Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har naji inajin tausayinta wlhy, fadeela tace,,

   kai aunty ba wani tausayi, wanda yayi mai kyau a'i ya sani, tace,,

   a'a dole zan kara ma suhymah magana don ta gyara, wannan karon dai shaakirah batai kokarin hanata ba, amman tasan wacece makwabciyar nata, daga nan suka sauya hiran tasu da wata maganar.

   Bangaren ummeetah kuwa yau ta bude ido, don sosai suka ziyarci wajaje kala kala, harda su beach, sosai tayi enjoying kafun yamma yayi su komo gida, har lokacin matar gidan bata dawo ba.

           
     

                        ***

     Tsaye yake jikin wardrobe dinta dake dakin, fuskan nan ba wani walwala, yana takaicin yanda har kwanakin weekend da sassafe take sa kafa tabar gidan, yau don rainin wayauma, tashi kawai yayi yaga har tayi ficewanta, ya danja tsaki da kara kai idanunsa kan kofan bayin daya jima da daina jin alamun saukan ruwa,,

    wanka ta kammala tun daxu, daure da towel take dabai fie iya cinya ba, a hankali take bude kafan tana lekowa, saita koma tana dan tsaki da fadin,,

   wai shi Baffan nan bazai futa bane, take korafi a zucci da turo baki, kuma gyara tsayuwanshi yayi, yana dada harde hannayensa da kyau bisa kirji, can dai da taga bashi da ninyar futa, futowa tayi tana faman jajjan towel kasa, da rufe yen santala santalan cinyoyinta,,

   kallo daya yayi mata ya basar da kauda idanunsa, ganin haka yasa ta nufi gaban mirror, kayan shafanta ta kwasa ta kara komawa bayin, sai data gama sannan ta futo, ta maida kayan inda suke, tare da tsayawa dan nesa dashi tana fadin,,

   Baffah plss, zan dauki kaya cikin wardrobe dina, sai wani hada fuska yakeyi, kusan 2minutes kafun ya juya yana bude wardrobe din, ya dan jima kafun ya juyo yana mika mata under wears, zaro ido tayi da dan mamaki, a kunyace ta amsa tana runtse ido kaman tayi kuka, kuma juyawa yayi ya binciko mata wata yer straight armless gown, bata fuska tayi sanda shima ta amsa da fadin,,

  Ba...affah nie wannan rigan yayi mun karama, yanda ta kira sunanne ya sashi wani lumshe ido, ya budesu a kanta da fadin,,

   nie kuma shi nace ki sanya, rigama ta sanya da shagwaba tana fadin,,

  nie nie wannan, hannunsa fa karamine jikina duk futowa zaiyi, dan shiru yayi, kafun ya wani basar da fadin,,

    ohhh, to ko dai kazanta kika bari a hannun, baki son in gani, a 80 ta zaro ido waje, ya daga mata gira sama alamar yes, juyawa tayi cikin bayin da sauri tana bamo kofan, yasa dan murmushi yana zama da fadin,,

  inkinsan wata baki san wata ba, can sai gata ta futo, tsaf ta kammala shiryawa sai wani cin magani takeyi, ta kariso inda yake zaune bisa mirror stool kafa daya kan daya, gashinta data tufke ta fara warwarewa da jawo gwangwanin wani hair spary dake bisa mirror, da gayya ta daga hannayenta duka biyun tana feshe gashinta dashi,,

  idanunsa na kallon kasa yake wani murmushin, amman ta gefen ido yake kallon duk abin da takeyi, wato so take ta nuna mishi babu kazantar daya kira mata, tsam ya mike da ruko kafadunta, yana fadin,,

   mu gani da kyau, a'i ta haka bana kallon komai, da sauri kuma ta make hannayenta, da kokarin kwacewa, ya rukota da kyau har jikinsu na gogan na juna, ta bayanta ya sakalo hannunsa daya, yayin da tai saurin daura nata hannun saman kafadarsa, dayan hannun yasa yana amsar spray din dake dayar hannunta, cikin ido suke kallon juna kafun tayi saurin kauda nata gefe, a hankali ya rankwafo da kanshi dai dai kunninta, da wani irin murya yake rada mata,

