Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

banda lafiya fa' "I no bazan wuce hakan ba kibarni insamu natsuwa kawai,


A haka ya gama jarabar shi ya kyaleta domin taki bashi gudun mawa don kar yace zai zarce hakan saida ya mike ya shiga bathroom ta sulale ta gudu itama saida ta fada ta watso ruwa tareda zubawa kirjin ta idanu ta dan karamin madubin dake bathroom din,


A Gaskiya Abdul karshe ne wajen fitina kalli y'anda ya sa k'irjin ta yayi jajur tsabar matsar da suka sha,


Saida ta dauro Alwala sannan ta dauro towel ta fito idanun ta a waje ta zuba mai ido domin ganin shi yayi dai dai akan gadon ta


" me kakeyi Anan Abdul? "Me kika ga inayi a nan? " Don Allah ka tafi Abdul kar Hajiya ta ganka,


"Ai sai kiyi Kizo kawai mu kwanta ni bazan kwanta nikadai ba bayan inada mata muna gida daya saboda ke fa nake nan gidan Amma kina korata to bazan fita ba,



Batada zabi dole haka ta hakura ta yi Salla sannan ta sha maganin ta ta haye gadon gefe ta kwanta ya mirgino tareda rungume ta gam cikin jikin shi




Baccin su sukasha mai dad'in gaske basu San lokacin da gari ya waye ba jin kiran Hajiya yasa ta bude idanu ta ware su akan fuskar shi bai ko San tanayi ba baccin shi yakeyi hankali kwance,



" zabura tayi ta d'an bugeshi kadan ya bude ido "Abdul kagani ko yanzu ya zamuyi gashi munyi lattin tashi har Hajiya ta fito '


Duk tayi tsuru tsuru kamar wadda tayi karya " tashi kawai yayi tareda dirowa ya sanya rigar shi da ya cire ya nufi hanyar fita tayi saurin shan gaban shi


"Fita zakayi ta ganka? " eh to kwarto ne ni da zan tsaya labe labe bakin ta sake ta ke kallon shi ya fita Hajiya na kishin gide tana lazimi


"Barka da Asuba Hajiyar mu' tsayawa tayi cak da Abinda takeyi tana mamakin wai a nan ya kwanar musu ko me,


Yana kokarin fita falon ta tsayar dashi " Abdullahi ya dawo "na am hajjo " rasa kunya Badai a nan ka kwana ba?


"A nan ne mana Akwai laifine? " babu d'an ubanka Mara kunya yanzu ko kunyar idona bakaji ba zaka kwana a nan,


"Kiyi fushi kawai ki bani matata yanzu mubar miki gidan ki ba bata lokaci


" ai kuwa duk rashin kunyar ka bazan baka itaba kuma yau sai ka bar gidan nan sai famar taku rawa yarinya kakeyi ina Ankare jiya har kusan barar da cikin kayi tsabar fitinar ka,


"Wai ke Hajiya meyasa kike cewa nine mai laifi itafa tace inzo intaya ta bacci tsoro takeji"


"Carbin hannun ta ta jefa mai tafi d'an nema oh ni salame ' yau naga zamani' dariya yasa ya fita Abin shi saida ya yi wanka sannan yayi Salla domin lokaci ya tafi



Itadai tama kasa fitowa saboda tsabar kunyar da Abdul ya sanya ta tunda tayi Salla ta shirya komawa tayi tayi kwanciya r ta duk da tanajin yunwa,



Saida Hajiya ta shiga tace " oh ni Ummu wannan marar kunyar yaron duk ya canja min ke yanzu ni kike jin kunya lallai,



"To fito ga dumamen da kikace zakici yau na dumama miki ga kuma kunun tsamiyar nan duka,


Ba tada zabi dole ta fito domin yunwar na azal zalar ta ta murje ta kwashi Abinci



Cikin shirin shi ya shigo falon yan zuba kamshi cikin wani milk colour material na maza mai kyau da kuma tsada ya mugun haduwa ya zauna kusa da ita,


" toh Hajiya ni zan tafi KD zamu fara aiki an fara kawo patients sati mai zuwa zaku zo bikin budewa ku duka kafin in tafi zan biya gidan wa incan tsoffin


"Toh Allah yasa afara a sa'a , Ameen " kallon Ruman yayi "madam zantafi ga makullin motar ki bance kije yawo ba idan zakuzo zanyi ma Ak magana ya hadaku da driver ya tuka ku


