Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suna hade da juna, cike da ba'a yake fadin,,

   wow, wato sunana ne ya koma sweet right?a tare suka sanya dan dariya shida  ma'ikatan wajen, don sun san wannan umurnin da ordern shine, ya cigaba da zaga wajen, ana wasa ana dariya, komai na tafiya dai dai yanda ya kamata, be wani jima ba yabar wajen,,

   daga nan kuma, wasu quarters dake can ta gefe ya nufa, ginin plat masu kyau, daya daga ciki lamido ne a ciki da iyalanshi, tun sanda su lado suka sa mishi tsama, kan hard dashi a muna munan da akayi, wancan mara mutuncin ya kwashe dukiyar dan uwansu, yabar garin, shine sadeeq ya sashi daya daga cikin ma'ikatan wajen, yana zaune a nan, koda yaje su gaisa baya nan, don haka direct wajen motar ya dawo,,

    suka tafi, yana farin cikin yanda komai yake tafiya dai dai, yana da buri sosai akan ummeetah, yana son wata rana duk wasu da suke dauka wani ba wani bane, kuma bai isa ya zamto wani abuba, to su gane cewa, duk zakaran da Allah ya nufa da cara fah............tom ku karisa sauran.

   sosai aka cika musu leda dasu guava, mango da sauransu, sai madaran shanu da aka dibo, da sunan tsaraban da suka samo rugan su ummeetah,,

    ko ciki driver be shiga da motar ba, suka sauketa bakin gate, driver ya bude mata booth, ta dauka farin ledan a hannu daya, sai karamin white bucket din dake dauke da nonon shanu fari tass, ta nufi cikin gida,,

   ya sauke ajiyar zuciya yana binta da kallo ta cikin motar, harta shige ciki, dai dai sanda driver ke shiga motar da fadin,,

   yallabai ina zamu wuce?, idanunsa lumshe yake fadin,,

  muje muyi sallah magrib tukun, zaka wuce dani guest house dina,,

   toh yallabai, shine abin da driver ya fadi, yana ma motar key.

  Ta shiga gida sanda aketa faman kiraye kirayen sallah magrib, sashen su ta nufa duk ta gaji, dai dai sanda munirat ta futo daga sashin, kanta a kasa rike da waya tana faman latsawa, dan motsin tafiya taji ta dago, a firgice tayi baya kaman zata fadin, tana kallon ummeetah a wani tsorace, da hasken futullun da suka kawata wajen, da dan mamaki ummeetah taja ta tsaya da fadin,,

  lafiya dai?kallo ta gama kare mata, kafun ta tsaya da kyau tana turo baki da dan katon muryan nan nata, take fadin,,

   ke ba ance yayan mu, ya tafi maida ki kauyen ku bane?shiru ummeetah tayi, kafun tace,,

   eh, amman a'i yau dama zan dawo, kaman zata kara wani maganan sai kuma ta fasa, ta nufi sashin su da sauri, don takai tsegumi, tana tafe tana kallon ummeetah, itama kallon ta bita dashi, kafun ta dan nisa tana wucewa ciki,,

  a falo taga auntyn su data dawo weekend gida, da fara'a ta tareta tana tambayarta ya mutanan gidan, ita dai ummeetah murmushin yake tayi, tana fadin suna lafiya, kafun ta wuce kitchen ta ije kayan, sannan ta wuce dakinsu, inda ta samu su hibbat anata gabatar da sallah magrib, itama hijjab ta cire,  tana daura ninya da shiga bayin dake nan dakin.

