Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hoto, ita kuma taki, don bata riga ta shirya ba, ummeetah tace,,

  zuhra ku bari su aunty janan su shirya, da sauri kuma ta kalli inda suhymah take tsaye tana mamakin me family Ribado wai sukeyi a nan,,

  aunty janan wannan itace aunty suhymah, matar Baffah sadeeq, da sauri itama ta kalli suhymah tana fadin,,

  ohk itace maman wanene naji kuna kira, Irfan ko?, ummeetah ta daga mata kai alamar eh, da murmushinta ta kalli suhymah tana fadin,,

  Allah sarki, auntyn mu sannu da zuwa, kie shigo mana, dai dai sanda su hibbat suka shigo wajen ita da kanin su janan din Afna&Amna, nan da nan suma suka shiga gaisheta a mutunce, tare da yinmata jagora zuwa ciki.

  idanu kawai suhymah ta baxa, ko zata hangi wanda ta sani, can kuwa ta hangi mrs. khamis dake zaune gefe daya, da sauri ta mike ta karisa gareta suna rike hannun juna da gaisawa, ita take labarta ma suhymah labarin komai, duk ta kidima cike da al-ajabi.

  tuni kanta ya dauki ciwo, kwakwalwanta ya dau caji, shin da gaske ne, ummeetah ne da ahali irin wannan, tasan family Ribado, tun kafun iftila'in daya sami mahaifinta ya afka mai, ya fishi nesa ba kusa ba, don kuwa ma suna daga cikin wadanda suka futo takaran president last year, sai dai basu cie ba, ta numfasa da ayyana,,

  ko dai bakin da munat tayi mun ne, kan cewa wata rana yarinyan zata zo tafie nie ya kamani, kai tsaye wani sashin na zuciyarta ke ayyana mata,,

  a'ah, gaskiya ne dai data sha fada miki kika gagara gasgatawa, kasa kawai tayi da hawayen dake neman cika mata idanu.

  sanda su mummy suka iso, suma 1000 1000 jikinsu yayi sanyi, suka sami waje kusa da diyarsu suka rakube, suma suna jin yanda abubbuwa suke sassauyawa, haj. falmata waje kawai ta samu tana kishingidewa kamar wacce jininta ke hawa sama sama, mummy kuwa a'ita gaxa cewa komai, sai ido suke bin ummeetah dashi dake faman shiga da futa na alfarma.

  a haka dai har matayen Alh. Rabi'u suka iso, da kayan azzikin siyayyan da akayi ma mai jego da diyarta, kowa sakin baki yayi yana kallon yanda yeyen banki sukai kuka, yen uwan maami ma sun iso da tasu kayan, ciki harda set din akwatunan dasu haj. yagana suka hada na auran muheet, jie sukai kamar susa ihu sanda akai kiransu daki suga kaya.

  ummeetah ce zaune can kuryan gado, sanye da wani lace ta hade tasha kyau abinta, tana shayar da zahra yayin da kadan kadan take satan kallon inda ake daddaga kayan.

  tayi dan tsaki tana kallon nonon da suka ciccika duk sun dameta, duk da zahra a tsotse ce, amma kullum cikin bata mata riga suke, ga nauyin da sukai mata, rai a dan bace take sauya ma zahra site din dayan nonon, dai dai sanda ta jiyo goggonsu shatu na fadin,,

  ummee bar yarinyan nan kije kie sauya kaya, wadanga sun jima a jikinki, ba musu ta zareta, wata matar kawunsu dake gefenta inna huraira tace,,

  kawota nan, mika mata ita tayi, tana mikewa tsaye tare da nufa gaban safe inda goggo shatu ke ciro mata wani skyblue din doguwar a ledanshi, sai farin gyalle shima a ledanshi tare da farin takalmi, ta mika mata tana dan dafe kafadarta tare da mata magana irin na uwa da diyarta.

  da idanu kawai su haj. falmata suke binta da kallo, duk sai suka jie sun raina kansu, ganin yanda ake ririta yarinyan kamar a maidata ciki, suna kallonta harta raba ta gefe ta fuce rike da kayan.

