Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin harshen turanci da irin son girman ta sai gashi Allah ya hada ta Aure da yaro karami kuma Allah ya sanya mata soyayyar shi sosai a cikin zuciyar ta don haka muna musu fatan Alkhairi Allah basu zaman lafiya kuma Allah ya kaimu nan da wata bakwai mu dawo suna,



Ta zauna aka tafa mata kafin A fara fito da Abubuwan motsa baki ma Aikata ne na mu samman na gani Ankwaso daga hotel suke rabon Abin cin,.



Nida na shirya rabo inayi ina zubawa a burgame Amma MOMY tayi mun bakin ciki yaseen,


A can gefe na hango y'an gayyar sodi su hauwa'u u Sulaiman da su Momyn suhaila sun zuba tagumi ga manyan jakun kunan su



Maman uku da ta kafa kafa dani kuwa tana gefe muna mazurai KUSKURE NA fan's kuwa ba show domin taron ba gayyar sodi duk haka muka kwashe muka nemi gudu saboda ba waku,


Meenat sarkin gulma ta maidoni ai wallahi ita gulmar bata isheta ba mu koma sai na gama kwaso musu labari,



A haka aka yi ta ciye ciye ni ko plate din kuli kuli ban samu ba gwara meena da mukhtar ya rage ta sud'e plate din shi,


Bayan Anfara mika musu gift Ruman ta mike zuwa wurin kawayen ta suka rungume juna "Agaskiya Queen Bakida kirki Badan bature ba bazamu San komai ba yanzu Aminci yace haka?


" don Allah Kuyi hakuri bansan taron yakai har haka ba saboda ni Ance kawai za a bude Asibiti ne Ashe su bidi'a suka shirya har haka'


"An bature ya fita Abakin ku kuce Abdullah,ta fada tana zuba dariya " aa kifada ai mungani ya yi winning zuciyar ki kiyi lokacin ki ne


Young crush ya burge ni ya sace zuciyar Queen karamin yaro ya zama babba " banson wulakanci mijin nawa ne karamin yaro to Yama fi manyan mutane in fada muku,


Dariya suka sanya mata Sumy tace Wallahi kedai bari gashi ina Kwasar takaici kinsan inada uwar gida kullum cikin raba miji ni Abin yana damu na,


Hajara takai mata duka "kedai anyi jara batu Wallahi kin shige su " Ruman tasa dariya Ashe Akwai aiki kenan,


Isowar su mukhtar ne da Abdullah yasa su yin shiru "hy my friend's " hello our husband hajara ta fada cikin tsokana


Mukhtar ya zuba mata idanu sai kallon ta yakeyi tun da ya ganta yaji shima fa babbar yarinya yake muradi tunda ya lura Sam mubena bata yin shi,


"Thanks for coming " you are welcome Allah yasa Alkhairi suka furta baki dayan su"


"Abdullah' mubena ta fada cikin wani irin salo tana tafe tana kara'i raya gaba dayan su suka juyo domin zuba ma sarautar Allah ido,


" please inason Muyi magana minti biyu, idanun shi ya zuba Akan Ruman data saki baki har hanci tana kallon sarautar ubangiji,



"Ke baki ganshi tare da iyalin shi bane kike cewa ya zo Kuyi magana? Mukhtar ya fada cikin hasala " and so malam ban kasa dakai ba badakai nake yiba,


Wani irin turirin bakin ciki ne ya turnike ta kamar zatayi ihu hajara ce ta ja hannun ta "Queen muje daga ciki muga yanayin gidan namu,



Dama ta k'agu don haka da sauri ta bisu sukayi cikin gidan batareda ta koma kan kowa ba,


Suna shiga falon ta fisge hannun ta ta nufi kujera ta zauna kamar tayi bindiga


" Sumy ce ta matso gab da ita ta zauna " Queen wacece wannan ? Wasu irin hawaye ne suka zubo mata kamar wuta,..


"Wace ce kuwa bayan sonshi takeyi kuma kuna ganin ina zaiki ta bayan Karamar yarinya ce tafini kuruciya sannan gata fara irin shi


Da na shirya zama Amma yanzu kam tafiya ta zanyi don bakin ciki kashe ni zaiyi inada mugun kishi akan Abdullah is better inyi nisa dashi before I do some thing stupid,


" Ashe Bakida wayo Ruman matan bariki zaki tafi kibar wa mijin ki saboda mugun kishin da baida ma ana ya ce miki yana sonta ne?


