Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Anymore zan nemi dangi na inyaso kiyi duk Abinda kikaga dama,


"Jeff kuwa komai a kan idanun shi koda likita ya nufoshi ya daga mai hannu domin ranshi na suya ko motsi kasa yi yayi ya nufota dakyar ya dora hannun shi Akan fuskar ta " Am sorry """"

"Kawai ya iya furta wa yana taku dakyar ya kalli su Hajara ku wuce da ita gida please nagode muku jikin su a sanyaye suka fita domin hankalin su yayi matukar tashi daganin irin wannan tashin hankalin


"Suna shiga motar su Sumy tace A Gaskiya Queen Alhakin wannan bayin ALLAH sai ya kama ki kin tarwatsa gidan mutane Hajara tace Alhakin Abdullah zai fara kamata,


" ta fashe da kuka " haba mana ku bakwa ganin illar Abin yanzu Ashe gwara da ban karbi soyayyar shi ba tun farko impact ni bazan iya soyayya da yaroba yaron ma shagwababben da ya Riga ya lalace da Hutu Abu kadan kuka kamar jariri sannan ku kalli Arzikin su ina ni ina shi ina yar talaka

"Ni kuma rufe wannan maganar kawai nagaji da jinta.......✍



*ku biyoni bashi zuwa dare my fans managed this one I love you All*


*Matar Soja*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KUSKURE NAπŸ™†*
_Love & Destiny_


_Written by Fenerh_


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*

~Dedicated to~
All my fan's

*Kuna ina ?yan uwana marubuta wato taurarin mu na Golden pen writers Association*
_Doctor Fati_
_princess_
_Ameshat_
_Maman Mamy_
_Dejer love_
_Ummu noor_
_Maman Ashfat_
_princess mazadu_
_Khadijat Hydar_
_tareda Zinariya ta_
*jin jinar bangirma zuwa gareku yan uwa na Allah ya kara daga darajar forum din mu Ameen ina matukar yinku*


πŸ…Ώβž‘1⃣3⃣

Saida suka mayar da ita gida sannan suka juya batareda sun shiga ciki ba domin suna fushi da ita sosai,


Ita kadai tasan halin da zuciyar ta take ciki tayi matukar kok'arin ganin ta dai daita natsuwar ta kafin ta shiga cikin gidan su


Gaba daya idanun sa idawan Akanta, ta na shigewa suka fara sana'ar,

Tana shiga ta same su kamar ranar Hajiya baban ta da kuma magaji " tashigo da sallama ta gaishe su,

"Kindawo? Inji Hajiya ta Amsa eh su hajara ne ma suka sauke ni suna sauri ne shiyasa basu shigo ba,.

" Toh ai ba komai, ta wuce ciki suka ci gaba da tattaunawa


"ina ganin ko yayi tafiya ne shiyasa baya zuwa Amma tunda ya biya kudin hayar shi daki na zaman shi ne,

" Kawu idan babu damuwa ku mayar mai da kudin shi kawai tunda ma ba zama yakeyi ba inaso in gyara gidan nan gaba daya,

"Hajiya ma dole ta bar wannan sana'ar,
Banason t'sirfa da da ka futa hanyar mu me yasa memu sai yanzu don ka dawo ka fara yimin salon banza ka barmin gidana haka kuma dakin ma da kake zance akan shi ko kai Bazaka iya gyara shi kamar y'anda ya gyara shi,

" Don haka kabar min gidana haka nan, Haba Hajiya baki yafe min bane? Ni na yafe maka tuntuni " ki yimin Alfarma in dauki nauyin da ke kaina don ALLAH,

"Kawu kasa baki, Magaji dake gefe ya kalle ta " Yaya kiyi hakuri kibar shi yayi Abinda ya kamata,


"Ina daga cikin daki naji kirji na ya buga " me hakan yake nufi? Baba na nason ya hana kowa zuwa gidan kenan? Ita da take sa ran ba Jeff hakuri ya dawo gidan su duk da tasan ba Abu ne mai yuwu ba tunda taga iyayen shi a gari bazasu taba bari ya dawo nan gidan da zama ba,

Abun duniya ya taru yayi mata yawa ga wani Abin tashin hankalin kuma Nasir ya kirata wai zai dawo ta tarbe shi da yamma


"Ita bashi bane damuwar ta , ita gaba daya hankalin ta na wurin Jeff ko ya jikin shi ?




