Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ban mu lokacin mu ai sai dan duwala kawai da kuma miski yanzu kuwa turare har da,mai warin bunsuru"


"Ba Abinda takeyi sai dariyar wai warin bunsuru in banda sharrin Hajiya"


Cikeda kulawa tace " ke dai Ruman bansan irin kiba " tace me kuma nayi yanzu kakus muna hira mai dadi"


"Yanzu a ce ko yar wayar zamanin nan baki ra ayin mallakar ta? " Hmm Hajiya mai zanyi da waya ? Wazan kira ? Baban ki " shi idan ya y'arda ni ke banaso ki y'arda shi'


"Ina so ki bashi hakkin shi na mahaifin ki nan take I don ta ya kawo ruwa domin tasan Hajiya na cikin damuwar rashin kulawar yaronta"


"Tace Hajiya ki daina sa damuwa da izinin Ubangi " Baba zai zo ya ganki kuma ni banida damuwa Sam tunda inada ke ban rasa komai ba sutura ko yar masu kudi bazata nunamin ba saboda kintsaya min a Rayuwa "


"Ta kuma rungume ta " ina son ki kakata Allah ya barmin ke har inyi Aure ingudu inbarki" cikin tsokana".

"Ta kai mata duka " matsa can Mara kunya tana zancen Aure in banda zamani "


"Haka sukayita raha a tsakanin su daga baya take bata labarin ai mai hayar su ya tare "


"Dazu yazo yagai sheta yaro kamar baya taka kasa baki ganshi ba bature sak Amma Yanajin hausa sosai" .



"Ta mike zunbur um " wallahi Saura kuma India tunda kinzauna da beyerabe kin zauna da Igbo yanzu kuma bature to Saura Aljani "

"Ta kai mata duka ta kwasa daki da gudu ita da kayanta tana dariya"



*Bayan sati biyu*

"Tunda sabon mai hayan su ya tare bata taba sa shi a,idoba saboda ba wai damuwa tayi da sha anin mutane ba"


Kuma gashi tana fita school abinta idan ta dawo bata zuwa ko ina kuma "




"Yau tun da ta tashi takejin cikin ta naciwo tun tana daurewa har ta kasa ta kira Hajiya " gaba daya hankalin tsohuwa ya tashi ganin Ummu Ruman dinta na faman juyi"


"Bata tsaya bata lokaci ba ta kira magaji yasamo musu napep sai Asibiti "


"Kafin wani lokaci tafara fita hayya cin ta cikin gaggawa likita ya karbeta ya fara bata kulawa "



"Sai kuka takeyi domin tasan damuwar ta tana tsoron kar likita ya gano yace zai fadawa Hajiya ko magaji tanajin bala in kunyar hakan tafaru"


"Tayi sa'a kuwa ya bata magun guna " yanemi da su basu wuri zai yimata tanbayoyi "


"Ta dukar da kanta kasa domin irin kallon da yake aika mata "


"Hajiya Ummu Ruman " yakira sunan ta a natse yana mai binta da kallo da kuma wani irin sihirtaccen murmushi "


"Kinsan kinada matsala? Tayi saurin dagowa tana mai zubamai idanu' eh that's means kinsani"

"Meyasa bazaki nemi solution ba " nasan Hajiya bata saniba kuma a Al adar bahaushe mace bazata iya kallon iyayen ta da irin wannan zancen ba"

"But u have to do something " kinada isashshiyar lafiya ' don haka Bawani Abu bane "

"Kinsan cewa irin ki a cikin mata sunada wuyar samu " da Watace da tuni ta fada sabon Allah "


"Bakida saurayi ne" tayi saurin kallon shi " saurayi kuma? " eh I mean boy friend "ta girgiza kai " aa "

"Wata irin Ajiyar zuciya ya sauke " zan iya samun numbar wayarka?


"Banida waya ni' tafada atakaice domin ta matsu ya sallame ta " haba Hajiya Ummu Ruman kamar ki a wannan zamani Bakida waya?