"Aa " kinsan cewa mijin ki na matukar kaunar ki me yasa kikeso ki wahalar dashi Ruman please ki barshi haka yaji da Aikin da zaifara ki kama mijin ki gam ki janyo Abinki a jiki Wallahi sai kin bani mamaki Amma idan kikayi sake


Wallahi duk soyayyar da yake miki zaki fita Azuciyar shi yanzu ma na janyo ki ne don k'arki kwafsa kijawa kanki raini domin nasan wannan Yarinyar rashin kunya ne kawai bata wuce eighteen,



"Sun dauki lokaci suna mata hira har saida Hajiya suka shigo sannan ta yi kokarin saita kanta suka zauna suka fara zuba hira,


" yanzu Ummu wannan gida saika ce mutum hamsin zasu zauna kuma duk na mutum daya lallai hadiza ta daure muku maciji Kuyi wasa da kai wannan gini kamar baza a mutu ba,



Gwaggo Amina tayi dariya cikeda jin dad'in jikokin ta cikin jin dad'i saidai su tayasu Addu'ar Allah ya basu zaman lafiya,



Yakuma sa da jinkiri suka Amsa da Ameen "ina Momyn da mama suke hajjo " Ruman ta tanbaya "suna can tareda y'an uwanta daga gani ta fada musu maganar musulun tar ta naga sunata fada duk da banajin ko bihin ai nasan fada,


" dariya suka sanya tare kuma da Addu'ar Allah yasa kar ta bi ra'ayin su ta koma ruwa,



Wayar ta ta fara danna wa tana neman layin shi Amma tanata ringing bai daga ba ita kuwa tuni ta kuma hawa wato suna can suna hira,


Sukuwa tun wucewar su Ruman ya kalle ta " ki fadawa mukhtar koma meye zai fada min he is my best friend sannan ya wuce wurin su Dady ya rungume shi "


I love you Dad " Abdullah kafa girma you are going to be a father in a next seven months


Am still your child Dady may Allah S.W.A bless you for me Tnk you so much ya fada yana hawaye,


"Baban Ruman na gefe yana maijin farin ciki ba Abinda yafi mai Dady irin Ace y'ar shi ta samu kwanciyar hankali a hankali ya furta Allah ya jikan ki Aisha,


Dakina Raye zakiyi Alfahari da yarki na Auren yaron yayanki da ke sonki fiye da kanshi


Matsowa yayi ya gaida baba yasa mai Albarka " Abdullah Allah yasa ku fara a sa'a ya kuma baka hakurin zama da iyalin ka'


Suka Amsa da Ameen "to mu zamu shiga gari munada sauran Abin yi kaga ma a samu bude company ba saboda rashin kammaluwar shigowa da sauran kayan Aiki '


" OK Dady, wayar shi na silent baiji kiran da take yimai ba ita kuwa duk hankalin ta ya tashi tana tunanin cewar suna can tare da Mubena'


Ita kuwa mubena wani irin bakin ciki ne ya turnike ta "Wayar ta ta bude ta fara rubuta mai massage " _Abdullah naso Muyi magana face to face kaki sai gudu na kakeyi to Wallahi yanzu na fara binka and I don't care About your wife "ina sonka Abdullah please give me a chance I will proved my love to you_



Haka ta bar gidan cike da zullumi idan ya ki ta ta shiga uku domin tana mutuwar sonshi kamar ranta,



Mukhtar ya biyoshi " please malam muje kamun rakiya inga Queen of heart dina Wallahi na Afka kafin inyi sake amun sakiya,



"Kai wai tsaya ina zaka kaita tafa fi karfin ka Kasani " Amma kaci uwar rainin wayo j dan ubanka ita wadda ka Aura sa arka ce?


To nima babbar yarin yar ta shiga zuciya ta zanshiga daga ciki inji waye babba ni ko ita "to wai ma intanbaye ka kodai da gaske Ruman tafi karfin naka ne?