Yasa hannun shi ya shafo cikin ta tareda dora mata kiss a,goshi ya mike ya zaro ATM ya Ajiye mata idan kina bukatar wani Abu Akwai kudi a ciki sai kunzo,


Zuba mai ido kawai tayi domin ya matukar burgeta har tanajin kishin fitar da zaiyi a haka


Kamar ta tsayar da shi takeji key din motar ta nuna wa Hajiya tasanya Albarka " Mahakurci mawadaci Ummu Allah yasa Albarka,


Sai mun shiga d'ani "ai ko yanzu ki shirya muje gidan su kaka magaji, to sai Anjima yanzu ki gama cinye Abincin ko,


Matar likita gashi laulayi ya tsaya cak Abinka da masu Abu, dariya kawai tayi domin ita Kanta ta y'arda domin irin magun gunan da ya ke dirka mata,



Yana fita ya turo mata text

_"I Always tink of you,but I always fail to know the reasons why.is there something else I should know about you? But there is one thing that I know is true. That life will always be sad without you._



_" caring for someone is easy but making someone care for you is hard. now I keep wandering how did you make it so easy for me to care for you' I love you so much_



Text msg din ya matukar tafiya da ita har batasan lokacin da t aika mai da simple reply ba,


_"thanks safe journey_

Murmushi yayi kawai domin ganin reply dinta yana tuna moment dinsu da ita a hankali ya furta,


I wish my eyes could speak what my Heart feels for you,........✍



*Matar Soja*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KUSKURE NA🙆*
_Love & Destiny_


_Written by Fenerh_

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


🅿➡3⃣8⃣

Ya isa Kaduna lafiya gudan shi ya fara wucewa ya sameshi tsab domin Akwai ma Aikata masu kula da gidan akoda yaushe


Bedroom dinsu ya fara shiga ya zubawa gadon su ido domin tuno da ranar da suka kwana a kanshi duk da bawai wani morewa yayi ba Aranar Amma bazai manta da moment din ba how he wish a ce yanzu ma tana zaune a cikin gidan shi da yafi kowa farin ciki


Ya matsu Matar shi ta tare tare dashi ya gansu dagashi sai ita tana bashi kulawa irin ta mata da miji Hmmm Allah ya sauke mai ita lafiya,



Hutawa ya farayi saida ya kwanta tareda janyo filon da ta kwanta akai ya rungume gam bacci mai dad'i ya daukeshi mai cike da mafarkin yana raya sunna da Abar sonshi karar wayar shi ya katse shi batareda yakai ga cimma burin shi ba tsaki ya buga tareda danna wayar ya sa a kunne batare da ya duba ba,


Saurin tashi yayi zaune domin jin muryar wadda ke kiran shi wato mubena,


"Ka fada min inda zan sameka a Zaria yanzu zan zo domin na kasa daurewa'


Shiru yayi kawai domin bai taba ganin mayyar yarinya irin wannan ba kofa sa'ar Matar shi batayi ba Amma sai rashin kunya,



" mema sunan ki ? "Mubena kardai har ka manta sunan ? " to ai ni sunan mace daya ne kacal bana manta wa dashi bayan na mahaifiyata wato my one and only wife,


"Wife? wasa kakeyi nasan Bakada mata As your Age don kana tsakiyar lokacin ka Bazaka taba bata rayuwar ka ba,


A matsayin ki na musulma a wane hadisin ne ya fadi cewar ni ban isa Aure ba?


" aa ba wannan bane ni ina maganar zamani da kuma wayewa da tazo , OK yanzu meyasa kika kirani?


"Inason mu hadu ne, " ina mukhtar ki fada mishi ya kawoki "no banaso yasani please OK ni ina Kaduna yanzu haka kuma ina cikin gidana so idan na fito zan nemeki



" Kafada min unguwar inzo "aa gidan matata ne nan banason kowace mace a ciki


Wani iri taji domin taji Alamar wulakanci a cikin zancen shi Amma mai nema baya fushi,


A haka Abubuwa keta tafiya akalla yayi kusan kwana biyar a Kaduna batareda ya bari sun hadu ba sunata faman shirye shiryen bude Asibitin shi da kuma company Dady,



A kullum suna kan waya da Matar shi ya matsu ta zo KD yayi matukar kewar ta ita,kanta tayi missing din shi sosai sai dai basar war da takeyi


