Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gilashi saikace wasu gasassun kaji'


Dariya kawai suka sanya har da Abdullah dake shigowa" ALLAH ya taimaki ran tsofaffi "kaima ALLAH ya taimake ka shaki yai kawai idan kuka maza iyayen ku zaku jama wa don yanzu sai mu tada balli muje gidajen mu zamuje'


Hmm gidajen da duk an siyar ai dama Plan su Dady suka hada muku bazaku koma ko ina ba,


Kabari d'an manzo d'an nan? Ya kyal kyale da dariya ganin irin zaro idanun da Gwaggo Amina tayi ' to wallahi yaya bazan y'arda ba haka kawai Ai d'an ki na zuwa yau ki fada mai na gama zaman gidan nan mutum ba cas ba as ina zan iya,

Kedai bari Amina ko shara saidai kullum wa innan masu guntayen sket din kullum keyi wai ni Abdullahi bazaku yi musu fada ba surika sa suturar Arziki?


" koda yake kuma ai turawan ne uwar... Hajiya mun dawo fa dama mun shigo ne mu fada miki k'arki yi tunanin muna waje'

Ruman tayi saurin kwabar Hajiya don tasan sarai me zata fada akan mahaifiyar shi bayan yana wurin kuma uwa uwa ce,


Yayi murmushi kawai don shima yasan kwanan zancen sannan ya mike " ni dai zanje in kwanta "Aunty let's go'


" Aa ba wani Aunty ka zauna Muyi hira kafin magaji ya shigo shima tunda ya samu ya fita yaki dawowa'

Ita ma mikewar tayi " Nina tafi kakus inada Abin da zanyi kafin inje school gobe in kwashi zero,


"Ku sauka lafiya" ta fita domin shi ya dade ya ficewa " ta fito cikin takunta Anatse kawai ji tayi ya rungume ta tsam har ta danji tsoro kamshin turaren shine ya sanar da ita waye'


Ya manna mata kiss a gefen wuyan ta saida tsigar jikinta duka ta mike " muryar ta a dakile "baka shiga cikiba?

Ya kuma manna bakinshi akan chicks dinta yana kara narkar mata da duk wani sauran kuzarin da yayi Saura a jikinta" ya zan tafi bayan baki fitoba ai kona shiga ciki zan kasa sukuni ne kawai muje kibani Abinci ko zan iya ci na dade banci wani Abincin kirki ba'


Ta d'an kwace jikinta kadan jikinta a matukar mace a zuciyar ta take fadin " wannan yaron ya faya son jiki'


Tayi gaba shima yana biye da ita Kamar wani jela,


Rike hannun ta yayi ya nufi hanyar dakinshi da ita " dan ja ta tsaya " mu zauna a falo mana bai dace ba mu shiga cikin daki,


"Ya kalleta wani iri " kinaso Dady ya gan mu ne atare? Tayi saurin girgiza kai " OK muje tom,


A kasan dakin ya sanya dadduma tareda jera plate da kuma ledar da ya shigo daita dazu ya kuma bude fridge din dake cikin dakin ya dakko fresh milk ya ajiye musu,


"Ya riko hannun ta ya zaunar da ita a kan Capet din sannan ya cire rigar dake jikinshi ya rage dagashi sai dogon wando da kuma singlet kawai,

Ya tankwashe kafafu a gaban ta " Aunty ki bude mana naman ko'

Ta d'an harare shi" kadaina cemin Aunty please " OK my Baby"

Ta kuma Harar shi ' nice baby? " na shigesu to ya kikeso in kiraki?

