Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi da yake hangowa a fuskar ta,



Cikin sauri ta sanya kaya tareda zura dogon hijabin ta ta dukun kune akan sofa'


Koda ya fito tsayawa yayi yana mamakin ta "duk lokacin da ya tabota zata badakai sai daga baya kuma ta botsare mai kuma girgiza kai yayi ya wuce gaban mirror ya shafa mayuka da turare masu kamshi sannan ya zura short nicer da singlet kawai ya haye ga donshi yana hangota har bacci ya dauke ta,



Wayewar gari
Ahankali take bude idanun ta na bacci domin jin Ana shafa mata fuska cikin wani irin siga,


Tar ta karasa budesu domin ganin ta dukun kune a jikinshi duk ya laulayeta suna fuskan tar juna tayi saurin wuntsilawa ta sauka tareda kallon jikinta,


Waro idanu tayi duka a waje " ina kayana ? Domin tik yayi mata tayi saurin janyo hijabin ta dake yashe a kasa ta daura,


"Abdul wai don Allah meyasa kakemun irin wannan Abun ne?


murmushi yayi tareda mika " Ya za ayi inkwana daki daya da matana Amma ta kwanta a kasa ni a gado bayan ina kallon ta impossible,



"Waye Matar ka? " Ummu Ruman' shirme kakeyi sai dai ko a mafarkin ka kake tunanin hakan,


"Aa a zahiri ne Amma inbaki y'arda ba ai nasha Amarci na a daren Shekaran jiya shiyasa nakasa daurewa kina baccin ki mai dad'i na dakko ki,



Saurin shafo jikinta tayi domin taji ko yayi mata wani Abun ta tuna hakan bazai taba yuwuwa ba batareda tasani ba bayan ma Akwai dinki a jikin ta,


" meyasa ka cire mun kaya? Murmushin shi yayi na tsokana tareda d'an kukan shagwaba kadan" yunwa naji shiyasa na cire miki kayan domin insha Abinci na,.



"Tayi saurin shafo k'irjin ta sai Alokacin taji yana mata wani irin mugun zugi,



" Innalillahi Allah ya hada ta da jarababben yaro,


Wucewar ta kawai tayi domin yin wanka domin tasan dole ma tayishi saboda ita ta d'auka mafarki takeyi Ashe a zahiri ne Abun ya faru'



Tana fitowa ta tayarda Salla Shikuma ya shiga domin Akwai tafiya a gaban shi'


Tana idar wa ta shirya cikin doguwar Riga har kasa saidai ta kamata dam ga kirjin nan sun kunburo kamar an hurasu sunkara cika fam hip's din ta ma ya fito sosai kamar rigar zata yage ta taje kanta tareda daure shi cikin ribon ta shafa powder ta dan murza wet lip tayi matukar yin kyau ta nemi dan karamin gyale mai v ta Yane kanta dashi ta sanya d'an karamin manne na diamond da ya siyo mata ta dakko farar boyfriend jacket ta dora sama saboda rigar batada hannu,



Tunda ya fito daga bathroom din yake tsaye yana kare mata kallo ta tafi da brain dinshi gaba daya ko motsi ya kasayi saida ta fesa turaruka ta juyo zata fita ta lura dashi a tsaye kamar ya sume,



"Saida tafara takawa zata fita ya janyo numfashi yayi saurin taku zuwa gareta fisgota yayi ya rungume ta tsam tsam a cikin jikinshi'


" Ina sonki Ruman ina sonki ya fara dora mata kisses a fuska har zuwa kirjinta kamar ya hadiye ta yakeji'


Ta fara kokarin kwace wa " kabarni mana saika bata min kaya da ruwan jikin ka' "Oh sory kece ai kika rikita ni " come I forget to gave you your promise,


Jan hannun ta yayi ya nufi gefen gadon da ita saida ya zaunar da ita sannan ya nufi Waldrop din ya Ciro wata Leda ya dawo gaban ta,


Budewa yayi ya Ciro wasu kwalaye guda biyu ya mika mata'