Sarkin naci kuwa Yanzu har kuka takeyi idan ta kirashi akan ya bata izinin zuwa wurin shi,


Har ya gaji ya daina daukar wayar ta sai dai msg idan ya karan ta ya share da ita


" yau Saura kwana daya a yi taron bude Asibitin yana zaune a cikin falon shi yana kurbar coffee wayar shi na kunnen shi yana waya da Abar kaunar shi '


"Baby na meyasa bazaki zo yau ba nafa daure sosai kusan sati daya ban saki a idoba ki zo yau gobe ina busy sosai bazamu samu sakewa ba,


" ai zaka ganni ko "bakya ganewa ne nafayi missing sosai Kizo mukasan ce tare a daren yau aiki ne ya rikeni kinsan da tuni na zo Zaria


" my Queen ya furta cikin kashe murya "um Kizo please " Hajiya tace sai gobe zamu shigo da wuri dasu Gwaggo Amina Amma Su Dady na zuwa yau,


Ki biyosu to "saidai munzo bye ta katse kiran " murmushi kawai yayi ya shafo sumar kanshi mai santsi da sheki "my wife ya furta can kasa




Su Momy sun iso KD sun hadu da mama balkisu suka fara aiwatar da shirin tarbon mutane domin y'an uwan Momy ma zasu zo daga UK


Mukhtar sun kayatar da wurin da sauran Abokan Aikin su wurin ya kayatar domin sun gayyato manyan mutane irin minister lafiya tareda sarkin zazzau da kuma mai gayya mai aiki wato gwamna daya tamkar da dubu malam nasir el rufa'i domin bude wannan Asibitin da zai bada gudun mawar shi a garin na Kaduna,



Bakin turawan sun iso nija An saukesu a gidajen da aka kayata domin ma aikatan Asibitin sun yaba da kasar ta mu da kuma garin na gwamna wato KD garin ilimi



Shidai ya matsu farin cikin shi ta iso yaga lafiyar Babyn shi kuma



Da wuri suka shirya ta yi wani haske na ban mamaki domin cikin ya shiga wata biyu yanzu tayi matukar kyau cikin dinkin ta na Senegal doguwar Riga shadda mai tsada ruwan goro taji design blue kamar wata Matar gwamna ta fito tana sheki

Ta sanya farin mayafi da kuma takalmi da jaka farare Hajiya tace nasha Allah uwar gidan baturen marasa kunya,


Saida ta dara sannan suka fito tana rikeda makullin motar ta suka rufe gidan su suka nufi gidan su Gwaggo Amina domin daukar ta don magaji shi a can ya kwana domin Dady ya Ajiye mai driver na kanshi ,



"Wai ni ina driver da zai kaimu naga kin tukomu zuwa nan " ni zankai ku ku dauro Alwala kawai'


"Wane ni Wallahi da sake kira driver da yace ko in kirashi kinsan halin shi ai bazaki kaimu lahira ba bamu shirya ba,



Dariya kawai tasa saida Gwaggo Amina ta fito cikin shirin ta itama tsoffin sun fito shar kana ganin su kasan suna da gata haihuwa tayi rana,


Driver ta kira ya zo suka wuce sunata zuba hirar su har suka isa Kaduna lafiya,


Kiran wayar shi tayi " mun iso ina zamu isa ? "Ku je gidan baba su Momy na can idan kin Ajiyesu zan iso in dauke ki yanzu'.



Surukan nasu sun tarbesu cikin girma suka basu wuri na mu samman tare da Abin motsa baki


Ita ma ta zauna domin ta matsu bata ga mijin nata ba Sallamar shi taji cikin daddadan muryar shi ta dago kanta akan wayar da take danna wa ta dora su akan nashi,



Idanun shi ya zuba mata tayi mugun tafiya dashi saida ya yi Ajiyar zuciya sannan ya tako zuwa tsakiyar falon


Batareda ya lura da duk mutanen dake zaune a falon ba ya fara kokarin nufota,


" Saurin mikewa tayi ta nufi dakin mama balkisu gudun kar ya bata kunya ya waske tare da zama kusa dasu Hajiya


"Tsoffi sannun ku da zuwa " yanzu ka ganmu shiryayye to sannu kaima ya shirye shirye,


Alhmdulillah ya d'an taba hira dasu kadan sannan ya mike ya fita waje wurin motar shi ya kira ta" kifito kafin in shigo cikin dakin ina waje,



