Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suhymah da fadin,,

  no, a nan zata zauna, a bazata taji maganan, don haka ta dago da sauri tana fadin,,

  what?sadeeq nan wajen yayi mana kadan mu zauna da ita, ka gane mana, idanunta suke neman rikita mishi lissafi, baya son mata musu, amman daya saci kallon ummeetah sai yaji ya daure yana fadin,,

    yess angel kie gane nima, plss ki barta ta zauna a nan din, rayuwan mu mukeyi, tana nata, ina ruwan mu da ita, atleast in tana nan zatafi taimaka miki da wasu ayyukan, shiru ta danyi kafun tayi wani murmushi tana fadin,,

  ouk hakane, amma dole......, tswwww jeki kawai, kafun nan ki dauki Irfan kie kaishi bedroom dinsa, mikewa tayi tana amsa mata, tare da nufa inda yaron ke kwance jikin baban, ya soma cuku cuku dagashi ya mika mata shi, hannunsa ne ya sauka a wani waje lokacin da yake mika mata shi bisa kafada, yayi saurin janye hannunsa, yana yer tsaki,,

  wannan ne dalilin da yasa suhymah ta dago kai tana kallonsa, gaba daya idanunsa sun sanja, tasan yen kayanta, don haka a hankali take bin ummeetah da kallo tun daga kasa har sama,,

  itakam tuni ta kama hanyar dakin Irfan, mamakin girman yarinyan takeyi, kaman za tayi mata magana sai kuma ta basar, kallonta ta dawo dashi kan mijinta dake faman daddauke kai, amma tana ganin last daya gama bin yarinyan da ido, tayi yer dariya sanda ta tuna wani abu da raya,,

  hmm, kayi ka gama, sai gani daga nesa, sadeeq sai suhymah only, amman a fili kuma sai tace,,
  
  hmmm yarinyan tayi girma, an samu waje, kaman wanda aka zuba ma fertilizer, murmushin yake yayi mata, ta gyara zama da fadin,,

    sai dai ina fatan za'a dauke idanu akan koma menene, da mamaki yake kallonta da fadin,,

  kaman yaya?ta daure fuska so serious take fadin,,

   kaman yanda kasan nie suhymah ba'a hadani da wata, sadeeq duk randa wani abu ya faru, ka sani zuciya nane xai buga na mutu, so becareful, dai dai sanda ummeetah taxo wucewa ta bayanta, zata koma nata dakin, shi fatama yake Allah yasa ba taji wannan maganar ba, ita dai ta wuce daki abinta ta maida kofa ta rufe.

   kauda kai kawai yayi da takaicin kalamanta, kufun ya dan tabe baki da fadin,,

    why not, to kisa pad lock kie kulle idanun nawa, dago kai tayi sukai 4yes, kawai sai tasa wani shu'umin dariya tana fadin,,

  haba baby ina kulle idanun, da wanne kuma zaka kalli mrs din naka, a'i na dai riga dana kulle zuciyarka, no need kuma in kulle idanun, hope yhu understand, ta karisa maganar da kashe mishi ido daya, dan tsaki yayi kafun ya mike yana kashe tv, da fadin,,

   to indan kinsan hakane kie daina mun irin wannan bana so, yanxun kie tashi muje mu kwanta, girgixa kai tayi tana cigaba da danna laptop din da fadin,,

  no no no, saina kammala da a'ikina, shiru kawai yayi kafun yayi yer tsaki yana wucewa ciki da tunani kala kala, ba abin da yake ayyanawa sai,,

   anya zai iya zaman aure da suhymah kadai, kaman akwai matsala.