"Open it' ya furta ta fara bude babban ta ga kwalin wayane sabuwa dal ta buga tsalle tareda rungume shi domin tana matukar bukatar ta,


Yaji dad'in y'anda ya sanya ta farin ciki kawai don ya bata y'ar wannan wayar,


Da kanshi ya bude dayan kwalin ya Ciro wata y'ar Karamar akwati tareda budewa,


Wow masha Allah sarka ce d'an kareriya ta zinari Akalla zatakai kusan million daya harda Agogon ta da kuma a war waro,


Duk da batasan zinari ba Amma tana ganin wannan sarkar ta gane ta zaro idanu waje domin Abun ya Bata tsoro sosai ina zata kai wannan sarkar tab idan tasa wannan tafita a nija ai sai yan fashi sun bita,



" Abdul: yayi saurin rufe mata baki " banason godiyar ji nine ya kamata in gode miki domin kin bani Abinda yafi komai tsada da muhimnci A Rayuwa Ruman nidai Addu'a ta shine kisoni ki nunamin a bayyane kowa yasani cewar kina sona

Ina mafarkin samun kulawar da ta dace a wurin ki '


"Don Allah ki taimaki Rayuwa ta k'arki bari Dady ya rabamu



" ke mallaki nace nikadai kuma na y'ar da da hakan "jikin ta yayi mugun sanyi taji matukar tausayin shi tasan yana sonta sosai itama kuma tana sonshi ita tasan Abinda ya gifta a tsakanin su muguwar kaddara ce kuma tana fatan Allah ya sa ta tsaya Anan,



" bari in shirya kinsan inada tafiya, ta ce OK a sanya ye, daukar sarkar tayi ta A dana ta dauki wayar ta tafita zuwa dakin Momy........✍





*Matar Soja*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KUSKURE NA🙆*
_Love & Destiny_

_Written by Fenerh_


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain✍🏽~*


🅿➡2⃣8⃣

Ya shirya cikin kana nan kaya tareda daukar wayayoyin shi da kuma system din shi kamar w'anda zaije Aiki,


Ya fito yana zuba kamshi tana zaune a falon tana faman danna wayar ta ya shigo, dago kanta tayi tareda zuba mai idanu domin ya mugun tafiya da ita,




Karaso wa yayi kusa da ita ya ya d'an duk'a kadan tareda hura mata iskar bakinshi ,

"Hy wannan kallon fa My Queen? Ta dawo daga tunanin da takeyi ta kauda kanta gefe'

" ni ba kallon ka nakeyi ba mema zan kalla? "Abin kallo mana ai nima inada Abin kallo bake kadai bace kikeda shi,

" ko baki y'ar da ba in nunamiki ta waro idanu tana mamakin halin Abdullah shi gaba daya sun raba hanya da kunya,


"Ni zan tafi My Queen kiyimin Addu'a ya danyi kissing fuskar ta har zuwa kirjinta sannan ya mike zuwa dakin Momy,
..


Ya dauki lokaci kafin ya fito yana Rungume a jikinta kamar wani jariri karaso wa yayi ya riko hannun Ruman ya ce " muje arakani,


Ba halin musu dole ta mike ya rike hannun ta suka fito Amma suna takowa wajen gidan wata kyakkyawar sabuwar mota budaddiya ta faka ,


A cikin wata yarinya ce baturiya ta dau wanka irin nasu na rashin kunya " yaja yatsaya tareda Sakin hannun Ruman yana murmushin jin dad'i ya nufi wurin ta,


Ita ma Momyn dad'in takeji domin Abun ya nuna a fuskar ta,


Tana fitowa ta D'ane shi "Natasha" oh my god longest time ya fada shima tareda bata fake a fuska,


Itama ta mayar mai " oh man I missed you so much,

"But am very angry with you' ta fada tareda bata fuska " ya kuma rikota zuwa jikin shi yana bata hakuri domin yasan laifin shi na zuwa bai nemeta ba,


Saida suka gama shirmen su sannan suka karaso Ruman da ta zuba mai idanu ranta na tafasa jitake kamar kirjin ta ya fito tsabar bakin ciki,


"Wallahi Allah ya wadaran rayuwar bature Sam ba tsari komai nasu ba Addini,


Wani irin kallo ta jefa mai w'anda ya kada y'an hanjin shi ta juya cikin gidan cikin sauri,
.

