Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

son kiyaye abin daxai bata mata rai, shi yasa zaiyi wuya kiga tana rigima dasu munirat, wani lokacin tana da fara'a, wani lokacin kuma tayi dif, kaman mai tarin damuwa, sanda take kallon mate din nata suna fama da rawan kai su sun zama enmmata, ba kaman munirat tarin samari kala kala, itama muhibbat bata da wani a'iki sai hira da samari a waya, ita dai babu ruwanta, don cewarta bata da lokacin wannan shirman, lokacin da ita kuma auntyn nasu mainat, ta dora karatun degree dinta a ABUzaria, sai dai weekend intaxo hutu, wannan kennan.

                           ***
     Manya kuwa kaurin wasa suna America, sanda suka sauko a birnin worshin town, murna wajan suhymah ba a tonawa, kaman taxo kasan kanin babanta, area ne, mai kyau suke zaune a ciki, cikin kyararran madaidacin plat din, kusa dasu neighbours dinsu, akwai mutum biyu en kasan su naija, Dr.ango da matarsa, mrs ango, wadanda suka kasance musulmai, tribe din yoruba, mace mai kirki, sai mr. vicent wanda ya kasance, journalist, shima da matarsa, suhymah aka barbace, ana jin dadi zaman kasan, bata nan bata can yawan bude ido,,,

   rana ta farko dazai fara futa office, sai daya kusa amai, wani irin coffee ne ta hada, sai kwan data soyashi salam, ya tabe baki, zaune kan madaidacin dinning din, yana fadin,,,

  what, suhymah meye wannan, ta make kafada da fadin,,,

   food, breakfast ne, ya dan rutse ido yana fadin,,,

   babu fa komai a ciki, tai far da ido tana fadin,,,

   of course, yafi kara lfy, kacie za kaji dadinsa, ya bata rai yana zuba mata ido, kawai saita tuntsire da dariya tana fadin,,,

  bakai kaki mu taho da wacce zata rika mana girkin ba, kaima ka dandana, shiru kawai yayi yana kallonta da mamaki, tare da tuno baiwar Allah ummeetah, kullum da kalan abin da za'ah ije na breakfast, ya numfasa yana mikewa da daukan briefcase dinsa, da raya,,,

  lallai yarinyan tana kokari, daga haka ya fuce daga gidan, tun daga ranan fridge dinsu cike yake da kayan zaki, basu hotel basu super market, don haka dan tinbin nan daya fara ajewa a gida, tuni ya baje, itama yanxun ba zama, kasancewan ta fara karatunta, sannan mr. vicent ya sama mata a'iki a nan wajan a'ikinsu, nan kuwa rashin zama ya dadu, sai can dare take dawowa, wannan ya shiga cikin sahun abin dake damunsa, don kullum duk ayyukan da yakan yie a office, saiya rigata dawowa, in yayi magana tace, ga karatu ga a'iki, dama yaronta tuni aka dauko mishi nani na musamman dake kula dashi, don haka ko shi bata da lokacinsa, suka cigaba da lallaba rayuwa a haka. 



                         ***
   Hankalin ummeetah bai kuma tashi ba, sai lokacin da muheet ya dawo kasan, ranar dai sashin aunty yagana, taga babu masaka tsinke, a sauke wancan a daura wannan, a bakin bintu take jin labarin dawowan nashi, ita bata ma sanshi ba, sai da muhibbat tayi mata bayani,,,

  ya diro kasan daga kasan china, inda aka samu ya hada degree daker, driver yaje suka kwasoshi, banda rawan kai babu abin da yakeyi, sanda mahaifiyar tasa, take jin kaman ta maida dan nata ciki,

  da yamma ummeetah ta dawo islamiya, sanye da hijjab dinta coffee har kasa, mai dauke da baj da kuma i.d card na makaranta, driver ya kwalla mata kira da yake can packing space, ta karisa wajan cikin natsuwa, magidancin driver ya mika mata wani bakin babbar leda, yana fadin,,,

  ummee taimaka don Allah kie shiga da sakon nan, na sashin haj. Babba ne, amsa tayi tana fadin,,,

