Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba " kuma da wuya yau ta dawo da wuri don suna taya kawar su shirye shiryen wata hidimar da zasuyi gobe'


"Wani irin faduwa gaban shi yayi " tareda kallon gefen da doctor Sulaiman yake" to shi wayene nata? Mutu miyar shi? What was that means?


"Oh no yayi saurin kawarda tunanin shi domin jin zuciyar shi na wani irin har bawa " ya runtse idanun shi tareda tattaro natsuwar shi ,


"Mama Aunty fa? Tafita ne? " wai Ruman? Ai tun karfe takwas ta bar gidan nan " Ruman""" Ruman''' A cikin zuciyar shi yake nanata sunan " what a name


"Sunanta mai dadi kamar y'anda take mai kyau"


"Mikamai hannu da Sulaiman yayi ya dawo dashi daga duniyar thinking " Abokina have a nice day' tanks ya furta a hankali '



"Ya fita tareda yima Hajiya sallama da kuma Alkawarin dawo wa da dare "


"Wata irin wa wuyar Ajiyar zuciya ya sauke bayan fitar doctor Sulaiman haka kawai yaji bayason gayen


" Hajiya sarkin sabo har ta saki jiki dashi tana bashi labarin yar jikar tata da kuma irin son girman ta " wani irin farin ciki yakeji kamar yayi tsuntsu ya ganshi a gabanta " cikin dubara ya tanbayi sunan makarantar su"


"Wai ko Fct' yayi murmushi domin ya gano me hakan ke nufi"


"D'an nan ka ko ci Abinci? Aa bana break fast da wuri, "a'a kaidai kace Bazaka iya cin irin Abincin mu ba'



" No ba haka bane idan nadawo zanci a ajiye mun. ya mike tare da fita yana mai yimata sallama.




"Kamar koda yaushe kofar gidan d'ankam yake da mutane " batareda ya ko kalli gefen su ba ya fara takawa har zuwa wurin da motar shi ke fake "


"Ga badaya sun zuba mai ido har ya bar unguwar,gulma cike da zukatansu


" Yana fita a unguwar direct G.R.A naga ya nufa yafaka kofar wani lafiyayyen gida mai tangamemen gate "yayi horn yakai kusan sau uku kafin a bude gate din'


" A zuciye ya fito ko kashe motar baiyiba ya fito yayi shigewar shi cikin gidan batareda da yako kalli mai yimai magana ba "


Gaba daya body guard din shi suka taso cikin girma mawa " welcome sir"


"Hannu kawai yake daga musu cikeda izza da kuma yanga ya shigewar shi cikin wani lafiyayyan falo mai kofar glass w'anda saida yayi Amfani da hannun shi ta bude


" Subuhanallah falon ya hadu iya haduwa komai najin dad'in Rayuwa Akwai Kamar a Dubai kujerun ma kawai Abun kallo ne ga wani irin plasma mai kamar cinema a jikin bangon falon


" Wata hanya naga ya nufa ya zuge kofar da ita ma glass ce ya shiga cikin wani hadadden bedroom Wanda yaji wani irin lafiyayyan gado batareda ya tsaya bata lokaci ba ya fara kwabe kayan jikin shi yana mai cilli dasu a kasan dakin "


Yarage dagashi sai short Hmmm " kallon shi nafarayi tundaga kasa har zuwa saman shi ina mamakin wannan wane irin yarone mai kwarjini da kuma cikar zati ko ta ina jikinshi gashine akwance mai daukar hankalin duk wata lafiyayyar mace "


"Ga wani irin fadi da yayi daga sama kirjin ma cike yake da suma " bathroom ya fada saida ya cika shi da ruwa sannan yashiga daga ciki ya dauki kusan rabin hour ruwan na ratsashi kafin yayi wanka yafito


"Wurin shafe shafen kuwa ai ya dauki kusan hour daya " shafa wancan shafa wannan "


"Saida ya shirya cikin shirin nashi wato kananan kaya wannan karon fari ne Jean's din harda rigar itama da rubutu ajiki *SHE IS MINE* yafito cikin shigar farare har takalmin shi


" yana baza kamshi ya fito tareda nufar wani irin dining table Wanda aka jera Warmer's masu daukar ido "


"Dagudu kukun ya iso tareda fara serving dinshi Abinci daban daban irin naturawa yafaraci cikeda yanga " bai wani ci dayawa ba ya mike ya nufi hanyar waje '


"Ak yataso da sauri yana yana rikeda wayoyin shi " who call? Yafada cikin natsuwa kuma atakaice " shima yabashi Amsa " your Dad and Momy ' yayi saurin Jan birki " ya karbi wayar " what did you tell my parents?


