Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mansion din, tana tafe tana juyowa da feeling so strange, kasancewan ita sabuwa ce a makaranta, shima dake zaune cikin motar yana kallonta, cikin shigar doguwar abaya milk colour, sai ta yafa mayafinta bisa ka white, kaman yanda kwalliyar jikin rigan yake fari, yer plat shoe ne fari a kafanta, sai farin cute bag dinta dake rataye bisa kafada,,

duk tafiya daya saita juyo ta kalleshi, tana tafiya kaman ba za tayi ba, shikam ya kasa tada motar, ji yake kamar ya rakata suyi karatun tare, tana hangeshi ta cikin glass din da yayi winning kasa, a hankali ya lumshe idonsa, yatsun hannunsa na dama yakai saman bakinshi,,

next juyowa da zatayi suka hada ido, kiss ya sakar ma hannu, yana hura mata ta iska, wani mugun zaro ido tayi, kafun ta juya tana runtse ido da dan murmushi, tunda tasa kai bata kara juyowa ba harta shige, shiko dan dariya yakeyi, yanda ta bace lokaci daya, kafun ya tada motar yana barin haraban wajen.

da suka tashima shi ya biyo ya dauketa, wani lokacin kuma in a'iki ya mishi yawa, ta dauki taxi, data dawo gida sallah kawai za tayi ta fara shirye shiryen daura abinci, kafun kuma lokacin tafiyansu makaranta da Irfan yayi su tafi.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiyar musu, sanda ummeetah ke cigaba da zuwa makarantanta, tana dada girma da wayau, da kara zama emmata, har lokacin da babban sallah ta riskesu, kudi yasa aka kashe musu baji ba gani can gida, harda ummeetah daya hada nata da munat.

Ranar da kayan suka iso, shi ya taho dasu gida, musamman ya futo dasu a falo, time din matarsa bata nan, su ummeetah kuma sun tafi makaranta ita da Irfan, jie kawai yayi duk cikin kayan babu wanda yake son gani irin na ummeetah, don haka ya shiga bude kayan,,

can ya bude wata yer madaidaciyar traveling bag da aka zubo mata dinkunan da aka mata, da sakon letter hibba yayi karo, yayi murmushi yana bubbude kayan nata,,

wow masha Allah kawai yake faman rayawa, sai hangota kawai yake cikin dinkunan, wata light green super wax mai adon flowers black ne ya tafi da tunaninsa, tun daga kan design din atamfar har dinkin sun matukar burgeshi, ya rika daga kayan, yana hango yanda zasu mata kyau a jiki,,

a haka suka dawo school suka sameshi, yana faman bubbude kayan, Irfan yaje da gudu yana ganin nashi kayan da zumudi, yayin da ummeeta tayi mishi sannu da gida tana wucewa dakinta, muryansa ne ya katseta da fadin,,

Humaira zoki dauka kayan kie, ba musu ta juyo, ya nuna mata jakar da ya gama barbatsalawa da fadin,,

gashi nan saiki maida kayan ciki, akwai wasu sakon da auntyn ki munat suka a'iko miki, zama tayi da murna tana fadin,,

Allah sarki auntyn mu, nagode Allah ya saka da alkhairi, ta kalleshi da fadin,,

Baffah plss zaka aramun wayarka inma auntyn mu godiya, yace,,

toh saikin shirya, da wani murmushin take maida kayan tana daddagawa, tafi daga wata red super english, alamar shine wanda yafi mata kyau, sosai ya kalleta da fadin,,

wanne yafi miki kyau tsakanin green&red din?

wannan?ta fada tana daga super wax din, yace,,

eh, murmushi tayi tana daga red super english din, yayi dan shiru, kaman zaiyi magana sai kuma ya dan tabe baki, yana cigaba da biyema Irfan dake furfuto da nashi kayan, ta kammala maida kayan tass, sannan ta dauki kayanta tai daki, acan ta kuma bubbudewa tana gani, sosai kayan suka burgeta, tana kuma godewa Allah daya hadata da masu sonta a rayuwa.

