Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fuskar da nake gani A mafarki na har ma na fada Abokina ina cikin damuwa kasan cewar mukhtar kwararre ne a wajen Art nan da nan na kwatan tamai irin yanayin fuskar da nake gani,

" Tunda nasamu wannan zanen A kullum saina tasa shi gaba ina kallo, kusan duk w'anda nake tare dashi yasan da dream girl dina wasu har tunanin kwakwal wata ta tabu sukayi,

"Momy na kuwa har hadani tayi da sychlogy doctor tayi cikin dubara ya dubani ya fada mata lafiya ta kalau kuma zai iya yuwuwa Abinda nake gani Gaskiya ne,

" Tun daga lokacin suka kara bani kulawa da kuma tattali har na shiga shekarar karshe a karatuna kuma a shekarar ne damuwa ta ta karu akan dream girl dina,

"Sakamakon mafarkin ta danayi muna making love batareda na gama tantance wacece ita ba Aranar na wayi gari nagan ni kaca kaca,

" Gaba daya na wuni da matukar baka tuwa da kasan cewata da ita ina mai burin dama zan kuma kwanciya bacci inkuma samun biyan bukata da ita kuma domin gaba daya Abin ya ki fita Acikin zuciya ta,

"Dakyar nake bacci saboda nasa Abin Acikin zuciya ta kuma tundaga ranar ban kuma wannan mafarkin ba sai Abin yazamar min damuwa sosai wani lokaci har kuka nakeyi ga ciwon Mara da ya sani gaba akan tsantsar sha awa da kuma soyayyar fuskar mafarki na har ma da daren mu na farko Acikin mafarki na da ita,

" A daddafe na kammala karatuna tareda kwalina na zama cikakken Likitan mata,

Na kammala ina shekara Ashirin Aduniya A lokacin nasan inada yancin kaina shiyasa na damu iyaye na Akan subani dama infita yawon bude idanu for the first time A Rayuwata,

"Domin inada kuduri a cikin zuciya ta na neman dangin mahaifina Duk da bai fadamin cikakken tarihin shiba na fahimci cewar shi d'an Nigeria ne,

" Da neman shawarr mukhtar na samu Dady na nafada mishi cewa inaso in shigo Nigeria ya fadamin inane garin su yake?

"Dariya kawai yayi irin ta manya ya fada min suna cikin Karamar hukumar Kaduna wato Zaria ya fadamin ne kawai a tunanin shi shirme kawai nakeyi saboda na taso cikin gata Sam bazan iya Rayuwa a Nigeria ba

" Lokacin da na fadawa mukhtar ya yi farin ciki ya fadamin cewar shima haifaffen jahar Kaduna ne don haka idan har nazo inne meshi zai tayani neman yan uwan Dady na,

"Lokacin da na gama shirina Dady kawai na fada ma kasar da zanje domin nasan idan Momy na ta sani Sam ba zata y'arda inje ba,

" Ita da kanta tayi min odar motoci har ma da security domin kula dani ta kuma basu damar A duk inda nake su kula dani da kuma lafiya ta,

"Ak wato Ahmde kabir Asalin dan Nigeria ne yana Aiki tareda Mahaifina kusan tunda na taso na gansu tare Amatsayin mai taima kamai Akwai Amana mai karfi a tsakanin mu dashi duk da kasan cewar ya girme ni,

" Yan mata kuwa tun bansan komai ba suka fara bibiya ta kasan cewar a kasar ba wani Abu bane ,

Na diro kasar Nigeria tareda taimakon Ak da kuma mukhtar kuma tun kafin inzo na bada umarnin Asiya min gidan da zan zauna,

"Aranar da naga gidan da Ak yasiya a cikin GRA Sam baiyi min ba kasan cewar. Nafi bukatar zama Acikin mutane nasa Ayimin cigiyar gida a cikin manyan unguwan nin dake cikin gari,