                        ***

    safiyar ranan tayi mata introducing komai da komai, duk wani a'iki daya kamata ta nuna mata, kafun su wuce kitchen, tai mata bayanin yanda zatai amfani da kayan wutan, tana fadin za'a kawo wasu kayan abincin, karta sake tabar mata gida da yunwa, ta gama zagayawa da ita ko ina, sai bedroom dinsu last,,

  sosai ummeetah tayi mamakin abin, sai dai bata tanka ba don karya zamo mata jangwam, ta gama zuba mata ruwan izza, kafun ta kammala nuna mata komai da komai, sauri sauri tasa kai ta fuce daga gidan.

   ummeetah dai bata bata lokaci ba, ta soma gyara ko ina, ta saka sabbin cottons da bed sheet ko wani daki, sanda ta shiga nasu bedroom din, wani abinma kunya take jin musu, tadai gama gyara ko ina tsaf a dadare, tare da wanke banyin dake bedroom din, nanma ta gyarashi sannan ta fuce.

   lokacinne aka danna door bell din gidan, ta futa wani bature ne tsaye da kayan su vegetables, fruit da sauransu, da alamu wanda taji madam dinne tayi order, dama tabar mata kudin, don haka ta bashi kudin, shi kuma ya bata kayan, ciki ta koma ta jera komai inda ya dace, kafun ta kunna hot plate din dake hade da kitchen drower tana daura girki,,

   lokaci kankani gidan ya zagaye da kamshin daddadan girkinta, ta kammala hadaddiyar fried rice din, tana shiryasu cikin wasu warmer, gefe daya kuma ta hada wani sweet fruit salad, ta sanya su cikin wasu salad bowl masu kyau gaske, da suka jima suna fama da kura, sai yaukam suka sami matsayi, ga kuma orange juice din data hada, ita dai a rayuwanta tana son yin girki, don haka ta iya kaloli na abinci iri iri,,

  bisa dinning table ta jera koma, sai ga gida ya zama gida, nata ta zuba a plate ta wuce daki, ta manta rabon da taci abinci sosai haka tun a can gida, kafun Baffanta yayi mata maganan tahowa nan,,

   ta kammala ta koma kitchen, tare da wanke kayan datai amfani dasu, tana maida ko wanne muhallinshi, karan school bus dinsu Irfan ta juyo ya saukeshi, yana faman knowking, wannan yasa ta nufi kofan don ta bude mishi.




*_masu comment&sharhi, ba abin da zance muku sai jazakallah, naji dadi sosai da irin ruwan comment din dana gani a last page dana turo, wannan ya bani tabbacin anayin book din matatace, kuyi hakuri naso ace ina bada daily update, to amma yana iya da nepan nigeria, duk da haka, in sha Allah zan cigaba da iya bakin kokarina, da fatan zaku cigaba da kasancewa da littafin matatace, fatan alkhairi mai yawan gaske_*




comment
share
vote



*matatace 2019*
Na meemartjj               


🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
[14/08, 14:29] Dala Grp: 🕯🕯🕯
*MATATACE*
🕯🕯🕯


story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjj


*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty Ummeetah and my Fa'ixation._

page 33~34

__________Yauma da gudu ya shigo gidan, dakinshi tayi mai wanka, tare da shiryashi tsaf, ya futo ya dauki biscuit harda su chocolate kaman yanda ya saba kullum, tare da nufa kofa zai fice gidan makota, da sauri ta rikoshi ya soma alaman yie kuka don ta sakeshi,

rigima sosai yake, shi tabarshi yaje gidan su misha, neighbour dinsu yaci abinci, daker ta lallashi da jan hannunsa zuwa dinning arean, ganin irin kayan abincin dake jere bisa dinning table din, a'i tuni ya ije kukan, ta bude tana fara zuba mai da murmushinsa yake fadin,,

aunty ummeetah fried rice koh, tace,,

eh za kaci koh?da sauri ya daga kanshi sama, tace,,

to zauna in sama, kujeran ya dane, yana blushing da zubar dasu chocolate din nan kasa, sosai yaci abincin, kafun ya mike ya fice wasansa.

ita ta maida su chocolate din, cikin fridge, tare da gyara inda ya bata, ta maida komai tsaf tsaf, daga nan ta wuce daki don tayi wanka.