Ya katse kiran ya zubawa hanya ido wata wawuyar Ajiyar zuciya ya sauke tareda zuba mata ido tun daga sama har kasa ji yake kamar ya ruga ya rungume ta yakeji,


Ta karaso idan ta akasa cikin takunta na burgewa har saida ta iso sannan yayi Ajiyar zuciya ya zagaya tareda bude mata mota ta shiga sannan ya zagayo tana kallon shi ta glass ya zauna,



"Muje gidan mu in rage zafi kar inkasa zuwa taron nan kin dagamin hankali da irin haduwar ki madam ya kalle ta da idanun shi dasuka canja launi


" kallon shi tayi itama ta dukar da kai "ba kace sai nayi wata biyu ba ina hutawa " riko hannun ta mai laushi yayi ya dora a saman jikin shi kinji y'anda ma koma daga ganin ki so dole ki taimaka in baso kike in kasa yin komai ba,



Zaro hannun ta kawai tayi daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaki Abdul ya shiga uku da jaraba ta fada afili batare da tasan zancen ya fito ba,


"Naji ni nacika jaraba Amma nagode wa Allah jaraba ta ta tsaya akan Matar Aure na ita kadai nakejin sha'awa,



Hannun shi ya dora saman cikin ta " ya baby na? shiru kawai tayi yanata lalubar ta har suka isa gidan su ya shiga tareda bude mata tafito ya riko mata jakar suka shiga daga ciki'




Tun daga falon ya Ajiye jakar ya cire mata gyalen ya sunkuce ta sai cikin dakin bai direta ko inaba sai gado yafara binta da kallo ta ko ina jikinta,


"Baby lau layin ya tsaya ko naga yanzu lafiya lau " eh sai lokaci lokaci nake d'an zazzabi Amma inacin komai "god ya ce kinyi kyau sosai my madam,


Murmushi kawai tayi ya rungumo ta tsam tareda Ajiyar zuciya " baby I really miss you '



Tuni ya fara dora mata kiss a ko ina na jikin ta yafara kok'arin cire mata Riga kenan wayar shi tayi kara tsaki kawai yayi yaci gaba da Abinda yakeyi


Kallon jikin ta kawai yakeyi domin ko ina nata burgeshi yakeyi fatar ta sai sheki takeyi tana santsi hannun shi kawai ke yawo akan jikin ta


Saida wayar ta kuma kara ya daga yana tsaki " wai kai meyasa kake haka ne banfada maka iyali na sun iso ba inason time tare da ita please "


"To d'an iska ai saika fito An fara taruwa kai kadai Ake jira ga su salis sun iso ma Amma kai kana can kana fitina don Allah ka fito malam yanzu,


" kai Wallahi Allah ya isa tsakani na dakai mugu kawai ka hana ruwa gudu 'dole ya diro ya nufi bathroom ya sheko ruwa cikin sauri ya fito tareda janyo kaya ya fara sakawa"


Madam ga kayan ki kitashi ki canja ba time mun tara manyan mutane kar mu barsu suna jira


Ta mike ita ma ya fito mata da wasu kayan less ne blue Riga da zani mai kyau da kuma tsada har tafi haduwa yanzu ya dakko mata pos da takalmi shi kuwa ya shirya cikin suit blue ya fito yayi kyau sosai ita kanta ya burge ta



Sun fito fes dasu kamar taurari ya riko hannun ta kana ganin ta kaga Matar d'an gata suna fitowa motoci tagani Jere kusan guda biyar ta tsakiyar aka bude musu security suka shiga sauran sai kace wani gwamna haka suka nufi Asibiti



Sun isa wurin taron jama'a sun hallara ga runfuna ta ko ina motocin na isowa wurin Kallo ya koma Kansu security suka bude mai motar ya fito tareda zagaya wa dayan gefen ya budewa Matar shi ta fito,



Sunyi matukar burge mutane mu samman kasan cewar shi karamin yaro Amma ya mallaki Abubuwa da dama na ci gaba


A gurguje taron ya kayatar sosai duk mutanen da suka gayyata sun samu damar hallara Anbude Asibitin cikin nasara