  toh, kaman ance juya gefen hagun kie, sai da gabanta ya fadi, don tunanin ta Baffah sadeeq ne, ganin irin kaman da sukayi, amman saita lura wannan yayi yaro da yawa, kuma shi fari ne, yana jingine jikin wata black camry, kanshi na kasa, yana faman waya, bakin nan bakin kirin don shaye shaye,,,

   ta gefen ido yake binta da kallo, yana faman wani kankance ido, ba abin daya tafi da tunaninsa irin tafiyarta najan hankali, harta kule ma ganinsa, lokacinne ya sauke wayan yana dagowa, da sauke wani ajiyar zuciya, tare da raya,,,

  wannan fa? 

   

    *plss readers kuyi hakuri dani, naso ace ina posting kullum kullum, amman saboda matsalan ciwon ido, shie yasa za kuga post din sai a hankali, sometimes ma sister na, ke taimako dayin typing din, in sha Allah zan samu dai inga na kammala wannan, daga shi kuma shi kenan, afwan muje a haka, taku haleematus sa'adiya*



comment
share
Matatace
*2019*

meemartjj...........✍🏻
🕯🕯🕯
*MATATACE*
🕯🕯🕯


story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjj


*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty Ummeetah and my Fa'ixation._


plss a rika ije karatun lokutan sallah, makaranta, tare da ayyuka masu muhimmaci, kar a manta da azumin sitti shawwal, a daure, a'ikin lada yana da yawa.

Da sunan Allah mai rahma mai jinkai

page 11&12

――――Safiyar ranan rike da jakarta ta futo, sanye cikin uniform din makaranta, wando da riga iya gwiwa, sai karamin hijjabin da yake daya rufe mata gwiwan hannu,,,

black after dress ne a hannunta, tana tafe tana budewa zata sanya, tare da tafiya da dan sauri, da alamu yau din tayi latti ne, dai dai sanda muheet ke ribas da motar da yake ciki, sanye da wata bakar google, cak ya tsaya yana dada winning glass din motan, ya bita da kallo harta kammala sanya rigan, ta bude karamin kofan tana fucewanta,,,

ya sauke ajiyar zuciya, yana kallon saudat dake seat din kusa dashi, kanta kasa tana latsa wayarta,,,

saudat wacan bab din, wai sashin maami take? sai lokacin ta dago kanta da fadin,,,

wacce wai?ya yamutsa fuska yana hararanta da fadin,,,

dallah yarinyan data futa sanye da uniform, nake magana, tai dan shiru kafun tace,,,

uniform, dark and blue ko? yace,,,

yap, kin santa?ta dan tabe baki tana fadin,,,

ummm nidai yaya muheet plss muje mana, kan wannan house girl dinne ka tsai damu, ya zaro ido da fadin,,,

house girl kuma, are yhu serious, tace,,,

of course, me a'ikin sashin maami ne, yace,,,

wow bab din ta hadu, amma kwana take koh, ta runtse ido da fadin,,,

oh shet, yaya muheet, zanfa rasa lectures dina, kwana take mana, ya zabga mata harara, yana maida tabaran idonsa daya cire da hararanta, da fadin,,,

karki mun ihu a mota, saiki sauka in fasa kaiki, kinsan muheet baahi da mutunci, shiru kawai tayi tana cigaba da danna wayarta, shikuma yana saaka mummunar kudirinsa a zucci.

ya kasa samun sukuni, waya mai tsada ya shiga wani plaza ya siyo, harya kira munirat zai bata, sai kuma ya fasa, yafi ganinta tare da muhibbat yasan maybe sunfi shiri, don haka yayi murmushi da plan dinsa daya shirya.

