Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaman kasar nan, a'ikinsu zan ije musu, wanda nayi Allah sa mishi albarka.……, kiran da take faman kwala ma ummeetah ne, ya dawo da dashi daga duniyar tunanin daya tafi, da sauri yake fadin,,

   me zata miki?, mikewa tayi da fadin,,

   kaya zata kaimun mota, shima  mikewan yayi, kafun yace,,

   no ki barshi kawai zan futa dashi, galala ta tsaya kallonshi, zatai magana yayi saurin tallafo fuskanta, a kunni yake rada mata,,

  am really gonna miss yhu, wani basarwa tayi, bakinshi daya hada da nata ne, ya dawo da ita kan network, ba shiri itama ta daura hannunta bisa kuncinsa tana maida martani.

   dai dai sanda ummeetah ta shigo dakin, da sauri ta juya ta futa, Allah yasa ma bata riga tayi sallama ba, wani dogon tsaki take ja tana komawa dakinta, idanunta a rufe suke don takaici, bata ankaraba ta kusa karo da kujera.

  da sauri ta tsaya da kyau, tana dafe kirjinta dake faman harbawa, idanunta ta runtse, bata san sanda ta kwala wata kara ba tana dafe ciki, minti biyu yayi yawa sai gashi ya futo, ganinshi kawai tayi a kanta ya rukota da fadin,,

  lafia, meya faru?, ta janye jikinta tana baya baya, fuska daure take fadin,,

   karo na kusa yie da kujera, dai dai sanda suhymah ta biyo bayansu, wani kallon tuhuma take mishi, ya dan sosa sumar kanshi da fadin,,

  eyah sorry, ki rika yie a hankali, amsa mishi tayi tana komawanta daki, shima nasu bedroom din ya koma tabi bayanshi da kallo, kafun ta wuce straight dakin ummeetah.

   tana rufe trolley ta sameta, cak ummeetah ta tsaya da abin da takeyi, gaban mirror ta wuce tana zuba ma kayan dake kai ido, ta dago wani turare tana jujjuyawa, kafun ta juyo da mamaki tana fadin,,

   daga ina wadannan suka futo?, wani irin natsuwa tare da dakewa ummeetah ta tattaro tana fadin,,

   Irfan ne ya kwaso su jiya, shine na daura a nan kafun in futa dasu, kirjinta ke wani irin bugawa fas fas, tayi dan shiru kafun ta sauke idanunta kan wani agogonshi dake bisa side drower, karisawa tayi ta daga agogan shima.

   tabbas taga Irfan dashi jiya, sai dai bata san a'ikenshi yayi ya dauko mai ba,,

   harda wannan?, ta fada a yatsine, kai ta daga mata da fadin,,

  eh, tsoro take ta lura da wasu littafanshi dake ije a wajen, bare kuma aje ga cikin safe wanda rabi da kwata duk kayan shine, nisawa tayi tana ije agogan da fadin,,

  kie kwasa dukkan kayan kie mai dasu dakina, kafun in wuce daku gidan shaakirah,,

  tom, ummeetah ta fada a takaice, ta tako a hankali kaman zata futa, sai kuma ta tsaya cak tana dan juyowa, wani kallon tsana take bin ilahirin jikin ummeetah dashi kafun tace,,

  tabbas kin mike kafa a gidan nan, kina makaranta mai tsada, sutura iri daya dana matar gidan, hmmm, ta fada da wani takaitaccen murmushin, kafun ta daura da fadin,

   toh kie san wani abu daya, zanje gida in dawo, dole inna dawo komai ya canxa, saina tabbatar na  tuna miki da rayuwanki na baya, ta nunata da dan yatsa kafun tace,,

   sannan soon zan hada miki abin da zaisa da hannunshi zai dauka ya koreki, kuma ya cilla kie kauyenku, kie daina ganin kin samu waje, tikitin daxai raba nie dake yana nan zuwa, dama zuwa yanxun na gaji dake, wata sabuwar zan dauko, sai kie zauna da shirin barin gidan nan da zaran na dawo, daga haka tasa kai ta fice.

