Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
_*KUSKURE NA*_πŸ™†
_Love & Destiny_


*Written by Fenerh*

✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER'S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍

❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our words, for it will cause you no pain_❄



https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


_Am back again my fan's , da fatan anyi Salla lfy ina Addu'ar Allah ya karbi ibadun mu Albarka cin Annabi da Al Qur'ani Ameen_

_Alherin Allah ya kaimu ku masoya littafai na ina Alfahari da dukkan masoyana dafatan zakuci gaba da karfafamin guiwa kamar koda yaushe'_

_"Kamar koda yaushe Na kuma dawo muku cikin wani sabon littafi Na mai suna KUSKURENA Wanda yake kunshe da zazzafar soyayya da kuma kaddara, dukkan cikakken musulmi dole ya dauki kaddarar rayuwar shi mai kyau ko Mara kyau sai dai muce Allah ya bamu i kon cinye namu jara bawoyin Ameen'_


_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah s.w.t da ya bani ikon ci gaba da rubuta muku sabon littafi na Allah ka kara dad'in tsira ga Annabin Mu Muhammad s.a.w_





*Da sunan Allah mai Rahama mai jink'ai*


πŸ…Ώβž‘1⃣
"Ummu Ummu""""' shine kiran da yayi sanadi yar farka warta da ga d'addad'an baccin da takeyi mai cikeda mafarkai masu dad'in gaske'


" Ahankali ta ke ware idanunta tana kallon wadda ke tsaye a kanta"


"Cikeda shagwaba tace " kai Hajiya yanzu bazaki barni inyi baccin ba bayan jiya dak'yar mutanen ki suka barni na runtsa"


"Hajiyar tace " ke wai bakya gajiya da bacci ne A rayuwar ki Ummu? Ta turo dan bakinta "Hajiya Ummu Ruman meye wani Ummu? Bawani dadi Kamar tsohuwa'


" toh naji yanzu dai kitashi ki shirya ko bazakije maka rantar bane yau?

"wani irin zaburowa tayi Kamar zata tun tsira tunawa da yau tanada lecture karfe bakwai kuma lecturer din ba mutunci ko kadan'


" Ta dubi a gogo ' na shiga uku Hajiya kika ki tashina da wuri gashi zanyi latti. " sarkin mita yanzu inace cewa kikayi bana son ki huta ?


"Nidai ki zabomin kaya kafin in watsa ruwa ta cire hijabin dake jikinta ta wurgar tareda kwasawa a guje tayi waje Hajiya na faman cewa'


" kinsan Akwai jama'a ko idan wani ya ganki Kamar diyar arna fa Gaki tubarkalla duwaiwai Kamar masaki 'daga wajen tace " wurin ki na gada ai keda ke tafiya dakyar saboda kiba'


"Nagode kya fito ki zabo kayanki shiryayya ' bata dai fitaba ta zabo mata Riga da zani shiga dai ta hausawa tareda hijabin da zai shiga da kayan ta fara gyara mata gadon tareda nannade hijabin data wurgar a kasa


" A guje ta shigo daure da towel Wanda ko haduwa bai gama yiba a kirjinta " Hajiya tace " Amma Ummu kun raba hanya keda kunya ' yanzu a haka kika ratso tsakar gidan nan?


"Idan wani ya ganki fa kuma kinsan gidan mu kowa shigowa yakeyi tunda ina Sana'a'

" toh ni ina ruwana da mutane nida gidan mu zanrika kame kame' ""aa Ummu gidana dai gidanku ai kinsan inda yake'


" Ni dai nan ne gidan mu tunda gidan kakata ne mai sona " ta rungumota cikeda so irin na jika da kakan da suka shaku '


"Cikin minti da bai wuce biyar ba ta shirya tareda daukar Jakarta ta rataya ta kuma zura hijabin ta

Hajiya ta zaro kudi a gefen zaninta ungo ki hau achaba Allah ya tsare ki daga sharrin mutum da Aljan


Ta karba tareda godiya bata tsaya wata kwalliyaba mai kawai ta shafa tadan murza powder tafito abinta shar Kamar ba jami'a zata ba takalminta plat ta zura tafita cikeda sauri duk da tasan tayi latti batason lecture ya wuceta'


