Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta zuba mishi su da alamar tambaya, kai tsaye yake fadin,,

mata da kishi, harta kira ta fada miki, zaro ido waje tayi da fadin,,

of course dear, kasan kuwa mai kalmar kishiya yake nufi, hmmm sadeeq ba zaka fahimta ba, amma duk randa wata mace tayi gigin kusantowa inda kake, nan ne zaka fahimce a'inihin me ake kira da kishiya, da dan yatsa take nuna ummeetah da fadin,,

ke kuma, for the last time, ina miki kashedi, daki cire hankalin kie akan mijinta, nasan halin gulma irin naku, in kin soma wani kalan mafarki toki farka tun wuri, saboda shi ba dai dai class dinki bane, ke infact duk arean nan babu kalan mijin da kika dace dashi, ta karisa maganar cikin tsawa tana runtse idanunta, kafun ta bude tana cigaba da fadin,,

kalan mijinki yana can kyauyan ku, rorarru kawai, wanda basusan hallaci ba, taja wani tsaki, sai da takai ayah sannan ta tuna ma mijinta na wajen, yanxun yana sa baki sai lamarin yafi haka, dan war tayi kafun tasa kai tana barin wajen, jikinta har rawa yake don masifa, ya bita da ido harta fuce,,

daskarewa tayi a wajen kawai, babu abin dake zuba a idanunta sai hawaye, ya sauke wani irin ajiyar zuciya yana binta da kallon tausayi, hannunta yayi kokarin kamowa, tayi saurin matsawa tana runtse idanu, kafun ta watsar da dukkan kayan dake hannunta, ta juya zuwa dakinta,,

ya mike da hanzari, tuni ta banko kofa tana sanya key, sannan ta saka wani kuka mai cin zuciya ta zame a wajan, tsaye yayi wajen yana runtse ido shima, kanshi ke wani mugun sara mai, sosai kukanta ke taba zuciyarsa, yafi karfin 10minutes a wajen tsaye shiru, kafun ya wuce bedroom dinsu, itama ummeetah kuka takeyi son ranta, kafun ta share hawayenta da daukan dangana, tana daukan alkwarin ko gaisar da uncle khamis din daga yau ta gama.

daki ya koma ya zauna bakin gado, kamar ya saka ihu, lamarin suhymah ya soma damunshi, kishinta yayi yawa, ta ina ma zai fara yinma marainiyar yarinyan nan adalci, no is enough, in ba zaka iya ba ka hakura wani ya dauka, kodan tayi rayuwan farin ciki, toh amma kaifa?shine tambayar da yayi ma kanshi,,

tsw......, ya so jan tsaki, cak ya tsaya sakamakon kalmar,,

innalilahi wa'inna ilaihir raji'un, daya zo bakinshi, hakane ummeetahce kwanaki ta tunatar dashi ba kyau yawan tsaki, ya rika maimaita kalmar da karanto duk addu'ar da yazo bakinshi.

haka ta futo ta cigaba da a'ikace a'ikacenta, shima wunin ranar yana gida, duk sai yaji ya damu da yanda ya ganta, idanu kawai yake binta dashi tana a'ikinta.


***

Daren ranan matarshi ce kwance bisa gadon nasu tana faman shirga bacci, yayin dashi yake kwance kawai ya kasa rintsawa, yana facing sama, da damuwa dauke a fuskanshi, tunanun nuka da komai sunmai caa a kwakwalwa, ya rasa mafita,,

na farko, yasan yana son matsrsa suhymah, kuma tana da kishi da har mamaki yakeyi, tun yana tsoron bakin kishin nata, harya fara bashi takaici, toh ta inama zai sanar mata ummeetah matar sace kuma kishiyarta, nisawa yayi da dan muskutawa yana raya,,

kai inaaa, baxai yuyuba, tama ina zai fara gaba daya, har ita yer ficikan yarinyan can, shie uncle dinta mijinta, kai da kamar wuya ta yarda, wani sashin na zuciyarsa na raya masa,,

