Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tafi ka girma da kuma shekaru,


" yanzu na fahimta wato saboda kana tarayya da manyan mata shiyasa kake tunanin nima zakayi dani?

"Listing nafi karfinka kai Bakayi kosawar da zaka ce nice dai dai dakai ba Am far beyond ur imagination,




" kallon kinyi KUSKURE kawai yake yimata cikin murmushin karfin hali " Roman Kinfi karfina? Haka kika ce?


"Kintaba ganin mace tafi karfin namiji? Eh ni nafi karfin ka karubuta ka Ajiye hakan'



" Hmmm time will tell Ruman nidai ba ruwana my fan's tana bukatar huduba muje zuwa yanzu aka fara.......✍
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KUSKURE NAπŸ™†*
_Love & Destiny_


_Written by Fenerh_


~Dedicated to~
All my fan's

_ina mai baku hakuri da rashin jina da kukayi sakamakon rashin wutar da muka samu Amma yanzu Alhmdulillah komai normal,bawai saboda rashin comments bane yasa kukaji shiru bazan taba yin hakan ba kamar yadda wasu sukayi tunani har ma sukayi sharhi akan cewa basu San me zasuyi su burge writers ba a kullum suna complained akan rashin comments ina so ku fahim ci wani Abu comments dinku yana da Amfani a wajen writers sosai domin yana kara mana karfin guiwa Sann kuma da comments dinku ne muke samu yi muku typin har ma da gyaran kura kuran mu don haka ina neman Afuwa ga w'anda na batawa rai masoya a koda yaushe ina Alfahari daku nagode_


πŸ…Ώβž‘7⃣

Tun dawowar ta daga school takejin zazzabi na rufeta ita kadai tasan y'anda takeji A cikin zuciyar ta,

Ganin Wankin hula zai kaita dare yasa ta nemawa kanta mafita ta,


"Ta gama yan kewa kanta Abinda yafi dacewa da ita'


" Washe gari sun tashi da jimamin rashin lafiyar Magaji don haka kawai ya yanke jiki ya fadi ' hankalin Hajiya yayi mugun tashi tayi mugun rudewa,


"Gwaggo Amina ce mai kwantar mata da hankali wato Matar magajin " Yaya kiyi hakuri da izinin ubangiji ba Abinda zai samu baban ja'afar,


"Tana share hawaye tace " Amina shikadai nake gani inji sanyi shikadai ya rage min "ya'yan namu guda biyu duk sun guje mu saboda mace,


" Kiyi hakuri kidaina zubar da hawayen ki akan su ni kaina na cirewa kaina tunanin wannan yaron ai duniya ce ta ishi kowa Riga da wando,


"Gashi Muhammadu tun Auren shi da yarin yar nan balkisu baifi sau biyu ya zo gida ba ko tunanin y'ar marainiyar ALLAH bayayi,

" Daina tunamin Amina ni yanzu zuciya ta tafi kar kata da dawowar ja'afaru ko hankalin d'an uwa na zai kwanta,


"Nasan komai yakeyi yana yin shine a cikin karfin hali Amma abin na cin shi a zuciya,


" Ita kanta gwaggo Aminar karace irin ta ba haushe Amma Abun na cimata tuwo A kwarya'


"Ruman da Shigowar ta kenan taji wannan zancen hankalin ta ya tashi sosai da jin wannan irin labari,


" tana bukatar Karin haske don haka har matsuwa tayi gwaggo Amina ta tafi taji Karin bayani,


"Tunda ta gai shesu ta shigewa war ta cikin dakin ta cike da tunani kala kala'


" Bayan tafiyar gwaggo Amina ta fito tasamu Hajiya'


"Wai wane labari nakeji dazu kuna yi keda gwaggo?