"A kofar gidan kuwa mutane ne dankam masu jiran Abinci kasan cewar sana'ar kakar tata kenan wadda da ita suke samun rufin Asiri kuma Allah yasa ma lamarin ta hannu komai basu nema sun rasa ba'


*JIGON LABARI*

Hajiya kaka mai Abinci tsohuwa ce da Allah ya jarabceta da haihuwar da daya tilo Wanda shine mahaifin Ummu Ruman Wanda mahaifin shi yarasu tun yana karami Hajiya kaka ita tayi ta dawai niya da danta batareda gazawa ba tayi wani Auren bayan rasuwar mijinta Wanda suka dauki kusan Shekara Ashirin batareda ta kuma haihuwaba har Allah ya dauki ranshi shima A lokacin ta Aurar da tilon d'an nata hadin zumunci ne da y'ar kanwarta wadda itama Allah ya dauki rayuwarta a sanadiyyar haihuwar Ummu Ruman '

Sunji mutuwar baiwar Allahr nan sosai kasan cewarta mace mai hakuri domin mijinta yayi Alfahari da Aurenta mace mai tawakkali da kaunar mahaifiyar shi'

Alhaji Muhammad saida ya dauki shekaru kafin ya kara Aure don gaba daya kaurace ma Garin nasu yayi wato Zaria ya koma Kaduna da zama yaci gaba da kasuwancin shi kafin daga baya ya samu wata mata sukayi Aure A halin yanzu yana da yara kusan biyar tareda ita


"Tun lokacin da Alhaji Muhammad ya Auri bilkisu komai ya canja A rayuwar Hajiya kaka don gaba daya mantawa yayi daita da tilon marainiyar y'ar shi,


A dole ta mike tafara Sana'a domin cikawa jikanyar ta burin ganin tayi karatu mai zurfi,

" Hajiya kaka tana zaune ne a layin Banaden dake kusa da kwango A cikin tudun wadan Zaria


Gidane mai dan girma irin na talaka mai daukeda da kuna kusan goma Wanda take zuba dalibai suna biyan haya Amma dakunan duk suna kallon waje ba sosai sukan shigo cikin gidan ba kasan cewar su dalibai sukuma suna zaune a ta cikin gidan mai daukeda ciki biyu da falo Wanda daya Ummu Ruman ke zama daya kuma na Hajiya kaka

Ba laifi komai suna samu najin dad'in Rayuwa da sana'ar Abincin da takeyi tanada tsofaffi masu tayata yin komai suma tana biyansu

Arayuwa Ummu Ruman ta tsani wannan Sana'a ta Abinci domin irin kattin dake taruwar musu akofar gida wai su suna siyan Abinci saboda Akwai runfa an jera kujerun katako tako ina Kamar wani restaurant


"A kullum Addu'ar ta tazama wani Abu idan tagama karatu ta taimaki y'ar kakarta

Ummu Ruman yarinyace mai diri chocolate colour mai tsada tanada dan tsawo fatar ta sumul sumul Kamar mai Rayuwa a cikin A.c ga wani dimple mai zurfi Wanda ko motsa bakinta tayi sai ya zurma kyakkawa ce tubarkalla wadda mafi yawan cin kawayenta ke kiranta da African Queen saboda kalar fatar ta mai sheki,

" Tayi karatunta a zenith primary & secondary dake unguwar kaya cikin ikon Allah tasamu sauke qur ani kafin ta fara zuwa F.c.e Zaria


Abu biyu yake ci mata tuwo a kwarya A rayuwar ta rashin kulawar mahaifinta da kuma rashin mijin da zata iya Aure ita kadai tasan irin damuwar datake ciki bawai ta rasa masu sonta bane aa ita kawai har yau bataga irin mijin datake buri bane don ita Sam ta tsani Auren karamin yaro gwara dan talatin da wani Abu zuwa Arba'in


"don gani n take yi tafi karfin karamin yaro ita kam shiyasa duk Wanda ya nemi kulata bata bashi fuska Sam saboda gudun raini