   wani nannauyar ajiyar zuciya ummeetah ta sauke, tana sulalewa bisa gadon, hawaye ke neman sauka bisa fuskanta, ta daure dai tana maida su, wani sashin na zuciyarta na raya mata,,

  ba laifinta bane, matar so ne, ko kadan kar kiyi tunanin hada kanki da ita, sosai ta saka wani sabon kuka, anya kuwa zata iya samu kashi hamsin na daga……, kasa karisa tunanin nata tayi, ta share hawayenta saboda dan cikinta daya fara mutsu mutsu.

  mamaki takeyi, waishi talaka kullum a mara y'enci yake, kauda abin tayi a ranta, tana cigaba da tattara kayan bogin da yace ta shirya, yana kaita airport ya dawo zaizo ya daukesu.

    Gidan DR. khamis suka nufa, sanda ya futo sun gaisa da suhymah tare da jajanta mata abin daya faru, don zuwa yanxun labarin abin daya samu mahaifnta ya zaga ko ina a kasan, canxa harshe kuma yayi sanda suke gaisawa da ummeetah, yana tambayarta tana dai kula da mijinta ko, ya babys din Baffanta suke.

   da kunya tayi dan kasa da kanta tana murmushi, ya cigaba da maganar yana kallon sadeeq da shima bajin abin da suke cewa yakeyi ba, amma yasa tabbas akan auransu yake magana, ita dai madam sai wani yatsina takeyi, Baffah kawai ta iya jie, a zuciya take ayyana,,

  kwa daiji da gulman ku, matarsa kuwa dake gefe ta cika da mamaki, har sanda sukai sallama da suhymah suka wuce airport da mijinta.

   daki ta sameshi ya sanar da ita komai, tare da gargadinta kan ta kama bakinta, sosai ta cika da mamaki tana sakawa da kwancewa.

               

                    £……£……£

   Zaune suke a wani dan madaidacin corridor, wanda yajie yen design sofa chairs harda wani dan karamin dispenser gefe daya, gefe kuma dakine inda akai admiting mahaifin nata, wanda ya tsaru yaji komai da komai na rayuwa.

   jiyan nan aka sanja musu dakin, bayan sunyi waya da sirikin nasu, waya kawai yayi aka sauya musu wajen, xuwa yanxun duk wani hidman abin da za'ayi daga wajenshi yake futowa, sosai yake iya bakin kokarinshi, kasancewan yanxun lamarin daya afka musu, dama yawancin yen uwan mahaifin nasu ba masu karfi bane, shine dama mashahurin mai kudin a cikinsu.

   to sanda ma yake da kudinshi ba wanda yake ba mawa, musamman iyalan nashi, da mahaifiyarsu tasa musu akidar tsanarsu don kawai ba sukai samu nashi ba, don haka ba wani farin jini ne dasu a familyn ba.

   yanxun hakama kadan daga cikine suka zo, sai wasu aminan azziki dai da baza a rasa ba, a hakama basu saduda ba, ko wani kalan bako yaxo da kalan wajen zamar da za'a mishi.

    sanda su maami suka iso ita da munat, a mutance dai aka basu wajen zama, suna zazzaune a corridor wajen, su zahira ne suka shigo tare da saudat da mummynsu ta taho da ita jiya.
 
  kusa da mum dinsu suka zauna, farar macace mai kiban gaske, sanye take cikin shiga na alfarma, ta wani dan kishingida da kujera, gefe ga yer wata cute bag ije tana faman jujjuya wata tsadaddiyar waya dake hannunta.