 

  *fatan alkhairi*
  

comment
share
Matatace
*2019*

meemartjj...........✍🏻
🕯🕯🕯
            _*MATATACE*_
     🕯🕯🕯

     

story&written by Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@meemartjj

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚

   *Dedicated to lovely sisters*
_Jameela ja'afar yakubu_
_Fateema ja'afar yakubu_
_Fa'iza ja'afar yakubu_

 

   _Ina masu son littafin matatace daga farko, wasu sunyi mun magana jiya, amman nayi updating wattsapp dina, don haka na rasa contact dinsu, zanyi sharing link na group din Matatace fans, duk mai bukata daga farko saiya sambado ciki, in sha Allah zai samu_

page 25&26

____________Binsu kawai take da idanu, suna faman maimaita zancan da turo baki, alama basu jie dadi ba, itakam basu san ta fisu shiga ciki halin damuwa ba, takaici yasa ta sa musu tsawa da fadin,,

   plss ku fuce ku bani waje, kun cikani da surutu, da sauri suka mike suna futa, saudat na daga kiran Najma, wadanda yau suka koma gida, duk baya 30minutes saisun kira sun tambaya brothern nasu ya dawo shi daya, ko kuwa da ummeetah, saudat ta kuma hada rai, da alama za suji mammunar batu.

   bayan futansu ranta yayi matukar baci, tana mamakin abin daya hana wannan a'ikin yin musu yanda ya kamata, gashi ko yau da safe sai da dan lelen nata yayi maganar yarinyan, tsaki taja tana raya,,

   bara dai na kira malamin nan, naji daga ina wannan matsalar take, ba bata lokaci ta doka mishi kira, ta danji sanyi sanyi, sanda yake mata bayanin, ta kwantar da hankalinta, komai sa anbi a hankali ake cin riba, da wani farin ciki kuwa take sauke wayar, tana kuma kishingida sosai jikin lallasar pillown dake bisa lallasar katifan dake bisa makeken gadon, da dan murmushi take daura hannuta saman kai da fadin,,

    haba gwara dai tayi gaba, taje can kauyen su ta nemi kalanta, rore roren fulani, taja tsoki da wani irin takaici, kwata kwata ta tsani yarinyan, yaron da take burin wata rana ya auro musu yer governor ko sama da hakan, shine za ace ya kare da house girl yer talakawa irinta, ina baxai sabu ba, baxai kuma taba sabuwa ba.

                      ***

     Tsararran gidane, ginin zamani dan madaidaci, wanda ke cikin fencing din da aka tsara mai dauke da tsadaddan gate, tun daga falon abin kallo ne, har zuwa cikin,bedroom din,,

   sanye yake cikin wata arabian jallabiya, mai yakakken hannu, turaruka ne da mayuka masu tsada zube bisa dresing mirror din da yake zaune bisa stool dinshi, gwiwan hannunsa na tokare bisa mirrorn, yayin daya dafe kanshi dake kallon kasa, da tafin hannunsa, idonsa a lumshe, da alama akwai abin da yake so, dan tsaki yayi yana mikewa, tare da nufa wajen tsararran bed din, da yaji shimfidu da matasai na alfarma,,

     babu wani wadataccan haske a dakin, bed site lamp ne kawi a kunne, gyara pillow yayi da kyau, yana kwanciya, da facing pop dake up din dakin, tsinstiyar hannunsa na dama ya daura saman kanshi, tare da jawo phone dinshi dake gefe, yafi 2minutes yana kallon numbern nata da wani kayataccan smiling, kafun yayi dialing, yana jin wani kewanta a tare dashi,,

   kaman jiran kiran nashi take tayi picking, da wani zafaffen kiss tai mishi sallama, tana fadin,,

   i miss yhu so much dear, ya runtse ido, sanda wani abu ke tsirga mishi tun daga kanshi zuwa yen yatsun kafansa, a dan rikice ya bude ido da fadin,,

   angel am in pain, i need yhu baby, shiru tayi da wani dariyan mugunta, tasan tabbas wannan voice din nashi ya tabbatar mata da abin da yake fada, ya dan bata rai da fadin,,

   so, yhu are enjoying it right? kinsan kuwa yanda nake jie?kaman tana ganinsa take kuma zukewa cikin blanket da take kwance ciki, tare da karkada gwiwan kafan data daga, tana sakin wani murmushi da fadin,,