"Jikinshi narawa yafara dialing number Dady " yana picking yafara yimai fada " ina yashiga tunjiya baka dauki waya naba ?


"Am sory Dady ya fada cikeda shagwaba " I was busy yerstaday " busy? Yes Dady I saw her and I no ware she is now "



"Dady katayani Addu'a kar Momy ta hanani Auranta. " saboda me? ur Momy is supporting u " no Dady she is a Muslim.



"What? Yafada cikin karaji " Don't let ur mother hear that "


"Cikeda sanyin jiki yace why Dady " u no why.


"Wasu irin hawaye ne suka biyo kuma tun shi ya janye wayar a fuskar shi " zuciyar shi na mugun bugawa ya fada motar shi Ak kawai ya shiga tareda tayarda ita Aka wangale musu get


"Sai bayan sunfita ya tanbaye shi ina zamuje? " F.C.E kawai yafada "



"Karfe shabiyu da kusan rabi suka danna motar cikin makarantar ' gabadaya dalibai sukabi lafiyayyar motar da kallo sunaso suga waye wannan a cikin wannan motar?


" Suna gefe sai hirar su sukeyi "Hajara Sumy da kuma uwar gayyar Wato Ruman " gefen su wani couse mate dinsu ne Abokin hajara sunata hira dashi duk da ba ruwanta da rayuwar samari Amma suna shiri sosai da Abdul sosai yana taimaka musu ta fannin karatu'



"Idanun shi ya sauka a lokacin da Ruman ta zauna a gefen Abdul tana mai nuna mai hand out dinta " wani irin mashi ya kuma cakar zuciyar shi " dama yana cikin damuwa "



"Batareda ya tsaya bata lokaci ba ya bude motar ya fito idanun shi jawur ya nufi wurin da suke Zaune " Wanda sai Alokacin Idanun su Hajara yakai kanshi


"Idanunta a waje ta tabo Sumayya dake gefen ta " Sumy kalli"""

"Cikeda kaduwa suka zuba mai idanun ganin su yake nufowa jikin su na rawa tareda jin dadi sosai saidai suna ganin yanayin shi sun San cewa a kidime yake "



"Idanun shi a rufe ya tsaya akansu kamshin turarenshi kawai ya sanarda ita cewar Akwai mutum akusa da ita Amma bata kawo shi bane "


"Yana huci ya riko hannun ta a firgice ta dago kanta domin jin wani irin shock a jikinta w'anda shima saida ya kusa faduwa saboda jin laushin hannun ta'



" you have to understand baby u are mine " banason ganinki da kowa ke tawa ce ki fahimci haka mana '


Ya fada cikin taushin murya irin ta gaji yawa gaba daya baki suka saki suna kallon shi har ita kanta tsoro ya kamata "



"Toh nima dai nace ba ayi komai ba Akwai aiki don haka muje zuwa ✍



*Matar Soja*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KUSKURE NA🙆*
_Love & Destiny_


_Written by Fenerh_

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
~Dedicated to~
All my fan's

💫GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫

_godiya cikin barrack fan's da irin comments dinku Amma ina neman kari, saboda inji karfin yi muku typin kamar yadda kuke bukata,ina mugun yinku masoya Fenerh_



🅿➡4⃣
"Wani irin kallo take aika mai mai cike da fitinu kala kala ga shi idanun jama'a ta ko ina Kowa ya natsu yana kallon su " ranta yayi mugun baci "


"Meye matsalar ta da wannan yaron? Zai zo ya y'ar fata a gaban students har ma da kawayen ta " cikin masifa ta fisge hannun ta batareda tunanin komai ba ta zabga mai lafiyayyan mari '


"W'anda atake hawaye suka biyo fuskar shi ya dafe gurin ya nabin ta da kallo.


" A rikice su Sumy suka taso suna me rike hannun ta da take shirin watsa mai wani marin "


"Hajara tace " haba Queen meye haka don Allah ? " ya zaki tanbaye ni meye haka bayan kina kallon irin renin da ya nunamin A gaban mutane.