toh kenan haka zatai ta zama matsayin mai a'iki, ana kuntata ma rayuwanta, inhar ba xaka iyaba why not ka sawwake mata, kamar yanda ka tsara, inma khamis dinne a'i ba wani mugun haline dashi ba, itama yarinyan kaga yayi dacen matar aure, kai tsaye wani sashin na zuciyarsa ke raya masa,,

ouk kai ka yarda kenan, ka rasa matar mutunci, karfa ka manta hadith din dake magana cewa, _duniya wajan jin dadi ne, amman mafi jin dadinshi, itace mace ta gari,,_

tsakanin suhymah da ummeetah wacece mace ta gari, ya kamata ka zaba, idan har kana da tunani, toh akwai wacce ya kamata ka furta sunanta, shin suhymah ko Umeetah, zumbur ya mike zaune da wani zufa dake tsatstsafo mishi, ya daga kanshi sama da fara jero wasu tunanin.

Matar data iya rikon addini, tsoron Allah, kyawawan dabi'u, zaman lafia, tausasan kalamai, tsaftar gida, tarbiyan yara, iya kula da miji, matar da zaka tankwara ta, bawai ita ta tankwara kaba,,

kai sadeeq, shin wai ina hankalinka yake, ka zabi ka zauna cikin kunci, wannan cutar da kaine, babu kyakyawan kulawa daga matar da kake so, shin so kawai iya a baki zai baka jin dadin nan na duniya, har abadan rayuwan kama,,

no, ya kamata ka ganshi a a'ikace, ka kuma sauya tunani, babu haram a cikin auran ku, don haka zaifi maka kasan abin yie, da sauri ya bude idanunsa, duk yayi zufa yana furta kalman,,

*ummeetah*, hakane itace, toh amman suhymah fa, akwai matsala fa in tasan.........,,

dallah shareta, wani tunanin ya katseshi, yana cigaba da raya,,

kanta aka fara kishiya, kamata yayi ka fara tunanin ta inda zaka sanar da wacan ita matar kace ba wannan ba, tunkan soyayyan wani ya shiga zuciyarta, dada kishingida bayansa yayi da jikin pillow, yana dan kada kanshi almar gamsuwa da hakan,

sai dai yana tausayinta yanxun daya kasance tana da ciki, tabbas yana tsoron wani abu ya samu cikin nan, sosai yake matukar son abin sake cikinta, yana son ye'ye a rayuwanshi, sai dai yasan halin suhymah, jubi yanda take shiga ma wasu fada akan kishiya, ya tuno kalmanta na zuciyarta zata buga ta mutu, da sauran su dai, dan tsaki yayi sanda ya dago daga kishingidan, yana dafe bakinsa da yen yatsunsa, da zuba ma waje daya ido yake nemo mafita,,

hakane, hakuri kawai zan cigaba dayi, har lokacin da Allah zai sauketa lafia, daga nan sai in fada mata duk yanda lamarin yake, komai ta fanjama fanjamjam, kai dai yanxun kasan hanyar da zaka sanar ma wacan kai mijinta ne, don ta zauna da shirin zaman auranka, da wannan mafitar ya dan samu natsuwa, yana komawa ya kwanta, tunani kawai yake ta inda zaibi ya sanar ma ummeetah shi mijinta ne, har wani bacci barowa ya kamashi.



Nata bangaren kuwa tun 2am, yau ta tashi ta dauro alola, tare da jera sallolin nafila, ta idda kuma ta zauna tasbihi, kwata kwata bata jin bacci, tana ta gaya ma Allah damuwanta, wajenshi take neman mafita, tasan duk runtsi a rayuwa, wata rana mahakurci mawadaci ne.



comment
share
vote

*matatace 2019*
Na meemartjj

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
[14/08, 14:29] Dala Grp: 🕯🕯🕯
*MATATACE*
🕯🕯🕯


story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjj

*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty Ummeetah any my Fa'ixation._


page 37~38

_________Firgigit ta farka daga baccin da takeyi, tare da zaburowa zaune, zufa takeyi ta ko ina, sakamakon mummunar mafarkin da tayi akan danta, taja dogon numfashi da dafe kirjinta dake bugawa kaman zai futo, a hankali take furta kalman sunan,,