  Haka aka cigaba da gabatar da shagalin suna, misalin 2pm babbar yarsu dake aure a saudia ta iso da yen yaranta, sosai suka sa murna ana rungume juna, DR.khamis ma dake zaune cikin su sadeeq da abokanshi a nan varender packing space da suke zazzaune, suka taso ana gaggaisawa.

  Alhamdulillah, ayi suna taro ya watse lafia, su mummy ma sun tafi da kayan suvenier da aka jibga musu, sai sumbatun wannan suna haj. falmata takeyi, harda korafin ba adalci, don tasan inda suhymah ce ta haihu baxai yie irin wannan hidiman ba, dole nema su mike susan abin yie.

    ***
  Karfe 6pm dot suka kammala packing kayayyakinsu da duk wani abu mai muhimmaci, don yau kaduna zasu kwana, yayin da shagargarin ranar za'a gabatar da taron bude makarantar, wanda yace dole sai ummeetah ta halarta.

  sun isa kaduna lafia, inda suka samu tarba ta mutunci daga wajen maami da wasu yen uwanta, da suka zauna nan suka tayata nasu sunan, daga nan kuma aka cigaba da shirye shiyen na gobe, sai hiran makarantar sukeyi, wadanda suka santa ana faman yaba kawatuwar school din.

   ***
  misalin 7am ne, tsakiyar dakin na hangota zaune bisa wata yer mirror stool, professional make up artists ce a kanta yayin da take tsantsara mata kwalliya na gani na fada.

  aka kammala kwalliyar tana shiryawa cikin wata tsadaddiyar swiss lace mare nauyi, style din riga da zani, peach colour ne sai dige digen golden dake jikin kayan, das ta kammala daura mata dankwalin kayan, da style na daurin ZB.

  ta zuba mata jewelry masu kyaun gaske, kafun ta dauko lafaya golden colour yaji kyau da tsada, ta shiga nada mata, kowa ya shigo dakin saiya yaba kyaun da tayi, takalmin dake kafarta ma yau weight shoe ne na kamfanin gucci, sai yer design cute bag dinta shima na kamfanin gucci duk golden colour.

  hotuna kawai suka kashe mata ta ko ina, don tayi kyau amma boss din yana zuwa yace ina a wanke wannan heavy make up din, ransu munat in yayi dubu ya baci, kamar zatai kuka take fadin,,

  kai yayan mu kudi fa mai tsada muka biya akai kwalliyar nan, banxa da ita kawai yayi daga zaunan da yake falon baki shida DR khamis dake faman tuntsire dariya, janan ta marairaice da fadin,,

  plss uncle sadeeq a taimaka, mun bada kudi da yawa, sai lokacin ya dago da fadin,,

  nima ku taimaka mun ku rufa mun asiri, wlhy ba advertising dinta zanje yiba, media ne zasu haska mu, kuyi mun wannan alfarman, karku damu zan biya kudin kwalliyar ko nawa ne, da dai suka lura da gaske yake, sai mikewa sukeyi ummeetah na faman cunno baki, don itama kwalliyar ta mata kyau.

  sai da suka kara mata hotuna, kafun a wanke shi tass, mai kwalliyan ma ta danji haushi, duk da an biyata kudin kwalliyarta, dole aka sake mata wani dan light make up din, kafun su kammala shiryawa aka fara tafiya, maami dai anyi anyi yau taxo wajen amma taki, dole su aunty batulah suka hakura suka barta, ummeetah taje tayi mata sallama sannan suka dau hanya.