Duk wani shirye shirye na sallah ya kammala, wannan karon ma tare suka futa siyyaiyan duk wani abu daya dace, lokacin da ummeetah ta gabatar da kalolin snacks kamar dai wancan, wannan karon har gidan DR khamis sun kawo mata nasu snacks din, matar sai wani daga hanci takeyi, ko a gefen zaninta, tayi ta mika musu abinsu.

***

Hankalinsa sosai ya bada bisa littafin dake hannunsa, wanda ke rubuce da business ownership a jiki yana karantawa, idanunsa sanye da wani farin glasses, yana zaune bisa makeken gadon nasu, ya mimmike kafa, yayin da take tsaye tana daddaga kayan da suka iso yau daga gida, sai murna take, don duk yawancin irin dinkunan da tace ma kannin nata a matane, ta daga wani pited armless gown na atamfa tana fadin,,

baby ina nuna maka dresses dina, shine kake wani sharewa ko, da sauri ya dago yana kallonta da fadin,,

sorry angel, karatu nake, wow yayi kyau, amman kinsan menene?kai ta kada alamar a'a, yace,,

wannan dayan gown din da kika nuna yafu mun kyau, ta dan tabe baki tana daga maternity gown din da yaji style na alfarma tare fadin,,

kai gaskiya ya cika so heavy, an rufe kayan da yawa, jubi wata uwar pencil hand nie ina zan kaishi, maybe ma kyauta dashi zanyi, duk cikin kayan shine baimun ba, marairaice fuska yayi da cire glasses din idonsa yana fadin,,

plss baby atleast for my sake, kie taimaka kisa mun inga yanda za suyi kyau a jikinki, dariya ta kwasa dashi tana fadin,,

Boo nah dan rigima, in kana irin wannan cat face din, kasan meye, kana tuna mun time din bikin mu da nace na fasa, ka shiga damuwa, ta karisa maganar cike da annashuwa, yai dan murmushin da fadin,,

so it funny angel? zaro ido tayi da fadin,,

of course, kama daina batun wannan zumbuli gown din, ba dani ba, maida glasses dinshi yayi da dan girgixa kai yana fadin,,

good, kiyi yanda kike so, daga haka ya cigaba da karatunsa, yayin da take cigaba da daddaga kayan, don ita nata daban suka iso.


comment
share
vote

*matatace 2019*
Na meemartjj
[14/08, 14:29] Dala Grp: 🕯🕯🕯
    *MATATACE*
          🕯🕯🕯


story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjj 

*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty Ummeetah any my Fa'ixation._

page 41~42

__________A wannan karon ma dai ummeetah ce ta shirya Irfan, light blue din shadda da yayi matukar musu kyau, komai nasu iri daya, kamar yanda suka saba, harta da agogansu, hulansu, takalmansu, size ne kawai ke banbanta, wannan karami wannan babba, matar gidan na bacci suka futa, ko kafun su dawo kuma taci na kafan kare.

    Zaune kawai yake a falon bayan da suka dawo, Irfan nacan gidan DR khamis, yayin daya dawo ya taras da matar gidan bata nan, waya yayi mata waita futa, yanxun zata dawo, ya sauke wayar da dan tsaki, kwata kwata baya son wannan dabi'an nata, zata futa ko izininshi ba zata nema ba, yaja tsaki tare da cigaba da zira ido yana raya,,

   ita kuma wanna bari naga ta inda zata bullo, ko abinci ya kasa cie duk sai yaji ya kosa yaga irin shigar da zatayi.

   wanka ta futo tana goggoge jikinta, ta zauna gaban mirror tare da kammala yen shafe shafenta, sannan ta soma shiryawa, kayan ta futo dasu, ta zuba ma red super english din da yaji dinkin pited riga da rapper skirt ido, har cikin zuciyanta kayan sunfi mata kyau da soyuwa, amman sai tayi dan tsaki da fadin,,

   ya zanyi nie A'isha, Affah ya hadani da a'ik......, toshe bakinta tayi tana kuma fadin,,

   Allah na tuba, daga haka ta soma shiryawa harta kammala tsaf, dakin ta gyara tana maida komai inda ya kamata, kafun ta nufi gaban mirror.