" Damuwar ta babbace domin Allah ya jarabceta da muguwar jaraba wadda ba kowace ya mace bace zata' iya daurewa ba ta kuma kame kanta musamman ita dake goyon kaka Ummu nada tsananin kula da kuma kiyayewa domin tana gudun Abinda zai janyoma kakarta shiga damuwa,
Karfin feelings dinta bai janyo mata fadawa cikin halaka ba saima kara kusanto ta da ubangiji Wanda a kullum take kokarin yin Azumi tareda Addu'ar Allah ya yaye mata wanna damuwar da ba maiyimata maga ninta sai Allah


"wann matsalar ko Hajiya kaka bata San ta da itaba domin duk rashin kunyar datake nuna mata bazata iya bari tasan wannan ba'

*Cigaban labari*


Allah ya taimake ta har ta isa bai shigoba tafada cikin kawayenta masu faman kwala mata kira Queen"""


"Daya daga cikin su wadda duk kusan sa anni ne da Ummu duk bazasu wuce Shekara Ashirin ba mai suna hajara tace " kai guys yau naga wani lafiyayyan yaro under twenty ya jiku da kudi da kuma tsantsar kyau kana ganin shi kaga Hutu da kuma class ina fada muku gayen first class ne wlh kai banma tunanin bahaushe ne dan nijeriya ,


"Gaba dayansu suka juyo domin jin zancen saurayi dan karami mai kuma kyau da kudi suna rige rigen tanbayarta " kai Sumy A ina don Allah ita dai Ruman juya musu baya tayi don basuda zance saina kana nan yara masu sauke wando a duwawu'


"Kudai kubari wlh a kofar shigo wata nan naganshi ya tsaya a jikin wata Arniyar mota harda body guard dinshi kai wallahi yaron ya hadu ban Masan irin kwatancen da zan muku ba gashi a lambar motar an rubuta *J 3* wlh nayi karshen gani yau"


"Shigowar malamin yasasu yin shiru domin baya wasa ko kadan suka fara daukar lecture


" Ana gamawa ta mike cikin sauri domin tasan halin kawayen nata basuda aiki sai zancen kananan yara bare sun samu sabon labari yau ai ba sauki

Tana fitowa taga duk su napep din sun ciccika gashi da yake Antashi ko ta ina ba mashina gudun kar su kuma biyota da zancen yasa tafara takawa tafe take tana nazarin Rayuwa da kuma damuwar ta kanta a kasa tafara jin kanshin wani Azababben turare


Batareda ta damuba taci gaba da takunta still kamshin na karuwa bata damu tasan ko na wayeba domin tasan tana kusa da Congo Akwai dalibai kala kala yayan masu da shi '


"Dady pls I don't want to stay in the hotel'and pls Dady tell ur body guard to stop following me I don't like it


" Taji wata irin murya mai dadi tana fada tasan kuma a waya ne ake maganar haka kawai taji tanason ganin mai muryar domin muryace mai dad'in sauraren

"Tana dagowa tayi saurin dauke kanta domin ganin exact gayenda hajara kebada labarin kamannin shi dazu ta ya tsina fuska saboda tana ganin shi tasan yarone saidai ace girman Hutu da kuma jin dadi '


Tayi wucewarta batareda ta kuma wai wayo shiba shikuwa saida ya katse kiran domin irin fuskar da ya gani a kusa dashi irin fuskar da yake mafarki a kullum take hanashi sukuni har tayi sanadi y'ar barowar kasarshi zuwa nan ko zai samu matsuwa fuskar da sanadinta yafara balaga yau a gabanshi ""


Wani irin juyowa yayi "Amma me bai ga koda inuwar ta ba ta bace bat

" wata irin razana yayi tareda bugawa bodyguard din dake kusa dashi tsawa " ware is she???? Yafada cikin karaji'


"Who are you talking A bout? "My dream girl " she is here right now we're did she go?