"Ba Abinda zanyi da itane " tafada cikin zakuwa " Hmmm ya janyo drower gefen shi " wata sabuwar waya ya zaro ya mika mata " gashi Akwai layi a ciki"



"Ta dago kai tana mai kallon me yake nufi? " ina nufin ki rike a wurin ki zamuyi magana " " wace irin magana kuma? Kedai ki karba'


"Aa nidai banason waya ta mike tsaye " zan iya tafiya? Toh ki taimaka ki gayamin Address dinki'


"Gaba kawai tayi domin yafara bata haushi don ta gama ganoshi " ko ledar magun gunan ta bata d'auka ba ta wuce


"Mikewa yayi da sauri ya d'auka ya biyota yasamu zasu wuce " yace ga maganin ta ta kula da Amfani dasu akan lokaci ":


" Hajiya tayi godiya " tace magaji nemo mana keken toh "

Har ya juya yace " Hajiya bari inkaiku kawai ina zuwa " batareda ya jira amsa ba ya koma ciki


"Nidai Hajiya bazan hau motar shi ba " kibani na mashin kawai ma hadu a gida" toh saboda me? Mutum da Aikin shi ya ajiye saboda ya taimaka mana sai mu watsa mai kasa a ido"


"Toh badani ba" ya fito tareda bude musu wata mota mai kyau Hajiya da Ummu suka shiga baya magaji kuma a gaba


"Saita madubin motar shi yayi daidai saitin ta yanayi yana kallon kyakkyawar fuskar ta yana tasbihi a cikin zuciyar shi '


" gaba daya ya gama bata haushi " shiyasa taki dago kanta " saboda yasan matsalar ta shine zai nemi ya shige mata ' ko Anfada mai ita y'ar iska ce ?"zatayi maganin shi kuwa"


"Suna tsaya wa Hajiya tafara koro godiya magaji ma nayi " tace Dan nan ka shigo daga ciki kaji " Allah yayi Albarka "Ruman kuwa tuni ta shige ciki tana mai jin haushin Hajiya"


"Har cikin falon su ya zauna masu Abinci suka kawo mai lafiyayye n tuwon shinkafa da miyar Agushi " ya zake ya kwashi tuwo harda santin shi " A gaskiya zanrika zuwa ina cin Abin ci kullum Anan Hajiya "



"Tayi dariya tareda cewa Matar ka fa' " Ai Hajiya ban da Aure kuma aiki ne yakawo ni nan iyayena na Kaduna kuma sun dade suna damuna akan zancen Aure ban samu Matar da ta dace dani ba sai yau "


" ina fatan Hajiya zaki bani jikar ki don bada wasa nake sonta ba ganin ta kawai danayi yau naji nasamu iyali na nima"


"Hajiya taji dadi sosai har cikin zuciyar ta domin tana kaunar duk mai kaunar Ummun ta " Allah yasa ku daidaita idan Matar ka ce "


"Allah ya sanya Alkhairi " yace Ameen Hajiya "


"Toh banji sunan mijin nawa ba? Hajiya sunana Sulaiman Abubakar mahaifina dan siyasa ne mu biyar ne a wurin mahaifin mu nikadai ne namiji sai kuma kanni na mata guda hudu a halin yanzu ina cikin shekara biyu da kammala karatuna a India inda na karanci Aikin likita"


"Kuma ina cikin shekara ta " talatin da biyar yanzu"


Ruman dake kwance cikin dakinta tanajin zancen su sai taji ya burgeta kadan saboda dama irin shi takeso bawai kananan yara ba under thirty "



"Don ita daga farko ta d'auka bai wuce shekara Ashirin da biyar ba saboda yanada jiki mai kyau Ashe hutune ya boye shekarun kuma gashi kamar Fulani "


"Ba laifi ya hadu daga fuska har zuwa wankan shi har ma y'anda yake abubuwan shi straight for word ba wata kwana"



Saida ya mata bayanin magun gunan sannan yace daga yau idan taji ciwo basai Ankawo ta Asibiti ba kawai su kirashi yazo"


"Yace toh kuma nabata waya taki karba" kyaleta kaidai koni nayita fama da ita in sai mata taki "



"Yayi dariya tareda karbar yar Nokia Hajiya ya yi plashing number shi yayi mata serving "


"Yaron ya shiga ranta farat daya Haka suka sha hirar su harda magaji saida aka nemeshi sannan ya tafi ".