***

yau ma a gajiye ya dawo, don,yafi na jiya ma, daker ya iya idda packing din motar ya futo, a duk sanda zai taho gida, to zuciyarsa ne ke kuna, na farko ka dawo gida matarka bata nan, na biyu ga yunwa, na uku ka tarda gida biji biji, kai so many things,,

ya balle murfin motan ya futo, da danjin dama dama, tunda yanxun yarinyan nan tana nan zata kula da wasu wajen, da gaba daya gidan zai dawo ya samu kaca kaca, shikam ya tsani ya dawo gida ya ganshi da datti, yaja dan karamin tsaki, yana kwaso ledojin daya saba dawowa dasu kamar kullum, yayin da briefcase din ke rike dayan hannun, ya nufi cikin gidan.

kai tsaye ya bude kofan yana shiga da sallama ciki ciki, lokacin tana zaune tana idda shiryawa, bata ma jie wani sallaman ba, Irfan ya zuba ma idanu, daya gama cin wasansa, ya kara dawowa ya zuba abinci yana cie, shima kallon daddyn nashi yakeyi, da yashe mishi baki, yana cigaba dai kai spoon daga plate din zuwa bakinshi, a hankali ya tako zuwa dinning arean, da mamaki yake kallon kayan abincin dake jere komai bisa tsari,,

daddy's boy ba oyoyo, meka samu haka mai dadi, ya fada maganar da kallon yaron dake fadin,,

aunty ummeetah ce ta dafa abinci mai dadi ta bani, dan zare ido yayi mai hade da daga gira sama, yana kallon site din dakinta da fadin,,

really?yace,,

yess, daddy and the food is delicious, murmushi yayi yana bin yaron da kallo, dake cin abincinsa cikin farin ciki, ko daga kamshin abincin ma kasan zai dadi, ya dan numfasa da fadin,,

i can see......., karan bude kofan da ummeetah tayi ne ya dakatar dashi, itama sai lokacin taji ihun maganan Irfan, shine ta futo, kyam ya tsaya yana kallonta ta kasan ido tana karisowa inda suke, sanye cikin riga da skirt na lace, kayan dai dai jikinta, tasha daurin ZB sosai da yayi mata kyau, kitson 2steps din nan ya zauna da kyau a gadon bayanta, magananta ya dawo dashi hayyacinsa tana fadin,,

Baffah sannu da zuwa, daker ya iya amsa mata, yana dan basarwa da kuma kallon shigarta na lokaci daya, yana maida idanunsa kan Irfan daya dage wajen bama cikinsa hakki, babban warmer dake wajen ta bude, ta dan zaro ido tana kallon Irfan da fadin,,

Irfan me kayi haka, abincin mummy da daddy ka taba, kana son yau tummynka ya fashe ne da cin abinci?da sauri ya dafe cikinsa yana fadin,,

a'ah bana so tummy na ya fashe, ya karisa maganar kaman zai kuka, a tare sukai dan dariya, yana kallon Irfan din da fadin,,

come on, don't carry, let me go and fresh up, sai inxo in tayaka cie koh, da murmushi ya daga kanshi sama, daga haka yayi hanyar bedroom dinsu, ummeetah na kuma gyara inda Irfan ya bata, tare da komawa daki.



Cak ya tsaya, idanu kawai ya saki yana bin dakin da kallo, musamman gadon daya jie sabon bedsheet, a lailayeshi da kyau, komai need,,

ya salam, ya fada, a zuciya kuma yake raya,,

kenan harnan yau ta shigo ta gyara, briefcase dinshi ya zube bisa gado, yana dan dafe bakinsa da tafin hannu tare da daga kai sama da fadin,,

oh my god, ya cigaba dabin dakin da kallo, har wani kamshin dadi yakeyi, gefe daya kuma wani kunya yajie musu, gani yake wajene dake tattare da sirrinsu, ya danja tsaki da raya,,

kai, suhymah baki yiba, can kuma wani sashin na zuciyarsa na raya mishi,,

to meye, a'i itama matar kace, ya zare suite din dake jikinsa, harda wani yer munafukin smiling so silent yake fadin,,

yess hakane, she is my wive, sai kuma ya soma jera wasu kalolin tunanin, yana faman jan tsaki, shap shap yayi wanka ya shirya, ya futo falon, har yana tuntube wajen yen stairs din dinning arean.