Duka ya kaimai " kana hauka ni ai ko mace hudu zan iya da ita bare mace daya "to ka shiga uku jara babbe naji ni ba RAGGON MIJI bane,

MAMAN MAMY shalelen golden godiya dubu gareki,


" nidai muje da Sallamar su suka shiga cikin falon lokacin Ruman ta shiga cikin dakin ta zama sukayi Mukhtar ya zubawa hajara ido da kanta ke kan wayarta tana chart



"Sannun ku Hajiya suka gaida Tsoffin sannan Abdullah yace "friend My friend want to talk to you



Kallon su tayi taga irin kallon da Mukhtar ke mata tayi murmushi domin ta lura da shi tun dazu a wurin taron " OK bani numbar ka zamuyi magana a waya domin tafiya zamuyi yanzu muna jiran Queen ne,



"Abdullah yayi saurin kallon ta ina take ? Ta shiga ciki " mikewa yayi yabi bayanta ya bar mukhtar da zubawa babbar yarinya ido ya kasa cewa tak saboda tayi mugun yimai kwarjini,



A tsaye take ta sauke rigar da ke jikinta daga ita sai tight iya guiwa sai bra ga shape dinta ya fito tsayuwar kawai yayi daga kofar dakin ya zuba mata ido cikeda jin dad'in ganin Matar shi a cikin gidan shi yau kuma har tana nuna mai so,



Kayan da ta cire dazu ta janyo tana shirin sawa ya karaso tareda rungume ta ta baya tareda sauke Ajiyar zuciya,


"My wife ya furta har iskar bakinshi mai dad'in kamshi ta bugi hancin ta gaba daya jikin ta ya gama mutuwa,



Kizo wai zasu tafi yanzu su Hajiya ma na kira driver zai mayar dasu' cire hannun shi tayi tareda da daure fuska ta matsa tareda mayar da rigar ta,


Kallon ta yayi cikin kidima" my Queen me ya faru kuma? Cikin masifa ta juyo batare da ta saka rigar ba kuma bata damu da yanayin da take ciki ba '



"Ka gama hirar da Mubena yanzu kakeda lokaci na? " wace mubena muke hira? Karka rainan wayo Abdul'


Dafe goshin shi yayi domin shi ya ma manta da wata mubena " Ruman please ki daina maganar ta inace nayi miki bayanin ta kuma kina gani ita take biyoni ko'


"To can ya rage maku inna tafi sai ta ci gaba da shige maka I can't take it,
Me kike nufi ya furta yana mai zubawa kirjinta dake cike fam da ido,.


" zan koma Zaria yanzu don haka kaje wurin ta kuji dadin hira har ni zankiraka kusan sau uku baka daga min ba

Wayar shi ya Ciro cikin rawar jiki " oh my god Wallahi nasa wayar a silent ne tun dazu shiyasa banjiba,


Fisgo wayar tayi domin jin wayar tayi karar Shigowar msge ta bude ganin sakon da ya shigo kawai hawaye ne suka zubo mata zurzur tsabar kishi tayi firo da wayar ta tarwatse


Bin wayar yayi da kallo y'anda tayi dai dai kafin ya maida idon shi akanta kuka tasa wiwi yayi saurin Jan baya ya rufe kofar sannan ya dawo kusa da ita cikin rawar jiki " haba Ruman wai meye haka please k'arki daga min hankali mana ina cikin farin ciki



"Kinsani na fada miki komai to me zaisa ki damu kanki ki kwantar da hankalin ki ki tallafi Rayuwata bazan taba iya ci gaba da aiwatar da komai ba idan bakya kusa dani,


Matsawa ya karayi ya shige jikinta " please matana ki daina damun kanki akan wata can'


Juyo ta yayi ya dora fuskar shi a tsakiyar kirjinta yana mai shakar kamshin humrar ta tuni komai ya fara canja mai


Nan da nan yayi connecting din duk wasu igiyoyin wutar dake hade da nata tayi saurin matsawa tareda kuma janyo rigar ta zata mayar ya rike


"My madam me kikeyi haka? Please ki bari mana na gaji kibar ni in samu Hutu a jikin ki kinsan na kwadaitu da ni'imar ki ya furta yana mai kuma shige mata



Bakinshi ya dora akan lips dinta yafara kokarin jefa harshen shi cikin nata tayi saurin janye wa domin wani irin turirin kishi ke dibar ta rigar ta kawai ta sanya taja mayafin ta dankwalin ta ma a hannu ta d'auka ta fita,


" dama ke muke jira zamu tafi kin shige ciki da miji kin manta damu'


Murmushi kawai tayi "muje to na shirya kallon ta sukeyi gaba daya suna mamakin wai su tafi " ke ai kina nan ko? Cewar Gwaggo Amina,


"Aa Amina kafata kafar ta sai ta haihu " kar ki tafi min da mata tazo kenan idan kuma kika tafi da ita Allah zamu bata '


"Ka dade baka bata dani ba dama shiru mukeyi dakai d'an kusun uwa kallon ta kawai yakeyi ta dauke kai "