Ya buga musu tsawa ""find her 'tareda dafe kamshi ya jefar da wayar hannun shi hankalin shi yayi mugun tashi '


" Haka suka gama dube dube suka hakura don ta bace musu bat cikin motarshi yafada tareda dafe kanshi dake mugun bugawa "shikadai yasan halinda zuciyar shi take ciki"


"Umma kuwa mashin ta haye batareda bata lokaci ba yakarasa da ita gidan su'


" tundaga nesa tafara hango jama'a a kofar gidan su ranta yafara baci domin itadai ta tsani sana'ar abin cin nan gashi ba halin ta wuce sai sun samata idanu"


"Daga nesa ta sauka ta sallami mai mashin din sannan ta karasa kanta a kasa batareda ta kalli kowaba tayi shigewar ta cikin gidan"


"Cikin ma masu Aikin Hajiya kaka sunata hidimar sallamar mutane suka fara gaishe ta'


" Cikin falon kawai ta fada ta samu Hajiya nata kirgar kudin cinikin ta gefen ta kuma wani kaninta ne da Ake kira magaji dan uwanta ne na jini duk wani Abu shi yake yimata itama tana taimakon shi sosai"


"Da sallamar ta ta shiga,
Ta gaida magajin sannan ta zauna gefen Hajiya tareda cewa" wash nagaji wlh ' toh sannu kinji yar Albarka tashi ga Abin cin ki nan ta janyo wata y'ar kula ta tura mata a gabanta


" Kamar kinsan yunwa nakeji wlh banci komai ba yau a makaranta" ta bude kular ta fara cin Alkubus dinta datake bala in kauna'



"Hajiya tace " magaji yanzu dole sai an hade mai da kuna biyun zai zauna? eh yaya kawai ki y'arda tunda ga dan fili har bayan gida sai Ayimin taciki na fada miki bature ne ba karamin kudi zai saki ba "


"Tunda kinga su kulu zasu tashi sai a hade ginin kuma bako kwandalar ki " toh magaji Allah ya taimaka na Amince"


"Ita dai Sam bata fahimci me suke fada ba ' Abincinta kawai takeci don bata wani son yin magana da magajin'



" Sai bayan tayi Salla tayi wanka tareda zura yar wata doguwar Riga mai Kamar rigar bacci don mugun zafi takeji yau ta sanya hular net a kanta domin kan yasha iska don ta jikoshi da ruwa bai gama bushewa ba"


"Ta karaso kusa da Hajiya " wai ni kaka me Magaji ke magana akai?


"Kedai wai wani bature ne ya nace inbashi hayar daki biyu yanaso ya zauna nadan lokaci ba yason zaman hotel" kuma zai gyara da kanshi ni banaso kinsan magaji da naci da kuma shegen son kudin tsiya "


"Kudai wallahi bazaku bar mutane su hutaba yaushe muka samu muka kori inya muri yanzu kuma bature "?


" Shima idan yace zai mana rashin hankali ai dole yabarmin gidana "


"Shiru kawai Umma Ruman tayi domin Abin nasu yafara isarta daga wannan sai wannan"




"Washe gari kam da wuri ta tashi ta yi musu gyare gyaren dakunan su don ba ruwanta da tsakar gidan don Akwai masu Aikin Abinci ga kuma yan hayar Hajiya


" Tayi wanka ta fito tsab tareda karbar kudi wurin Hajiya sannan ta wucewarta F.c.e'


"Addu'a takeyi Allah yakawo musu dauki A rayuwar su "


"Yauma daga isarta kawayen ta suka fara tarar ta da zancen wannan saurayin " tayi kicin kicin " Kudai wlh kunaban kunya dan wannan yaron ne kuke wa wannan rawar jikin?


"Ke yaro da kudi babbane Nidai na mato wlh " inji hajara "Sumy tace " nima dai tun banganshi ba naji a gaskiya ya burgeni kinsan ni da kaunar sabon jini "


"Allah ya kyauta soyayya da kana nan yara ko raini nifa wlh natsani kula jarirai " suka sheke da dariya harda tafawa "hajara tace " wlh ki bar raina Allura karfe ce ke baki karanta littafi da nace kije ki karanta labarin namiji baya kadan"


"Na Aisha Ali garkuwa kiji Aikin yara " Kudai kula sani da yawarku baruwana da shirme "


"Yau kuwa suna tashi suka ce binta zasuyi domin suna son suci Abin cin Hajiya kaka dama hakan sukeyi wani lokacin " Sumy tace Hajara kinsan bazata hau motar ki ba muje ta same mu