" Kallon ta takeyi cike da sanyin jiki tayi Ajiyar zuciya cikin damuwa tace'


"D'an uwan mahaifiyar ki shima tun lokacin da yatafi karatu kasar turawa ya hadu da wata baturiya ta mallake mai tunani bai kuma wai wayo mu ba,

" Saboda mun nuna mai KUSKUREN shi na Auren shi da Ahalil kitabi Akwai lada aciki kuma Addinin mu baiyi hani ba Amma Akwai kalubale da yawa da mutum yake fuskanta ko akan tarbiyar yaran su,


"Nidai har yanzu kaina na cikin duhu " naji kunce d'an magaji ne," eh shine mahaifin Aisha wato mahaifiyar ki,


"Amma mai yasa baki taba fadamin kaka na bane? " kaji mun shirme ko da can ba kakan ki bane shi?


"Aa Hajiya shima bai taba nuna min Akwai kusan ci mai karfi tsakani na dashi ba,

" Ba ma wata shakuwa a tsakanin mu har ma ina nuna mai tsana ban San cewa shi ya haifi mamana ba'


"Kuma duk hakan tafaru ne sanadiyyar nuna son kudin shi da yakeyi a fili'


" Wani irin murmushi tayi irin na manya " Ummu' takirata da murya mai ma anoni da dama'


"ALLAH ne gatan mu magaji dan uwana ne gatan mu duk Abinda yakamata a ce mahaifin ki yayi mana shine duka ya dauke duk da shekarun shi kuwa'


"Duk hidimar makaran tar ki shine da wahalar shi da yakeyi Ruman kin taba tunanin waye yake tallafa mana kuwa?

" kina tunanin da wannan sana'ar ce kawai nake baki gatan da kike samu?

"Magaji yazame min d'an uwa yazame min kani ya zamemin yaya yakuma zama min uba duk da yana kanina,


" Duk tsawon shekarun nan Ummu magaji yana cikin rashin babban danshi kuma ga mahaifiyar ki ita ma ta tafi gashi dagani har shi ba wani zuri'a garemu ba,


"Shi guda dayar ta tafi shi kuma w'anda ya kamata ya kula dashi ya yi nisa bayajin kira kamar mahaifin ki'

Ta karasa tana mai share hawaye " Ummu Ruman jikinta yayi mugun sanyi sai yanzu ta gane meyasa Gwaggo Amina ke yawan kallon ta a duk lokacin da zasu hadu gashi duk y'anda Hajiya kaka zata matsa mata da zancen zuwa gidan su bata y'ar da taje.


"Ta gano cewar Ashe ta tafka babban KUSKURE nakin ba wa innan bayin ALLAH kulawa'


" Ummu ni Kaina ban kyauta wa magaji ba yakamata insanar da ke matsayin shi kodan ki shiga jikin su suji sauki suma Amma Banyi ma dan uwa na Adalci ba na gane KUSKURE NA a kan hakan yanzu'


"Tayi saurin rungume ta Bakida laifi my kakus nice mai laifin da naki Sakin jiki dasu Amma daga yanzu zan basu kulawa sosai kodan in rage musu damuwa,


" Da kanta ranar ta shirya ta Debi Abinci mai dan yawa tasa a kula ta nufi gidan su " Magajin na shinfide a bakin icen da ke gidanshi Gwaggo Amina na gefe tanata yimai fifita


Gaba daya taji ba dad'i sunyi mugun bata tausayi ta manta rabonta da takawa taje gidan tunda tayi wayo"



"Su Kansu sunyi mamakin ganinta " ta gaishe su cike da jin kunyar su" ya mai jikin ? Ta fada batareda ta kira sunan shi ba kamar y'anda tasaba fada'


"Ya Amsa cike da jin dad'i ina yaya take Ummu? " tana nan zuwa Anjima kadan'


" saboda rashin sabo tarasa y'anda zatayi ganin wanke wanke a gefen rijiya ta mike cike da jin kunya ta kwabe hijabin ta tafara wankewa duk da gwaggo Amina tace ta bari Almajiri zaiyi'


"Bayan ta gama ta share gidan tas har ma da dakin gwaggo Amina duka ta gyare gidan yafito tsab duk da itama Gwaggo Amina ba laifi Akwai tsaftar"


