Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya k'eru iya k'eruwa duk da yanada k'aran cin shekaru jikin shi na da matukar daukar hankali yanada k'ira irinta zaratan maza



Ga sajen nan nashi irin na gayun yanzu dake kwance Kamar Ana shafa mai relaxer yana sheki'

" Ta dauki lokaci tana karemai kallo yana mai kara cike sauran dan gurbin da ya rage A zuciyar ta,


"Shigowar wata yarin ya budurwa ya mugun daga mata hankali domin Yarinyar tana cikin muguwar shiga ta sanya wasu irin Riga da sket da suka gama bayyana komai na jikin ta,

" Tunda ta shigo gidan idanun ta ya sauka a kan shi direct ta nufe shi tana mai cewa wow wannan irin sabon jinin fa kuma gashi bature,

"Ta fara takawa cikeda y'an ga da kara'i raya


" Hy handsome "Wani irin daure fuska yayi tareda d'an kallon ta kadan irin na reni sannan ya kawar da kanshi

" hy kawai ya furta " jikinta na rawa ta janyo kujera a gefen shi ta zauna kamar zata fada jikin shi,

"Nace ba. "don ALLAH Aunty bilki na nan? Wani irin kallon kin rainamin wayau kawai ya jefeta da shi bai ce mata komai ba,


" Ya d'ukar da kanshi kan wayar shi ya fara danna wa tareda manna ta akan kunnen shi ya fara magana cikin harshen turancin shi mai tsada ta saki baki kawai tana kallon shi gaba daya ya tafi da tunanin ta,


"Ruman na hango komai gaba daya ranta ya gama baci Wato budurwar tashi har cikin gida yake kawo ta lallai,

" Tsananin bacin rai bata San lokacin da ta fita tsakar gidan ba jikin ta na tsuma ta nufe shi a lokacin yana kan magana kawai ganin ta yayi Akansu tana huci'


"Wani irin murmushi ne ya bayyana akan fuskar shi nan take ya riko hannun yarin yar dake gefen shi" um baby muje ko inaso in dan sha iska ya furta cikin wani irin salo tareda kashe mata idanu Wanda ya mugun Jan jinin jikinta


"Ta saki idanu tana mai mamakin bature da hausa rad'au a bakin shi


" Mikewa kawai tayi kamar wata jela Ruman kuwa zuciyar ta kamar zatayi bindiga tsabar kishin da ya tokare mata kahon zuciya,


"Yayi saurin kallon gefen ta da wutsiyar idanu yana mai hango tsananin kishin shi a cikin kwayar idanun ta wani irin farin ciki ne ya rufeshi kamar ya taka rawa don murna,


" Har ya fara takawa ya d'an dawo baya kadan " Aunty na kinga baby ko ? Don ALLAH ki nunamin guest room mu dan huta kadan,

"Ya fada cikin kunshe dariya " cikin tsananin masifa tace " banason raini da iskanci koni sa'ar kace da zaka tanbaye ni wani guest room to bansani ba idan kaga dama ka wuce hotel ku kwana I don't care,

"Yayi saurin taron numfashin ta " really? Amma idanu na sun nunamin you really care,


"Ta zabga mai harara tareda komawa kan Yarinyar ta watsa mata mugun kallo tareda Sakin tsaki mai karfi ta wuce fuuuu kamar iska,

" Wani irin nishad'i ke dibar shi gaba daya damuwar dake ranshi cikin kashi goma yanzu bai wuce kashi daya ta rage ba, tana shigewa yayi saurin Sakin hannun ta' tareda komawa kan kujerar ya zauna,


"Ta kuma biyoshi " muje in kaika guest room din Nasani " ni yar yayar Aunty bilki ce sunana safiyya amma anfi kirana da sopy ,


"Ya d'an hade rai kadan tareda kallon ta " Am shekarar ki nawa kuma? Ta ce Shekarata Ashirin da takwas kaga kuwa zaka samu Abinda duk kake bukata Awurina,

"Hmmm me kikeso dani yanzu'? Ina sonka ne ta fada batareda ko jin kunya ba, to ai kin girme ni sosai ni banason tsohuwa nafison sweet sixteen,


" Nan take ranta ya baci domin ta fuskan ci tsabar wulakanci ne kawai yayi mata" banason rainin hankali kace nayi maka tsufa ita wannan budurwar taka data wuce bata girmeni ba?

