Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

banza ba sa'ar shi bace,

" Kuma bazai taba yima yar kanwar shi guda daya tal da kasa ta rufewa idanu Auren dole ba bayan laifukan da ya tafka bayan rasuwar ta iyayen shi na bukatar taimako ya tsallake su ya barsu cikin wahala

Kuma yanzu da ya kamata ya gyara komai sai yazo ya bata ba don Haka dole Abdullah ya bar zancen Ruman,


"Yasan shi mai laifuka ne A wurin tilon iyayen da suka rage musu gasu Alhmdulillah yanzu sunada rufin Asiri sosai da zasu tallafe su don haka dole su gyara KUSKUREN su,



" Tana fita taci karo da Nasir " tayi matukar mamakin ganin shi A yanzu domin ya fada mata bazai dawo ba sai karshen sati saboda suna Aiki a Ibadan,


"Kanta a kasa ta nufi wurin motar shi, tun daga nesa ya zuba mata idanu A Gaskiya idan ya mallake ta ya gama sa'a a rayuwar shi,


" Tayi sallama ya Amsa cikin nishad'i ya bude mata gaban motar ta zauna batareda ta kulle ba ta gai sheshi cikin ladabi,

"Hmmm sai kika ganni ko? Eh ta fada " tunanin ki ya korani daga wurin kwadago na' " ni ba ruwana, " ke ko keda ruwa har ma da tsaki " gaba daya kin hanani sukuni kinsani duk ma fita a hayyaci na shiyasa kawai na dawo ayita takare,


"A Gaskiya zan turo manya kafin inrasa tunani na saboda soyayyar ki gaba daya nakasa (concentrating) a aiki na,


" ita dai kanta na ga screen din wayarta tana kallo ba tareda tana danna komai ba"


"Tun Fitowar ta yake kallon ta a gefe yana zaune a cikin motar shi zuciyar shi na turiri kamar zatayi bindiga idanun shi kamar zasuyi Aman wuta,


" Bayan dazu ya ganta da wani kuma yanzu ga wani ya kuma zuwa bayan ta sani sarai baya so tasan cewa yana cikin fushi saboda ta nunamai cewar shi ba komai bane take yin Abin da taga dama toh zai ko dauki mataki akai,


"Wani irin mugun reversed yayi ya fisgi motar shi da gudu ya bar unguwar,


GRA ya koma yana shiga ya kira Ak " Kafada wa Dady na ina GRA koda ya tanbaye ni, ya datse wayar tareda jifa da ita ta tarwatse a jikin bango wata irin kara yasa tare da dafe kanshi dake matukar sarawa kamar zai rabu kashi biyu,


"Kuka ma Rahama ne Ashe dama zai samu yin kukan ko zai rage jin radadin zafin da zuciyar shi keyi,



" lokacin da Ak ya fada ma Dadyn shi sakon Hankalin shi yayi matukar tashi sosai' nan take ya nufi GRA domin yasan Abinda ke damun yaron nashi,


"Saboda ya kira shi da cewar su hadu A gidan Hajiya kuma yasan yazo ganin Ummu Ruman a waje ne sanadin komawar shi,



" Motar shi na fakawa ya fito ya shiga cikin sauri, yasameshi cikin mugun yanayi " Son meke faruwa ?


"Dady kirji na zai fashe ya furta dakyar yana mai dafe kirjin " Abdullah "
ina neman Alfarma a wurinka amatsayina na mahaifin ka,


"Ya maida hankalin shi sosai akan Dadyn shi" Dady tell me zanyi maka ai kai Mahaifina ne " Inaso ka cire son Ummu Ruman a cikin zuciyar ka,


"Wani irin mikewa yayi tareda yin baya da sauri idanun shi gaba daya a waje " Dady what????