"Sunyi matukar farin ciki ganin gudar jinin su yau a cikin gidan su har tana musu hidima,


" Haka Hajiya ta sameta ta sake sosai harda y'ar hirar ta suka zauna cikin farin ciki tareda dauke wa juna kewa,




"Kasan cewar unguwar su daya saidai d'an tazara dake tsakanin su yasa suka kai karfe goma kafin su dawo gidan su,

" tayi matukar farin cikin kasan cewar ta a cikin kakanin ta a yau jinta takeyi A cikin ni shad'i,


"Tana dawowa ta janyo wayarta taga miss call ba iyaka daga bature sannan kuma da su hajara,


" nan take tayi dialing number hajara " tana d'auka ta sa mata ihu" sai Matar bature """""


"Tayi saurin cire wayar a,kunnen ta " Zaki ciremin dodon kunne" sory Amaryar turawa dama yaya nasir ne yasani gaba inbashi numbar ki shiyasa nakiraki domin inkarbi izini


Kuma kinsan ni ina team bature don haka bazamu bada numbar ba ta katse kiran kit"


"Sakin baki tayi kawai tana kallon wayar tare kuma da mamakin halin hajara,



" Tayi ta kallon nubar shi kamar tana son ganin wani Abu a cikin numbar daga baya ta wurgar da wayar gefe tayi baccin ta"



"Gaba daya hankalin shi a tashe yake ga wannan mayyar da Momyn shi takawo gaba daya ta hana mai ruwa gudu gashi yau kwana biyu baisa Farin cikin shi a idoba,


" Hajiya da Kanta tayi cigiya wai bataga bature ba kwana biyu ko lafiya?

"Tana jinta sarai ta kyaleta Amma duk lokacin da zata wuce sai ta kalli kofar dakin nashi,


" Wai da gaske yakeyi bazai kuma dawowa gidan ba? Takewa kanta tanbaya?


Batason tuna nin shi da take faman yi dole ta daukar wa kanta,mataki,





Fitowa yayi cikin gayu irin na samarin da sukejin sunkai kuma sun cika maza yana sanye cikin farin tree quarter hade da Riga Armless Mara hannu ya sanya tsadaddiyar facing cap mai dauke da sunan new york Kafar shi ta kalmin da yafi kauna ne wato canvas farare ga lafceciyar waya itama fara a ta kaice komai na jikin shi fari ne shi baya kaunar kowace kala idan ba fari ba,



"Takunshi yake cikin isa ya shigo falon da iyayen shi ke zaune harma da Linda " tana ganin shi ta taso cikeda iya yi tarun gume shi tareda manna mai kiss a kumatu,


"Oh Darling u are looking gorgeous""

"Ya dan ture ta kadan tareda daure fuskar shi tamau ya matsa ya gaida iyayen shi yace musu zai fita ya dawo,


" oh Tnk goodness u are going out so take Linda with you so that she can do shopping'


"Tayi wani irin karar jin dad'i " tank you mom in low I love shopping,


"Come on Darling let go" tafada cikin zakuwa "bakin ciki kamar yayi ihu ya kalli uba nshi da ido ya nunamai yayi hakuri suje,


" Yayi kwafa yayi gaba tana biye dashi batareda ya damu da itaba ya fada motar shi itama ta shige " escort dinshi suka taso yayi saurin tsayar dasu,.



"Ji yakeyi idan har yau bai sata a idoba Akwai damuwa don haka direct f.c.e ya wuce bai damu da Linda dake gefen shi ba "


"Yayi sa'a suna zaune a wurin zaman su tunda ya kunna kan motar shi ya hangota tana zuba dariya ita da kawayen ta ga badaya ya shala da kallon ta har saida yaje gab dasu ya faka motar kamar wani irin mayen karfe ne ke janshi zuwa gareta,


" ya ma manta da Linda dake cikin motar tana ta zuba kamar kanya hankalin shi naga tauraruwar zuciyar shi,


"Fitowa yayi cike da takunshi na isa kamar wani sarki " Tunda ya faka motar shi gab dasu su hajara suka fara murna,


"Lokacin da yafito kuwa ita kanta uwar gayyar ta shagala da kallon shi har ma taji ya burge ta for the first time,.