  sweetheart karka damu, muryan kama kadai ya tabbatar mun da haka, kasan wani abu?nima nayi kewan ka, ba zaka gane ba, saika dawo, ta wani sanyaya murya da fadin,,

  my baby boo, my honey, komai naka ne, just came back soon, nan kuwa ya dada rikicewa da fadin,,

  i will in sha Allah, my angel kie zuba ido kawai, baxan iya kara good 7days ba, ba tare dake kusa dani ba, i miss ur huge body baby, ta dan bigi kirjinta da fadin,,

   we miss yhu two darling, yawwa na tuna, akwai abin da nake son tambayarka,,

  what?shine abin daya fada yana kuma sauraronta, ta yamutsa fuska kafun tace,,

   dama wannan ummeetah tare kuka futa yau? yana dan daga gira sama yake fadin,,

  ohh, eh kinsan naje nayi zumunci yau dinnan, shine ma dalilin da yasa kika jie duk na gaji haka, ta tabe baki da fadin,,

  sweetheart kaima ka sone, amman na fada maka basai kana wahalar da kanka ba, gaisuwa a waya ma ya ishesu, yanxun dai fada mun inda kaje da yarinyan, tunanin ma gidansu zaka maidata, da naji ance tare kuka tafi, shiru yayi yana neman abin dazai fada, kawai saiya maida zancan wasa da fadin,,

   ba ko ina, rako kawai tamun, mmuka dan zaga gar........,,

  sadeeeeeeeq, shine abin data fada cikin karaji, da sauri yake dan kauda wayar daga kunninsa, yana dan dafe kunnin, alamar karan ya shigeshi, kafun ya maida wayar yana dan smiling, dama yasan yanxun za suyi da ita, ya numfasa da fadin,,

  angel come on, kinsan wasa nefa nake miki, zaki fasa mun dodon kunni, wani yer munafukan tsaki taja, kafun ta fara fadin,,

   kaga sadeeeeq nace kabar mun irin wadannan wasan, ko zaka mun, ka rika hadani da yer senator, minister irina, ba irin wancan jahilan ba, dangin matsiyata, tswsss, ta kuma jan tsaki, sosai abin ya sosa ranshi, yana kuma maimaita word din a zuciyarsa,,

   jahila, jahila, kai ummeetah ta wuce matsayin a kirata da wannan sunan, ko ba komai yasan yarinyan is very interlengent, yatsina fuska ya danyi da fadin,,

   ouk, ammm inajin tare fa zamu dawo, saboda ta rika taimakawa da wasu a'iki a cikin gidan, hope kin fahimta,,

  dududu dummm, shine,abin daya sauka a zuciyarta, bata san me yasa ba, hakanan kawai yanxun bata son kuma yarinyan kusa da ita, amman data tuna wani abu sai mazewa tayi da fadin,,

  ouk sai kunxo, hope xata kwaso duk wani kwaxanta na a'iki, saboda akwai responsibilities da yawa da zasu taru a kanta, wannan maganan nata ma, sai daya yayie ta juyata a kwakwalwan shi, kafun yayi dan murmushin yake da fadin,,

   ba matsala, ma daman gimbiya tah tayi farin ciki da hakan,,

  of course, why not, hutu nanefa, kaga sai in kara narkewa a kasan US, ta fada cike da zumudinta, shidai murmushi yayi, kafun suyi sallama yana katse wayar da kuma nazarin kalamanta,,

  ya dan numfasa sanda idanunsa fess suka sauka kan hotanta dake manne jikin desktop wallpaper din wayar, dama na yaronsa Irfan ne a lockscreen wallpaper din, sai nata a kan desktop din, murmushi yayi yana zuba mata idanu, sanye cikin shigan mutunci ansha dauri, tana murmushi sosai,,

  kaman wasa kuma hotan ya soma juye mai na yarinyan, daro idanunsa yayi waje, amman har lokacin ita yake gani, hotan ya zauna rass, har yafi a'inihin wanda yake kai kyau, dan tsaki yayi yana murza idanunwansa da yen yatsunsa, kafun ya bude, yanxun kam a'inihin hotan dake kai yake gani, ya kuma jan wata yer tsaki, da sauke ajiyar zuciya, kafun ya maida wayar yana ijewa daga gefe daya, ya kuma gyara kwanciyansa da kyau, ayyana abubbuwa masu dama.