Tasha matukar mamakin y'anda su hajara suka dauke mata wuta sai wani shan kamshi sukeyi suna share ta " Abun ya matukar da munta saboda tana son taji ko ya samu sauki,


"Lokacin da Aka tashi kuwa suna fitowa suka yi wuce war su batareda sun koma kanta ba,


" Ta fito tana takowa ta ga mota tasha gabanta " Tasan waye ba kowa bane face doctor Sulaiman sarkin nacin tsiya,.

"Hajiya Ummu Ruman Ataimaka min don ALLAH Ashigo Ayimin wannan Alfarmar har yana hade Hannayen shi Alamar roko,

" bata da zabi domin yana yi mata kwarjini sosai shiyasa take kokarin kauce wa haduwar su Bata so tayimai rashin mutunci,

"Har suka isa kofar gidan bata cemai komai ba shi kadai ke surutun shi ita hankalin ta yayi nisa sosai,


" Sai da ya tafa hannun shi akan fuskar ta ta dawo hankalin ta " munzo gida hajiyata me kike tunani haka inata zuba nikadai?

"Ta kalli kofar gidan su ta d'an kalli gefen shi " nagode sosai ta fara kok'arin fita motar,

"Ummu" ya kirata " ta tsaya tareda Amsa wa " Don ALLAH ki rufa min Asiri ki bari in turo iyaye na Ayi zancen Auren mu "Wallahi na mugun matsuwa,


" wani irin kallo tayi mishi don ita zancen nashi ta bata kunya Amma shi ko Ajikin shi " ta dukar da kanta kawai ta kasa cemai komai "ki taimake ni don ALLAH kinji,


" Inaso in gama karatu na banaso in hada karatuna da Aure nafi so ingama karatuna, Hmm yayi d'an murmushi,

"Bakya tunanin lalurar ki? Ya kamata kiyi wani Abu Akai kuma nima Gaskiya na gaji da zaman gauran taka " ina bukatar mata Atare dani kinga Azumi ya kusa' inso samu ne kiyi Azumi A gidan ki,


"Shiru kawai tayi mai don batada Amsar maganar shi " kije kiyi Shawara zuwa gobe zandawo inji ra ayin ki Akai,


"A k'agau ce ta fita motar dan mugun haushi yake bata A halin yanzu tunda yasan matsalar ta dole ya dame ta da zancen Aure,


" Tun daga tsakar gidan su ta tsaya cak domin jin kamshin turaren da yafi kowane turare da take shaka kamshi mai shiga zuciya


"Ta kalli kofar dakin da take tunanin yana ciki zuciyar ta na bugawa kamar An dasa ta Awurin ko kwakkwaran motsi ta kasa yi,


" Lafiya Ummu ki karaso mana tunanin me kike yi "Tayi saurin kallon gefen da Hajiya take " ta karasa "Hajiya waye Acikin dakin can?

" Mai daki mana, ta bata Amsa a takai ce " Amma naji baba yace ya tashi ai,

"To ai sai ki Kore shi ko " kuma k'arki ji da wai y'anda zaki zauna Anan gidan shima yana da yancin zama Acikin shi


"Kanta yayi mugun daure wa ta ce " ban gane me kike nufi ba kakus?