Irfan, ta dan damu, tana jie kaman taje ta dubo shi, ninyar tashi take tsaye, sai kuma ta fasa tana komawa ta zauna, da dafe karamin cikin dake jikinta, ta sauke dogon ajiyar zuciya, tana sakin murmushin sosai, kunna fitilan dake gefen gado tayi, da juyawa ta kalli site din da yake kwance yana bacci, ta isa kusa dashi a hankali tana kwanciya, da ruko hannunsa, sosai ta zuba ma fuskarshi ido tana murmushi,,

komai ina yine saboda kai baby nah, i luv yhu so much dear, ta fada da kissing dinshi gefen kumatu, kafun wani bacci barawo ya saceta.

sanye da rigan bacci mai karamin hannu ta futo, wanda ya saukan mata har kasa, sai wata yer turban data rufe kanta dashi, sauri take ta nufi kitchen, sai dai tana futowa daga dakinta, shima yana futowa daga nasu, sai da kirjinsa ya wuni buga, da sauri tayi baya baya tana komawa daki,,

runtse idanunsa yayi da dan cice baki, kafun ya budesu tass a kanta data futo sanye da hijjabi ta nufa kitchen, sosai ya bita da kallo, tana burgeshi sosai a duk lokacin da irin haka ta faru, komai na jikinta saiya motsa, yayi dan murmushi daya tuno farkon haduwarsu sanda ya koma gida,,

Umeetah, ya fada yana nufa inda take, cak ta tsaya sai dai ta kasa juyowa, har gabanta yaxo, kallo daya taimai ta kauda idanunta da fadin,

ina kwana Baffah, sai daya gama karantar fuskanta na wasu yen sakwanni, kafun yace,,

lfylau, kin gama fushin?shiru tayi, yana cigaba da fadin,,

meya sa kikai kuka jiya?kyalla mishi idanuwa tayi da alamar tambaya, yace,,

yadai, tambayarki nake baby mai hakuri, jarumar fulani, murmushi ta samu kanta da saki, yaji dadi sosai daya ga hakan kan fuskanta, cikin wani sanyin murya yake fadin,,

meya faru, kie fada mun inji mana,,

bakomai, kawai dai naji kewer Affah nane, ta fadar maganar da idonta da suka cicciko, yayi dan shiru, jikinshi yayi sanyi, direct yake fadin,,

dama akwai wata magana da nake so munyi, tana da muhimmaci sosai, yanxun............,

girki............, ta katseshi tana zaro idanu waje, kafun yayi wata magana ta wuce da sauri tana fadin,,

girki na daura, zan duba karya kone, bat ta bace a wajan, da dan mamaki yake binta da ido, kaman zai bita ciki sai ya fasa, maganar na bukutan natsuwa sosai, ranshi a jagule ya wuce ya futa, shiya rasa gane kan yarinyan nan.


£££

............Tun sanda mahaifyarta ta zuge Abbansu yace bata da wani miji daya wuce Alh. Ribado, wanda ya kasance tsoho ne, kuma da mata uku, hankalinta yayi dubu ya tashi kullum cikin rusa kuka take, maami ke lallashinta tare da taimakonta da addu'a, itama a nata bangaren tana yie, duk ta yamutse, tana mamakin hali irin na mahaifyarta, shima nashi bangaren ya shiga tashin hankali, don harya yima mahaifinsa magana, ana shirin turawa.

zaune suke a fallon mijin nasu, bayan sallah shan ruwa, tana yayyanka mai fruit ta dayan site din, da take zaune, yayin da maami ke zuba suga a furan data kammala dama mai, shikam yana daga tsakiya, sanye da farar kal jallabiya, sai wata yer tabarau dake idanusa na kallon labaru, yana kallon labarun da ake watsowa a tv, maami ce ta fara magana da fadin,,