" Saidai Akayi rashin sa'a bamu samu hakan ba sai dai haya da farko naki Amince wa da hakan Amma daga baya dole na Amin ce kasan cewa na bako a garin kuma ina bukatar in binciko dangin mahaifina,

"A ranar da Momy na tasan cewa ina Nigeria tayi fada sosai har ta tashi hankalin Mahaifina ni da kaina na bata hakuri tareda kwantar mata da hankali,

" ta daga hankalin ta sosai domin Abinda take gudu kenan kuma ya faru bata kaunar ko Mahaifina ya shigo Nigeria bare kuma ni,

"Shigowa ta Nigeria nasamu Karin haske sosai akan Addini na domin har wani malami mukhtar ya hadani dashi domin ya kara wayar min da kai Alhmdulillah

Now am a Muslim sakamakon karbar musulunci danayi A hannun wannan malamin

Gani A tushen Mahaifina ta ina zanfara neman dangin shi?

" A gefe daya ga muguwar damuwar da ke kara Addabar zuciya ta dangane da fuskar mafarki na wato my dream girl,

"W'anda Abin har yazamar min jiki kwatsam ban zata ba kawai ranar na ganta A zahiri batareda nasa ran ganin nata ba tsabar shock da kuma da kuma tsananin tashin hankali ya hanani koda motsawa har ta bacewa gani na,

" Aranar hauka ne kawai Banyi ba sakamakon samu da rashin da nayi w'anda har ya janyo min ciwo har iyaye na nakira tareda fada musu naga fuskar mafarkina A zahiri...............✍

*Da fatan masoya bature suna biye da ni domin yanzu ne wasan zai fara kuci gaba da biyoni*

*Matar Soja*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KUSKURE NAπŸ™†*
_love & Destiny_



_Written by Fenerh_



https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*

*A Gaskiya d'an Adam mai iya mai sai Allah Ada can idan naji marubuta na complaine Akan readers sai suyi ta bani mama ki, ince meyasa suke bata ransu Akan wasu mutanen, Ashe su kadai suka San irin Abubuwan da suke gani, wallahi burina in nishadan tar inkuma fada kar daku my fan's Amma wasu basa tsaya wa suyi tunani wane irin lokaci kake kashe wa kake tsaya wa ka tsara musu typin? Munada iyali munada Aikin yi rubutu ra ayine kawai ba wai dole bane ni Anawa bansan Saura ba idan har nagama typin nayi posting duk wasu sakonni da suka shigo sai bayan na rufe data nake karan tasu domin Abubuwan da yawa zakaga mutum kusan goma ta prvt suna neman ka tura musu littafi bayan ka gama typin kabi grp sama da Ashirin kayi post, A Gaskiya raina jiya yayi matukar baci Akan wata bai war Allah da ta fada min magan ganu masu zafi Akan tayi magana ban Amsa taba, don Allah yan uwa shin kuna tunanin irin datar da muke konawa domin tura muku littafi shin kuna tunanin cajin da muke cinyewa a wurin typin shin kuna tunanin sauran lokuta da ya kamata mu bawa yayan mu? Ni dai ina neman Afuwar duk w'anda na batawa rai ya yafe ni dan Adam Ajizine Allah yasa mudace.*

πŸ…Ώβž‘1⃣1⃣
"Wani irin sanyi jikin Ruman yayi Gaba daya jikin ta ya gama mutuwa murus ba haka taso labarin ya kareba,

" ALLAH sarki Ashe haduwar su mukaddari ne Ashe haka yake sonta ? lallai ta y'ar da ALLAH shine mai y'anda yaso,


"Wani irin shauki takeji Acikin jinin jikin ta "Wayyo ALLAH kar ka hukunta ni ta wannan hanyar,ta furta Ahankali tareda dafe saitin zuciyar ta,


" Yanzu Ashe shi musulmi ne kenan me meyasa taki tsaya wa ta saurare shi ya fada mata labarin da bakin shi kila bazata tafka irin shirmen da ta tafka mishi ba,

"Ta fara tuno lokacin da tafara ganin shi a bakin Congo da kuma haduwar su Inna Idear shopping complex da irin ruwan masifar da kullum take zabga mai,


" wani irin runtse ida nun ta tayi ta tuno da irin marin da ta zabga mai A cikin gidan nan,

"Zunbur ta mike tunawa da irin dramar da suka kwasa dazu wani irin murmushi ne ya subuce mata"


"Ta samu kanta cikin tsananin farin ciki Ashe haka yake sonta?