    Gaba daya hankalinshi ya bada kan labaru da ake watsowa cikin TV, wani sassanyar kamshi turare ne yasa shi dago kai, yana juyawa ta barayin da yake jin kaman kamshin na futowa, kyam ya kura mata idanu, ta dan juya baya tana rufo kofan dakin, kafun kuma ta juyo, bata kalli inda yake ba ta wuce hanyar kitchen, suman zaune kawai yayi a wajen,,

  dankwalinta ne yafe bisa kanta, cikin shigar light green super wax din, dinkin pited play wanda yaji style na high neck, amman saiya kasance up shoulder daga dan sama, hannayen rigan nan daya bude yaji tsagu ta gefe daya, sai rapper skirt din daya zauna yayi mata kyau, tas ta dauke cikin hips dinta masu matukar daukan hankali, cikin nan a lafe kamar bata cin abinci,,

   ya dan numfasa yana mikewa tsam, da komawa site din kujreran dake facing kitchen zuwa bedroom dinta, yanda zai samu daman kare mata kallo da kyau, da wannan ta kuma futowa daga kitchen din, zata koma bedroom, tayi kaman bata san da mutum zaune a wajen ba,,

  umm umm, yayi mata gyaran murya da kyau, dan tsayawa tayi tana cice baki daga juyen da take, kafun ta juyo da murmushi a fuskanta,,

  ohh, Baffah sannu da zuwa, ta fada cike da waskewa irin yanxun ta lura dashi, shiko gogan sai faman binta da ido yake,,

   sai yanxun kika san dani, sha nayi idonki sun makance ne, ya fada maganar da wani basarwa, fuskanta daya sha light make up ta dan bata, a zuciya yake raya,,

  tayi kyau sosai, inama ta hada da daurin dankwalinta, kai tsaye yake fadi,,

   shi dankwalin baya dauruwa ne?sai data tabi dankwalin ta kalloeshi tana fadin,,

   a'ah kawai dai haka nake sonshi, ya dan yatsina fuska da fadin,,

   a'ah nie kuma ba haka nake sonki da shiba, a daurashi yanxun in gani, zatai magana ya bata rai da fadin,,

  bansan kie da musu dani ba, ba bata lokaci ta soma daura dankwalin, ya zuba mata idanu da wani murmushi, ganin hakane yasa tana dan turo baki, ta juya mishi baya tana cigaba da daurawa,,

  zaune yake kafa daya kan daya, baisan lokacin daya waresu ba, yana yarda remote din dake hannunsa, don karo da tallan hips din da take mishi, itama jin da tayi remote ya fadi ne, yayi saurin dawowa da ita hankalinta daga abin data a'ikata, da sauri ta juyo tana baya baya, kafun ta shige daki, gaba daya ya daskare a wajen,

   tafi minti biyar kafun ta futo, rana ta farko da yaga tayi dauri mai step step, saita futo da gashi nan ta tsakiya, sai kyallin baki kawai yake yie, sosai yayi mata kyau, gaba daya ya manta da wani TV da yake kallo, sai ita ya maida TVn,,

  kallonta kawai yake duk inda ta wulka, har sanda ta gama hada mishi abincin da yace ta hada mishi nan falo bisa center carpet, ta kammala komai ta mike da shirin barin wajen, ya taso zaizo ya zauna, jie yayi kaman ya rungumeta, daker ya iya saisaito natsuwarsa yana ruko hannunta da fadin,,

   zaune kie ta yani cin abinci, zaro ido tayi da fadin,,

  naci fah nawa daxun, niyyar zama yake, dole itama ta bishi suka tankwashe kafafu tare bisa carpet din, fusakan nan kamar za tayi kuka yake fadin,,