Yayi saurin kiranta" Ruman My Queen wait Amma ina ta shige da gudu ya bita Amma kafin ya shiga har ta shiga dakin ta kulle ta ciki,


Yayi kiran duniya taki budewa gashi ana jiranshi dole ya tafi,


Ko Sallamar Natasha bai tsaya yiba ya wuce domin itace sanadi gaba daya ta bashi haushi,


Momy ma kiss kawai ya manna mata ya wuce' Tunda ya shiga mota ya dafe kanshi tareda runtse idanun shi" oh Allah help me "


"Wayar shi ya bude ya tura mata message " Am sory my Queen she is just a childhood friend noting else'


"Tana jin tafiyar shi ta fito ta yi zaune a bakin gadon tareda dafe kanta tana mai jin zafin Abun a cikin zuciyar ta,


Wayar da ya bata ta janyo domin duba numbers Amma babu kodaya'


Karar Shigowar msg yasa ta saurin dubawa taga sakon shi ta karanta tareda zabga uban tsaki " kai ka sani'




Nigeria
"Jafaru ban gane ba kayi mun bayani ina kuka kaimun yarin ya?

Hajiya dake zaune tareda su Gwaggo Amina har ma da magaji' gefe daya kuma baban Ruman ne har da bilkisu tana sauraran gulma,


" Inna kiyi hakuri Ya tafi da ita ne can kasar waje ba Abuja ba sai bayan ya tafi ya kirani yake fadamin kuma kafin inyi magana ya kashe wayar shi Amma yau dinnan zanje,



"To mai zaisa ya tafi min da yarinya batareda sanina ba? Gwaggo Amina ta ce" yaya ai dama damusa tayi gudu d'anta yayi rarrafe? rashin hankalin da suka shuka dole yayan su suma suyi


"Ni me zaisa ya dauke ta ma ya tafi da ita wata kasar ?

" Wallahi ku saurareni idan wani Abun kuka kulla to zaku war ware shi in wani Abu yasamu jikata duka ranku sai ya baci'


Magaji dake gefe yayi shiru sai yanzu ya dago idanun shi cikin bacin rai" yarinya daga zuwa wurin bikin kawarta sai kawai muji wai Abdullahi ya dauke ta wannan wane irin shirme ne?


"Dama kundawo cikin rayuwar mune don ku tayar mana da hankali? To ai da baku dawoba kuci gaba da zama da wa inda kuka zaba fiye damu ,

." waini dakata kodai wannan dukiyar bata Allah da Annabi bace? Kodai siyar min da jika zakuyi?


"Haba Inna ya kike fadar haka Kuyi mana zaton Alkhairi kuma inaso ki sa Aranki ba Abinda zai faru da Ruman yau dinnan zanje UK din zuwa jibi zan dawo miki da Ruman dinki'


" Mama ki kwantar da hankalin ki don Allah bakomai Abdullah bazai cuci y'ar uwar shi ba ki kwantar da hankalin ki'


"Muhammad kamun shiru " ai nasan dama ba son Ruman kake yiba don haka komai ya sameta Bazaka damu ba,


"Haba MAMA kidaina fadar haka Ruman fa gudan jini nace ya Zanki ta? " yo sau nawa Meka sani akan rayuwar ta,

"Don haka Jafaru kafata kafarka nidai ka kaini wurin jikata'


" Shiru kawai tayi domin Abdullah ya sakashi a uku dama idan har ka sabawa naka iyayen kaima sai y'ay'an ka sun yi maka fiye dashi'


"Yanzu ta ina zai fara fadawa iyayen shi cewar Aure Aka daurawa Abdullah da Ruman?.



