Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da za suyi suka futo, cikin farar jallabiya ya shirya sannan ya fuce zuwa masjid din dake kofar gidan nasu.

  ta jima bisa dadduman bayan ta idar, kafun ta shafa addu'an tana mikewa da nad'e dadduman, da sallama ya shigo yana tura kofan ya rufe, ya karisa shigowa da fadin,,

  kai kai kai, dama haka ake sanyi a rugar taku?, da sauri ta juyo bayan ta amsa mishi sallamar da yayi tana fadin,,

  sanyi kuma?, sai dai maybe don asuba ne,  ta karisa maganar dai dai sanda ya iso inda take gaban wardrobe tana sanya dadduman data ninke, kirjinshi kawai taji saman bayanta, yana runtse ido da fuzar da hucci daga bakinshi yake fadin,,

  Humaira don kina cikin hijjab ne, amma kinji hannu na kuwa, wardrobe din ta karisa rufewa, kai tsaye ya birkitota ta gabanshi, yana zirara hannunshi ta cikin hijjabinta, a rikice ta fiddo ido waje, saman kirjinta ya sauke hannun, bata samu damar cewa wani abuba, saboda sakon daya isar mata, a kunni yake rada mata,,

  kinji ko baby, da sanyi fa, muryan ta kuma narkar da ita, tana wani lumshe idanu, yanxun duka hannayenshi na cikin hijjabin, yayin da yasa hannu daya yana tallafo bayanta, wanda ya taimaka wajen hada ta da jikinshi, ya zaro dayan waje yana zare hijjabin dake jikinta, sanye take da yer vest wanda ya tsaya iya cinya, sai zanin dake jikinta na atamfa,,

   umm umm, ta fada tana runtse ido da rike hannunshi dake kokarin balle zanin data daura can kasan mara, tsam ya tsaya yana kare mata wani kallo, magana yake son yie amma ya kasa, kawai saiya daura hannunshi ta bayan kanta.

   dai dai inda tayin packing gashinta, ya dafe yana dan karkata kan nata, kafun ya hade bakinsu waje daya, a zabure ta sakar mishi hannunshi data rike, tana dafe kuncinsa, shi kuma ya samu damar balle zanin nata.

  hannunshi ya maido samar fuskanta, sai daya tabbatar sakonshi ya gama isar mata, sannan ya dauketa cak sukai kan gado, ( hmmm, lamarin yana bukatar sirri.) 
 


    A tare suka kammala shiryawa, kai tsaye suka wuce falon farko, inda suka samu Irfan zaune bisa dinning table yana karin kumallon da baba balarabu ta kammala jerawa a wajen, suma zama sukayi sukai joining dinshi.

  sai da suka kammala, sannan ummeetah ta gyara wajen, suka koma kitchen ita da Irfan suna creaming birthday cake din da za tayi.

  can Irfan ya fice wasanshi da yaran fulani da suke shigowa gidan, da farko mai gadi ya fara hanasu, sai ummeetah tace ya barsu suna shigowa.

  kullum ko haka za axo a cika mata falo, musamman idan gen a kunne yake, ana kallo hoton mutane a jikin bango, bama a tvn bango ba( funny).

   tana cikin daidaita kullun cake din cikin cake fan ya shigo, ta bayanta kawai taji an rungumeta, bata damu ba don tasan mijinta na kusa da ita, abin burinta ako da yaushe, ya runtse idanuwanshi yana kissing gefen kuncinta kafun yace,,

  baby fulani nah ina sonki fa sosai, soyayyar kie tamun mugun kamu,,

  yakai na aunty suhymah?, ta fada tana dago idanuwa, shima dagowa yayi yana kallonta, kafun yayi magana wayarshi ta fara ringing, ya fara cuku cukun cirowa a aljuhun yana kallonta,,

  my angel, ya fada yana kyasta mata ido daya da murmushi, da sauri ta kauda kanta tana wani hade rai, daraf ya haye bisa kitchen drower sanye da kananun kayan dake jikinshi, ya katse kiran yana maida mata da video call, sanda ta dauka sai da ya jefa mata kiss kafun yace,,