Allah ya taimakeki ran mai gida, dan murmushi yayi da fadin,,

Haj. Indo kinsan watan ramadan ne, kina samun lada da yawa fa, bacin haka a'ike ganinki sai an cika form, uwar gida ran gida, yagana dake gefe ta hada rai, maami kuwa murmushi tayi da fadin,,

haba wane nie Abban kamalu, a'i in kowa zaya cika form, banda kai mai gida ran gida, gefe kuma ga kanwata dake morar kuruciyarta yanxun, kaga bana shiga hakkinta da yawa ba, yana yer dariya da kallon yagana, kafun ya maida kan uwar gida yana fadin,,

ohh lallai wato ku yanxun kun zama manya kenan, ta dan tabe baki da murmushi take fadin,,

a'imu yanxun mun girma, Abban kamalu an dade tare, wanda kuma suka xo daga baya kaga sai mu barsu suci nasu raguwan moriyar, kuma ina jin dadin yanda aka maida mun kai basaraken sak, har naji inajin maka kirari mai gida na,,

sosai take zuba mishi kirari, cikin raha, shikam sai yer dariya farin ciki yakeyi, so serious ya kalleta yana fadin,,

kai amman dai yau sai naji kamar na baki kyautar mota uwar gida sarautar mata, cikin zakin muryan nan nata da yeyenta sukai gado take fadin,,

haba haba, Abban kamalu babu soyayyan nan, babu ita yanxun, in dane cewa kawai za kayi ga makulli gida da mota ma, dariya sosai yakeyi, duk haushi ya kama yagana, tana faman harare harare,,

lallai ne, wato ta lura haj. Indo nada rainin hankali, ta rika abu kamar bata san meke faruwa ba, lokaci daya kuma ta zauna ta gasa maka mai zafi, tama kasa cewa komai, don gani tayi kaman sun manta da itane, ya sassauta dariyansa yana fadin,,

haj. Indo ta Alh. Ameenu, toh yanxun fadamun ke me kike so, tana yer dariya na barkwanci take fadin,,

nie ban dakko da zafi ba, akwai abin da nake so sama da warware batun auran diya tah, cikin raha yace,,

ina sauraran kie, nan suka zauna suna tattaunawa, a karshe yace dole zaiyi tunani akai, suma su Alh. bature da yace su turo, su dakata da zuwa, wannan ba karamin tada hankali mummy yayi ba, cikin zafin murya take fadin,,

gaskiya baxai yuyuba, nikam ban yarda ba, bafa zai yuyu ayi auran cin amana da yeta fa, mijin matar abokin yarta nefa da suke mutunci, niko sam baxai yuyu ba, shiru mijin yayi mata, sai maami ke fadin,,

Allah sarki, yagana kie gane mana, shifa irin wannan auran ba yau aka fara ba, koda kuwa nacin amanan ne, ka yarda da mutum yayi maka butulci, kuma bawa bashi da yanda zaiyi, tunda shi aure nufin Allah ne, cikin wani huci take fadin,,

hmmm, haj.Indo kenan kie daina wani lauye lauye, kie futo fili ki fada mun abin dake ranki, a'ishi aure nufin Allah ne kamar yanda kika ce, amman nawa labarin auren yasha baban dana munat, kuma dole wanda nake so shi zata aura, murmushi yayi da fadin,,

a'ah dakata tukuna, daina shiga hurumin daba naki ba, sannan don Allah abarni da zancan haka, maami ta mike da fadin,,

toh ranka shi dade a tashi lafia, nie sai da safe ku, Allah ya huci zuciyarki, yace,,

Allah ya tashemu lafia, daga haka ta fice abinta, itakam sai kumbure kumbure takeyi, yace,,

dan miko mun fruit salad din nan, a zuciye take fadin,,

kaje uwar gida sarautar mata ta baka, murmushi kawai yayi, ya jawo furan data dama yana sha, da zuzuta yanda furan taji suga, duk haushi ya kuma kamata, fuwww kuma ta mike ta fice,,

kishi kumallon mata, ya fada da dan dariya, shi yasa harga Allah yake daraja uwar gidansa, don yasan bata irin wadannan haukan.

sosai munat taji dadin zancan da maami taxo mata dashi, sai dai kuma data tuna da sihirce sihirce irin na mummynsu, musamman da maami tace mata, ita bata saukko ba kan batun auran, rasa mafita tayi, amman data tuna wani abu, farin cikine ya kamata tana latso numbern masoyin nata.