"Dady kasan me kake fada kuwa? Ahankali ya fara yimai bayani tareda rokon shi yana girgiza kanshi tare da zubowar wasu Azababbun hawaye da yake jin su kamar tsiyayowar jini a cikin idon shi,


" Dady kana nufin kamar in dauki bindiga ne in saita kaina da ita kana nufin kamar zarewar numfashi na ne zanyi da karfin gaske Dady kafi kowa sanin matsayin Roman a cikin Rayuwa ta,


"Kaine da kanka kake tunanin in hakura da soyayyar ta " Dady How? Tell me.


"Ya durkushe a gaban uban " Dady saboda ka gyara KUSKUREN ka kakeso ka jefani cikin wani hali? Saboda wani dalili Mara tushe kake so ka jefa Rayuwata cikin had'ari?.


"Mikewa yayi ya share hawayen shi ya kalli uban shi" I thought komai yazo karshe na d'auka lokaci yayi da zan samu farin Cikina but Am mistaking komai ya kara lalacewa,


"Dady anything can happened kuma duk Abinda ya faru ba KUSKUREN mu bane kune zakuyi sanadin jefa mu Acikin mummunan had'ari


" ya juya Dady na kwala mai kira ya futa fuuuu'

"Shigowar Momy tana mai watsa mai mugun kallo cikin harshen ta kamar kullum tafara zubomai ruwan turanci


"I no u are hidden something from me , A matukar hasale ya fuskan ce ta yabata Amsa " eh na nema iyayena kuma na dawo kasata ta haihuwa har na nema transfer kuma nasamu zanci gaba da Rayuwata A kasa ta idan zaki iya ki zauna idan ba zaki zauna ba ki tafi Amma ni da yaro na mu nanan ba inda zamu koma...........✍



_*Hmmm Akwai magana my fan's ya zata kasance ne wai? Ku dai ci gaba da biyoni muji wane irin KUSKUREN ne za a tafka,*_

*Matar Soja*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KUSKURE NAπŸ™†*
_Love&Destiny_


_Written by Fenerh_

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain✍🏽~*


_*Am sory my fan's Akwai uzurori da dama shiyasa bakawa samun post A kullum Aruwan*_

πŸ…Ώβž‘1⃣5⃣

Tun tafiyar Nasir ta fada tunani domin tayi ta zuba idanu bata ganshi ba tun dawowar ta tayi matukar shiga damuwar rashin ganin shi,



Wasa wasa har kwana biyu bata saka shi a idanun ta ba duk inda hankalin ta yake ya gama tashi gashi taga Hajiya ko damuwa batayi wani tunani ne ya shige ta ta mike zunbur ta fita zuwa gidan kakan nin ta,


"Tayi matukar mamakin y'anda aka buge gefe daya Ana zuba wani ginin dakin gwaggo Amina ta shiga tsohuwar har tafara murmurewa tayi sallama,


" Aa Ummu yau An tuno mu? Ta gai sheta tareda tanbayar kakanta " Ai malam ya fita bai yi wurin ku ba? tace " aa ni bangan shi ba,


"D'an uwanki kwana biyu baya gari na tanbayi uban yace min wai tafiya yayi,


" Tafiya kuma? To ina yaje haka ? Take yima kanta tanbayar kodai fushi yayi domin zuciyar ta na bata ba inda yaje,

"Ta ji ba dad'i a cikin zuciyar ta domin tana matukar son ganin shi sai yanzu ne take gane cewar ba karamin shiga cikin zuciyar ta yayi ba she really needs him,


" Yanzu ina zata ganshi? Wa yarta ta Ciro ta fara duba numbar shi a karon farko tayi dialing Amma wayar tashi a kashe zuciyar ta ta fara har bawa da karfi,


"Barin gidan tayi batareda tayi wani kwakkwaran tunani ba takoma gida,


" Ke kuma daga ina haka? Hajiya ta tanbaye ta "Gidan gwaggo Amina, shine baki fadamin ba? Naga kina Salla ne kuma ba dadewa zanyi ba,


" Wai Ummu kuna waya da Abdullahi kuwa? Cikin sauri ta Amsa "Aa " kila bai dawo ba dan ko jiya Jafaru ya fadamin yaje wurin Abokin shi a Kaduna,