Sai gayyatar liyafar da suka shirya A harabar gidan shi


Iyayen sunyi matukar Alfahari da yaron nasu ita kanta ya matukar burgeta A wurin duk da ranta ya baci da ganin wata Yarinya da take mai shishshigi a wurin duk da tagan shi a tare da Matar shi Amma bai sa ta fasa shige mai ba ranta ya baci sosai shiyasa duk da gundura a wurin


"Su Hajiya sun yi matukar farin ciki da ganin cigaban gudan jinin su gashi An zuba kayan Aiki sosai na zamani a Asibitin Domin sauka kawa mata wajen haihuwa


Domin sun kwashi kwararrun likitoci ta fannin mata wato Gynecologist domin bama mata taimako dangane da matsalolin haihuwa sannan Akwai gefen yara suma Annemi likitoci da zasu bada tasu gudun mawar ,



Sun shirya nufo gida domin gudanar da walimar da suka shirya su Momy nata kaiwa da kawowa domin kayata Abun kasan cewar harabar gidan nada girma aka zuba kujeru da runfuna gaba daya a harabar gidan ga security tako ina


Suna isowa suka shiga daga ciki shida Matar shi domin shirya wa



Gaba daya zuciyar ta a jagule take domin ganin irin y'anda y'an mata ke shigewa mijin ta a Gaskiya hankalin ta ya tashi sosai,


Har batason ta tafi ta bar shi a yanzu gwara ta zauna da kayan ta tabashi kulawa,



" yana lura da yanayin ta duk jikinta yayi sanyi suna shiga cikin dakin su ya rungume ta
A hankali ya dora habar shi akan Kafada r ta


"Miss Abdullah Jafar what is wrong? batasan lokacin da hawaye suka fara zirarowa daga idanun ta ba tsabar kishin da ke cin zuciyar ta,



" naga y'an mata sunata shige maka ne ni dai Wallahi banyar da ba kawai ni....

Dariya yasa tareda zuba mata idanun shi masu dauke da tsantsar soyayyar ta


"Madam haka kike kishina " wow Gaskiya naji dad'i don haka zan kara Aure kodan inga kishin ki"


Duka takai mai cikeda shagwaba "nidai Wallahi banyar da ba tasan ya mai kuka, wani irin farin ciki ne ya kara rufe shi wato tana sonshi sosai har haka itama,


Juyo da ita yayi ya rungume yana Ajiyar zuciya cikeda tsantsar farin ciki " madam relaxed ya kamata ki duba tarihin soyayyar mu the you tink Akwai sauran space a zuciyar Abdullah akan wata mace?



Nop ke kadai nakeso Ruman banso wata mace ba tun farko sai Yanzu da na sami mafarki na bazan iya Rayuwa da kowace mace ba idan ba ke bace,


"Am only yours and you are mine for ever insha Allah don haka ni ki cire damuwa a zuciyar ki


Sannan y'an mata da kike gani duk cousin's dina ne turawa y'an uwan Momy na me zanyi dasu nifa jinin zage Zagi ne ki gane ina Alfahari da Asalina da kuma kasar mahaifina,


Sannan Mubena a hankali ya war ware mata komai don haka kisa a ranki ni nakine


Rungume shi tayi gam tareda dago bakinta ta hade da nashi ta aika mai da wani salon sunba w'anda saida ya kasa tsayawa da kafar shi'



Sannan ta zare bakin ta dakyar numfashin shi ya tsaya " wow baby zaki kashe ni da salon ki Gaskiya ina bukatar irin shi Anjima don haka ki shirya min OK'


Dage mai gira tayi cikin salon ta tareda murmushi "karka damu my one I promise " zaro ido yayi cikin zumudi "da gaske ? " uhm zanyi sake ne kadangaru suyimin wawaso,


Kyalkyalewa yayi cikin jin dad'i "suwaye kadan garun? " suna nan da yawa irin su mubena "to wannan Mubena ta kiyaye ki k'arki mata rotse


" ai kuwa gwara ta fitar min hanyar miji tun ban karta ba, rungume ta yayi yana mai jin wani irin nishad'i Mara iyaka a yau Ruman din shi tana nunamai kulawa


Agaskiya bazai taba mantawa da wannan ranar ba


Kiran wayar shi da Akayi yasashi mikewa "oh my god mun manta da mutane baby tashi mu shirya we have the whole night today



Kaya ya kuma bata wata doguwar Riga kamar wedding gown pink hade da d'an mayafin ta ta shirya ciki rigar tayi masifar daukar ta


