Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

khadija su mama bilki magaji da kuma Gwaggo Amina



Taso ace da ita za ayi tafiyar Amma ba hali saboda jaririn ta Amma zata roki Abdul ko umara ne suje kafin lokacin Aikin hajji,bad'i,



Suna tafiya ta fara gyara gidan tareda da taimakon y'ar Aikin ta domin tarbon mijin ta da zai iso,


Kawata gidan tayi da kwalliya mai tsari da kuma ban sha'awa ga wasu balloons data jejjera ta ko ina na welcome back da kuma happy birthday ,



"Sai bayan ta gama gyara gidan ta shiga kitchen ta hada mai lafiyayyan cake tayi mai simple decoration da happy birthday d'an gata na,




Ta shirya mai dishes masu dad'i sannan ta dawo kan Babyn ta ta shirya shi tsab tayi mai ado da wata T-shirt da aka bugo mai na mu samman da sunan shi a baya haneef gaban kuma J ne da golden ga d'an Jean's dinshi ta sanya mai socks da canvass fari na yara yaron kamar ka sace shi ka gudu'



Ta mikawa mai taimakon ta kafin ta shiga ta sheko nata wankan ta shirya cikin farar doguwar Riga kamar wedding gown mai net ta sama ta gyara sumar ta ta feshe da hair freshener kafin ta bi ko ina na jikinta da kamshi kala daban daban,




Tayi matukar kyau kamar sabuwar Amarya jin karar tsayuwar mota yasata fitowa da turaren haneef ta kara feshe shi kafin ta Rungume shi ta fita kofar falon domin tarban mai gidan ta,




" kallon shi takeyi cikeda so ga wani kwarjini da ya karayi yana sanye da wani tsadadden eyeglass na matasan yanzu jikin shi sanye da fararen suit wani irin farin ciki ne ya lullube ta ganin farin cikin ta ya dawo



Saida ya janyo briefcase dinshi sannan ya nufo cikin gidan cike da jin dadin yau ya dawo gidan shi bayan wata daya da yakwashe a England,



."tsayawa yayi turus domin hango tauraru wa mai haska zuciyar shi tsaye tareda bouncing baby dinshi cikin shiga ta Alfarma ga wani kyau da ta kara kana ganin ta kasan tana cikin kwanciyar hankali,



"Ajiyar zuciya ya sauke ya cire glass din ya nufota cikin kasala da kuma so'

Hannu yasa ya dauki yaron shi kafin ya rungumo ta gefe daya yana mai binta da ido gaba daya murna ta hanashi koda furta kalma daya,



" welcome home d'an gata na" ta furta wani cikin wani irin salo' kara matse ta yayi a gefen shi "tank you matar dangata


" ya kuke? "Alhmdulillah ta furta kafin ta bude kofar suka shiga ta kunna bouncing light dake rubuta welcome back and happy birthday to you d'an gata'



Ta jikin katon screen din TV ma haka ga wasu decoration da suka matukar burge shi " tuni gajiyar shi ta ware ya fara bin dakin da kallo ga katon cake din da ta shirya a tsakiyar falon a gefe da kwalbar tsadadden wine da kuma glass cup,




"Zuba mata ido yayi cike da Ma anoni da dama tare kuma da tanbaya,
" baby All this?



"Yeah my husband happy birthday , janyo d'an gadon yaron yayi dake falon ya shinfide shi kafin ya rungume ta tsam


" tank you my wife "kinsan ni na manta cewar yau na kara girma who told you?


Dagowa tayi " nataba jin momy ta fada shiyasa na rike date din how can I for get something special?



"I love you baby.. Saurin rufe mai baki tayi da hannun ta " nop not now muje kayi wanka kafito Muyi celebrating,



"Za a tayani ko domin kinsan dai a matse nake ko? Eh shiyasa bazan tayaka ba zaka hana mu celebrating, kaje inka shirya kafito,


Ta samu ya shiga dakin 'nan ma wani surprise din ya tarar gadon ma a tsakiyar shi ta Dan gata na aka rubuta da fulawa gefe kuma wani kyakkyawan kati ne da rose ja akai wani irin murmushi yayi ya d'auka,



*_may this day be the beginning of Another beautiful year for you. May there be pleasant surprise, Lot's of joy and infinite happiness wish you a very happy birthday D'AN GATA NA_*