"Tayi Ajiyar zuciya mai karfi Ta shige cikin dakin ta ta fada kan gadon ta still tana so ta ji muryar shi ko kuma ta ganshi,


" meyasa zai yi tafiya bai fada mata ba? Ai ko a waya ne ya kirata she is very worried zuciyar ta ta kasa natsuwa,


"Washe gari ta tashi kwata kwata jikin ta ba kwari,


" Zuwan mahaifin ta ne ya dan rage mata damuwa domin ya ce ta shirya su shiga Kaduna tare kasan cewar weekend ne,


"Taji dad'in tafiyar domin tana sa ran ganin Abdullah A can,


" Hajiya ta kalle ta " ki kiyaye Ummu domin baki San Halin Matar ubanki ba ki Bata girman ta ALLAH ya kiyaye,


"Tunda suka kama hanya babanta sai janta yakeyi da hira " Ummu bakya bukatar komai dangane da karatu ko wani Abu?

"Ba komai baba, " idan har kina bukatar wani Abun ki fadamin in munje zanyi kokari in bude miki Account kema idan kina bukatar kudi basai kin jira ba kinji.


"Nagode Baba ALLAH ya kara budi " Ameen Ummu kiyi hakuri kinji da sha anin Rayuwa komai nada lokaci kuma ko wane bawa da irin tashi jarab tar,


"Sun isa lafiya gidan babanta ba laifi babban gidane har da katoton gate tayi Zuru tana watsa idanu " yanzu Anan gidan mahaifin ta ke rayuwa ?

"Ya barsu Acan koda yake Alhmdulillah sun gode wa ALLAH basu taba rasa komai ba na Rayuwa Hajiya da kaka magaji sun tsaya mata,


Tunda motar ta tsaya naga wasu yara sun fito da gudun su guda biyu maza suka rungume shi,


" Baba oyoyo, ya daga karamin cikin su " Oyoyo Abdul Faisal ina sauran suke? "Suna ciki " OK ga Auntyn ku nan tazo ku je wurin ta,


"Suka maida kallon su wajen Ummu da gudu suka rungume ta Aunty welcome, ta rungume su duka domin taji dad'in ganin y'an kannen ta,

" Suka wuce cikin katon falon hamshakiyar na zaune ta dora kafa daya kan daya ga sauran yaran maza guda biyu a gefen ta ta ci Ado cikin wani irin lafiyayyan less daurin nan kuwa kamar na magajiyoyin karuwai,


"Ta karasa kusa da ita ta tsuguna " Mama ina wuni " ta d'an kalleta kadan ta dauke kanta gefe" lafiya. Shine kawai Amsarta sauran yaran ma kallon ta sukeyi wani iri'


"Abin ya Sosa mai rai sosai ya buga musu tsawa " bakwa ganin yayarku ne? Kun tsaya kuna zuba mata idanu,


"Sukayi saurin gai da ita suna kallon ta itama dai kallon su takeyi tana ganin su taji sunyi bala'in shiga Ranta abinka da jini


" Amma har cikin zuciyar ta bataji dad'in y'anda ta Amsa ta ba, Baba da kanshi ya kalli babban "Adam ka shigar mata da jakar ta dakin can na kusa da na maman ku,


" Ina lami ? Ta kawo mata Abinci ya shige cikin dakin shi ranshi nayi mishi suya,


"Ita ma bin bayan Adam din tayi ta shiga dakin da Aka nuna mata " ita kuwa Matar gidan ta bi mijin ta a baya w'anda tun shigar shi yake zagaye dakin,


"Ta shigo tana ginshira " kallon ta yayi A wulakance" Balkisu Wallahi kin kaini bango wato rashin kaunar har takai kiga Yata gudan jinina kiyimata wulakanci ko?


"To wai kuma yanzu Muhammad me nayi? Kingani ko Ace yarana shida Amma bazaki iya boye suna na ba saboda rashin da'a.