"Kace Ruman ko Ummu kamar y'anda Hajiya kefada,

" Hmm u are special to me so Dole ne ma in zaba miki special suna


"Da kanshi ya Ciro musu naman a cikin poilpepper yana nan da zafin shi ya juye akan katon plate din tangaran ga gashin ya gasu harda wani source din cabbage da Albasa da kuma kayan miya a gefe wow"


_A Gaskiya raina ya biya🀧_


Ya sanya fake ya dibo tsokar tareda nufar bakinta da shi' tayi saurin kawar da kai " zanci da kaina kaima kaci naka'


Hmm ki cigaba da mun wayau da munyi Aure bazan y'arda ba don kiji,


Saida sukaci suka koshi sannan ta zuba mai coffee ya fara sha ita kuwa ta tsiyaya fresh milk kadan a cup ta fara sha a Gaskiya ta dade bataci Abinci irin na yau ba,

Yana seeping coffee A hankali yana binta da kallon soyayya da kuma imaging inama ace Andaura musu Aure ne A yau da Gaskiya bazai bar wannan daren ya tafi a banza ba,


"Don idan ALLAH ya mallaka mai ita to burinshi na duniya ya gama cika,


Ta Ajiye cup din tareda kallon shi ganin ga badaya ya Ajiye cup din hannun shi ya zuba ta gumi yana Kallonta'


" Abdul lafiya ? Me kake tunani haka? Ke nake tunani " bayan gani a zaune akusa da kai,.

"Ina mafarkin ranar da zan mallake gaba dayan ki ranar zan iya bacci kuwa saboda tsananin farin ciki?

Me zai hanaka bacci? Murna da farin ciki na mallaki Matar da nake so " ai ko yanzu ka mallaki ni'


"Da Saura tunda bamuyi Aure ba " I want to see you as my wife Ruman shine mafarkina,


Mikewa tayi " zanje inkwanta bacci nakeji ta duka tareda kwashe plate din da suka bata " saurin karba yayi ya Ajiye '


"Wa yace ki wahalar min da kanki ? Kibarshi Mary zata kwashe su,


" ta juya zata fita domin taga irin kallon da yake mata kamar zai lasheta,


"Yayi saurin rikota " ta runtse idanun ta domin tasan za arina "Abdul ka barni in wuce bacci nakeji'


" k'arki tafi don ALLAH bangaji da ganin kiba " dare yayi, " ki kwanta Anan ga gado please " ya dora habar shi akan kafadarta ya hade Kansu wuri daya,


"Idanun ta ta zaro duka waje tareda kokarin raba jikinsu ya kara damke ta ta hanyar sanya Hannayen shi duka biyu a west dinta yana lumshe idanun shi domin jin dad'in yanayin da yakeji"


Numfashin da yake saukewa awuyan ta bakaramin daga mata hankali yake yiba ta fara kokarin kwace jikinta domin yayi sanadiyyar jefata cikin mugun yanayin da ta dauki lokaci bata shiga ba'


"Please Abdul ka daina" ta fisgo maganar da kyar "menayi ? Shima ya bata Amsa dakyar still yana nan manne da ita kamar chewingum,


" Ruman stay hare with me please " banaso kije ko ina inaso inkwanta a kan jikin ki mai laushi kamar y'anda nake gani a mafarki na idan kin barni yau bazan iya bacci ba bayan yanzu zuciya ta ta gama yadda da cewar kinaso na,.


Kasan hakan bazai taba yuwuwa ba,

Ko Aldarmu bai dace ba bare kuma A addinan ce, ta fada cikin karfin hali tareda cire hannun shi a jikinta ta nufi dakinta da sauri tana jin wani iri a cikin jikinta,


Bathroom kawai ta fada batareda ta tsaya tubewa ba ta sakarwa kanta ruwan sanyi har saida tayi Ajiyar zuciya,


Saida ta dade a hakan kafin ta fito ta tube kayan da suka jike sannan tayi wanka mai kyau tareda dauro Alwala,


A haka ta samu ta yi sallar isha tareda yin nafila raka'a biyu.


Tunda ta fita ya koma gefe kawai ya dafe kanshi bayaso tayi nisa dashi koda na minti daya ne burinshi kawai su kasance tare har Abada,


A ranar dakyar bacci barawo ya daukeshi ita kuwa kwana tayi tana saka da war wara,

Har cikin zuciyar ta tana kaunar shi Amma Sam batason yawan taba jikinta da yakeyi tasan sai tafi cutuwa saboda irin lalurar da take damun ta ta wani gefen kuwa tana ganin laifin kanta da kuma jin kunyar Abinda ke faruwa a tsakanin su wane irin Abin kunya ne zuciyar ta takeson ta jefata a cikin shi?