   sorry Humaira nah, kin dan tayani zama toh, ina cie ina kallon wannan kyakyawan shigar taki, yanda yayi maganar ne ya bata tausayi, ta zauna tana zuzzuba mishi abincin, shikam sai faman ba idonsa abinci yake, kafun yaba ma bakinsa, spoon daya ya diba na abincin har zai kai baki, sai kuma ya maida ya ije da fadin,,

   kai Allah kinyi kyau, yhu look just like a princess, i like this ur shining lipstick, abin nashi ya soma bata dariya, amman ba zata iya ba, don har yanxun tana gani wani kimarsa a idanunta, tama rasa abin cewa, sai bin juna suke da ido, kafun ta kauda nata, ya jefo mata tambaryar,,

  me yasa baki saka dayan da kikace yafi miki kyau ba?, da sauri take fadin,,

   baka son wannan ne?ya dan girgixa kai da fadin,,

  a'ah gani nayi kince wacan yafi miki kyau, nayi tunanin shi zaki sanya, har zatai magana sai kuma ta dan basar da fadin,,

  eh, duka a'i ina sonsu dama, shiru kawai yayi yana binta da kallo, wato ya gane ta lura yafi son wadannan ne, shi yasa ta sanya su,,

   lallai hankali ba'a girman jiki yake ba, baiwa ce, duba da irin draman da suka tafka da suhymah, duk da ita batai nata shirin ba, amman bari ta dawo yaga nata hankalin, ya ayyana hakan da faman zuba mata ido, ta yamutsa fuska tana fadin,,

  Baffah plss kaci abincin ka, aunty suhymah zata iya dawowa a ko wani lokaci fa, maimakon yayi mata magana, sai zuba ma yen labbanta dake motsi ido yayi, yana faman smiling kafun yace,,

  toh ki bani a baki, sai data zaro ido, kafun ta saka hannayenta biyu tana rufe fuska, yayi yer dariya da soma enjoyig abincin, sai daya kammala tass, sannan ta kwashe kayan tana barin wajen, baya gajiya da binta da ido, harta shige kitchen.  

  dai dai nan matarsa ta dawo, ta budo kofan tana shigowa da fadin,,

  sweetheart, murmushi ya sakar mata, taxo ta zauna kusa dashi tana manna mishi kiss gefen kumatu, tare da kallonsa tana fadin,,

  sorry baby, na barka kai kadai ko, bari naje ciki na shirya maka, yau ranar naka nefa, yace,,

    really, ta mike tana barin wajen da dan dariya take fadin,,

    show, favourite outpit dinka zan saka, daga haka ta shige daki, shikam kanshi ya daga sama, da kishingida bayansa jikin kujera yana lumshe ido, ummeetah ce kawai ke faman masa gixo a duniyar tunaninsa, ta dan bata lokaci kafun ta futo, tayi kyau sosai, harda heavy make up dinta, ta kariso tana wani karairaya da fadin,,

  hello!idanu ta zuba mishi a yanayin da yake ciki, tasa hannu tana bubbuga kafadarsa da kiran sunanshi, ya dan bude idanunsa firgit, gira ta daga mishi sama alamar lfy,,

  ya dan girgixa kai da murmushi, yana kare mata kallo cikin shigar armless pited gown din, wanda yaji tsagu tun daga kasa, har kusa tsakiyar cinya, kwata kwata abin bai mishi suga ba, sunan a dinka atamface kawai, amman wannan zubin readmade ne, hakanan ya kakalo murmushi da fadin,,

  kinyi kyau, nice outpit, sarere ta tsaya da mamaki tana kallonsa kafun tace,,

  hmm sadeeq zaifi kyau ka fadi gaskiya, don nasan ba gaskiya ka fada ba, ya gane mai take nufi, toh kayane ya matseta sosai, ga tumbin ya futo duk sai yaki mata kyau, dama gashi tayi kiba, dole ya mike tsaye kamar yanda ya saba mata a duk sanda tayi kwalliya, ya rudar dashi,,