"Waye ta girmeki? Ya kalleta sama da kasa duk ta wani k'ode a fuska tsabar bilicin ga wani gashin dokin da ta sanya har duwawu ita Ala dole ta hadu sai wani irin mugun dinkin sket dogo ne har kasa Amma yasha tsagu har zuwa cinya wai musulma,


"Ganin irin kallon rainin wayon da yake mata yasa ta wucewa ciki fuuu batareda ta kuma sauraran shi ba,


Shi kam zuciyar shi na cikin nishad'i sosai da kuma farin ciki'


" Ruman na shigewa dakin ta fada kan gadon tareda Sakin d'an marayan kuka " Ashe haka take da bala in kishi ? Ita kam bazata iyaba wato haka yake ji a duk lokacin da ya ganta da wani, Ashe kishi masifa ne kai ita kam Wallahi zuciyar ta zata buga,


Yana zaune a wurin har mukhtar ya dawo ya sameshi A wurin cikin wal wala,

"Abokina ya nagan ka cikin farin ciki ne? Murmushi kawai yake saki tareda shafo sumar kanshi,

" Shigowar baba ne ya tsayar dasu da hirar da sukeyi, ya iso wurin su cikin fara'a " Abdullah kana nan ? " eh baba zan d'an yi kwana biyu Anan,


"A to hakan yana da kyau bari inturo yaran nan su kaika dakin ka ko.


" ya wuce cikin tsananin farin ciki, Adam ne ya fito yayi musu jagora mukhtar ya kwaso mai kayan da yasan duk zai bukata suka shiga daga ciki gefen baki,


"Tunda tazo ta ci Abinci bata kuma marmarin saka komai a bakinta ba tana kwance a wurin ta kasa ta b'uka komai,


Karan wayar ta ya dawo da ita daga duniyar tunani da kuma damuwa,

Tsaki taja mai k'arfi domin ganin numbar mai kiran bakowa bane face Doctor Sulaiman sai da ya kira sau uku kafin ta yi picking tana d'auka ya sauke Ajiyar zuciya,

" Alhmdulillah farin Cikina ya kike? Ta daure kadan ta gai she shi, hope dai ba na tashe ki Abacci bane?

"Eh, Ruman ina cikin farin ciki sosai A yau, " Meka samu ? Na samu Abinda yafi komai muhimman ci A wurina wato burin raina,

"Meye wannan Abun? " kece Ruman iyaye na sunje har An karbi gai suwa na kuma rokesu banason Auren mu ya dauki lokaci nima A matse nake kamar Amarya ta,

"Tunda kin Amince banason A dauki lokaci gwara A shafa kawai in mallake ki gaba daya,

" Ai gaba daya jinta dauke wa yayi na wucin gadi har wayar ta kubce a hannun ta batareda ta shirya ba,

"Gai suwa ita da Doctor Sulaiman? Kirjin ta na mugun duk'a ta sulale ta sauka kasa zufa ya fara tsiyayo mata Ako ina na jikin ta,


" na shiga uku ni Ummu Ruman ya zanyi da zuciya ta? "Yau she ta y'arda da zancen Auren shi da har zai tura iyayen shi batareda Antanbaye ta ba zasu k'arbi zancen Aure,


" Wallahi da sake " kirjinta ya kara bugawa lokacin da ta tuna da Abdullah duk da ya juya mata baya Amma ita tasan bazai taba daina sonta ba,


"Sopy kuwa tana shiga side din Aunty bilki ta wurgar da jakar ta ta Afka har uwar daki bako sallama ita kanta ta tsorata da ganin ta kamar guguwa,


" Ke lafiya daga ina haka? Wai sai yaushe zaki yi hankali ki kuma natsu, "sai ranar da kuma kukayi hankali tunda kuma ai bawai tarbiyyar ce da kuba kuma muma y'ay'an ku a wurin ku muke koya,

" To Mara kunya naji kimun shiru tunda ke Bakida ta ido,

"Nidai Aunty bilki wane yaro ne wannan baturen? Ta yatsune baki " ke ina ke ina wannan kanin bayan naki kuma?


