Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nakeso Wallahi banaso ta sani nafiso shi ya fada da kanshi idan sun tanbaye ni sai ince na y'arda Amma haka kawai bazan iya furtawa ba,


Lallai kuwa zaki tafka KUSKURE babba Queen, nidai ki tayani Addu'a,


"ALLAH ya sa mudace gashi kin haukata min yaya na ko jiya ya kirani wai bakya daga mai waya,

Kibari kawai ni tashin hankalin da nake ciki baya bari na ko kallon wayar inyi ,

Toh ya shirin Auren Sumy ? Ke muke jira ai ya kamata mu San Abinyi lokaci na tafiya,




Karfe biyu ta shigo gida lokacin tayi mugun gajiya ga kuma wata uwar yunwar dake Azal zalar ta ko gefen su Hajiya bata kalla ba ta shigo falon tareda tube Hijabin jikinta burin ta kawai ta sakar wa kanta ruwa ko zataji sanyi Ajikinta,


Tun Shigowar ta cikin falon idanun shi suka sauka akanta jikin tsananin mamakin me yakawo ta nan kuma saboda ko kofar falon bai fita ba bai kuma San da zuwan su gidan ba,


A jikinta taji a lamar ana kallon ta tayi saurin daga kanta tareda kallon tsakiyar falon,


Tsaya wa taki cak har tana Sakin hijabin dake hannun ta domin ganin shine zaune hannun shi rike da wani dan karamin glass cup yana shan ruwa daga shi sai short nicer da kuma singlet,


Yayi y'ar rama kadan ga fuskar shi ta kara fayau da ita kyan shi ya kara fitowa ga sumar kanshi na sheki kallon shi takeyi kamar ta hadiye shi tsabar sonshi da ke kara huda jinin jikin ta,


Tunda suka hada ido sau daya ya dauke kanshi tareda maida hankalin shi a kan TV dake kunne a bangon falon,

Jikinta yayi mugun sanyi da irin halin ko inkula da ya nuna mata kaddai ya hakura da ita?


Ko dai har Dady yayi mai iyaka da itan ne? Tayi saurin dafe kirjin ta saboda mugun bugawar da yayi,


Dukawa kawai tayi ta dauki hijabin ta ta nufi hanyar dakinta tana tafiya tana waiwayen shi Amma ya dauke kanshi ko kallon ta baiyi ba,


Tana shigewa ya ajiye cup din hannun shi tareda runtse idanun shi ya kai ma iska naushi wasu irin hawaye ne da baisan ranar daina zubar suba suka rinka Ambaliya a kumatun shi,


Dady ya shiga tsakanin su kuma yanzu ya dakko ta ya kawota har cikin gidan bayan yasan cewa zuciyar shi bazata taba hakura da ita ba idan har zai rika ganin ta a kusa dashi,


Ahankali ya Mike ya na tangadi kamar yasha wani Abu ya nufi dakin shi yana tafe yana kallon kofar dakin da take ciki'


"Tun shigar ta dakin ta fada kan gadon tareda dafe k'irjin ta " wani irin sonshi ne ke kara fisgar ta ga kuma wani irin mugun feelings akan shi da take ji don tana tuna irin yanayin da ta ganshi lokacin da ta shigo'


Tasan ALLAH yayi mai kira irin ta zaratan maza kamar ba karamin yaroba ba Abinda yake mugun burgeta a jikinshi irin wannan sumar dake kwance ako ina ajikin shi,


Nan da nan taji tsigar jikinta na mikewa wa har wani irin yam takeji a jikinta don zuciya da sake sake har ta hangota kwance a cikin wannan kyakkyawan kirjin nashi mai fad'i