ya zauna da bismillah, gariN rawan jiki ma ya kasa bude warmer, dole sai daya kirata, a natse take yin komai, ta bude tare da fara serving dinshi, ta kasan ido kawai ya zuba mata ido, komai take burgeshi takeyi, ta kammala zuba mai yana jawo plate din fried rice da daukan spoon, sosai yake kallonta da fadin,,

yawwa aunty ummeetah sannu da kokari, dago kanta tayi tana kyalla mishi en idanuwa, wani big smile ya sakar mata, dole yasa itama tai dan murmushi tana barin wajen,,

ya maida hanakalinsa kan abincin dayin bismillah ya fara cin, gaba daya ya shiga rudu saboda dadin abincin, ya fara tunanin to dame tayi girkin ne?, santee kenan, haka dai ya cigaba da ba cikinsa hakki babu wasa, kafun can kuma yaji karan tsayuwar motar matarsa da surutunta da makota.

tafi 5minutes kafun ta shigo da kayan wasu paper bags a hannunta tana fadin,,

sweetheart, ta zube paper bags din bisa cushion, tare da bubbude ledojin daya shigo dasu daxu ya zube a wajen yama manta dasu, ta kariso inda yake tana fadin,,

sweetheart me yasa ka bata kudinka, yarinyan nan batai girki bane? turus tayi da kallon hadadan abincin dake cikin plate din, da murmushi ta jawo kujeran kusa dashi tana zama da fadin,,

wow am hungry wlhy, wannan ma kai ka siyo, ta karisa maganan tana kallonsa, kai ya kada mata, kafun ya dibo abincin a spoon yana kaiwa bakinta, ta bude baki ta amshe, shi kuma yana bata amsa da fadin,,

a'ah, shima wacan basan kinsa ayi wannan bane, shi yasa na taho,dashi, tayi wani far da ido kafun tace,,

eyyaah, kaga yanxun bamu da matsalan abinci, sai ka daina shiga restaurant daga yau ko baby, mun gama da wannan matsalar, murmushin yake yake mata, da fadin,,

hakane, itama ta dibo abincin zata mika mishi, da sauri yake fadin,,

no Alhamdulillah, just go on, ta wani daga gira sama, cike da enjoying abincin take cigaba da cie, ya mike yana zuba orange juice din cikin wani glass cup, tare da komawa seating room ya zauna da wani irin nishadi,,

ya mance rabon daya cie abinci irin haka, tun mrs ango na kusa dasu inta kawo musu daddadan abincinta, sosai ya kishingida jikin kujeran, da daura kafa daya kan daya, duk sip daya saiya kalli sashin dakinta yana faman zambada mata albarka.

Daren ranan ma, ummeetah ta dada kashesu da wani salon abincin nata, har mamaki matarsa ta rika yie, shi da ba ma'obacin cin abinci dare ba, amma tana mamakin wanda yaci yau, (ah dama be samu bane) shidai murmushi kawai ya mata,,

safen ranan sai da kowa yayi breakfast sannan suka futa, a yanxun har mamakin kanshi yake, yanda yake rawan jikin ya dawo gida a kullum ya tafi office, sabanin can da, da kwata kwata baya son tuna wani abi mai suna komawa gida.