" mikewa tayi tareda janyo wayar da ta manta da Sha aninta ta kunna ta "Ganin ba wani caji tayi saurin plugin dinta ta koma gefe zaune tana kallon wayar tana kuma Ayyana cewar da ma zai kira ta yanzu,


" Akwai tanbayar da take so tayi mishi " Wacece wannan Yarinyar da ta gansu ranar har take kokarin rungume shi,


"Wani dogon tsaki taja tareda mikewa ta duba Agogo kusan karfe biyu na dare Amma gaba daya bacci ya kaurace wa idanun ta burin ta kawai gari yawaye,


" Ganin Sam tunanin shi bazai bari ta runtsa ba yasa ta mikewa ta fita cikin Sand'a Batareda ta tashi Hajiya ba da take jin munsharin ta har cikin falon su,


"Dakin da ya zauna ta nufa ta dade a kofar dakin tana tunani " Ko dai ya kwashe kayan shi Aciki ne? Ta tura kofar dakin tayi matukar mamakin ganin kofar Abude saida ta leka ko ina tar da haske " Kamshin shi din nan mai mugun tsada ya fara yimata welcome,.


"Ta wani lumshe idanu tare da Jan numfashi ta shaki kamshin har cikin kwakwal war ta,

" tayi matukar mamakin ganin komai Acikin dakin shin yaushe suka kawo duk wa innan kayan?

"Ganin system din shi Ajiye a gefe tayi matukar mamaki da saurin ta ta kulle dakin ta karasa jikinta na rawa ta bude tareda kunna ta,

" Ta kara sakan kancewa da lamarin shi sosai ganin Hoton zanen fuskar ta a fuskar system din shi,

."a nan ta fara tunani Wato kawai ikon ALLAH ne ya kawo shi gidan su haya batare da yasan gidan su bane?


"A Gaskiya zataso jin karshen labarin nashi tana so ta sani shin har yanzu yana kaunar ta kamar da?


" Aranar kwana tayi tana yimai bincike a cikin system har ta isa cikin folder dinshi ta hotuna


"Masha ALLAH ta furta Alokacin da ta fara karo da wani kyakkyawan Hoton shi yana zaune Abakin Beach dagashi sai gajeran wando wuyan shi sanye da towel fari sai wani irin kwamemen sun glass da yayi masifar yimai kyau,


" Hannun ta takai Akan sajen fuskar shi da yasha gyara ta shafo shi A hankali domin Abin yayi matukar kayata kyakkyawar farar fuskar shi,


"Ahankali ta rika bin hotunan shi da kallo kowane yayi matukar burgeta ta dauki lokaci tana kallon shi,


" Kiran sallar farko ya dawo da ita hayya cin ta ta yi saurin zabura ta mike da sauri har da system din ta kulle kofar ta koma cikin dakinta ta yi sa'a Hajiya bata farka ba,


"Alla Alla takeyi gari ya waye ta isa makaranta saidai kash tuni fuskar ta ta baci saboda tunawa da tayi yau basuda school kasan cewar Asabar ne,



" Tunda gari ya waye ta rasa ta ina zata fara wayar ta kuwa tana manne da ita ko da Ace zataga kiranshi gashi ita Gaskiya bazata iya kiran shiba ya Renata,

"Tafiso yanzu idan ya kirata ta daina yimai wulakanci batareda ta nunamai cewa ta damu da shiba,


" Yau Hajiya kanta taga canji "Ruman da sai tayi da gaske take tashi Abacci yau ita ce ta tashe ta har ma tayi sharar gida kafin Afara sana'ar Abinci,


" Binta kawai takeyi da idanu" Ummu zonan, ta karaso cikin mutuwar jiki " gani Hajiya, " meke damun zuciyar ki?