  hi sweatheart, ina missing dinki fa sosai, itama daga can dan dariya takeyi da fadin,,

  i miss yhu too my boo, ina Irfan d'ina?, da sauri yace,,

  mrs. sadeeq naki ke kadai, murmushi kawai tayi tana mamakin yanda yake wani walwala da farin ciki, kafun tace,,

  ouk, our son hope yana lafia?, yace,,

  lafia lau, sai dai yaron kie kawai kika sani, baki tambaya yer fulani nah ba?, sai lokacin ummeetah ta dan saki ranta daga batawan da tayi, koba komai ya nuna tana da muhimmaci itama, suhymah daga can tace,,

  oh sorry, na manta yaka samesu, hope maman baby na lafia?, ta karisa maganar cikin dakewan zuciya, sosai yaji dadi yana fadin,,

  lafia lau, gatanan tana faman tutturawa, ana tamun preparation ne na birthday dina, bari ku gaisa, ya karkata ma ummeetah wayar da fadin,,

  Humaira ku gaisa da auntyn kie, sai da hankalinta ya tashi sanda tayi karo da katon cikin ummeetah, ummeetah ta gaisheta, ta amsa mata ba yabo ba fallasa kafun ta daura da fadin,,

  thanks for taking good care of my husband, itama tana mamakin sanjawan aunty suhymahn, tayi dan murmushin yake da fadin,,

  never mind, it my job, daga haka suka kuma musayan murmushi, kafun ya janye wayar yana kiran mata Irfan dake fallo.

  da tsallensa ya kariso yana amsar wayar, tana ganinshi tasa wani murmushin farin ciki, suna cigaba da amsa wayar ya fice daga kitchen din, yanda ummeetah ta lura yanxun mahaifiyar nason danta, tayi murmushin jin dadi, koba komai shima yasan dadin uwa kamar kowani d'a.
  
  zamansa ya gyara da kyau bisa kitchen drower din tare da zuba mata idanu, kasa ta duka tana bude oven din dake hade da standard gas cooker, tare da saka cake din a ciki, ta maida ta rufe tana mikewa a natse, dai dai sanda yake fadin,,

  madam ina jinki, maimaita tambayar da kika mun daxu?,,

  na'am, ta fada da wani basarwa, murmushi kawai yayi kafun yace,,

  inkin manta bari na tuna miki, bata dubeshi ba ta cigaba creaming icing sugar data hada da butter, kallonta kawai yakeyi da burgewa, komai nata cikin natsuwa da tsafta take a'iwatarwa, ganin tayi mai shiru ya sashi kai hannu yana dago habarta, suka kalli juna, ido daya ya kashe mata kafun yace,,

  me yasa kike son hada matsayinki dana suhymah?, ya lumshe idanu yana budewa da fadin,,

  kima daina wannan mafarkin, bcos madam di nah ta dabance, yess saboda ita tana so nah, dole matsayinta kinga zai banbanta, kasa cewa komai ummeetah tayi tana hadiye wani kunci.

   hawaye ne kesan sakko mata saman fuska, da sauri ta kwace fuskanta, ta daure tare da cijewa tana maidasu don dole, shikam sai tsura mata idanu yayi yana son yaga reaction dinta,,

  baby ko kinji haushin abin dana fada ne, kina kishi ne?, da sauri ta dago kanta ga mamakinshi sai yaga tayi wata yer dariya, tana nunashi da spatula din da take auna madara cikin icing sugarn da tayi creaming, kafun tace,,

  Baffah nie ne zanyi kishin ka, a'ah ko kadan, bamma gama fahimtar mai kalmar kishin yake nufi ba, kawai dai ko dazu maganar ce taxo bakina na fada, amma bada wani meaning nayi ba, tana gama fadan haka ta cigaba da zuba madaran, sai data sanya iya quantityn da take bukata sannan ta cigaba da mixing dinshi.