    Humaira nah, ke mai tsaftace a'i, yhu so clean baby, yanda yayi maganar ne ya sata wani irin lumshe idanu, yayin da kirjinta ke bugawa da sauri da sauri, jin hakanne ya sashi dagowa yana sassauta rikon daya mata, a fuska yake hura mata iska, ta bude idanu tar a kanshi, gira ya daga mata sama da fadin,,

   enmmata ya dai, bata fuska kuma tayi tana kokari kwacewa, ya saketa kai tsaye da fadin,,

   waike ba'a iya wata yer harkan azziki da kene, sai ki fara wani bata rai, taji abin da yace, amma saita wani basar kaman bata jiba tana kokarin barin wajen, hannunta ya ruko da fadin,,

    zoki zauna in gyara miki gashin, ba musu ta zauna bisa mirror stool din da fuskantar cikin madubin, cikin natsuwa ya soma mata oiling gashin, mamaki takeyi tana kallan yanda yake bin komai daki daki, ko ita sai haka, ta wani lumshe ido sanda yake bata wani hair massage, ta cikin mirror yake kallonta kafun ta juyo muryansa cikin kunninta yana fadin,

   haka nake son kie rika gyara na zara'u in sha Allah, da sauri ta bude idanunta, da fadin,,

   wace zara'u?kai tsaye yake fadin,,

   ye'ta ce, da murmushi sosai take fadin,,

   ohh yarinyan da auntyn suhymah zata haifa, a'i iri daya da sunan Innatah ne ko Baffah?shima da murmushin yake fadin,,

  eh, amma ba yarinyan suhymah bane, yai dan shiru yana nazarin fuskanta da fadin,,

   yarinyan da zaki haifa ne, dif ta dauke dan murmushin dake kan fuskan, kowa da abin da yake sakawa, kafun ya sanja zancan da fadin,,

   gaskiya zamu zo mu bude saloon ne, irin wanna spackling, ya karisa maganar da kama mata gashin dake faman kyallawa da ribbon, yana cigaba da fadin,,

   ko baki so, insa a bude miki wata huge beauty saloon, waya kawai zanyi a a'iwatar ranki shi dade, dariya yake bata inya kirata da wannan sunan, bata san sanda tayi wani dan far da ido ba, tana fadin,,

   nikam bana ra'ayin saloon, ta karisa maganar tana dagowa da kallonshi, gaba daya babu wani annuri daya rage a fuskanshi, duk sai taji kuma ba dadi, yana kammala goge mata gefen gashinta, ta mike da juyowa sosai tana fadin,,

  amman inkai kana so, to nima ina so, ba tare daya ce mata komai ba ya wuce bayin dake dakin, itama ta dafa mishi baya, ganinta kawai yayi a bayanshi, suka sakar ma juna murmushi, sanda ta taimaka mai ya wanke hannunsa, tare suka futo, yana fadin,,

  nie a suwa zaki so abin da nake so?tana murmushi da fadin,,

   yhu as my sweet uncle, maganar taxo mishi a bazata, hannayensa yasa yana tallafo fuskanta sosai, kafun ya marairaice da fadin,,

   Humaira plss……, bana son na kasance sweet uncle dinki, na fusan na kasance matsayin ur sweet husband, ya karisa maganar da kokarin hadata da jikinsa, da sauri ta kwace kanta tana baya baya, da wani kalan shagawa take fadin,,

   no yhu are my sweet uncle, not my sweet husband, shi kuma ya biye mata da fadin,

  a'a, am ur sweet husband, not ur sweet uncle, kokarin kamota yakeyi sanda suka maida lamarin wasa suna zagaye dakin, dariya sosai takeyi, tsayawa yayi kawai yana zuba mata idanu tana faman tsalle kan gado cike da annashuwa,,

   sosai dariya ke mata kyau a fuska, ganin yana kara kawo hannune kaman zai kamata, ya sanya ta dira tana nufa kofa, shima bayanta ya biyo, da sauri ta rigashi futa…………, cak ta tsaya da dariyan da takeyi, sakamakon karo da su kayi ta turo kofan shigowa da fadin,,

    sweetheart!shima dake shirin futowa ya tsaya cak, kafun yaja da baya yana komawa ciki.