"La Hajiya me kika gani? ba Abinda banganiba y'ar nan kinada damuwa ne? " aa bakomai " ko dai kinaso kibi ubanki ne?


"Nan da nan nasamu kaina da daga mata kai domin dai banda mafita' ta bata rai " Yanzu Ummu gudu wa zakiyi kibarni ni kadai?


"Aa ni na isa kawai inaso inje ingansu ne indawo ta karasa kusa da ita ta rungume ta " haba my kakus ai bazan iya Rayuwa babuke ba,

"Ta ture ta " ni sakemin wuya kin wani shakeni "Idan kinyi Aure fa dani zakije?

" Sosai kuwa idan badake ba ba inda zani' to naji naki shirmen sakeni nidai

"Yauwa kakus Anjima zanje wurin Hajara, baki kawai ta saki tana kallon ta cikin mamaki" ta fara taba wuyan ta " Ummu Bakida lafiya ne" kaji Hajiya ni kalau nike

"Yo keda kullum take faman rokon ki kije Amma kirikiri Saiki ki zuwa yau ko keda kanki kike cewa zakije,


Akwai Abinda zan Amso ne nakirata wayar bata zuwa naji ALLAH ya kaimu,


" A gurguje ta ga ma Aikin ta ta shirya cikin doguwar Riga Abaya mai shape baka harda wasu igiyoyi a gefen ta dake kara tsuke rigar ta dakko wani farin breziya hijab tasan ya ba wata kwalliya tayi ba Amma tafito kamar wata balarabiya,


"Ta sanya wani farin takalmi mai dan tudu da yar Karamar jakar shi mai doguwar igiya ta rataya ,

" Wayar ta ta d'auka ta jefa cikin jaka tafito kamar ka saceta ka zura da gudu


"Hajiya sai tasbihi takeyi tare da binta da Addu a ALLAH ta tsare min ke daga sharrin makiya ya kareki daga mugun ido,


" ko tsakar gidan su masu Abincin Hajiya Kallonta sukeyi wata tsohuwa da suke kira baito tace "Masha ALLAHU zinariya kinfito das dake tubarkalla,


" Wani irin farin ciki take ji domin tasan shima sai ta burge shi idan har ya ganta,



"Tana isa kofar gidan su hajara suna fitowa ita da Sumy " Sunyi matukar mamakin ganinta gashi tafito a ainihin Queen dinta,


"Suka sa shewa da ihun ganinta " tace shegun gari ina zuwa? Hajara ta ya tsuna fuska "Asibiti, " Waye ba lafiya?


"W'anda kike kokarin kashe wa' wani irin faduwa gabanta yayi " wa kike nufi zan kashe Hajara?

"Ta furta muryar ta na cracking,
" Abdullah mana tunjiya yana Asibiti yaron shi ke fada min yanzu'.
"Waye Abdullah? To bature,


" what Asibiti? Tuni kirjinta ya buga jikinta ya fara rawa har jakar hannun ta tazame tana shirin faduwa,


"Su Kansu kallon reaction dinta sukeyi" Sumy tace Wallahi sai Alhakin yaron nan ya kamaki " hajara tace duba jiya saboda ciwonki duk ya rikice " koda na kirashi daga baya lafiyalau yake nasan kece sila Wallahi


"Idan kika kashe musu yaro Bazasu yafe miki ba, hawayene masu zafi ke yawo a kan fuskar ta" Don ALLAH kumeje nidai inganshi inyaso daga baya kwaci gaba da fadan,