kaiwa take tsakanin kitchen da dinning area, tana shirya abincin dare, falon sit babu kowa, sai karan fanka dake a'iki, both na dinning area, da seating room,,,

ummeetah, ummeetah, shine abin da taji a tsakar kanta, ta juyo rike da warmer data idda ijewa bisa dinning din, tana kallon muhibbat dake karisowa inda take da wani irin murmushi, tana kuma mamakin labarin da take dauke dashi a bakinta,,

ta kariso tana jan hannun ummeetah dake jikin dinning chair, da fadin,,

banxa na, zo muje kie gani, daga nan suka wuce bedroom, ita dai ummeetah ana janye da hannunta, bisa gado suka zube, muhibbat na murmushi da yake hakora take fadin,,

ke baby, kakanki ta yanke sa'a, kinyi wata mai zafi fa, ta karisa maganan tana zaro wayar a kwalinta, mai kyau da tsada, tare da fadin,,,

tararan, cike da mamaki ummeetah ke fadin,,

muhibbat nifa ban gane ba, ta tura mata kwalin wayan tana fadin,,

ummh kie amsa mana kie gani, amsar wayan tayi, tana shafa kwalin a hankali, hakika wayan ta mata kyau, ta rika jujuyawa, kafun ta kalli muhibbat da fadin,,

kinji dadi enmmata, wayar tayi kyau sosai, ta kuma yashe baki tana fadin,,

ke bafa nawa bane, na kine uncle muheet ne yace ina kawo miki, wani,irin zaro ido tayi da fadin,,

nie kuma, na shiga uku, da sauri take toshe mata baki da fadin,,

dalla kie a hankali, kar aji, asha wani abin ne, wayace fa kawai, kuma dan uwan mune, nace fa miki fa, kanin aunty mainat ne, kara daga wayar tayi tana dubawa, muhibbat na cigaba da fadin,,

nima yace, indai na baki kika amsa, zai saimun irinta, cike da yarinta take dafe hannun ummeetah da kuma fadin,,

ke wayar fa mai tsadane, kinga daya siya mun, sai muyi anko, ke zamu faso gari da wulakanci, a hankali ummeetah ta sauke ajiyar zuciya tana fadin,,

nasan wayar nada tsada, shi yasa nake tunanin abin da zaisa ya bani, muhibbat kie tuna fa nifa yer a'ikine a gidan nan, kuma kinsan yen site dinsu sun tsani house maids, ko shima irin auntyn mainat ne?yatsa ta daura bisa labbanta tana faman kifkifta ido da fadin,,

haka nefa, kuma fa, shima uncle muheet bashi da wani kirki sosai, ta kalli ummeetah cike da wauta tana fadin,,

toh me yasa ya fara siya miki, kofa munirat bata dashi, karami irin nawa take rikewa, ummeetah tace,,

toh nima a'i ban sani ba, kinga rike wannan wayar kie maida mishi, ta karisa maganan da daura mata wayar a jikinta, sai lokacin ta tafa hannu da murmushin ta, tana fadin,,

haka ne, yess na gane, sonki yakeyi, ta kai mata duka kafada tana kuma fadin,,

banxa na, kie gane manah, dama yace mun kina da hankali, yana ta yabon ki, ashe wann........ kyam ta tsaya da magana, ganin ummeetah na kallon bakin kofa cike da tsoro, a hankali ta juya tana kallan wacce ke tsaye jikin kofa tana jinsu, kafun ta juyo tana dan runtse ido, tare da taba fuska, fuska daure ta kariso tana fadin,,

good yayi muku kyau, kuban wayar nan, da sauri ummeetah ke dauka tana mika mata, ta zuba ma muhibbat rankwashi, wacce ta dafe kai tana kuma rufe ido don kuya, tai hanyar futa tana mata nunata da fadin,,

ke koh, na rantse muku duk wani rawan kan da kuke fama dashi zan goge muku, kubar ganin kun girma, daga haka ta fice daga dakin, tana tsaki da raya,,

muheet, shi wai yaron nan, duk inda yake sai yayi halin nashi, to ya rufa mata asiri.