Son kanin ta kuma har takai ga furta mishi hakan kuma shine dalilin da yasa yake kara shige mata tareda kokarin jefata cikin mugun yanayi,


A Gaskiya da zuciyar ta zata yimata Adalci da ta cire mata soyayyar shi ko zata samu ta tsira da d'an sauran mutumcin ta, Amma kuma Abdullah fa?


Taga irin farin cikin da ya shiga sakamakon bayyana mai irin soyayyar da take mai sai Alokacin ta tuna da wayar da ya siyo mata takuma kalli gefen kayan da ya tilo mata tsabar farin ciki,

Wani irin tausayin shine ya kuma ratsata tasan duk ranar da aka daura mata Aure da wani sai ya fita shiga tashin hankali,



Ranar bacci kaurace mata yayi ta tashi tareda shirya kayan A cikin Waldrop tayi plugin wayarta a caji sannan ta fara jero nafilfili tareda neman zabin ubangiji,



"Saida tayi sallar Asuba ta mike domin Sam batajin bacci ta gyara dakinda take tsab ta baza kamshi kota ina sannan ta nufi kitchen ta samu Mary harta fara aiki ta fara taimaka mata suka hada lafiyayyun dishes karfe bakwai sungama komai tafito tana mai bin kofar dakinshi da kallo,


" Wannan Ajebon ko yatashi ? Take Ayyana wa a zuciyar ta ' kawai ganin shi tayi Agaban ta yana numfashi sama sama ga zufa na tsiya ya a jikinshi yana rikeda gorar ruwa jikinshi sanye da y'ar Karamar riga Armless da kuma tree quarter kafar shi sanye da canvas ta waro ido waje " daga ina haka?


Bakya ganine daga jugging morning exercise ta d'an tabe baki ta kauce ya d'an bata fuska ki tsaya mu gaisa to ko kinaso inrungumo kine kowa ya gani'

Tayi saurin tsaya wa tareda kallon shi " ya marai raice fuska " nidai Gaskiya banga Alamar na shiga cikin zuciyar ki ba irin wannan rashin kulawar banason shi ya kamata yanzu da kika ganni kidan rungumo ni inji dumin jikinki Amma now look ko gaisuwa bamuyi ba kike kokarin guduwa,



"Shigowar Dady ne ya hanata bashi Amsa tayi saurin yin gaba " Dady ina kwana " lafiya kalau Ummu ya bakunta hope bakya samun matsala da hause help din ko?

Ba komai Dady, ya karaso shima tareda gaida Dadyn " Good morning Dady ya furta cikin daure fuska Alamar yana fushi da uban ,


Morning ina fatan ka shirya tafiya Kadunan ko? Yes wanka zanyi inyi break fast sai in wuce " OK that'good.


Ya wuce ciki ya waiga ko zai ganta Amma tuni ta gudu abinta ya girgiza kai kawai tareda yin kyakkyawan murmushi ya wuce shima nashi dakin cikin sauri yake shirya wa,


Masha ALLAH shine Abinda na fara furtawa lokacin da ya fito cikin wata irin sky blue din shadda sabuwa dal tana sheki Anyi mata dinki na yayi da yaji aiki mai kyau kafar shi cikin takalmi mai kyau baki ga Agogon Rolex sai sheki yakeyi yatsun shi kuwa wasu irin Azurfa ne manya na maza masu tsadar gaske sumar kanshi ta kwanta tana sheki ya fito kamar yaune za a daura musu Aure'



Falon yatsa ya yana karewa kofar dakinta kallo tareda kallon Agogon hannun shi karfe kusan takwas,


Dakin ta ya nufa kai tsaye ya shiga batareda ya jira komai ba " subuhanllah. Shine abinda ya furta yayi saurin jingina da bango,