" To ni bazan iya ba " Sannan kuma me tazoyi nan gidan kuma? Ya kalleta wani iri"waye?

"Wadda kukazo tare mana, ta fada cikin rashin damuwa wani irin kallo ya watsa mata " y'ar tawa ce wata " bilkisu y'ar Cikina Yata ta fari y'ar kanwata jinina mata ta tafari Matar da nafiso fiye da kowace mace Aduniya bayan uwar da ta haife ni ke kanki da tana duniya bazan taba Auren ki ba,


"To Aikin gama ya gama nice Matar ka uwar yayan ka maza har guda biyar don ta haifi mace shine me ko Kanaso ko bakaso ni dai ce uwar yayan ka kuma yayana keda gida ba ita ba,


" na miki uzuri kwakwal war ki nada matsala Amma ki sani ina son Yata kamar y'anda nake son sauran don haka ki shiga tai tayin ki kina wulakan ta min ya Wallahi zaki fuskanci hukunci,



"Tunda ke bakisan mutunci ba kin nuna Sam bakya kaunar kowa nawa ya kusan ceni har mahaifiyata to baki isa ba kuma Wallahi sai na nuna miki karshen ki ya zo,

" ya wuce Abinshi bathroom ya barta tsaye sheke ke ta wuce da sauri dakinta ta fara danna wayarta Ana d'auka a dayen gefen tace " hello Mama wai ya kukayi da malamin nan Muhammad fa gaba daya ya canja yau har y'ar shi ya kawomin,

"Banajin me Ake fada a dayan gefen saidai Amsar ta" yanzu shi kenan bazai kuma Amfani ba maganin?

"Ta kashe wayarta ta koma ta zauna tareda zabga uban ta gumi,


" Ummu kuwa tunda Adam ya raka ta dakin ta ta ce ta gode ta nemi gefen gadon ta zauna tana ware idanu tana kallon ko ina na cikin dakin


Gadone da kuma sif dinshi kawai da mirror ta cire hijabinta ta kalli wata kofa da take tunanin ban daki ne ta fada tareda dauro Alwala ta tayar da Salla tana idar wa lami na jero mata lafiyayyan Abinci bata wani jin yunwa ta koma kan gadon ta janyo hand bag dinta ta Ciro wayar ta


"Number Sumayya ta fara kira ta sanar mata tana Kaduna tana dawowa zasu fara shiri sun dauki lokaci kafin ta kira Hajara ita ma sun dauki lokaci har Tanayi mata zancen yayan ta ya fadawa su Abba maganar su,


" gaban ta yayi mugun faduwa tunawa da Abdullah ta ce sai Anjima tana katse wayar ta fara neman layin shi yau kusan sati daya rabonta da shi,

"Cikin sa'a wayar ta shiga Amma tayi ta ringing bai d'auka ba takira yakai sau bakwai hankalin ta yayi matukar tashi dabara ta fado mata ta tura mai text msg,

_*A'm in KD*_

Kawai ta tura mai shi kuwa a lokacin ya na kwance a dakin Mukhtar yanajin ringing din wayar ya shareta yasan ita ce " me zata fada mai duk da yana matukar kewar ta Amma yana tsananin fushi da ita sosai,


"Shigowar msg din yasa shi janyo wayar ya bude " da sauri ya mike zaune' me tazo yi kuma?


"Nan yayi dialing back a lokacin har ta cire rai zuciyar ta tayi mugun tsinkewa A Gaskiya takai makura yanzu kam ta y'arda tana mutuwar son shi,


" ji take kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a kusa dashi tayi missing ta bata da yakeyi tana tunano irin y'an da yake rudewa a duk lokacin da yake tare da ita zuciyar ta tafara raya mata

"Tasan koda bai gamsar da itaba ta hanyar sex tasan he is very romantic gashi yana matukar kaunar ta ita ma gashi ta Afka cikin kogin son shi,