" Cikin yan kwanaki kadan sukayi mugun sabo da Doctor Sulaiman kullum yana gidan Hajiya idan yataso aiki "


"Mutu miyar ma ta dan fara sakewa dashi har suna dan hira idan har tana gida Amma " taki bashi fuskar abin da yake nema wato soyayyar shi gareta '




"Yau tana zaune a falo tareda Hajiya suna hira Magaji yashigo tareda sallama" suka Amsa ya dan fara zolayar ta " yau banga mutumin nakiba ?


"Hajiya ta Amshe zancen " wai likita? " eh. " yaje Kaduna yau wai Ana neman shi a gida"


"toh ALLAH yadawo dashi lafiya' Ameen.


" tana gefe batareda ta tanka musuba ta mike zuwa cikin dakin ta"


"Yaya yau bature zai dawo fa. " bangane bature ba da waye a cikin dakin? Yaron shi ne Ashe sai yanzu yake mun bayanin ogan na zuwa wai yadan yi tafiya ne "


"Toh Allah yakawo shi Sannan yanzu bana bukatar wasu masu hayar bayan shi sauran dakuna biyun a barma masu Aikin surika zama a ciki"




"Kamar kullum kofar gidan na Hajiya kaka yana cike d'ankam da mutane " wasu masu siyan Abinci wasu kuma yan zaman kashe wando "

Suna faman sana'ar wato tsegumin da suka saba' " wani yafara magana " ba_ba kwana biyu banga Babyn nan ba ' dayan yace " kai ai kallo ya wuceka "dazu ma tafito " wallahi kullum kamar ana kara k'erata "


"Ai kaidai bari " Wannan ta manyan yara ce " ina ma inama.......



"Maganar su ta tsaya ne dai dai lokacin da wata irin Arniyar mota ta kunno kai zuwa kofar gidan " A tunanin su wucewa zatayi domin sun San duk mamallakin wannan motar wani ne a Nigeria "


"Duk da kasan cewar duk Wanda yake Rayuwa a wannan unguwar yasaba ganin motoci kala kala Amma wannan ta daban ce "


"Saida aka dauki mintico kafin mamallakin motar yabude ta " a hankali yake zuro kafafunshi zuwa waje " wasu irin takalma ne irin na matasan yanzu sawu ciki farare tas "


"Fitowar shi ya mugun fadar min da gaba don ni Kaina bankawo shi bane " yau ina body guard din sukaje? Saboda tsegumi na da gudu naleka numbar motar domin gasgata zargina"


*J5* na gani a jikin motar gaba daya Kaina ya kunce " me hakan yake nufi?


"Shi din ne kuwa Amma meya kawoshi gidan Hajiya kaka? Kaddai Ace shine zai kasan ce a cikin wannan dakin da aka gyara ?


" Kara kallon shi nakeyi yana Amsa waya cikeda izza dakuma yanga kamar bayason magana "


"Gaba daya gayun dake wurin sun raina Kansu duk da sun San cewar sun girme shi nesa ba kusa ba Amma yaron yanada k'warjini da kuma cika ido ga kuma kare zance wato masu gida rana"


"Suna ganin shi sun San cewar ba bahaushe bane kodai bature ko kuma balarabe " ya karaso da earphone a kunne yana maganar "


"Excuse' me da ya furta cikin kwarewa da wani irin salo shi ya dawo da shuwagabannin magul matan daga karemai kallo"


"Wani mai shegen salo a cikin su yayi saurin cewa" Can I help u ? "Yace yes please" Am looking for .... Saida ya kalli faskekiyar wayar hannun shi sannan yace " Hajiya kaka" Hause,



"Cikin rawar jiki yake cemai ai ga gidan nan " jikin shi narawa yayimai jagora kasan cewar gidane da kowa yakan shiga "


"Shikuwa yana kallon unguwar da kuma kofar gidan A zuciyar shi yake aiya nawa " Anan zai zauna ?