Y'anda Abin ya faru,

Malam Abubakar mai Almajirai shine w'anda ya musuluntar da Abdullah ya kumasan tarihin komai da kuma dalilin zuwan shi Nigeria'


" ya sameshi tareda mukhtar yayi mai bayanin komai dangane da sharadin mahaifin shi akan cewar in har ya fadawa wani nashi zancen soyayyar shi da Ruman bai yafe ba,


Bayan dogon nazari dattijon ya hanga ya hango cewar barna na iya Afkuwa domin a wannan zamanin w'anda ma ya rayu a cikin musulunci tun haihuwar shi ya yakare bare kuma w'anda bai gama sanin haram cin komai ba yasan Al adar bature ba tsari idan har bai dauki mataki ba za a haifi da Mara ido'


Yasa ya samu wakilai guda biyu ya wakiltasu waliyai ya nemi Abdullah da ya bayar da sadaki A daura musu Auren jikin shi na rawa ya bada dubu Dari biyar domin baida wasu kudi da yawa a hannun shi a lokacin,


Sai bayan Andaura ne ya bawa malam number Dady,

.Dady yayi matukar firgita da Abinda Abdullah yayi ya kuma kirashi yayi mai fada sosai kuma ya fada mai ya rubuta mai Sakin Ruman ya turo tun kafin kowa ma ya ji


"Daurin Auren yazo dai dai da ranar sa lallen Sumayya Abdullah da kanshi yayi ma su hajara bayanin komai ya kuma rokesu da karsu fada mata don Allah shine kuma ya shirya musu dinner da yaje har ya dauke Ruman a wurin,


Shiyasa hajara ta dage wajen sawa Ayiwa Ruman gyaran jiki sosai,


Domin tun kafin A daura Auren tasan shirin shi'

" kinsan halin kawar ki bazata taba bada hadin kaiba idan har na tsaya wasa inaji ina gani zata Auri wani bayan tana sona kuma ga Dady na,




Sunji dad'in lamarin saidai sun San Akwai matsala nan gaba a cikin family,


Sai yanzu Dady ke da yasanin rashin fadawa iyayen shi da kuma d'an uwanshi Abinda ke faruwa gashi yanzu komai ya kwabe,





Hajiya dai ta dage zata UK jama'a Bayan sun fito Dady ya kasa zaune ya kasa tsaye a dole ya samu d'an uwanshi ya yi mai bayani tareda bashi hakuri'



"Murmushi yayi mai cike da jin dad'i" Alhmdulillah nagode wa Allah " kasan cewa A kullum tunani na bai wuce waye Ummu zata Aura ya rike mun ita Amana ba,


"Naji dad'in wannan Al amarin a Gaskiya kuma nayi farin ciki'


" Amma banji dad'in y'anda ka hanashi fada ba Yanzu kaga KUSKUREN ka a nan ya nuna ma zamani
Dariya kawai yayi '




"Bilkisu kuwa wani irin farin ciki takeji don a tunanin ta Asirin ta ne ke aiki Tunda har aka gudu da Ruman,


Wani gefe kuwa dariya take yiwa sopy " shegiyar yarinya ba kin nace sai kin sameshi ba to shi ya dauke y'ar uwar shi sun tafi sheke aya a kasar waje " Allah yasa ta dawo musu da ciki muga karyar soyayya nasan bakin ciki zai kashe tsohuwa,



Dariya kawai takeyi Abunta' Hajiya dai ta shirya tsab su magaji na kara zuga ta,


"Karfe daya jirginsu ya daga zuwa UK' tafiya ta tafo Hajiya za'a UK,



Tun tafiyar Abdullah take zaune a cikin dakin gaba daya jikinta a sanyaye yake Momy ce ta shirya cikin zuwa Aikin ta ta leko ta ce ta shirya ta bita saboda zaman kadaici ba dad'i,


