Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne ta danji saukin lafawar ciwon har tafara yunkurin mikewa zaune tana mai dafe gefen cikin ta,


"Idanun ta sunyi mugun kadawa ga hawayen wuyar da ke sauka a fuskar ta'


" Ta ware idanun ta a dai dai lokacin da ya dora tafin hannun shi mai laushin gaske a kan fuskar ta yana kokarin goge mata hawayen,


"Nan da nan ta matsa nesa dashi tareda watso mai wani irin kallo, Wai meye haka ne? Sai Alokacin ta Ankare da inda take tayi saurin dira daga kan gadon har tana kokarin burgewa,


" Da hanzarin shi ya cafko ta zuwa jikin shi "kin gani ko da yanzu bana kusa irin wannan mikewar da kikayi sai kifadi,


" Ta fara kici kicin fisge jikinta Amma ina ya riketa tamau har wani Ajiyar zuciya yake sauke wa jinta a cikin kirjin shi,


"Kuka kawai ta saka mai mai dan karfi ta fara dukan kirjin shi " Wai menene kake yi haka bana son iskan ci na fada maka " ka daina tabani idan har ka saba taba yan iskan yan matan ka to ni ba irin su bace,


"Tana fada tana kokarin ture shin" Shshshhh relaxed Princes ki natsu jikin ki ba karfi ki bari in nema miki saukin zafin jikin nan don ALLAH,


"Ya furta dakyar don shi gaba daya jinta Acikin jikin shi ya gama sauya mai yanayi,

" Ka sake ni ka daina tabani' impossible ke ma kinsan bazai taba yuwu wa ba idan ban taba ki ba wa zan taba?

"Cikin zafin rai ta furta kawruwan ka, murmushi kawai yayi " Baby a Gaskiya zakiyi kishi sosai ,

"ALLAH ya kiyaye inyi kishin ka ai sai ka damu da mutum zaka yi kishin shi,


" Yanzu bakya tausayin Rayuwata? Na gaji wallahi nagaji ki tausaya min ki sassauta ma Rayuwata baby,

"Ya furta yana mai kara matse ta a kirjin shi duk da ta takure jikinta ta tokare shi bai hana shi matse ta gam ba kamar zata gudu"


"Banki mu dawwama a haka ba " zanso ki taimaki rayuwar mu dukkan mu muna bukatar juna,

"Ni ko bakyaso na kitaimaka ki Aure ni zankoya miki sona Ahankali,


" ke kanki kina bukatar Auren nan princess ki bani goyon baya cikin lokaci kadan zancire miki wannan ciwon domin ni kadai keda maga nin shi

"Wani irin karfi taji tareda tunkude shi " wai don ALLAH kai wane irin yaro ne haka? Nace bana sonka bazan Aure ka ba dole na?


"Tuni zuciyar shi ta kunburo shi cikin zafi ya rikota tareda manna ta a jikin ginin dakin,


'Yana huci " Dole ki soni dole ki Aure ni kuma am warning you kar inkuma kuma ganin ki tare da wani namiji inba haka ba Wallahi kinji rantsuwa zanyi miki Aikin yarintar da kike kiramin,


"Ki Aure ni shine maslaha inba haka ba wallahi zakiyi Dana sani na har Abada,


" Tana mutsu mutsu still bakinta bai mutu ba "Nace bazan Aure ka ba do your worst,


" Kuma a gaban idon ka zanyi Aure kana gani watch and se.....

"Carab ya rike lebenta da hakorin shi ya dan ciza da karfi ta saka karar wuya kafin ta dawo dai dai ya karasa da bakin shi cikin nata yayi sa'ar samun harshen ta mai laushi ya cafke kamar lolipop ya fara tsotsa yana fitar da wani irin numfashi mai zafi saboda tsabar kishi dake cinshi kuma ga tsantsar sha'awar ta dake manne da gangar jikinta,


" jikinta yayi lakwas ta ma kasa kwatar kanta daga jikinshi tsotsar ta yakeyi a hau kace kamar zai cinye mata bakin,


"Kukan da ta sakane yasa shi sararawa daga dogon zangon da yafara zuwa, jikin shi ya mutu murus tasamu ture shi ya fadi a gefe tareda dafe kanshi idanun shi jajur,


" Wallahi banyafe maka ba ta watsar da miyan bakinta tareda goge wa ALLAH ya isa d'an iska kawai ina da na sanin ranar da na fara ganin ka wallahi meyasa kake so ka shiga Rayuwata?