" Man in white, Hajara tafada a hankali don ya tafi da tunanin su, Sumy kuwa ai ta kusa suma Shikuwa ai ya shagala da kallon ruhin shi,



"Linda kuwa taji bala'in kishi ganin shi wurin y'an mata " yanzu saboda wa innan Black's din yake mata wulakan ci?



"Tafito cikin matukar hasala ta nufoshi " tana zuwa batare da tunaniba ta rungume shi ta baya,


"Oh baby u keep me waiting please am so tired let go back I wants you to massage my body ,


" ta fada tana mai kara shigewa jikin shi gaba dayan su suman tsaye sukayi suna kallon Asalin karuwanci,



"Ruman kuwa wani irin kululun bakin ciki ne ya tok'are mata makogwaro

" jitake kamar ta Amayo wuta saboda Abinda takeji a kirjinta,


"Kallonta yakeyi yana nazarin yanayin ta yana kuma mai jin bakin cikin Abinda Linda tayi mai bayan yafara hasko nasara a idanun ta,


" Mikewa kawai tayi ta zari Jakarta ta wuce batareda tace musu komai ba " wani irin numfashi yaja tareda hankade Linda


"Ya mata wani irin mugun kallo " find your way before I come back if not u will gate it from me.

"Ya bita cikin sauri yasha gaban ta " tayi saurin dagowa "idanun ta sunyi mugun ja cikeda masifa ta dago kanta suka kalli juna cikin ido,


" out of my way"' ta furta cikin hasala " bazan matsaba sai kinfadamin Abinda ya bata miki rai"


"Wallahi zan maka wulakanci idan baka matsaba " koda yake bakasan mutum Ciba domin hanyar da mutunci yabi kai baka bishiba,


"Tunda ka nunawa duniya kai tantiri ne har kake yawo da karuwa wadda tafi ka girma da kuma shekaru,


" yanzu na fahimta wato saboda kana tarayya da manyan mata shiyasa kake tunanin nima zakayi dani?

"Listing nafi karfinka kai Bakayi kosawar da zaka ce nice dai dai dakai ba Am far beyond ur imagination,




" kallon kinyi KUSKURE kawai yake yimata cikin murmushin karfin hali " Roman Kinfi karfina? Haka kika ce?


"Kintaba ganin mace tafi karfin namiji? Eh ni nafi karfin ka karubuta ka Ajiye hakan'


" Hmmm time will tell Ruman nidai ba ruwana my fan's tana bukatar huduba muje zuwa yanzu aka fara.......✍
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KUSKURE NAπŸ™†*
_Love Destiny_



_Written by Fenerh_


✍✍✍✍✍✍✍
GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION
✍✍✍✍✍✍✍✍

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

~Dedicated to~
All my fan's

*Allahu Akbar Kullu nafsin za'ikatul maut Allah ya gafar ta miki Aisha Allah yasa mutuwa ta ka sance Hutu a gareki*

_Masoya littafi na ina godiya da Addu oin ku a gareni da masu yimin magana ta prvt ba Amsa don Allah Kuyi min uzuri karku ce ina yi muku wula kanci abubuwan ne da yawa ina neman AfuwaπŸ‘_

πŸ…Ώβž‘8⃣

Ta wuce shi cikin sauri yana mai bin bayanta da idanu " y'anda take tafiya cikin natsuwa amma ko ina na jikin ta na motsawa


"Juya wa yayi cike da bacin ran Linda, ta bata mai shiri "Ya nufi wurin su Hajara dake tsaya kamar stature Suna kallon drama,


" Hannu ya fara mikawa Sumy "Hlo Sumy how are you?

" Jikin ta na rawa har tayi nisa ta tsaya kallon su "Hy batur......