A tankamemen falon mahaifiyar tasa ta iddashi, zaune kafa daya bisa daya, yana kallon wani American series, ta zauna kusa dashi, tare da daga mai kwalin wayar saitin fuskarsa, da sauri ya mike yana zaunawa da kyau tare da kallon wayan yana hada rai da fadin,,

what!waya baki wayar nan, ta zabga mai harara da fadin,,

muheet don Allah ka rufa mun asiri, yarinyan nan marainiyace, plss inaso ka kama girman ka kawai, ya dauke kansa da wani fidda sautin fito daga bakinsa, tace,,

nasan kunin keji, so, inason ka futa harkanta kawai, da sauri yake fadin,,,

anki din, anki a futa harkanta, ina ruwan kie, nifa bana son takura, ke kinfi son muyi ta rigima ko?cikin zafi tace,,

ouk, toh mu zaba, na lura kwata kwata baka so........

wai me yake faruwa ne, kuka cika mun falo sa surutu, wannan ne ya katse ma mainat maganan ta, ta dago kai, rai bace tana kallon mahaifiyar tasu, dake sanye cikin dikin atamfa bubu gwon, na alfarma, ansha daurin nan da aka futo da kananun kalaba da tayi ta kasa, an kama da ribbon, sai bakin da yaji bakin jambaki sama sama, ta zauna kujeran dake facing dinsu tana kuma fadin,,

me yake faruwa?ku kullum baku iya koyi da Najma da zahira ne, koni da yer uwata, amman sai fada, kaman kuna ganin hanjin juna, mainat ta soma fadin,,

mummy kiyi ma muheet magana, sai kuma tayi shiru,,

tswssssssss, yaja wani dogon tsaki, tare da komawa ya kishingida, itama dan tsaki mummyn tayi, tana dan kishingida ta gefe daya, tare da danna tab din dake hannunta, take fadin,,

baxa amun bayanin me yake faruwa ba kenen?dan rutse ido tayi da takaici tana fadin,,

mummy kiyi masa magana kawai, ya futa harkan ummeetah, da sauri yake fadin,,

waike meye matsala na dake ne?ina ruwanki da alaka mu da ita, da sauri mummyn ta dago,daga jikin kujeran tana fadin,,

wait, wacece ummeetah, tai dan shiru kafun tace,,

yarinyan da take ma maami a'ikace a'ikacen sashinta, a razane ta dago tana dafe kirji da fadin,,

what!ta kallesa tana fadin,,

me a'iki, a gidan nan, nie yagana, ganin haka yasa mainat yin dan dariya, tana kuma fadin,,

mummy kin gani har phone ya siya mata, don raka asara, a rikice take nunasa da yatsa da fadin,,

muheet ka kiyaye nie, ka koma cikin hankalinka, ya zumburo baki da fadin,,

wai mummy meye matsalan, don na nuna ina son house gir.....

kul!ka gyara kalamanka, inason tayi can, kayi can, bana son na kara jin zancan nan, na kasheta, if not ranka zai mumunar baci, ya runtse idanu da dan daka kafafunsa, kaman wani yaro da fadin,,

nidai gaskiya a barni na huta, naga abu kuma ina so, sai a takur...... cikin zafi ta mike zaraf, taku bai wuce hudu ba ta iso garesahi, sai jin wani lafiyayan mari yaji a kumantunsa, mainat dake gefe ta zaro ido cike da mamaki, tana sauraran kalaman mummyn tasu dake fadin,,

kaci gidanku da so din, wannan ya zama first and last dazan kara maka gargadi akan yarinyan nan, mikewa yayi dafe da kumatu kamar zai kuka yake bin mummyn tasu da kallo, lallai ya manta last data dauki hannu ta daura a jikinsa, shiko duk abin daya wahalar dashi, to yafi kwallafa ma ran samu, ya fice da falon yana fadin,,

ko ana so, ko ba'a so, dole na samu abin da nake so, ta zaro idon da wani damuwa dake damunta, kafun ta koma tana zama da dan dafe kanta, ta kalli mainat da fadin,,

ina wayar? ban nan, da sauri take mika mata, ta zabga mata harara da fadin,,

munafun munafun, kema tashi kibar mun falo, da sauri ta mike tana barin sashin, sanda saudat na fadin,,

mummy Allah, yarinyan ma kije ki ja mata kunni ne, tana jujjuya wayar, kafun mummyn tasu ta mike itama tabi bayarta rai bace,,

ummeetah, bata jiba bata gani ba, aka hauta da masifa, tatas tayi mata, tare da mata concrete warning akan danta, hankalin ummeetah ya tashi, don tunda taxo gidan wannan ne tashin hankali na farko data gani, don haka taji wani tsanar muheet dinma, ta kara kiyayewa akan abin dazai hadata dashi.

shiko tun daga ranan idanunsa na kanta, ya hanata sakat, sun gabda zana jss exams dinsu, ya takura masu sai dai su rika zuwa wajanshi lesson, ita dai taki zuwa, su muhibbat kadai ke zuwa, hakan ya kara sashi cikin damuwa.