"Ki shigo daga ciki tukun sai kiji koma meye, haka jikinta na rawa tana ta ALLAH ta ji dalilin dawowar shi bayan ya mata Alkawari bazai kuma zuwa gidan ba,


" Ta tube hijabin ta ta Ajiye jakar ta sannan ta dawo falon ta fada jikin Hajiya ta rungume ta "

"Kara sani zakiyi y'ar wofi inaji da zufa na dama ya lafiyar kafar take ke Abu ba kadan ba,

" Ta tuntsire da dariya tareda kara matse ta " ina sonki kakata ki barni in more don ALLAH nayi kewar hawa kafar ki kwana biyu,


"Eh dole Kice haka mana ni gaba daya ban gane miki bane kwana biyu duk kin janza daga Ummu da na sani zuwa wata daban,

" Aa Hajiya ni ban canja komai ba nice dai y'ar jikan yar ki Ummu Ruman y'ar lelen Hajiya kaka mai tuwon yan gayu...


"Sallamar shi ta dawo da ita daga shaki yan cin da take yima Hajiya kamar Andauke wutar lantar ki ta tayi dif tareda juyowa ta kalle shi,


" ya d'an rame sai dai yayi mugun yi mata kyau cikin shigar shi A kullum wato fararen kaya sai wani tashin kamshi yakeyi ga wani haske da Annuri dake haska fuskar shi,


"Batareda ya ko kalli gefen ta ba ya ce" Mama sannu da hutawa,

"Aa kar ka wani cuceni kace min mama ni ban haife kuba kaida wannan shakiyiyar ku nemi iyayen ku, ta fada cikin raha fuskar ta dauke da tsananin farin ciki,


" Wani irin murmushi yake fitar wa a fuskar shi mai ta fiya da tunanin mace ita kanta ta manta da kanta wajen kallon shi yana lura da yanayin ta,


"Kaka Ashe Aunty ta dawo? Eh gatanan ta sani gaba " Ummu kinga ikon ALLAH ko Ashe muna tareda gudan jinin mu bamu sani ba,


"Tayi saurin tashi zaune nan take brain dinta ya hasko mata komai " kardai Ace shine d'an gidan kawunta mai Auren baturiya?



"Impossible kenan Ana nufin shi din Ai nihin jinin ta ne ta kalle shi ya daga mata gira daya toh ya Akayi suka gano hakan?


" Ummu ga Abdullahi nan dazu suka zo da uban shi nan mahaifin ki ya nemo shi dama su suna zumun cin su tunda Abin tsiyar iri daya suka kulla,



"Tayi matukar mamaki Ashe ba banza ba taji mutumin ya tsaya mata Azuciya Ashe kawun ta ne yayan mamar ta,


" Hajiya bakin ta baiyi shiru ba " Ai jafaru da Muhammadu sai dai ince ALLAH ya kiyaye na baya da fadawa sharrin mace shedaniya

Ikon Allah yanzu dama shi jinin ta ne meyasa bata fuskan ci hakan ba tun a labarin da ta karan ta kuma haduwar ta Asibiti da babanshi taga tsantsar kamannin kaka magaji Ashe shine kawunta Allah mai yadda yaso,



" Yana zaune kamar bai Santa ba haka ya nuna bayan hada ido sau daya da sukayi bai kuma kallon gefen ta ba kanshi na kan wayar shi yana faman danna wa,


"Daga karshe ma mikewa yayi " Kaka bari infita zanje inga super market dina da Ake aiki a sabon gari sai na dawo'.


"ALLAH ya taimaka yasa kar kayi halin iyayen ka kazama sai y'anda mace tayi dakai,

"Ahab sai dai kar Akuma Hajiya tawa ma har mijin k'an tace sai na zama saboda ita idan nayi wasa yake aiya nawa a zuciyar shi,

" A fili kuwa , " ina kaka ni bazan dauki mace ta juya niba "Yanzu haka zuwa na nan garin nasamu wata " yar yarin ya har mun dai dai ta kafin Azumi kila kusha biki,

"Ya furta tareda matsewa " wani irin kallo ta jefeshi da shi kirjin ta na dukan uku uku bai ko kalle ta ba yayi ficewar shi daga gidan,


"Wannan me yake nufi da hakan? Da gaske ya samu wata macen yana so? Wacece ita?

