tana kokarin kwacewa, tuni ta fara kuka sosai, sanda taji yana kokarin riko hannunta, hijjab din ta zame, tana barin masa a hannu, tare dayin wajen kofa a kidime, tana jan handle din, amman kulle yake gagam, kuka take sosai, hankalinta ya tashi matuka, don bata taba cin karo da irin wannan matsalan ba,,

muheet kuwa tsaye kawai yake, da hijjab a hannu, surur jikinta ya matukar rikitar dashi, ba abin da yake ayyanawa irin,,

ashe haka yarinyan ta wuce tunanin ninsa, shaitan kuma na zugoshi da fadin,,

karka sake wannan damar ta wuceka, zaka samu abin da kake so, a fili kuma yana fadin,,

yess, hakane, baxan iya barin wannan kayan ba, ya dan runtse ido, dasa harshe yana lasar labansa na kasa, kafun ya jefar da hijjab din, ya kuma yo kanta, ummeetah dake jikin bango tana zufa da faman rera kuka, ta kara juyawa wani site din, tana faman rokansa, shiko beji be gani.

A katuwar jeep din mai dauke da tambarin companyn A A sadeeq, akayi packing dinsa, a packing space din gidan, bayan gate man ya bude musu gate, drivern ya shigo da motar, da sauri ya futo zai bude mishi kofan,,

dai dai sanda ya bude da kanshi ya futo, a wani gajiye, rike da dark blue din suite a hannunsa, ya rage sai farar botton shirt din mai hannun long slip a jikinsa, wanda yasha toking da wani classy belt,,

wayane a kunninsa, kusan tun sanda ya shiga motar yake wayan, har yanxun daya futo, da alamu wani abokin business dinshi ne, daga driver har gate man dake tsaye gefe, da hannu yake amsa musu gaisuwansu, ya nufi bayan motar da jingina yana cigaba da waya, yayin da yake facing hanyar daxai kai mutum boys quarters din,,

can kuma ya cigaba da dan tafiya yana wayar, dodar ya mike hanya, ganishi kawai yayi a site din, wata yer doguwar farar kujera ya gani, bisa floor din dake entrance din wajan, ba bata lokaci ya samu waje yana zama da dan harde kafafu, yana cigaba da amsa wayar,,

kaman daga sama yaji kaman alamun kuka, da farko yasha gixo ne kawai na kunni, can kuma yaji abin kaman da gaske, da sauri yake matsawa da wayar daga kunninsa, yana dada saurara, zaraf ya mike, yana kuma kara wayar a kunni da fadin,,

plss excuse me, daga haka ya katse wayar yana maidawa aljuhun wando, tare da fara knowking kofan, yana bin windows din da suka jie tafka tafkan cottons ta ciki, shi mamaki yake ma waye a cikin boys quarters din yanxun,,

jin haka yasa ummeetah sakin wani ajiyar zuciya, amman kafun ta kuma wani kwakwkwaran motsi, muheet ya iso gareta, cikin sauri ya matseta tare dasa hannu ya rufe mata bakin, duk yanda taso ta fidda sautin magana ta kasa, tana jie aka rika bubbuga kofan, amman yayi lakwas kaman babu kowa a dakin,,

oga kuwa daya lura, gixon kara ne kawai kunninsa ke masa, yasa shi dan tabe baki yana juyawa,,

iya karfinta tasa tana yanka mishi cixo a hannu, ya cikata yana wancakali da ita bisa tyles, da kwala ihun,,

ahhh, cikin murya irin ta gardawa, da yafi fitowa, a razane sadeeq ya kuma juyowa,,

what!da gaske fa, akwai abin dake faruwa ciki, ya karisa da nufin kuma knowking kofan, sai dai muryanta ne ya tsai dashi, tana faman fadin,,

don Allah na rokeka, karka cutar dani, plsssssss yaya muheet, nifa kamar kanwar kace, don Allah ka taimaki rayuwan yarinya marainiya irina, cikin bacin rai ya zabga mata harara, besan lokacin da yake fadin,,

over my death body, duk wani kururuwanki, da iface iface kie gama, amman ina tabbatar miki, da bamai zuwa nan ya kwace kie, yau gidan daga nie sai ke, duk rowan kie yarinyan saina lasa zuma, kuma bari na kara fada mik, baki da matsayin daya wuce na yer a'ikin gidan mu a wajena,,

dan rutse ido yayi, zuciyarsa na rayo masa,,

ummeetah, tabbas voice dinta ne, muheet kuma, sai yanxun ya tuna ma da yaron ya dawo fa, to amman ummeetah, she is still young, me zes..... sautin kukanta ne, ya kuma katseshi, ya numfasa yana bin basket din dasai yanxun ya lura dashi a wajan, wani kuna zuciyarsa ke masa, sanda yake jie kaman ya bude ido ya gashi ciki, sai kuma ya dai daita natsuwarsa da fara fadin,,