  ***
  Tun misalin 9am jama'a ke kaiwa da dawowa a haraban makarantar, tsayawa faduwar kyaun wannan waje ma tabbas kauyanci ne, makaranta ne babba daya amsa sunanshi makaranta.

  a farfajiyar makaranta aka shirya wasu design tables masu dauke da 6-6 chairs, sai bangaren da akayi wajen zaman manyan baki, sai kuma inda MC zai tsaya, gefenshi wani long table ne mai dauke da wasu files, littafai, uniform, da sauransu, wajen dai yasha decoretion na alfarma.

  kansu na rawa suka nufi a'inihin maina gate din makaranta, sanye da wasu pited gown da suka jie style na rashin dabi'a, Najma ce gaba gaba wajen yinma security gard din da suke wajen rashin mutunci, saboda sunki barin wasu friends dinsu da suka xo wajen basu da pass.

   daker dai suka bar kawayen nasu ba don halinsu ba, sai don isowan oga da yace abarsu su shiga, tare dasu Baffah audu ma daya gayyato su da kanshi, duk yasa aka barsu suka shiga.

  suna shiga dai dai sanda aka bude gate din gaba daya, dakkakun motocin na karisa shigowa, kowa sai daya bie motocin da idanu, har suka kammala packing a inda aka tanaza don hakan.

  su hibbat da Amna suka fara futowa daga motar farko, kafun su aunty batulah, Amrah da sauransu su karisa futowa, motar karshe aunty janan ta futo daga gidan gaba, yayin da dan uwanta Abdulmu'iz ya karisa futowa mazaunin driver, duk suka bisu da kallo Najma na fadin,,

  wow zahira guy dina wannan Air post din, Abdul mu'iz Rabi'u……...,,

  Ribado fulani, zahira ta karisa da mamaki, kafun ta kalli yer uwanta tana fadin,,

  wai me Ribado's family sukeyi a nan?, kie lura dasu Afnah da yarsu janan, saudat ta dan tabe baki kafun da fadin,,

  maybe yayan mu suka sanie k……......, maganarta ya tsaya cak, sanda ummeetah ta ziraro da kafarta waje tana karisa futowa, aunty munat ma ta futo ta dayan site din rike da zahra dake cikin showel, cikin in ina munirat ke fadin,,

  um……ummeetah, ko ba ita bace?, duk da mamaki suka bisu da kallo tare da gazawa wajen fadin wani abu, Najma tayi karfin halin fadin,,

  ko……dai sun santa ne?, dai dai lokacin da suke takowo zasu wuce inda zasu zazzauna, zahira tayi saurin jansu bayan wani mota, karsu gansu suna kallonsu, dai dai sanda khaleefa da zuhra suka xo wajen suna kara ma ummeetah hoto, da ido suka bie yarinyan da kallo saboda tsabar kamaninsu da ummeetah.

  gaba daya dai su zahira kasa gane komai sukeyi, gwiwa ba laka suka koma inda suke zazzaune, sai gulma da kin gasgata abin da suka gani, jira kawai suke axo kararrama yayansu don suga yanda idon makiya za suyi.

  mummy da yer uwan tah, haj falmata suna zaune site din barayin baki sai kus kus suke da takaici, wai don sadeeq ya maida sunan maami a makarantar,(hmmm).

   taro yayi taro waje ya gama cika da manyan bakin da aka gayyata, ga kuma dumbin jama'ar dake wajen, wasu suna cikin shiga irin ta nairori, yayin da wasu suke cikin shiga na rufin asiri, gaba daya dai waje daya suke zaune, abin da aka bama wadancan, shi za'a bama wadancan, a takaice dai babu banbaci tsakanin juna.

   wani royal chair mai axababben kyau, aka nuna ma ummeetah three seater ne don ta zauna, ta samu gefe daya ta zauna, yayin da can saiga suhymah sun shigo ita da surayya.

  sai data neman mata wajen zama, kafun ta kariso cikin shigar sutura irin na ummeetah, sai dai ita gyale ne ba lafaya ba, itama ta samu waje tana zama bisa doguwar kujeran da ummeetah ke zaune, ba yabo ba fallasa suka gaisa, ana jiran shigowan oga at the top.