   saudat ne kawai ta iya gaida maami, amma sauran sai yatsina sukeyi kamar basu ga sauran bakin da suke dakin ba, zahira ta ruko hannun mum din nasu da fadin,,

   mum plss i need money, cike da muryar kasaita take fadin,,

   yhu need money, me za kiyi dashi?,  zumburo baki tay kafun tace,,

  mum, zan sai pad nefa, yer dariya akayi yanayin yanda tayi maganar, mum din ta bude yer jakanta tare da zaro kudi ta bata, mummyn su munat dake gefe ta kalleta da fadin,,

  kuje pharmacyn hospital din ku amsa kawai, sai a sa cikin lissafi,,

   ouk, ta fada tana mikewa, saudat ma ta mike, banda Najma data manna kanta bisa kafadar mum din nasu, tana faman daddanna waya, munat ce ta kallesu tana fadin,,

  ku baku iya gaisuwa bane ko?, zahira ta fara fadin,,

  ohh, aunty munat ban ganki bane, ta gaisheta tana gaida maami, itama Najma a sangarce ta dago tana gaidasu, zahira ta mika mata hannu da fadin,,

   twin sist zo muje mana, make kafada tayi tana fadin,,

   a'a kuje, nie na gaji fa, futa su kayi tare da saudat, munat ta dan zaro ido waje kafun tace,,

  oh nie, wato Najma kina nan da son jikin ki na fama, kuma narkewa tayi jikin mum din nasu, cike da barkwanci wata abokiyar wasansu ke fadin,,

   a'i wannan shegen kalailaitan tsiyane da ita,,

  ummhumm, shine abin da mum din nasu tace, ta kuma gyara kishingidan da tayi tana shafa fuskan yarinyan da fadin,,

  auta nah, a'i duk haka suke, dama dama ma zahira, amma wannan da big sisternsu sai du'ai, ta karisa maganar cike da kasaita, kallonta kawai wasu yen uwan keyu, inda sabo sun saba, duk sanda suka zo haka zatai ta nuna musu iko da izza na kudi, munat tace,,

  ahh, a'i ita aunty suhymah karshe ne, last da naga hotonta, mum abuja kinga yanda tayi kiba, ta kusa yinki fa a jiki, murmushi ta saki, duniya tana son yeyenta, don haka ba abin daya fi mata dadi kamar hirarsu, tana fadin,,

   a'i suhymah ta fini ma killa, toh a gida AC, a mota AC, a office ma AC, itafa bata iya komai, sai dai a dafa a bata ta cie, gidane daga ita sai miji, sai kuma yer a'iki, mummyn su munat tace,,

   daughter nah a'i akwai son hutu, yer dariya tayi da kallonta tana fadin,,

  kinsan yanxun mukai waya da ita, a jirgi fa take, common zaman jirgi, shine duk ta isheni da fadin,        mummy na gaji, mummy na gaji da zaman jirgin nan, a tare suka sa dan dariya, harda wasu yen wan mijin nata da suke na yake maami dai abin bai burgeta ba, munat tace,,

  a'ito Najma ina jin ita zata biyo, gashi nan harta fara narka kiba itama, dariya suka kuma yie mum din na fadin,,

   autanah a'i ita nata lamarin ya girmi na kowa, ita da tace mun, mummy nifa duk cikin samarina masu zuwa a motan nan bana sonsu, kuku nake jira yaxo na aureshi, sai da ya rika dafo mun abinci ina cie, sai lokacin maami ta rike haba da fadin,,

   wuwww, a'iko da gaske take, dariya aka kuma yie, mum din na dada make murya da fadin,,

   hmmm Najma, itafa tace electronics din kitchen ma basa burgeta, saboda ta tsani ta tsaya gabansu ma, serious fa zata kalleni tace, mummy kinmun addu'a Allah ya bani kuku, wani dariyan suke kuma yie, munat na fadin,,

  lallai Najma da gaske kike, hiran suka cigaba da yie, yayin da yen uwan dad din ke rakube a gefe, sai da suyi dan murmushin yake in anyi dariya.

   maami kam tuni ta tsunke da lamarinsu, wato bacin ummeetah nacan tare dasu, da d'anta ne har yanxun zai rika nikar a'ikin gida, yayi na office ya dawo yayi na gida, kasa tayi da kanta kawai, tare da kuma shiga tsananin damuwa sanda ta tuno da auran muheet da ummeetah.

  sanda madam ta iso, tafi kowa yatsina ga yen uwan nasu, sai kunkunai take wai sunxo sun cika musu waje, sai da mummyn su munat ta zungureta sannan ta lura da maami tana gaisheta.