"Tace toh gobara yau zan hau muje kawata " baki suka saki gaba dayan su suna kallon ta domin tun tsawon zaman su bata taba y'arda ta hau motar kowace kawa"


"Kuma yanada nasaba da irin hudubar Hajiya da kullum take fadamata ta kiyaye bin yaran masu maiko don gujewa wulakanci Amma a gaskiya. Ta fahimce hajara na matukar kaunar ta sosai'


" Hajara iyayenta masu haline sosai mahaifin ta na aiki a karkashin matatar mai dake Kaduna wato NNPC Allah ne ya hada kaunar su da Sumayya da kuma Ummu Ruman, Sumy itama ba laifi mahaifinta dan kasuwa ne sunada nasu rufin Asirin '


"Suna isowa kofar gidan ta bude ta fito Sumayya ma haka hajara ce ta karshen gaba daya sa idawan kofar gidan Hajiya suka watso masu ido suna mamakin daman kawayen wannan mai girman kanne?


" Sudai wucewarsu sukayi cikin gidan suna tafe suna raha irin ta kawaye,



Wani daga cikin yan zaman kashe wando yace " a gaskiya Allah yayi halitta a nan kasan saboda kawai inrika ganin Babyn nan nake zama kofar gidan nan'


Shima na kusa dashi yace wlh nima haka nifa ganinta kawai ya wadatar dani can ma wani yaci "ai Hajiya ta ajiye Diamond wlh irin wannan kayan ai mutum dole ya huta


" Kaifa dan iska ne ina zaka kai wannan mai girman kan tsiyar wlh ko iya tunkarar ta bazakayi ba domin Allah ya mata kwarjini da yawa'


Anan dai sukayita surutan su sukuwa sunkule cikin dakin Hajiya sai kwasar gara sukeyi don Abin cin gargajiya yayi a Rayuwa'


"Sunata zabga shaftar su " Hajiya na gefen su tana dariya domin tana kaunar su har cikin zuciyar ta don suna son tilon jininta Hajara tace " kakus don Allah Kice Ruman taje gidan mu '

"Saidai mu muyita zuwa Amma ita bata taba leka gidan mu ba " toh Kuyi hakuri kawar takuce murdaddiya kunsani sai hakuri

"Toh Nidai Hajiya yayana zai dawo daga America next week wlh dole tazo domin zamu hadamai walimar kammala karatu nshi idan bata zoba zanyi fushi da ita


" toh ai kunfi kusa nawa idone, saida suka yi kat suka sauke farali Ruman ta rakasu suka wuce domin Sumy na kofar doka ne ita kuma hajara GRA saita sauke Sumy zata wuce gida"




"J kuwa Kamar yadda nagani a jikin motar shi yau ma ya dade a wurinda yaga dream girl dinshi jiya Amma har yamma shiru haka dole ya hakura ya kara gaba tareda damuwa mai tarin yawa


" Domin jiya baiyi bacci ba kwana yayi yana tunanin fuskar ta da yagani a fisge tafi kyau a reality she is damn beautiful ya dafe saitin zuciyar shi yana mai hango tsantsar kyanta da yagani ga wani kallo data aikomai mai tsaya wa a zuciya'

Juyi kawai yakeyi yana dafe cikin shi Wanda yazamar mai farilla a duk lokacin da zai tuna dream girl dinshi "



Bayan kwana biyu an gama gyara ko ina na gidan Hajiya kaka ita kanta mamaki takeyi waye wannan yake hasarar kudin shi shida ba dadewa zaiyi ba"


An baza tile's har tsakar gidan hardasu A.C ga wata solar da suka wani kafa gudun matsalar nefa Ruman ma cewa tayi hasa rarre ne kowaye '


"Yau da wuri suka tashi kasan cewar jumu'a ce tana sauri ta sallami su hajara domin tanaso ta danyi shopping a inna idea shopping complex Hajiya ta bata dubu biyar


" domin tanada bukatar wasu Abubuwan "