"Ina nasan shi impact meye had'i na dashi? Saboda kana haya a gidan mu " that's doesn't give you the right to hold my hands "


"Gaba daya ta sakasu a cikin duhu suna bukatar bayani. A ina tasan shi? Haya a gidan su? Wannan dan gayun bature ?

" Abdul kuwa ai shi tuni ya ware "kowa mamakin karfin halin ta yakeyi ,

Kwasar kayanta kawai tayi ta yi wu cewar ta Jikin hajara na rawa ta fara bashi hakuri domin yaron yayi mata kwarjini sosai da bazata iya kallon idon shi ba"


"Ashe ranar kallon tsoro tayi mai Ashe duk zancen da sukeyi Ruman ta sanshi shiyasa take musu masifa"

"Hakuri suka ci gaba da bashi " ya share hawayen da kebin kuncin shi " Kuje karta hau bike please banaso '


"Maganar shi a takai ce kamar tana yimai wuya da sauri Sumy ta bita ita kuwa hajara bata gama kallon wannan baturen ba"


"Tareda mamakin bature da jin hausa ? " ki bata Hakuri please friend,

"my name is Hajara and the other one Sumayya but we call her Sumy " nice to meet you Hajara yafada cikin wani irin salo tareda mika mata hannu kamar y'anda Al adarsu take'


"Ta noke tareda girgiza kai ta fara tafiya cikin sauri ya bita " tell me more About your friend please ""


"Tsaya wa tayi cike da mamaki " Eh kifada min Ina son inji komai a kanta " ya fada cikin shagwaba " ita mamakin shi ma takeyi namiji da saurin kuka kuma gashi shagwababbe "


"Gaskiya baza su taba dai daitawa da Ruman ba "

"Ina jinki ' Am sory kaga yanzu muna Sauri zamuje gidan sune munada party gobe na taron brother na so till next time in mun kuma haduwa "


"No problem muje gidan nima a can nake zama, idanun ta a waje " kafin tace wani Abu yayi gaba tabishi cikeda tan bayoyi "


"Suna tsaye a jikin motar Hajara sai ruwan masifa take zubowa tana ganin su tare tayi saurin bude gaban motar ta shige Sumy sai ido kawai take binsu da shi saida ya karaso kusa da su ya dan duk'a yana kallon fuskar ta ta glass din windown motar "


"Ya dauki lokaci a haka Sannan ya mikawa Hajara hannu Give me the key. Jikin ta na rawa ta mika mai "


"Hannu kawai Yama Ak ya taso da gudu " drive them. Cikin bada umarni su basu ma fahimci mai yake nufi ba saida ya bude motar hajara ya shiga " tayi saurin jiyowa "


"Kafin tayi wani Abu yayi lock din motar tafara ruwan bala'i ya fisgi motar batareda ya saurareta ba ya harba ta" suma ganin ba suda zabi dole suka bi Ak



"Instead of ya kaita gida aa hanya ya d'auka saida sukayi nisa da gari sannan ya faka a gefen titi still tana kan rabtaba mai masifa "


"Ya kife kanshi jikin sitiyarin motar Ya saki kuka mai tsaya wa a zuciya,


" Gaba daya wuta dauke mata tayi ta tsaya tana mai kallon shi saida yayi mai Isar shi San nan ya dago idanun shi farare da suka canja kala zuwa kalar ja'


"Jikinta yayi sanyi sosai' juyowa yayi dakyau yana mai fuskan tar ta, cikin kwantar da murya yafara magana.




"Me yasa bakyajin y'anda nakeji a zuciyata' ya dafe k'irjin shi " my heart is beating very fast, zan iya mutuwa idan ta cigaba


"Am begging you Roman"" yafadi sunan ta cikin wani irin salo,


"Ki taima keni I no u hate me but please Roman Am begging you please Allow me to be with you I love you mothern my oun life



" baki San tsawon lokacin da na d'auka ina wahala ba tun ban ganki ba am here only bcos of you help me " ya karasa maganar shi cike da gajiya wa


"Wani irin kallo take yimai " ni kakeso ? Yes I love you and I can do Anything for u please"""'"


"How old are you?