***

.........Haka kwanakin sallah ke ta matsowa, lokacin da ko wani fanni ake gabatar da shirye shirye, tass aka repenting gidansu, da zuba wasu sabbin kayan ciki, yeyen banki dai sun jie jikinsu, sai faman mita take me yasa zaya sanya sabbin furnitures har dakin ummeetah, shidai yasan yanda yayi ya lallabata, aka bar maganan,,

bangaren ummeetah kuwa a'ikene sukai mata yawa, shi yaxo da kayayyaki na girke girke, yana son classy special dishes, baki za suyi, abin dabe taba a shekaru uku da suka zauna, duk salla celebretion baki suna son kawo musu ziyara, amman sai yayi ta kakkaucewa.

wannan karo kam, Alhamdulillah, safiyar ranan salla, ita ta shirya Irfan cikin dinkin dakakkiyar shadda brown colour, wanda yaji a'iki na alfarma komai dan dai dai, hannun nan yaji links, ga hular sakin nan mai tsada, ta zira mishi yen sadals shoe dinshi masu kyau da tsada,,

sosai yayi mata kyau, sai faman yaba yanda yayi kyau take, tana fesheshi da turare mai dadin kamshi, shiko tsalle yake da murna yana faman yashe baki, yana tsaye yana kallonsu, Irfan ne ya fara ganinshi yasa ihu da fadin,,

daddy happy sallah, tsam ta waigo, yana murmushi yace,,

same to yhu dear, da sauri ta kauda idanunta, yayi matukar kyau, komai nasu iri daya dana danshi ne, a zuciya take raya,,

masha Allah, amman saita basar tana kammala shirya Irfan, tare suka futo falon rike da key din mota, tana tunanin masallaci zasu je, don harda DR. khamis dake jiranshi a waje, yana ta faman cuku cukun ciro waya a aljihu, ta kasa daurewa tana kuma kallon Irfan kafun tace,,

kai gaskiya kunyi kyau, Allah ya maimaita mana, da sauri ya dago kai yana daga mata gira sama da fadin,,

da gaske harda nie, kai ta daga sama tana fadin,,

ehmana, yayi dan dariya da fadin,,

banyi tunani ba, kasancewan kallon yatsinan da naga ana mun, amman duk da haka nagode, murmushi kawai tayi a zuciya tana raya,,

nikam bansan wannan kallon yatsinan da nake ba, ta daga ma Irfan hannu suka wuce, ita kuma ta shige dakinta, yayin da matar gidan kecan tana faman shirga barcinta.


sanda suka dawo, harta kammala gyaran gidan, ta jera abinci da komai da komai, Irfan ta zuba ma naman data soya, tare da hadaddiyar dabun kajin cikin plate da lemon juice a cup, ya futa kenan ya shigo shima, tsayawa kawai yayi yana kallonta, har lokacin kayan bacci ne a jikinta, tana ta wanke wasu plate cikin dish washer,,

sannu da zuwa Baffah, ta fada sanda ta juyo ta lura daya shigo, ya wuce kai tsaye yana bude tukwanen girkin da amsawa da fadin,,

yawwa, sannunki da a'iki, ina nawa abin dadin, ya karisa maganan yana kallonta, dariya yaso bata, kaman wani yaro, ta nufi standard table din dake tsakiyar kitchen din, da dauko wani plate mai dan fadi data rufeshi da dan uwanshi, sai lemon juice din dake sama, shima rufe da wani yer cover, ya kariso da dan murmushin yana fadin,,

duka wannan nawa ne,,

eh, ta fada, ya amsa da murmushin yana fadin,,

Allah miki albarka, nasha yaron kie kadai kika sani, sink ta nufa da cigaba wanke wanke tana fadin,,

k'ani nah dai, da sauri ya juyo yana kallonta, ya d'aure fuska yana fadin,,

nie kuma nace d'an kine, murmushi takeyi daga juya mai bayan da tayi, da yashe yen hakoranta, dama da biyu ta fada, shikam yafi 2minute, yana kallonta da wani tunanin, kafun ya nisa yana barin kitchen din.

sosai ya tara baki, wanda yawancin su turawa ne, harda DR. khamis, daga daki da tayi wanka tana shiryawa, tana jin muryansu da shagalin da akeyi, harda su madam suhymah data makale kusa da miji kaman wata magnet, shida jefi jeki kike jiyo muryansa ana hira tare da raha, ranar haka suka wuni amsar baki, har dare kafun kafa ya dauke.

yen kwanaki haka dai suka rika amsan baki, ummeetah na kallon jama'a iri iri ana kawo musu sallah gifts, kafun a samu gidan ya dan natsa.