"tundaga bakin plaza din taga wasu motoci a Jere guda uku masu matukar daukar ido farare tas bata kuma bi takansu ba ta shige wajen Cosmetic's Tafara siyan turarukanta da kuma manta a kullum'



Ta gama ta biya tareda daukar ledarta ta fice " kanta a kasa take tafiyar ta domin ta tsani hada ido da mutane don ana yawan fada mata wai idanunta na daukar hankalin mutane'


"Jin kawai tayi tayi karo da mutum har ledar ta tafadi kasa " cikeda masifa ta dago tafara zazzaga balai "


"are you blind? Kuna tafe bakwa kallon gabanku sai shegen kallon mata tun baku tafasa ba zaku kone gari' tunda tafara magana bakinta kawai yake kallo da gefen kuma tun ta dake lobawa ga sexy eye's dinta har wani sheki sukeyi gaba daya ya shagala da kallon ta



" Har ta duka ta kwashi kayanta tayi gaba bai dawo hayya cin shiba "wani irin firgita yayi ya fisgo numfashi tareda waiga wa yau ma Kamar walkiya ta bace'


Ita kuwa tagane shi sarai shine mutumin hajara kuma w'anda tagani ranar nan " mai shegen kallo ta yi tsaki mtswwww ......✍


*hope u are enjoying my story fan's?*


_*MATAR SOJA*_
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
_*KUSKURE NA*_πŸ™†
_Love & Destiny_


*written by Fenerh*

~Dedicated to~
All my fan's

✍✍✍✍✍✍✍
_GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION_
✍✍✍✍✍✍✍

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

πŸ…Ώβž‘2⃣

"Tunda ya fito yake waigen inda zai ganta Amma ko walkiyarta bai gani ba "

Cikin motar shi kawai ya fada tareda dafe goshin shi yana mai fitar da hawaye masu zafi'

Saida ya dade yana jinyar zuciyar shi kafin kafin yabasu umarnin tafiya'

I pad dinshi ya bude tareda dialing number wadda naga an rubuta *Momy me*


"Tana received ya saka mata kuka gashi suna ganin juna da yake video call ya kirata"

Wata mace nagani kyakkyawa duk da a cikin waya ne ina ganin ta nasan ta gama haduwa tareda mallakar Hutu na garari"


"Kuka kawai ya saka mata kamar wani jariri " gaba daya rikicewa tayi tafara tanbayar shi " what's wrong my baby??

"Why are you crying? Da kyar ya saita kanshi tareda furta" I saw her a gain Momy ""


"Then why are you crying ? "She is gone again momy I lost her again """


"Cikeda kulawa tareda karfafa mai guiwa take tausar shi da cewar kar ya damu zai ganta "


"Duk hankalin ta ya tashi bata kaunar bacin ran gudan jinin ta




*Ummu Ruman*
" Tana fitowa mashin ta haye ta wuce gida Abinta hankali kwance batareda tunanin komai ba"


"Tana isa ta samu mutanen nata wato sa idawan unguwar kamar kullum ta shige warta cikin gida batareda tace musu tak ba "


Masu Aikin Abincin Hajiya sai sannu suke yimata tana Amsawa, ta shige falo tasamu Hajiya na sana'ar wato girga kudin cinikin ta"


"Tayi sallama tareda karasa wa da gudu ta rungume ta " ta manna mata kiss a kumayi " I love you my kakus"


"Ta furta cikeda tsokana " aa Nidai dagani kar ki karya ni " da wannan manyan katarorin naki da kika A jiye " tasa dariya "


"Hajiya hips ba katarori ba " ai ni banida jiki saidai diri mai kyau irin na kakus dina "


"Tasa dariya cikeda kaunar jikan yar ta tace " to kiyi Addu'ar Allah ya rabaki da idanun bata gari " don wannan karuwan jikin naki Ruman harma kin fini ai tubarkalla "


"Shiyasa nake dinka miki hijabai banason fitan ki da gyale " nima bana sha'awar gyale n ai "


"Ta fito da siyayyar da tayi ta nuna mata " Hajiya tace " sarkin turare kedai bakya gajiya " ai kamshi yayi ne Hajiya "


"Toh ku naku ai zamanin daban namu

Please Login or Register in order to submit comment