" Kallon ta yayi cike da mamakin sunan da ta ke kokarin bashi,


"Bature? Is that my name? Ya fada cikin murmushin shi mai tsada, su Kansu dariya suka sa'

" Cikin jin kunyar shi hajara ta ce" we don't no your name that is why we call you with that name,


"Ya kuma yin murmushin " OK no problems my friend, by the way Am Abdullah"


"Gaba dayan su sunyi shocked da jin sunan don Sam basu zata hakan ba,


" Cikin Sakin baki suka ce " wow Abdullah nice to meet you tareda shaking hannun shi dukansu'


"Hajara da baki baya shiru ta kalle shi " to meyasa kullum sai inga motocin ka Anrubuta J Abayan su we thought...... Tafada tana mai son jin kwakwaf,


"Ya d'an yi dariya kadan tareda waigawa wurin da mutu miyar ta tsaya, duk Abinda sukeyi idanun ta nakan su gaba daya jin ta takeyi a takure har su hajara sun bata mata rai


" ya ma za ayi su wani rikewa namiji hannu kirjin ta har zafi yakeyi'


"Cikin fushi ta shige warta Aji batareda lokacin shiga daukar lecture yayi ba,


" Har Aka tashi a makaran ta ranar bata kuma sauraran su hajara ba sai wani matse musu fuska takeyi "suma da yake sun iya sai kawai suka shareta '


" Da mamakin ta yana zaune a saman motar shi koda suka fito direct suka nufe shi,.


"Tana gefe gaba daya hankalin ta na kansu sukuwa sun saki jiki sosai sai hira suke kwasa daga baya ma motar shi suka shige hajara na gaba kasan cewar yau driver ya kawota don haka suka wucewar su,


" Saida suka fita ya kalli hajara " Friend kina tunanin hakan shine dai dai?


"Trust me my friend that's is the right idear just watch and see"


"A sanyaye ya kalle ta Am scared banaso inrasa friend dinki idan na rasata numfashi na zai iya tsaya wa,


" Wai don ALLAH ni yaro ne? Kallon shi tayi cikin tausayi domin tarasa Amsar da zata bashi'

"Meyasa ita kadai take ganin yarin tata? Meyasa take tunanin tafi karfina? Meyasa take ganin kamar bazan iya bata kulawa ba?


" Ni nasan nine dai dai da ita ni nasan zan iya mata zan bata gata fiye da tuna nin ta,


"Ya karasa cike da damuwa " friend u no it's hurt me A lot when I saw her with another man,


"Inada kishi mai zafi Akanta I can do Anything bcos of your friend"""


"Gaba dayan su tausayin shi ya cika musu zuciya " yaro danye sharaf ALLAH ya jarabce shi da son mace mai murd'adden ra ayi, mace mai kafiya,


"Sumy harda hawaye ta goge ya juya gefen ta su " ina zamu nufa?

"Ni ina G.R.A Sumy kuma kofar doka'
Cike da mamakin ta yace shima ai .G.R.A yake meyasa basu taba haduwa ba?

" tace ikon Allah ne yasa tana mai Jim farin ciki har suka sauke Sumy itama ya kaita nasu gidan tareda nuna mata gidan su cike da mamaki take kallon gidan don kusan kullum sai sunyi maganar wannan gidan


"Don yafi kowane gida dake unguwar haduwa kuma basu taba kawo cewar Akwai mutane a ciki ba,



" Ruman kuwa bayan tafiyar su gaba daya ranta ya gama baci " su hajara sun bata mata rai sosai " yanzu saboda wani banza can daban zasu wuce su barta?

Ko a gida Hajiya takasa gane kanta A ranar daga baya ma shirya wa tayi kawai tayi wuce warta gidan su magaji,


"Gwaggo Amina saida ta tanbaye ta" Ummu yau lafiyar ki kalau kuwa?