                        ***

   Ta kammala share ko ina na site din nasu, dama karfe 7am ta kammala yin shara, zuwa 8:30 ta gama dasu moping tana wani a'ikin, sai da yau har kusan 9am tana moping, ta gama da wasu wajen tana na falo, wanda yake karshe, kaman an tsunguleta da sauri ta saki mopern cikin bucket, tana nufa kitchen inda tiriri ke tashi.

     karaman tukunya ne daure bisa gas cooker, ta ciro kwai da hantar da take dafawa, tare da maida sanwan indomie da zata dafa, tuni kitchen din ya dume da kanshi, sauri sauri ta gama yayyanka kwan da hantar, kafun ta koma tana dicing green paper dasu albasa, idanunta sai yaji yake, tana gogewa, ga uwar zufa da takeyi,,

   mainat ta shigo kitchen din da sallama, ummeetah dake daga can wajen cookern ta amsa mata, tare da daurawa da gaisheta, amsawa tayi tana nufa wajen katon freezern dake gefe daya, da daurawa da fadin,,

  ummeetah anata a'iki ne?

   eh, tace tana kuma share zufa, ba tare da ta kalli inda take ba take bude freezern da fadin,,

   toh sannunki da a'iki, ta karisa maganan tana ciro manya fresh mangos din guda biyu cikin freezern, ta nufi zink tana wankewa a fanfo, tare da zarar wani karaman plate a plate hanger, ta zuba ciki, ta hada da yer karamar wuka daga gefe, har zata wuce, idanunta suka sauka bisa ledan indomie da aka tsira har kusan biyar, kusa da inda ummeetah ke girki, ta kuma san ummeetah ma indomie be dameta ba,,

   toh waye ya sata wannan a'ikin da sassafe, gashi ko a'ikin da takeyi a falo taga bata gama ba, tasan kuma ba maami ban....... tunaninta ya katse sanda saudat ta shigo kitchen din ta kofan baya, tana faman kwala kiran,,

   kee ummeetah kin gama mun girki nah, turus tayi da ganin auntyn nasu dake binta kallon da tuhuma, sai kuma ta turo baki tana wani waskewa da kallom ummeetah dake hada uban zufa da fadin,,

  madam yunwa fa nake jie, ace comon indomie har yanxun baki gama dafawa ba, ran mainat ya baci, tana kuma gyara tsayuwa da fadin,,

  wait ummeetah dama ita ta saki wannan a'ikin?a sanyaye tace,,

  eh, nama kusa gamawa, zaro ido tayi da maida kallonta kan saudat, dake dafe da kitchen drower tana faman ciccika, da fadin,,

   ke ina masu a'ikin dake site dinku, don kinibibi saikin kwaso girki kin kawo nan a miki, don iskanci ba zaki iya dafawa da kanki bane, turo baki ta kuma yie da fadin,,

   toh gani nayi masu a'iki da yawa, no need in tsaya wahalar da kaina, finally tunda ubana na biyan su kudi bautarsu, a harzike take fadin,,

  idan ubanki ya biyasu kudin a'iki, kina sa mana gas a slinder ne, come on kwashe tsiyar kie ki bar kitchen din nan, ta soma dan daddaka legs dinta da fadin,,

  kai nifa aunty munat kin takura mun, kie.......,,

   shout up nonsense, nace ki kwashe kibar kitchen dinnan tom, ke kuma kashe mana gas din nan, kie wuce kije kie karisa a'ikin da kike yie, ba musu ummeetah tayi abin da aka sata, tana barin kitchen din, ta zabga ma kanwar harara da kwasan indomie tana zube mata a hannu, tana kuma fadin,,

  kun daiji kunya wlhy, ita rayuwa sauwa sauwa ake daukanta, kuma ya zama na karshe da zaki kara kwaso tsiyarki ki kawo nan site din, daga haka ta juya tabar kitchen din, kuka sosai ta saka tana runguman indomien da nufa site dinsu.