muheet kana jina, bros dinka ne, plss open the door, ya dan runtse ido da takaici yake dukan iska da fadin,,

ohh shet!bros kuma, meya kawo shi, yaushe ma ya dawo?ya rasa amsan tambayan, can bangaren sadeeq ya kuma gyara murya yana fadin,,

yaa bros, ka bude kofan mana, plss magana kawai zan maka in wuce sauri nake, ya dan nisa, kafun ya duka inda ummeetah ke wancakale jikin bango, ta kasa tashi, shashshekan kuka kawai takeyi, ya damko gashinta datai packing, yana daura yatsansa bisa lips dinshi da fadin,,

shishshsh, dole ta gimtse kukanta don azaba, yana mata concrete warning, akan zai bude kofan, karta sake bros dinshi ya fahimce wani abu, intai haka ta kwace kanta, zai barta ta tafi, daga haka ya cikata yana nufa wajan kofan,,

da wani barinkanci ya bude kofan, yana tsayawa kane kane, da yike cotton ya rufe ciki, yana washe baki da fadin,,

yaaa bros yaushe a gari, kallon kallo suke da juna, kafun yasa hannu yana wani hankadashi ciki, sosai yayi can baya kaman zai fadi, shima ya kutsa kai ciki, ya dawo bisa kafafunsa yana taran gabanshi cike da wani borin kunya, da fadin,,

bros muje daga waja ne mana, bebi ta kan shiba, yake kuma tureshi gefe da kalle kallen karamin falon, kafun ya fara kiran,,

ummeetah!kasancewan be hangeta ba, tana yashe a kasa, mararta ke wani irin ciwo, ta dafe hannunta biyu bisa tyles, kanta a kasa yayin da gashinta ya yarfo ta gaba yana rufe mata fuska, kokarin tashi take, idonsa caraf a kanta, da raya,,

anya wannan itace, kai sai dai wata yer a'ikin, a hankali ta dafe tyles tana mikewa, kafun tasa hannu rana gyara gashin kanta, tun daga kasa ya fara kallonta har sama, itace dai, ummeetan daya sani, itama tana kallonsa da zufan daya jika mata fuska,,

ta kuma zaro ido da mamaki, tana kallon fuskan da ko kadan a mafarki, bata taba sawa zata ganshi ba, yaxo taimakon ta, da wani reverse yake kara kai mata duba, tun daga sama kuma har kasa, kafun ya dan runtse ido, a zuciya yake raya,,

itace kuwa ta girma haka?can kuma sai ya juya da kallonsa kan muheet, dake tsaye gefe yana faman sosa keya,,

wani kishine ya tokare mishi kirji, ya watsar da suite din nan kasa, yana wani kai mishi shaka, tare da hadashi da jikin bango, cikin sauri, muheet ke rike hannun dan uwansa dasa ihu, jin irin azaban shakar da yayi mishi, ya kafe shi da idanunsa da suka kankance don bacin rai, kafun ya dunkule hannu kaman zai kai mishi nushi, yana cije baki da fadin,,

matar....... sai kuma ya tsaya da maganar, yana fasa kai nushin, tare da kuma shakeshi, muheet kuwa jin za'a kusa kashe shi, yasa shi fara mutsu mutsun kwacewa, ko kadan amman ya kasa, ummeetah dake can gefe jiki na rawa, take fadin,,

Baffah sadeeq zay....... jin hakane ya sashi juyowa a wani fusace, yana dawo da kallonshi gareta , tuni ta hadiye sauran maganan, ya cikashi da barinshi nan zube bisa gwiwowinsa, yana dosar inda take da fadin,,

uban me kike a nan, baki bace ba, ganin yanda yayo kanta ne, ya sata kwada ihu, tana yin baya tare da nufa kofa a sittin, yayi saurin rukota, saiji tayi ya damko damtsen hannunta cikin sauri, ya juyo da ita tana wani irin girgixa, komai na jikinta sai daya motsa, be tsaya wata wata ba, ya wanketa da mari, ta kuma saka kuka, yana fadin,,

a haka kike nufin fita waje, ke mahaukaciyar ina ne, ko suma masu gadin tallata musu jikin zaki yie, ta soma girgixa kai da fadin,,

a'ah, na rantse Baffah sadeeq ba talla zanje mus.......

shushshsh, ya fada da daura manunin yatsanshi bisa tattausar labbanta, masu dan kauri, kafun ya wani jawota tsakiyar falon, inda hijjab dinta yake yashe yake nuna mata, a balake ta dauka tana sakawa, tare da barin falon a firgice, shima suite dinsa ya dauka yana bin bayanta, da wani kuna da zuciyarsa ke masa, dai dai sanda muheet ya mike yana faman fadin,,