                         ***

  kwance yake bisa gadon suna waya, tun futowarta wanka har sanda ta kammala shiryawa cikin doguwar rigan bacci mai santsi, a hankali ta kariso wajen gadon tana zama gefe daya, pillow ta dauko ta dora a jikinta, tare da dafawa tana zuba tagumi, kadan kadan take jiyo sautin dariyanshi, yana fadin,,

   miss yhu too kisha famun babyna plsss, tsam ta mike tsaye tana maida pillow inda yake, tare dayin dan tsaki kasa kasa, hanyar futa ta nufa, da ido yake binta, ganin tana ninyar ficewa ya sashi saurin katse wayar gaba daya, tashi yayi ya zauna da kyau yana fadin,,

   Humaira yadai, ina zaki?, a hankali ta dan juyo fuska ba walwala, ta kauwar da idanunta gefe tana fadin,,

  xan koma daki nane, kaga ba dama mu kwana mu biyu, tunda kuna waya da aunty suhymahnka,,

    suhymahnka, shine abin da yake ayyanawa a zuci, kafun ya kalleta yana fadin,,

   ouk, sorry na ije wayar, dan murmushi tayi da wani kalan tunanin, kafun ta kariso inda yake kwance yana mika mata hannu, nata hannun ta saka a nashi tana zama gefenshi, dai dai sanda wani kiran nata ke shigowa wayar.

   my angel, shine abin da ke rubuce, ta tsare screen din da idanu, kafun taga yana kokarin amsa kiran, kai tsaye ta dafe hannunshi, kirjinta ne ke wani irin bugawa, ta dan runtse ido da zafin dake taso mata kasan zuciya, kafun ta dan bude kadan ta kalleshi, kamar yanda shi yake kishingide ya zuba mata idanu,,

   Baffah plss ka barshi dare yayi fa, ta fada da dan kakkauda idanuwa, ajiyar zuciya ya sauke sanda ta zare wayar a hannunshi ta kashe gaba daya, tare da ijewa gefe, muryanshi ta juyo dake fadin,,

   Humaira ko kema kin fara kishi nane?, mikewa tayi ba tare data kalleshi ba zata bar wajen, caraf taji ya cafke hannunta ta baya, cak ta tsaya, cikin wani irin murya taji yace,,

   plsss kiban amsa, sosai ta runtse idanunta, saboda yanda kirjinta ke bugawa, amma saita dake tana dan juyowa da fadin,,

   kishi kuma?, nie basan yanda ake jiba, ya dan lumshe ido tare da budewa yana fadin,,

   come on, nifa mijin kine, kullum muna tare, ya kamata ace kina jin wani abu a kaina, ya karisa maganar yana daga mata gira sama, sosai taci serious tana kauda kanta da fadin,,

  nifa Baffah gaskiya bansan wannan karatun ba, kawai dai nasan kana matsayin miji nane, kuma inama Affah na biyayya ne, kan auranmu daya hada, tare da cika mishi alkwarin da yace in mishi, in sanya ka farin ciki sannan in maka biyayya, ta karisa maganar da murya kaman zatai kuka.

   sansaransan ya tsaya yana kallonta har takai karshe, kasa cewa uffan yayi harta zare hannunta a nashi, tana komawa ta dayan site din tare da hawa gadon, zama tayi tana jawo blanket ya dan juyo da fadin,,

   amma…….., sai kuma yayi shiru, kadan ta kalleshi kafun ta koma tana kwanciya da kyau, har ta shafa addu'an bacci, yana kallon wani waje yayi shiru, da kulawa ta kalleshi tana fadin,,