  tare dasu Abba, Alh. Rabi'u da wasu manyan baki suka shigo, waje na musamman aka musu suma suka zauna, yayin daya nufa kujeran da matayenshi suke zaune ya zauna a tsakaninsu, ummeetah dai sai satan kallonshi take ta gefen ido, don sai yanxun ma ta ganshi da kyau.

  cikin shigar shadda golden colour, yasha kyau na kammala ba a magana, madam suhymah dai sosai ta juyo tana kallon mijin nata, sai taji gaba daya a duniya kamar yaune ta fara sonshi, murmushi ya sakar mata yana karkata hankalinshi gefen da take da fadin,,

  madam yadai da irin wannan kallo?, itama murmushin ta maida mishi, kafun tace,,

  yhu look handsome dear, sai daya dan kalleta, don ya tabbatar da shin da gaske ita dince kuwa, ya murmusa mai sautin yana dan kuma kishingida site din da take, serious yake fadin,,

  na ganki tare da wannan kawar taki, wato angel ba zaki daina hurda da ita ba ko?, cikin sanyin jiki take fadin,,

  oh surayya wai, Allah sarki sweetheart itace take shishigemun a'i, yace,,

  hmmm, kie dai san hanyar da zaki bie ku rabu da juna, don kwata kwata yarinyan batai mun ba,  sai da gabanta ya amsa a 20-20, dai dai sanda DR. Zaidul Abideen ke bude taron da addu'a, professional islamic doctor, yana kammalawa kuma aka mike don gabatar da national anthem, sai da aka kai karshe, sannan kowa ya koma ya zauna a inda yake, yana kuma nanata mata,,

  kin daiji abin da nace ko, kanta kawai ta iya jinjinawa, tana kallon inda surayya take, da hadiye wani miyaun wuya, daga nan suka cigaba da dan kus kus dinsu, na mata da miji, yana sanar da ita wani abu daya kamata ta sani, amma ayyuka sunsha kanshi, ganin haka ya saka zuciyar wasu farin ciki.

  ko anan an nuna da tasu akeyi, nan da nan kansu ya fara fashewa, ko lura da yanayin mood din dake fuskanta basu yiba, ummeetah kuwa saita kauda kanta gaba daya, duk da abin ya dan mata zafi,,

  ko da ba zata hada kanta da aunty suhymah ba, itace ta farkon farko, kuma ta a'inihin daya sha fada, wasu cikin nata itama harsun fara tayata kishi, ita dai dauke kai tayi tana kallon students din da aka shirya cikin shigar butter milk din school shirt, sai black trouser or skirt, school anthem suke yie ba abin dake tashi sai sunan,,

  *_A'eesha Humyhra Academy,_* ko kadan ummeetah bata kawo komai ba a ranta, don yawancin sunyi tunanin sunan maami yasanya ma makarantar, su mummy duk sun kuma kulewa, yayin da ita oga kecan a rude ma take fadin,,

  sadeeeeq ko dai don ka daina so nah ne, za kace haka, ko don saboda ka zaba ka bata makarantar ne, zaka bani wanna……...,,

  maganarta ya katse sanda yaran suka kammala, ana kiran sunanta matsayin wacce zata bata tarihin mijinsu A A sadeeq, hawayen da suka taru a idanunta tayi kokarin mai dawa, da jinjina kai yake bata karfin gwiwa, ta mike ta futa filin kamar wacce kwai ya fashe ma a ciki.

  maganar kawai takeyi amma gaba daya hankalinta baya jikinta, da rawar murya ta kammala tana dawowa seat dinta, daga nan kuma aka cigaba da kiran mayan mutane suna bayani a wajen, tare da yaba kwazan wannan mai makaranta.

  sosai ummeetah ta natsu da tafiya duniyar tunani, wato ta lura a bayanan da akeyi, makarantar a'inihi na marayu aka ginashi, zasu zauna matsayin staff students suna karatu kyauta.