      *_za kumun uziri makarantar littafin matatace, yen kwanakin nan ina busy, gashi mun koma makaranta, wlhy abubbuwan da yawa, in sha Allah xaku rika jina, maybe inna turo yau baxan turo gobe ba, har Allah yasa littafin ya kammalu, Allah ya datar damu alkhairi…………taku Haleematu sa'adiya._*


comment
share
vote

*matatace 2019*
Na meemartjj
[14/08, 14:29] Dala Grp: 🕯🕯🕯
    *MATATACE*
          🕯🕯🕯

story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjj 

*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty Ummeetah any my Fa'ixation._

page 43~44

_____________Da wani kallon rainin wayau take kare ma ummeetah kallo, tana cigaba da karisowa a hankali, tuni ummeetah ta soma tunanin amsar da zata bata, inta tambayeta, sai da aka zabga mata harara kafun tace,,

   ke dawa kuke wannan wasar banxan?, tayi maganar tana faman yatsina fuska, kafun ummeetah tace wani abu, ta wuce hanyar bedroom dinsu tafe bisa takalmanta masu tsinin gaske, kamar ba zata kara magana, sai kafun ta juyo tana fadin,,

   bana son wasan banxa a cikin gidana don haka kikiyaye, next time na dawo na kara ganin hakan na faruwa, ranki zai baci, daga haka ta shige daki abinta, ajiyar zuciya ummeetah ta saki, dai dai sanda ya karisa futowa shima, gefenta yaja ya tsaya yana kokarin ruko hannunta, da sauri ta janye jikinta, cikin sanyi ta juya ta koma daki, da ido ya rakata da kallo, kafun ya juyo yana sauke wata ajiyar zuciya, tare da wucewa dakin nasu.


      tsaye ya sameta gaban mirror, tana kare ma cikin dake jikinta daya fara futowa kallo, sai faman blushing takeyi tare da shafawa da hannu biyu, salamarsa ya sanya ta juyowa tana dada fadada murmushin dake kan fuskarta,,

   sweetheart, babyn mu yana kicking sosai fa, ta karisa maganar da nufowa inda yake, hannunsa ta kamo tana daurawa saman cikin, yanda ya lura tana matukar son wannan cikin, ba kaman lokacin na Irfan ba, ta dafe kafadarsa da fadin,,

   sweetheart ina son babyn nan da yawa, ina jie kamar child dina na farko zan haifa, kaima kana so ko?da dan murmushi yake fadin,,

  ehmana, sai da ba kamar yanda na so na Irfan ba, suhymah har abada baxan taba mance ranar da Irfan yaxo duniya ba, that's the most happies day of my life, murmushin dake kan fuskantane ya dan dauke, ta sakeshi tana nufa gado da fadin,,

   Boo dama kana cikin gidan nan na shigo?, zama yayi bisa wata sofa chair dake gefe yana fadin,,

   eh, meya faru?ta zauna bisa gadon da dan mamaki tana fadin,,

  am suprise, ya akayi ni ban ganka ba?, ya dan yatsina fuska yana daura kafa daya kan daya da fadin,,

   dama ya za'ayi ki ganni, nima sanda zaki futa a'i ba ganinki nayi ba, shiru tayi da barin zancan, don bata son ya fara mata korafinshi na tsiya, a cewarta.