" wani irin murmushi yayi mai dan sauti ya kalleta dakyau don yasan me take nufi da hakan ,

"Am twenty years old ' kallon shi tayi a dage

" saboda raini zakace kana sona bayan na girmeka da kusan shekara daya " ko dan kaga kayi girman jiki ka kuma Ajiye wani irin munafukin saje a fuska shi zai baka damar cewa kana sona"


"Listen mister man Am not your mate understood


"Ta yaya zan fahim ci cewa Kinfi karfina?

" kin taba ganin mace tafi karfin namiji?

"Ni kece mate dina kece dai dai dani ke nake so Roman ke kadai saboda ke na baro kasata batareda nasan cewa kina nan kasar ba


" that is our destiny ke kaddara ta ce tun lokacin da nafara zama namiji nafara mafarki dake zuciya ta na fadamin zan ganki zamuyi Rayuwa tare zaki soni zaki Haifa min yara"


"Dariya kawai ya bata ta wani kalle shi irin kallon ka raina ni "


"You are dreaming. Kallonta yake cikin idanunta kallo irin mai cikeda tsananin so da kuma sa daukar wa


"Am not dreaming, my dream has Already come true u are in front of my eyes "


"Cike da takai ci " you no what ? Just take me home before I do something stupid


"Ban sanka ba bansan sunan ka ba daga ina kafito kawai naganka ne a hanya sai kuma a cikin gidan mu da sunan haya ,


" Me kake nema a wurina? Nasan ba sona kakeyi ba don ALLAH ka fita a Rayuwa ta kaga jinsin mu ba daya ba shekarun mu ba daya ba ban San kuma Addini ba"


"Gaba daya jikin shi yayi sanyi" mu samman y'anda tafara zubar da hawaye " jikin shi na rawa yakai hannun shi zai share mata hawaye tayi saurin bugemai hannu " don't touch me,


"Listing to me please " kina maganar shekaru " ni nasan zan Isar miki k'arki raina namiji


"U are not man enoughp

" wani irin kallo ya ke yima ta "Roman u will regret your word's

" Kaine zakayi dana sani bani ba kuma Sunana Umma Ruman ba Roman ba,

"Dariya kawai yayi " OK naji nifa bakyason kisan ni waye ?


"I don't bloody care just take me home,


" Hmmm Roman ki kula ina sonki magana da wani namiji kamar kinamin wasa da Rayuwata ne bakiji y'anda najiba da bayanki da wannan yaron ba


"Ki rike wannan tunda na iya barin iyayena masu matukar kaunata saboda sonki to ba Abinda bazan iya yiba ki kiyaye wannan


" Bai kuma kallon gefen ta ba ya Yata yar da motar sai gidan su tunda ya fara tafiya take kallon shi domin ya bata tsoro " to wai shi meyake nufi da ita ne?



"Karamin yaro yana mata rainin hankali,

Yana fakawa ta bude motar ta fito ko kallon gefen shi batayi ba ta shige cikin gidan fuuuu kamar iska " tun a tsakar gida ta cire hijabin ta saboda tsabar jaraba ta fada falon Hajiya bako sallama " tasamu su hajara sun mimmike kafa sai hira suke kwasa da Hajiya gefe kuma Doctor Sulaiman ne har sun saba dashi saboda yanada saurin sabo"


"Batareda ta tsaya ba ta shigewar ta cikin dakinta ta fada kan gadon tareda Sakin kuka mai karfi


" Hajiya tace ALLAH ka taimake ni " waya tabomin ita yau ? Suna rige rigen shiga dakin ita da su Sumy " kowa sai faman tanbayar ta yakeyi lafiya?


"Ba Amsa saida tayi mai Isar ta sannan tayi shiru tareda saita kanta " Umma lafiya waya tabaki ? Hajiya ta tanbaya


"Kaina ke ciwo ta fada cikeda shagwaba tana sharbe" mtsww Hajiya ta ja tsaki tayi ficewar ta tana mita" ALLAH ya shirye ki wallahi sai kace Karamar yarinya"


"Doctor Sulaiman kuwa duk ya rude ganin y'anda ta shigo cikin gidan ya d'auka ko ciwon ta ne ya tashi saida Hajiya tamai bayani ya natsu tareda yin dariyar ta "


"Yaji takara shiga ranshi saboda yana kaunar mace mai shagwaba A rayuwar shi "


"Ita kuwa Hajiya na fita ta mike zaune " duk suka haye gadon suna son jin bayani " lafiya kuka zuba min idanu haka?


"Lafiyar kenan ki fada mana Meke faruwa mu bamu gane komai ba ki sanar damu kawai muna jira.