***

Yau da wani irin ciwon kai ta tashi, ga ciwon mara da takeji yana taso mata, kai harda su mura, haka dai ta cigaba da ayyukanta, ta kammala shirya Irfan ya tafi school, dama matar gidan tun safe ta fice,,

shima dake bedroom ya kammala shiryawa kamar yanda ya saba, dauke da briefcase dinshi ya futo sai ratsatsiyar I-pad din dake hannunsa, da screen dinta yayi ratsa ratsa, harya futo falon, sai kuma yayi dan tsaki yana karisawa dinning arean,,

kayan dake hannunsa ya ije bisa dinning table din yana juyawa cikin bedroom din, dai dai sanda ummeetah ta futo kitchen, da kallo ta bisa, tasan fushinsa be wuce kilan wanda matarsa ta shayar dashiba jiya, kan yayi bakuwar da take a bokiyar a'ikinshi,,

maybe ko tasan wani labari ne kan kyakyawar black american lady din, shine makwabciyarta ta rada mata gulma a waya, musamman ta dawo, da masifa suka kare yana hanata tana yie, sanda dukkanninsu suke nuna zallan kishinsu, ummeetah dai na daga daki tana kallon komai, in ranshi yayi dubu ya baci, kwana tayi masifa, safe nayi kuma ta fice, ta sauke ajiyar zuciya tana raya,,

Allah shi kyauta, yasa ta gane, daukan cup taxo yie, kan dinning din, bisa kaddara hannunta ya bugi I~pad dinshi dabe zauna da kyau ba, jie kake a kasa fass, ummeetah ta zaro ido yayin da kirjinta ya shiga dukan uku uku,,

dai dai sanda ya futo dakin, da sauri ta duka ta dauko I-pad din, kuma rudewa tayi, don yau fuskanshi babu alamar wasa, da wani tuhuma yake kallon hannuta, can kuma yayi dan kwafa yana karisowa inda take da amshe wayar, ya dauki briefcase dinshi,,

Baffah kayi hakuri don Allah, ta fada da sauri, yana wani cin magani, da soma barin dinning area din yake fadin,,

nace kin mun laifi ne?a dadare tace,,

a'a, kawai dai duk d'a na gari baxai so ya bata ma iyayanshi rai ba, cak ya tsaya bai juyowa ba yake fadin,,

wa yace miki nie baban kine, toh tun wuri ina baki shawarar kie goge wannan matsayin, tayi kwal kwal da fadin,,

amman naga bani da kowa sai kai, kai tsaye ya juyo da fadin,,

a'i nima bance, ke ba tawa bace, sai daya fada maganar kuma yayi dan shiru, itama shirun tayi, ya kuma bata rai yana dan tsaki da fadin,,

akwai maganar da nake so muyi inna dawo, kie sani kuma yana da muhimmaci, in sha Allah dana dawo zamu tattauna, ko takan breakfast bai tsaya ba, ya juya ya futa da damuwa kala kala.

hannu ta saka a kai, kawai saita saki kuka, kafun ta shiga yarfa hannu da fadin,,

na bani na lalace, nie A'isha na kara mishi wani damuwan, nayi mishi asarar dukiyarsa, me yasa ban lura bane, bisa kujeran dinning din ta zauna tare da kifa kanta jikin table din,,

kuka takeyi sosai, can kasan zuciyarta kuma tana tsoron abin da zasu tattauna, sai da tayi me isarta, sannan ta mike ta karisa a'ikinta, da ker ta koma daki, wanka tayo ta saka wata yer riga tare da komawa tabi lafiyar gado,,

zazzabi ne mai zafi ya rufeta, gaba daya sai taji maraicinta ya dawo sabo, tana kewar daginta da mahaifinta, tasa wani kukan, sanda ta tuna ko mahaifyarta bata sani ba, duk wani kunci ya taru ya mata yawa.