  shikam be iya furta komai ba, wannan abin nata ya fara damunshi fa, haushi abin ke bashi in tana mishi irin wannan basarwan, so yake ya kamo bakin zaren, amma shegen bakin wayaunta baxai taba barinshi ya fahimce komai ba, tana murmushi ta dago da fadin,,

  na manta ban baka warm birthday wish dinka ba, kafun yayi wani magana ta dibo kullin icing din data gama creaming a spatula, tare da shafe mishi a gefen kuncisa, ta wani dan rankwafar da kanta tana fadin,,

  happy birthday to my swedie husband, wani murmushi ya saki yana kuma nanata sunan a zuciyarsa,,

  swedie husband, da sauri yaga ta dafe bakinta tana fadin,,

  oops, sorry ama jooooking, i mean my swedie uncle, wani kalan harara ya zabga mata yana fadin,,

  Humaira na zama abokin wasan kie ko?, da soyayyan nawa zaki rika wasa, kanta ta cigaba da girgixawa tana dariya, ganin ya lakuto icing din data shafa mai a fuskanshi yayo nata dashi, yasa ta fara matsawa da baya da baya.

  dirowa yayi yana shafa mata saman hanci, bai mishi ba ya kara dibo wanda ke cikin bowl din, itakam sai ta fara shirin guduwa tana dariya, center table din dake kafe a tsakiyar kitchen din suka fara zagayewa, abinki da mai tsohon ciki bata kai ko ina ba ya cafkota, tare da sakata cikin jikinshi suna wani dariyan a tare,,

  ummeetah wlhy nayi kewarki da yawa, sai na tuna rayuwan mu a US, kefa?, da sauri tace,

  nima haka, nayi kewarka sosai, ta fada tana wani kankameshi, me kuma ta tuna sai tayi saurin zare jikinta, hannunta ya ruko yana daga mata gira, da hannu take nuna mishi waje da fadin,,

   na manta baba balarabu na waje dasu iya ammu, plss karsu shigo……..., harara ya jefa mata daya hanata karisa maganar, yana fadin,,

  wacece kuma wata iya ammu?, sai data yamutsa fuska kafun tace,,

  matar Baffah lado ne da wasu kannin Affah, suna dan wanki ne a rijiyar gidan nan, ya dan tabe baki kafun yace,,

  tasu rijiyar fa?, tace,,

  wayyoo rafi ne kuma da dan tafiya, dai dai nan Irfan ya shigo da gudu dake fadin,,

  aunty ummee wani yaro yaxo yana ta fillanci kamar wajenki yaxo, daddynshi dake murmushi yace,,

  ho ho ho, Irfan mudai mun zama kuramen karfi da mai da yaji, da sauri yake fadin,,

  daddy ehman, duk yanda nayi musu english ko hausa basa bani amsa, kuma nie bana jin abin da su kace, dariya ummeetah keyi tana tambayarshi abin da yaron yace, ba bata lokaci ya maimaita mata, duk idanu suka zuba mata, ta wuce wajen oven da kamshin cake ke futowa tana dukawa da fadin,,

  ance ana neman mai gidan a waje, murmushi kawai yayi ya nufa hanyar futa da fadin,,

   hmmm, kedai babyn nan komai naki na daban ne, daga haka ya fice, ita kuma ta ciro cake din da harya so fara konewa, tana kuma nanata kalamanshi na karshe, Irfan ya iso suna cigaba da a'ikin cake din tare har suka kammala.



      ***
    Ya samu dattijan garin, harda liman daya dada tsufa, suka gagaisa, tare da mishi godiyar hidman da yake musu a garin, don har an kafa foundation din islamic school din da ummeetah tace, tana son a gina saboda karancin ilimin dake ga yen garin, harda wasu ma makotan su, sosai ya gama jin bukatunsu kafun suyi sallama.

  sai da yayi sallar azahar sannan ya shigo gidan, komai tsaf tsaf banda kamshi mai cike da salama ba abin dake tashi a gidan, harga Allah shi yasa yake son ummeetah, so mai tsanani, komai da yake so ta sani ta kuma san yanda zata gabatar dashi.