Ta Dade tana sanya wa zuciyar ta Abinda Sam bazai taba yuwuwa ba sannan ta mike dakyar ta fada bathroom ta watsa ruwa tareda dauro Alwala saboda la'asar ta kusa ta yi Salla tareda Addu'ar ALLAH ya kawo mata mafita sannan ta shirya cikin wata doguwar rigar shadda blue wadda tasha stone work kamar wata sabuwar Amarya ta daura dankwalin kayan sannan ta feshe jikin ta da turaruka masu sanyin kamshi ta kalli Kanta a mirror ita kanta tana mamakin irin wannan kwalliyar da tayi a dai dai wannan lokacin,


Ta fito hannun ta rike da wayar ta sai baza kamshi takeyi kanta a kan wayar tana duba sakon da Nasir ya aiko mata,


Kamshin turaren shi da kuma zazzakar muryar shi mai tsaya wa arai tayi mata welcome,

Tayi saurin daga kanta tareda kallon shi yana sanye cikin kana nan kaya farare kamar koda yaushe ya fito kamar ka sace shi ka gudu,

Yana tafiya cikin natsuwa waya yakeyi akan Aikin ginin su na company kawai ji yayi yayi karo da mutum wayar dake hannun shi da tata gaba daya suka tarwatse


Tun Fitowar ta da ta dora idanun ta akanshi ta kasa cirewa batasan lokacin da ya karaso kusa da ita ba,


Tundaga kasa ya fara kare mata kallo tayi masifar tafiya da shi


Har ya dire akan fuskar ta da d'an yi ma make up kadan zuciyar shi na har bawa cikin sauri yayi saurin saita kanshi ya duka tareda kwashe wayar shi da ta watse ya mike batareda yace mata komai ba,


Gaban ta na faduwa tayi saurin kiran sunan shi,


"Abdul' yaja ya tsaya kamar an dasa shi tareda dunkule hannun shi yana mai jin bugun zuciyar shi na karuwa,


Ta matso cikin karfin hali har zuwa gaban shi ta kalle shi cikin ido,


" Abdul nayi maka laifine? Ya dan kalle ta shima idanun shi duk sun juya " me yafaru?


"Abdul don't play innocent " tunjiya nazo gidan nan ka ganni kuma Amma ka nuna baka ma damu dani ba bayan ba haka muka rabu ba


"Meye ya canja? " komai ma ya canja kalli y'an da kake share ni Abdul bayan ba haka kakeyi mun ba ta furta kamar zatayi kuka,


"Yaya nake miki a da da banayi yanzu? Ta ya mutse fuska kamar zatayi kuka" haba Abdul ka fa canja sosai Abdul din da nasani A kullum yana son kula dani yana damuwa da Al amurana Amma yanzu ko kallo na ma bakason yi,



"" Hmm meye Amfanin kulawar bayan bakya so Kince Kinfi karfina har ma kin iya bawa wani namijin dama ya turo to kuma yanzu me kikeso inyi?


Gashi Dady ya ce infita hanyar ki don haka mu yi zumunci kawai dama kin girme ni don haka I a continue calling you my Aunty ko ba haka kikeso ba?


Ya fada yana kallon yanayin ta" kanta ta fara girgiza wa " no Abdul ta furta dakyar idanun ta na fitar da ruwan hawaye'


Yayi saurin dora hannun shi akan fuskar ta yana mai share mata hawaye " ya isa haka please ya furta muryar shi na rawa" horon zaiyi min yawa kibarni kawai da Abinda yake damuna don't furnished me with your tears please,


I can't take it,seaing you crying hurt me A lot
Ta rike hannun shi tareda yin dariya kadan " I no you still love me ta na share hawayen ta da hannu daya,


"Ruman koda ace ina sonki meye Amfanin shi yanzu bayan Dady ya shiga tsakanin mu kuma kema bakya son.....