"Cikin tsananin jin zafin zagin da ta surfa mai yasashi saurin mikewa ya kuma nufota gadan gadan,


" Ni kike zagi Roman? Nagode, Saboda kawai ina sonki kike yimin wulakan ci? Na farko kina fadamin zakiyi Aure da wani kato agabn idona ya furta yana runtse idanun shi saboda jin zafin wannan furucin,


"Nayi kissing dinki ne saboda inkoya wa bakin ki ladabi kar ki kuma kiramin sunan wani namiji da sunan zaki Aura idan har bani bane'


" Inada matukar kishi akanki ke tawa ce ni kadai Wallahi Roman Duk ranar da kikayi KUSKUREN Auren wani namiji to saidai kije da Cikina jikin ki


"Gidan kowaye kuma wallahi zamu je gidan tare, ke nifa idan naso zandauke ki inbar kasar nan dake wallahi ba w'anda zai kuma ganin ki zamuje Muyi rayuwar mu dagani sai ke sai yarana da zaki haifamin


" Kallon baka isaba kake yimai, shikuwa ya dage sai zuba mata ruwan bala'i yakeyi karo na farko da ta hasala shi har ma yarasa Abinda zai furta mata yafara zubo mata shirme"


"Ke ko uwata ce ke tunda ina sonki I don't care kuma dole kisoni,


" Haba don ALLAH so kike ki kasheni kinaso ki samun ciwon zuciya ne na daure na kusan shekaru ina neman ki kuma bayan na ganki kinaso ki bijirewa zuciyar da ta taso cikin mafarkin mallakar ki kece kika raini zuciya ta ta yaya kike ganin zan iya Rayuwa batare dake ba?


"Ya durkushe a gabanta ya samata kuka mai ciwo " Ina cikin damuwa mai dinbin yawa Ki sasauta min please nagaji""""""



"A zahirin Gaskiya taji tausayin shi Amma batajin zata iya Amince mai ganin Wankin hula zai kaita dare yasata Sauke Ajiyar zuciya,


" Naji Yanzu ina ka kawoni? " muna Zaria hotel, ya furta a takai ce " kallon shi tayi ida nunta a waje " Hotel? Innalillahi wa inna ilaihirraju un,

Nan da nan bacin ranta ya dawo sabo " kazo ka mayarda ni inda ka dakko ni mikewa yayi tareda kallon ta " cikin ya daina ciwo?


"Eh ka mayarda ni, are you sure? Yes please take me back,


" Saina duba lafiyar ki Kayimin wannan Alfarmar inaso inyi checking dinki,


"Mikewa kawai yayi tareda karasa wa kan wani dan karamin table ya janyo brief case dinshi na aiki wata y'ar Karamar na ura ya dakko ya kunna ta mai kamar computer,


" Kallo kawai take bin shi da shi " ki kwanta, ya furta ko baki y'arda dani ba har yanzu? Wallet dinshi ya dakko tareda budewa ya Ciro mata I D card dinshi,

ya haska mata shi akan fuskar ta Doctor Jeff J ta gani A rubuce tana kallon shi cikin mamaki dan wannan yaron?