" A hankali tayi musu bayanin komai tundaga ranar da tafara ganin shi har zuwa ganin shi da tayi a gidan su da kuma Abinda ya fada mata A yau"


"Gaba dayan su suka runkun kumeta dakyar take numfashi " ku sakeni meye haka ?


"Ai dole mu rungume ki mu shafi tabaraki ko ALLAH zai bamu baturen mai son mu Kamar haka "

A Gaskiya ke mai sa'a ce Queen " tana musu kallon kun hau kace " wace irin sa"a ? Karamin yaron ne sa'a kuma daga gani ba musulmi bane


" aa ba kyau k'arki yi saurin kafirta mutum haka kawai" hajara tafada "


"Kije ke ki sameshi ki fada mai kina sonshi ya fita hanya ta "


"OK yana ina? Oh zuwa zakiyi? " Sumy muje " tayi saurin rikesu " ku wuce gida sai mun hadu gobe please banaso Hajiya ta sani "


"Tsaya wa sukayi suna mamakin ta "


"Sun sallami Hajiya ta rakosu Sulaiman sai binta yakeyi da ido Ita kuwa ko kallon gefen shi bata yiba

" Suna fitowa tsakar gidan suka same shi a tsaye " cike da iya yi hajara ta matsa kusa dashi '

"Hy friend. " Hy" ya fada yana kallon Ruman kamar ya had'iye ta


"Ta Ciro wani dan karamin I v ta mika mai " u are invited' hope u will come " ya fara duba wa tareda cewa " sure.


"Ya kalli gefen Sumy " hy Sumy how are you? Cike da jin dad'in ya kira sunan ta ta washe baki " _Am cool_


"Ita kuwa koma warta tayi batareda ta kuma bi ta Kansu ba


" Ya mika ma Hajara key din motar ta tareda cewa tank's " tace u are well come.


"Sun rabu tareda sabo mai karfi ya shige cikin dakin shi ita kuwa bata kuma lekowa waje ba tana son yin wanka Amma saboda kar ma ta hango shi ta hakura ,


" misalin karfe takwas na dare ta leko domin Gaskiya ta matsu ta yi wanka " A hankali ta shigewar ta " tana fitowa ta daura Alwala sannan ta shigewar ta tareda Ajiyar zuciya'


"Shikuwa tun Fitowar ta yake kallon ta don kar ta koma yasa ya boye karta gan shi har tayi Alwala ta shige "


"Koma wa yayi cikin dakin domin yayi jin yar zuciyar shi da kuma gangar jikin shi


" Wani iri yakeji a duk lokacin da ya ganta A Gaskiya idan har ba a mallaka mai ita ba Akwai matsala


"Yana mugun jin feelings akanta ba karamin kai zuciyar shi nesa yakeyi ba a duk lokacin da take kusa da shi ya tuna moment ago y'anda ta ke komai a natse ga tsab ta'


" Wani irin mur mushi yayi lokacin da ya tuna da irin son girman ta bayan ita kanta kuruciya na damunta "


"I love you Roman ya furta deeply,


" Juyi yafara yi kamar kullum idan yayi tuna nin ta ,



"Ruman kuwa yau marar ta taki bari ta runtsa tun tana daurewa har ta fara birgima akan gado " ganin Abin yafi karfin ta tafara hawaye tareda Addu'ar Allah ya yaye mata wannan jarabawar


"Tanason yin Azumi Amma tasan gobe ba halin yin haka saboda hidimar dake gaban su


Gashi yin Azumin shine yafi mata sauki domin yana rage mata damuwar


" Ni shin da take fitar wa yasa Hajiya shigowa dakin domin tana zaune a falo "


"Ta shigo a rude Ummu badai kan bane ko?


" tana dafe da Mara tace " Cikina Hajiya zan mutu" .
"Jikin Hajiya na rawa tace na shigesu ni yar nan wannan wane irin Abu ne haka?