  ya karisa falo na biyu inda aka jera kayan abinci da snacks kala kala, kai ba kamar birthday cake dinnan, ya tafi da tunaninshi, cikin wani yellow material lace ta futo bubu gown yaji stones na alfarma, cikin dake jikinta ya zauna dass cikin rigar.

  tasha design fashion daurinta na zamani, gashinta na zube ta tsakiyar daurin dankwalin, yayin da fuskarta tasha make up sama sama, duk da kurajen da suka dan bata mata fuska bai hanata futowa rass ba, kamshi kawai ke tashi a jikinta.

  tazo ta zauna kusa dashi, sai kallon bakinta yakeyi da yaji light pink lip stick, Irfan ma tasha mishi gayu, yana makale kusa da daddynshi duk ya kosa a yanka cake suci naci, shima kam gogan abin da yake bukata kenan.

  cikin natsuwa suka gabatar da komai, basu tashi ba sai da ake kokarin kira sallar la'asar, shida Irfan suka wuce masallaci, yayin da ta kwashe kayan tana gyara wajen, kafun ta shiga ciki, sai lokacin idanunta suka kwakwallo don in bata manta ba, yau yace mata da yamma zasu koma, dole inta idar da sallah ta fara hada musu kayansu.
[14/08, 14:29] Dala Grp: 🕯🕯🕯
    *MATATACE*
          🕯🕯🕯
  

story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjj 

*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty Ummeetah any my Fa'ixation._

page 71~72

__________Tsaye take ranta duk a jagule ya shigo dakin, tana ta hada kaya cikin trolley bag dinshi, da dan mamaki ya zauna bakin gado yana fadin,,

  Humaira yadai, ko har kin gaji da nine?, da sauri ta dago, don harga Allah sai yanxun ta lura da gaske mutum ne ya shigo, duk da yayi sallama harta amsa, amma hankalinta nacan duniyar tunani, ta sauke ajiyar zuciya da fadin,,

  Baffah ba kace yau zaku koma ba?, sai da yayi shiru na wasu yen seconds, kafun yayi murmushi yana fadin,,

  madam wasa nake miki, naga da farko kamar ba aso zuwan nawa bane, shi yasa nayi ninyar guduwa yau, amma tunda an amsheni har nasha paw paw, kinga kuwa zama ya ganni, da sauri tasa tafukan hannunta tana rufe fuska, wani irin dadi ne ya diran mata, yace,,

  kinga maxa kie maida kayan nan, kie shirya mun dan futa kiyi tattaki name ciki, daga nan nima sai in dan bude ido da kallon gari, ba musu ta maida kayan, ta sauya kaya zuwa riga da zani na wata super english.

   ta saka blood red din hijjab, saboda kwalliyar dake jikin atamfa na blood red, tasha kyau suka futo shima ya sauya kaya zuwa manyan kaya, a gida suka bar Irfan dake wasa shi da yara.

   Tafiyansu suke hankali kwance, lokacin da suka keta wasu gonaki, suna tafe ummeetah na mishi bayanin wasu bishiyoyin dabe san ko na menene ba, don itama dan zaman da tayi yasa tasan gari sosai, sai yamma liss sannan suka dawo gida.



  ***
  Tunda suka dawo wani bacci bacci ke dibanta, tana yin sallar isha'i tabi lafiyar gado, lokacin daya shigo baccin nata yayi nisa, don haka falo ya koma yana cigaba da yen dube dubenshi a laptop.

  sai misalin 10pm ya tattara komai ya ije, tare da mikewa ya shiga dakin, da sallama ya tura kofan dai dai sanda take bude idanuta tar a kanshi daga kwancen da take, yayi dan murmushi yana fadin,,