" tayi farin ciki sosai kobanza zata rage tunani ta shirya cikin Riga da wandon Jean's rigar ta sauka har kan guiwarta saidai batada hannu sai ta kuma dora wata boyfriend jacket din akai ta nemi mayafi ta nade kanta irin na musulman America ta saka wani takalmi mai d'an tudu ta dauki wayarta ta fito tana baza kamshi,


Momy ma ta yi matukar burge ta ta rungume ta tareda manna mata fake a gefen fuska " looking great my daughter'


"Tayi dan murmushi " tank you Momy, security ta ko ina suka shiga motar Sun fara tafiya kenan a cikin lafiyayyar lemoxen din Momy wayar ta tayi kara tasan shine don ba w'anda zai kirata sai shi,

Kin dagawa tayi ya kuma turo mata da msge Tanaji " Momy kuwa tana aikinta a laptop,


Wayar Momyn ya kira tayi picking " hy son ya fara zuba mata shagwaba ta d'an kalli Ummu dake wasa da wayarta tayi connecting da laptop dinta ta haska mai Ruman'


"Muryar shi kawai taji " hy my Queen " please kiyi hakuri fushin ki zai jefani cikin matsala ki rufamin Asiri'


Murmushi kawai ta aika mai tareda gyada kai tana kallon shi yana kwance a tafkeken gado lafiyayye dagashi sai boxer'

"Baby Am missing you " dole ce tasa natafi da ba inda zan tafi inbarki. Wallahi kamar indawo,


Baby ki warke please kafin indawo inba hakaba zan iya hauka cewa kin lasamin Zuma mai wuyar mantawa pray for us so that everything will be Alright,


"Ajiyar zuciya kawai ta sauke tana mai binshi da kallo ita har mamakin kanta takeyi wai wannan yaron ne ya gama da ita shine ke Jan ragamar rayuwar ta shine sirrin ruhin ta A Gaskiya jarumtar shi tasanya ta kara kaunar shi ya nuna mata Asalin jarumta,


Jinshi take sosai a Gaskiya ita kanta tasan cewa tana matukar kaunar shi Tunda har ya rabata da pride dinta bataji haushin shiba ya kamata ta kyamaci hakan a matsayin ta na y'ar musulma " shin wai meke faruwa da itane haka Anya tayiwa Hajiya Adalci?


"Ruman ya kira sunan ta " what are you thinking? Ta girgiza kai " Momy ta karbi laptop din ta ce ya barsu sun iso office ya kira Anjima'


Ya zaro ido" office da Ruman Momy Noo please tell driver to take her back '


"Why son ? Yace Akwai maza da yawa bai y'arda ba su kalle mai mata saidai ta koma gida tanajin rigimar shi '


Haka kuwa driver ya koma da ita gida bayan har sunkai company tana sauka ya kirata ta d'auka


" Meya sa kake mun haka ? Abdul ka raboni da kasata ka Rabani da pride dina kuma yanzu katafi Abunka ka barni a nan fitar ma yanzu ka hana inyi saikace wata Matar kulle,


"A sanyaye take maganar domin yanzu Sam bata iya daga mai murya batasan dalili ba,


" am sory my Queen nayi laifi Amma ki fahimce ni " soyayyar ki ce sanadi ina kishin ki"


"Banason ko kallon ki wani namiji yayi kiyi mun Alfarma daya Ruman don Allah no matter what k'arki bari a rabamu zan iya rasa Rayuwa ta,



Wani irin dad'i takeji har cikin zuciyar ta domin Yanzu ta kuma sakan kancewa da irin soyayyar shi a gareta


Don da jikinta yake so ai yanzu ya samu zai gujeta amma sai karuwa da soyayyar ta tayi a cikin zuciyar shi


Meyasa batajin bakin cikin Abinda yayi mata? " saboda kinason shi kema wata zuciyar ta fada mata,



A haka ta wuni daga kwanciya sai Sallah ita kadai a gidan kamar mayya sai kuma su Helen mai aiki,



Sai washe gari su Hajiya suka iso Uk tayi wujiga wujiga a lokacin ma Momy ta fita ita kuwa bacci kawai takeyi hankalin ta kwance,



Kamar a mafarki taji muryar Hajiya " Ummu Ummu " ta d'an bude idanun ta domin gasgatawa


Wani irin ihu ta buga domin bata yi tunanin ganin ta ba,


"Aa sakeni ja'ira bayan kintaho kinbarni inashi ja irin yake da ya taho dake?