"Tace kalau take kawai kanta ke dan ciwo nan kuwa damuwa ce fal cikin ranta'




" Washe gari kuwa da wuri ta wuce makaranta duk da yau ta tashi cikin mugun yanayin marar ta har ciwo takeyi kadan kadan saboda rashin baccin da batayi ba sosai da dare tana ta faman juyi da kuma tunani'



"Abdullah kuwa bayan komawar shi gida ya tarar da fadan Momy sosai " yi yayi kamar ma baisan mai yafaru ba cike da jin haushin Linda dake zaune tana matsar hawayen munafurci,


"Yace " Momy please I beg of you tell this girl to stay away from my life I don't wants her please """ ya fada tareda hade hannun shi'


"Wani irin tasowa tayi zata nufoshi yayi saurin daka mata tsawar da dole ta koma jikin Momy ta lafe,


" Ya matsa kusa da ita kamar zai fisgota jikin shi har rawa yakeyi'


"Stay away from my life or else you will regret, I don't love you or any of ur stufidity,


" Momy please tell her to go back from ware she came from we don't needs her hare,


"Oh come on my boy don't say that u no why Linda is here she is hare to help you I didn't forced you to love her or Mary her she is here to satisfied your needs I don't wants you......


" oh stop Momy what are you saying ?how many times Dady told you that is prohibited in our religion,


"Wani irin firgita tayi tare da zabga mai wani irin kyakkyawan mari " Jeff ta fada jikin karfi sunan da ya dade baiji takira ba,

"Tsawon rayuwar shi " Ruman ce ta fara dora mai hannu tunda yake da iyayen shi basu taba dukan shi ba har dai Momyn shi da bata son komai ya same shi yau itace da kanta ta mare shi,


"Wasu irin hawaye ne masu ciwo suka fara bin kuncin shi, ita kanta Linda jikinta yayi sanyi,

" Jeff are you going to followed your father religion? tafada cikin karyewar zuciya,


"Cikin dauriya da kuma dakewa yana mai kawar da fuskar shi gefe" yes mom..... Saurin daga mai hannu tayi " don't call me that,

"I no why, is All bcos of ur stupid dream girl, yayi saurin matsawa kusa da ita tareda riko hannun ta " Momy noooo"

"U hv to understand" I realized Islam is the true religion I have been research All that long,


"Just stop I don't won't to listing, "now listing to me carefully I want let you do that,


" cikin zafin zuciya ya matsa gefe tareda share hawayen shi "u don't have the right to stop me Momy and I will Mary my dream girl insha ALLAH with you or without y....


" marin da ya kuma ji ne ya dawo dashi cikin hayya cin shi ya dafe kumatun shi cikin tsananin mamakin w'anda ya mareshin,


"Dady"" yafada cikin rawar murya'

"Cikin fushi ya nufi Matar shi tareda fara lallashin ta tayi saurin tureshi tafara zazzaga mai bala'i da cewar ya zuge mata yaro zai koma Addinin shi bayan ba haka yayi mata Alkawari ba'


" Kallon mamaki Abdullah yabi uban dashi "Dady u promised her? Hmmm yayi wani irin murmushi mai ciwo ya goge hawayen fuskar shi zuciyar shi na suya"

"I understand Dady meyasa zakayi haka " har yanzu Ashe baka gane "KUSKUREN ka ba Dady? Kamar y'anda kake fadamin

" Dady na gane ina wahala ne sakamakon zunibin da ka Aikata yake wahalar dani yana daya daga cikin dalilin da yasa ni na dawo Nigeria saboda hakan ne kawai zai sa ku dawo Nigeria Amma hakan Sam bai yimin Amfani ba,


"Kumin Alfarma kai da Momy please ku tattara ku koma inda kuka fito I don't needs you here you are just increasing my problems,


" uban ya daka mai tsawa shi kuwa ko gezau ya kama hanyar waje batareda ya kuma cewa komai ba'


"Wani irin kuka uwar tasa mai cin rai Dadyn ya fara lallashin ta ita kanta Linda kuka takeyi tana mai tausayin wannan familyn ita kam dole ta koma inda tafito don tasan batada sauran Amfani,



