Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duka duka ba sufi guda talatin ba, a hankali yake furta,,

  maami sarkin cin kwai, yai dan murmushi yana nufa cikin gidan, ta kofan kitchen din, dai dai nan itama ta futo sanye da hijjab din data maida, kasa kasa take kallonsa da fadin,,

    ina kwana Baffah, sosai ya zuba mata idanu, na wasu yen sakanni, kafun yace,,

   yane, umm hmm, ta kasa fahimta yaren nashi, tana kwalalo mishi ido, ya dada gyara tsayuwa da fadin,,

   kinga dena zuba mun wannan kwan fitullun, dama haka kike zama, ana zuwa ana kallon na bulus ko?zaro ido tayi, gabanta yac rass, ashema ya ganta, kafun ta dan runtse ido, dajin kunya, ko a jikinsa yana cigaba da fadin,,

  sa'idu me kula da kajin maami yaxo yaga na bulus, shima muheet  ya zago ya dan rage zafinsa ko?idanu ta bude ta kara zuba mai da mamakin kalamansa, ya kuma daure fuska yana fadin,,

   ba nace kie daina zuba mun wadannan fitullun ba?ta kauda idanunta da sauri, rai bace yake kuma fadin,,

   haka kike zama ana zuwa ana ganin ki, maybe daga ke sai daurin kirji ko?,  da sauri ta girgixa kanta da kwallan da suka cika mata ido,,

   Baffah Allah ba haka bane, akwai ve...... ta kasa karisawa, wannan karon kasa kasa yake kallonta, yasan ba hakan bane, amman sai yace,,

   akwai me, me yasa kika gudu ciki to?wani kallon ta kara bashi kafun ta kauda kanta gefe, tana wasa da gefen hijjab dinta, da fadin,,

  akwai......., ta kasa karisawa, ya dan basar da kallon kayan wanke wanken da suke baje bisa tabarma,,

   wannan kayan fa, ke kika wanke duka?ya jefo mata tambayar cikin sauri, ajiyar zuciya ta saki, jin ya saki wacan zancen, kai ta daga da fadin,,

   eh, ya kalli wanda take shirin wankewa kuma yana fadin,,

   wa'innan fa, tace,,

    suma nie zan wanke yanxun, shiru ya danyi, daga site din wankakkun, ya koma da kallonsa site din wadanda bata wanke ba, kafun yace,,

   duk kuma kayan maami ne? sai data dan nisa kafun tace,,

  a'ah, gana maami nan, wannan kuma na mummyn su munirat ne zan wanke yanxun, besan sanda yabi kayan da hararan kasan ido ba, kafun ya dan tabe fuska yana fadin,,

   asamo wasu su karisa a'ikin, ya maido kallonsa sosai gareta da fadin,,

   kije kie soma harhada kayanki tun yanxu, jibi zamu bar kasan, wani irin zaro ido ummeetah tayi a kanshi, shima dan baya yayi, a hankali yake fadin,,

   toh nida electricity, bafa sai dake nace zanje yiba, muryanta na rawa, da idanunta da suka kawo kwalla take fadin,,

   toh Baffah ina zaka kaini?cikin gidan ya nufa da fadin,,

  inda na futo, tuni yaji sautin kukanta na tashi sosai, tana faman jero mishi,

   Baffah don Allah ka tausayawa rayuwata, kayi hakuri ka barni, nie bana son zuwa, in laifi na maka ka yafe mun, baxan kara ba, amman ka barni dasu auntyn mu da maami, don Allah karka kaini wajen aunty suhymah, cak ya tsaya be juyoba, har cikin zuciyarsa yake jin dacin kukanta, tare da tausaya mata, yasan don me take ma kukan, amman saiya dake da juyowa yana fadin,,
 
   ummeetah yaushe muka fara haka dake, ina magana kina jayayya, da sauri ta kada kanta da fadin,,

  a'ah Baffah ba haka bane, kayi hakuri, nie dai.....,,

   shout up, ya fada idanunsa a kankance, tare da nuna cikin gida da dan yatsa yana cigaba da fadin,,

   bana son wani magana, wuce ciki kawai kie fara hada kayan kie, ba musu ta shige tana cigaba da rera kuka, ya sauke wata ajiyar zuciya shima yana shiga ciki.   