" wow ya furta a zahiri bazai iya furta irin farin cikin da ya tsinci kanshi ba tubewa kawai yayi domin yayi saurin shirya wa ya koma falon yakuma ganin farin cikin shi,



Towel ya daura ya nufi bathroom a nan ma ruwan kanshi fulawowi ne a ciki ko ina decoration ne a jikin kofar yaci karo da wani katin



*_wishing an. Amazing day and many great thing to come to a wonderful person in my life, happy birthday D'an gata"_*




Dariya yayi irin ta jin dad'in nan ya juyo kawai domin farin ciki bazai barshi ba ya nufo falon domin ya kuma ganin ta don bazai iya nisa da itaba a y'anda yakejin shi a halin yanzu she drive's him crazy.......✍



"U too my fan's u are driving me crazy with ur comment I love you wujiga wujiga mun kusa kai karshen labarin Ruman da Abdullah da izinin ubangiji




*Matar Soja*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KUSKURE NA🙆*
_Love & Destiny_


_Written by Fenerh_

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


🅿➡4⃣7⃣

Dubawa ya rikayi bai ganta ba ya duba ko ina har kitchen kafin ya koma dakin wayar shi ya d'auka ya kirata'.


"Wai kina ina ne? Dariya tasa " sai ka shirya zaka ganni kayi sauri ina jiranka' saurin wurgi yayi da wayar ya nufi bathroom cikin sauri ya yi wanka ya fito ya samu kaya a jiye a gefen gadon


D'auka yayi ya duba rigar t-shirt ce mai guntun hannu polo an rubuta Happy birthday d'an gata a gabanta da bayan ta ya girgiza kai lallai na zama d'an gatan daga gani


A gurguje ya zura tree quarter din fari shima sannan yasa rigar ya feshe jikin shi da turarukan shi masu kamshi da tsada,



Yana fitowa ya sameta cikin shiga irin tashi saidai ita dogon wando tasa skintight ya kamata dam tata Rigar Armles ta dan kulle ta kadan a gefe,


Tana ganin shi ta juya mai bayan rigar ta "Matar d'an gata yagani da manyan harafi sannan ta dago mai yaron shi shima cikin irin shigar " d'an gata son a tashi rigar ,


Bazai iya musalta farin cikin shiba a yau karaso wa yayi cike da kauna ya rungume ta tsam wasu hawaye masu dumi suka fara zubowa a idanun shi,


"I love you so much my life kin gama bani duk farin ciki a Rayuwa murmushi tayi ta dago shi ta girgiza mai kai ta na goge mai idanun shi,


" kafa girma yanzu ga shekaru ga kuma yaron ka u are now a Dady so stop shedding tears ,


"Kece kike sani kuka baby kin maidani d'an gatan da gaske domin ba gatan da nake nema a duniya fiye da naki a yanzu,


" am sory my husband nayi wauta a baya banason in kuma tafka KUSKUREN da nayi ina kokarin gyara Rayuwa ta data iyali na ina Alfahari da Auren miji daya tamkar da dubu,


"Am very proud of you' ts furta tareda manna mai fake' Harar wasa ya mata " bansan irin wannan kiss din wayon Abani baki insha son raina'


"Saika ce ka koshi baby karka damu yanzu dai muje mu karasa celebration din mu,



Ya dauki d'an shi yana mai fake " baby me kike ba yaron d'an gata yayi irin wannan kibar?

"Abincin dan gata yakeci Shiyasa yayi jiki ta fada tana nunamai kirjin ta tareda dage mai gira da kuma kashe ido daya,


" zuba masu ido yayi zai kai hannu tayi saurin rikeshi ' not here baby come let me feed you first,


Sun ciyar da juna cikeda so da tattali sun yanka cake suka ba juna a baki kafin ta kira mai kula da yaron ta ta bata sauran suje su raba suma,


Kafin suka tattara sai bedroom domin akara sa babban celebration a can,
Tsit kakeji da daren nan sai ihun Abdullah kawai da nake jiyowa daga falo domin kin binsu nayi na tsaya lashe ragowar makulashen kar ayi bani,



Har kusan karfe ukun Asuba ina jiyo su kwana sukayi suna jaraba sai haneef yayi kuka suke tsayawa su lallashe shi