                          £££

  Da murnanta yau ta tafi school, kowa ya ganta yasan tana farin ciki, hibbat kenan an kara zama enmmata lokacin da suke ajin karshe a sakandare, jakarta fal cimgum, da take rabama kawayenta,,

  ss3art suka nufa ita da wasu friends nata, lokacin break ne don haka dalibai da yawa suna waje,,

   hey guys, jidda phakee ta fada da suke zaune bisa desk sunyi group ana faman surutu, sadiya deeni na karawa da fadin,,

   khadeeja ibrahim ya dai, naga kina ta wani blushing ne?, ta zaro ido waje tana dibo cimgum da fadin,,

   finally aunty nah zatai aure, jidda ta amashe cimgum din da fadin,,

   wow, good news, Allah sanya alkhairi, ummalkhari idris na fadin,,

   Allah sarki auntyn ummeetah ko?hibbat ta daga gira da fadin,,

  yawwa yer uwa ashe dai baki manta ba itafa, yer harara ummalkhari ta jefama hibbat da fadin,,

   tayaya zan manta, bayan wajen zaman mu daya a islamiya, kullum kuma taxo sai tayi maganar auntynsu kafun a tashi, i really miss that nice gal, ta fada da wani marairaicewa irin na yeyen zamani, hibbat tace,,

  me too sister, naso ace tana nan zamuje sunan baby Na'ima, da sauri ummalkhari ke fadin,,

   wow, hakanefa kinsan tare mu kaje bikin, kai ranar anyi wulakanci, gasu Namcy dai har an sauka, ummeetah tayi missing this tim……...,,

   tswww, shine abin da munirat ta saki tana mikewa, daga dandalin data hada a class din nasu da fadin,,

   malamai dalla karku ishemu da maganar wata da bamu san taba, so change the topic, jidda phakee na fadin,,

   yess, tunda mu bamu santa ba, a sanja hiran kawai, tsaki ummalkhari tayi, dai dai sanda wata mate dinsu ta shigo class din tana fadin,,

   khadeeja ibrahim ance kina raba engagement cimgum na yayarki, kafun hibbat tayi magana karaf munirat tace,,

   Asiya kabeer gashi, yaya tace, yes nie munirat, ta karisa maganar da mika ma yarinyan nata cimgum din dake cikin nata jakar, yer tsaki hibbat tayi da zabga mata harara tana fadin,,

  yess she is ur sister, and she is my sweet mum, daga haka tasa kai ta fuce daga class din kawayenta na dafa mata baya, tsaki munirat tayi da kwaikwayon muryan hibbat tana fadin,,

    yeyenyeyen, tswww, sai kuma taja tsaki, tana komawa wajen kawayenta.


                       ***

      zaune take cikin mota tana driving, a hanyarta na zuwa wajan a'iki, tunda ta futo take tafe tana duba wayarta, rana ne mai matukar muhimmaci a wajenta, da bata mantawa, ranar data mallaki mijinta abin sonta, tsawon shekarun da sukai aure da juna, duk rana mai kama ta yau shike fara wishing dinta,,

  Happy anniversary, amma wannan karon ta rasa dalilin da yasa bai tura mata ba, harta isa office bata daina duba wayarta ba, ko zata ga text dinsa, sharewa tayi ko zuwa can ajima zai turo mata, sai dai shiru, dole dai rai bai soba ta fara tura mai, don takan so ya fara wishing dinta, saboda hakan na nuna mata cewa tana da muhimmaci sosai a wajensa.

   time din da sakon ya shigo shima yana office a'iki sun masa yawa, harga Allah sai daya ga sakon sannan ya tuna dame yayi, tabbas besan dalilin daya sa ya manta ba wannan shekaran, a daddafe ya bata reply yana komawa kan a'ikinsa.