Allah ya isa, ba kuma zan taba yafe maka ba, mugu kawai, kullum burinka bai wuce ka zalunta ma mutum b..... a zuciye ya juyo yana dawowa gareshi ya wani daukeshi da mari, ya dafe kumatu daja da baya, kan yayi wata maganan ya kara kai masa wani marin, yayi masa uku lafiyayyu,,

ba shiri muheet yayi saurin shigewa bedroom yana rufo kofa, da cigaba da surfa mishi Allah ya isa, yayi hanyar futa da ayyana,,

baka da laifi, laifi nane dana saurare wannan yer rainin hankalin, na bar mata yarinya, a karshe zata sa akaini a baro, ya tsalleke basket din dake bakin kofa har lokacin, yana nazarin irin tarkon da muheet ya dana ma yarinyan, amman yafi ganin laifin mainat, bari yaje itama ya sameta.


comment
share
Matatace
*2019*

meemartjj...........✍🏻
[14/08, 14:29] Dala Grp: 🕯🕯🕯
*MATATACE*
🕯🕯🕯


story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjj


*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty Ummeetah and my Fa'ixation._


page15&16

--------------Umeetah bata zame ko ina ba sai sashin su, cikin sauri take shiga bedroom dinsu, tare da zama bakin gado tana dafe kirjinta dake bugawa kaman ya futo, da kuma sauke ajiyar zuciya, tana dan rufe ido,,

muryansa taji a can falo, suna gaisawa da babah balarabu sama sama, haryanzu muryan cike da bacin rai, taji yana fadin,,

ina mainat take?babah tace,,

a'ikam sun futa tare da maami, dan tsaki yayi, kafin ya kuma fadin,,

wannan yarinyan fa ummeetah,,
yanzu naga ta wulka daki, cewar babah da sauri, ganin ran maza a bace yake, cikin takun izza yake nufo hanyar bedroom din, jin haka yasa ummeetah mikewa cikin sauri ta shige bathroom, tare da tsiran wankan dole,,

ya daga cotton din kofan, yana bin kofan bathroom da yake jin alamun saukan ruwa da kallo, ya zabga ma kofan harara, kaman shi yayi mai laifi, tare da sakin labulen, ya wuce kitchen, still da zuciyarsa dake cigaba da suya, a nan ya tarda ita yana fadin,,

wacece tasa ummeetah takai ma muheet abinci?babah tace,,

a'iko inajin ladiyo ne, don ita ta kirata,

wacce ladiyo kuma?ya kara jefo mata tambayan, tace,,

mai ma haj. karama yen a'ikace a'ikace, tsaki ya kuma yie, yana wucewa da fadin,,

babah don Allah koba ummeetah ba, kar a kara ba wata yarinyan ta abinci takai mishi, da sauri tace,,

toh, in sha Allahu, daga haka ya futa ta kofan backyard din.

itama a kitchen ya sameta zaune, zata fara cin abinci, ta mike da sauri, zaton tah muheet ne, sai da ta mike ta fara washe baki da fadin,,

a'ah, uban masu gida, kaine a garin namu, lale lale marhaban, ya yatsuna fuska, cike da muryan nan na yangan da kasaita, yana fadin,,

uhmmm hmm, nagode, ance kice kika ba ummeetah abinci takai sashin muheet ko?cikin dan inda inda, harda dan zufanta na rashin gaskiya take fadin,,

a gafarceni ina nayi laif....... ya dan daga hannu da fadin,,

kinga ba wannan dogon turancin ba, don Allah dai bahba a kiyaye, nan gaba koba ummeetah ba, kar akara ba wata yarinyan takai mishi abinci, kaman ta zube take dukawa da fadin,,

to......to.....toh, in sha Allahu an gama, be tsaya sauraran taba, yayi hanyar cikin gidan ta ciki, saudat ta mike daga laben da take da sauri tana koma cikin falon,,

ke, shine ya tsada ita, ta juyo tana mishi sannu da zuwa,,

mummy fa, bata nan ne?yake tambayarta,,

eh, taje office, saima lokacin ya tuna, koda beje can dayan sashin companyn nashi ba, inda take manager a wurin, ya juya yana komawa sashin maami, da fadin,,

kibama wancan matar key din sashin baki a gyara mun, daga haka ya fuce,,

tom, shine abin da saudat tace, tana sauke ajiyar zuciya da raya,,

su yaya muheet anyi halin kenan, shi kuma sai wani masifa yakeyi kamar wata yer uwanshi, hmm baisan halin yarinyan nan bane, ita da

Please Login or Register in order to submit comment