   *_Hakika jiya naga ruwan comment dinku, kuma ya sanya nie farin ciki, na samu matsalan network da banba wasu reply ba, amman dai ina kuma fadin mucccchhh luv, Allah ya datar damu alkhairi, ya bar zumunci, luv yhu all_*

  *fatan alkhairi*


comment
share
Matatace
*2019*

meemartjj...........✍🏻
[14/08, 14:29] Dala Grp: 🕯🕯🕯
            _*MATATACE*_
     🕯🕯🕯

     

story&written by Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@meemartjj

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚

   *Dedicated to lovely sisters*
_Jameela ja'afar yakubu_
_Fateema ja'afar yakubu_
_Fa'iza ja'afar yakubu_

_Ina yen team din, da basa so ummeetah ta koma U.S, sakon gaisuwanta tace, HI🙋🏻_


page 27/28

___________Hankali tashe ta nufi dakinsu, da kuka ta fada gadon da hibbat ke kammala gyarawa, sororo tayi kafun ta shiga tambayarta abin daya faru, mainat ma sautin kukan ne, ya futo da ita daga nata bedroom din zuwa nasu, da mamaki take tambayar hibbat,,

   ita wannan me aka mata?,,

  nima auntyn mu, ban saniba kawai dai naga ta shigo tana kuka, ta bata amsa da dan damuwa, numfasawa mainat tayi da zama kusa da ummeetah tana fadin,,

  oya ummeetah tashi kie fada mun meke faruwa?ba musu ta tashi zaune, da share hawayenta tana fadin,,

  auntyn mu don Allah kie taimaka mun, Baffahn mune wai zai koma dani can wajen aunty suhymah, ni bana son zuwa, na fiso na zauna da ku, cike da mamaki mainat ke fadin,,

  yayan namu ne yace haka, da sauri take daga kai alamar eh, ta mike tsam da fadin,,

  kaii, bari naje muyi magana, daga haka ta fice daga dakin, ummeetah na cigaba da zubar hawaye tare da sauke ajiyar zuciya, kafun ta daga kai tana kallon hibbat data zuba mata idanu tana murmushi, cikin shashsheka take fadin,,

   hibbat plss ku taimaka mun, bana son zuwa, a hankali ta sulale bisa tyles, ummeetah ta bita da kallon mamaki, ba shamaki ta zuba hannunta a lallausar tafin kafan ummeetah, tana dago kyakyawan kafan, tare da dagowa da kallon ummeetah take fadin,,

   ummeelolo kinji dadi, ko airport ban taba zuwa ba, gashi ke kafanki zaya taka har cikin jirgi, so happy for yhu, jiki a sanyaye ummeetah ke fadin,,

   hibbat nie bana son zuwa fa, cika kafan nata tayi, da balla mata harara tana fadin,,

  dalla banxana, kasan fa zaku futa, wayyoo jirgi da dadi, shiru kawai tayi tana binta da kallon wauta irin na hibbat, ta manta jirgin zata haune taje tayi a'ikin da za'a azabtar da ita, kawai saita kara sa sabon kuka, hibbat na ganin kaman na dadi ma takeyi, ita ta samu wannan daman a'i sai murna.

  

  Yana zaune a falon, yayin da maami ma ta futo suna hira sosai, sai wani fara'a yakeyi, ta zauna kusa da maami tana faman turo baki, amman koda ta gaishe shi, sai gani tayi ya amsa da walwala, ta kalli maami dake kallonta tana fadin,,

  maami kinji wai ummee........, ta katseta da fadin,,

  ummeetah ko?karki damu, maganan da muka gama yanxun kenan, maimuna kinsan bana son tashin hankali, tafiyanta can ne nake ganin kaman za a samu natsuwa, saboda nan dinma matsala ta fara kunno kai, cike da dan damuwa take fadin,,