  Humaira, shiru kawai yaga tayi mai tana faman wurwurga ido, ya kariso yana zama kusa da ita cike, cike da dan damuwa yake sanya hannunshi saman wuyanta da yake zafi radau,,

  baki jin dadi ne?, ya fada maganar yana kallonta da take kokarin mikewa, sai lokacin tayi dan murmushi tana girgixa kanta da fadin,,

  a'ah, bayi zanje ina jin fitsari, da sauri ya ruko hannunta yana fadin,,

  ouk muje in taimaka mi……, bai samu daman karisa abin daxai fada ba, saboda wani damka da tayi mishi, ta ruko damtsen hannunshi sosai tana runtse idanuwa da cije baki, a rude yake fadin,,

  Humaira lafia?, kuka ta sanya tana fadin,,

  wayyoo Baffah ciki nah, marata wlhy zai cire, ka taimak……, sai kuma ta kasa karisa maganar tana kuma runtse ido da cije baki, kafun yayi wani magana tace,,

  plss Bahba balarabu ka kira mun ita, yace,,

  ouk to cikani in mike, daker ya iya banbareta daga jikinshi ya futa don kiran bahba balarabu.

  kusan a tare suka dawo dakin, har lokacin ummeetah na kwance saman gadon tana faman juyi da mimmike kafafuwa tana matse yen yatsunta, ta mika mata hannu da wani azababban ciwon mara da yake taso tana fadin,,

  Bahba cikina zai fashe, itama ruko ummeetah tayi tana mata sannu da fadin,,

yie hakuri baxai fashe ba, shikam a rude yake fadin,,

  Bahba haihuwan ne, ko zamu tafi asibiti ne?, tace,,

  a'ah, d'annan bar maganar wani asibiti dare kuma yayi, a nan dinma in sha Allahu zata haihu lafia, yanxun kayan haihuwan nema abinji, ta mike tsaye da fadin,,

  ke shatu daina hada kafafuwan nan, bari inje in dauko dan abin dana tanada, daga haka ta fice daga dakin, kanshi ya dafe, da wani jin haushin kanshi.

   tabbas babu abin daya siya mata na kayan haihuwa, dama gobe ne yayi ninyar su shiga kasu…, tunaninshi ya katse lokacin da bahba balarabu ta dawo dakin da wasu zannuwa biyu, sai lokacin ya tuna da wani abu yana fadin,,

  bahba bari na dauko wasu kaya da maami ta bani in taho dasu, maybe baxa a rasa abin bukata ba a ciki, tace,,

  yawwa do Allah maza ka dauko, yanxun haka kayan haihuwan nema ta bada, bai tsaya wata wata ba ya fice can waje, garin sauri har yana manta key din motar a nan falo.

  kasan tyles ta shimfida mata zannuwa masu kauri guda biyu, sannan ta taimaka mata daker ta sauko kasa, tana kwanciya a wajen wani sabon abu ya dura mata, ta runtse idanuwa tana kankame hannuwa da fadin,,

  innalilahi wa'inna ilaihir raji'uuuuuun, dai dai sanda kan baby ke sawo kai waje, bahba balarabu ta yashe baki tana fadin,,

  Alhamdulillahi, cikn hikima tana sanya hannu sankaceciyar babyn ta futo subul, kuma fadada murmushinta tayi, yayin da ummeetah ke sauke wasu tagwayen nishi masu karfi, tana komawa da baya bisa pillown data tada kai dashi ta kwanta, lokaci daya kuma taji kamar an cire mata ciwon.
 
  shikam ko da yaje babu key hannunshi, da hanzari ya kuma dawowa ya dauka sannan ya fice, trolley ne dan madaidaci ya dauko, cak ya tsaya, tun daga kofan falonsu na biyu kake jiyo sautin kukanta da take tsandarawa.

  yama kasa cewa komai, shin mafarki yakeyi ko mene, kukan dai kamar jaririya yake jie, kar dai ace har ummeetah ta haihu, da sauri ya karisa shiga ciki dauke da kayan a hannunshi.

  tuni ya samu har bahba balarabu ta yake cibiya, tare da jawo mahaifar waje, ummeetah na kwace da zufan da ya gama rufe fuskanta, itakam bahba sai goge jaririyan take dake lullube cikin zani, tana faman ma mutane rigima, akwatin dake hannunshi ya dire yana fadin,,