"Nidai ki fadamin kawai " to d'an uwan baban Adam ne a ina kika ganshi?


"Yana harabar gidan Amma mugun d'an wulakanci ne Amma ban damuba tunda na dora idona Akanshi to ko sai nasamu biyan bukata ta koda ba zai Aureni ba sai mun hole na dan lashi sabuwar zuma ,


" ke dai Wallahi bakida, hali kullum kina nan kamar karya akan zancen maza sai sun hade miki gaba da ta bayanki zaki natsu,

"Aniyar ki ta biki tunda ke bakiyi ba nima bazan taba samun hakan.... Ya isa fitsararriya tashi ki wuce na gode,

" Ai Wallahi bazan tafi ba ni yunwa ba nikeji'

"Bari insa Abaki Abinci kici kinsan baban Adam ma gari don haka kibar gidan nan tun bai ganki ba,


" mijinki ya cika matsala Wallahi Aunty kawai daga yaga ina shan shisha zai wani tsane ni don ma bai ganni da mai karfin doki ba,


"Tsaki tayi ta mike da kanta ta wuce tareda kawo mata,Abincin kala kala har da exotic juice na kwali ta Ajiye Mata,

Saida ta cinye tas ta shanye juice din sannan ta mike ta tafi,

sai baza idanu takeyi A harabar gidan ko zata ganshi Amma bata ganshi ba A dole ta wuce ba tareda taso hakan ba,




" Har karfe goman dare Ruman na zaune ga Abinci an Ajiye mata ta kasa cin shi Baban ta ya leko sau biyu yana tanbayar ko lafiya take?

"Tace lafiya kalau tana karatune bayan gaba daya hankalin ta a tashe yake har ta matsu gari ya waye ko zata koma Zaria taje taji mai ke faruwa?


" Shi kuwa Abdullah yayi bacci cikin farin ciki domin jin shi yakeyi kamar Anyi mai bu shara da Auren ta,


"Dakyar taga waye war garin tana idar da Salla ta hada kayanta domin batajin zata iya kara kwana daya A Kaduna,

Burinta kawai ta ganta gaban Hajiya domin ita ce kawai zata bata Amsar da take bukata,


" Kicin ta fada da kanta ta hada break fast domin taga Alamar Matar gidan sarauniya ce, ta gama shirya komai ta Ajiye musu dakyar ta d'an sha ruwan tea duk ta k'osa baban ta bai fito ba




"Sai karfe takwas suka fito Alokacin tana zaune A falon Baban ta cikin fara'a ya karaso " Ummu har kin tashi?


"Eh ina kwana Baba? " lafiya lau ya bakunta ?

"Lafiya kalau, ga Abinci A table na shirya, ya fadada fara'ar shi " To keda kanki ina lamin take ?

"Ina so inyi ne shiyasa kawai nace ta huta, " OK to kin kaiwa d'an uwanki?


"Ai su ma basu tashi ba, Abdullah nake magana yana guest room ki shirya mai shima,


" Tace to ta mike jikinta A sanyaye tana son ganin shi Amma idan ta tuna da zancen Sulaiman sai hankalin ta ya tashi ya zatayi da rikicin Abdullah?


"Ta shirya mai komai ta dora a tray ta nufi hanyar da take tunanin yana ciki,

Sallama ta fara yi taji shiru sannan ta tura kofar ta shiga

Daddadan kamshin shi ne yayi mata welcome ta ware idanu tana mai duba ta ina zata ganshi ko ya fita ne?