" ta fita ta rarumo wayarta tafara laliben numbar doctor Sulaiman Amma shiru bai daga ba " ganin Wankin hula zai kaisu tsakar dare yasa ta ruga waje " Wanda yayi dai dai da Shigowar shi " A kidime ta fara cewa dan nan katai makeni kar in rasa ta ita kadai ta rage min ita kadai nake gani inji dadi"


"Cikin rudu yafara tanbayar ta Mama waye ? Ummu,,, Ai bai ko gama jin baya nin ba ya fada cikin falon

" Tun daga shigar shi ya jiyo kukan ta dakin kawai ya fada mai dauke da sassanyar sanyin ta da kuma na turaren wuta


"Batareda tunanin komai ba ya rikota " w'anda saida sukayi Ajiyar zuciya a tare duk da tana cikin ciwo.



Jikin shi narawa batareda ya damu da Hajiya ba yafara kiranta " baby" what happened?


"Hajiya ma sai salati take duk ta rude A hankali ya kwantar da ita ya fita da saurin shi sai gashi dauke da wata yar Karamar Akwati ya bude tareda Sanya mata wata irin na ura akan yatsan ta ya kunna Hajiya na tsaye tana kallon ikon ALLAH"



"Ya dauki lokaci sannan ya cire ya Cire ya kalleta sai juyi takeyi tana rike cikin ta " Ya Ciro sirinji ya zuko ruwan Allura Hajiya ta fita da Sauri domin ita kanta ta tsani ganin tsinin Allura "


"Ya Ajiye agefe tareda dagota cak kamar wata y'ar baby ya rungume ta sannan yasa hannun shi ya yaye Hijabin dake jikin ta "


"Wani irin mugun bugawa kirjin shi yayi domin daga ita sai towel wannan hijabin ne dama ya rufe jikinta tun Fitowar ta daga wanka ko Salla batayiba tafara jin ciwon ,



"Dakyar ya iya dai dai ta kanshi ya dan kawar da kanshi ya zame towel din tareda janyo hijabin sannan ya laluba yayimata Allura Wanda saida tayi wani irin zillo ta shige jikinshi


" w'anda yayi sanadi yar daukewar numfashin shi na kusan min tuna sai dakyar ya jawo shi ya samu ya mike cikin tangadi ya tattara kayan Aikin shi ya fito bai ko iya yima Hajiya bayani ba tana godiya ko iya Amsata batayi yayi waje



"Dakin shima kasa komawa yayi " yana fita wayar Ak ya kira " yace suzo yanzu'


"Cikin minti goma suka iso harda body guard din shi yace su kai shi G.R.A



" Ita kuwa bayan yimata Allura bacci ne mai dadi ya dauketa Hajiya a kusa da ita ta kwanta tareda zare mata Hijabin tana mai yimata mitar rashin sa kaya"


"ALLAH dai yasa a hannu ya miki Allurar "



"Gaba daya ranar bai runtsaba ciwon shi ya dawo danye sharab dama shi kadai yasan irin famar da yake yau gashi yayi ganin Abin da zai dameshi


" laps dinta kawai yagani hankalin shi yatashi Inaga yaga mai gaba dayan


"Ranar tsabar fitina har kuka yayi gashi ciwon yafi na kullum" ai Ak da gudu ya fita ya kira numbar MAMAN shi " yamata bayani domin gudun faruwan wani Abu yasan idan har wani Abu ya sameshi tsab za akulle shi saboda tsaron lafiyar shi yake tare dashi"


"Gaba daya ta tashi hankalin ta cikin daren taso ta biyo private jet dinsu Amma Dadyn shi ya bata hakuri ta jira Gari ya waye shima zai je "



"Sam bata cikin hankalin ta shi yasa bata tsaya tunanin komai ba ta hakura da maganar shi


" Kafin safe kuwa har suma yayi gaba daya hankalin Ak ya tashi


"Ganin Wankin Hula zai kaishi dare yasa suka kwashe shi sai Asibiti " cikin gaggawa suka Amshe shi tareda daura mai drip "



"Koda gari ya waye garau ta tashi Abun ta kamar ma batayi ciwo ba Hajiya tafara cewa " kai nagode wa wannan yaron ya taimake ni ALLAH ya mai Albarka "


"Cikin kidima tafara tariyo Abinda ya faru jiya " ranta yayi mugun baci domin ta tuna komai "


Shi kenan zaiji dad'in rainata dakyau ya shigo har cikin dakinta yaga gadon baccin ta✍



*ku taromin Ruman fa my fan's tanada matsala babba mutumin da ya taimake ki?*


_*Matar Soja*_
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KUSKURE NA🙆*
_Love & Destiny_


_Written by Fenerh_

~Dedicated

Please Login or Register in order to submit comment