Tayi saurin rufe mai baki batareda ta shirya ba ta furta" I love you too Abdul I really do, bazan iya Rayuwa da kowane namiji ba bayan kai Kaine farin Cikina ina sonki kamar y'anda kake so na Abdul,



Jikin shi na rawa ya riko kafadunta " said it a gain please Ruman tayi saurin dai daita Tunanin ta domin ta d'auka a zuciya take zancen batasan ya fito fili ba tayi saurin zare idanu zata waske ya riketa tamau tareda riko hannun ta ya nufi dakin shi da ita,



Yana shiga ya kulle kofar tareda zaunar da ita akan kujera irin ta hutawar nan dake cikin dakin ya zauna a kasa fuskar shi na bayyanar da Annuri


Ita kuwa duk kunya ta gama rufeta wai itace ta furtawa kanin ta cewar tana sonshi


"Ruman look at me please"" ya furta Ahankali " ta dago kanta kadan cikin jin kunya ta kalle shi " da gaske kinason Abdullah? yaushe kika fara sona don ALLAH? Meya sa kika ki nunamin hakan kiketa wahalar da Rayuwa ta ?


Ta kalle shi cikeda jin tausayin shi dake kara ratsa jijiyoyin jikinta "Abdul Am sory kasan dalili na tun farko ta yaya zan iya nunawa duniya cewar kanina nakeso"


Ya hade rai " kinga matsalar ki ko songirma "gashi taurin kanki yanaso ya jefa mu cikin matsala wai ma da shekara nawa kika girme ni ? Da kullum zakiyi zancen shekaru


Ya mike tsaye tunawa da yayi da kashedin Dadyn shi" ya girgiza kai " is to late now Kinriga kinja mana Ruman don haka yanzu bamuda wata mafita saidai kawai mu hakura tunda har kin fitar da mijin da kikeso ya juya zai fita tayi saurin riko hannun shi hawaye na bin kuncin ta,


Tana girgiza mai kai" Abdul yanzu zaka iya hakura da ni? Yanzu kana nufin zaka barni in Auri wani bayan gaka ?

Ya kuma juyowa zuwa gareta " haka kika zaba tun farko shiyasa kika yita nuna taurin kai " yanzu ya kikeso inyi Dady ya fadamin idan har na furtawa wani a cikin family ina sonki bai yafe mun ba,

Don haka yanzu kece kawai zaki nema mana mafita ki fadawa Hajiya kawai ko Baba Muhammad sune kawai zasu iya tsaya mana,


"Bazan iya ba Wallahi inajin kunya" ya matse fuska yafara kokarin cire hannun ta Acikin nashi ta kara rikeshi tamau ,

Ki sa kemun hannu intafi Ruman fada kawai kikeyi Kice wai kina sona idan har kina sona mai zai hana ki fada wa magabatan mu ,


Jikinta na rawa ta fada kan kirjin shi tareda rungume shi kamar zasu fadi ta sanya kuka mai ratsa zuciya,


"Wallahi bani nace Sulaiman ya turo ba ni bana sonshi Amma bazan iya kallon idon Dady infada mai hakan ba bayan yana ganin ya isa dani " please Abdul do something,


Wani iri yakeji tun daga kan babban yatsar kafarshi har zuwa kwakwal war kanshi ya sanya Hannayen shi duka biyu ya zagaye ta kamar zasu maida juna ciki,.


Sun dauki lokaci yana manne da ita Ajikinshi saida yaga suna shirin zubewa sannan ya dan fara sassauta rikon da yayi mata,


Ya dan dagota kadan tareda yin murmushi " my Aunty ki dan sassauta min haka mana wannan irin matsa ai Saiki sa tsohuwar damuwa ta tashi kinsan dani dake s....saurin rufe mai baki tayi tana dariyar jin kunya



Kibar ni infada mana " ina sonki fiye da kaina my Dream kar ki Auri wannan gayen zuciya ta zata buga ke ko ganin ku a tare banason yi don ALLAH ki daina kulashi kafin mu samu mafita,


Ta yi saurin share hawayen ta " tareda kada mai kanta kadan yace " tank you Amma yanzu za arika bani kulawa ko? Inaso soyayyar mu ta zama sirri kafin mu nemi mafita kinji don ALLAH k'arki kuma juya min baya I can't bear to loose you