  Bahba har anyi haihuwan?, da murmushi take fadin,,

  Allah ya kawo mata da sauki d'annan, ga d'iya mace an samu, Allah ya raya, da sauri ya amshe babyn har hannunshi na rawa, ya rungumeta a kirjinshi yana kallon sabuwar jaririyan da yanxun taxo duniya,,

  barakalla, masha Allah, shine abin da yake faman nanatawa a zuciyarsa, don yarinyan ko a girman jiki ba'a cewa komai, ya karisa inda ummeetah ke kwance dishi dishi take satan kallonsu shida yarinyan, suna matsowa gareta tayi saurin damtse idanuwanta, kusa da ita ya dan duka yana shafa kanta da fadin,,

  sannun ummeetah, Allah ya albarkaci rayuwan kie, a zuciyarta ta amsa, amma a fili saita kuma damtse idon, saboda wani kunyar jaririyar da taji tana yie, shikam duk tunaninshi zafin haihuwan ne ke dibarta, a hankali ya duka yana kissing saman kanta daya gama jikewa da zufa, kafun ya dago yana kuma jera mata sannu.

   Bahba balarabu dai tana can ta fiddo da kaya waje, sai yashe baki takeyi, tana yaba ma maami dasa albarka, babyn ta amsa ta kuma gogeta da olive oil mai kyau da ta gani cikin akwatin, kafun ta nadeta a zannuwa biyu, ta kuma mika mishi ita, suka futa falo yana faman jijjiga manne da ita a kirji.

  gareta bahba balarabu ta koma, sai data gyarata tsaf, sannan ta taimaka mata ta koma daga dan saman gado ta kishingida, nan ma bahba ta gyara wajen tsaf komai ya daidaita.

  ruwa mai kyau ta dibo na zafi, ta zuba mishi dettol sai kamsh yakeyi, kafun ta amso yarinyan taxo ta wanketa tass.




   ***
  Shidai sadeeq sai blushing yakeyi, a daren nan duk wanda zai iya sanar mawa sai daya kira ya sanar musu.

  maami ma ta rufe wayarta, munat kuwa don murna da dadi ta kasa bari goben yayi, sai data kira wayar Abba lokacin mummyn su na dakin, shi kuma ya shiga bayi, harara ta zabga ma wayan tana jawowa da fadin,,

  ko waye da uwan daren nan oho, ganin numbern my daughter ta kuma san ko wacece, ya sanyata dan tabe baki da fadin,,

  ko lafia?, da sauri ta daga wayar, jin muryan munat da doki ne ya sanyata tsayawa tayi sansaransan, itakam daga can bangaren take cigaba da fadin,,

  Abba albishirinka, ka kara zama wani grand papa din, plss ka fada ma maami itama ta……, a tsawace ta tsaida ita da fadin,,

  ke munat natsu, meye haka kin kira kina faman ma mutane ihu, lafian kie kuwa?, jin muryan mummy ne ya sanya gabanta faduwa, amma don murna sai ta cigaba da murmushi tana fadin,,

  wayyoo mummy murna fa nakeyi, na kara zama mummy munat, harara ta zabga kafun tace,,

  wacece kuma ta haihu?, da dariyanta take fadin,,

  ummeetah mana, dadadada dassssss, shine sautin da kirjin mummy ya bada, lokaci daya zufa ya rufeta tana fadin,,

  me ta haifa ne?, cikin doki munat tace,,

  namiji, sai da dukkan jikinta ya mutu a zaune, munat na sauya maganar da fadin,,

  oh sorry mummy, baby girl ta haifa, ajiyar zuciya ta sauke mai karfi tana dafe kirjinta da fadin,,