Ta ajiye tray din kenan ya fito daure da towel a kugun shi sai da gabanta ya fadi ga wani irin bugawa da kirjinta keyi na ganin shi ba kaya Ajikin shi,

" sumar kirjin shi duk ta wani kwanta saboda ruwa ta fara zare idanu ganin irin kirar halittar shi a bayyane gargasa ko ta ina har akafar shi da kuma Hannayen shi wani irin tashi tsigar jikinta ta fara yi,


"Shikuwa yana fitowa idon shi ya sauka akanta tayi mugun tafiya da tunanin shi cikin shigar zani da Riga ga rigar ta kamata daf a jiki komai ya bayyana ya fara bin jikinta da kallo tundaga kasa har saman ta,


" idanun shi akan hip's din ta da yafito cikin single zanin da ta daura ga kuma k'irjin ta fam kamar sa faso Riga,

Ita ta fara dawowa cikin hayya cin ta tayi saurin kallon shi dakyau ganin irin kallon da yake jifar ta da shi ta kalli jikinta tama manta Sam ba hijabi ajikinta tsabar damuwar da take ciki,


Tayi saurin juyawa zata fita, dakyar ya janyo numfashi ya nufeta cikin sauri tareda riko tsintsiyar hannun ta,

Tayi saurin juyowa tareda watsa mai idanun ta da suka kara rikita mai lissafi jikinshi na rawa ya kara narkar mata da idanun shi A cikin nata


"Anan yake kara aika mata da sakonni masu wuyar fassara,

" Tuni jikinta ya mutu murus ta kasa koda motsa dan yatsan ta ga wani irin feelings dake saukar mata ta hanyar riko hannun ta da yayi da Hannayen shi masu mugun taushi,


Ya kara matsowa idanun shi a cikin nata dakanshi ya kara turata jikin kofar tareda riko kugunta da Hannayen shi duka biyun


Ya manne Ajikinta kamar wani magnet, Atare suka sauke Ajiyar zuciya

Wani irin shocked yakeji a cikin jinin shi nan take ya,fara fitar da wani irin mugun numfashi,


Bakinshi dai dai kunnen ta yafara magana Ahankali yana mai busa mata iskar bakinshi dake kara zuke ruwan jikinta


"Stop please Abdul..

Ta furta dakyar ta fisgo maganar,


" what? Menayi kuma?


"Ta kasa bashi Amsa domin bai fasa Abinda yakeyi ba hannun shi na kan West dinta still


" Nayi laifi ne Aunty na?

Wani irin fisge jikinta tayi domin ta tsani kiranta da yakeyi da Aunty

Jikinshi na rawa ya kuma fisgo ta zuwa jikinshi


Don't please,

K'arki fara raba gangar jikina da naki idan har sun hadu .
Ya furta cikin rada

"Yadan dawo da fuskar shi akan tata ya fara shakar numfashin ta yayi kasa da idanun shi zuwa saman rigar ta da yake hango dukiyar fulaninta ya ja mugun numfashi tareda Addu'ar ALLAH ya mallaka mai su zai more,


" kokarin ture shi take karayi Amma yaki Sakin ta kokarin hada bakin shi kawai yake yi da nata


"Ka daina kaga kai ba mijina bane mijina na Zaria kuma kaima budurwar ka na nan don haka ka sakeni,.


Wani irin cafka ya kaiwa bakinta da sauri yayi nasarar cafko harshen ta ai tuni ya matse ta gam a jikin kofar ya fara tsotsar ta da saurin shi yana Sakin numfar fashi masu wuya,

Saida ya dauki lokaci yana tsotar lips dinta tuntana mutsu mutsu har jikinta ya saki ta kasa koda motsa dan yatsanta gaba daya ya gama kashe mata lakar jiki,


Saida yaji numfashin shi na fitowa dakyar ya iya Sara ra mata ya zare bakinshi ya kara shigewa jikinta tareda janyo hannun ta ya dora akan kugunshi

" please hold me. Ya furta dakyar.