Ta yi murmushin da ya kusa tafiya da numfashin shi domin dimple dinta yayi mugun lobawa " please my dream ki d'an rage yimin irin wannan murmushin idan kikayi wata rana zai janyo inyi aika aika,


Koda yake Am still a small kid har yanzu ban kosa ba ko tayi saurin bude baki tajuya da dan guduna domin tasan tsokanar ta yakeyi yayi dariya mai dan karfi kadan yabi bayanta yayi saurin riketa,


" muje ki rakani mu siya waya tunda kinfasa mana garin kallon masoyin ki ta kalle shi tareda dukar da kanta cikin jin kunya,



"Muje kaga su Hajiya kafin mu tafi " ya waro ido sannan ya riketa cikeda jin dad'i da kuma nishad'i ji yake kamar karsu fita suyi ta zama a cikin dakin suna shan soyayyar su Amma ina yasan zaman Sam bazai haifarda da mai idoba,


Tana gaba yana biye da ita cikin jin dad'i har suka isa gefen da su Hajiya suke suna zaune sai hirar su sukesha da ka gansu kasan suna cikin kwanciyar hankali,


Da sallama suka shiga " Aa kaga turawa dama kana garin ? Inji Hajiya tafara tsokanar shi" eh Granny ina nan bansan da zuwanku ba sai yanzu my d... Tayi saurin taron numfashin shi " yanzu nake fada mai kuna nan kuma,

Yayi dariya domin dama da gangan yaso fadar my dream din sundan dade a wurin su suna d'an hira har saida ya matsu da kanshi yake mata signal akan sutafi,


"Hajiya zamuje shopping yanzu zamu dawo nida Abdul' ta fada cikin dakewa kamar ba komai a tsakanin su,

" to kudawo lafiya kardai Kuyi dare ta mike tare da cewa to tayi gaba shima ya bi bayanta dakinta ta koma yana biye da ita kamar bindi har ta bude world rob batasan yana biye da itaba saida ta Ciro gyalen da zata yafa taji yace " ki canja kisa hijab,

Tayi saurin kallon shi yana tsaye a bakin kofar ya harde hannu a kirjin shi yana mai binta da kallon so da kuma birgewa ,


"Biyoni kayi har cikin daki idan wani ya ganka fa?
Waye zai ganni ? ai tunda kika Amsa cewar kina sona bazan barki kihuta ba har sai na takura miki kin Amince kinfada wa su Hajiya Andaura mana Aure kowa ya huta,

Dariya kawai tayi tareda Ciro katon hijabi ta sanya ta kalle shi " Wannan yayi? " saida ya kare mata kallo sannan ya daga mata Hannu Alamar yayi ta sanya takalmin ta Mara tudu,

"Muje ko ta furta bayan ta karaso kusa dashi ya sauke Ajiyar zuciya yana mai kallon ta kamar zai hadiye ta,

Hannun shi ya sanya tareda fisgota zuwa kirjin shi saida ta d'an ji tsoro " Abdul ""

Ta fada da d'an karfi shikuwa ai tuni ya fara shinshina dai dai wuyan ta tana d'an ture shi "Abdul muje mana dare zaiyi man...


Kasa karasawa tayi sakamakon kiss din da ya manna mata a kumatun ta kafin ta kara motsawa ya kuma manna mata a goshi gaba daya ya kashe mata jiki da zafafan kisses dinshi dake tasiri a jinin jikinta nan take jikinta ya fara rawa,


" Abdul stop" ya furta dakyar tana nokewa " ya d'an girgiza kanshi kadan yana kara cacumar ta dakyau ,

"How can I stop my body? I can't Ruman Allow me please"


Kar kiyi kokarin raba jikina da naki don ALLAH yana maganar still fuskar shi na kan yawo akan tata ya hade goshin su wuri daya,