Tayi matukar kokari domin duk jarabar ta bata isa ta kamo Abdullah ba saidai tayi dauriya domin tadauki Al washin bashi kulawar da duk yake nema A Rayuwa,




Sai karfe goma safe suka fito cikin shiga ta Alfarma a gurguje ta shirya musu break fast sukayi cikeda tattalin juna ga d'an su a gefen su,



Tsaraba ya kawo musu kala kala ita da yaron shi na suturu da kuma sarkoki da takalma ga wata waya sabuwar yayi mai matukar tsada da ya kawo mata,


Shima yaron harda ke kunan hawa da kuma na zama dana kwanciya kala kala,


"Baby duk mu kadai wannan tsarabar ? " uhm ai bangama ba Anjima zamuje kika wani Abu ,


"Rungume shi tayi tana godiya sosai kamar zata Goya abin ta shikuwa Jinshi yake kamar bashi ba a yau ya gama samun Ummu Ruman ciki da waje y'anda yake bukata,




Karfe hudu na yamma suka fita cikin shigar Alfarma cikin katuwar motar shi tana rungume da yaron ta Asibiti ta fara rakashi ya d'an duba sannan suka nufi gidan su mukhtar,



Tarike musu tsaraba mai yawa a nan taci karo da Mubena suna tsayawa ita,kuma tana tsaye sa wani saurayi ga hijabi har kasa daga ganin ta tasamu natsuwa a Rayuwa,



Ido ta zuba musu gwanin burgewa " what a family ita kanta tasan Ruman tayi sa'a a rayuwar ta ta dukar da kai tana maijin kunyar rayuwar ta ta baya ,


Cikin gidan suka nufa batareda sun kula ta ba mama ta tarbesu cikin mutunci suka gaisa tayi ma Ummu maraba,


Yau Yata tazo bani mai gidan ingani haka tayi ta haba haba ya tanbayi mukhtar tace yana ciki ka shiga,



Barin ta yayi da momy ya nufi sashen mukhtar "sun tari juna cikin farin ciki, 'ai nasan kana bukatar time jiya kar inyi mugun gani yasa naki zuwa gidan ku,


" ka kuwa kyauta domin da kazo bazan kalle ka ba, nasani nima dai Saura sati biyu Kasani ko,?


Eh amma dai munrigaku ai" nidai ya zancen Abun an kammala? "Eh bari in shirya muje ko? 'No zan mata surprise ne



" fitowa yayi bayan sun gama maganar su da ta shafesu sukayi sallama da mama tareda Ajiye mata tsarabar da sukazo mata da ita,



Suna fitowa zata shigo ta dukar da kai cike da kunya "ina wuni yaya Abdullah ta fada cikin ladabi"


"Dariya taso bashi ya Amsa ita kuwa Ruman tuni tayi mota don ta tsani Yarinyar sosai,


Saida ya tsaya ya bata hakuri tace ba komai itace zata bashi hakuri sannan ya nufo motar tayi tab tacika


" zama yayi yana dariya "wannan fuskar fa matar d'an gata?
" banza tayi mai shima bai kuma cewa komai ba saida suka isa na sarawa bakin wani katon super market ya faka a gefe ya fito kafin ya bude mata ya karbi yaron shi yasa a Kafada,


"Ya riko hannun ta ta fito ta zubawa rubutun wurin ido cike da mamaki ganin rubutun dake jiki DAN GATA SON super market gefe kuma wani katon saloon ne da aka rubuta DAN GATA WIFE saloon sai a dayan gefen kuma wani katon kamfani ne da idan bata manta ba a wurin ne kamfanin da aka mallaka wa Haneef wato kyauta r haihuwar da Dady ya mata,



Gaba daya duk girman wurin ya zama mallakin su kenan? Wasu hawaye ne masu zafi suka biyo kumatun ta tayi saurin rungume shi ,



" ya dagota yana dariya "meye na kuka matar d'an gata? Muje daga ciki kigani' ki ajiye hawayen nan sai munje gida kinayi ina tsotse wa ta d'an bugi kirjin shi kadan yace " Auch sai na rama,

Da sauri tayi gaba domin zai Aikata suka shiga ciki, wurin ya kayatar da ita komai Akwai a wurin ta kasa bakin magana sai hawaye kawai take maida wa,



Sai gab da magrib suka nufi gidan su cike da jin dad'i,



A gurguje.