Idan baki rikeni ba zamu zube akasa kin kashe min kuzarin jiki yau bazan wuni da lafiya ba Tunda har kika motso min da kwantacciyar damuwa ta

"Ina mafarkin kasan ce war mu A tare a gadon Auren mu bazan iya cire ki a zuciya ta ba Ruman kin zama jini da ruwan jikina idan baki Acikin duniya ta my life is useless please don't leav me,


Dakyar take iya tsayuwar ta d'an rungume shi kadan domin ya mugun bata tausayi domin tasan idan har yaji zancen Sulaiman Akwai matsala ita kanta hankalin ta A tashe yake


Sai kara shige mata yakeyi Kamar zai shige jikinta yana fitar da Ajiyar zuciya


Sai da taga lokaci na tafiya ta fara ture shi daga jikinta


Ya dan saketa kadan tareda sauke idanun shi akan towel din shi dake kokarin kwance wa sakamakon Hajiya babba data kunburo tanason yimai tonon silili ya d'an runtse idanun shi yaja da baya tareda datse kofar ya juya rike da key din,


" dakyar ta gyara tsayuwar ta ta kalleshi da idanun ta da suka k'ank'ance

"Ka bude min kofa zanfita Zaria nake son zuwa,
.
" ta wani irin juyowa

Oh kinyi missing samarin ki ko? Ya fada yana hada fuska

Ni kiyi zaman ki Anan kawai me zakiyi a Zaria hankali na yafi kwanciya idan ma Hajiya ce zanje in dakko ta

Karatun ki ne kawai kuma matsalar " tank god kina last year da kin gama zan fadawa baba ya dawo dake KD


"Ta kalle shi cikin matukar mamakin shi har ya gama fushin kuma ya dawo hanya,


" Fuskar ta ta hade ta kalle shi " akan me zan dawo Kaduna?


Saboda nan nake bukatar ganin ki,

Kaine wa?. " w'anda kike so,

" ni na fada maka ina sonka?

"Idanun ki sunfadamin haka harma da gangar jikin ki Akwanakin baya duk lokacin da jikina ya taba naki bakya karbar hakan Amma ayau naji canji sosai da ni kadai nasan me naji..........✍



*Matar Soja*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KUSKURE NAπŸ™†*
_Love & Destiny_

_Written by Fenerh_


✍✍✍✍✍✍✍✍
GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION.
✍✍✍✍✍✍✍✍

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


πŸ…Ώβž‘1⃣7⃣

Wani irin kallon da take jifan shi da shi ya kara tun zura zuciyar shi zuwa ga shaukin ta,


"Kok'arin dawowa yayi shi Sam ya manta da yanayin da yake ciki burin shi kawai ya jishi A cikin jikinta bayaso su rabu koda na minti daya ne,

Saurin ja baya tayi ta hade rai " ka bude ni infita inaso inje da wuri'

Amma ai nace ban y'ar da ba ko.

To ubana saboda kana waye da zaka hanani zuwa inda nake so,

"Saboda ina d'an uwanki yayan ki kuma mijinki uban yayan ki watara na da izinin ubangiji,

" Harara ta kuma jefamai banason rainin wayo ka bude ni nace ko'

Zaro idanun shi yayi waje " Aunty tun yanzu kikeso in budeki?

To aini banida matsala dama mai neman kuka bari kigani ma, ya fara matsowa yana kokarin kwance towel din dake daure a jikin shi

Wani irin zabura tayi ta runtse idanun ta gam tareda fara masifa

Banason iskanci Abdul ni ba haka nake nufi ba ka budemin kofa nace infita,


Numfashin shi taji gab da fuskar ta " oh come on Aunty na ki bude idanun ki me zaki gani da zai tada miki hankali ni da ban gama girma ba ma kinfa sani ban gama balaga ba ai ko?

"Nidai don girman ALLAH Abdul ka bari' wata irin Ajiyar zuciya yayi

" Say it again please I like it call me Abdul please""


Tayi saurin bude idanun ta ta kalleshi gab da ita idanun shi duk sun juye

Aranta take mamakin karamin yaro da shegen rashin kunyar tsiya,

"Ko me yasani a game da rayuwar Auren ma oho?