"Jeff? That's means hasashen ta yazama Gaskiya shi ba musulmi bane kenan subuhanllah Amma Gaskiya ya cuceta da ya hada jikinta mai tsarki tareda nashi mai najasa,


" Yanzu ne ma takejin ta kara tsanar shi a cikin zuciyar ta wai gawa tayi tareda kallon inda hijabin ta yake ta fisgoshi ta sanya ta dauki Jakarta ta rataya ta nufi hanyar fita


"Dan tsaya wa tayi duk yana tsaye yana binta da idanu " a dacan mamaki nakeyi a duk lokacin da naga kayi wani Abu w'anda ya sabawa Addini Amma a yau na fahimci dalili,


"Rashin sanin hukun cin Addini na yasa kake mun dabi unku na kafirai kuma ya hudawa, ta Yama zakayi tunanin bin hanyar da nakebi bayan kai ba ita kake bi ba ,


" Ni musulma ce kuma ba haushiya mai cikakkiyar tarbiya da kuma sanin hakkin Addini na ina rokon ka dakabi hanyar ka inbi tawa gaba daya tsarin ka ya kauce wa Addini na,


"Gaba daya ta gama birkita mai lissafi ta hanashi koda motsi yakasa koda furta mata kalma daya,


" Har ta bude kofar ta fita tana maibin harabar wurin da idanu " ALLAH ya isa ta furta a cikin ranta yanzu saboda iskanci zai kawota Hotel salon wani ya ganta Ayi mata kallon y'ar iska,



"Kafin ya ce ya saita tuna nin shi ya dawo cikin hankalin shi tuni tafice
Da gudun shi ya biyo bayanta Amma ko inuwar ta bai hango ba ta bace bat,


" Har fitowa yayi yana wai gawa ta ko ina Amma bai hangota ba haka ya juya zuwa cikin dakin matsaloli sun sakoshi gaba ga damuwar family ga kuma nata da yafi komai damun shi a halin yazu'


"Tana fita Adaidaita ta hau sai gida,

" isarta kofar gidan ta ga bakuwar mota a fake a gefe Amma bata kawo komai ba ta shigewar ta cikin gidan,


"Tayi sallama a kofar falon nasu cikin sanyin jiki " Aka Amsa jin muryar kakanta magaji da kuma wata bakuwar murya yasata daga kanta ta fara binsu da idanu gabanta yayi muguwar faduwa domin ganin mahaifin ta durkushe a gaban Hajiya kamar yana neman gafara,



"Ta saki idanu ko gaishe su ta gagara yi maganar Hajiya ya dawo da ita cikin hayya cinta ,

" Ummu kindawo? Shi kanshi sai Alokacin ya kara ware idanun shi akanta " cikin tsananin farin ciki ya zuba mata idanu yana fitar damurmushin jin dad'i,


"Ummu Ruman dina ce ta koma haka? Eh Ummu da ka wulakan ta ce gatanan ALLAH ya Albar kace ta,

" ka ganmu nan muna nan a inda ka barmu ba Abinda ya same mu " Ai dai duniya ce Muhammadu ta ishi kowa Riga da wando ai ko baka zo ka sauke hakki na na uwa ba kazo kaga yar marainiyar ALLAH da tayi rashin uwa tun haihuwar ta,


"Don ALLAH Hajiya kiyi hakuri na tuba ki gafar ce ni nakasa daurewa ne bazan iya daukar rashin Aisha ba Idan har zan zauna a nan hankali na bazai taba kwanciya ba,


" toh yanzu gujewa yar da ta Haifa ta barmaka shine Abinda kake ganin ya dace Ace kusan shekara sama da goma rabon daka waiwayo mu


"Kana sane dagani har d'an uwa na muna bukatar ku kodan shekarun mu d'an uwanka ja'afaru har yau bai wai wayo gidaba


" wallahi kubi a hankali hakkin iyaye ba wasa bane don haka ni na gama magana ta idan kungyara to idan kunki kuwa duniya ce gatanan w'anda ma bai shigo ta ba jiran shi takeyi,.

"Aa yaya k'arki yimai baki don ALLAH ki gafar ce shi tunda har yagane KUSKUREN shi,


" ni dai ina tsaye ina mai bin mahaifina da idanu idan nace bana bukatar shi a taredani nayi karya mu samman Yanzu da nake cikin rudu da kuma damuwar zuciya,


"Zonan Ummu ya furta A hankali' cikin natsuwa nafara takawa na karasa kusa dashi ina isa na fada jikin shi nasa kuka mai ciwo w'anda na rasa na menene?