  maami toh karatun tafa?tace,,

  eh, wannan ma munyi magana, yace zata cigaba acan, ta maida hankalinta gareshi, tana cigaba da fadin,,

   kuma kullum ina fadin, d'a dai na kowa ne, don haka ka sanya ido da kyau, karda a maimaita abin daya faru a baya, kaji na fadama, ta karisa maganan so serious, hakan ya sanya shi fadin,,

   in sha Allah maami, za'a kiyaye da kyau, addu'anku kawai nake bukata, da murmushin jin dadi take fadin,,

   yayie kyau, Allah yayi albarka, kullum cikin yin muku ita nake, Allah yasa wannan tafiya ta kasance mai dumbin alkhairi a gareku gaba daya, da sauri ya dago yana kallon maami, kafun kuma ya waske yana jujjuya addu'an, mainat ma taji dan sanyi da abin da yace, dajin dadin addu'an maami take fadin,,

  Ameen maamin mu, ummeetah baiwar Allah, kallonta yayi tana wani mazewa, yayi saurin kawar da zancan da fadin,,

  ammm, naba kawu basheer wasu kudi, za'a fadada dakin kajin can naki, nan da sati daya za azo miki da guda dari biyar, kie fara dasu  kafun in dawo, komai da komai na ciyarwansu zanbar ma kawu basheer din, in Allah yasa musu albarka za'a amfana dasu, da dan murmushin murna take fadin,

   toh Allah yayi albarka, cikin zumudi mainat tace,,

  lah yayanmu, infa suka fara kwai, kullum sai an dibi kwai kimanin 500, dan hararanta yayi da fadin,,

  ba zasu kai haka ba madam, amman dai za'a samu sosai, maami tace,,

   nie indo ina zan kai kwai har kimanin guda dari biyar ma, da sauri yace,,

    a'ah, maami za'a fara futa miki dashi kasuwa ne, tace,,

  ohh, Allah sarki na kasuwanci zan fara, mainat na fadin,,

  maami ehmana, dama ya za ayi ki cinye kwai har guda dari biyar a rana, dakuwa ta watsa mata da fadin,,

   kinga naki, dariya su kayi gaba daya, tana kallonsa da cigaba da zuba mishi addu'a, yana faman amsawa da ameen, ya kalli mainat da fadin,,

  su wa'ema ya kamata azo a fara business, ta bata fuska da fadin,,

  maami kin gani ko, maami na fadin,,

  a'i jarin ne, da zaka bata shikenan, saita fara ko a cikin gida ne, su yarinya ma sunce ka basu jari mai tsoka, Allah yayi albarka,,

  Ameen, yace, da karawa da fadin,,

  can naga kamalu shima ya fara business na kayan kitchen, ya samun rigima yana son wasu kudi, zaisa wasu kaya a shagon nashi, naji dadi sosai, don yafi zaman haka ya kalli mainat da fadin,,
 
   kema zan turo miki da wasu yen 300k, kie fara jan wani abu, kar kuma a sake a tafi mun da kudi a iska, sosai tasa kara da fadin,,

   Allah dai ya biya, sai babban yayanmu, thank yhu, kallonta kawai yake da mamaki yana fadin,,

  meye haka?300k dinne kike ma wannan haukan, da sauri take fadin,,

   yess, yaya sadeeq dubu dari uku no be joke, harna fara jin wani zufan dadi, yawwa saura na ummeetah, kasan ya kamata ayi mata siyayyan wasu kaya kafun ta tafi, US ba kusa bane, shiru yayi tana fatan ya amince, don ta dauki wani alkwari, kawai saiji tayi yace,,

   zan hada in turo miki gaba daya,,

   yeeeeeee, that's my bro, hararanta yakeyi, itakam maami na musu dariya, suka cigaba da hiransu.