***
Gaba daya a yen kwanakin hankalinsa yayi gida, hakanan yake jie a jikinsa akwai abin da yake tafiya ba dai dai ba, lokacin kuwa daya samu labarin wasu yen mastala daya shafi harkan kasuwancin nashi, ba bata lokaci ya soma shirye shiryen dawowa, tare yaso yayi musu biza, amman tace ita ba zata jeba, yana mamakinta wani lokacin jin kasan take kamar na haihuwanta, dole shi kadai yayi ma kanshi biza, ya dawo cike da kewar kasa Nigeria.

Ranar wata sunday flight dinsu ya sauka a Abuja international airport, misalin 10pm, hotel ya sauka, safiyar ranan 8am dot tayi mishi a cikin babbar company.

***

A hankali ta bude karamin kofan, dake jikin gate din zata futa, yau sanye take da hijjab din haddanta, bisa kayan makarantan bokonta, sai school bag dinta dake rataye a baya,,

gabanta yace rass, cin karo da fuskar muheet da tayi shima zai shigo, da sauri tayi baya tana bashi hanya zai wuce, shima ruko hannunta yayi, kaman wacce ya rike zata fadi, ta fisge hannunta cikin zafi tana kuma ja da baya tare da watsa mishi wani kalan harara, rayuwanta ta tsani namijin dazai rike mata koda yatsane,,

ya karisa shigowa da wani mugunta, yana shan gabanta, da tayi nan sai shima ya matsa, kanta na kasa kaman tasa kuka don bakin ciki,,

pin pin, shine abin daya sasu waigawa gefe, driver ne kejan katuwar motan, kirar matrix, daya taho da ita daga packing space, gate man na kokarin bude gate din, dai dai sanda glass din baya yake sauka, yana zaune ransa ya nuna rashin jin dadin abin da dan nasa yayi,,

mutallab, kaga naka, zaka bata hanya ko kuwa, da dan sauri yaja gefe yana sosa kai alamun jin kunya, ummeetah na fadin,,

ina kwana, yace,,

lfylau, wuce abinki, da sauri tabar wajan tana futa, ya kalli dan nasa da girgixa kai yana furta kalman,,

Allah ya shirya, daga haka driver ya maida glass din sama suka wuce, ya fuxxar da iska daga bakinsa, yana jin zafi sosai a zuciyarsa, gaskiya yaufa yakai makura, dole ne yasan abin yie, daga haka ya wuce site din mahaifiyarsu.

a'iki take sosai a kitchen din, ta sauke wannan ta daura wancan, ya shigo da dan dariya yana fadin,,

haj. ladiyo, ta juyo itama da dariya tana washe baki da fadin,,

a'ah, kaga uban masu gida, babba dan babba, an tashi lfy, ya yamutsa fuska da fadin,,

qlau nake, dama wata alfarma naxo nema, tace,,

ka fada koma menene an gama, yai dan murmushi yana fadin,,

yawwa ladiyo, daman nasan zaki mun, plss so nake yau indai kin kammala girki, kiba wannan ummeetah, me a'iki nacan site din ta kawo mun, tace,,

wannan kawai, yace,,

shi kadai, tace,,

angama, ya zaro farare, har hudu ya mika mata da fadin,,

wannan na cefane ne, yer dariya tayi da guda tana fadin,,

Allah yayi albarka, in sha Allah za kaga yanda kake so, yai hanyar futa, har yakai kofa ya tsaya yana fadin,,

kifa tabbatar ita kika ba mawa, har tana sarkewa wajan fadin,,

to....to....toh, ba matsala, daga ya fice daga kitchen din, tana dan kulle kudin a gefen zani.