A tsaye take gaban mirror tana shafa mai a jikinta towel ne iya kar shi guiwar ta ta dora kafarta daya akan stool gaba daya cinyoyin ta a waje suna zuba sheki gasu masha ALLAH,



Sulalewa kawai yayi ya nufi falo ko karyawa bai tsaya yiba ya kira driver yace yayi driven dinshi don bayajin zai iya tuki a halin da yake ciki domin idanunshi sunyi mugun ja tsabar fitina irin ta yaran zamani'


Sai bayan fitar shi taji kamar motsin Shigowar mutum tayi saurin wai gawa bataga kowaba ta cigaba da shirin ta,




*Ya labarin sopy*
Washe gari bayan ta dawo ta tarar baya nan lokacin sun dawo Zaria tayi bakin cikin rashin samunshi da batayiba ta tsaya tana cizon yatsa,


"Waini Aunty wannan budurwar kyakkyawa da nagani a nan gidan fa?


Yarin yar baban su Faisal ne da uwarta ta mutu ta barmin damuwa gashi nan tun ba aje ko inaba tafara zamar min matsala,


Shikuma handsome fa" Saunawa Zanfada miki dangan takar su ? Don ALLAH ki barni da tawa damuwar da nayi nasarar rabasu da shegiyar uwarsu yanzu komai ya lalace mun gashi malam yace Asiri bazai kuma aiki a jikinshi ba,


"Ga Shawara Aunty inada wani boka ki bude Aljihun ki kiga aiki da cikawa tayi saurin rikota " da gaske? ALLAH Aunty " to yanzu' kamar nawa zam bayar ?

Ko dubu Dari ki bayar zuwan farkone idan naje sai Muyi jinga dashi,


"Har dubu Dari Aikin da tsada Gaskiya bazan iya ba " ta mike tareda kakkabe rigar ta " to ke kika sani ni ina ruwana kinganni nan aiki zanje amun muna nan zakiga bature na yadawo kisa idanu kisha kallo ke kuma bakin ciki ya kashe ki.........✍



*kash wallahi to type is not easy my fan's please managed*


_*Matar Soja*_
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KUSKURE NAπŸ™†*
_Love & Destiny_


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*



_Written by Fenerh_

✍✍✍✍
GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION.
✍✍✍✍

*_My fan's ako ina ina matukar godiya da kuma irin kaunar da kuke yimin inajin dad'in Addu oin ku Allah yasaka muku da Alkhairi ya kuma sadamu da Alkhairi na duniya da lahira baki daya I love you All_*

πŸ…Ώβž‘2⃣2⃣

Tunda ta fito take baza idanu tana duba ta ina zata ganshi Amma har tabar gidan bata sashi a idoba daga bayane zuciyar ta take bata may be ya wuce batareda ya nemeta ba,


Taji haushi sosai tareda kallon jikinta domin kwalliya tayimai ta musam man daga cikin dogayen rigunan da ya siyamata masu kyau da,kuma tsada,


Haka ta shiga ta sallami su Hajiya suna yimata tsiya driver ya kaita school batareda ta jira hajara ba,


Abdullah kuwa tunda suka dauki hanya ya kishin gid'a a bayan mota yana mai cije lips d'inshi shikadai yasan yanayin da yake jin kanshi har ALLAH ya kaisu lafiya,



"Bayan suntashi school gidansu suka dawo harda su Sumayya domin sunfara shirye shiryen Auren sumyn a gefen su Hajiya suka baje sunata tsokanar ta " Hajjaju mai tuwon yan gayu a Gaskiya munyi missing sosai Su Dady basu kyauta mana ba da suka hana business,


"To ja'rai kutashi kubamu wuri muhuta tunda kuka shigo Kaina yafara ciwo " Amina ke ko basu isheki ba?


"Ai ni yaya tashi zanyi inje inkwanta tunda haka akeson ganin mu ba cas ba as,


Kai kuzo muje mudan ci wani Abu yunwa nakeji bazanci Abincin tsofin nan ba, eh lallai Ruman wato iyayen ki sun rabamu da karfi da yaji tun bakiyi Auren ba ko?