***

yauma daya kasance safiyar weekend, kitchen take tana ta faman hada breakfast, banda kamshi ba abin da gidan keyi, ita kanta madam dake daki abin na debota, dama sakin ciki take taci abinci son ranta, duk ta kosa girkin ya kammala, karshe ma falo ta dawo ta zauna kafa daya kan daya, tana jiran baiwa ta sauke taci,,

ta dan dauki lokaci yau a kitchen din, har tana tunanin kome ta tsaya yine, tana shirin kwala mata kira ne, sai gata da kaya sosai, ta soma shirya dinning din kamar yanda ta saba, ta gama ta koma kitchen sai gata da falsk mai kyau, shima ta mishi waje na musamman, dai dai saitin kujeran data lura me gidan ya saba zama,,

dai dai sanda ya budo kofan suka shigo da sallama, sanye cikin wasu sport wears masu tsada, dark green, komai iri daya dana danshi, harta goran ruwa dake hannunsu iri daya, sai dai na hannunsa babbane, yayin dana hannun Irfan ya kasance karami dan dai dai, da alama morning exercise suka je suka dawo, ummeetah da bata raina abin kallo ta tsaya tana binsu da ido, sosai suke burgeta in suka sa kaya iri daya, kaman daga sama taji wani tsawa tana fadin,,

madam!firgit ta juyo da kallonta gareta tana wani yer harara da fadin,,

excuse me, me kike kallo ne?girgixa kanta tayi da fadin,,

bakomai, ta zabga mata uwar harara da fadin,,

oya do ur work, daga haka ta cigaba da latse latsen wayarta, Irfan ne ya taho dinning din da gudu, yana kokarin kai hannu cikin abincin, da sauri ta rike hannunsa tana fadin,,

no, ka bari ka wanke hannunka first, daga haka ta jashi zuwa kitchen, ta kasan ido ya bita da kallo harta wuce, ya dan numfasa yana nufa bedroom, ta dago kai da mika mishi hannu tana fadin,,

baby welcum,,

thanks ya fada ba wani walwala, yana mika mata hannu suka dan kashe, daga haka ya wuce ciki, yana kokarin cire jacket din dake saman kayan.

sosai ta zuba ma dinning table din ido, bakinta a tabe, tana wani yatsina fuska, Irfan dai tuni ya fara cin abincinsa, dai dai sanda ya iso dinning din, har yai wanka ya shirya cikin wasu kananan kaya, da murmushi yake fadin,,

wow so beautiful, ta dan dubeshi ko ita mace ya burgeta, sai dai kishi, don yau dishes din na daban ne, ya jawo wata plate mai dauke da glass cover, ta cikin murfin yake bin kwan da su kayi shape din queens cake, sunyi kyau sosai, ya dan dubeta da murmushi yana fadin,,

angel wannan fa, meye sunan shi? tabe baki ta kuma yie, tana budewa da dan tattabawa kafun tace,,

umm, gayinan dai egg ne kaman, dan murmushi yayi, ya gane bata san ko menene ba, Irfan yace,,

daddy egg costard, haka aunty ummeetah tace sunan sa, yace,,

wow yayi kyau, ya maida ya ije yana cigaba da bin sauran abincin da kallo, dogon tsaki taja ya dan kalleta da fadin,,

what's going on?,,

abincine naga yayi yawa, bana son banar abinci, ban fiye son iyayi da yawa ba, don haka dole ta gyara, yai dan shiru kafun yace,,

ouk yanxun dai ya kamata muyi test kafun nan, ba bata lokaci ya soma zuba serving dinta da kanshi, sanda suka fara cin abincin, lukus yaji bakinta, can ya dan dakata da fadin,,

so yadin?murmushin yake tayi da da daga kafada tana fadin,,

anyway, ita taga zata iya, saitai tatayi, sosai taso bashi dariya, dan murmushi yayi da girgixa kai, lamarin suhymah sai du'ai, ta daure fuska da fadin,,

what's funny kuma?,,

nothing ya fada da dan rankwafar da kanshi yana daukan fork din dake gabansa, kafun ya cigaba da cin abincinsa, can kuma ta jawo flask din dake kusa dashi tana fadin,,

wannan fa?ta bude, sosai ta taba fuska da kallonsa tana nuna mai da fadin,,

baby meye wannan?shima sosai yasa murmushi yana amsan flask din da fadin,,

oh my god, tamba ne, suhymah favourite kunu nane fa, ya jawo wani cup yana kokarin zubawa da fadin,,