***

Office ne babba, wanda yaji abubbuwa na more rayuwa, ya kawatu iya kawatuwa, a tsakiya can, wani classic table ne mai girma, mai dauke da wani design chair mai jujuyawa, sai ta dayan site din dake dauke da kujeru suma masu kyau na zama, guda biyu da suke facing juna,,

kayane sosai bisa table din, su desktop, files, da sauran su, wasu duma duman sofa guda biyu dake gefe daya, 3seater da 2seater, ga wani tsadaddan dispenser dake can gefe yana a'iki, banda wani karamin fridge, dake kusa da wani dan madaidacin dinning table mai shegen kyau, mai dauke da da kujeru hudu, kai kaya dai iri iri,,

sadeeq ne zaune yana wasu yen rubuce rubuce, sanye cikin navy blue din american suite, ya bada hankalinsa sosai, bayan ya kammala amsan baki masu zuwa yin mishi sannu da zuwa, da sauran ma'akatan wajan, dagowa da sauri yayi, tunawa da lawyern da P.A, dinsa yace, yana son ganinshi, ya numfasa yana jawo tellphone jikin land line, tare da latsa wasu yen numbobi, maganan da befi na 2minutes ba yayi, yana ije wayar,,

dai dai sanda barister ke sawo kai ciki, sanye da black suit, da red file dinshi a hannu, bayanshi kuma wasu mutane ne, su biyu dukunsu kaman ninsu daya, sai dai daya ya girmi daya a shekaru, kallo daya zaka musu, ka gane fulanin dajine, duba da irin shigar da su kayi, rigan yadi na roba daban, hakama wondan kalanshi daban, sai takalmin roban da suka kwama a kafafu,,

ya nisa yana mamakin wadannan mutanan, sun fiye naci, kafun ya mika ma barister hannun suna gaisawa da mutunci, ya nuna mishi daya daga cikin kujerun biyu da suke gabanshi alamar ya zauna, su kuma suna tsaye sun kara hada rai, baibi ta kansu ba, ya maida hankalinsa wajen barister dake introducing kanshi, ya gama yan ciro wata yer paper a file dinshi yana mika ma sadeeq, amsa yayi, sosai yake maida hankalinshi kan paper, kafun ya dago da yer murmushi yana nuna su da fadin,,

sune wadaddan ko?,,

eh sune, ya jawo wayarsa dake gefe yana fadin,,

plss 2minutes, ya kara wayar a kunninsa, yana kinshingida jikin kujreran, tare da dan dubansu a yatsine yake nuna musu sofa chair din da fadin,,

zaku iya zama, suma suna kumbura, suka sami waje suna takurewa waje daya, shiga uku ya daga wayar da furta kalman sallama, ya amsa mai, be bari yace komai ba yake fadin,,

barr. Abdullah.....shiru ya danyi kafun yayi dan murmushi yana fadin,,

oukk, nace Abdullah, ka gane ba alfarma nake nema ba, ya kuma yin shiru, kafun yayi yer dariya mai sauti da fadin,,

plsss kaga saurareni, daga haka ya zayyane mishi komai, kafun ya karisa da fadin,,

ouk ina jiranka, ya sauke wayar, yana komawa da kiran numbern angel dinshi da yake tason kira yaki shiga, yai dan tsaki, dai dai sanda wayar barister ya dauki ringing, kallon juna sukayi, cikin girmamawa ya daga wayar, shima basu wani jima suna magana ba, ya katse kiran, bayan ya gama da faman fadin,,

ouk sir, yes sir, ya sauke wayar yana kallon sadeeq dake kallonsa shima yana fadin,,

toh mu zamu wuce, barr. Abdullah, ya zayyane mun komai, nagode kwarai daka fahimce magana na, ya dan numfasa yana tasowa daga kishingidan da yayi da yakefadin,,

hope dai babu sauran wani matsala, mikewa barister yayi da fadin,,

no, ranka shi dade, a'i mun gama magana, ya mika masa hannu suka kuma musabaha, kafun barister ya juya, yana kallon fulanin da fadin,,