"Ina dreva mutafi na matsu ingan ni a garin mu Amina muje " Ummu kira dreva mutafi yamma nayi'


"Amma sai munje gidan baba ko? Me zanyi mai muje gida kawai ai mun gaisa,


" tashi kawai sukayi gaba daya ran hajara ya baci domin Ruman nada taurin kai da zai iya cutar da ita zata tafka KUSKURE........✍


_*Kuyi mun Afuwa NEPA na tsiya sunki bamu wuta y'anda yakamata don Allah Kuyi managed"*_



*Matar Soja*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KUSKURE NA🙆*
_Love & Destiny_


_Written by Fenerh_

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*



🅿➡4⃣0⃣

Sunfito yana biye da ita suna shigowa motar baba na sawo kai cikin gidan tare da Dady,


Cikin sauri sukayi parking suka fito "Mama Dama ku zamu d'auka don baba ya tafi shi tun dazu,


" ai gwara da kuka zo domin wannan marar kunyar so yake ya rike min yarin ya kamar bata da gata'


"Haba mama kibar mai Matar shi mana ku zo muje kinga aiki zasu fara kar ku kasa mai hankali kuma Kunsan Aikin shi na bukatar natsuwa,


" to ubana tunda yarinya bata ra'ayi sai inyi mata dole ? "Duk tsawon rayuwar da mukayi mukadai me yasa memu sai yanzu a rika kawo mana salo akan banzar dukiyar ta ku " ke wuce muje kinji'


"Sumy muje ko hajara ta fada cikin fushi ta nufi motar ta batareda ta kalli Ruman ba Sumy ce tayi karfin halin cewa " Hajiya sai kunzo'



Matsawa tayi kusa da su "Wucewa zakuyi kubar ni ? Nifa tare nakeso mutafi daku


" sai kibi su Hajiyar dake daure miki bamu ba ko ki hau taki motar ki kai kanki Amma ba a tamu motar ba "bazan kuma cewa komai ba Ruman ki kalli mijin ki don Allah yana bukatar ki a kusa dashi Amma kina so kitafi ki barshi " duk Abinda ya biyo baya kiyi kuka da kanki '

Fisgar motar ta kawai tayi ta wuce batare da ta kula ta ba bin bayan motar tasu tayi da kallo tareda mamakin irin daukar zafin na su,


Baban ta dai tunda Hajiya ta fara sababi yayi tsit Dady dai cewa kawai yayi "innar mu muje to Gwaggo Amina ta shiga tareda tausaya wa jikan nata saidai kawaici irin nata ta kasa cewa uffan ,



Baba ya kalli driver dake gefe " ita ka kawo ta ya furta tareda kallon Abdullah da kallon tausayi suka shiga mota,


"To Kefa ? Zan shiga tawa Hajiya ai zamu hadu a gidan baba naji yace sai munje can tace to '


Suna wucewa ta nufi motar ta tareda cewa driver muje' " saurin matsowa yayi cikin fushi ya riko ta cikin sauri tare da hade rai " Ruman k'arki bar gidan nan idan har inada hakki Akanki idan kuma kintafi ban yafe miki ba kuma Wallahi zaki gane KUSKUREN ki haba so hauka ne ina binki kina botsarewa sai gara ni kike kamar wani yaronki Wallahi nagaji kuma k'arki sake kibar gidan nan,


Sakin ta kawai yayi ya fita a gidan bayan ya gargadi mai gadin da kar ya sake ya bude mai kofar gate sai da izinin shi tareda Sallamar driver,



Kallo kawai ta bishi da shi cikin mamakin irin birki cewar da yayi domin bata taba ganin fushin shi ba ba tada zabi dole ta koma cikin fushi,



Dakin ta shige tareda kulle wa ta koma kan gadon ta kwanta kawai tana tunanin irin rayuwar da zata gudanar a cikin wannan gidan


Cikin ta ta shafo domin jin yana kugi don Bata wani ci Abin cin kirki ba duk yau dole ta mike ta nufi kitchen dinta da ya gaji da haduwa da kuma kayan Amfani na zamani ,


Store din ta bude kayan Abinci ne birjik komai Akwai ta kalli buhun flour ta fasa ta debo ta dawo firij ta debo kwai ta fasa domin taji tana ra'ayin
Cin wainar fulawa


Ta danyi grinding su tarugu da Albasa sannan ta nemi frying fan ta fara suya bayan ta zuba kayan d'an dano,