" Zuciya ta Sam bata min dadi har zafi take yimin akan Abubuwa da dama,


"Hannun shi ya dora A saman bayana yana bubbugawa " kiyi shiru kinji my doughter ki yafewa babanki nayi KUSKURE ki gafar ceni zangyara duk tsawon lokacin da na d'auka bama tare da izinin ubangiji,


"Kukan ta karuwa yakeyi ita tasan tana farin ciki da ganin shi duk da cewar tana fushi da shi sannan kuma a dayan gefen zuciyar ta ta suya a sakamakon Abinda yake mugun damun ta a halin yanzu,

" ita kanta tasani( she needs a shoulder to cry) don haka yanzu da tasamu dama take rusa kukanta mai cin zuciya,


"Ummu Hajiya ta kirata" Meya faru Akwai Abinda yafaru dake ne naga lokaci baiyi ba kika dawo,


"Banajin dadi ne shiyasa na dawo, subuhanllah dukan su suka furta a lokaci daya' Badai ciwon cikin bane ko? Inji Hajiya

" shine ta furta tana mai tashi daga jikin mahaifin ta" sannu suka fara jero mata yace " suje Asibiti Adubata " magaji yace ya kamata kam don tana wahala wancan karon sai da Aka kaita Asibiti,


"Mikewa tayi cikin dauriya tace " naji sauki sosai ai yanzu,

"Toh kije ki kwanta kidan huta Ai yau kina Azumin ko? Cewar Hajiya, ta Amsa da" eh sai yanzu ta tuna da zancen wai ta tashi da Azumi domin tunjiya takejin Alamar damuwa kuma gashi ba aje ko ina ba ya karya mata Azumi,


"Don tanajin Ajikin ta har wasu irin ruwa suka fito mata Alokacin da yake kissing dinta,


" A haka ta shigewar ta daki tabar su a falon tana shiga ta yi wurgi da jakar ta ta cire hijabin shima ta Ajiye ta fada kan gadon ta tana mai runtse idanunta,


"Ahankali takai hannun ta saman lips dinta tana shafawa saboda wani irin sululi suke yimata,

"Saboda irin tsotsar da yayi musu " wani irin Yarr takeji tsigar jikinta na mikewa "wai meyasa suke yimata haka? Don sunga ALLAH ya jarrabeta da lalura suke Amfani da wannan damar tata ta yawan shawa'aw shiyasa ta tsani Sulaiman A kullum zancen shi ta Y'ar da suyi Aure ya nema mata lafiya,


" Kwana biyu ta samu lafiya nasir baya gari tasan yana dawowa zai tada zancen Aure baisan cewa a halin yanzu ita kanta tafishi matsuwa ba,


"A Gaskiya Auren ta shine kawai mafita, to wazata Aura? Tafara tunani Akan Sulaiman a Gaskiya yayi mata hundred pacent saidai Sam bai kwanta mata ba sai kuma nasir shi ma ya hadu kuma yakai ta Aure shi kodan Amincin su da Hajara bazataki jinin ta ba,


" Amma me zuciyar ta bata tare da shi ' to tana wurin wa? Jeff kai tsaye Abinda ya fara zuwa mata kenan A ranta tayi saurin runtse idanun ta

"Is impossible taya ya zuciyar ta zata fada kan soyayyar karamin yaro? Tayaya zata fada son Arne baya hude ina?

" tayi saurin girgiza kanta bazai yuwuba A Gaskiya ba Gaskiya bane a take ta kara yanke ma kanta sha wara dole nema ta fisgeshi a jerin tunanin ta "nasir shine kawai ya dace dani kuma shima daga ganin shi jarumi ne,


" A Gaskiya Aure take so yanzu yana tanbayar ta zata bada kai a wuce wurin ko zata samu saukin Abun


"Wani irin bugawa k'irjin ta yayi tunawa da tayi da warnin din shi dazu, tsaki kawai tayi " shirmen banza ta mike cike da kasala ta zame rigar jikinta tana mai bin kirjinta da kallo ta dan karamin madubin dake banne da bangon dakinta,


"Ita kanta tasan takeru halittar kirjin ta ita kanta burgeta takeyi bare kuma da namiji,