  yayin da kuma aka sirka da manyan yeyen masu dashi, su kuma zasu zauna a matsayin private students, su biya adadin yawan kudin da aka yanka musu, dashi za a samu ana cigaba da sponsoring karatun wadancan marayun, sosai ta yaba da wannan tsarin makaranta, tabbas kuma Baffahta yayi abu mai kyau a rayu……...,,

   hannun daya dan kyasta mata ne, ya sanyata sauke wani ajiyar zuciya tana juyowa site din da yake, da dan murmushinta take fadin,,

  Baffah mungode daka taimaka yen uwa nah, lallai ka nuna muma marayu ye'ye ne, yana wani dan fiddo ido waje yake fadin,,

  oh dama kema marainiya ce?, da sauri tace,,

  no am sorry, inhar ina tare dakai bana jin kaina matsayin marainiya, amma a wannan gabar ya zama dole su amsa wannan sunan,na yen uwanah, kafeta kawai yayi da idanu, ganin ya tafi da yawa ne, ya sanyata cikin dan dibara ta taba kafadarshi saboda ya juyo nemanshi da akeyi a filin, sai daya sauke ajiyar zuciya kafin ya mike ya bar wajen.

  wajen aunty mashkura ya amsa micro phone, don itace MC a wajen, kasancewar itama ma'aikaciya ce a wani tsadaddan makaranta dake saudia, to kuma sunyi appliating tasu makarantar da wancan na kasan saudia, tun kan ya gano ummeetah yer uwan sune, da ita aka rika komai tana basu taimako.

  da addu'a ya bude zancenshi tare da sallama irin ta addinin musulunci, komai yakeyi kawai binshi da kallo take, matuka yau din nan ba karamin kara burgeta yayie ba, ya dan sace kallon inda take na wasu yen dikikai kafun ya numfasa da fadin,,

   da farko ita dai ba marainiya ba ce, ya kuma yin dan shiru sannan ya cigaba da fadin,,

  ta kasance yer gatan mahaifinta, murmushin kan fuskanshi, sannan taurari da suke kawata farin cikin rayuwanshi, uba ne daya tsayu don yaga rayuwar yershi guda daya tal, ya inganta duniya da lahira, yayi wani dan murmushi kafun ya juya yana kuma kare mata kallo, jikin mutane da dama yayi sanyi a wajen, da raunin murya yake cigaba da fadin,,

  daga karshe kuma ta zamto marainiya, a sanda ya tafi ya barta a wannan duniya, mai rikita rikita da tarin abubbuwan ban mamaki, hawayen da suke fal cikin idanunta suka wanko samar fuskanta, yayin da zuciyarta ke wani irin kunci.

  lokaci daya tarihin rayuwanta na baya ya shiga dawo mata, yayin da take sauranranshi yana cigaba da bada kadan daga cikin tarihin rayuwanta, mutane da dama sun tausaya mata.

  anxo wajen da dole ta firgice da mamaki, shikam sai dada nanatawa yakeyi, mutane da dama sun shiga halin mamaki, yayin da wasu cikinsu ciki harya duri ruwa, wasu kuma amanarshi ne yake dada basu mamaki, shikam a wannan gabar da murmushinsa yake nananata fadin,,

  ita dai wannan marainiya, a yanxun itace shahararriyar yer kasuwan dake da mallakin A A sadeeq trading company, haka zalika shahararriyar yer kasuwan dake da mallakin A A sadeeq furnitures, A A sadeeq NIG LMT,  A A sadeeq farm house, kai suna da matukar yawa etc. kawai……..., nan kuwa aka saka tafi, yaja numfashi kafun ya cigaba da fadin,,

  ba kowa bace face shugabar wannan makaranta mai albarka, wacce a yanxun in sha Allah zamu kirata taxo ta bama dalibai goma daga cikin daliban mu, Admission dinsu da hannunta, in Allah ya yarda.

  yayi dan shiru yana bin mutanen dake wajen da kallo da wani murmushi, ganin yanda kowa ya zaku yaga wannan wacece, numfasawa ya kuma yie kafun ya cigaba da fadin,,

  plssss put ur hands together, to the mother of leaders of tomorrow, ba kowa bace face marainiya kuma uwar marayu, *_A'ISHA  ALIYU SADEEQ,_* pls ku bata hannu, ya karisa maganar muryanshi na amsa kuwa cikin micro phone din, lokacin da dukkan jama'ar wajen suka dinke da tafi, sautin haduwan tafukan hannu kawai kake jie.