"Cikin ya tsuna fuska yake takawa yana shiga cikin gidan " first ting da yafara cin karo dashi shine wani Almajiri dauke da kwanon sauran tuwo miyar kubewa da wani ya rage aka juyemai '


"Wani irin kauce wa yayi tareda cewa" goodness wat tha hell " ai da sauri ya juya batareda ya shiga ciki ba " fadawa kawai yayi cikin motar shi yafara danna wayar shi"


"Batareda bata lokaci ba yafara ruwan bala'i " AK wat the he'll is that? are kidding me?


Batareda naji Amsar dayan da yake kira da A k ba yayi hangin wayar shi tareda fisgar motar shi yabar unguwar ya hau babban titi kenan ya uban wani burki Wanda yayi kusan hada dan karamin hatsari "


"Gaba daya mutane suka fara duramai Zagi Wanda shi Sam hankalin shi baya jikin shi burin shi kawai ya kara ganin wannan kyakkyawar fuskar da ta hana rayuwar shi sukuni fuskar dake hanashi bacci fuskar dake sanyashi ciwo a duk lokacin da ya tuna ta "


"Wani irin juyawa yayi domin bin mashin din da take kai ya koma inda yafito " domin yayi Alwashin bazai kuma bari ta kubce mai ba again don zai iya mutuwa muddin ya bari ta bace mai a yau'



"Tabbas zuciyar shi zata buga " duk surutun mutane bai dameshi ba "burin shi kawai yau yaga farin cikin shi wato his dream girl"


"Dai dai kofar gidan da yabari ta sauka tareda biyan mai mashin din tafara takun ta cikin natsuwa batareda tunanin komai ba"


"Saurin sauka yayi batareda ya tsaya kulle kofar motar ba cikin sauri yabita lokacin har tasa kanta zuwa cikin gidan "


"Tsaya wa tayi domin jin wannan kamshin da bata mance mamallakin shi kafin tagama wani tunani yafado cikin gidan "



"" wani irin mugun karo suka gabza Wanda yayi sanadi yar tayi baya tana shirin zubewa kasa " cikin zafin naman shi ya fisgota " batareda bata lokaci ba ya Rungume ta cikin kirjin shi "


"Ita kuwa ta gama sadakar wa zata zube kasane war was " jinta a cikin wani kirji mai bala'in kamshi da kuma ni'ima " yasata bude idanunta "


"Sai akan fuskar shi mai cikeda da Annuri da kuma tsantsar yarinta" tayi saurin tureshi tareda fara koro ruwan bala'i"


"Au saboda rashin kunya biyoni kayi gidan mu ? Har kake kokarin Hada jikin ka da nawa " wallahi Allah ya isa " batareda ta jira komai ba ta shigewar ta"


"Sukuwa yan tsegumi tuni sunyi cin cirin do suna kallon wannan dramar ta Ruman da kuma kyakkyawan gayen " tareda tanbayoyi masu yawa a zukatan su"


"Biye yake da ita kamar gaula har zuwa cikin falon Hajiya batareda damuwar komai ba yake binta kamar jela..........✍



*Akwai cakwakiya kenan jama'a Ruman da Bature Wanda zan warware muku waye shi idan har kuka ci gaba da biyoni A cikin wannan littafi nawa mai suna KUSKURE NA*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KUSKURE NA*🙆
_Love & Destiny_

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
_written by Fenerh_

~Dedicated to~
All my fan's


💫GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫

*Jama'a don Allah duk w'anda yaga kuskure a cikin rubutu na hanya Abud'e take' domin dan Adam ajizi ne tara yake bai cika goma ba, nagode*

🅿➡3⃣

"Tafara tsorata da lamarin wannan Aljanin yaron " cikin zare ido ta waigo shi jin takun shi a bayanta cike da masifa tafara " waikai dakikin wane garine ?


"Wane irin jakanci ne haka? Dabba ne kai da zaka shigo cikin gidan mutane batareda izini ba " koda yake idan nayi la'akari da yanayin ka nasan kasar da kafito Akwai karan cin Addini da kuma tarbiya"


"Jin hayaniyar ta yayi sanadi yar Fitowar Jama'ar dake gidan har ma Hajiya dake sanye da hijabin ta hannun ta rike da carbi tana istigifari da Alamar Salla ta idar "


"Kowa yakasa cewa komai ganin irin wannan had'add'en gayen yaro a tsaye ba Abinda yakeyi sai kallon ta "

"Hajiya tayi saurin taron ta ganin irin zagin da take shekawa bawan Allah"

"Haba Ummu " wannan ai batarbiya bace ' kin saki baki kinata zagin d'an mutane " ba irin tarbiyar da na baki ba kenan "


"Hajiya idan ba raini ba ya zai rika bina sai kace ni sa'ar shi ce?


" Salati Hajiya ta saki domin jin son girman na Ruman ya girmama " yo wannan Zatace ta girma?


"Shikuwa tuni ya dawo cikin natsuwar daga dogon tunanin da ya tafi " ya kalli tsohuwar mai cikeda kwarjini da kuma haiba "dattijuwa mai kyau da kuma kyan hali tareda ta wakkali"


"Karasa wa yayi cike da ladabi " Mama ina wuni? Cikeda lafiyayyar hausar shi mai hade da wani irin salo irin na Wanda yatashi cikin harshen nasara "


"Nine w'anda zai zauna a nan gidan, muryar shi cikin natsuwa ga wani irin salo mai dad'in saurare "


"Ita kanta tayi mugun jin mamakin wai hausa yakeyi " ta zaro ido tana kare mai kallo y'anda ya tsuguna gaban Hajiya "

"Ko zagin da tayi mai da hausa tayine da gangan bata taba kawo yanajin hausa ba"


"Kuyi hakuri don Allah bata sani bane shiyasa " ya juya cikeda wani irin kallo mai tattare da fassarori daban daban"

"Na farko wahala ta takare nabiyu tausayin kanshi na uku tsantsar so mai cikeda damuwa.


" Cikin gaji yawa tareda sanyin jiki yace " Aunty kiyi hakuri ba ke nake bi ba '


"Ita kanta jikinta yayi sanyi sosai Amma hali irin na Ruman tayi wucewarta batareda ta kuma furta komai ba "

"Binta yayi da kallo harta shige cikin falon su" ya kara matsawa kusa da Hajiya " mama Don ALLAH Kuyi hakuri da abinda ya faru"


"Aa yaro kai zanba hakuri da irin Abinda jikata tayi maka ka yi hakuri kaji ba haka halinta yake ba An samu kuskure ne ALLAH ya huci zuciyar ka "

"Yace bakomai Mama ya wuce"

Isowar Ak ya tarar da wannan dramar " domin yazone da zancen sun Fasa zama domin ogan baya son gidan kuma ya sameshi a ciki "


"Ya karaso Yace "Oga' yayi saurin daga mai hannu " Ware is the room?


"Cikin rawar jiki ya nufi kofar da shi Sam tun zuwa nshi bai lurada itaba wato itace farkon shigowa gidan "


"Ya bude mai tareda cewa" hare is the room sir.

"Ya shiga tundaga falon dan madai daici ba laifi sofa guda dayace a ciki Wanda Ak ne yasakata hade da dan center table karami sai dan madai daicin plasma A.c da dan karamin firij duka a cikin falon

" cikin inner room din kuwa katuwar katifa ce irin hutadda gadon ka din nan taji duvet da kuma pillows gefen ta kuma harda mirror cikeda kayan kayan kanshin da yake Amfani dasu masu matukar tsada da kuma kamshi mai tsaya wa a rai"


" sir' hannu yayi saurin dagamai " atakaice yace " just go I will call you.



"Yana fita ya fada kan katifar mai dauke da lallausan kamshin room freshener Wata irin Ajiyar zuciya ya sauke tareda fitar da hawaye masu mugun zafi da radadi '



" shikadai yasan halinda zuciyar shi ke ciki'


"Ruman kuwa tana shiga cikin daki taji gaba daya ranta baya mata dad'i yanzu wannan ne zai zauna musu a gida?


" Hajiya na shigowa ta rufeta da fada " Ummu banson rashin tunani yanzu saboda Allah me yayi miki banson rashin da'a fa'


"Cikeda dauriya ta taso ta rungume ta " yi hakuri my kakus nayi laifi '


"Amma ina fatan ba shine mai hayarki ba?


" Shine. "sai yaya? " tab a she Akwai aiki kenan, " babba kuwa " kuma ba ruwan ki da shi ki kiyayeni'


"Don nafi kowa sanin halin ki, " halina mai kyau ne ko Hajiya ta? Eh amma watarana Akwai gyara a ciki ki kiyaye wulakanta mutum ko yaya yake'


"Kinga wannan bawan Allah bakisan ko waye shi ba Meya kawo shi dan gidan waye oho don haka ki kula "


"Banason ki yi sanadin jefa mu cikin wata damuwar muna zaman mu cikin rufin Asirin Allah'



" A gaskiya tayi nadamar Abinda tayi sosai ita kanta tasan ta zake da yawa haka Hajiya ta cigaba da Jan kunnen ta tareda nasohohin da 'ya kamata duk wata uwa tagari tabawa y'ay'anta,


"Ta tafi ta barta cikeda nadamar zagin da tayi mai ta tuna irin kallon da yake aika mata lokacin da take surfa mai Ashar Ashe duk yanajin ta "


"Ita Sam batayi tunanin yaji hausa ba da gangan tayi zagin


" kiyi hakuri Aunty shine Kalmar da tafi komai tsaya mata a zuciya "


"Ta dade a kwance cikin tunani kafin ta mike tayi Wanka tareda dauro Alwala "


"Tun Fitowar ta tasamu kanta da kallon kofar dakin nashi " ko yana ciki?


"Ita take wannan tunanin " to ina ruwana ko yana ciki?wata zuciyar ta kuma cewa,


" ya dade a kwance yana tunani kala kala daga karshe yafara jero murmushin shi mai kayatar wa



"Yana tuna y'anda take magana muryar ta very sweet her lips wow ya wani irin rintse idanu nshi tareda cije lips dinshi kadan ' tunawa dayayi da irin kirar jikinta


" he never imaging her structure kullum fuskar ta kawai yake gani a mafarkin shi ko haduwar da yayi da ita sau biyu fuskar ta kawai yake kallo but today """"""""" Hmmmmm.


"Yasan His dream girl is Awesome she is very sexy she have everything he wants her Boob's hip's her kissable mouth " more especially her expensive colour

"Ruman ta hadu iya haduwa shiyasa takejin tafi karfin kula duk wani karamin yaro bawai don kudi ba aa nata ra ayin kenan.