" tunanin ta ya katse ne Alokacin da taji karar wayarta jikinta na rawa ta kalla ganin special numbar shi yasa ta daga kiran cikin kasala da kuma tsananin mutuwar jiki muryar ta ta koma wata iri domin tariga ta shiga wani yanayi mai wahala,


"Tana picking tace" heloo ta furta akasalan ce yaji muryar ta har cikin kwakwal war kanshi " hy kawai ya iya furtawa domin shima jin muryar ta duk ya birki ce,


"Tafiya ba sallama, ta furta a kasalance, " eh because you doesn't care , who said so? You are. When? All the time


"Hmmm " why Roman? What? Kinaso ki samun hauka, ni yaushe? Kinfini sani, meyasa kike mun haka? Any way na hakura gashi na samu y'ar baby A nan tana mugun sona tace in kaita wurin Aunty na,


"Wani irin bugawa zuciyar ta tayi ta runtse idanun ta har wasu irin hawaye suka taru a cikin idanun ta'

" kinsan me Aunty na? Ya kuma fada ta kasa bashi Amsa,

"Itama tanada komai da yake burgeni kuma nasan ita batafi karfina ba ni Banyi mata karami ba ta y'arda da ni tasan zan gamsar da ita fiye da tunanin ta,

" kinsan meye kum..... Kit ta katse kiran kamar ta kurma uban ihu ta rufe bakinta tana runtse idanun ta " Wayyo najawa Kaina ya juya min baya bayan ya gama cutata ya cusamin kaunar shi cikin zuciya ta Wayyo ni najawa kaina,



"Tunda ta datse wayar yayi wurgi da ita gefe tareda dafe kanshi

" A haka mukhtar ya same shi ya dafa shi " friend what is wrong?

"Ya dago kanshi tare da girgiza wa " yaya zanyi Mukhtar? Tana guduna yanzu ta kirani ina ma yi mata maganar nasamu wata macen Amma ko a jikin ta ta katse min waya,


"Dariya yayi" Abdullah that's means tana son ka kuma kishi ne yasa har ta katse kiran don haka zan baka shawara ,

"Wace irin Shawara haka kawarta ta fadamin cewar tana sona ni banga Alamar hakan ba bayan kullum tana kula wasu mazan daban,


" patients my friend ka yi kamar y'anda na fada maka you will see da kanta zata dawo hanya, kai ni gani nake ma kamar tana sonka ne nima nayi tunanin haka but taki ta bani hadin kai,


"Yanzu ya zakayi da Dady ko ta y'ar da sannan kuma what About Momy? Just for get,


" Damuwa na kawai insamu hadin kanta dole su daura mana Aure, ALLAH ya y'arda.



"Sai da tayi bacci ta tashi sannan taci Abincin ta dai ci ne kawai ba don tanajin dad'in shi ba saboda bakinta Sam ba Apatite,


" Saida ta yi wanka ta janyo yar Jakarta ta Ciro doguwar Rigar jallabiya mai dogon hannu ta dan kamata kadan daga kasa kuma ta bude haka ta fito fuskar ta batareda ta yi wani make up ba powder kawai ta dan shafa sai wet lip Amma wani irin Annuri da kuma sihirtaccen kyau take fitar wa,

"Ta samu Mama a falo ta gai sheta ta Amsa kadaran kada ham ta samu gefe ta zauna tana bin kallon da sukeyi itama gaba daya yaran hudu suna wurin ba w'anda ya kulata


" Sun dauki lokaci a wurin duk da kowa sha anin gabanshi yakeyi Amma ta danji damuwar ta ta ragu saboda program din yayi matukar burgeta,

"Baban su ya fito yayi matukar murnar ganin su duka A zaune a wuri daya cikin jin dadi ya kalleta " Ummu kintashi?