  ummeetah dai gaba daya kanta yayi zafi, ta koma mutum mutumi a wajen, shin wai da gaske ita A'isha Aliyu yake nufi, koda dai labarinta tabbas ya gama badawa, to amma dama Affah ya bar mishi dukiyarta a wajenshi ne?·

   bata dame bata wannan amsar,sai hannunta da taji an ja, ba kowa bace face aunty mashkura, dole ummeetah ta mike ta biyo bayanta ana cigaba da bata hannu.

  cikin sanyi take takawa da ganin komai kamar a mafarki, lokaci lokaci kuma takan dago idanunta ta kalli site din da yake tsaye, sai data fara sanya hannu a wasu takardu, wanda take da yakinin na makarantar ne, kafun a fara kiran sunan students din one by one.

 ko wanne yaxo zata bashi, admission later, uniform, hade da materials na karatunshi, haka suka cigaba da zuwa suna amsa tare da mata godiya, sai faman haskasu ake a media.

   wani farin ciki ne ke ratsa zuciyarta, ganin yaran duk marasa galihu ne, ko ba komai zasu samu taimakon wajen samun rayuwansu suma ya inganta, lallai Baffahta ya cancanci jinjina mai yawa, bisa wannan tsarin tunanin da yayi.
 
  last but not the list, aka kira wata yer yarinya da bata wuce 6to7years a duniya ba, yanayinta kawai ya nuna zallar rashin natsuwa dake tattare da rayuwanta, duk da an mata shiga mai kyau da tsafta, ta kariso ummeetah na mika mata nata kayan, kin amsa tayi kawai tana zuba ma ummeetah idanu, irin ye'yen nan ne masu shegen wayau, hawayen da suka cika idanunta ne ya sanya jikin ummeetah yin sanyi matuka, a hankali ta duka gaban yarinyan tana dafa kafadarta da fadin,,

   ba kya son kie zauna a makaranta ne?, da sauri ta girgixa kanta alamar a'ah, ummeetah tayi murmushi tana mika mata file din dake dauke da Admission later, dai dai sanda hawayen suka wanke fuskan yarinyan, cikin shashshekar kuka take fadin,,

  aunty don Allah kie bama Abban mu shima, yana son karatu kullum shike koya mana karatu, don Allah kie taimaka mishi naga kina da kirki, murmushin yake kawai ummeetah ta iya mata, don tana hangen kunci mai tarin yawa a idanun yarinyan, cikin sanyi take fadin,,

  me yasa kike son in taimaka mishi?, da sauri aunty mashkura ta iso tana manna ma yarinyan speaker itama a gaban riga, tayi kwal kwal tana cigaba da fadin,,
 
  aunty saboda yana taya maman mu a'iki, yana samo mata kudi, baya bari tayi wankau da gugan da takeyi yanxun, yana siyo mun sabbin silipers, bana yawa ba takalmi, hakama su yaya azima duk yana siya musu, sannan yana kaimu makaranta da kanshi, ya kuma koya mana in bamu iya ba, sannan in nayi kuka yana siyamun sweet da biskit, ta hade hannayenta waje daya alamar roko tana fadin,,

  aunty don Allah kie taimaka Abbana shima, don ya dawo gidan mu, maman mu tace duk yana yin wadannan abubbuwan ne saboda rayuwan mu ya inganta, kuma mu zamto abin alfahari a rayuwa, na rokeki ba don halina ba, da sauri ummeetah ke fadin,,

  zan taimaka mishi, amma shie Abban yana ina?, yen uwanta dake zaune daga can duk suka sanya kuka, harda mahaifiyarsu dake dukunkune kanta cikin hijjabi tana matsar kwalla, yarinyan ta numfasa da murmushinta take share hawayenta da fadin,,

   yana sana'ar seda jarida a bakin titi, shine wani mai mota mare tausayi yaxo ya bigeshi, kuma yayi tafiyarshi, haka aka dawo da Abban mu kanshi duk jini, kuma ban kara ganishi ba, mama tace yaji tsoro ne da motar nan ta bigeshi ya tafi wani waje, yanxun bani dame siya mun silipers, don Allah kie taimaka mishi, ina son Abba nah.