Ta dawo da saurin ta ta rungume ta " wa ya isa ya rabani da kakus d'ina ai sai mutuwa don ko Aure zanyi tare zamuje,


"ALLAH ya tsare ni da mugun gani ni da nayi nawa Auren tareda ke mukaje ko wani ya rakani?


" Mu za a fara akanmu "to mutuwar ma muyita tare " tayi saurin Sakin ta haba haba Hajiya " keda kinkusa tafiya nida yanzu na fara zaki wani jani muje tare idan kinje ina gaida mazajenki da kuma Umma na sai bayan ta furta jikinta yayi mugun sanyi nan take Annurin fuskar ta ya kauce,


Ta rasa soyayyar uwa domin ubangijin da ya halicceta yafimu bukatar ta uban ma gashi yanzu tafara samun kulawar shi Amma ana kokarin rabasu dashi,


Wuce wa kawai tayi kawayen ta suka bita domin sukansu sunsan maraici na damun kawarsu domin wani Abun sai uwa idan karasa ta karasa babban bango,


Duk da Hajiya tayi kokari sosai Amma soyayyar uwa daban ce ita kanta gwaggo Amina saida ta dan share hawaye tunowa da gudaliyar yarta mace ALLAH ya gafarta miki Aisha' ta furta Ahankali Hajiya ta Amsa Amin don nabiyyun Rahmati



"Dakinta ta nufa dasu tundaga falon suka fara zuba santin haduwa har zuwa cikin dakin da take zama " Wow Queen a Gaskiya kina morewa irin wannan daular kekuwa mai zai Bata miki rai?



Kuna zagina ne kawai ku bakwa ganin wadda kuke ciki? Ina aikema kinsan yanzu kinyi mana nisa muna bayanki gimbiyar bature'


Ke wai ma ina yake ne kwana biyu meye labari? Tayi murmushi sannan ta labarta musu Abinda ke faruwa tareda gaya musu A yaune ya wuce Kaduna basu ma samu haduwa ba ta nuna musu sabuwar wayarta har ma da shopping din da yayo mata'


Sunata zuba shewar su irinta kawaye tareda tayata murnar samun masoyin Asali tayi saurin kwabar su " Hajara kinsan Akwai matsala nafada miki komai'


"Mtseew ke Wallahi kinada Abin haushi wannan mayen Sulaiman din kifada mishi bakya sonshi kawai ni kibarni da Hajiya wallahi zan fada mata,


Ki rufamin Asiri Mana wane irin Abin kunya ne wannan ALLAH kunya nakeji kubar zancen kawai muga y'an da ALLAH zaiyi damu'



Mudai ba ruwan mu idan komai ya kwabe ni gashi nasa Dadyn mu ya takawa ya Nasir birki na fada mai Anfitar miki da miji yanzu Dady yace idan har bai fito da mata ba zai hadashi da duk wadda yaga dama kuma nima my Mr right ya shirya ta fada tareda rufe idanu irin najin kunyar nan, duk suka cafke tareda sa dariya


Sumy tace " kuce duk zamu shige daga cikig
A lokaci daya kenan?


Kedai bari Ajere zamu shige ALLAH dai yakai mu y'an mata muma muji Abinda kowa keji'


Ruman ta zaro ido " me akeji y'ar iska da kikeso kije kiji? dad'i mana soyayya'

Suka sanya dariya tareda kai mata duka " ke jarababbiya ce Wallahi " to idan an kaiku kar ku more kutsaya kunya kuga kunya wallahi,


Har ma dai ke Queen " waike mai kawaici idan bature yasameki ko hmmm"

Ki fada mana wannan yaron mezai iyayi saidai mu wahalar da juna, shewa suka kara sawa,



Har karfe hudu suna gidan tare sukayi girki suka koma gefen su Hajiya suka sallamesu sannan suka wuce,



Karfe takwas na dare wayarta tayi kara ta d'auka da sauri a lokacin dama tana kwance Adakin ta tana faman tunanin shi,



Wata irin Ajiyar zuciya suka sauke baki dayan su " My dream" ya furta deep down saida taji muryar har cikin kwakwal war ta " ya kake?