"Cikin sauri suka fada motar jikin su na rawa suka nufi Asibiti...........✍


*Kuyi hakuri da kadan zamu hade masoyana na Asali love you All*



*Matar Soja*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KUSKURE NAπŸ™†*
_Love & Destiny_



_Written by Fenerh_
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽~*


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*


~Dedicated to~
*Umar Dalha &Nabeela*
_U are the best Among the rest guys, muna Alfahari daku A Gaskiya ku ne cigaban golden Allah ya kara tsare mana ku ya kuma kara d'auka ka mana forum din mu_


πŸ…Ώβž‘1⃣2⃣

Tundaga harabar Asibitin suka fara cin karo da security kamar Wani governor ne Aka kwantar ga kuma motocin su kowane dauke da harafin J

"Hajara na fakawa ta fito cikin sauri tana ware idanu burin ta kawai ta dora ida nunta a kan kyakkyawar fuskar shi,

" Ak dake tsaye a gefe ya fara hango ta cikin sauri ya matso kusa da su "Welcome madam,


" Hajara ce da Sumy suka Amsa shi yayi musu jagora zuwa daki na mu samman da Aka kwantar da shi,

"Ita gaba daya zuciyar ta tana wurin shi shi kawai take son gani,suna kawai reception Aka dakatar dasu,


" Tayi saurin waro idanun ta tanabin mutanen dake cikin reception din da idanu " Gaban ta yayi mugun faduwa ganin fuskar wannan bawan ALLAH duk da tana cikin rudu Amma taji wani iri Ajikinta,


"Sai kuma wata baturiya dake zaune Agefen shi cikin wasu tsadadden suit na mata Riga da wando bakake har ma da cover shoe kana ganin ta kasan Hutu da naira sunyi muhalli ko Akasar turai,


" Cikin rawar jiki suka fara gaishe su cikin harshen turanci " hannu kawai Momy ta daga musu Dady ne ya Amsa su cikin halshen hausa ",


" Ak ya matsa kusa da Dady yayi mai bayani cewar ita ce yarin yar da Jeff yake so,

"Ya kwabe shi da cewar kar ya bari Tara taji ya tafi kawai domin suna zancen ne cikin Halshen hausa,

" Kallon ta yakeyi cikin wani irin yanayi tare da jin kaunar ta har cikin jinin shi'


"Ya kalli Momy da gaba daya hankalin ta nakan system din ta tana tura sako "Yayi mata bayanin Abokan Jeff ne sunzo gai sheshi "


"Kallo ta watso musu mai cike da tan bayoyi " yayi saurin nuna musu dakin yace suje yana ciki,

"Itace kan gaba domin duk A k'ag'auce take jikin ta na rawa ta tura kofar dakin,


" Shikadai ne Akwance idanun shi Arufe yana sanye da farin singlet da kuma tree quarter 'Fuskar shi sai sheki takeyi duk da yana cikin ciwo ga dakin na fitar da wannan unique kamshin na jikin shi Akoda yaushe,


"Tunda ta shigo dakin yafara motsa idanun shi Hajara ce ta fara karasa wa kusa dashi cike da tausayin shi Sumayya ma ta bita " suka Ajiye basket din da suka zo da shi na dubiya,


"Ita kuwa ganin shi a kwance gaba daya jikinta ya gama yin sanyi wani irin tausayin shi ke ratsa ta,


" Ta ma kasa karasa wa kusa da shi, Shigowar Dady ne ya d'an dawo da ita cikin natsuwar ta" Ya shigo yana mai bin Ruman da idanu yana jinta har cikin tsokar jikin shi


"My son ka bude idanun ka Your dream girl is here ya furta Ahankali cikin kwantar da murya,



" Ahankali ya fara motsawa tareda dafe kanshi da dayan hannun shi ya motsa bakinshi kadan,

"Saida ya kuma mai maitamai sannan yace " Dady bazata zoba ta tsane ni wai ni yaro ne, "Dady da gaske ni karamin yaro ne bazan iya rike Aure ba?