" haka kawai taji komai ya fice mata Aka duk wal walar ta ta bace mikewa kawai tayi cike da mutuwar jiki ta shige daki kayan jikin ta tafara tubewa tana jifa da su,

"Saurin hadiye Abinda ya fito ya tokare mata mak'ogoro tayi, me yake da mu na? Idan ma yasamu wata macen sai me ina ruwana,

" Duk yadda taso Abin ya fita Azuciyar ta Amma Abin yaci tura,

"Bai dawo gidan ba sai kusan karfe goma na dare lokacin tana zaune ta mike kafa A gefen Hajiya daga ita sai wata yar t shirt da ta kamata dam ta daura zanin Atanfa kanta ba dankwali sai kalaba kanana da Hajara tayi mata tayi parking dinta da katon ribbon ta sake shi a gefen wuyan ta


" ta tasa Awara a gabanta tana ta faman ci tareda dangwala yaji " Hajiya kin San me?
"Ina fa zan sani tunda kinsani gaba kamar mai neman gafara ke idan dai Awara ce tsab za ai miki Asiri da ita,



" Wata irin dariya tasa har tana kware wa " kai Wallahi kakus kinada Abin dariya


Dariyar ta ta tsaya ne tsab lokacin da ya sawo kai cikin falon tareda sallama yana sanye cikin farin tree quarter da kuma farar t shirt kamar kullum dai,


"Ta fara gyara zamanta ta dan juya mai baya" ya gaida Hajiya tace " Sai yanzu? Aa na dade da dawo wa naje can gidan tsofaffin can ne kuma na tsaya jiran Momy na ta dawo daga Abuja a yau,

"Kuma naje hira wurin budurwa ta" Wani irin kallo ta aika mai yayi murmushin gefen baki" Sannu Aunty na ya kk?


"Wani irin bakin ciki ya tokare mata makoshi dan rainin hankali itace Aunty shi yau,

" Um Aunty A taimaka min da laptop dina zan danyi bincike idan kina bukata ne kuma ki rike duka" ya fada cikin yanayin zolaya

"Wani iri ta kalle shi wannan kamar maye waye ya fada mai ita ta d'auka bayan ba Wanda ya san ta d'auka


" Wani irin kallo yake aika mata akai kaice domin tayi masifar yimai kyau bai taba ganin tsawon gashin ta ba sai yau duk da kalaba ce akan Abin ya burge shi har ma ya dauki hankalin shi sosai,


"Ina ita umman taka take Abdullahi? Tana GRA ban gaya mata komai ba nafiso Dady ya fada mata to ALLAH ya kyauta,

" Mikewa kawai tayi domin jin ta takeyi A takure tunda ta mike ya kafe ta da idanun shi kamar ya janyo ta zuwa jikinshi wani irin numfashi yaja dakyar,


"Zata kashe ni wannan Yarinyar Wallahi tanaso ta haukata ni da gaske, ya runtse idanun shi Alokacin da ta karasa shigewa cikin dakin,

" Mikewa yayi dakyar domin ita yazo gani Amma ganin ta Sam ba Alkhairi yana tangad'i yace kaka saida safe,


"ALLAH ya tashe mu lafiya yana shigewa cikin dakin shi direct bathroom ya fada ya dauki bokitin ruwa mai sanyi ya sheka a jikin shi,

" ko zai samu natsuwar shi ta dawo ya dauki lokaci a tsaye yana diga kafin ya dan samu sauki ya tube kayan tareda dauro towel ya fito zubewa kawai yayi akan gado ya kife tareda fitar da zazzafan numfashi,


"A Gaskiya Dady na dawo wa gobe dole zai San Abinyi don yakai mak'ura he can take it Anymore,


" Wallahi idan har baso sukeyi ya Aikata mugun aiki ba su Aura mai ita kawai Azauna lafiya kuma shi baiki A daura gobe ba don ji yake yi kamar yayi mata fyade idan har ya ganta a kusa da shi,


"Shi Dadyn Kaduna ma kawai zai samu Ayi wadda za ayi kawai, wani irin natsuwa ce ta kama shi Alokacin da ya tuna da cewa Ruman jinin jikin shi ce y'ar uwa Abin yana yimai dad'i sosai