Ita dai tasan ALLAH ya jarabceta da muguwar soyayyar shi da batasan lokacin da ta shigeta ba,

Kuma tayi mata mugun kamu,

Aunty na" ya furta da k'yar ki jirani inshirya muje tare tunda kinason zuwa yanzu ki bari muci Abinci tare please na manta ranar da na zauna naci Abinci da kyau kiyimin Alfarma don ALLAH.


Matsawa kawai tayi kusa da tray din ta fara hada mai shayi " kake ka sa kaya tom,
.
Yayi murmushi sannan yace " toh Aunty na,

Banaso" meye bakya so? Bansani ba, ya dan d'ara kadan ya Sosa kanshi domin ya lura batason yana kiranta da Aunty,


Ya wuce Abinshi ya janyo wata Leda mai dauke da kaya d'inkakku masu shegen tsada da kuma kyau


"Ya Ciro wani material milk colour dinkin matasan yanzu ta juya mai baya domin tasan Abinda yake shirin yi


" ya zura wandon shi Sannan ya sanya farin singlet ya dawo kusa da ita ta gama hada komai a plate ta turamai Irish da kuma kwai gefe ga tea mai kauri da toasted bread


Ya riko kafadun ta ya zaunar da ita a kan daddumar dake shinfide akasan dakin shima ya zauna kamar zai shige cikin jikinta tana shakar tsadadden kamshin shi da ya gama wanka da shi,

Ita dai wannan kamshin na mugun tasiri a hancin ta ya sanya fake ya debo Irish da kuma kwai ya nufi bakin ta dashi,.

Tayi saurin dauke kanta " ni fa nakoshi kaci kawai .

Ashe kuwa bakyaso inci kenan ya fada a shagwabe domin yau ya samu damu sosai a wurin ta,

Ita ma kamar wani sihiri ta biye mishi yau kwata kwata ta kasa sarrafa zuciyar ta ,

Ta karbi fake din ta ci kadan saboda ya debo da yawa sannan ta Ajiye sauran

Saurin d'auka yayi ya cinye sauran tareda lashe fake din ya kuma debo wani ya mika mata a haka suka danci Abincin sosai kuma duk ta rage sai ya cinye ya kuma lashe cokalin,


Yana maijin dad'in yanayin sosai ji yake dama su dawwama a hakan Amma ina yasan halinta ko tayi kamar ta saki jiki Anjima kadan sai ta botsare kuma,


"Sai da suka kusa cinye wa saboda ita kanta Akwai yunwa a cikin ta sosai don jiya Sam ta kasa cin Abinci sosai,


Ta yunkura zata mike yayi saurin riketa " ina zakije?

Zan sallami Baba ni zantafi yanzu" ya marai raice fuska kadan,

Wallahi kinaso A wayi gari aganni gawa Roman ke Sam baki damu da damuwa ta ba kinsan irin damuwar dake cikin zuciya ta kuwa?


Matsaloli sun yi min yawa ga Momy na sannan Dady na yanaso inyi mai Abinda bazan taba iyawa ba A Rayuwata

Sannan babbar matsala ta yanzu kece" Roman kece babbar damuwa ta kece matsalar Rayuwata ki tausaya min na gaza hakuri na ya kare


Wai don ALLAH menene Aibuna?


Kokarin matsawa ta farayi domin yau yanaso tayi Abin kunya don yana gab da sata cikin mugun yanayin da gangar jikinta bazata iya d'auka ba,


Ya kara manne mata Ajiki " please Roman horon ya isa haka bansan wane irin Jan Aji bane wannan ni nasan kina sona ki y'arda kawai Muyi Aure ko ma samu kwanciyar hankali gaba daya,


Wallahi Aure nake bukatar Muyi kafin inrasa lafiya ta da kuma Rayuwa ta gaba daya kwanan nan ni kadai nasan irin wahalar da nake sha saboda ke


Me yasa banajin hakan a sauran mata? Meyasa ke kadai nake son kasan cewa da ita kece kawai burina kece kawai mafarkina kece kawai nake so ki soni ko da kadan ne Wallahi ba zancen raini a cikin soyayyar mu ba haramci a ciki


Wani iri takeji a cikin jikinta a hankali ta samu damar mikewa " muje zarian mu dawo, kawai ta iya furtawa


Ya mike ya kalle ta" zaki Amince min Muyi Auren ?