   

                    ***

Tun suna kallon abin nata wasa, har suka fara tausaya mata, kuka takeyi sosai, da fadin bata son zuwa, batun wanke wanke ma ta manta dashi, ba tasan yanda aka kare dashi ba, abin daya dameta ya dameta,,

   da ker maami ta lallasheta, ta hakura zata bishi, ba don ta soba, har zazzabin wahala sai data fara yie.

   bata kuma melewa ba, sai da taji shagargarin ranan, auntyn su tace taxo ta tafi saloon, don da yamma yayansu yace, zai zo su wuce, kuke takeyi haikam, kafun tasa dangana da shiga tayi wanka tare da futowa tana shiryawa,,

   hibbat na zaune bisa gadon, ta zuba mata idanu, ta dan kalleta da fadin,,

   sist lafia?ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, da fadin,

  hmmm ummeetah kinji dadi, America, jirgi, inama inama  nice k......,  da sauri ta rufe mata bakinta da fadin,,

   a'ah hibbat kar kice haka, kar kiso kasancewa kaman nie, hibbat a'ikatau fa zanje yie, ga wahalar da zan sha, tsaki hibbat tayi da fadin,,

  never, never sister, kin wuce wannan matsayin, ke mutum ce kamar kowa, mai daraja da kima, kie manta da wannan shegiyar aunty suhymah, kefa yanxun big girl ce, ba kaman da ba, in kin zauna a da ta cibgi banxa, a'i yanxun ba zama za kiyi ba, maintain ur class baby ina fada miki, numfasawa ummeetah tayi da murmushin yake tana fadin,,

   sist ba zaki gane bane, karki fatan ko makiyin kine, ya hadu da axabar dana hadu dashi, gurin aunty suhymah, ta karisa maganan da hawaye, jikin hibbat yayi sanyi tana fadin,,

   Allah ya saka miki, in sha Allah yanxun kam kinfi karfin hakan, karki damu yer uwa, soon soon sakayyanki zai futo, ummeetah ta nisa da fadin,,

    Allah yasa haka, dai dai sanda auntyn su ta shigo da kaya niki niki, tsiya take musu har lokacin basu tafi saloon dinba, da sauri suke karisa shiryawa, ta koma tana shigowa da wasu tsadaddun trolley, masu kyaun gaske,,

   nan hibbat tasa ihu tana kuranta kyaun akwatunan, guda biyu babba da mabi dashi, suka soma zaro kayan undies ne, dogayen riguna da gyalulluka masu tsada, harda yen takalma, mainat na nuna mata da fadin,,

   kanwata kin gani, kayan kine sunyi kyau, murmushi kawai tayi don kayan duk babu wanda za ace be yiba, harta colour din akwatin daya kasance pusher pink, yayi mata kyau, can kuma kaman an tsunguleta ta kalli agogan bango tana fadin,,

   oh my god, yayan mufa yace 5pm zaizo ku wuce, gashi har 11:30am yanxun, ku rufa mun asiri, kuxo ku tafi saloon dinnan, inaso har kitson in an kammala muku, ta kalli hibbat da fadin,,

   hibbat a'ikinsan shop din rubado ko?telah nah,,

   eh, tace, mainat na fadin,,

    yawwa, plss za kuje ku amso dinkin dana bashi jiya, kuyi sauri plss, ku dawo da wuri, don yayi mun warning daya zo wucewa za suyi,,

   tomm, suka fada su duka biyun, bayan sun amsa kudin kitson suka wuce, ummeetah na mamakin yanda ake shiryata zuwa magasa, koma dai meye tabar ma sarki Allah.

  
                       ***

   Be jima da shigowa ba, suma suka shigo, ya zauna nan falon maami, sanye cikin wasu kananun kaya da suka amsheshi, ya kara futowa young Alhaj dinsa, yasha wata white american jacket, sai zuba kamshinsa na alfarma yakeyi,,

   sai faman hada rai yakeyi, ganin yanxun ma zata shirya, saudat da munirat ma suna makale kusa dashi, don daga site dinsu yake, kowa rike da yer sabuwan wayan daya siya musu, hibbat ma aka bata nata, sai murna take tana godiya,,

   suka rika bin yanda ake ma ummeetah da kallo, tare da zubama yayar tasu ido, dake shirya zafafan dinkunan dasu hibbat suka amso, cikin trolley din, masu axaban kyau, sun kasa fahimtar meke faruwa ne,,