Tana dan zamewa saboda irin tasirin Abinda yake mata Ajiki "Abdul please ta kira sunan shi da ya kuma tsuma zuciyar shi batareda ta shirya ba ya manne bakinshi akan nata,


Ya fara tsotar lebenta na kasa a hankali yana d'an hura mata iskan hancin shi dake fita dakyar cikin gwama numfashi batasan lokacin da ta kara tallafo keyar shi ba ta fara tsotar leben shi na sama,

Ai tuni ya manne ta gam ya fara tsotar bakinta kamar zai cire mata shi a hau kace kafin ya samu damar cafko halshen ta yana mishi lafiyayyan tsotar da ke shirin dauke numfashin su ba Abinda sukeyi sai gwama numfashi mu samman shi da Sam ya kasa control din kanshi ji yakeyi idan ya tsaya numfashin shima tsaya wa zaiyi,


Jin yana kokarin daga hijabin jikinta yasa tayi saurin saita natsuwar ta tareda kwace lips dinta daga nashi dakyar yaja numfashi tareda Sakin ta ya fada kan sofa yana gwama numfashi mai wuya,


Ita ma dakyar ta iya tsaya wa da kafafunta kafin ta fita daga cikin dakin da sauri tana fita ta zauna akan kujera tana runtse idanun ta tareda matse cikinta ita kadai tasan irin namijin kokarin da tayi wajen hana zuciyar ta biye mishi,


Tana haka ya fito har ya canja kayan jikinshi zuwa wasu daban ta d'an kalle shi kadan ta dauke kanta " idanun shi gaba daya sunbirkice kamar wani Masha yi,


"Muje ya furta a kasalance mikewa kawai tayi ta wuce gaba yana mai binta a baya sai famar cije lips dinsa kawai yakeyi,


Shi ya bude mata kyakkyawar sabuwar motar shi suka shiga ya tayar da ita saida suka hau titi ya d'an kalle ta


" Ruman zuciya ta bazata iya jure wa ba nagaji Na matsu kizama matata kiyi wani Abu akai don ALLAH kafin in fada halaka ya fada tareda riko hannun ta daya yafara murza wa a cikin nashi,


Wallahi dakyar nake samun bacci inada karfin sha'awa mu samman akanki saboda kece muradin zuciya ta

Wai shin kinajin irin y'anda nakeji kuwa ? Ya janyo hannun ta zuwa kirjin shi ki taba kirjina kiji y'anda yake bugawa da karfi


Ruman ki tallafi Rayuwa ta ina cikin garari kulawar ki kawai nake bukata ke kinsan soyayyar mu mukaddari ce ALLAH ne ya sanya min soyayyar ki Acikin zuciya ta ba yin Kaina bane,


A hankali ta zame hannun ta tareda dukar da kanta kasa " yanzu' ya kake so inyi Abdul bayan na fada maka nima ina...



_"Say it please I wants to hear it a gain from your mouth "Ruman say u love me please "_


Kallon shi tayi " muna kan titi ne fa ka kalli gaban ka ya ki juyawa still yana kallon ta " tsoron me kike ji? K'arki mutu to ai idan ma mutuwar ce tare zamu tafi don bana fatan in mutu inbarki saboda zaki zama rabon wani nafiso mutafi tare


"I love you" ta furta da sauri saida ya kusa Sakin kan motar saboda y'an da Kalmar ta shige shi


"Yayi saurin tsaya wa tareda juyowa dakyau yana fuskan tar ta" woo My dream tank you yana Sakin murmushi mai kayatar wa _I love you more and more my dream_


"Abdul muje magrib nayi fa" ai ni to idan har zakiyita kiran sunana a haka bakya so mutafi kenan don kina jefani cikin yanayi,

"Meyasa Bakajin kunya ta ne wai? Hhhh yayi dariya " ina namijin zan tsaya jin kunyar wadda wa tarana da kanta zatayi min wanka,