                        ***

  yau da wani nishadi ya dawo gidan, yasan dai yau ranane da matarsa take girmamawa fiye da ranar haihuwanta, maybe ya dawo ya tarda ta dawo gida, sai dai wayam ya dawo yaga bata dawon ba, daga kitchen ta futo sanye cikin wata doguwar rigan atamfa, sai karamin viel din dake yane a kanta ta yafa,,

   Baffah sannu da zuwa, ta fada sanda take amsar briefcase din dake hannunsa, da dan murmushi yake fadin,,

   yawwa sannu yer albarka, daga haka ta wuce gaba yana bayanta, har dakin nasu,

   ta dire mai briefcase din zata futa, yayin daya zauna bakin gado yana dan tsaki, da fara kokarin cire neck tied dake wuyansa, ya kalleta da fadin,,

   plss Humaira a hada mun ruwan wanka,,

   toh, ta fada da juyawa zuwa bayin, na wasu yen mintoci kafun ta futo da sauri tabar dakin, yana lura da ita amman saiya tabe baki yana basarwa, ita dai tayi ficewaerata tana komawa kitchen da cigaba da a'ikinta.

    kusan 30minutes kafun taji yana kuma kwalla mata kira, ta hade fuska da korafi tana fadin,,

   kai, kai nifa……nifa, sai kuma ta wuce tana amsawa da,,

   na'am gani nan, da sallamarta ta shiga, tana faman hada fuska, kallo daya tayi mai ta kauda fuska, sanye yake cikin wata light blue bathrobe yake, tsaye gaban mirror, taja ta tsaya daga gefe yace,,

    ba tsayawa za kiyi ba, kaya zaki bani cikin wardrobe, ba musu ta soma duba mai, cikin kananan kaya ta ciro mai wasu, tare da ijesu need bisa gado, tana kokarin barib dakin ya juyo yana fadin,,

    wai saurin na meye haka, tsayawa tayi tana runtse ido daga bakin kofan da take, da dan yatsa yake nuna mata gefen gado yana fadin,,

   oya koma kie zauna, har saina gama shiryawa, zaro ido tayi waje  yayi juyawarsa, har kusan minti biyu tana nan tsaye,,

  baki jiba, ya fada murya a dake  jin yanda yayi maganar ne ya sanya ta samu waje ba shiri ta zauna, sai daya gama abin da yakeyi gaban dresing mirrorn sannan ya shiga takowo zuwa inda take, sosai ta takarkare kai a kasa tana wasa da yen yatsunta, kusa da ita ya zauna jikinsu na gogan na juna, tsam ta dan matsa nesa dashi,

   da mamaki yake binta da kallon nazari, baya son yanxun take irin wadannan abubbuwan, yana son su saba kodan ya huta da wulakancin da suhymah ke mishi, ya hade fuska da fadin,,

   meye hakan yake nufi?kirjinta na dukan uku take girgixa kai da fadin,,

   bakomai, yace,,

    bakomai, to meyasa zaki matsa?ido suka hada da juna tayi saurin kauda nata, murya sanyi sanyi take fadin,,

    kawai naga kamar bai dac...,,

    get out, da sauri ta dago kanta da kyau, yayi kokari wajen kakalo mata murmushi yana fadin,,

    jeki cigaba da a'ikinki, itama dan murmushin tayi tana mikewa ta fuce, kitchen ta koma, duk sai taji bata a'ikin da natsuwa, tana jie kamar tayi wani abu dabai dace ba.

   

     Barayinshi kuwa rai a dagule ya ya kammala shiryawa, falo ya futo ko abincin dake dinning din bai kalla ba, ya soma kokarin bude fridge tare da jawo drink na roba, ya balle murfin yana jawo wani glass cup tare da zubawa,,

   rike da cup din yake sauka stairs din dake dinning arean, yana samun waje cikin daya daga cikin kujerun dake falon ya zauna, dai dai sanda wayarsa ke ringing, bisa side table din dake jikin kujeran ya ije drink din, yana kokarin zaro wayar daga aljihu, wani yer fake smile yasa sanda yake daga wayar da fadin,,

    ango mijin amarya, daga can site din Abdullah ke fadin,,

   yess, ka fadi ka kara, nine nan Abdullahi ango mijin maimunatu, ya dan fiddo ido waje kafun yace,,