"Banida lafiya' ya bata Amsa,
" meke damunka ? Kece kikaja min ai.

"Ni da bamu koyi sallama ba ai fushi ma nakeyi dakai ni'

" to bake bace kika ja nakasa tsayawa Muyi sallama,

Danayi me? Nashigo naganki ba kaya gaba daya kintayar min da hankali tunda nazo ban iya yin komai ba gashi gobe zanje Abuja Momy na nason gani na,


Tunda ya fara maganar gabanta ya harba " ya ganta dazu? Ashe shine ya shigo taji kamar motsin mutum'


"Meyasa ka shigomin daki ba sallama " Am sory baby ai yanzu kinga na janyo ma Kaina damuwa Wallahi jinake kamar indawo indan rage mugun zafin da kika hadamin ina cikin wani hali'


Muryar da yake Amfani da ita kawai itama daga mata hankali takeyi kamar dama dagan gan shima yakeyi don ya sata itama cikin wani yanayin,


Wani irin mugun nishi yake fitar wa tare da numfashi mai tafiya da bargon jikinta " baby''' ki daure a daura mana Aure kar infada halaka bazan iya ba Wallahi na gaza nafada miki nikadai nasan irin karfin sha'awa ta'


"Kar wani Abu ya faru Kice nine bayan KUSKUREN ki ne ni ba ruwana,


Katse wayar kawai tayi domin ita kama batasan yazata yi dashi ba gashi ya jefa ta mugun yanayin itama,


Aranar Shikam bai samu bacci ba yasha magani har ya gaji Amma baiyi mai aiki ba,


Da safe kuwa jirgi yabi zuwa Abuja domin Momyn shi tasa shi gaba da fitina a cikin yanayin ya isa Abuja"



Can din ma rigimar ta tasa shi gaba akan sai yabita sun koma American ya dai lallaba ta akan ta bari ya kammala ginin da sukeyi bawai don ya y'arda da tafiyar ba,



Tunda ta katse kiranshi bai kuma kiranta ba har kusan sati daya da tafiyar shi Wanda yayi kwana uku a Abuja ya dawo Kaduna yana dirowa ya wuce gidan baffan shiwato baban Ruman,



Yaji dad'in y'anda ya dawo gidan da zama duk da ba ruwa nshi da shiga cikin gidan Abincin shi kuwa a restaurant yake ci domin ya lura Matar gidan sai A hankali,



Sopy tayi nasarar karbar kudi a wurin Aunty bilki tana fita wurin bokanta ta nufa akan yayi mata nata Aikin da kudin dama wayo tayi mata kawai'


"Yayi surkullen shi kar sannan ya kalle ta" meye sunan yaron? Tama rasa mezata fada don maganar Gaskiya bata sani ba'


"Bansan sunan shiba " kajimin shashashar banza to ungo wannan turaren idan har biyan bukata kikeso dazaran yashaki kamshin koda kadan ne zai biya miki bukatar ki jeki tsinanniya Anan ta tule mai kudin Aunty bilki tayi gaba,


Tana farin cikin zata D'ana sabon jini ta nufo gidan Aunty bilki tareda zabga mata karya boka yace zai fara aiki a yau zataga canji'



Tanata sintirin zuwa gidan Amma har kusan sati biyu basu haduba,.