Dariya tayi cikeda mamaki " Hajiya ta kece a UK ? "Eh y'ar wofi dana nima ya kawoni,


" kai naji dadi Wallahi domin nayi ke warki sosai "matsa can a ina kikayi kewata keda ke baccin ki hankali kwance ni kuwa inata fama da tunani " ai dana sani bazan zoba,


"Yi hakuri my kakus nan ma ai gidane' eh ina baturiya take? Badai tayi miki komai ba ko? " kai Hajiya don Allah kiyi shiru Wallahi Momy batada matsala kune baku fahimce taba,



"To naji Yanzu ina Abdullahi yake? " baya gari tunjiya ai" dama dole ya gudu Tunda baida Gaskiya ina nan ina jiranshi zai dawo ya sameni'



Dariya kawai takeyi domin tayi matukar farin cikin ganin kakar ta mai sonta,


Mikewa tayi " bari inkawo miki Abinci da Kaina kakata'



"Kallon dakin kawai takeyi tana ganin Aljannar duniya A ce yayansu ke Rayuwa cikin wannan daular ' ai dole su manta da iyaye,



Abincin Hajiya kebi da idanu " Ummu ina Abincin yake sai ganye d'anye kawai nake gani '


"Ai Hajiya shine Abincin " wannan ? Babu tuwo ? "Hajiya tuwo a nan tab ai Wallahi ko masara basuda ita ta tuwo sai dai ta gwangwani,


" aa da sake kiramin Jafaru "yo ko a makka ai Akwai wurin masu tuwo bare nan,


" shigowa yayi dakin yana dariyar Hajiya domin ya na jinta " Inna sannu ya gajiya? Ai har yanzu Akwai ta Tunda banci tuwoba,


"Jafaru wannan ai yafi makka nisa ko? " Hhh eh Inna Akwai tazara a tsakani"bari a kawo miki Abincin da zaki iya ci'



"Ai ni da ka fadamin har kuka ta zan riko mai kyau da kuma garin dawa Amma wannan ai mutum zai horu ,


_" nima nagaji da cin burodi_


"Saida tayi kat da namomi tanaci tana tanbayar Ruman" Amma wake musu yanka kaddai mushe muke ci?


"Dariya Ruman tayi tace " to kidaina ci kawai Kakus dina nayi ke warki Wallahi sosai "


Gafara can a ina?
Haka sukasha hirar su har zuwa dawowar Momy,


"Hajiya tayi matukar mamakin irin tarbar da ta samu a wurin Momy don har Dukawa tayi wajen gaisheta,


" ke ce ta mike tunda batajin hausata' ta ce ma Ruman dake kallon gaisuwar Hajiya da Momy kamar ta tuntsire saboda dariyar da ta kunshe,


A gefen Dady kuwa gaba daya masifa ya sauke wa Momy akan cewar ita ke daurewa Abdullah gindi shiyasa ya aika ta Abinda yayi yanzu' kuma ta fada mai ya dawo ina jiranshi yabani takardar yarinya don bazan dauki sakar cin shiba.....✍


*Matar Soja*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KUSKURE NA🙆*
_Love & Destiny_



_Written by Fenerh_
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain✍🏽~*

_Domin ki SA'ADATU BINT ABDULLA, Uwar marubuta ina matukar farin cikin y'an da kike bibiyar wannan littafi nawa Wannan shafi sa daukar wace ga duk wani member na BOYAYYEN AL AMARI kuma muna neman Alfarma da ki karasa mana wannan labarin kafin Muyi zanga zanga, masoya ina Alfahari da ruwan comments_