  Alhamdulillah, munat dake can jikinta yayi sanyi tana fadin,,

  mummy lafia?  wani dogon tsaki taja tana fadin,,

  ban saniba, wacce bata san ciwon kanta ba, tunda kanwar yagana ta haihu a'ikya rika irin wannan murnan, marairaice murya tayi tana fadin,,

  eyah mummy kisan yaya sadeeq dan uwa nah ne, dole in tayashi farin ciki, plsss kie fada ma maami tayi yer jikalle, sai gobe ina nan shigowa gidan, plss mummy kie fada mata fa, tana wani daddaga hanci tace,,

  naji, daga haka ta yanke kiran, dai dai sanda Abba ya futo daga bayin sanye da jallabiya, yana fadin,,

  yagana lafia dai? ke dawa cikin daren nan kike ta masifa, da dan borin kunya take fadin,,

  oh, wlhy munat ce ta kirani sai hauka take, wai duk murnan matar yayansu ta haihu ne, da fara'anshi yake fadin,,

  masha Allah, yer fillon tashi ne ta sauka, ban wayar nan in mishi congrat, ba musu ta mika mishi wayar tana fadin,,

  Abban su naga kaima kana wani farin ciki ne, kamar ba fushi kakeyi dashi ba, dan murmushi yayi kafun yace,,

  yagana kenan, ko can da nayi fushi ne saboda boye mana lamarin auran da yayi, amma zuwa yanxun bani da hujjan dazan cigaba da fushi dashi, tunda na gama tabbatarwa ita din matar shine na sunna, sosai ta rika mamakin yanda kowa ke farin ciki.

  ko da itama tayi farin ciki, tabbas lokaci yayi da zata ma daughter magana su mike tsaye suyi waje da yarinyan can, tun kan tayi haihuwa na biyu ta haifo d'a namiji, ta rika jin dan dama dama da ba namiji ummeetah ta haifa ba.
  



    ***
  Ruwa itama bahba ta sanya mata ta gasa jikinta, sannan ta futo ta shirya, sanyi taji tana jie, don haka tace ta sanya safa a kafarta sai ta saka hijjabi, haka kuwa akayi ta lafe bisa gado cikin blanket, har sanda bahba ta tasata da zazzafar kunun kanwan data dama mata.

  gyara mata danki tsaf ta kuma yie, sai kamshi mai jego kawai ke tashi, bayi ta koma ta wanke shi tare da kwasa zannuwan da suka baci, tayi bayin dakinta dasu don ta wanke.

  a falo ta wuce shi ya tasa yarinya a gaba sai kallo yakeyi, yana amsa wayar da sukeyi da Abba, gefenshi kuma zam zam ne da zuma, harya mata huduba, bahba balarabu tayi murmushi tana karisa futa da fadin,,

  yen yen zamani kenan, mikewa yayi tsam bayan sun kare wayar ya wuce ciki, kusa da ita ya zauna, tana jinsu ta kuma wani narkewa da baccin karya, da murmushin farin ciki kawai yake kare ma fuskanta kallo, kafun ya kira sunanta da fadin,,

  Humaira plss kie bude idanunki, nasan ba bacci kike yiba, shiru tayi mishi, ya ruko tafin hannunta yana fadin,,

  don Allah kie bude idanunki, kie tashi kie kalli farin cikin kie a hannunki, tunda fa kika haifeta baku hada ido ba, ga mamakinshi sai yaga ta kuma gyara kwanciya, dan shiru yayi kafun ya rike kanshi yana fadin,,

  ya salam, Humaira kie taimaka mun kaina ciwo, a rikice ta bude idanuwa, tana yunkurowa da dafe wajen tana fadin,,

  ina ne, nan?, meya sa……, kit maganar nata ya tsaya, sanda yake mata wani murmushi da kashe mata idonshi daya, da sauri ta koma zata kwanta, ya ruko damtsen hannunta da fadin,,

  kin isa, amshe tah, marairaice fuska tayi tana fadin,,

  Baffah don Allah kayi hakuri, nidai baxan iya ba, ta karisa maganar tana wani daddauke kai daga kallon yarinyan, galala ya tsaya yana kallonta, kafun ya daura mata yarinyan kan jikinta yana dan nazarinta, ture yarinyan ta shiga kokarin yie, ya hade fuska a tamke

Please Login or Register in order to submit comment