"Ai na leko naga kina bacci hope komai lafiya? Ta dan zame tareda gai sheshi yaji dadi sosai y'anda take bashi girma tafi sauran y'an uwanta da ba w'anda yayi tunanin gai sheshi,



" Ya zauna yana mai fuskantar ta" Na kira Abdullah ya fadamin yana nan garin yanzu haka yana hanya ma tareda Abokin shi,

"Wani irin dadi ne ya rufe ta taji wani dadi ya ratsa zuciyar ta,

" Gaba daya ta k'agara ta sashi a idanun ta " sai kallon hanya takeyi,


"Karfe kusan biyar suka iso gidan tun daga harabar gidan kamshin shi ya fara yi mata iso' tashi kawai tayi ta koma cikin dakinta gaban ta na faduwa,


" Sallamar shi cikin daddan muryar shi yasa ta runtse idanun ta tanajin wani irin kaunar shi na bin kowace gaba ta jikin ta,


"Suka fara gai da Baba mama bilkisu ma ba laifi ta karbesu' Baba ne ya tura Adam " kira Auntyn ku yanzu ta shiga ta fito ga d'an uwanta,


"Tun kafin Adam ya iso ta mike tareda daukar wayarta ta fito falon kan ta akasa,.

" Tun da ta sako kafar ta ya zuba mata idanu gaba daya ji yakeyi kamar ya ruga da gudu ya rungumota cikin jikin shi cikin dakewa ya dauke kanshi ya mayar dayan gefen tareda fuskewa,


"Ta samu wuri ta zauna mukhtar ne ya fara gai sheta yana mai zuba mata,idanu domin gasgata Abinda yagani tabbas itace wadda ya zanama Abokin shi fuskar ta saidai A zahiri tafi haduwa,


" Hmm Ashe dole Abokin shi ya haukace , ta Amsa Ahankali shikuwa ya tsare gida ya daure fuska gaba daya kamar bai gane taba,


"Babane ya katse mata fargabar ta" Abdullah kana cikin garin nan kaki zuwa saida na kiraka ko? Wato nan ba gida bane kenan Ace ina nan garin zakaje wani wurin,

"Ya dukar da kanshi kasa" Baba kayi hakuri nayi laifi bazan kuma mai maitawa ba' OK " yaushe zaka koma Zaria?


"Zan dan kwana biyu Anan Akwai kamfanin da muke ginawa da Dady Anan " eh ya fadamin munje kuma munga ginin ya na tafiya sosai,


"Ya mike " to ni zanfita " Ummu ki basu wani Abun motsa baki mana saikace wata bakuwa,


"Ta mike cikin jin kunya ta nufi hanyar da take tunanin kitchen ne ta ga firij ta bude ta dakko musu drinks da ruwa ta dora a tray ta hado da cups ta kawo musu,


" Ga badaya jikinta rawa yakeyi duk bataji dad'in y'anda yake dauke mata kaiba duk zuciyar ta ta gama tsinkewa da lamarin,


"Baba na fita mama bilki ta tashi sauran yaran kuwa suna gai sheshi suka fita yarage daga su sai TV da kuma mukhtar dake kallon wani irin salon so,

" Ya kalli Abokin shi " ni bari infita daga waje idan ka gama ka sameni ko? Nop muje kawai me zan tsaya yi? Da saurin ta ta kalle shi gaban ta na faduwa jikin ta na rawa tamike itama


"Mukhtar na gaba shima ya fara takawa zai bishi tabishi da sauri tareda shan gaban shi ta zuba mai idanu ta marai raice gaba daya tarasa gane mai,


" Cikin kasalalliyar murya ta kalleshi " please Abdul enough ""


"Ya kalleta da kyar tareda watsa mata idanun shi masu daukar hankalin ta ta fara karema sajen fuskar shi kallo gashi ya fito cikin wani farin yadi mai shara shara har tana ganin farar singlet din shi

" Yayi mata kyau sosai Agogon shi sai sheki yakeyi " idan kin gama karemin kallon intafi?

"Tun kafin kuma kiga yarintata zanje tafi ne baby na jira na......