   naga sai wani farin ciki kakeyi, kamar wanda zaiyi auran farko, shima daga can bangaren dan tabe baki yayi da fara'a yana fadin,,

    of course, kamar yafi hakan ma zance, munat tace mun an kusa samun karuwa a nan, uwar gidance ko amarya?, wani dan yatsina yayi da murmushi kadan akan fuskarsa yake fadin,,

   uwar gida mana, da sauri Abdullah ke fadin,,

   wow congrats my aboki, gaskiya naji dadin wannan labarin, sai daya kai karshe ma ya gane nashi fahimtar, dan runtse ido yayi yana budewa da dan dariya yake fadin,,

  kaga sorry, ka rikatar dani ne, amaryan zan cema, shiru yayi daga can bangaren, kafun yayi yer tsaki da fadin,,

   Allah sadeeq ina fada maka ka farka fa, ya kamata ka samo bakin zaren da zaka warware al-amura, ya kake zaune har yanxun a duhu ne, ya dan runtse ido da budewa yana fadin,,

  yhu know my suhymah, baxan jure ganin wani abin ya sameta ba, zuciya na zata raunana, jinjina kai yayi kafun yace,,

  ouk har yanxu baka futo daga bakar sakan da aka sanya kaba kenan, da dan mamaki yake fadin,,

   as in how?yace,,

   manta kawai, amma ina baka shawara ka dan kara rike addu'oin nan, ka gane sosai nake baka shawaran nan da gaske, mutanan kafa wajena suka dawo, kawunnan ummeetah har office, ina fada maka rashin mutuncin be kare a nan ba, sai da suka hada harda office din Abba sunkai karanka, nadai san mai na fada mai daya nemeni, saika nemo muku maslaha tun abubbuwa basu jagule ba, runtse idanu yayi yana nazarin kalaman Abdullah, kafun suyi sallama kowa na ije wayar.

   toh ta inama zai fara, zuwa yanxun so yake su fahimce juna sosai da ummeetah, yayi dan tsaki yana kurban drink din dake hannunsa, da kuma ayyana,,

   tabbas zanyi amfanin da shawaran Abdullah, to amma yarinyan can ta ina zan bullo mata ……, dai dai nan yaji wayarsa na kuma ringing, da dan tsaki yake dago wayar, sai kuma yayi murmushi ganin sunan,,

   daughter deeja dake yawo saman screen din, kai tsaye ya amsa kiran da sallamarsa, daga can bangaren ta amsa tana gaisheshi cikin girmamawa, amsa mata yake da fara'a yana fadin,,

   enmmatan maami, ya mutan gidan suke, ina maami naki take?,,

   duk suna lfylau, maami kuma na gida, ta fada da daurawa da fadin,,

   uncle sadeeq, plss dama ina son ka hadani da ummeetah ne za muyi magana, ya mike yana fadin,,

   ouk bani wasu yen minutes in bata wayar, amma kina inane nake jin surutu haka? da sauri take fadin,,

    gidan wata friend dinmu ce data haihu, yace,,

   ouk Allah shi raya, ya karisa maganar dai dai sanda yake karisawa bayan ummeetah data bada hankali tana blanding kayan miya, hannunta kawai taga ya zaro dake jikin handle din blander, da sauri ta waigo a dan firgice tana kallonsa, baice komai ba ya damka mata wayar a hannunta, haka kuma fuska ba walwala ya juya yayi hanyar ficewa abinsa,,

  ajiyar zuciya ta saki tana kallon cikin wayar, murmushine ya subuce mata, da doki ta daga wayar suna gaisawa, tare da juyawa sosai tana kashe blander dake cigaba da a'iki, dai dai sanda take zaro ido da fadin,,