Nima ko ALLAH idan mukayi Aure zaisha shagwaba don narkewa zanrikayi komai sai kinyi mun da kanki har shafa mai da sa kaya,


Ta zaro ido waje " da girman ka zanyi ma wanka? " kai Aunty na ni yaushe na wani girma nifa ko yanzu zan iya tube wa a gabanki bayan ni har yanzu karamin yarone..........✍




*_Abin ya girmama Abdullah ni nayi nan baruwana kaida fan's dinka_*


Masoya Afuwan network nayimin Abinda yaga dama


*Matar Soja*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KUSKURE NA🙆*
_Love & Destiny_



_Written by Fenerh_

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain✍🏽~*

🅿➡2⃣1⃣

Tafiya sukeyi kamar karsu isa wurin da zasuje saboda farin cikin da suke ciki Abdullah kuwa baya minti biyu saiya kalleta fuskar shi dauke da wani irin kayataccen murmushi da kuma Annuri na farin ciki,


Pz sukaje ya zabo masu wayoyi masu kyau da kuma tsada har saida taso tayi gaddama akai ganin uban kudin da ya fitar domin siyan waya kawai,


"Kinfi karfin komai a wurina my dream banaso inkuma baki Abu kiyi kaddama a kai, ko bakya sona ne kamar yadda kika fada?

Ta kalle shi " meyasa zakace haka gani nayi kawai wayar tayi tsada da yawa,

"Amma duk tsadar ta bata kai ki ba ko? Yafada yana dariya,

Daga nan ya wuce da ita Inna I dear shopping complex tunda ya faka ya juyo tareda riko hannun ta daya " Baby na kin tuna Abinda yafaru Anan?


Tayi dariya kadan tareda kawar da kanta gefe , shima dariyar yayi sannan ya fito ya bude mata kofa " muje my Queen "


Ta kalle shi " kaima zaka fara kirana da wannan sunan ko?

"Uhm ai Gaskiya ne you are a Queen ya d'an matso kusa da ita kamar zai rungume ta " and you the Queen of my heart


"Ina sonki sosai Ruman' tayi saurin wai gawa saboda idanun mutane dake kallon su" muje Abdul kaga ana kallon mu'

"To shine me? Ni dai muje mema zakayi Anan daka kawo mu?

" Muje kiga me zanyi ya riko hannun ta ta fisge tana dariya ALLAH Bakada kunya Abdul,


Tayi gaba yabi bayanta yana mai Bata Amsa " idan naji kunyar ki na fada miki nizan sha wuya shiyasa nake cire kunyar don zata cuce ni nan gaba,


Sun shiga gefen kayan kwalliya ya riko hannun ta tareda matsowa gab da ita ya rada mata "My dream ki dauki Abinda kike bukata anan ,


"Ta kalle shi " ni banason komai Anan mu tafi kawai" ban y'arda ba ya wuceta tareda fara Kwasar kayan kwalliya kala kala da turaruka masu tsada da kuma kamshi saida ya cika dan karamin Kwan don dake Ajiye domin irin hakan,

Sannan ya jata zuwa gefen kaya ya fara zaba kamar zai bude wani d'an karamin shago saida ta riko hannun shi" Abdul ya isa haka mana ya zanyi da wa innan kayan bayan wa inda Dady ya siyomin,


"Idan Inayin Abu ki kalle ni kawai banason magana ya fada yana d'an bata fuska,

" kayi hakuri tom nayi shiru " uhm that's better ya cigaba yakoma kwaso mata jakun kuna da kuma takalma designers,


Haka takoma gefe kawai tana kallon shi har ya kwasa iya kar y'anda yakeso sannan ya biya aka kwashe musu zuwa mota,


Saida ya cika seat din bayan motar shi tab da kaya sai binshi takeyi da ido don Abin yaso bata tsoro saika ce hauka,

Suka nufi gida bayan ya tsaya ya siya musu gasassun kaji suna isa ana kiran Salla ya bude mata motar ta fito,..