  hannunsa daya ya sakallo ta bayanta, yayin daya tallafo fuskanta da dayan, a daidai kunni yake rada mata wasu kalmomi, sai faman tuntsura dariya take, yakai bakinsa zaiyi kissing dinta, tayi saurin dafe bakin da tafin hannunta tana fadin,,

  a'ah sweetheart karka bata mun make up,  cikata yayi ya koma ya zauna, ta jawo i-phone dinta, tana zama kujeran dake facing dinshi, wanda ya juya ma kitchen baya da fadin,,

  kaifa ba daman ka rungume mutum saika wani rikirkice, ta karisa maganar da yin masa gwalo, daura kafa daya yayi kan daya, yana kallonta da fadin,,

   shi yasa na cikaki, saboda nasan kona rikirkicen ba abin dazan samu, tana latsa wayarta take fadin,,

   sosai kuwa, don gaskiya kwalliya na maka, kuma baxaka bata munba, murmushi kawai yayi yana zuba ma kofan kitchen da har lokacin ummeetah ke ciki, can sai gata ta futo, dinning ta nufa, a hankakali take harhada kayan dasu Irfan suka bata shi dasu misha, kasa kasa yake kallonta, so yake su hada ido, can dai dta dago kai tana kallon inda yake,,

  ido daya ya kashe mata, yana sakar mata kiss ta iska, da sauri ta juya da wani murmushin a fuskanta ta juya zuwa kitchen din, shima murmushin yakeyi yana binta da kallo, da suka hada ido da matarsa, sai ya shiga daga mata gira sama, akayi wani far da ido ana cigaba da danna waya.

    haka sallah ta kare kullum da shigarta na daukan hankali, yayin da ita matar gidan tun shagargarin ranan ta koma bakin a'ikinta, ranar ta uku ma balcony din gidan suke zaune, wai dole sai yayi musu hoto ita da Irfan, shidai ya fake da daukarta hoto, sosai ya rika musu hotuna, mrs. khamis dake ta cikin gidanta tana kallonsu, kyacewa da dariya tayi tana tafa hannu da fadin,,

   lallai madam suhymah mijinki na lokaci, bake mai miji ba jarababbe ba, zaki gani ganin idonki, wannan kuwa bazan tsaida ba, nima in samu hankalin mijina yabar wajen, daga haka tayi shigewarta ciki abinta.
 

                           ***

   Fuska ba walwala ta futo daga cikin motan, shima futowan yayi daga maxaunin driver fuska cike da walwala, black suite dinsa ne rataye a hannu daya, daya cire ya rage sai farar ta ciki, sai briefcase dinshi dake rike dayan hannun,,

   tsayawa yayi yana kallonta ba tare daya rufe motar ba, harta zagayo ta inda yake, fuska bace tana mika mai hannu, alama ya bata suite din da briefcase din ta karisa mai dashi ciki, kamar yanda ta saba kullum suka dawo, murmushi sosai yakeyi yana binta da wani irin kallo, da bata fahimtar kona menene,,

  ta amsa briefcase din, tana amsar suite din kamar zai sakar mata sai kuma ya rike, da sauri ta dago kanta tana kallonshi, dukkansu rike da rigar, shima ita yake kallo, ta bata fuska cike da shagawaba tana fadin,,

    Baffah plss ka bani in shiga ciki, kamar zai magana kuma saiya fasa yana sakar mata, daga haka ta juya ta wuce ciki, dan dariya yayi, kafu ya rufe motan yana bin bayanta.