Allah ne ya kaddara hakan domin yazama iznah ga Momyn shi hakkin su na iyaye ne ALLAH ya kwato musu ta karfin Addu'a,

" ALLAH ya sanya soyayyar jinin shi A cikin zuciyar shi tun bai San da ita ba har ALLAH ya hada su, ALLAH mai girma ALLAH buwayi gagara misali,

"Bai San y'anda zai misalta farin cikin shi ba Alokacin da Dadyn shi ya nuna mai mahaifin Ruman Amatsayin kawun shi ga dangan taka mai karfin gaske A tsakanin su ta kowane gefe,


" Yasan yanzu ba Abinda zai hanashi mallakar Ruman saidai ikon ALLAH, tuni Annurin fuskar shi ya canja lokacin da ya tuna da Momyn shi domin yasan da Akwai sauran rina A kaba Sannan ga Ita kanta Ruman din kuma,

"Wadda ya sani sarai yanzu ta fara son shi tsabar taurin Kaine kawai ke dawai niya da ita ,


" Yayi wani irin murmushi da ya tuna da irin kallon hotunan shi da takeyi A kullum ta system din shi, Abinda bata sani ba system din shi na hade da camerar wayar shi da zarar aka bude ta sai ta nuna mai Abin da Akeyi da ita kuma shi yake tai maka mata wajen bude folder din,


"Ya hango tsantsar kishin shi A cikin kwayar idanun ta A lokacin da yace yana da budurwa,


Ganin tunanin shi zaiyi yawa ya mike tareda dauro Alwala domin yasan idan ba Salla yayi ba yau bashi ba bacci cikin lafiya,


" Washe gari kuwa tun da ta tashi ta yi Salla tayi sharar ko ina na gidan domin yanzu duk ba masu Aikin Abin cin babanta ya hana sanaar cikin kwana biyu kacal Abin yafi komai yi mata dadi yanzu gidan su zai samu lafiya da mutane,



"Sai kusan karfe bakwai ta kammala komai har ruwan shayi ta dafawa Hajiya ta soya mata kwai tace Hajjaju gashi yanzu ba cin tuwo ko funka sau da safe,

" ta kai mata duka ta gudu " ai ubanki ne duk yaja haka kawai ya hanani Sana'a ta so yake in zauna ba cas ba as sai dai ya kawo min Abincin da ba gamsar da ni yake ba,


"Yanzu kakus duk wa innan kayan Abincin da nagani ina zaki kaisu?


" Gidan ku zankai su y'ar kunnen uwa, ita dai ta shirya Abinta tafito fes cikin Riga da zani na Atanfa ta yafa ta yafa farin gyale tareda takalmin su cikin kayan da baban ta ya kawo mata ne,

"Kusan karo suka gwabza da Doctor Sulaiman yana sawo kai cikin gidan yayi saurin ja baya " Tuba nake gimbiya nazo ne inkai ki makaran ta bai kamata kina hawa mashin ba bayan gani kuma jiya na kasa runtsa wa inaso inzo inji shawarr da kika yanke akan zancen Auren mu,

"Duk maganar da sukeyi yana tsaye a gefe yana kallon su idanun shi yayi jajur kamar gauta saboda Azabar kishi..........✍

*Kuyi hakuri ntwk na wahalar dani sosai msges dina na shigowa slowly shiya sa bayi muku post ba kamar y'anda nayi niya ba ku gafar ce ni komai sai Allah ya y'arda kuci gaba da biyoni masoyan kwarai*


*Matar Soja*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KUSKURE NAπŸ™†*
_Love & Destiny_

_Written by Fenerh_

πŸ§šπŸ»β€β™€ *SARAUNIYAR TAURARIN G,P.W.A* πŸ§šπŸ»β€β™€


✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽✍🏽

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


πŸ…Ώβž‘1⃣4⃣

"Wani irin tafasa zuciyar Abdullah takeyi domin tsananin kishi da ya rufe mai idanu nan take fuskar shi fara ta canja zuwa ja tsabar takaici ya bugo kofar dakin garab har sai da suka tsorata,