i wonder where she got the ingredient, tabe baki ta kuma yie, Irfan na fadin,,

daddy nima inaso in sha, ya ja wani karamin cup yana zuba mishi, shiru tayi, kawai saita ije fork din hannunta da fadawa duniyar tunani, can kuma kaman an tsunguleta ta kalleshi da fadin,,

ya akayi tasan favourite dinka ne?ko a jikinsa yake fadin,,

ban sani ba,,

ummeetah, ummeetah, shine abin data shiga kwala mata kira, da sauri ta futo daga kitchen din, sanye da karamin hijjab din da take sawa in zata a'iki,,

aunty suhymah gani, rai a dagule take fadin,,

ina kika samo wannan tamba yake kome, sannan ya akayi kika san favourite din mijina ne?kyam ya tsaya da kallonsa kasa kasa kan ummeetah dake dan gyara wuyan hijjabin, hannunta duk flower, yai dan murmushin takaici hali irin na matarsa,,

karaf suka hada ido, da idanu yake mata bayanin abu a fuskanta, yasa dan yatsansa yana mata alamar a kuncinsa, a hankali tasa hannu tana dan goge kumatunta, kallonta suhymah takai kan mijinta, yayi saurin wani waskewa, kafun ta maida hankalinta kan ummeetah dake magana cikin natsuwa, da fadin,,

nie bansan favourite dinshi bane, kuma maami ce ta bani in taho mai dashi, ta sauke wata ajiyar zuciya tana dukawa da cigaba da cin abincinta take fadin,,

is better, shikam sai yayi murmushi da fadin,,

Allah sarki maami nah, Allah ya saka ma uwa mai son danta haka da alkhairi, infact my special thanks goes to all A'isha Humaira in the whole world, ya karisa maganar yana kallonta sosai da murmushi, kafun ya dan waske,,

itama murmushinta ta gintse da satan kallon site din da madam suhymah take hakince, da alama ta manta wani abu, kadan ta dan kalli mijin nata tana murmushin yake, a zuciya take zambada ma uwar mijin zagi son ranta, juyawa tayi zata koma kitchen, taji yace,,

ummee look, ta juyo yana karisa fadin,,

plss a lallaba wannan, saboda ramadan dake zuwa, ina son kunun taba sosai, karaf tace,,

sweetheart saika wani tsaya rokanta, dole za tayi, ta maida hankalinta sosai kan ummeetah tana cigaba da fadin,,

ki tabbatar mijina bai rasa komai ba, daya bukata, daga shi har ita mamakin kalamanta sukeyi, ta daure da fadin,,

toh in sha Allah, tabe baki ta kuma yie tana cigaba da cin abincinta, shima ya cigaba da enjoying kunun dake faman kamshin gyada, da sauran kayan hadi, da yaji na musamman.

***

Haka ummeetah ta cigaba da rayuwan gidan, ba laifi tana jin dadin zaman gidan, don matar gidan bata fiye zama ba, bare ta fiye takura mata, ayyukan gidan kuma ba wasu masu yawa bane, matsalarta daya shine ta gaji da zaman waje daya, don kullum daga cikin gida sai compound din gidan inta futa, kafun wani dan lokaci ta sanja, sosai ta kara cika, da girma mai tsafta, harta skin colour dinta ya sanja, hankalinta kwance take rayuwan gidan.


Yau ta kasance wata friday, da wuri ta kammala ayyukanta, wanka tayo ta kuma gyara kanta, yau cikin wani real fulani dress ta shirya, riga da zaninsa, sai ta saka wata farar top a cikinta, rigar fulanin daya kasance armless amman ya sauka har kasan cibinta, dai dai lent din riga,,

dan tsaki tayi bata fiye son taga kaya ya kamata ba, da yike kayan ya dan jima, tun suna js2, da su kayi wani cultural dance na seniors dinsu da zasu futa, kayan yana mata kyau sosai, saita futo a usulin fulaninta, wasu da basu san fulani girl bane, a wancan ranan tasha surutun, kaman fulanin gaske, ita dai kawai sai dai tai musu murmushi,,