" no you are a big boy my son, ka bude idanun ka gata Akusa dakai " Come my daughter ya fada yana mai kallon ta '


"Jiki A sanyaye tare da matsanan ciyar kunyar shi ta kara matsawa ya janyo hannun ta ya dora Akan fuskar shi,

" gata Akusa dakai open ur eyes kaji my son, shi kuwa kamar A mafarki ya ji lallausan hannun ta akan fuskar shi,


"Ya d'ora hanun shi Akan nata ya damke shi tamau batareda ya bude ida nun shi ba "Ya jikin da hajara ta furta yasa shi bude ida nun shi domin shi duk A tunanin shi mafarki yakeyi,


" Ya sauke idanun shi atsakiyar nata da suka cicciko da hawayen tausayin shi "Yakara damke hannun ta kamar zata gudu,


" Ya dauki dogon lokaci yana mai bin fuskar ta da kallo har ya sauko zuwa jikinta yana kare ma surar ta kallo tayi mai kyau sosai A cikin wannan shigar da bai taba ganin tayi irin ta ba,


"Ya fara kokarin tashi zaune still hannun shi na damke da nata ' sukuwa su hajara tuni Dady yayi musu Alama da su fita yarage daga shi sai ita Adakin ,


" Ki gyara min filo zan zauna " kanta na duke ta ce " Sakar min hannu in gyara ma tom,


"Idanun shi na yawo ako ina na jikinta " ki gyara min A haka, ta dan kalle shi da gefen ida nu ita gaba daya bata son kallon shi wani irin kwarjini yake yimata sosai gashi ba wani kaya Ajikin shi ga shi ya yaye bargon da ya rufa da shi


"Wasu irin gargasa ne ta ko ina Ajikin shi sunyi wani irin lub club Alamar suna samun lafiyayyun mai da kuma kulawa,

" Tsigar jikinta har wani tashi takeyi Abinka da dama...... Um ba ruwana,

"Yana kwakume da hannun ta a haka ta gyara mai filon ya zauna da kyar ,


" Me ya kawo ki ? Shine maganar da ya fara jifanta da shi,


"Tayi saurin kallon shi cikin idanun shi yaji kallon har cikin kwakwal war shi nan take ya fisgo hannun ta ta fado gefen shi har tana dan buge mai gefen cikin shi yayi saurin dafewa yace Ashhh,


" Jikinta ya fara rawa tayi saurin dora hannun ta saman wurin " Sory ba da gan gan bane ta fada kamar zatayi kuka,

"Kaji ciwo ne? " ya dan kalleta idan har ba gizo idanun shi ke yimai ba yaga Alamar damuwa kwance Acikin ida nunta

"eh ciwo wurin yake yimun tun tuni, likita bai duba kaba ne ? Likita baida wannan maganin " maganin wannan ciwon yana wurin mafarkin zuciya ta,.

"Ya furta yana mai kara murza hannun ta Akan marar shi dake dunkule da wani Abu da yakeji Awurin

" jin Abinda yakeyi yasa ta saurin janye hannun ta ya kalle ta cikin marai rai cewa" meyasa kikazo? Nasan bakya sona kin tsane ni saboda ni yaro ne ko?


"Kinga irin ciwon da kika jamun ko ? Meyasa kikazo wurina ? Nasan kinzone kawai ki karamin ciwo bawai kindamu dani bane nasan my friend ce ta janyo ki,


" Wasu irin hawaye masu zafi suka fara fitowa cikin idanun ta tana mai matukar jin tausayin shi


"Batareda ta shirya ba ta fada saman faffadan kirjinshi tasa mai kuka, wani iri yarrrrr yafaraji tun daga kan yatsar kafar shi har zuwa cikin tsokar kwakwal war kanshi,