  nan da nan ummeetah ta kammala goge falon, ta share glasses din windows, tare da feshe turaren kamshi a ko ina, kamar yanda ta saba kullum, sannan ta nufi daki don tayi wanka.

    zaune suke a falon ita da maami, suna yer hira, ta gama fere mangos din tana yayyankawa da santi sai fadi take,,

   maami kinga lokacin bikin ummeetah indan mu kaje garinsu, nasan dole can zata koma ayi biki, amman a nan za tayi aure, maami tayi yer murmushi da fadin,,

  wato a nan kuke so tayi aure, tace,,

  eh maami, indan mu kaje bikin har mango day sai munyi, dariya maami keyi, tana mata tsiyar santi, tace,,

  maami a'i mangwaron ne akwai zaki sosai, irin na gidan gona nefa, maami tace,,

  hakane kam, har dama gwaiban ma duk masu kyau ne, irin na can, ta kuma yanko mango tana kaiwa bakinta, dai dai sanda mummy su ta shigo saudat da munirat biye a bayanta, da ker ta iyayin sallama ciki ciki, maami ce ta amsa mata, yayin da mainat ta hadiye mangon da ker, da tunanin abin daxai faru, maami da fara'anta take fadin,,

   a'ah, maman munirat kece da kanki,,
 
eh, ta fada fuska ba walwala, tare da ja ta tsaya bayan kujera, da daurawa da fadin,,

   ina wannan diyar matsiyanta take, gunta naxo, cikin dar dar mainat ke fadin,,

   wace mummy?maami dai sharewa tayi kaman bata san me take cewa ba, don ta lura da yanda ta shigo, ba azziki a ciki, kwata kwata bata iyawa da hayagagan kishiyar nata, ita mutum ce mare son tashin hankali, ta zunguro ma mainat ashar da fadin,,

   wannan kanwar uwar taki ita nake nufi, a'ikin gane yanxun ko ?ina take ta fada cikin tsawa, kafun ta dan juya tana kallon saudat dake site din hagunta da fadin,,

  ke meye ma sunanta?

   ummeetah, ta fada cikin sauri, tako shiga kwala mata kira, ummeetah dake daki tana kammala shiryawa gabanta yace rass, hibbat ma dake bacci da sauri ta farka, a tare suka futo falon, cikin dan takun kasaita take isowa inda ummeetah take da wani kallon tsana, kafun ta fara fadin,,

   ke saudat tayi kama da tsaranki, ko kuwa tayi miki kama da kalan yagaggun fulanin nan na cikin daji, uban waye ya baki daman da zaki fara taka rashin mutunci a cikin gidan nan, fada mun inji!ta karisa maganan cikin tsawa, wanda yasa ummeetah danja da baya, gabanta na cigaba da faduwa, kafun tace,,

   kiyi hakuri don Allah,,

   yimun shiru munafuka, shi kadai kuka sani, gulma da kinibi, wato kinci kin koshi kin ije body da kyau, hutu ya zauna, za'a fara tsula rashin mutunci, ke harki insa ta saki a'iki ki kiyi, ta nisa da nunata da dan yatsa tana fadin,,

  ya zama na farko ya zama na karshe, daga yau, daga yau, ba saudat ba, ko munirat ta sanyaki a'iki kika kiyi, to ranki zai mummunar baci, bauta shi kika zo yie, mu kuma mu biyaki kina jie, baki da wani suna daya wuce na yer a'iki, useless kawai, a'ikin jini da kyau, ta karisa maganan da kamo kunnin ummeetah ta wani murde, tuni idanunta suka kawo kwalla tana fadin,,