  lah Na'ima ce harta haihu da gaske?, sai kuma tayi dan shiru kafun tace,,

   bani ita, bani ita muyi magana, kusan minti daya kafun ta fara fadin,,

   lallai Na'ima barka da sauka, sai kuma ta dafe bakinta da murmushi tana fadin,,

   na manta maman baby zance uwar gidan sultan, kuma yin shiru tayi kufun tace,,

    ummm, yer rainin sense dama wata ba keba, duka duka yaushe akai bikin, kedai Allah ya raya mana babyn mu, dama kince zaki auran nan dai kiji me ake jie, to gashinan kinyi har Allah ya kawo rabo mai amfani, ta karisa maganar a hankali tana harara mai dauke da dan murmushi, bacin yana kusa da ita baxai ji meta fada na karshe ba,

   a hankali ya lumshe ido, da shiga wani irin yanayi, kafun ya kara budesu tass a bayanta, don ta juya mai baya, itakam hankali kwance take cigaba da fadin,,

   oho dai, ke kika fada, a cigaba dajin dadi lfy, kufun nan da wata shekaran ma a kara shan wani sunan, kinga lokacin nima na dawo muxo mu dau sabon baby, can kuma tai dan dariya da fadin,,
 
  Na'ima baki da dama, Allah ya shiryaki, kinga nie a'iki nakeyi, basu ummalkhari wayar mu gaisa, sun dan jima suna gaisawa da kawayen nata na islamiya, kafun suyi sallama da hibbat, koba komai taji muryan yen kawayenta, tana sauke wayar da wani irin murmushin farin ciki.

    diff kuma murmushin nata ya dauke, sakamakon takunsa da taji ta bayanta, taja ta tsaya cak daga shirin juyowan da take kokarin yie, yayin da gabanta ya bada wani irin rasss,,

  kenan yana cikin kitchen din, shine abin da take ayyanawa a zuci, hankalinta yakai makuran wajen tashi, kafun tayi wani kwakwaran motsi taji ya hadata da bayanshi, da sauri ya ruko hannunta dake kokarin tika mishi waya da kasa, ya amsa cikin natsuwa yana maida ta cikin aljihunsa, kafun yasa hannu yana birkitota ta gaba, hannunsa nata bayanta, sosai ya hadata da jikinsa,,

   kallon mamaki sosai yake mata, ya dade da gane cewa wayau kawai take mishi, amma shima yau din sai ya wani basar kaman bai taba fahimtar wani abu ba, itama dago kai tayi cike da wani borin kunya tana kallonsa, idanunta harsun kawo kwalla, ganin irin bacin ran dake kan fuskan shine ya sanya ta kara shiga rudu, cikin wata irin murya da bata san yana dashi ba yake fadin,,

   Humairaah karyaaa..., baki na rawa take fadin,,

   Baff……, shishshs ya fada da dora yatsanshi bisa labbanta, idanunsa a kankance suke yana bin fuskanta da kallo, kamar yaune rana ta farko daya fara ganinta, cire yatsashi yayi yana tallafo fuskanta da kyau yayo sama, kafun ya sauke nashi kan nata fuskan, da sauri ta runtse idanunta, cikin wani salo yake shafa kuncinsa ko ina na fuskanta, tana juyo numfashinsa dake futa da kyar, dayar hannun dake bayanta yasa yana kuma jawota jikinsa sosai, muryansa a wani irin rikice yake fadi,,

   Humai……rahhh plssss fada mun me ake jine in akai aure……...kie sanar dani don Allah, sosai maganar ke tasiri har cikin kwakwalwanta, ya dakata da abin da yakeyi yana hada fuskansu waje daya, dishi dishi yake kallonta, har lokacin muryansa abnormal yake fadin,,
 
    fada mun……...manaaa me ake jieee,  umm……hmm come on say something, ya karisa maganar murya so cool, dole ta bude idanunta kadan kadan dake zubada hawaye, cikin muryan kuka take fara fadin,,

   Baff..., caraf ya kama harshenta, bai kara barin ta samu damar furta komai ba, ya shiga a'ika mats da wani sakon sumba mai wuyan fassarawa, kafufunta ke

Please Login or Register in order to submit comment