"Kishiga ciki zanje masallaci indawo kisa Mary ta hada min coffee yunwa nakeji ina dawo wa zanci Abinci'


Ta ce " to ta wuce dauke da ledar wayoyin su ya sa mai gadin su ya kwashe mata kayan zuwa cikin gidan,


Saida ya shigo da kayan ma ta kara ganin yawansu tana mamakin irin dukiyar da ya narkar a banza yanzu'


Bathroom ta fada saida ta watso ruwa sannan ta nemi wani Riga da wandon Pakistan pencil ne wandon ya kamata dam sai rigar da tasha tsagu tundaga kasa har zuwa kusan hips dinta daga sama ma ta kamata dam komai ya bayyana tayi kyau sosai ga sumar ta datasha gyara ta kameshi a gefen wuyanta da ribon tareda kitse bakin shi,


Sai baza kamshi takeyi kamar wata sabuwar Amarya sannan ta sanya hijabin ta ta tayar da Salla, saida ta idar ta tuna sakon shi na coffee da kanta ta mike ta nufi kitchen din,


Tundaga farkon kitchen din ta fara tasbihi tana ganin exactly irin wa inda ake nunawa a TV Abin ya mugun burgeta da kyar ta gano wurin da gas cooker din yake tana tunanin y'anda zata kunna Mary ta shigo,


"Can I help you ma'am? " yeah please come and on this gas for me I want to make coffee'


Da taimakon Mary ta hada mai lafiyayyan coffee ta sanya a dan karamin flask mai kamar jug saboda kar ya huce ta dora shi a wani madai daicin tray ta dora cup da kuma spoon guda daya ta d'auka tareda nufar falon da shi w'anda yayi daidai da dawowar shi daga masallaci,


Tun Fitowar ta ya zuba mata ido yana Sakin kayataccen murmushi saida yaga zata nufi dining sannan yayi gyaran murya "

Tayi saurin juyowa ta kalleshi tareda Sakin kyakkyawan murmushin da ya bayyana kyawon fuskar ta,

"Ya fara matsowa kusa da ita yana tafiyar shi mai daukar hankali da kuma isa na irin mazan da sukejin suna cikin lokacin su'


" Coffee din ne Anan ? " eh "muje dakina muci Abinci I keep something for us,

Ta dan kalle shi irin rashin yardar nan " inaso inje wurin Hajiya ni banajin yunwa kaga batasan mundawo ba karsuyi tunanin ko muna waje ga dare yayi".


"OK muje mu gansu mudawo yanzu I need your time gobe inaso inje Kaduna induba Aikin mu,


Ta wuce gaba yana mai bin bayanta da kallo tareda jin wani irin sauyin yanayi dake ratsa jinin jikinshi"


"Yayi saurin matsawa kusa da ita " my Queen irin wannan Adon zaki dauki Alhakin dan karamin yaro fa tayi saurin kallon jikinta " wane ado nayi Anan ?


"Kayan bacci ne fa" kai wallahi bazan y'arda ba idan munyi Aure kirika sanya wannan kayan ba ai zaki wahalar dani sosai ni Nafisan ganin ki dagake sai y'ar sexy sleeping dressed,


Ai da sauri ta wuce don batason jin rashin kunyar shi Sam baida kunya kokadan wallahi " dariya ya sanya na yadda ta sanya sauri tayi gaba batareda ta jira ta karasa jin sauran zancen


"Da Sallamar ta ta shiga ta samu gwaggo Amina da Hajiya kawai suna hira ta sanya dariya cikin shaki yan ci" Hajiya kaka mai Abinci ta zama y'ar fursuna yanzu bakuda aiki saidai kuci kuyita zabga hira ko kuma kallo ,


"Ai dole kiyi dariya tunda iyayenki sun kunshe mu a cikin wannan gida kota ina

Please Login or Register in order to submit comment