  Baffah dare yayi, ka kwanta kayi bacci, ajiyar zuciya ya sauke yana sulalewa a hankali bisa pillow, tare da facing sama, idanunsa har lokacin a bude suke tar, ita kuma dishi disho take kallonsa, kafun taga ya kara numfasawa, ba tare daya kalleta ba yake fadin,,

   ina son kie iya mota, zan koya miki, kina so?, idanunta a lumshe take fadin,,

   indai kana so, nima dole in so, murmushi taga ya saki, kafin ya juyo yana facing dinta yana fadin,,

   Humaira babu dole kiso abin da nake so, da sauri ta bude ido, ya jinjina mata kanshi da fadin,

   yess, tunda bani a ranki, plsss kie yafe mun inna miki wani abin na takura a rayuwar auran mu, girgixa kanta tayi da fadin,,

   nie baka mun komai ba, har abada na yafe maka duniya da lahira, nice ya kamata na nemi gafararka, don Allah karka kwana da bacin rai, inhar abin dana fada akwai abin daya bata ma rai kayi hakuri, ta karisa maganar kaman zatai kuka, sosai yake murmushi da kallonta,,

    ina son wadannan tausasan kalaman naki, suna tafiyar da zuciya na sosai a kanki, ya fada maganar da wani lumshe idanuwa, kafun ya miko mata hannu yana fadin,,

   na saba da jikinki plss give me a hug, ba musu ta karisa gareshi, tsam ya rungumeta, ya soma wasa da harshensa wajen kunninta, cikin wata sarkarken murya yake fadin,,

   kiyi hakuri, zaman tilas bashi da dad'i, Allah ya nufa ni mijin kine, kuma nie ina son abina, Humaira ina sonki amma banji dadi ba dana takura ma zuciyarki, nie kaina bansan lokacin dana fara sonki ba, cikin kasalallan murya take fadin,,

   Baffa……, yatsanshi ya dora bisa labbanta har lokacin bakinshi nakan kunninta yace,,

   shishshish, dole tayi shiru ya cigaba da fadin,,

   gobe zan fara koya miki motar, nasan ke jarumata ce, dan kankanin lokaci zaki iya, upper 3weeks masu zuwa baxan samu zama ba, nasan zaki iya koda driving kanki zuwa school ne ko?.

   kanta ta daga alamar eh, don gaba daya ya gama kashe mata jiki da wasannin da yake mata, harshensa taji saman lips dinta yana wasa dashi, cikin sarkewan murya yake fadin,,

  come on take it, ba musu ta bude nata bakin tana zira mishi nata, lokacin kankani kuma labarin ya soma sauyawa, don haka na tarikito komai nawa nayo waje, sleep tight.

   Shagargarin ranar ya soma koya mata motar, sosai ta maida hankalinta, sai gashi ba a wani jima ba, ta fara kwarewa, suhymah kam ana can naija, tuni mahaifinta ya samu sauki ba laifi, daga karshe aka sallamesu bayan ya koma tafiya a wheel chair, gashi ko baki babu, to sai muce Allah ya kara lafia, Allah ya bamu ikon yin imani da kaddara mai kyau da mara kyau, Ameen.



                    £……£……£

  Da fara'anta ta dago kai tana fadin,,

   finally dai lokaci yayie, yau saura sati daya biki, ga kaya nan an hada komai da komai, yanxun Abban sadeeq kai muke jira ka bamu adress, saboda en uwa da zasu zo gobe akai kayan, murmushi Abba keyi da zuba ma set din akwatuna har guda biyar idanu, kafun yace,,

   anya haj. yagana wadannan kayan ba suyi ma amarya yawa ba, fuskanta cike da annuri take fadin,,

  ko kadan Abban sadeeq, nasan gidan girma za akai, kaga kuwa dole muma mu nuna bajintarmu, musamman irin kudin da dan uwanshi ya a'iko a hada mishi laifen, kaga shima dole muyi abin da zaiji dad'i, Abba ya jinjina kai tare da fadin,,

    good, maganar kie gaskiya, don na lura kina jie da auran mutallab dinnan, da sauri take fadin,,

   ah ba dole ba, bikin d'a guda sukutum, a'i dole ne inyi iya kokarina a bikin muheet don kyece raini, shiru kawai Abba yayi,,

   d'a guda sukutum, bacin sunan da take yawan kiran sadeeq dashi ne, har yakan jie dad'i inta fada……, ita ta katse mai tunani da maganar da take fadin,,