Tana suya tana ci saida tayi nak sannan ta wanke Abinda ta wanke duk Abinda ta bata ta gyara wurin tas sannan ta koma dakin domin watsa ruwa tana fitowa ko mai bata shafa ba ta bingire'
Sai bacci,




Abdullah kuwa shima gidan baban ya koma domin Sallamar bakin su y'an uwan momy domin zasu wuce suma,



"Akwai yar kanwar momy mai suna Madonna da ita kawai ta rage domin tace ita zata d'an tsaya kwana biyu domin tana son ganin Jeff a cewar ta don ta dade tana sonshi tun suna UK Amma yaki bata fuska don haka zatayi Amfani da wannan damar ta samu cikar burinta,



Hajiya na ganin shi tace " kai wai ina take nufa zamu tafi? "Bazata jeba ku tafi Abinku ai ni keda umarnin da zan bata ba keba,


" Abdullah" uban ya buga Mai tsawa "kana hauka ne ko uwar mu sa'ar kace da kake fada mata Abinda kaga dama'


" barni da shi d'an wofi ai gashi ga ummun jiki magayi ba yace yaji ya gani ba,



Shidai wucewar shi yayi tareda su mukhtar zuwa Asibiti domin ya fadamai Ankawo wata emagency kuma ana bukatar shi a wurin don haka ya wuce Abin shi,.




Bai dawo gidan shi ba sai dare ya shigo a matukar gajiye bai kai ga hutawa ba momy ta kira shi yazo ya dauki Madonna ta dameta ita gidan shi zatazo


Tsaki yayi kawai ya ce tasa driver ya kawota shi ya gaji kuma yasan Akwai matsala tsakanin shi da Ruman saboda rawar kan Madonna ga Ruman da d'an banzan kishi,



Kallon falon yakeyi batareda jin motsin komai ba kamar ba mai rai a cikin gidan ya mike cike da gajiya ya nufi cikin dakin,



Dai dai lokacin da ta fito daga wanka tana daure da towel iya guiwa sumar ta a jike hannun ta rike da karamin towel tana tsane gashin kanta


Kamewa yayi ya zuba mata ido gaba daya ji yayi gajiyar da ya kwaso ta ware matsawa yayi cikin tafiya a hankali


Ji kawai tayi Anrungume ta ta baya, zabura tayi domin ta tsorata don batasan ya dawo gidan ba,


"Relaxed gimbiyar Abdullah nine mijin ki' Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta b'anb'are hannun shi akan k'ugunta


Binta yake da wani irin kallon kauna da tsantsar sha'awar ta dake cikin jinin shi akoda yaushe,



Juyawa tayi ta nufi Waldrop domin neman kayan da zata sa Mara nauyi, ya zubawa bayanta ido duk ta motsa kafa sai ta motsa da jinin jikin shi domin ta matukar kunno wutar sha'awar shi nan da nan idanun shi suka juya kala,



Wata rigar bacci ta Ciro doguwa mai rubi biyu rigar ta matukar karbar surar jikinta malam Abdullah na tsaye gaba daya ta gama kone mai ruwan kai,


Matsawa yayi kusa da ita" madam fushi kike dani saboda na hanaki tafiya ko? "Ruman kina sona kuwa kamar y'anda kika fada da farko?


Yakamata ki bar duk wani shirme mu rungumi rayuwar dake gaban mu, ya matse ta gam a jikin shi tareda shafo cikin ta " kin ki bari mu natsu bare har inbaki kulawa dake da my unborn child,



Shiru kawai tayi ya juyo da ita suna fuskan tar juna, ta zuba mai ido tana kallon cikin kwayar idon shi'


"Bakada lafiya ne? Shine maganar da ta fara yimai' " eh mana ' Meke damun ka? "Kece damuwa ta Ruman kin sani idan har kin mun sassauci komai zaizo min da sauki"


"Girgiza kai tayi kawai " bari in hada ma ruwa kayi wanka' ta fada still fuskar ta a daure ya saketa cikin jin dad'i yace tanks my wife,



Saida ta hada mai ruwan ta fito tasame shi ya tube ta kawar da kanta ya wuce yana kallon ta, gaban mirror ta matsa ta d'an shafa mai tareda humrar ta mai d'an taushin kamshi sannan ta samu wuri guda ta zauna tareda daukar wayarta ta kirasu hajara,



Har lokacin fushi hajara keyi da ita cikin kwantar da kai ta fara nusar da ita"Queen naso infada miki cewar Anfasa Aure na da sadeq saboda mahaifiyar shi taki y'arda wai na bude ido da yawa sunfi son ya Auri yar secondary'