" Ta dauki lokaci kafin ta daura zani ta zura katon hijabin ta tafito domin tana bukatar wanka kafin tayi sallar Azahar da takawo jiki,


"Suna zaune a y'anda ta barsu tunda ta fito idanun su suka zuba mata kowane su na tanbayar ta jikinta " ta Amsa taji sauki,


"Mahaifin ta har wani Annuri yake fitar wa Afuskar shi na ganin gudan jinin shi mai matukar kama da mahaifiyar ta, fuskar ta na tuna mai da tsohuwar Matar shi da yarasa,



" Tana fita ya kalli mahaifiyar shi "Hajiya kiyimin izini inje da Ummu Kaduna ta saba da yan uwanta koda na sati dayane,


" Hmm wato ita Matar ka tafi karfin tazo gidan ku ko?" har ma da yaranta bazasu zoba sai ita da take babba itace zata bisu ko?


"Aa yaya k'arki yi haka kibashi dama ya gyara KUSKUREN shi da yafada don haka ki barshi suje don ALLAH,

" Magaji bazan taba rabashi da yar shiba naga har yanzu bai gama sai tuwa ba gwara inbari yadawo kan hanya da kyau bazan bashi yarinya ba suje can su cutar min da ita ba


Tanajin muhawarar su kuma ita kanta zataso tabar wannan garin kodan wannan mayen yaron dake son dagula lissafin rayuwar ta,



"Shikuwa bature tun bayan komawar shi dakin ya zube Akan gadon ya na kuka mai ciwo soyayyar ta tafi komai daga mai hankali babban tashin hankalin shi a kullum soyayyar ta karuwa takeyi a cikin zuciyar shi,.


" yana kwance ya fara tuno surarta a dazu datake kwance yayi Ajiyar zuciya "I truly love you my heart desire ba gangar jikin nake bukata ba kece gaba dayan ki burin raina ki ceci Rayuwata,


" shi kadai yake sanbatun shi har zazzabi mai zafi ya fara rufeshi " har zuwa dare yana kwance ya dukun kune a cikin blanket sai rawar sanyi yakeyi


"Yayi ta kokarin yayiwa kanshi Allurar da ya hada dazu domin yayi mata Abun yaci tura don haka dole yayi dialing number Ak,


" Shikuwa dama duk sun gama karade garin Zaria suna neman shi Amma shiru duk hankalin iyayen shi ya gama tashi don suna mugun son dan nasu ,


"Yana d'auka yace " kazo Zaria hotel yanzu" ya furta dakyar ya kife wayar batareda ya kashe ba don A lokacin numfashin shi dakyar yake iya fitar da shi "


"Yana fada wa iyayen gaba daya suka dunguma zuwa Zaria hotel cikin tsananin tashin hankali'


" Alokacin da suka isa gaba daya ya gama fita hayya cin shi duk sun gigice A rikice su ka kwashe shi zuwa Asibiti Momyn shi sai kuka takeyi kamar ranta zai fita,



Tana famar kiran sunan shi " cikin gaggawa suka bashi gado domin bashi taimakon da ya dace



"Har kusan karfe daya idanun Ruman biyu takasa koda runtswa haka kawai takeson jin waye shi tana son tasan shi waye ,


" Atake ta mike domin tunawa da dan karamin diary din shi da ya bata ranar ta dakko jakar ta ta ciroshi tareda zuba mai idanu kyakkyawan diary ne dan karami kamar wani Po's.. .......✍


*masoya kuci gaba da biyoni domin jin wanene Jeff ko kuma muce Abdullah shin wai meye gaskiyar lamarin nan Kudai ci gaba da biyo*

*Matar soja"*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KUSKURE NA🙆*
_Love & Destiny_

_Written by Fenerh_

💫GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫

~Dedicated to~
All my fan's

*Alkhairi bashi kadan jinjinar ban girma zuwa gareki _HAUWA'U MUHAMMAD USMAN_ wato (REAL SMERSHER) godiya marar Adadi ALLAH yakara miki d'auka ka*