Bayan y'an satuka Alhazai sun dawo su Dady sun shirya wa su Hajiya tsantsa reren gida a Kaduna domin yace hidimomin su yafi yawa a Kaduna gida guda ya gina musu saidai kowa na gefen shi ya zuba musu y'an aiki ta ko ina basa cas basa as,



Momy na Aikin ta hade da business dinta na kasar ta "magaji w'anda ya zama Alhaji a yanzu ya yi wata irin kibar jin dad'i,




Haneef yayi wayau sosai yaro d'an wata uku yayi kamar dan wata shida saboda jin dadi, kullum yana wurin kakan nin shi mu samman Dady zaizo ya dauke shi yaje dashi gida idan yana free haka ma momy yaro mai gata,



.

Anyi bikin su hajara itama tana nan a Kaduna suna soyewar su da mukhtar Sumy ma ta haifi y'ar ta


..

Bayan wata tara'

Haneef yayi wayau yanada kusan shekara Ruman ta samu hutu da jin dadi na duniya ga miji mai sonta suna shirin tafiya umara daga can zasuyi Aikin haji kafin su dawo kasan cewar Azumi ya karato,




Haneef dai anyaye shi tuni momy ta d'auka sukuma suka dunguma sai kasa mai tsarki domin sauke farali tare dasu hajara



" ibada suke gabatar wa cikin natsuwa domin tayi matukar farin cikin ganin ta a gaban ka'aba da take mafarkin zuwa gashi Allah ya kawota dole ta dage da gode wa ubangiji da yamata baiwa,



" suna kasa mai tsarki har suka yi Azumin su suka yi umara tareda Aikin hajin su kafin su tattara su wuce us wurin y'an uwan momy su mukhtar su sun juya nija domin Asibiti ba Abdul shima baya nan,



"Suna kwance a kan gadon su ya rungume ta bayan sun gama hutawar su" baby kin tuna Meya faru a wannan gadon'



"Juyowa tayi tana mai kallon idon shi " ya zan manta da wannan gadon bayan a kanshi aka barkeni a kai aka nunamin KUSKURE NA


Dariya yasa ya rungume ta tsam ya ce "yau ma sai na nuna miki KUSKUREN ki domin kinki bani dama in baki twins to yau sai kin bani Abdullah da Ruman,

Wutar ya kashe tareda shigewa cikin bargo bayan ya wurgoni da Biro na da ya tona min Asiri domin faduwar da yayi


" toh shugaban munafukai sai a barmu haka ko? Jawo kafafuna nayi cike da sanyi wato Abdullah duk tsawon rayuwar su da Ruman yana Ankare dani Amma ko na burodi bai bani ba,



To my fan's ku taimako dana jirgi don dagani a us za abaroni tunda Asiri ya tonu,



"A nan nakawo karshen wannan lbr masoya Abdullah da Ruman har ma da Fenerh fan's ina matukar godiya agareku,

Godiya Mara iyaka ga..✍

Golden pen writers
Umar dalhat jigon golden

Nabeela jinin dan gwate ina godiya Allah yabar kauna,.

Princess Fatima mazadu ina jinjina


Oum Deedat Allah ya kara hazaka,

Maman mamy shalele jinjinar ban girma

One luv jakadiyar golden

eedatu
Fareedaty
Dr fati sabitu
Lipton girl
Prince's
Etc


Ina jin jina gareku y'an golden Allah yakara hazaka da kuma hada kanmu,



Godiya gareku yan group din
Beneficial writers
Boyayyan Al amari
Mom General fan's
Sidiya fans
Raina kama fans
Maman nurul huda fans
Nayi nadama fans
Meye Asalina fans
Smersher &hubbey fans
Novel makeup & kitchen
Rudani fans
Momyn ihsan

My precious groups
KUSKURE Na fans ✍
KUSKURE NA fan's 2
KUSKURE Na
Fenerh fan's

Kuna sani nishad'i kunada yawa bazan iya fadar kuba Amma kusani duk ina sanedaku ina kuma Alfahari da ku kune ke bani karfin guiwa da bazar Ku nake taka rawa Alherin Allah ya kai muku masoyan Asali.



Alhmdulillah Alhmdulillah Alhmdulillah

"Rabbana inna na amanna fagfirlana dhunubana wa qinaa adhaban nar(I)"

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment