Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shigo da ita domin sai yanzu ta lura da ko ina na dakin glass ne,


"Wasu irin hawaye ne na takaici suka fara zubo mata " kazo ka bude ni intafi malam kar ka tayar min da hankalin tsohuwa ,


"Tasowa yayi yana tangadi har ya iso kusa da ita yasa hannun shi a jikin kofar sai gashi ta zuge,


" Tana fitowa falon ta fisgi jakar ta yayi saurin riko hannun ta " ina zakije?


"Bana son iskan ci ka daina tab'ani ni ba y'ar iska bace,



" Ni shine kuma yanzu na fara taba ki "now tell idan ban tabaki ba wa zan taba?


" Ba yau bane na fara taba ki baby" saidai Akwai banbanci "A da ina tabaki a mafarki na yanzu kuma A zahiri ne,


" ya kai hannun shi kan fuskar ta, tayi saurin gocewa " da zafin naman shi ya fisgota zuwa kirjin shi Wanda yayi nasarar hadewar k'irjin su wuri daya for the first time yasamu y'anda yakeso'



"Saida ya jingina a jikin kofar glass din saboda wani irin dad'in da ya ziyarci ko ina na jikin shi'


" wani irin mugun numfashi yake fitarwa jikin shi na rawa ya kara gyara tsayuwar shi domin ya samu damar more taushin Albarkatun kirjin ta dake mugun dimautashi a yanzu,


"Ji yake kamar ya dagota ya cire hijabin domin zaifi jin dad'in morewa da kyau inda halima baiki ace hannun shi yaje Kansu ba'


" Ga badaya ya juya ragamar tuna nin ta " shine namiji na farko da tafara taba jikin ta harta kai ga runguma gaba daya ya sauya mata kuzarin jikinta tsigar jikinta duk ta mike ta ko ina,



"Da kyar itama take fitar da numfashi kafin tayi wani yunkuri ya dora lips dinshi a kan nata,



" Kusan faduwa yaso yayi daga jikinta saboda laushin dake kan lebenta " ita kuwa jin dumin halshen shi akan lebenta ya dawo da ita daga duniyar shaukin Abinda ya fara dora ta akai yana kokarin zura harshen shi a cikin bakinta tayi saurin hankade shi ya zube a wurin'


"Zubewa kawai yayi a kasa ya fara juyi tareda zubo war hawaye masu zafi " cike da wahala yace " Noo baby,,,,


"Zan iya rasa lafiya ta idan har kika gujeni don ALLAH kibarni Koda ajikin ki ne zan danji sauki kadan ki taima keni zan iya mutuwa wallahi yafada yana mai sanya mata kuka mai tsinkar da zuciya,,,



" wallahi bazan yafe maka ba ALLAH ya isa tsakani na dakai "dama nasan me kake bibiya to kuma ta ALLAH bataka ba


" Mikewa yayi dakyar ya nufeta yana mai zubar da hawaye " say what ever you want Roman ni nasan soyayyar ki ce take hadda sa min fitinar ki meyasa banajin hakan a sauran mata?



"Ya fara share hawayen shi " yanzu naji ki y'ar da ki Aure ni please koda Asirri ne idan har kina gudun Ace kin Auri karamin yaro please''



"Wani irin tsanar shi takejin tana kamata domin ta tsani namijin da zai nuna yana son jikin ta ,


" I danunta suka kada sosai cikin tsananin bacin rai tace " ka budemin kofa kafin inyi maka lahani na fada maka''


"Ta fada cikin karaji kallon ta yake yi wani iri " yafara tafiya da baya baya har ya dangana da center table din dake Ajiye a gefen kujerun mai dauke da kayan marmari da kuma yar Karamar wuka akai ya daukota yanufo gabanta da wukar,


"Idanun ta a waje ta d'auka zai caka mata itane Amma sai taga sab'anin hakan yana zuwa ya damki hannun ta ya danka mata wukar'


Ya ja hannun ta dai dai saitin zuciyar shi " ki kashe ni kawai Roman please kill me' ki la antani kamar yadda kikace I will be happy



"Meye Amfanin Rayuwata idan har bazan yita tareda ke ba? Kece cikon numfashi na idan bakya cikin duniya ta my life is useless,


"Da inada dama bazan bari ki fita ko ina ba banki mu kasan ce a haka ba daga ni sai ke,


"Ganin fadan ta bazai yi Amfani ba kawai ta durkushe a wurin tasa kuka mai tsuma zuciyar masoyi,


" wani irin suya kirjin shi yafara yi yayi saurin durkushe wa a gaban ta jikin shi na rawa hawayen shi na Ambaliya kamar kogi,


"Ku rufama zuciya ta Asiri kukan ki tamkar digar dalma ne a kahon zuciya ta da inga kukan ki gwara ni mutu,


" I promised you daga yau bazan kuma takura rayuwar ki ba gidan ku ma nasan bakya sona a cikin shi daga yau bazan kuma zuwa ba ko Ak bazan bari ya kuma zuwa ba,


"Idan har zuciyar ki zata yimiki sanyi kiyi farin ciki

" Amma kimin Alfarma ya share hawayen shi cikin dakewa ya mike tareda dakko wani dan karamin diary ki rike shi a wurin ki please "


"Wayar shi ya daga tareda kiran Ak yana isowa ya bashi umarnin ya mayarda ita gida shi da kanshi ya mike ya dakko mata wata Leda mai tanbarin inna idea shopping complex ya mikawa Ak " karike mata,



"Jikin ta yayi mugun sanyi ya bata tausayi sosai Amma taki y'arda ta nuna hakan,


" bai iya fita ba kawai ya haye gado tareda fashe wa da wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai saurare,


"Zuciyar shi suya takeyi shi kanshi yasan yayi karya yace zai hakura da ita " I can't yafada cikin kuka"



"Jikinta yayi matukar yin sanyi har suka isa kofar gidan su bata iya cewa komai ba ya miko bata ledar ta karba harda godiya ita kanta bata San dalili ba da takasa karbar Abinda yafito a hannun shi"


"Hajiya kuwa hankalin ta ya tashi ganin har kusan karfe biyar ba labarin Ruman har magaji ta kira tafara fadamai ko zai je makaran tar ne ?


" Gashi batada lambar kawayen ta,


"Kaga Amfanin waya ko da Ace tana da ita ai koma meye zamu sani bari ta dawo dolenta ta rike waya nida ita ne'


" tana rufe baki tana shigowa cikin sanyin jikin ta,bakinta dauke da sallama,


"Tun bata zauna ba Hajiya tafara sababi " Yanzu kekuwa Ummu ina kika tsaya har karfe biyar duk kin daga min hankali?


"Muna gidan su Hajara ne, tafada kai tsaye batareda ta shirya karyar ba tafito daga bakinta ita kanta mamakin Abin takeyi da takasa fadawa Hajiya komai akan bature'


" Amma zakije meyasa baki fada min ba kin tayar min da hankali' kiyi hakuri my kakus tafada cikin karfin hali domin ta matsu ta keb'e kanta ko zata iya sarrafa tunanin ta'


"Bakida lafiya ne Ummu?
" lafiya ta kalau kawai gajiya ce.


"Toh kije kiyi wanka ki dan huta duk da yamma tayi sosai,


" Dama a kage take mikewa kawai tayi da jakar ta har ma da ledar da ke hannun ta tayi shigewar ta cikin dakin ta'


"Hijabin ta kawai ta iya cirewa ta fada kan gadon ta tareda runtse idanun ta tana mai tuna moment ago,


" yarrrr tsigar jikin ta ta kuma mikewa sakamakon tunawa da tayi da irin rungumar da ya bata " har yanzu tanajin cent din turaren jikin shi atare da ita duk da ta cire hijabin,


"Wani iri takeji sosai ajikin ta w'anda Sam ta kasa sarrafa kanta ga wani irin shauki mai wuyar fassara atare da ita duk sakamakon tunawa da lallausan kuma tsadadden jikin shi da tayi,

." Duk da yana da karan cin shekaru amma jikin shi Sam bai nuna ba zaka d'auka shekarun shi sunkai irin Ashirin da biyar din nan,


"Ta dade A cikin yanayin kafin ta samu ta mike zaune tareda janyo ledar da ta shigo da ita ta bude,


" wata irin Arniyar wayace kirar Samsung galaxy grand 9 sabuwar yayi wadda bata taba ganin ta koda wurin kawayen ta ba Mu samman hajara da duk sabuwar waya tafito sai ta canja'



"Duk da bata kaunar waya wannan tayi bala in burgeta kuma for the first time taji zata iya rike waya a hannun ta,



" Kodan shi ne ya bata? Meyasa taki karba a hannun Doctor Sulaiman? Ko nasir ya bata waya taki karba Amma wannan gashi ta karba batareda tasan ita bace kuma ta y'arda zata rike'


"Bata gama tunani ba sako ya shigo Sai a lokacin ta San wayar akunne take kuma har ma da layi a ciki tafara juyata kafin ta bude sakon,

*I may not be the one you love and I may not be the most important person in your life, . but just hope that one day u will Also love me the way I do*
_hope u will Accept my small gift_
*I love you*

" Duk da sakon ba wani Abu na burgewa bane aciki Amma ta samu kanta da karan tashi ba Ad'ad'i,


"Ranar da kyar taga waye war gari, wayar ma Sam bataso Hajiya tagani Amma tasan bazata iya boyon waya ba


" Kafin ta fita ta nunawa Hajiya tareda karyar yayan hajara ne ya bata,


"Ummu" Hajiya ta kirata " ta Amsa tareda zama kusa da ita' Me yasa kike wa Sulaiman yawo da hankali?


"Ni kuma menayi mishi shidai ke wahalar dakanshi ba ruwana ni'


" Ki bi a hankali duk kin daga ma dan mutane hankali kullum yana hanyar gidan nan gashi ko kallon Arzikin ma yanzu baya wani samu,


"Cikin kosawa ta mike " Sai na dawo mayi maganar " Dawo nan tunda kinyi waya samin lambar ki kar akuma irin na jiya,


"Hajiya bazan dade ba zan dawo da wuri yau " kuma ba wai na gama sanin kan wayar bane sai naje ankoya min,


"Adawo lafiya toh ki kiyaye don ALLAH yabada sa'a,


" Da wuri ta isa makaranta ta samu su Sumy basu isoba saida ta dauki lokaci kafin suka iso da shewar su suka rungume ta "Sai Queen ,


" Idanun hajara yakai kan wayar hannun ta ta waro idanun ta duka waje

" My dream phone """
Ta fada cikin ihu tareda Amshe wayar " ke y'ar gari Kice kinshigo gari'


"Waye ya baki wannan mai zafin don ALLAH?

" Sumy ma tace ke kyama tanbaya ai kinsan waye " cikin jin dad'i suka dafe ta " our young crush?

"Kai kawai ta daga musu, wani irin ihu suka saka tareda tafawa " kinsan kudin wayar nan kuwa two hundred plus fa " wani kaya sai Amale,



"Ki na kamshi my Queen"

"Haka sukayita kururuta wayar kafin su shiga Ajin ita kanta Abin yabata mamaki wayace za a siya harta sama da dubu Dari?


" to ita ko a mafarkin ta bai wuce ace ta rike yar Nokia torchlight ba sai gata da Galaxy grand Hmmm""



Bature kuwa tun fitar ta ciwo ya dawo sabo Ak ciki Gaggawa ya kira iyayen ya fada musu hankalin mahaifan shi ya mugun tashi atake suka biyo jirgi suka iso Zaria,



"Linda kuwa ta iso Nigeria don har da ita suka iso Zaria " taci wani irin takalmi kamar ta fado kasa ta karye tsabar tsini ga sket dinta kamar ya yaye rigar kuwa iya kacinta wurin nono cibiyar da ciki duk a waje ga wani kwamemen glass Kamar horror da ta hadu da Jan gashin kanta da tayi dying,



"Kana ganinta kaga American's din nan da idanun su ke bude sosai wai da sunan waye wa"

"Tunda suka iso take like da shi a gaban iyayen shi sai faman shafa shi takeyi yana kwance shi bai Masan tanayi ba yanata kanshi'


." sai kusan karfe dayan dare ya farka daga dogon baccin da yayi na Allurar da,likita yayi mai'


"Ahankali yakejin numfashin mutum a jikin shi yafara bude idanun shi a hankali yana mai sauke su saman Fuskata


" Wani irin zabura yayi ya hankade ta a jikin shi w'anda yayi sanadiyyar farkawar ta " oh darling u hv wake up tafada cikin slang English dinta,


"What are you doing in my room and on my bed?

" Tafara kokarin rikoshi zuwa jikinta tareda zame yar ficiciyar rigar da ke jikinta ta y'ar agefe " ya kalle ta cikeda kyama yana mai kallon wani irin bushashshen kirjinta,


"Cike da tsana " out of my room, ya fada cikin tsawa " I said get lost'



"Mayyar kokarin rikoshi takeyi " come on Darling u no why am here so just for get it and let enjoy our night together,


Ya kwanta jinya saboda sha'awa amma yanzu yatashi yanacin karo da mummu nar surarta gaba daya feelings dinshi ya gudu"



"Tsaki ya buga tareda mikewa ya barmata dakin wani daki dake kusa da nashi ya fada tareda datse kofar da ki don yasan halinta batada zuciya kokadan,


" Ya janyo system dinshi ya fara research din da ya dauki lokaci yana yin shi kuma yana kan neman haske akai har yanzu.......✍




*A Gaskiya wannan karon ina fuskantar karan cin comments dinku fan's sanadin hakan yake hanani yi muku typin kamar y'anda nayi kuduri*


*drop ur comments please*



*Matar Soja*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KUSKURE NA🙆*
_Love & Destiny_


_Written by Fenerh_


~Dedicated to~
All my fan's

_ina mai baku hakuri da rashin jina da kukayi sakamakon rashin wutar da muka samu Amma yanzu Alhmdulillah komai normal,bawai saboda rashin comments bane yasa kukaji shiru bazan taba yin hakan ba kamar yadda wasu sukayi tunani har ma sukayi sharhi akan cewa basu San me zasuyi su burge writers ba a kullum suna complained akan rashin comments ina so ku fahim ci wani Abu comments dinku yana da Amfani a wajen writers sosai domin yana kara mana karfin guiwa Sann kuma da comments dinku ne muke samu yi muku typin har ma da gyaran kura kuran mu don haka ina neman Afuwa ga w'anda na batawa rai masoya a koda yaushe ina Alfahari daku nagode_


🅿➡7⃣

Tun dawowar ta daga school takejin zazzabi na rufeta ita kadai tasan y'anda takeji A cikin zuciyar ta,

Ganin Wankin hula zai kaita dare yasa ta nemawa kanta mafita ta,


"Ta gama yan kewa kanta Abinda yafi dacewa da ita'


" Washe gari sun tashi da jimamin rashin lafiyar Magaji don haka kawai ya yanke jiki ya fadi ' hankalin Hajiya yayi mugun tashi tayi mugun rudewa,


"Gwaggo Amina ce mai kwantar mata da hankali wato Matar magajin " Yaya kiyi hakuri da izinin ubangiji ba Abinda zai samu baban ja'afar,


"Tana share hawaye tace " Amina shikadai nake gani inji sanyi shikadai ya rage min "ya'yan namu guda biyu duk sun guje mu saboda mace,


" Kiyi hakuri kidaina zubar da hawayen ki akan su ni kaina na cirewa kaina tunanin wannan yaron ai duniya ce ta ishi kowa Riga da wando,


"Gashi Muhammadu tun Auren shi da yarin yar nan balkisu baifi sau biyu ya zo gida ba ko tunanin y'ar marainiyar ALLAH bayayi,

" Daina tunamin Amina ni yanzu zuciya ta tafi kar kata da dawowar ja'afaru ko hankalin d'an uwa na zai kwanta,


"Nasan komai yakeyi yana yin shine a cikin karfin hali Amma abin na cin shi a zuciya,


" Ita kanta gwaggo Aminar karace irin ta ba haushe Amma Abun na cimata tuwo A kwarya'


"Ruman da Shigowar ta kenan taji wannan zancen hankalin ta ya tashi sosai da jin wannan irin labari,


" tana bukatar Karin haske don haka har matsuwa tayi gwaggo Amina ta tafi taji Karin bayani,


"Tunda ta gai shesu ta shigewa war ta cikin dakin ta cike da tunani kala kala'


" Bayan tafiyar gwaggo Amina ta fito tasamu Hajiya'


"Wai wane labari nakeji dazu kuna yi keda gwaggo?


" Kallon ta takeyi cike da sanyin jiki tayi Ajiyar zuciya cikin damuwa tace'


"D'an uwan mahaifiyar ki shima tun lokacin da yatafi karatu kasar turawa ya hadu da wata baturiya ta mallake mai tunani bai kuma wai wayo mu ba,

" Saboda mun nuna mai KUSKUREN shi na Auren shi da Ahalil kitabi Akwai lada aciki kuma Addinin mu baiyi hani ba Amma Akwai kalubale da yawa da mutum yake fuskanta ko akan tarbiyar yaran su,


"Nidai har yanzu kaina na cikin duhu " naji kunce d'an magaji ne," eh shine mahaifin Aisha wato mahaifiyar ki,


"Amma mai yasa baki taba fadamin kaka na bane? " kaji mun shirme ko da can ba kakan ki bane shi?


"Aa Hajiya shima bai taba nuna min Akwai kusan ci mai karfi tsakani na dashi ba,

" Ba ma wata shakuwa a tsakanin mu har ma ina nuna mai tsana ban San cewa shi ya haifi mamana ba'


"Kuma duk hakan tafaru ne sanadiyyar nuna son kudin shi da yakeyi a fili'


" Wani irin murmushi tayi irin na manya " Ummu' takirata da murya mai ma anoni da dama'


"ALLAH ne gatan mu magaji dan uwana ne gatan mu duk Abinda yakamata a ce mahaifin ki yayi mana shine duka ya dauke duk da shekarun shi kuwa'


"Duk hidimar makaran tar ki shine da wahalar shi da yakeyi Ruman kin taba tunanin waye yake tallafa mana kuwa?

" kina tunanin da wannan sana'ar ce kawai nake baki gatan da kike samu?

"Magaji yazame min d'an uwa yazame min kani ya zamemin yaya yakuma zama min uba duk da yana kanina,


" Duk tsawon shekarun nan Ummu magaji yana cikin rashin babban danshi kuma ga mahaifiyar ki ita ma ta tafi gashi dagani har shi ba wani zuri'a garemu ba,


"Shi guda dayar ta tafi shi kuma w'anda ya kamata ya kula dashi ya yi nisa bayajin kira kamar mahaifin ki'

Ta karasa tana mai share hawaye " Ummu Ruman jikinta yayi mugun sanyi sai yanzu ta gane meyasa Gwaggo Amina ke yawan kallon ta a duk lokacin da zasu hadu gashi duk y'anda Hajiya kaka zata matsa mata da zancen zuwa gidan su bata y'ar da taje.


"Ta gano cewar Ashe ta tafka babban KUSKURE nakin ba wa innan bayin ALLAH kulawa'


" Ummu ni Kaina ban kyauta wa magaji ba yakamata insanar da ke matsayin shi kodan ki shiga jikin su suji sauki suma Amma Banyi ma dan uwa na Adalci ba na gane KUSKURE NA a kan hakan yanzu'


"Tayi saurin rungume ta Bakida laifi my kakus nice mai laifin da naki Sakin jiki dasu Amma daga yanzu zan basu kulawa sosai kodan in rage musu damuwa,


" Da kanta ranar ta shirya ta Debi Abinci mai dan yawa tasa a kula ta nufi gidan su " Magajin na shinfide a bakin icen da ke gidanshi Gwaggo Amina na gefe tanata yimai fifita


Gaba daya taji ba dad'i sunyi mugun bata tausayi ta manta rabonta da takawa taje gidan tunda tayi wayo"



"Su Kansu sunyi mamakin ganinta " ta gaishe su cike da jin kunyar su" ya mai jikin ? Ta fada batareda ta kira sunan shi ba kamar y'anda tasaba fada'


"Ya Amsa cike da jin dad'i ina yaya take Ummu? " tana nan zuwa Anjima kadan'


" saboda rashin sabo tarasa y'anda zatayi ganin wanke wanke a gefen rijiya ta mike cike da jin kunya ta kwabe hijabin ta tafara wankewa duk da gwaggo Amina tace ta bari Almajiri zaiyi'


"Bayan ta gama ta share gidan tas har ma da dakin gwaggo Amina duka ta gyare gidan yafito tsab duk da itama Gwaggo Amina ba laifi Akwai tsaftar"


"Sunyi matukar farin ciki ganin gudar jinin su yau a cikin gidan su har tana musu hidima,


" Haka Hajiya ta sameta ta sake sosai harda y'ar hirar ta suka zauna cikin farin ciki tareda dauke wa juna kewa,




"Kasan cewar unguwar su daya saidai d'an tazara dake tsakanin su yasa suka kai karfe goma kafin su dawo gidan su,

" tayi matukar farin cikin kasan cewar ta a cikin kakanin ta a yau jinta takeyi A cikin ni shad'i,


"Tana dawowa ta janyo wayarta taga miss call ba iyaka daga bature sannan kuma da su hajara,


" nan take tayi dialing number hajara " tana d'auka ta sa mata ihu" sai Matar bature """""


"Tayi saurin cire wayar a,kunnen ta " Zaki ciremin dodon kunne" sory Amaryar turawa dama yaya nasir ne yasani gaba inbashi numbar ki shiyasa nakiraki domin inkarbi izini


Kuma kinsan ni ina team bature don haka bazamu bada numbar ba ta katse kiran kit"


"Sakin baki tayi kawai tana kallon wayar tare kuma da mamakin halin hajara,



" Tayi ta kallon nubar shi kamar tana son ganin wani Abu a cikin numbar daga baya ta wurgar da wayar gefe tayi baccin ta"



"Gaba daya hankalin shi a tashe yake ga wannan mayyar da Momyn shi takawo gaba daya ta hana mai ruwa gudu gashi yau kwana biyu baisa Farin cikin shi a idoba,


" Hajiya da Kanta tayi cigiya wai bataga bature ba kwana biyu ko lafiya?

"Tana jinta sarai ta kyaleta Amma duk lokacin da zata wuce sai ta kalli kofar dakin nashi,


" Wai da gaske yakeyi bazai kuma dawowa gidan ba? Takewa kanta tanbaya?


Batason tuna nin shi da take faman yi dole ta daukar wa kanta,mataki,





Fitowa yayi cikin gayu irin na samarin da sukejin sunkai kuma sun cika maza yana sanye cikin farin tree quarter hade da Riga Armless Mara hannu ya sanya tsadaddiyar facing cap mai dauke da sunan new york Kafar shi ta kalmin da yafi kauna ne wato canvas farare ga lafceciyar waya itama fara a ta kaice komai na jikin shi fari ne shi baya kaunar kowace kala idan ba fari ba,



"Takunshi yake cikin isa ya shigo falon da iyayen shi ke zaune harma da Linda " tana ganin shi ta taso cikeda iya yi tarun gume shi tareda manna mai kiss a kumatu,


"Oh Darling u are looking gorgeous""

"Ya dan ture ta kadan tareda daure fuskar shi tamau ya matsa ya gaida iyayen shi yace musu zai fita ya dawo,


" oh Tnk goodness u are going out so take Linda with you so that she can do shopping'


"Tayi wani irin karar jin dad'i " tank you mom in low I love shopping,


"Come on Darling let go" tafada cikin zakuwa "bakin ciki kamar yayi ihu ya kalli uba nshi da ido ya nunamai yayi hakuri suje,


" Yayi kwafa yayi gaba tana biye dashi batareda ya damu da itaba ya fada motar shi itama ta shige " escort dinshi suka taso yayi saurin tsayar dasu,.



"Ji yakeyi idan har yau bai sata a idoba Akwai damuwa don haka direct f.c.e ya wuce bai damu da Linda dake gefen shi ba "


"Yayi sa'a suna zaune a wurin zaman su tunda ya kunna kan motar shi ya hangota tana zuba dariya ita da kawayen ta ga badaya ya shala da kallon ta har saida yaje gab dasu ya faka motar kamar wani irin mayen karfe ne ke janshi zuwa gareta,


" ya ma manta da Linda dake cikin motar tana ta zuba kamar kanya hankalin shi naga tauraruwar zuciyar shi,


"Fitowa yayi cike da takunshi na isa kamar wani sarki " Tunda ya faka motar shi gab dasu su hajara suka fara murna,


"Lokacin da yafito kuwa ita kanta uwar gayyar ta shagala da kallon shi har ma taji ya burge ta for the first time,.

" Man in white, Hajara tafada a hankali don ya tafi da tunanin su, Sumy kuwa ai ta kusa suma Shikuwa ai ya shagala da kallon ruhin shi,



"Linda kuwa taji bala'in kishi ganin shi wurin y'an mata " yanzu saboda wa innan Black's din yake mata wulakan ci?



"Tafito cikin matukar hasala ta nufoshi " tana zuwa batare da tunaniba ta rungume shi ta baya,


"Oh baby u keep me waiting please am so tired let go back I wants you to massage my body ,


" ta fada tana mai kara shigewa jikin shi gaba dayan su suman tsaye sukayi suna kallon Asalin karuwanci,



"Ruman kuwa wani irin kululun bakin ciki ne ya tok'are mata makogwaro

" jitake kamar ta Amayo wuta saboda Abinda takeji a kirjinta,


"Kallonta yakeyi yana nazarin yanayin ta yana kuma mai jin bakin cikin Abinda Linda tayi mai bayan yafara hasko nasara a idanun ta,


" Mikewa kawai tayi ta zari Jakarta ta wuce batareda tace musu komai ba " wani irin numfashi yaja tareda hankade Linda


"Ya mata wani irin mugun kallo " find your way before I come back if not u will gate it from me.

"Ya bita cikin sauri yasha gaban ta " tayi saurin dagowa "idanun ta sunyi mugun ja cikeda masifa ta dago kanta suka kalli juna cikin ido,


" out of my way"' ta furta cikin hasala " bazan matsaba sai kinfadamin Abinda ya bata miki rai"


"Wallahi zan maka wulakanci idan baka matsaba " koda yake bakasan mutum Ciba domin hanyar da mutunci yabi kai baka bishiba,


"Tunda ka nunawa duniya kai tantiri ne har kake yawo da karuwa wadda

Please Login or Register in order to submit comment