   shap shap ta futo wanka ta kammala shiryawa, ta futo sanye cikin riga da skirt na material, sai dankwalinsa yafe bisa kanta, tana rike da hijjab dinta a hannu, kusa da maami ta karisa ta zauna, tana zame dankwalin, maamin na sanya mata maganin dundruf din dake hannunta, da fadin,,

  gashi nan maimuna ta sanya miki daya cikin jakarki, in kinyi kitso, sai ki rika sawa, duk zasu futa kinji, cikin sanyi tace,,

   toh maami, yayin da hibbat ta dakko flask din abinci da plate tana fadin,,

  ummeetah, kici abinci tunda kince yunwa kike jie, ta fara xuba mata abincin a plate ta gama, ta sanya mata spoon tana mika mata, dai dai sanda maami ta gama sanya mata maganin, ta maida dankwalinta bisa sabbon kitsonta, maami na fadin,,

   maxa kicie abincin, hibbat miko mun magungunanta, inta kammala tasha, ba musu hibbat tayi hakan, mainat dai nacan wajen akwati sauri sauri suke komai.

   ta kasan ido yake binsu da kallon mamaki, yanda yaga ana mata wani shiri sosai, kafun ya dan tabe baki, yana duban wrist watch din dake hannunsa, da dan tsaki, maami ta kallesa da fadin,,

  yie hakuri yanxun zata kammala, sauri sauri ta gama cin abincin, maami na ballo mata maganin zazzabin ta bata, tare da mika mata ruwa a tambulan tasha, ta mika ma hibbat ledan maganin da fadin,,

   mika ma maimuna ta sanya mata ciki, da sauri ta amsa tana mika ma auntyn nasu, tsaf aka kammala shirya mata komai, ya mike sanda yaga tana saka hijjab dinta, maami ma sanye da hijjabinta, ta mike don yin musu rakiya zuwa wajen mota, mainat na janye da babban trolleyn, yayin da hibbat ke janye da karamin, sai da suka futa, rige rige suke su samu hibbat dake baya, munirat na fara fadin,,

  hibbat wai ina za'a da ita? da murmushi take fadin,,

   U.S mana, tare zasu tafi da uncle dinma,,

   what!shine abin da saudat ta fada cikin karaji, da karawa da fadin,,

   kina nufin, tare zasu tafi cikin jirgi, hibbat tace,,

   ehmana, yanxun ma haka Abuja zasu wuce, jibi 7am flight dinsu zai tashi,,

   hu ummm, shine abin da munirat ta fada cikin big voice dinta, suka fara kallon kallo da juna, kafun su juya suna fara hada hanya, kowa na rige rigen yakai tsegumi, hibbat ta dan girgixa kai, cike da tsanar halayensu, kafun ta wuce wajen motar, driver na kammala sanya kayan cikin buth. 


    Hankali tashe ta kariso wajen, tana binsu da kallo, da suke Tsaye suke wajen motar, maami na kuma jaddada mishi magana daya, kafun ta jefo tambayar,,

  a'ah son, dama da ita zaka koma?,,

  eh mummy, ya fada da murmushi yana karawa da fadin,,

   wannan karon Allah ya nufa da itan za'a, kinga hankalin daughtern ki zaya kwanta, murmushin yake tayi, tana bin ummeetah dake cikin shiga na alfarma, a'ah, wannan batai kama da kalan yer a'iki ba, kai gaba daya ba haka taso ya kasance ba,,

  ta rika binta da kallo, yayin da hibbat ta ruko hannunta kaman zatai kuka, tuni itama idanun ummeetah suka kawo kwalla, mainat na fadin,,

  o'o, hibbah wai yaushe zaki girma ne, kuka fa zaki sata, ta bata rai da fadin,,

   auntyn mu zanyi missing dinta ne fa, da gaske kuka take son yie, da murmushi mainat ke jawota da fadin,,