Kazo muje nidai tom" OK ya furta a kasalance ya dakko rigar shi ya zura ya dauki key din ya bude ta ya kwashi wayar shi tareda daukar agogon shi ya daura ya zura takalmin shi ya kara fesa turare sannan ya kalle ta


"Aunty na nayi kyau?

Kallon shi kawai tayi tayi saurin fita yana biye da ita a baya yana bin jikinta da kallo tana kara tafiya da ima nin shi,


" ji yake kamar ya turmushe ta ya cire Abinda ya dunkule mai a Mara da dadewa,


"Suna shigowa Baba ya gansu cikin jin dad'i ya kalle su " aa Ummu a she kuna tare na duba ban ganki ba inaso infita


Abdullah ya fara gai sheshi cikin jin kunya " Abdullah ya Bakunta?


Ya Amsa a hankali, Ummu ni zanfita sai gobe zaki koma ko?


Tace "aa yanzu zamu tafi da Abdul"" yayi saurin kallon ta domin yana son y'anda take kiran sunan shi


OK toh ba damuwa idan kin tafi weekend zan zo in kuma dakko ki ko?

Ya zaro ATM ya mika mata yace " ga Wannan serving account dina ne ki rike A hannun ki idan kina bukatar kudi kafin in bude miki naki"



Lallai ma baban Adam wato tun yanzu ka fara nuna banbanci ko to ba komai kuje kaida ALLAH,

Dukansu suka juya tareda kallon ta


"Wai bilkisu yaushe ne zakiyi hankali ne? Aa a turu aka kwantoni karewar rashin hankali ka dai shirya Gaskiya malam,


Yanzu shekara nawa kukayi ke da yayan ki kuna cin kudin don kawai na bata dan wannan zaki nemi ki tayar min da hankali to kije bazan yi Adalcin ba tunda ke Adalcin kike yiwa kanki,


Abdullah ya kalle shi" Baba ka karba kawai basai kayi wahala ba zan rika bata duk Abinda take bukata,

Aa Abdullah fita hanyar ta kawai kuje ALLAH ya kiyaye hanya,.


"Ran ta yayi mugun baci domin ya y'ar fa ta a gaban wannan shegiyar y'ar tashi,

Duk sai tayi maganin su ta raya A zuciyar ta,


Ruman dai kayanta kawai ta dakko ta yafa katon gyale akanta ta fito rike da wayar ta a hannu,

." mama na tafi ta ce ma bilkisu " wani irin harara ta zabga mata batareda ta Amsa ba ta wuce Abinta, Abun ya kona mata zuciya Amma tasa Aranta sai ta saita Matar nan kuma duk sati sai tazo gidan taga tsiya ita da gidan ubanta,


Tafito tana takawa Ahankali cikin tafiyar ta mai bala'in daukar hankali saidai tana fitowa taja tai turus ganin wadda ke tsaye a jikin motar Abdullah, wato sopy,


"Ta sanya wasu Riga da wando da sukayi mugun d'ame ta kamar wata tsohuwar karuwa,

.nan da nan zuciyar ta ta fara turiri ta rataya yar Karamar jakar ta ta nufi hanyar fita kawai batare da ta kuma kallon su ba yana lura da ita tun Fitowar ta ya zuba mata idanu ji yake kamar ya ruga da gudu ya sunkuceta batareda tasha wahalar tafiya ba,



Amma ganin ta nufi hanyar waje da sauri ya fisgi motar shi tareda bade ta da kura ya bi ta a baya,


Tafiyar ta kawai takeyi batareda ta saurare shi

Please Login or Register in order to submit comment