" Tayi saurin kallon kofar baya wurin ya Riga ya shige ciki Abinshi badon taso ba ta ce suje zasuyi maganar Ahanya,


"Ga badaya hankalin ta baya kanshi tana tunanin haduwar ta da shi domin tasan ya fada mata baya kaunar ganin ta da kowane namiji,


" Bata San meyasa ba Sam bataji dad'in fushin nashi ba, har ya sauke ta Acikin makaranta jikinta a matukar sanyaye,

"Ya na tsaya wa ya juyo yana mai fuskan tar ta" Ruman please " ki bani izini Jan Ajin ya isa haka ina matukar bukatar iyali Atare dani ki taimaka ki bani dama,

"Zuciyar ta tayi nisa cikin tunanin halin da Abdullah ke ciki " shi kenan ba damuwa ta furta Ahankali,



"Cikin tsananin farin ciki yace " nagode sosai yau zanyi bacci har da minshari tank you so much,

"Wani irin kallo ta aika mishi dashi w'anda ya kara tsima shi, ita kuwa tunani takeyi why yake yi mata godiya?

" Sai kace ta ce Zata Aure shi, ta bude motar ta fita shikuwa ya juya cike da farin ciki,


"Yau ma kamar jiya Su Hajara sai shan kamshi sukeyi cikin dauriya ta samesu,


" Wai me yake faruwa ne haka? Nayi muku wani laifin ne kuke share ni?

"Bako daya.inji hajara " Banajin dad'in yadda kike wahalar da yaron mutane ne,

"Wata Ajiyar zuciya ta sauke" yanzu duk Akan Abdullah ne kuke yimin haka? Amma ku tuna nice kawar ku bashi ba kafin ku sanshi ni kuka fara sani bai kamata sanadin wani Ace mun samu matsala ba,

"Kuma Abdullah din nan da kuke gani ba y'anda za ayi na Aure shi yana matsayin kanina,

" kamar yaya kanin ki ? Eh he is my brother, Ahankali ta war ware musu komai " sunyi matukar farin ciki da jin wannan labari,


"Sumayya ce ta kalle ta ta d'an daure fuska" Queen " tsakanin ki da ALLAH bakya son shi ?

"Wani iri tayi sannan ta kalle su fuskar ta tayi matukar sau yawa " idan nace bana son shi nayi ma kaina karya kuma Banyi wa Kaina Adalci ba,

"Ina son shi sosai " Amma bakwa ganin cewar ba ta y'anda za ayi Muyi Aure bayan har yanzu Akwai sauran sarkakiya mahaifiyar shi bazata y'ar da ba,

"Kai ni kaina ko son shi zai kashe ni bazan taba y'ar da in Aure shi ba saboda Sam ba tsari A cikin lamarin Da ma Ace ba mu hada jini ba ba w'anda zai San na girme shi Amma yanzu ko jama'ar gari sun isa su zage ni


" ku kun sani na tsani Auren karamin yaro shi kanshi bansan lokacin da yayi nasarar cafke zuciya ta ba ina matukar kaunar shi nasan ina nuna mai hakan ALLAH kadai yasan mai zai faru A cikin Family,


"Shiru kawai sukayi suna tunani " Amma idan har kun dai daita kanku ina ganin iyayen ku zasuyi matukar farin ciki mu samman Hajiya ma,


"Ni ko bama zai yuwu ba kawai mu bar zancen, "to soyayyar da kukewa juna fa" soyayyar da yake nuna min dai ni bazan iya furta mai soyayya ba yana matsayin kani na,

"Hmm Ummu zaki tafka KUSKURE babba Arayuwar ki idan har baki dai dai ta tunanin ki ba,

" Ku taya ni Addu'ar ALLAH ya cire min son shi daga cikin zuciya ta kawai my friends,