Wayar ta tayi kara ta duba ganin sunan hajara yasa ta saurin dagawa


" yanzu kun manta dani Besty " ba wani nan kece dai kika manta damu yanzu dai idan kun gama shanya jama'ar kufito muna jiranku,


Wani irin ihun murna ta sanya Aminan ta sunzo tayi saurin sanya bakin takalmin ta mai tsini gashi tayi simple makeup ta Yane fuskar ta da d'an karamin mayafin rigar mai dogon hannu ce gashi ta fito kamar Amaryar balarabiya



Da y'ar Karamar Po's dinta mai kyalli masha Allah shima ya kuma shirya wa cikin farin suit da fararen takalmin ga Agogon shi na Gucci mai tsada


Kallon junan su kawai sukeyi cikin burgewa kowa na kyasa haduwar d'an uwan shi,
Haka suka fito yana rungume da hannun ta irin na turawa.....✍



"Acan na hango y'an kuskure na fan's cike y'an gayyar sodi Niko nace waya basu invitation? Ina jiran Amsarku



Daga taku har kullum

*Matar Soja*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KUSKURE NA🙆*
_Love & Destiny_


_Written by Fenerh_

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

🅿➡3⃣9⃣

Sunyi matukar daukar hankalin jama'ar dake wurin duk y'an uwa na wurin har ma da kakan nin su Hajiya bakin ta har kunne ganin irin hutun da Allah ya kawo ma yar jikar ta


Mikewa Akayi ana musu tafi mukhtar na gefe shida mubena 'wani irin kishi ne ya turnike ta yanzu saboda Matar shi ne yake mata wulakanci


Me Matar tashi ta fita da zai wulanta ta har haka, harara kawai take zubawa Ruman, ita dai tana nan like da mijin ta har suka isa wurin da Aka tanadar musu



Aka fara gudanar da taron inda mukhtar ya mike ya fara bayanin sanadiyyar taruwar su a wurin "



Daga nesa ta hango Aminan ta sun kame a kujeru sunata zuba hira dasu Hajiya su MOMY ma duk suna gefe tareda y'an uwanta da sukazo


Dana duba wani gefen kuwa iyayen su ne maza tareda Abokan su suma sunata faman tattaunawa atsaka nin su


Cikin natsuwa mukhtar yafara jawabi kamar haka, "Assalamu Akaikum jama'a munayi muku barka da zuwa wannan d'an karamin taro da muka hada domin cigaban Abokin mu d'an uwan mu da kuma mu kan mu baki daya,


Da farko mu nayiwa iyayen mu barka da zuwa tare da godiya ga duk Alkhairin su a gare mu Allah yasa ka musu da Alkhairi,


Akwai dalili da dama da ya tara mu a nan na farko domin murnar bude Asibitin mu sannan na biyu domin taya shi murnar Auren shi da ba mu samu yi ba tun farko don haka muka ga ya dace yanzu mu d'an hada mai d'an kwarya kwaryar taro


Kafin zuwa lokacin da Matar tashi zata sauka mu hada gagarumin fati yanzu ma mun sassauta ne saboda Akwai iyayen mu Anan,


" mahaifan mu Alhaji Jafar Ahmed da Alhaji Muhammad zubair muna matukar godiya agareku

Sai kuma iyayen mu mata "our mother MOMY Khadija you are highly welcome thank you so much m'am


" mama balkisu muna miki barka da zuwa sauran baki da suka zo daga nesa dana kusa duk muna muku bar ka da zuwa ,


"An nayi suya na manta da Albasa kakar mu Hajiya kaka barka da zuwa manyan kawayen uwar gida kuma muna yi muku barka da zuwa,



" nidai ina gefe na kure a daka bakina har wuya ina zura wuya ina jiran Akira suna na Amma har ya gama introduction dinshi bai kirani ba don ya rai nan wayau Asha wuya tare dani Amma ko barka da zuwa Anki yimin kuth,

Ya bada takai taccen tarihin Abdullah da irin nasarar da ya samu a karatun shi tundaga farko har zuwa kammalawa r shi,



"Sai tarihin Asalin soyayyar shi da Ruman yana fada cikin raha" kowa na dariya banda ni na zabga uban tagumi saboda haushi



Saida yakai Aya sannan ya zauna Aka kira Hajara tazo ta d'an bada tarihin Ruman har zuwa yanzu a takaice

Please Login or Register in order to submit comment