🅿➡2⃣9⃣

Ruman tasamu wal wala sosai da kuma farin ciki zuwan Hajiyar ta, Abdullah kuwa tunda yasan sunzo bai kirata ba har tsawon kwana biyu ga shi Dady ya je meeting a Chicago Momy kuwa kullum tana wurin aiki watara na ma sai dare take dawowa,


"Hajiya kaka kullum mita " Wace irin Rayuwa ce wannan mata aiki miji aiki shima tilon d'an su yawo sunemo su bashi ya kashe '


"Kallon ta kawai takeyi domin ta saba da halin Hajiya mai tuwo'



Yau kusan sati biyu da zuwan su Hajiya Wanda yayi daidai da tafiyar Abdullah A zaune suke a cikin katon falon Ruman na kwance a langwabe haka kawai batajin dad'in jikinta wani iri yakeyi mata gashi bakinta Sam baya mata wani dad'i,


Ga muguwar kewar Abdullah dake damun ta yaki bari suyi waya saidai kullum ya turo mata da text msg fiyeda sau goma a rana a yanzu ne takejin mugun sonshi na kara shigar ta wani irin kewar shi ke damunta Hajiya kanta taga rashin wal walarta



" Karar wayarta yasa ta duba domin tasan ko waye zai kirata gashi tana cikin matukar bukatar ganin shi a yanzu,


Mikewa tayi ta nufi daki kafin ta fada gado tayi received " A jiyar zuciya suka sauke a tare " Baby ina hanya ke warki zata kasheni I can't keep myself away from you anymore zanzo ayi mai yuwuwa nasan Hajiya na nan,


"Baby ina sonki sosai bazan iya Rayuwa bake ba dakyar nake iya bacci daren jiya kuwa ban runtsa ba saboda ke warki da kuma tunanin ki


" nasan dinkin mu ya warke ko? Ki shirya mun a yunwa ce zanzofa "aa Abdullah a Gaskiya bazan kuma y'ar da wani Abu ya shiga tsakanin mu ba kasan fa babban laifine wannan muka aika ta


" Abdullah ina kiran Kaina babba a she ni nafi kowa kuruciya domin nasan nice nabaka gudun mawar da har ka aika tamun a binda muka aikatan don haka banason hakan ya kuma faruwa saida igiyar Aure akan mu,


Murmushi yayi mai kayatar wa "kin yarda zaki yi Rayuwar Aure dani Ruman?

" kin y'arda cewar ni zan Isar miki? Kin Amince nine zan iya baki kulawar da kikafi bukata?


"Eh Abdul na gane KUSKURE NA nakin Amince maka tun farko da hakan bai faru ba


" Ruman kina sona? "Eh Abdul soyayyar da nake maka ta hanani ganin laifin Abinda Kayimin ka dawo na shirya fada ma kowa ina sonka,


" wani irin ihun murna ya sanya tareda farin ciki' nagode sosai Ruman bakisan irin farin cikin da kika jefani ba " I love you so much ki jirani nan da thirty minit zan shigo UK,



"Wani irin farin ciki ke bayyana a kan fuskar ta ta mike tareda kallon kanta a madubi domin ita tana mamakin matukar canja war ta


Kullum Hajiya tanbayar ta takeyi " Ummu wannan cika da kikeyi duk zaman wuri daya ne ya janyo ko ?


Ita bata taba lura da muguwar canjawar da tayi ba sai yau komai nata ya kara cikowa musamman kirjinta da sukayi fam fam dasu itama tafara y'ar da da canjin muhalli ne da kuma Hutu da yake ratsata,



Fitowa tayi falon cikin wal wala" aa Albishir aka yimiki da zuwa makka wannan fara'ar da nake gani a fuskar ki tun safe ban ganta ba sai yanzu,


"Ba komai kawai canjin yanayi ne'


Bayan minti goma ta tsinci kanta da son yin wanka ta shirya cikin tsantsar ar riyar kwalliya wata doguwar Riga mai tsagu tundaga kasa har zuwa kwabrin ta ta sanya tight a ciki mai shara shara ga rigar

Please Login or Register in order to submit comment