     da mamaki fadeela dake packing mota kofar gidan DR. khamis ta kafesu da idanu, kafun ta kalli yer uwanta tana fadin,,

   aunty salma look, wancan ba sadeeq din madam suhymah bane?itama ije wayar tayi tana kallonsu, kafun tace,,

   shine mana, tabi ummeetah da kallo sosai tana cigaba da fadin,,

  koya dai ya kara aure ne?fadeela data idda packing kasa cewa komai tayi, har sanda suka ga shigewansu ciki, sai kuma ta kyace da dariya, tana kashe motar da kokarin balle murfin motar ta futa, take fadin,,
 
   bari dai inje gun aunty shaakirah inji, maybe akwai news fa, daga haka ta fice, itama wacce aka kira da salmar futowa tayi tana rakata da fadin,,

   Allah ya shiryeki fadeela.

    

                         ***
    zaune take cikin bedroom dinta, sanye cikin wata light pink din riga high neck, mai  pencil hand, sai blue jeans din daya kamata, yaji adon stones daga can sama,,

  gaban mirror take zaune ta xuba ma kanta idanu, gashinta ke lilo data kama a tsakiyan kai ya sauka kasa, a hankali ta lumshe idanunta, jikintane yayi yarrr, sakamakon tuno da hot kiss din da Baffanta ya bata cikin mota, kawai don ya rike yen yatsunta, tayi saurin kwacewa, shine ta samu wannan horan, da sauri kuma ta runtse idanu gam tana taba fuska kafun ta budesu, caraf idanunta suka sauka bisa wata yer design card, dake rubuce da,,

  _it's your day, happy sweet seventeen,_ murmushi tasa tana picking card din, da fara budewa, gaba daya birthday wishes ne a ciki, Irfan ne ya turo kofan da fadin,,

   aunty ummeetah happy birthday, juyowa tayi da murmushi tana amsa masa da,,

  thank yhu, hannunsa rike da wata chocolate birthday cake, da sauri ta taso ta taimaka mai da amsa, bisa side drower ta ije tana fadin,,

  wow beautiful, is this mine?da fara'arsa yake fadin,,

    yes, daddy ya siya miki, dai dai sanda ya shigo dakin shima, tsayawa kawai yayi bakin kofan yana kallonta, sai tayi mishi kama da chocolate barbie toy, da sauri ta nufi wajen wardrobe tana ciro wani hijjabi, tam ya daure fuska suna hada ido ya zabga mata harara, ba shiri ta maida tana jawo wani karamin veil da yafawa bisa kanta, yayi dan murmushi,,

  Irfan ne ya jawo hannunsa suka zauna, ta yanka cake din, sai blushing takeyi, kallonta kawai yake suna shiriritarsu ita da Irfan, gaba daya ta sanja mishi sai yaga ta kara girma da zama big girl, kafun yace su shirya zasu futa, Irfan sai murna yake, after dress kawai ta saka, ta kuma shirya Irfan sannan suka futo.

   yana tsaye bakin motar yana jiransu, Irfan ya fara shiga baya, ita kuma harta kama handle din motan na gaba, yayi saurin sa hannunsa, sakar mai tayi ya bude mata kofan ta shiga, tare da gyara mata after dress dinta daya sauko, sannan ya maida kofan ya rufe, kafun shima ya shiga motar suka wuce.

   komai a idanun fadeela ya faru, dake leke ta windown gidan DR. khamis, yen uwane ga matar gidan, yayin da salma babar cikinsu wajen a'ikinsu daya da suhymah, don haka suka zama kamar kawaye, itama suna zaune da mijinta ne a kasan.