" yana tausayawa zuciyar shi da ta jarab ce shi da sonta juyi kawai yakeyi tareda shakar kamshin jikin ta da ya manne a jikin shi wani irin tashi tsigar jikin shi keyi


"Sakamakon tunawa da yayi da irin rungumar da ya yimata " Ashhhh ya furta da dan karfi tareda danne marar shi


"Oh my God ya furta a hankali' wayar shi ya janyo da kyar tareda neman numbar Ak "


"Cike da wahala yake magana a wayar " yace " zanturo maka sunan wani magani please ka kawo min yanzu "


"Ya kife wayar tare da nishi mai wuyar fitowa,


" cikin mintin da bai wuce sha biyar ba Ak ya kawo mai maganin " cikeda kulawa yafara tanbayar shi me ke faruwa ?


"Cikin jarumta da kuma karfin hali yace ' am OK please don't tell any one am going to be Alright"


"Yace " OK sir but please take care of ur self " I will don't worry "


"Bayan yasha maganin bacci mai dadi hade da mafalkai masu dad'i ya dauke shi "



"Washe gari da wuri ta shirya ta bar gidan domin sun shirya dasu hajara zasuje wani waje kafin lokacin lecture.




" Sun fara shirye shiryen dawowar yayan hajara daga outside country har anko suka buga na wani tsadadden code less su uku Wanda hajara ta dauki nauyin dinka musu '

"Sumy kuwa wasu irin tsadaddun jakun kuna designers da takalmin su ta siyo musu " ba yadda zatayi dasu domin ta San tanakin Amsa zasu fara complained


"Shiri sukeyi na musamman Hajara na cikin tsananin farin cikin dawowar d'an uwanta






" ya makara sosai yau saboda rashin baccin da bai samu ba jiya da wuri sai kusan Asuba ya samu ya rintsa a gurguje ya fada bathroom



"Ya dad'e a tsaye yana tunanin y'anda zai fara wanka a tsaye " yasaba da kwanciya a cikin jacuzzi ruwan dumin ya ratsa shi Amma gashi shine da wanka da wannan ,


"Rashin mafita yasashi runtse ido tareda fara wankan shi cikin natsuwa da kuma kyal kyale jikin shi ta ko ina



" karfe kusan goma yafito cikin shigar shi a koda yaushe wato kana nan kaya yana sanye cikin wandon Jean's baki tareda farar rigar T-shirt wadda aka rubuta *COOL* a gabanta



"Kafarshi na sanye cikin takalmin shi kamar kullum wato canvass fari ga wani Annurin kyau da fuskar shi ke fitar wa daka kalle shi zaka hango tsantsar kuruciyar shi


" cikeda natsuwa yake takawa zuwa cikin gidan " tunda yafito ma aikatan Hajiya kaka duk suka zubo mai idanu har mada masu siyan Abinci suna kallon Hutu da kuma wayewa "


Kofar falon nasu yayi sallama " w'anda Hajiya ce zaune a gefen ta kuma doctor Sulaiman ne suna hira kamar y'anda suka saba"


"Cikeda fara a tace ' shigo ciki dan nan Ak kaima kazama na gida " ya kutsa kanshi cikin falon " kamshin shi mai matukar tsada ya musu sallama " shi kanshi doctor Sulaiman kallon shi yakeyi "


"Yasan daga ganin wannan Ajebo ne " Amma meye dalilin shi na zama cikin wannan gidan duk irin hotels din dake cikin Garin na Zaria "


"Tuna nin shi ya tsaya ne a dai dai lokacin da ya mika mai hannu cikeda ladabi sukayi musa baha da lallausan hannun shi mai kamar Auduga



" Ya gaida Hajiya yana mai bin ko ina na falon da kallo " ba laifi ko ina fes domin Hajiya kaka Akwai tsafta sosai ga falon su ba laifi Akwai kayan more Rayuwa dai dai na mai karamin karfi tundaga firij TV da kuma kujeru "



"Wani irin ni shad'i yakeji a cikin zuciyar shi " yanzu Anan my dream girl take Rayuwa ? Yana mai Addu'ar dama tafito yasata A idanun shi '



"Hajiya ta katse mai tunani lokacin da take magana da Sulaiman" mutu miyar taka ko batasan kadawo

Please Login or Register in order to submit comment