  Abban sadeeq nace a taimaka, inason yau a sanar dani inda muheet ya samu mata, kaga kodan kai kayan laifen nan da za'ayi, ajiyar zuciya ya sauke kafun yace,,

    haj. yagana tah kenan, karki damu, kinsan baxan xaba ma mutallab abin dazai cutar dashi ba, ki cigaba dabin lamarin da addu'a, in sha Allah kwanan nan zaki san komai, marairaice fuska tayi, don harga Allah ba haka taso ba, kafun tace,,

   toh akwatunan fa ina za a kaisu, shiru ya dan yie kafun yace,,

   karki damu, zansan yanda za ayi dasu, dole ne dai akaima amarya abunta, ya karisa maganar cike da barkwanci, murmushin yake tayi kafun ta mike tabar falon, futan ta kenan muheet ya shigo.

   kwab kwab kwab, kawai kake jie, karar wata uwar cover dake kafarsa, zama yayi fuska kamar battle field, yana faman jero tsaki ciki ciki tare da kunkunai, cike da takaici Abba ya kalleshi yana fadin,,

   kacie gidanku, wai me yasa kai baka da da'a ne,  baka iya sallama bane?, baki ya turo kafun yace,,

   Abba nayi sallama fa, baka jie bane, girgixa kanshi yayi kafin ya kalle akwatunan sannan ya kalleshi da fadin,,

   wannan lefan amaryan kane……, wani irin buga kafa yayi yana fadin,,

  ohh my god, Abba nifa bana son auran nan, nace bana……, da sauri shima yake fadin,,

  kai kaga naka, ina magana kana magana, mutallab wani irin yaro ne kai, atleast ka barni na gama fadan abin da zance ma, kasa yayi da kanshi yana fadin,,

  sorry Abba, dan tsaki yayi kafun ya cigaba da fadin,,

   dama yarinyan da kwanaki kace mun kana son aura ne, wacce take a'iki a sashin……, da sauri yake fadin,,

   Abba ummeetah, yace,,

  of course ita, to shine na hada auran, amma kasan mummynku bata so, inhar kayi wani abin da tasan maganar, to shikenan ba ruwa na, kuma fasawa za ayi, cike da murna yake fadin,,

  Abba baxan fada mata ba, i promise baxan fada ba, indai ummeetah ce matar dazan aura to ina so, yauma a daura auran, murmushi Abba yayi yana fadin,,

   shashasha, ka bari yayanku tukuna ya dawo da amaryan taka, kuma indai baka natsu ba ka daina shashancin da kakeyi, ina tabbatar maka, ko anyi auran saina sa an raba, da sauri yake kuma fadin,,

   Abba na rantse na daina, yanxun yaushe zasu dawo?,,

  hmmm, Allah yasa, Abba ya fada kafun ya daura da fadin,,

   ina tunanin sai nan da friday, ko kuma safiyar ranar daurin auran, duk yanda ya kama dai yace zasu dawo in sha Allah, wasu a'ikine sukai mishi yawa, shidai muheet sai wangale baki yakeyi, jikin nan daya kwallafa ma rai kawai ke mishi gixo a idanu, yayin da Abba ya daura da yin mishi nasiha mai ratsa jiki, yayi wani likimo kamar yana saurara da gaske.

  yana gama mai ya sallameshi, futowa yayi ko site din bai idda fita ba, ya ciro ratsatstsiyar wayarsa yana dialing wani number, da murnansa yake fadin,,

  baksow kana jina, plsss ku tanadar mun club mai tsada yau, ka gane ne, ko nawa ne kudinshi ku tanadar mana, a zuba beers masu tsadan gaske, tare da zafafan chikas, ka gane ne, dan shiru yayi kafun yace,,

   karka damu, kadai kayi mun abin dana saka, p~man ne yayi mun kyautar wata yer kwalban turare na fesawa, amma akwai kamshifa, yasa wata uwar dariya yana fucewa daga sashin gaba daya, tare da cigaba da amsa wayar.