  toh in kinyi missing dinta, ba gani ba mummynki, da murmushi itama ta rungumeta tana fadin,,

  hakane my sweet mum, tuni ummeetah ta balle da kukan tausayin rabuwa da mutanan da suke sonta, itama kuma take sonsu, zuwa kuma ga inda ba'a kaunarta, hibbat ma tasa kukan, mainat ma sai da tai kwalla, tana kauda fuska, maami na fadin,,

  sabo tirken wawa, ita ta lallashe su, mainat ma tayi dauriyan maida kwallanta, shidai yana tsaye yana kallon ikon Allah, ta riko hannun ummeetah da fadin,,

  ummeetah kiyi hakuri, bawai don bamu sonki bane zamu barki ki tafi can, in sha Allahu wannan tafiyar naki babu musgunawa, zai zame miki alkhairi da yardan Allah, kai ummeetah ta daga da fadin,,

  toh auntyn mu, suka hada ido da mummy ta balla mata wani uwar harara, da kallon mainat tana raya,,

   sanabe da munafunci, an riga da an koya miki, tswssssssss sai kuma dan ja tsaki, ya bude gidan gaba yana kallon ummeetah da fadin,,

  oyah zoki shiga mu wuce, kuna bata mun lokaci, ba musu ta zare hannunta ana mainat, tana kallonsu maami, ta shige motar, maami na musu addu'an fatan sauka lafia, yayin da mummy ta zaro ido da kallon mamaki yanda ya wani bude mata motan, harda gyara mata hijjab sannan ya maida kofan rufe,,

  akwai matsala a lamarin nan, haka kawai ta nufi site dinta tana ayyanawa, barr. Abdullah da yanxun ya shigo gidan, ya futo daga motarshi yana nufo inda suke, da sauri yake gaisheta da taxo gittawa, amman ta gagara amsawa, duk da tasan matsayinshi yanxun na sirikinta a gunta,,

  amma black stomach ya rufe mata ido, ta shiga ciki da nufin lalubar yer tata don ta tsaida wannan tafiyar, ta gummace ummeetah tayi ta zama a nan din.
 

  shidai ya wuce inda abokin nasa ke tsaye, cikin mutunci suka gaisa da maami, ta amsa mai da fara'a sanda ta juya tabar wajen,  hibbat ma ta gaishe shi, sannan suka kuma sallama da ummeetah, ta koma ciki da dan gutun hawayenta, tsiyan abokai suke ma juna, mainat dake gefe tana faman ciccika, ya kalleta yana fadin,,

    sweetheart aymun a'ikin gafara, wasu ayyuka ne suka rikeni,,

   what!shine abin da sadeeq ke fada da dorawa da,,

   dan sake fada inji, ya kalleta yana kallonshi da maimaita,,

    sweet......hearttt, ya kada kai a hankali da fadin,,

   kut, kafun ya kalleta yana cigaba da fadin,,

  wato dake xa'a hadu aci amanar matar aboki nah ko mainat?yanda yayi maganan ne, ya basu dariya dukansu, shima da yer dariya yake fadin,,

  a'ah, it not funny, sauri nake yanxun ina kan hanya, amman za muyi waya da both of yhu, Abdullah yayi gyaran murya da fadin,,

  muna jira ranka ya dade, yayi wani murmushi, yana bude kofan baya da shiga, Abdullah ya sako kai ta ciki yana fadin,,

  baka jiba, nima za muyi waya, don ban gane irin wannan dawowan ba, da komawa, harara ya jefa mai suna yer dariya, tare da kuma musabaha da juna, sukai sallama, driver nayin ma motar key, sanda ummeetah ke yinma auntyn nata waving ta glass, itama tana maido mata, har motar ta idda futa daga gidan, su mainat kuma aka nufi site din baki da heartbeat din nata, don ta bashi wajen zama na musamman.