" ya dora Hannayen shi saman bayan ta yafara bubbuga mata Ahankali,


"Shshhh kiyi shiru haka please meye na kuka idan har ba so kike inkarasa mutuwa ba, kinga irin halin da damuwar ki ta sanya ni ko,

" Bata dagoba still tana manne dashi "ya sanya hannun shi ya dago fuskar ta ya dora halshen shi akan kumatun ta yafara lashe hawayen fuskar ta cikin wani irin salo,


" tuni kukanta ya tsaya cak domin jin irin salon da yake yi mata da halshen shi akan fuskar ta tayi saurin janyewa cikin sauri tana mai gyara zaman dan karamin hijabin ta ta mike zunbur daga gefen gadon"


"Jikin shi na rawa ya diro daga kan gadon duk da baya jin karfin jikin shi" riko hannun ta yayi cikin rawar murya " ina zakije? please don't leav me please ya fada hawaye na bin kumatun shi,


"Idan tace batajin shi har cikin jinin ta tayi karya Amma zancen Gaskiya ko soyayyar shi zata kashe ta bazata iya Auren shi ba,

" Ina ita ina dan baturiya tafara kokarin fisge hannun ta" cikin tsananin zafi nshi ya mannata da jikin kofar har kirjin su na hadewa " numfashin shi na fita da sauri ya hade fuskar shi da tata,

"Kashe ni kikeso kiyi ko? Dama kinzo ki karasa ni ne ko " jikin shi narawa idan har kikayi sanadin da iyaye na suka rasani Bazasu taba yafe miki ba domin kece sila,


"Sakin ta yayi ya koma kan gadon yasa kuka tareda kwanciya ya juya,mata baya, jikinta na rawa ta koma bakin gadon " Karufa min Asiri kaga su Momy na nan kar su gane komai

"An fada miki basu sani bane? Ba abinda kika zaba ba kenan " go just leav,


"Saurin mikewa tayi domin Sam bazata iya da wannan shagwababben yaron ba a Gaskiya,


" Tana fita ya cigaba da kukan shi yana furta " inkin tafi zan iya rasa hankali na please come back,,,


"Shigowar Momy cikin dakin yasa shi tashi da saurin shi ya riko hannun ta" Momy please if you truly love me stop her from going tell her to come back,


"Yana wani irin kuka "tafara lallashin shi jikinta na rawa " relaxed my boy and tell me who is she?

"She is the one Momy she is the one I love she is my dream girl Momy please do something,

" Ya karasa da kyar numfashin shi na carkewa ya tafi luuuu zai fadi dakyar ta iya rikeshi kasan cewar shi namiji ta buga ihun da ya dawo dasu cikin dakin da gudu "Har da Ruman da ke cikin tsananin Rud'u,


" Suna shigowa Dady ya tallabeshi ya dora shi akan gadon likita ya shigo da gudu domin bashi taimako ita kuwa sai wasu hawaye ne kebin fuskar ta su Kansu su hajara ya mugun basu tausayi,


"Karar marin da ya ratsa kumatun ta ya dawo da hankalin su duka awurin da karar marin tafito,

" Ruman ce dafe da kuncinta Momy na huci Akusa da ita tafara zazzaga ruwan masifa cikin harshenta na nasara,

"" idan har yaro na ya mutu sai kema kin mutu yaro tun tasowar shi kin hana rayuwar shi wal wala kin hanashi sakewa kullum muna yawon Asibiti yanzu kuma kinbayyana kinaso ki kashe min shi,


"I will never forgive you for that " Tara Dady ne yadaka mata tsawa "what. are you doing?


" Cikin fada ta koma kanshi da bala'in tace duk shine Silar faruwan komai tayi data sanin Auren shi kuma da bata Aure shiba bazata haifi yaron ta dashi ba,

"Shima ranshi ya baci " nine nake Dana sanin Auren ki da kika hana ni zama cikin yan uwa na kuma kisa Aranki ki Ajiye not

Please Login or Register in order to submit comment