  sosai ummeetah ta toshe bakinta da kukan dake zuwan mata, kawai saita rungume yarinyan tana sanya sabon kuka, lallai marairaici yana da zafi, sai dai akwai hanyoyi da dama da Allah yake tallafa musu, tabbas basu taba wulakanta a rayuwa, ta dago yarinyan tana share mata hawaye da fadin,,

  in sha Allahu rayuwan ku zata inganta, zaku zama abin alfahari kamar yanda mahaifinku yayi buri, in sha Allahu sai mafarkinshi
ya zama gaskiya, ta mika mata file din da sauran kayan, yarinyan ta amsa tana kwararo mata godiya tare da addu'a mai dumbin yawa, sai da aka cire mata speakern dake gaban rigarta sannan ta koma wajen zamanta, ummeetah ta rakata da ido yayin da aka cigaba da basu hannu.

  ajiyar zuciya kawai ta sauke, da hawaye take bin marayun ye'yen da suke tafi fuskansu cike da annuri, masu wayaun cikinsu harda kuka dadi, kawai saita juya tana kare ma mijinta kallo, dake tsaye har yanxun yana kallonta cike da burgewa,,

  yanxun duk ta dalilin tausayi da amana irin nashi, dumbin marayun nan za suyi farin ciki, murmushi ta saki mai dauke da ruwan hawayen dake cikin idanunta, yayin da dimple dinta suka lotsa, lafayanta ta dan ruko, jie kawai tayi kafafunta na sassarfa tana zuwa gabanshi batai wata wata ba ta rungume kayanta, tana sakin wani marayan kuka da fadin,,

  wlhy Baffah nah ina sonka, kai alkhairi ne a rayuwa nah, i truly love yhu darling, mutumin a'i sai yayi sansaransan, ummeetah fa ta manta da wasu dumbin jama'a dake wajen, don dagowa tayi a kideme tana bin fuskanshi da kisses, tare da kara rungumesa, shima mai da hannunshi yayi yana rungume yen kayanshi, da wani murmushi yake dan bubbuga bayanta, nan kuwa aka kara sa tafi, raf raf raf.

  ta dago kanta da hawaye sharashara take kare mishi kallo, shikam wani tsananin farin ciki ne dabe san na menene ba, ya makale mishi can kasan zucci, a hankali ta kara manna mishi kiss saman kuncinsa, kafun ta dago da fadin,,

  miji nah nagode daka tafiyar da dukiya na ta hanyar alkhairi, shidai banda blushing ba abin da yakeyi, ganin yanda tabi ta kanannade hannunshi, speakern gaban lafayanta ya cire, kowa ya zuba musu idanu, da dan murmushi yake fadin,,

  hmmm karfa kuyi mamaki, kar kuma ku manta ita din……..., sai kuma yayi dan shiru, yana wani miskilin murmushi, kafun ya cigaba da fadin,,

  tana da wani suna mai matukar muhimmaci a waje nah, wanda shine……...,,

  *MATATA CE,* ya karisa maganar da wani sigar alfahari, gaba daya wajen ya amsa da tafi, yayin da wasu suke faman kwashewa a waya da camera, itama kasa kawai tayi da kanta tana murmushi, da sassauta rukon da tayi mishi, don sai yanxun wani kunya ya kuma rufeta.

   hmmm su mummy fa ba'a magana, bare kuma oga suhymah da tuntuni tayi sumar zaune a wajen, daya daga cikin kawayen su zahira

Please Login or Register in order to submit comment