🅿➡🔟

"Ja afar Muhammad shine Asalin sunan Mahaifina,

" Anhaifeni a United kingdome Nataso cikin gata fiye da tunani ba Abinda narasa najin dad'in Rayuwa domin mahaifan Momy na mutane ne da suka shahara da dukiya akasar ,

"Nayi karatuna Amakaranta mafi tsada kuma ina shekara goma sha hudu na kammala da karatuna na mataki na biyu w'anda a take na fada jami'a fitattaciya wato University dake U.S.A,

" Wanda nakaranta Aikin Likitan ci ta fannin mata wato (gynecology) kasan cewar kasace da aka samu cigaba ko mai kankantar yaro zaiyi Abinda yake Ra ayi,

"Abu biyu ne tunda na taso yake daure min kai shine " banbanci da nake fuskanta a tsakanin iyaye na "nafarko banban cin Addini na biyu harshen da Mahaifina yayi kokarin koyarda ni da kuma gayamin Akan hukun cin Addinin shi,

" Mahaifiya ta kuwa duk ranar Sunday zata jani zuwa church domin Muyi bauta Amma a gefe daya Akullum Mahaifina na kokarin fahim tar dani Akan Addinin Gaskiya,

"A duk lokacin da naga yayi Salla nakan tsayar da shi da tanbayoyina Amma Alokacin duk bayanin da yakeyimin Sam bana fahimtar kodaya,

" Domin gani nakeyi Sam ba Addini bane idan na hada damu da muke zuwa church ana kide kide da kuma Raye Raye kullum muna cikin nishad'i,

"Tunanina ya fara canjawa ne Aranar da nafara haduwa da wani d'an Nigeria mai suna mukhtar a lokacin ina shekara ta goma sha bakwai wand's shima karatune yakawo shi mun kulla Amintaka a tsaka nin mu a sakamakon ganin shi cikakken bahaushe " shi kuwa yayi mamakin jin hausa A bakina bayan gani sak bature,

"Sakamakon zamana da mukhtar wato harshena ya kara kwarewa ta fannin hausa Ahankali mukayi mugun sabon da har gidan mu yake bina mukwana iyayena suna kulawa dashi sosai saboda suna matukar sona fiye da tunani

" Duk da Momy na ba ta cika zama bane kullum tana hanyar yawo zuwa garuruwa domin bunkasa business dinsu na family

"Mahaifina ma Ya samu daukaka sosai ta hanyar mahaifiyata Wanda har yakai ga samun matsayin jakadan Nigeria dake can kasar ta America,

" Yakan shigo Nigeria kai da kai sakamakon Aikin shi duk da na lura tun taso wata Akwai wata tarzoma Atsaka nin iyayen nawa,

"A kullum Mahaifina na fadamin inkiyayi zina inkuma kiyaye shan giya kasan cewar komai na kasar ba doka zakaga kana nan yara da zuwa club's susha giya suyi ta zina ce zinace,

" ban taba jin sha'awar yin ko daya daga cikiba duk da ina da Abokai da dama da suke kokarin Jana zuwa Aikata hakan,

"Mukhtar ne yafara yimin tanbayar da ban taba kokarin sanin Amsar ta ba " Shin ya Akayi mahaifina ya hadu da Momy na har sukayi Aure bayan ba Addinin su' daya ba?

"Duk da ya fadamin ba haramun bane ya halasta Auren Ahlil kitab,

Abin ya dame ni sosai har ya hana ni sukuni na samu Dady na na tanbaye shi,

" Dady a ina kuka hadu da Momy har kukayi Aure?