                        ***
   A daki kuwa cike da tashin H mummy  ta kira suhymah, don su tattauna, amman ga mamakinta, saiji tayi yarinyan na dariya da fadin,,

  aunty karki damu, indai nine Allah kawo su, kinsan wacece suhymahnki, so karki samu damuwa, cike da tashin H, take fadin,,

  daughter bana son wata matsalane tanan, ba kiga yanda yarinyanfa ta dawo bane, gwara koma meye ace muheet ya dauka, da dai ace tanan site dinki......, tai saurin katseta da fadin,,

  No aunty karki damu, kin manta da alkwarin da malaman nan, ta mana ne, da kuma irin kudin da muka kashe, plss ki daina cewa haka, babu wanda zata samu, inma muheet din, koma ba shiba, tuna mata da wannan ne yasa hankalin mummyn ya dan kwanta, tana sauke ajiyar zuciya, da cigaba da yen kulle kullensu,,

   itakam munirat tuni tasa kuka, ba kaman saudat dake bala'inson taga sun futa waje, koba komai waccan yer a'ikin ta rigasu d'ana cikin jirgi, kuma tasan yayansu kudin VIP seat yake biya, don haka bakin ciki ne fal ransu.

  

                       ***

Tunkan su isa taji yayi waya, ayi musu loging dakuna guda biyu, a tsadaddan hotel din daya saba sauka, nan kuwa suka sauka, tafka tafkan dakuna,,

  sanda ummeetah taga dakin da zata kwana ita daya, sai data dan tsorata, hakanan ta shiga ciki ta zauna shiru a marainiyanta, a haka aka kawo mata abincin dare,,

  shikam be wani huta ba, ya nufi gidan sirikansa, iyayan suhymah yaje yakai gaisuwa, ya jima kafun yayi musu kakkaban yeyen banki, harda kanin nata da suka cajesa kudin wasu laptop masi tsadan gaske, kaman ubansu bashi dashi, shi kuma ya dauka ya basu, daga nan ya dawo,,

  sai da yayi mata sai da safe, kafun ya wuce nashi dakin, yayi wanka yana kammala shiryawa cikin wasu kayan bacci, abin dake damunsa na damunsa, ya kare dai da jawo laptop, yana ma matarsa video call, nan dai suka lalace da hiran yanda sukai kewar juna.


                          ***

   safiyar ranan sun kammala da shirya komai, harda ummeetah dake zaune a nata dakin, ta shirya tsaf, shi take jira, don taji ana fadin 7:30 zasu tashi, harta breakfast an kawo mata tayi,,

   knowking kofan a kayi, ta mike cikin sanyi, sai data leka kaman yanda yace ta rika yi, sannan ta bude kofan, ganin yana waya yasa ba tace komai ba, ta juya don komawa inda take zaune,,

  kyam ya tsaya da waya bisa kunninsa, kaman wani dolo, zuciyarsa na faman ayyana masa,,

  ummeetah ce wannan, a rayuwamsa yana matukar son yaga mace tayi shiga irina na al~ada, sanye take cikin dikin wata flowing gwon da tayi mata matukar kyau, daga rigan har hannun rigan susha style na zamani, mai zaman kanshi,,

   cikin sabbin dinkunan da aka mata ne, ga colour din atamfar ta dauketa, tasha daurin maryam babangida, wanda yayi mata cass, sai tafkeken tufkan two steps din da aka mata ya sakko ta kasan wuyanta, wani viel ne mai tsada yafe bisa kafadarta na dama, kafarta sanye da takalman Zara masu dan tudu,,

  ya manta rabon da suhymah tayi mishi irin wannan dresing din, tunda suka koma can tafi gane ma kananun kaya, koda dama tun a nan din, su tafi gane mawa, duk da yasan traditional wear din sufi mata kyau, (ahh, wannan gaskiya, sunfi rufa ma jikin asiri).

   ta koma da tafiyarta najan hankali ta zauna, sai lokacin yayi dan firgit yana waskewa, tare da cigaba da sauraron matar nasa dake faman kwalla kiran,,

  hello sweetheart, hello hello!, ya numfasa yana kuma gyara wayar da kyau bisa kunninsa, da karisawa ciki, hannunsa rike da wasu papers ya zube, bisa table din dake gefen

Please Login or Register in order to submit comment