A wannan halin Irfan ya dawo school, daker ta iya sanja mishi kaya daga inda take zaune, yana faman jera mata sannu, kafun tace yaje dinning yayi lunch dinsa, ta koma ta kwanta tana faman juye juye.

Da wuri yau ya dawo office din, duk ya gaji, ya nufi cikin gidan sanda ya hangi Irfan nacan na wasanshi, da sallama ya kutsa kai ciki, sai dai yau shiru kakeji sabanin da, da zata amsa sallamar sannan ta futo yin mishi sannu da zuwa,,

harya kai bakin kofan bedroom dinsu, jira kawai yake yaji muryanta tana mishi sannu da xuwa, tunaninshi maybe tana wani abinne, amman shiru, don haka yana dire jakar hannunsa bisa gado, zuciyarsa kawai ke azazzalar son ganinta, straightforward ya wuce bedroom din nata, yana dan tura kofan da furta kalmar sallama,,

can ya hangeta kwace ta kifa cikinta, kanta bisa pillow, yayin da halve din jikinta ke rufe cikin duvet, a hankali yake karisawa inda take, yana kuma jiyo shashshekan kukanta, har inda fuskanta ke facing ya karisa idanunta a rufe, hannunsa yakai samam neck dinta, wani huci yayi mishi sallama, dai dai sanda ta bude idanunta yana fadin,,

ya salam, meke damunki?a rude ta soma kokarin tashi, don bata san ya shigo ba sai yanxun, shima da sauri yakai hannunsa kafadunta yana taimakonta ta zauna da kyau, shima zaman yayi yana kuma kai hannunsa saman wuyanta da fadin,,

ke dama baki da lapia ne, baki magana ba?shashshekar kuka ta cigaba da yie, ta kasa kallon cikin idonsa, ranshi ya soma baci, jie yake ciwon kamar a jikinsa yake,,

ina magana kina jina, donme zaki zauna da ciwo haka, ya fadi maganar da dan tsawa, maimakon tayi magana, sai ta kara fashewa da kuka, ya kuma rudewa sassauta murya yayi da fadin,,

Humaira plss calm down, kie natsu ki fada mun damuwarki, shiru tayi mai, yana cigaba da fadin,,

suhymah ce ta miki wani abin?, kai ta kada alamar a'ah, ya gyara zama da kyau da fadin,,

toh koni ne na miki laifin?nanma kai ta kada mishi a'ah, ya numfasa da fadin,,

ouk Irfan ne?, sai lokacin tace,,

ba ruwan Irfan, nice, ta fada maganar da sigar kuka, da mamaki yace,,

ke kuma?kai ta daga sama da fadin,,

nice na maka laifi, Baffah don Allah kayi hakuri, bada ninya na fasa maka I~pad ba, kanshi ya dafe da takaici, shi sai yanxun ma ya tuna anyi abin don harya manta, ya dago idanun da suka kankance don bacin rai yana fadin,,

oh my god, ummeetah what have yhu done to ur self, ya zaki dauki lafin da bekai ya dawo ba, harya shafi lafiyanki, kina hauka n........., sai kuma yayi shiru ganin tana kuma barkewa da wani kukan da fadin,,

don Allah ka yafe mun, nasan bai dace bane, in maka asarar abu, i should have watch up clearly, kai ya jinjina don kalamanta gaskiya ta fada, hannunta ya ruko da shima yayi zafi radau cikin sanyin murya yake fadin,,

wannan ya wuce, ummeetah yau koda kece kika fasa, kaddara ce kuma dole inyi hakuri, tunda ko a hannuna zai iya fashewan, barema bake kika fasa ba, plss kibar wannan kukan, ya dan nisa kafun yace,,

jiya da dare auntyn kie ta fasa shi, itama mistakely ne, na fada miki gaskiya ne, don kie daina sa ma kanki laifin da bake kika yiba, kukanta ta tsagaita dashi tana sauke wani ajiyar zuciya, ta danji sanyi sanyi daya kasance ba itace tayi barnan ba, so cool kuma take kuma

Please Login or Register in order to submit comment