"ALLAH ya zaba mana mafi Alkhairi, Guy's ni dai ending of this semester Zanyi Aure jiya My D ya turo Sumy ta fada cike da farin ciki,


" suka buga tsalle suka Dane ta " Wayyo dadi zamu sha biki " Amma yarin ya kin shamma ce mu Wallahi " Hajara ta fada tana kai mata dukan wasa,


"Wallahi nima ban yi zaton Abun zai faru da sauri ba na d'auka idan ya turo za a dauki lokaci Amma suna zuwa baffa na ya tsayar nan da wata daya cif,


" ALLAH ya nuna mana sai Muyi shirin Kwasar shoki Ashe kawa za a shige daga ciki " idan kin shiga zaki bamu labari ya lamarin yake,


"A ranar sun wuni cikin nishad'i da kuma farin ciki bayan ta shin su saida suka fara sauke ta sannan suka wuce,

" Tun Shigowar ta take kallon kofar dakin shi har ta shige cikin falon Hajiya ta sameta Azaune ta kurawa TV ido,

"Da sallama ta karasa tareda gai sheta ta zube akasa tareda cewa washh nagaji,.

" Aikin gona kika je ne? Da kike cewa kin gaji " aa nidai Yunwa nakeji meye Akwai?

"Ga d'an wake nan shi nayiwa babanki da kuma kawunki gashi nan a cikin kula idan zaki ci" baba ya zone ? Eh suna gidan Magaji tareda kawun ki Amina babu lafiya,


"Me yasa meta kuma? Damuwa ce kawai da take boyewa ta bayyana yanzu ai sayi wa Kansu karatun ta natsu Alhakin iyaye yawa ne dashi,


" sanin mitar Hajiya yasa ta mike sum sum ta shige saida tayi wanka ta shirya tareda sanya doguwar Rigar Atanfa ta murza dankwalinta kamar wata sabuwar Amarya sannan ta zauna cin d'an waken ta,


"Sai kusan magrib baban ta ya shigo tareda mahaifin Abdullah " cikin matukar farin ciki ya kalle ta " Ummu zo nan A she Yata ce ke ?


"Bai karasa maganar shi ba Hajiya ta tari numfashin shi " ina fa zaku sani tunda kun watsar da iyayen ku akan mace Wallahi ku kiyayi duniya duk Abinda ka shuka sai ka girbe shi,


"Ganin Fadan Hajiya bazai kare ba yasa na mike sum sum na fice gaba daya daga cikin dakin domin in basu wuri su tattauna,

"Tayi matukar farin cikin da kawunta bai yi zancen soyayyar da Abdullah ke yimata ba kuma bai tona cewa taje har Asibiti hai she shi ba,


Yau ta ji dad'in fadan Hajiya, kujera ta janyo ta zauna tareda kunna wayarta ta fara bude sakonni kala kala da suka shigo atake wasu daga Nasir wasu kuma na Abdullah ne,


" Sallamar yaro ne ya katse mata Abin da takeyi " wai Ana sallama da Ummu Ruman," waye ke nema na ta tanbaya?

"Wani mutum ne a mota, tayi Jim tana tunani ko sarkin naci ne ya kuma dawowa again' " kace ina zuwa saida ta dakko hijabin ta ta kalli Hajiya " ina zuwa Hajiya Ana sallama dani zan je inga ko waye?


"To ba damuwa dama hakan kikeyi da tuni ai munsha buki, ta wuce cike da jin kunyar baban ta da kuma kawun ta,

" Jafaru idan ka gama shiriritar ka sai ka shirya yar ka Magabatan yaron da ke neman ta zasu turo cikin satin nan dazu yake fadamin sun dai daita ta kuma Amince " ina jiran ta zauna in kuma tanbayar ta Anjima in har ta Amsa to sai ku sa buki kawai ko ya kukace Kaine ubanta,


"Jikin shi yayi sanyi sosai yaso yayi zancen Abdullah Amma tunda har tana da tsayyaye bazai so kanshi ba dole ne ta taushi dan shi yayi hakuri ko

Please Login or Register in order to submit comment