" bata bari ya karasa ba ta daga mai hannu " please stop Abdullah......✍


*Fan's Kuyi hakuri da Matar Soja*


*"Love you All*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KUSKURE NAπŸ™†*
_Love & Destiny_


_Written by Fenerh_

✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATI✍🏽✍🏽✍🏽

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*_Assalamu Alaikum masoya na ina matukar farin cikin irin kaunar da kuka nunamin Agaskiya banida bakin da zan iya gode muku da shi sai dai ince Allah ya bar kauna da soyayya ya muku sakayya da mafificin Alkhairi, kuma ina mai baku hakurin rashin jina da bakuyi ba kwana biyu saboda tafiyar da na d'an yi Amma Alhmdulillah Allah ya dawo dani lafiya zanci gaba da suburbudo muku posting,_*


πŸ…Ώβž‘1⃣6⃣

"Idanun shi ya zuba mata domin ganin irin tsananin bacin ran da ya hango a kwance a kan fuskar ta,


" Aunty me nayi kuma yanzu'? Gaba daya ta ma rasa irin Amsar da zata iya bashi domin ya d'aure ta da jijiyoyin jikinta da irin kallon da yake jifanta da shi da ida nun shi masu matukar burgeta,


"Nace ina sonki Kince bakya sona, Kince ni ina yimiki rashin kunya saboda ni karamin yarone yanzu kuma nazo Banyi miki rashin kunyar ba zantafi kin hana ni, " _Now tell me what do you wants Again um?_

"Yana mai jifanta da idanun shi da ke kara tun zura zuciyar ta zuwa ga kara kaunar shi,

" Ta kasa koda motsi ta rasa me zata furta tayi saurin matsawa ta juya tareda nufar kofar dakin da ta sauka,

"Tunda ta juya baya ya tsaya cak tareda zuba mata idanu ji yake kamar ya bita ya rungume ta ko zai samu d'an sassaucin Abun da yake damun shi,


" Fita kawai yayi duk ko ina na jikin shi ya saki " Yana fadawa mota ya dora kanshi a kan sitiyarin motar tareda rintse idanun shi zuciyar shi na matukar suya A shi kadai yasan irin tarin damuwar dake cin shi A rai,



"Mukhtar ne ya dafa shi "Abokina ya dai? Ya dan dago da kanshi ida nun shi sunyi jajur kamar wuta,

" Mukhtar nayi wa zuciya ta famu na kara wa Kaina da muwa ganin ta na kara hauka ta zuciya ta sosai ina ganin soyayyar ta ce Ajalina don ina mai tabbatar maka idan har ban mallake ta ba to zuciya ta na gab da bugawa in mutu,


"Aa kar ka fadi haka da ikon ALLAH sai ka mallake ta, Yanzu dai muje ko?


" Ya gyara zaman shi " zanje in dakko kayan da zanyi Amfani dasu ina son kasan cewa tare da ita banaso Muyi nisa da juna ko da kuwa ba zata kula ni ba,


"OK ba damuwa ka fita,kawai me zan kawo maka? System dina da kuma brief case kawai, ya fada a takai ce,


" fita kawai yayi ya koma gefen wata bu shiya dake harabar wurin ya zauna akan kujerun robar dake wurin tareda dafe kanshi da hannun shi daya,



Tunda ta shiga dakin ta kasa natsuwa zuciyar ta na bugawa har wasu irin hawaye masu dumi ke bin kuncin ta " Yanzu ya zatayi ta fahimtar dashi cewa tana matukar kaunar shi ita ma?


"Ta yaya zai fahimci cewar ita ma soyayyar shi tayi mugun yi mata kamu?

" matsawa tayi ta jikin window din dakin dake harabar gidan tasan sun riga da sun wuce Amma Abin da ya bata mamaki bai wuce ganin shi da tayi Azaune ba a wurin,


"Wani irin farin ciki ne ya rufe ta taji Kamar ta ruga da gudu ta shige jikin shi ta shaki wannan kamshin nashi mai shiga zuciya,

"Idanun ta ta zuba Akanshi tana karemai kallo a Gaskiya ya mugun haduwa

Please Login or Register in order to submit comment