    Yau suhymah ta iso da sisters dinta kai sai rawa yakeyi, sashin mummy suka wuce kai tsaye, tunda ta shiga ko keyarta ba a kara gani ba, can suke sha'aninsu da shirye shirye.

                        ***

   Kadan kadan a cikin bacci take juyo muryansa, sallama yakeyi da muryan kuka, da sauri ummeetah ta farka tana mikewa tsaye, dai dai sanda shima ya bude idanunsa, ya dan dago da sauri yana kankance ido irin na mai bacci tare da fadin,,

   wannan ba muryan Irfan bane?, hanyar futa tayi da fadin,,

  eh shine, kokarin mikewa zaune ya fara yie, dai dai sanda ummeetah ta dawo dakin janye da hannun Irfan wanda jikinshi ke kyarma, hannu ya mika mishi yana fadin,,

   zo yaron daddy, meya faru ne?, da muryan kuka ya shige cikin jikin baban nashi yana fadin,,

   daddy i have a scary dream, plss zan kwana a nan, rungume yaron yayi sosai, yana rarrashinsa, ummeetah dake zaune gefensu ta dafa kanshi tana fadin,,

   Irfan kayi addu'an bacci da zaka kwanta?, kanshi ya girgixa alamar a'ah, tace,,

  eyah sorry, laifi nane da ban saka kayi alola ba, yace,,

   sai an sashi yayi, da girmanshi, yaron yace,,

   daddy am sorry, na manta ne, share mai hawaye tayi tana fadin,,

  kayi shiru kaji, tsakiyar gadon ta gyara ya kwantar dashi, sai ajiyar zuciya yake saukewa, da alamu mafarkin mai ban tsoro yayi, ya kamo hannun daddyn yana dorawa bisa damtsen hannunsa da fadin,,

   daddy danne mun nan zafi yake mun, ba musu yayi mishi abin da yace, a haka har bacci ya daukeshi, sosai ya basu tausayi, har suma sun kwanta, saiya jawo wayarshi yana daga hannun rigar cute jallabiyan dake jikin yaron,,

   what, shine abin daya fada yana dan zare ido, da sauri ta dan yunkuro tana fadin,,

   meya faru?, sai daya sauke ajiyar zuciya kafun yace,,

   tabon allura na gani a hannunshi, da mamaki take fadin,,

  allura, yaushe akai mishi allura?, yace,,

   shine nima nake tunani, Irfan ya dade rabon da yayi ciwo, dukkansu shiru su kayi, yana faman shafa waje, ummeetah tace,,

  karka damu, bari safe tayi saika tambayeshi, maybe ko a school ne aka mishi bai fada ba, kanshi ya jinjina alamar gamsuwa da maganarta, kafun ya saki hannun yaron, ta jawoshi sosai tana tofeshi da addu'a tare da gyara mishi blanket, a hankali ta koma ta kwanta,,
  
    haka zaki rika ma twin babys dinmu addu'a ko?, ta tsinkayi muryanshi a cikin duhu, murmushi kawai tayi tana wani lumshe idanu da fadin,,

   bacci nake jie, sai da safe,,

   Allah bamu alkhairi, ya fada a takaice, gaba daya ita da Irfan baccinsu sukeyi, amma shi saiya kasa yana faman sakawa da kwancewa, lokaci lokaci yana kuma duba hannun yaron, har wani baccin barawo yaxo dai ya saceshi.

     Breakfast take jerawa bisa dinning table din, yayin da yake zaune cikin wasu

Please Login or Register in order to submit comment