"Ruman a lokacin nan duk macen da ta samu ta shiga daga ciki ta godewa Allah ni yanzu da ni nasamu irin mijin ki Wallahi ko fita zaiyi sai kabi kaya na Amma ke kin samu dama kina tsula tsiya


Wallahi kiyima kanki fada' Abin ya matukar daga hankalin ta domin ta tausaya wa Amini yar tata don tasan irin son da suke yiwa juna



Fitowar shi yasata yin sallama da hajara tace zasu yi magana da safe , dariya tayi " oh mijin na kusa ne?



Kedai sai da safe "Allah ya zaba miki mafi Alkhairi Besty' tace Ameen,


Tashi tayi ta nufi wurin shi ta karbi towel ta fara goge mai jiki yana binta da kallo kamar zai cinye ta " na canja maka ne?


Ajiyar zuciya ya sauke "aike kullum cikin canji kike wai meke damunki ne ? Yau ki hau hanya gobe ki kauce,


Dariya kawai tayi ya fisgota zuwa kirjinshi yafara kokarin neman bakinta" nidai Aji dani Jan Ajin ya isa ko'



Ya na shirin sa bakin shi Madonna ta fado cikin dakin cikin karad'i "brother" sukayi saurin kallon ta ya hade girar sama da ta kasa'


"Madonna what is this ? Can't you nock before enter ? " oh sorry bro "hy sis in low'

Ta fada tana dagawa Ruman hannu irin na turawa, ita dai ta sankare tana mamakin mai zaisa ta fado musu daki haka kuma ma ba suntafi ba me ta tsaya yi ita ?


Yana rungume da Matar shi still" ya kalleta tareda bata umarnin komawa falo zaizo ya nuna mata guest room,



Sai bayan ta fita ya kalli Ummu "my Queen kiyi hakuri Madonna cousin sister dina ce zata yi kwana biyu a nan kafin ta koma UK,


Shiru kawai tayi domin tasan Akwai matsala zama da wannan dangin yahudawan,



" idan Akwai matsala kifada kawai yanzu insa a mayar da ita wurin Momy?

Saurin girgiza kawai tayi kafin tace "ba wani matsala ita da gidan d'an uwanta' " aa gidan ki ne kinfini mulki dashi my Queen it's your palace'


Da kanta ta nuna mata daki sannan ta bata Abin motsa baki domin Akwai komai na bukata a cikin gidan



Yaji dad'in ganin y'anda ta sake har karfe goma sha daya suna zaune a falon suna kallo tareda hira tsakanin Abdullah da Madonna ita dai tana kallon su



Matsowa yayi kusa da ita "my Queen muje mu kwanta dare yayi mikewa yayi tareda riko hannun ta, ta zuba musu ido tanajin wani iri ace akan wannan mai duhun kan ce ya baro kasar su ya dawo nan gashi batada ko wayewa '


Kallon ta takeyi cikeda hassada har ta mike suka shige ciki jikin shi na rawa, suna shiga ya fara koro zalamar shi a fili cikin rawar jiki ya fara aiwatar da son ranshi,



Kallon shi takeyi cike da mamakin shi y'anda yake aika mata sako kamar zai cinye ta gaba daya yanayin da ya shiga ya tsoratar da ita '


Rike hannun shi tayi dake yawo a jikinta " Abdul " dakyar ya iya Amsata da um' please kabini a hankali mana kana tsorata ni fa'


"To ai kece kullum kafin in samu sai na wahala ya furta cikin rawar murya tuni ta fara bashi taimako ta birkita mai tunani kafin kace mai ya fara shawagi a sararin samaniya ,



Ranar sun murji juna domin tayi na mijin kokari wajen ganin ta gamsar da shi kuma ya gamsun d'ari bisa d'ari wani irin runguma ya yi mata hawaye na zuba mai a idanu tareda rokon ta,


" please my wife k'arki ce zaki tafi ki barni again bazan iya hakuri ba ina bukatar kulawar ki idan kika barni zan iya fadawa halaka don Allah ki cigaba da bani irin wannan kulawar dama haka kika iya birkita mutum amma kike wahalar dani?



Rungume shi tayi itama cike da so domin ji take kaunar shi ta lunku a cikin zuciyar ta


Ranar sunyi kwanan farin ciki w'anda har saida suka makara wurin tashi

Please Login or Register in order to submit comment