yauma kam tayi kyau sosai, komai ya zauna masha Allah, ta gyara packing din kitson kalaban data ma kanta, tare da ziraro da yen guda biyu ta gaba, daya sauko har kasan wuyanta, ta maida wata yer black viel ta yafa,,

samun kanta tayi da zizara wetlips din da kullum ke ije bisa mirror, sabanin wani lokacin da iyakanta kajol a ido, ko powder, nan kuwa labba suka dauka dau, ta mike tana kuma gyara dakin nata, door bell ta jiyo yana faman kara sosai,,

da sauri ta futo, tana kallon agogon dake jikin bango, dai dai lokacin da Baffanta ke dawowa ne yau, don haka kai tsaye ta wuce don ta bude mishi, cak kuma ta tsaya bakin kofan, tunawa da tayi, kai tsaye shi yake shigowa, don haka tayi tunanin ta leka tukuna, ilai kuwa bashi ta gani ba,,

wani kyararran namiji ne, fari kyakywa, bata inda be haduba, shima zai iya kaiwa sa'anin Baffanta, sai dai tana tunanin ko shima dan nigeria ne, don farin fatar shine yayi yawa, shi yasa take wasi wasi, juyawa kuma tayi, sauri sauri ta koma daki ta sako wani hijjab dinta har kasan gwiwa, sannan ta dawo donta bude kofan.

tana bude kofan yana fadin,,

sorry na dame ku ko...... cak ya tsaya kuma da maganar yana fadin,,

wait fulani girl right?ya karisa maganar da kallon kasan zaninta, sai da tai dan war kafun ta dan gyada kanta da fadin,,

eh, sosai yake murmushi da fadin,,

masha Allah yer uwa nah, but amma ya bansan kiba?ya karisa maganar da dan mamaki, shiru ummeetah tayi da rasa me zata cemai, ya cigaba da zubo surutu yana fadin,,

ko ke siste......, sai kuma yayi dan murmushi da fadin,,

ooh sorry, na dameki da surutu ko? haka nake i talk too much, amma mai amfani fa, naxo ganin mai gidan ne, hope yana nan, sai lokacin ta sauke ajiyar zuciya da fadin,,

Baffah sadeeq?yayi dan dara dara da ido da fadin,,

Baffah?da sauri take fadin,,

oh sorry, i mean uncle sadeeq, magananta kanshi abin burgewa ne, a zuciya yake raya,,

wow i like her skin colour, kafun yace,,

ouk uncle din kine?

eh, ta fada da daurawa da fadin,,

kuma baya nan, dan murmushi yayi yana fadin,,

na dame kie da surutu ko?toh na tafi, inya dawo kice DR. khamis ne yaxo, karki manta sunan fa khamisss, sai anjima baby fulani,,

to sai anjima, ta fada a hankali tana komawa ciki da rufo kofan, ajiyar zuciya ta sauke da dan girgixa kanta, kafun ta wuce daki.

***
ya dada murza kan steery yana sakin wani murmushin kan fuska, sosai yake jin dadim motar tasa, da kullum take cikin sanyi da kamshi mai dadi, gefe daya ga wankar Mshareef dake tashi so cool, mai taken _kin hadu enmmata,,_

ya dan gyara seat belt din daya dan matseshi, yana cigaba da driving dinsa cikin kwanciyar hankali, tare da sakin murmushin mai sauti time to time, ba aba abin da yake tunawa sai dadaddan kamshin abincinta da kullum yake masa sallama, da kuma sassanyan kamshin freshner dake zagaye da gidan da yaji tsafta, sosai gidansa ya canxa zuwanta, kai harta Irfan ya rage futa yawo gidajan makota, ga karatun addinin daya fara rike bakinsa, musamman karatun al~qur'an,,

dama shine mai koya mai, wani lokacin kuma bashi da time, kullum kuma cikin wakan zai sanya

Please Login or Register in order to submit comment