Don tasan bazata taba samun Abinda takeso ba gashi ta saba da harka kwana biyu An tauyeta,
Shiya gari na wayewa ta hada kayanta tabi mota zuwa Abuja kafin lokacin tashin jirgi,


" yana fita Ya wuce Zaria hotel ya kama daki a nan ya kwana duk da baya kaunar zaman hotel,

Da sassafe ya nufi kofar gidan su Hajara lokacin dai dai tafito zata tafi maka ranta tana ganin shi ta fara'a Amma ganin yanayin da yake ciki jikinta yayi sanyi,


"Ta bude kawai ta shiga ganin baya cikin yanayi mai kyau kawai gai suwa sukayi ya tuka batareda yace mata komai ba'


" Har suka isa cikin makarantar,


"Ruman na zaune Alokacin ciwon nata yafara damunta sosai har wani gumi take karyowa'

" Tunda ya dora idanun shi akanta yasan batada lafiya cikin sauri ya faka motar shi yafito batareda ya kulle ba ya nufeta da gudun shi kasan cewar makarantar bawasu mutane bane suka taru shiyasa ba w'anda ya lura da halinda take ciki,


"Zama yayi A gefen ta jikin shi na rawa ya riko hannun ta Roman " lafiyar ki? Meke damunki? Duka ba tanbaya sai cije lebe takeyi idanunta sunkada sosai saboda Azaba'


"Hajara ta karaso itama cike da rudewa " Queen "" lafiya? Meke damun ki " Cikina tana mai kokarin zamewa kasa ya rikota tareda mikewa ya dagata cak kamar y'ar tsana,


"Bayan motar shi ya ce hajara tabude mai ya sakata Aciki " ya gyara mata kwanciya " sannan ya kulle "

"Cikin sauri ya shiga tareda karbar jakar ta A hanun Hajara " bai jira komai ba ya fisgi motar ya fita batareda ya kuma sauraran hajara ba,


"Taso ta bisu taga halinda kawarta ke ciki Amma ina ya wuce Abinshi da ita'


" Bai tsaya da ita ko inaba sai Zaria hotel dakin da ya kama ya kinkimeta saida ya shinfide ta a kan gadon sannan ya cire dogon hijabin dake jikinta,


"Wani irin harbawa zuciyar shi tayi " Domin ganin zunzurutun shape dinta da ya bayyana A zahiri kasan cewar tana sanyeni da doguwar rigar Atanfa dinkin zamani ya kamata dam daga sama har yana hango layin nonuwan ta da suka kunburo rigarta kamar zasu fasa kirjinta,


"Wani irin numfashi yaja tareda dafe marar shi "za ayi biyu kenan ya furta a hankali' wata irin kara ta sanya tareda wani irin juyi Wanda saida ya juya da lamarin tunanin shi gaba daya har ma da zuciyar shi yakarasa cikin karyewar zuciya ya rungumo ta zuwa kirjin shi,

Atare suka sauke Ajiyar zuciya yakai hannun shi saman wuyanta ya shafo wani irin hucin zafi jikinta kefitar wa " Oh my god" ya furta hawaye na zubowa a idanun shi ,


"Ajiyeta yayi a hankali yashiga bathroom ya fito dauke da wata yar roba da ruwa hannun shi rike da karamin towel ya Ajiye akan side drowe din gadon...........✍


*Kuyi hakuri da irin turancin dan koyo my fan's please managed Anyi mana Rasuwa ne A makota muna baran Addu'ar ku*


_kucigaba da biyo_

*Matar Soja*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KUSKURE NAπŸ™†*
_Love & Destiny_


_Written by Fenerh_


~Dedicated to~
*My Zinariya*

*ina mugun yinki my Real gold Zinariyar Golden pen jinjina ta mu samman Allah yabar min ke*

πŸ’«GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONπŸ’«
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*

πŸ…Ώβž‘9⃣

"Ahankali ya janyo yar Karamar Akwatin shi ya hada ruwan Allura ,

" W'anda a lokacin

Please Login or Register in order to submit comment