   eh naji, ta zabga mata harara da fadin,,

   shegu, da baku iya gadon azziki ba, da sauri mainat ta taso tana shiga tsakani da fadin,,

  mummy wannan bai dace ba, serious wannan ba laifin ummeetah bane, tayaya kaman saudat za tace sai an mata girki, intaje gidan mijinta wa zaixo ya mata, kuma fa wani a'ikin tak........,,

  tasss!shine abin da taji sama kuncinta, ta dafe kuncinta da sauri, tana kallon mahaifyar nata dake faman huci, da fadin,,

  uban wa kike fada ma wannan maganan, yer banxan yarinya, ka haifi da amman baka haifi halin saba, har kina da bakin da zaki shiga cikin wannan maganan, bayan akan yer a'iki mare usuli, kika doki yer uwanki ta jini, tuni idanun mainat ya cika da kwalla tana kallon saudat dake harare harare, da murgudan baki, da fadin,,

   nie saudat na dakeki, mummy yanxun akan saudat zaki mareni, gaskiya fa na fada, shin........, gwalon da saudat ta sakar mata ne, ya sata yin kan yarinyan a fusace, tako damkota, jie kake tass tass, da sauri mahaifyar ta nemi shiga tsakani, amma fadan ya kaure, saudat ma neman ramawa take tana faman zagin yer uwan, sai lokacin maami ta taso da sauri, tsawa daya tayi ma mainat ta saki saudat tana huci ranta yayi matukar baci, yayin da mummyn ke neman kara yo kan mainat din da wani cin mutuncin, maami ce tayi saurin shiga tsakani tana fadin,,

  ko daya, be dace kiyi haka ba, yagana ba'a goyan bayan karami a gaban babbansa, kamata yayi keda mainat kie mata fada akan koma menene tayi, ta kalli mainat dake zubar kwalla tana fadin,,

   ba mahaifyarki hakuri,,

  kiyi hakuri mummy, maami ta kalli saudat da fadin,,

  kema ba yer uwanki hakuri, matsayin tana gaba dake, tana kukkumbura tace,,

    sorry, wucewa dakinta kawai mainat tayi tana shashekar kuka, alama abin yayi mata zafi, itama mahaifyar fuwww ta wuce da yeyenta, maami ta girgixa kai tana bin bayar saudat don ta rarrasheta, ummeetah ko kuka mare sauti ta saka, inama ita aka mara ba auntyn suba,,

  hibbat ta jata daki tana bata hakuri, ummeetah sai kuka take, ba tasan me yasa ba kalman mare usuli keta mata yawo akai yau, duk da ba yaune rana ta farko da aka fara fada mata haka ba, ranan dai haka kowa ya wuni sukuku, musamman mainat da tunda ta shiga daki bata futo ba,,

  har dakin ummeetah ta bita ta bata hakuri, da fara'anta take nuna, kar ummeetah ta damu, ya wuce be dameta ba, ummeetah dai futowa kawai tayi amman tasan ta fada ne, don har fuskanta yayi jaxur don kuka, da yike itama fara ce, maami ma rai bace ta wuni ranan, tana tunanin mafita, kwata kwata bata son tashin hankali.

  ita kuwa mummy cin alwashi tayi, koda musgunawa irin wannan sai ummeetah ta gaji tabar gidan, an fara kenan.

 
                        ***

    Yau tun sanda ta kammala a'ikin safenta, ta fara futa da kayan wanke wanke, ta kammala futa da komai, tare da hadawa da wasu kaya dake saman cabinet, ba a fiye amfani dasu ba, lokaci lokaci takan kwashe in taga sunyi kura ta wanke, sannan ta kara maidasu inda suke,,

  yauma hakan tayi, sanda maami ta shigo ma taga tana kwasan kayan, cewa tayi data barshi ma, zuwa wani lokaci, itace dai take son tayi tana fadin,,

  maami gwara a wanke kawai yanxun, in ba haka ba, wasu kuran zasu kuma yie, murmushi kawai tayi ta futa da fadin,,