toh bayin Allah ku tashi muje ko, da sauri babban ciki ya mike da fadin,,

kaman yaya, kaima ya baka cin hancinne?dan zaro ido yayi, sadeeq na dada gyara zama da murmushi, indai wannan ne ba yau ya fara gani ba, yasan dai bakon abune, a wajan shi baristern dake fadin,,

kunga ku muje, zan muku bayanin koma menene, na zaunan ya kuma gyara zama da fadin,,

gaskiya mufa ba inda zamuje, a dakeka a hanaka kuka, ya cinye mana dukiyar dan uwa, ya kashe shie, sannan duk inda muka kai kara, sai aki bin mana hakinmu, gaskiya na gaji, babu inda zan motsa, dayanma ya harzuko da fadin,,

wannan shine magana, kawai maganin zaman lfy, ya bamu dukiyar dan uwan mu, kowa ma ya zauna lfy, kan barister ya daure, ya shiga lallabasu ya samu su fita, koma menene, sa karishe waje, kar susa suji kunya, amman suka tubure, tare da hardewa bisa kujeran, ganin haka sadeeq ya taso cikin tafiyar kasaitan shi ya futo table din yana zuwa ta site din da suke, da yatsa yake nuna musu kofa da fadin,,

ko ku futa da azziki, ko kuma insa a futa daku da rashin mutunci, kallonsa suke da wani irin tsana, karamin na fadin,,

toh kasa a futa damu din, sa a futa damu, kaman goguwa babban ya taso sai gaban sadeeq din, hannu bibbiyu yasa yana cacume mishi kolar riga, yana kumfar baki da fadin,,

kai ko, kabar ganin ka kwashe dukiyar dan uwan mu, na rantse maka sai naga bayanka, kaji ka san........sadeeq ya zaro ido da matukar mamaki, dai dai sanda barister ke finciko dan fulanin yana fadin,,

ku wasu irin mutanan banxane, kunsa wanene shi kuwa? nasan haka halinku yake daban taimaka muku ba, bunch of idiots, ku wuce mu futa, jiki a sanyaye sukai haryar futa, babban na fadin,,

yallabai kayi hakuri, raine ya baci, ko kallansa be yiba, hankalinsa nakan sadeeq dake rike da tellphone a kunni, ransa matukar bace, yana kiran securities, ya kammala yana ije wayar da kallon barister dake fadin,,

ranka shi dade, don Allah kayi mun a'ikin gafara, bansan haka mutanan nan suke ba, amma za'a dauki mataki sosai, ya dan runtse ido da takaici a hankali yake furta harafan,,,

pls yhu can get out of my office now, da girmamawa yake fadin,,

thank yhu sir, am very sorry, dai dai sanda securities suka iso wajan, suka tasa keyar mutanan biyu, shima barister ya futa da jawo mai kofa.

ya rika ganin wani dishi dishi, saboda tsaban bacin rai, a hankali ya juya yana komawa seat dinsa, sai kuma ya fasa,,yana nufa wajen dinning din, ba tare daya ankaraba yaji yayi karo da kujera, gwiwansa ya daki dinning chair,,

ouch, ya salam, ya dafe gwiwan, jin irin azaban dake kamai har tsakar kanshi, yayi san tsaki, yana jawo kujeran da zama, tare da dafe gwiwan hannunsa bisa dinning table din, yana dafe kanshi da yayi kasa dashi, da yen yatsunsa, zuciyasa na ayyana sunanta,,

ummeetah, koda yaushe itace matsalanshi, dama shi kullum zuciyarsa a wani kuntace yake jinsa, bare damuwanta ya kunno kai, ko yaya sai hankalinsa ya tashi, yafi karfin 20minutes a haka, kafun yaji anyi knowking kofan, ya dan dago kai da fadin,,

yes come in, ya turo kofan a hankali yana karisawo ciki, sanye cikin black suit, wanda befi tsaransa a shekaru ba, murmushi yake sosai da fadin,,

ya mutumin, meke faruwa ne?ya kariso yana dafa kujeran da yake zaune,

Please Login or Register in order to submit comment