Ganin sati biyu tun ranar da ya kirata ta katse bai kuma kiranta ba gashi zuciyar shi na wahala sosai akan tunanin ta don haka dakyar yaga wayewar Garin na jumu'a ko Aikin bai duba ba ya buga mota sai zazzau,

_birnin shehu gari mai tarin y'an mata garin Ilimi garin manoma garin Albarka_



"Saidai yayi mugun gani daga isowar shi ya hangota a zaune a gaban motar Doctor Sulaiman suna magana " wani irin uban cin birki yayi tareda buga kanshi da sitiyarin motar shi,


Kasan cewar motar a bude take da sauri ta waigo gabanta na bugawa taga shine ya dawo bayan Sam batayi expecting dinshi ba saboda ya daina kiranta,


Tayi matukar damuwa da rashin ganin shi da kuma kin kiranta da yayi,


Dago da kanshi yayi idanun shi sunyi mugun ja tsabar kishin da yake cin zuciyar shi,


Doctor Sulaiman ya kalle ta " Amarya ta ko kanin namune yazo? Tayi karfin halin daga mai kai ta saki fara'a domin Hajiya tayimai bayanin komai yanzu yasan dangan takar dake tsakanin su da shi'



Fitowa sukayi tareda jiran Fitowar shi


Ranshi a matukar bace ya fito daga cikin motar wato duk kashedin da yayi mata bataji ba shiyasa ta ki ko neman shi a waya wato tanason wannan jakin saurayin nata ta nunamai cewa batason shi wato yaudarar zuciyar shi kawai takeyi ko lallai yau zai nuna mata KUSKUREN ta,



Ya fito cikin takunshi na natsuwa da daukar hankali gashi yasha wanka kamar kasace shi ka gudu tunda ya fito ta zuba mai idanu domin ya masifar tafiya da ita kyanshi kullum karuwa yakeyi a idanunta,


Yana isowa ya sanya Hannayen shi duka biyu a Aljihun wandon shaddar shi ya watsawa doctor Sulaiman mugun kallo kafin ya maida jajayen idanun shi akanta gashi ya matsa gab da ita gabanta na faduwa'


Oh ALLAH wannan yaron zai y'ar fani a gaban wannan mutumin,


"Kanin mu sannu da zuwa ya hanya? Juyowa yayi cikin kallon wulakanci ya ce " ita tafada maka ni kanin ta ne ? Shikuwa doctor cikin rashin fahimta yace " eh

"Bata fada maka Akwai wata Alaka ta daban ba bayan kanin ta? Aa meye Alakar taku?

Ya kara matsawa gab da fuskar ta " Har numfashin su na haduwa " baby na why kika kasa fada mai matsayina "Alright now bari in nunama waye ni, cikin zafin nama ya fisgota tareda manne bakinshi akan nata idanun ta a waje gaba daya shock ya kamata domin bata taba tunanin Abdullah zaiyi mata irin wannan wulakancin ba,


Shikuwa doctor Sulaiman ai kusan mutuwar tsaye yayi " macen da zai Aura? Itace wani ke kissing a gabanshi Yarinyar da yake ganin ta kamila Ashe tantiriyar y'ar iska ce no Wonder ta daina damuwa Ashe ta nema wa kanta mafita zuciyar shi kamar ta fito haka yakeji,


Saida ya tsotse bakinta na kusan minti takwas sannan ya saki yayi wucewar shi cikin gidan yana Sakin mugun murmushi,


Ita kuwa yana sakinta tsabar bakin ciki ta sanya kuka kawai domin ya mugun wulakan ta ta a gaban doctor Sulaiman,


Juyowa yayi idanun shi jawur " nagode Ummu da irin mugun wulakancin da kika yimin ba laifin ki bane laifina ne da nakasa gane wa tun farko na nace A tunani na kece macen da ta dace da Rayuwa ta but Am mistaken kema Bakida banbanci da sauran mata Amma kinban kunya tur da muguwar dabi'ar ki kirasa da wazaki yi lalatar saida kanin bayanki "I hate you,



Ya buga motar shi da karfi ya fita a d'ari ba Abinda takeyi sai kuka tareda jin wata irin tsanar Abdullah a cikin zuciyar ta ta dauki lokaci tana kuka kafin ta wuce cikin gidan cikin jin zafin Abinda ya aika ta mata,


Shi kuwa yana hangota ta window tun Shigowar shi har tafiyar Sulaiman sannan ya juya zuwa dakinshi wasu hawaye na zarya akan fuskar

Please Login or Register in order to submit comment