  ummeetah sarkin a'iki, haka dai ta kammala futa da kayan tass, can wajen fanfo inda suke wanke wanke takai kayan, ta ware wadanda suka baci na abinci daban, donsu bintu take jira ta kwaso na sashin su munirat sai su wanke tare, tunda kullum haka sukeyi, sannan ta ware masu kuran waje daya,,

  dan tsaki ta saki tana kallon sashin su munirat din, da mamakin abin daya hanata kwaso nasu kayan tun dazu, ta koma cikin gida ta dakko babban tabarma, tare da shimfidawa, ta hada ruwan kumfanta tare da sauran kayan ruwan dauraya, ta soma wanke kayan masu kura, tana kikkifesu bisa tabarman, har dasu plate hanger duk ta wanke,,

   bata wani jimaba ta kammala wanke wadannan, tana kuma kallon sashin su munirat da dan tsaki, har yanxun bintun bata zoba, bare su fara wadanda suka baci da abinci, ninyar fara wanke wadannan takeyi, munirat ta futo daga sashen su, tana tafe tana tumbatsa kamar yanda aka sabar musu, a yastine ta kalleta kafun ta sanar mata cewa, ance taje ta kwashe kayan wanke wanken site dinsu, don yau bintu bata zoba, daga haka tayi juyawanta ta koma,,

   tsam ta mike tsaye, sanye da yer black hijjab dinta iya gwiwa, da take sanyawa indai zata futo waje, ko da taje mummynsu na kitchen din ana harhada mata kaya harda na saman cabinet suma, ita dai taga munirat ta rada ma mummyn magana a kunni, sai gani tayi ana sauko da kaya, suma taje ta wanke sunyi kura, ranta bai soba, don yaukam sauri take ta kammala a'ikinta, ta rage ma bahba balarabu wasu a'ikin, don taje kasuwa, sannan ta tsefe kai ta tafi kitso, ga kuma isslamiyya da zata,,

   hakanan ta kwaso kayan zuwa site dinsu, suma wani tabarman daban ta shifida, zata fara wankewa, gaba daya taji tana jin wani irin zufa, ta koma cikin kitchen din ta cire hijjabin ta ije waje daya, tare da futowa kanta tsaye ta nufi wajen famfon ta fara a'ikinta,,

   sama sama ta fara jin kamashin turaren da taji kaman ta sani, ta tsaya cak da wanke plate din hannunta, tana shakan iska tare da hadawa da runtse idanunta, da sauri kuma ta bude idon tana jan ajiyar zuciya, tunawa da tayi kamshin turaren Baffah sadeeq ne, takai dubanta gefen hagunta wayam, ta gefen dama ta juyo da kanta,,

  can wajen wani dakin kajie dake ta bayan, ta hangesa tsaye, cikin wata light green din shadda, kanshi ba hula, sai kafansa dake sanye da takalma sau ciki masu tsadan, tana iya kallon fuskanshi ta gefe, indanunsa na cikin dakin kajin da yake kallonsu ta cikin net,,

  tsam ta mike, tana kallon jikinta a hankali, wata shegiyar vest ce data futo da dukan shape din dake jikinta, ta matseta sosai, sai zani data daura bisa kunguru, shi yasa take saka hijjabi in zata futo, gashi ya hanata sanya kaya matsatsu, a hankali take takawa baya baya, ta nufi wajen kofan kitchen din, tana zuwa dai dai nan, tayi sauri juyawa tana shigewa ciki, harda sauke ajiyar zuciyarta tana fadin,,

   Allah nagode ma, bema ganni ba,,

   tswssssss, shine abin daya fiddar daga bakinsa, yana binta da harara, bayan shigewarta, da ayyana,,

   ita kwata kwata bata san ta girma bane, don iskanci zata rika zama da irin wadannan kayan, kwafa yayie, da komawa yana cigaba da kallon kajin, layers ne masu kwai,

Please Login or Register in order to submit comment