  ta sheke da dariya, tana komawa ta zauna, da fadin,,

  ohh niee fadeela, ana tafka drama a gidan can, shaakirah data futo daga kitchen ta zauna tana fadin,,

   a'i fadeela ba kiga komai, indai lamarin gidan can ne, nie dariya ma yanxun abin ke bani, salma ce ta nisa da fadin,,

  plss ku daina mana, this is not funny, wai me suhymah ke yine haka, ina mamaki fa har yanxun ba zata gyara ba, shaakirah ta tabe baki da fadin,,

   hmm aunty salma kenan, suhymah ta wuce duk yanda kike tunani, mace sai kace makauniya, farkon sanda ta kawo yarinyan nan gidanta, sai dana mata maganar, kinsan amsar data bani, tayi dan dariyan takaici da fadin,,

  in daina damuwa, mijinta ba jarababbe bane, he is not after ladys, tana da yakinin in zasu shekara 100 a haka, babu abin dazai faru, fadeela tace,,

  o-lala, wai me take takama dashi ne haka, haka fa taso yinmun wannan rainin wayon don muna mutunci da mijinta, shikenan data zo gidan mu sai kika tana wani daddaure mun, salma tace,,

   a'i bata son kishiya, ko sunanata ta tsana jie, ni kuma kullum ina fada mata in bata son kishiya, ta maida hankali wajen tsare hakkokin mijinta, suhymah kullum a office take rayuwa, zanzo in sameta sannan in tafi in barta, shaakirah dake faman daga hanci tana fadin,,

   toh, bata samu baiwa ba, komai house girl din take mata, gashi ta tsani house helpers, kinga ko tsohon nan mr. jerry, haka take wahalar dashi da a'iki, ko mijinta bai sashi a'ikin da take sashi, bare wanda take cikin gidanta a'i sai abin da kuma ta gadama, mikewa tayi da nufa kitchen tana cigaba da fadin,,

   kinsan brothernta daya rasu shekarun baya, wai house girl din gidansu yace yana so, shine dad dinsu yace baxai aureta ba, a yanda take bada labarin kaman sun kore yarinyan ne, shine shi kuma yasha poison, yanda na lura lamarin ya matukar girgixa su, gaba daya laifin kuma suka daura kan yer a'ikin, ta karisa maganar tana daga kitchen, sauke ajiyar zuciya su kayi, salma na fadin,,

   eyyaah, hearttouching story, amma sune basu kyauta ba, da basu hanashi auranta ba, tai dan shiru kafun ta cigaba da magana cike takaici take fadin,,

   na rasa me yasa wasu gidan, idan boko yai boko, ije na addinin suke gaba daya a gefe, meye laifi don ya aure yer a'iki, itama naga a'i mutumce kamar kowa, ko kuma kiga idan kudi yayi kudi, sai kiga mutum yabar yeyenshi suna rayuwa kamar ba yeyen musulmai ba, wannan ba yie bane, yafi alkhairi ga mutum yayi abin daya kawo shi duniyar nan, ta karisa maganar rai bace, fadeela tace,,

   inko hakane, to suhymah na gabda girban abin data shuka, don jikina yana bani wancan yarinyan ba matsayin yer a'iki kawai take zaune ba, kai Allah ya nuna mun wannan ranar, dariya suke tare da shaakirah data dawo falon tana zama da fadin,,

   kai fadeela baki da dama, salma tace,,

   plss ku daina, bana son kuna ma kawata irin haka, kunsan yanda ta tsani kishiya kuwa, gaskiya zan sameta mu kara tattaunawa sosai, da sauri shaakirah ke fadin,,

    aunty salma, indai suhymah ce kalma daya zata rika nanata miki, mai cike da kwarin gwiwa, tana fadin,,

    _Nasan abin dana taka, mijina na daban ne cikin maza,_ ta karisa maganar da dan kwaikwayon muryan suhymah, dariya suka kara shekewa dashi, salma na fadin,,

  toh nie salma, meye ta taka har haka, mazan yanxun ma ka musu biyayyan yaka kare, bare ita da take yanda tai ra'ayi, shaakirah ta tabe baki da fadin,,

   oho mata, naga kamar lamarin nata dai kamar ba haka tabar mijin ba,,

   what!salma ta fada da fiddo idanu waje, kafun ta jinjina kai da fadin,,

   lallai inko hakane ta kulla alaka da dana sani babba, ta kuma kama hanyar da ba zata taba bulle mata ba,

Please Login or Register in order to submit comment