"Yayi matukar mamakin irin tanbayar da nayi Amma bai yi kasa Aguiwa ba ya fadamin komai,

" irin KUSKUREN da yayi na barin kasar shi ta haihuwa tareda barin iyayen shi masu matukar bukatar taimakon shi kasan cewar shine babba a wurin su kuma soyayyar Momyn ka itace Silar komai domin nayi mata Alkawarin bazan taba barin taba domin har matsala tasamu da iyayen ta a sanadin Auren mu,

"Shiyasa kaga duk lokacin da zanje Nigeria muke samun matsala da ita domin tana tunanin bazan dawo ba,

" Amma nasan ALLAH bazai barni ba tunda na watsar da hakkin iyayena Akan mace "kuma ba akan komai nayi hakan ba saboda girman Alkawarin da na daukar ma Kaina akan ta banaso ALLAH ya kamani da karya Alkawari,

" Alokacin kaina ya daure domin banga wata hujja da zaisa yaki nashi iyayen ba saboda ita tana tare da nata A kullum, A nan take na dauki Alwashin sai na gyara komai idan har na kammala karatuna ni zan je neman dangin Mahaifina,

"Bayan kwana biyu munje church tareda mahaifiyata bayan gama service na mike nayima pastor din mu tanbayar da ya kasa bani cikakkiyar Amsar ta

"Who is Jesus? Wato waye yesu?

Amsar shi " My son Jesus is god and he is the son of god our god your god and the god of the whole universe

"Aa Tayaya zai fadamin cewar Jesus ALLAH ne kuma dan ALLAH ne, ciki wanene Gaskiya

" na kuma tanbayar shi ya za ayi a ce shine dan ALLAH kuma yayi mulki?

Tanbayar da kawai nayi mai kenan ya fara kame kame tareda nemamin yafiya a cewar shi na Aikata mugun sabo ,

"Na dawo batareda samun wata gam shashiyar Amsa ba na samu Dady na shima na tanbaye shi,

" Dady wanene ALLAH? Cikin jin dad'in tanbayar ya cemin " ALLAH shine w'anda ya halicci komai da kowa shine ma mallakin sama da kasa shine nake yiwa Sallah A kullum nake rokon shi yafiya kuma yake yafemin,

"Wanene Jesus? " Annabi Isa A.s. bawan ALLAH ne Kuma Annabin ALLAH ne Wanda kafin shi Anyi Annabawa da dama kuma bayan shi Anyi Annabin karshe w'anda yafi kowane Annabi girma da daraja shine 'Annabi (Muhammad s.a.w),

"Amsar tashi ta shige ni sosai har ma na kwana da Abin Araina bayan gari ya waye naje makaranta muka hadu da mukthar shima nakara yimai tanbayoyin da nama Dady na ya bani Amsa kamar y'anda Mahaifina ya sanar dani ya hada har ma da hikimar shi domin y'anda zan kara fahimta,

" Ahankali nafara research akan Karin haske dangane da Addinin mahaifina wato Addinin musulunci kuma A kullum ina kara samun haske A cikin shi,

"Kaina yana dauremin sosai daga karshe na tuna da Mahaifina ya taba fada min Aduk lokacin da Abubuwa suka fi karfin ka ka kai kukan ka Wurin ubangiji zai war ware maka matsalolin ka,

" Ina kwance a katoton gadona dake cikin dakina kawai na kalli sama domin bansan irin Addu'ar da yakama ce niba " shin zanyi ta church ne ko kuma ta musulmi? To kuma ban iya Addu'ar musulunci ba

Kawai na furta "Oh god show me the right way bansan hanyar da ta dace dani ba Ance Kaine mai war ware matsaloli ALLAH ka war ware min nawa matsalolin,

" A ranar na kwanta da wuri na yi bacci mai dad'in gaske har da makarfkin da nakira da mabudin Rayuwata

"Mafarkin fuska mai Annuri fuska mai cikeda haske " Fuskar da bansan Meya kawota cikin mafarkina ba koda na farka na dade ina ganin wannan kyakkyawar fuskar a idanuna,

"Natashi A kasalance gaba daya wunin ranar da tunanin fuskar nayi shi,

" Har ma maifiyata ta damu da yanayin da tagan ni Aciki Banyi kasa a guiwa ba na fada mata naga wata fuska a mafarkina kuma Abin ya dame ni sosai,

"Wasa wasa komai na Rayuwata ya fara canjawa don kusan kullum sa inayi mafarkin wannan fuskar kamar ibada Ahankali zuciya ta Afka cikin soyayyar

Please Login or Register in order to submit comment